DAGA
DANO BALARABE BUNZA
SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA
JAMI’AR USMANU ƊANFODIYO, SAKKWATO.
Email: danobunza@yahoo.com
Phone number: 07035141980
Tsakure
Waƙoƙin bakan Hausa na ɗauke da turaku
daban-daban, wasu na ɗauke da yabo a inda ake
samun wasu ƙumshe da habaici da zambo
da ire-irensu da dama. Wannan takarda ta ƙunshi
nazari tare da sharhin waƙar Ɗanƙwairon
Biu a kan jigo da salo wadda ya yi wa Doctor Bukar Usman Biu. An tattauna
abubuwa masu dama da suka haɗa da ma’anar
kalmar amali da kirarin amali. Abin da ya biyo baya shi ne, an nazarci turakun
da ke cikin waƙar da suka shafi yabo da
ilimi da halayen kirki irin mutunci da riƙon
amana da taimakon jama’a da kuma kyauta. Biye da wannan kuma shi ne nazarin
salailan da suka fito cikin wannan waƙa
da aka yi nazari da suka haɗa da salon kamance. An
sami kamancen fifiko da salon kinaya da kuma na kambamawa. A ƙarshe kuma, an rufe takardar da kammalawa.
1.0 GABATARWA
Masana da manazarta adabin Hausa musamman na fannin rubuttun
waƙoƙi da na baka sun daɗe
suna bayar da gudummuwa ta hanyar nazarin waƙoƙi daban-daban. Sun sha gudanar da nazarce
nazarce, kan jigo da salo da kuma zubi da tsarin waƙoƙin Hausa da marubuta suka
rubuta da kuma waɗanda makaɗa
suka rera. Waɗansu kuma kan sami wasu abubuwan da waɗannan
su yi nazarin su Maƙasudin nazarin kowace waƙa shi ne fitowa da abin da ake buƙata a wannan ɓangare.
Nazarin waƙa ba karamin aiki ba ne
saboda manazarta na matuƙar burge makaɗa
da marubuta kam ganin yadda suka tona asirin abubuwan da suke faɗa
da ba su tsammanin a fahimta, idan aka warware zare da abawa, sai mamakin yin
hakan ya kama su tare da sanya su a cikin gulbin tunanin yadda aka yi
manazartan suka gano haka ba tare da sun tambaya an gaya musu ba. Abin da ya
kawo wannan shi ne, baiwar da Allah ya yi wa al’umma mai yawa ce, kuma kowa da
irin baiwar da aka yi masa. wasu masana an hore musu baiwar nazarin rubuttun waƙoƙi, wasu kuma an azurta su
da baiwar nazarin na baka. kamar yadda Bahaushe ya ce, “Buƙatar dara a kasa”. Ke nan, kowane fanni na
da ƙwararrin sa. A kan haka ne aka sami ɗaliban
waɗannan
masana suna koyi da abin da aka koyar da su a ɓangarorin
da aka ambata a sama, suna rawa da bazar malamansu. Wannan ne ya sanya da aka ƙyallaro waƙar
da Ɗankwararor Biu ya yi wa Dokta Bukar Usman Biu,
sai aka aza ta a sikelin nazari gwargwadon hali.
2.0 MA’ANAR KALMAR AMALI
Asali kalmar ‘amali” ba Bahaushiya ba ce, Balarabiyar kalma
ce da ake kira ‘Amal; Da Bahaushe ya are ta sai ya yi mata ƙarin wasalin i ta koma ‘Amali’
yadda zai ji daɗin faɗar
ta. Kalmar ‘amal’ na nufin aiki a cikin
harshen Larabci . Su kuma Hausawa suka ɗauke ta suna amfani da
ita a matsayin mai yin aiki. A Larabci kalmar amal na matsayin aiki (verb), a
inda a Hausa take matsayin ma’aikaci, wato subject da
Turanci. Idan aka ce amali a Hausa, ana nufin raƙumin
da yake gwarzo ko mai juriyar aiki fiye da sauran raƙuma. Wannan ne dalilin da ya sa aka ba gwarzon raƙumi sunan amali. Sai dai waɗansu
kan kira shi amale, wanda yake duk abu ɗaya ake nufi.
Akwai wasu ma’anoni biyu da aka kalato daga wasu ƙamusan Hausa da suka ba da ma\anar kalmar
amali/amale kamar haka: ƙamusun Bayero University
Kano ya tayar da ma’anar kalmar haka:-
Amaale: Su, nj. Mc-amaliya. Jam-amaalai riƙaƙƙen mahaukacin raƙumi,
kirari, wani kaya sai amale, wace Ayagi mai ɗan doro? (pg:15).
A ƙamusun Bargesry kuwa, ga
abin da aka ce: A.M Fem. Amaliya, plural amalai of ahoda; 1. (a) A full.grown
Camel (-amali) (b) Salutation to a Madaki 2.Full-grown donkey 3. Largest of the
three trings of instrument called molo .
A ma’anar ƙamasun Jami’ar
Bayero, Kano amale har ya kai a kira shi mahaukaci domin ƙosawarsa. Idan aka dubi ma’anar
ƙamusu na biyu kuma, za a tarar duk abu ɗaya
ake nufi da ma’anar Kamansun farko da aka ambata. (A Full-grown camel).
2.1 KIRARIN AMALE/AMALI
Ba amale kaɗai ke da kirarin a cikin
dabbobin gida ba. Akwai dabbobin da ke da kirarin da ake yi musu na gida da na
daji. Jaki da kare da sa da rago da akuya na da kirarin da ake yi musu
kasancewar su dabobin gida. Idan aka yi zancen kirari, dabbobin daji ma ba a bar
su a baya ba.
Ba da nisa ba, akwai kirarin da ke cikin kamusun Hausa na
Jami’ar Bayero a daidai shafi na 15 inda aka ce kirarin amale shi ne:-
‘Wani kaya sai amale, wace Ayagi mai ɗan
doro?”.
Bayan wannan kuma, akwai wani kirarin da aka yi wa amale inda
ake cewa:-
Amale ka fi gayya aiki:- Ma’anar da wannan kirari ke nunawa
ita ce, aikin da amalen raƙumi ke yi ya fi wanda
taron mutane za su yi. Abin da yake gaskiya cikin wannan magana shi ne, amalen
raƙumi na iya fara aiki tun fitowar rana har zuwa faɗuwarta
ba tare da yin raki ko nuna kasawa ba. Ita kuma gayya, ba yadda za a yi a fara
ta, ba a kare ba ko a daina aiki ba har faɗuwar rana.
Akwai kirarin amali a cikin wata takardar Aminu 2012, da yake
kirarin amale ya shafi madugun da ke tare da shi, shi ma na madugu ya shafi
amale. Ga kirare-kiraren kamar haka: -
“Wada nika dubin masu biyar raƙumma,
Kamar kwatancin soja,
Don kullum cikin shiri suka kwana,
Makiyayin amali ba shi da kwana,
Makiyayin amali ba shi da hutu,
Makiyayin amali ba shi tsoron yaƙi,
Ko da bindigogi aka yi,
Maza ana son sayen amali,
Wai mutuwa aka tsoro,
Na tambaye ku shin dai jama’a,
Kwam mace cikin duniyag ga,
Halama raƙumi yac ci shi?
Ai mutuwa ko kan gado tana iske mutum”.
Mai yin wannan kirari shi ne Illon Geza, sananne a fagen yi
wa maduggai kirari tare da rakumman da suke tu’ammali da su. Ga wani kirari
kamar haka:-
“Jaji so nikai in ji amali shina hidda ƙoƙiya shina ɗibga
cida, ya ɗora hiƙar
hauru, ya ɗora hidda kunfan baki.
Rannan ko ka ci magani ɗari kana katse mai,
Maza kowas sai amali ya sai mutuwa,
Matar mai amali ba ta nesa ga wanka,
Maganin amali Allag gyara,
Allah shi kiyaye ‘yan maza ga bakin mugu”.
Haka kuma kirare-kiraren amali bai tsaya a nan ba kurum.
Akwai su da dama sai dai a kawo kaɗan don kar misalan su yi
yawa.
Ga wani kirari da aka yi wa amali:
‘Garagiji fataken Allah,
Masu gardama suna maikaiwa,
Ku ka sa ma’auniya ta yi guɗa,
Kwanon tsaba ko shina sule shi komo ahu,
Maza majaya amali ko da kwanan hwarin’.
‘Masu biyar raƙumma,
A ba da mugun sassaƙe
ida turewa,
Kyawon mahaukaci ya ida turewa,
In dai ɗaki na ruwa, awaki ka hwaɗi,
Ko an rufe ɗaki da mahaukaci ana buɗewa’.
‘Ina masu cewa,
Rikon amali ba duk magani ba ne, sabo ne?
Ai da rakumi da damisa da kura da kada,
kowa kag ga sun bari tsarin Allah na’.
3.0 NAZARI DA SHARHIN JICO DA SALON WAƙAR ƊANƙWAIRON
BIU TA DOKTA BUKAR USMAN BIU.
Makaɗa da mawaƙan Hausa na matuƙar
ƙoƙari domin ganin sun yabi
waɗanda
suke buƙatar yi wa hakanan ta fuskar asali da kyauta da
iya gudanar da mulki da ilmin da Allah ya azurta wani da shi da abubuwan da
suka yi kama da haka. Alal haƙiƙa an sami makaɗi mai suna Umar Idris
(Danƙwairon Biu) ya yi wa Dokta Bukar Usman Biu waƙa tare da yaba shi ta fuskoki da dama. Za a dubi
fuskokin da makaɗin ya yabi wannan bawan
Allah a cikin nazarin wannan waƙa tare da yin sharhin
abubuwan da aka gabatar. Da farko, za a ɗauki jigon wannan waƙar ya zama soma-taɓi
kafin abubuwan da za su biyo a baya. Ga yadda nazarin waƙar zai kasance:-
3.1 TURKEN WAƙAR:
Hausawa na cewa, “Nashin ƙasa,
babu kure”:. Masana sun bayyana cewa duk waƙar da aka yi, rubutacciya ce ko ta baka, ko ana
rasa komi a cikinta dole ne a same ta da muhimmin saƙon da aka gina ta a kansa. Ana kiran saƙon jigo a rubuttun waƙoƙin Hausa, a inda sunan
yake turke a waƙoƙin baka na makaɗan gargajiya. Waƙar da ake nazari a nan na ɗauke
da babban turken yabo. Sai kuma saƙon
ya kasu daban-daban kamar yadda nazarin zai nuna. Ga al’ada
waƙar baka na tare da amshi wanda ita ma wannan waƙar da Ɗanƙwairon Biu ya yi wa Dokta Bukar Usman Biu tana
tare da wannan amshi daga bakin yaran makaɗin.
3.1.1 TURKEN YABO A CIKIN WAƙAR DR. BUKAR USMAN
BIU
Soyayya ko kuma so a taƙaice
ke sanya makaɗi ya yabi wani ko wasu a cikin waƙarsa. Akan yi yabon da ba na gaskiya ba bale
wanda aka taki dahir? Hausawa sun ce “So hana ganin laifi”
Duk mai son ka da wanda kake so ba ku laifi ga junanku. Umar Idris (Danƙwairon Biu) ya nuna soyayya matuƙa ga Dr. Bukar Usman a cikin waƙarsa, da yake ɗiyan waƙoƙin da za a kawo ke
tabbatar da haka ba faɗa kawai ba. Idan aka dubi
amshin waƙar da makaɗin
ya ba yaransa, ya isa a gano cewa saƙon
waƙar yabo ne. Ga amshin waƙar kamar haka:
Dokta Bukar Usman Biu Jarumi,
Malaminmu kuma babanmu ne,
Mazan ƙwarai, ku bar kaura da
shi.
Da za a dubi kalmomin jarumi da malami da baba da mazan ƙwarai da aka ja wa layi a ƙarkashi, wannan kaɗai ya isa a fahimci mai
adawar mutum ko wanda ke kushe shi ba zai kira shi da su ba sai dai ya kira shi
da wasun waɗannan kalmomi domin abin ya koma suka. Kalmomin
suka da ke waƙiltar na yabon da aka ja
wa layi a sama su ne, raggo da jahili tare da faɗar babu haɗi
tsakanin kifi da kaska bale ma a kawo alaƙar
haihuwa da za a kira sunan baba. A maimakon mazan ƙwarai kuma akan iya amfani da mutumen banza duk
dai domin nuna akasin yabo, wato zagi. Wannan amshi da ke sama yabo ne na ƙoli a idon wanda aka yi wa shi da manazarta su
kansu. Saƙon wannan waƙa na ƙoli
shi ne yabo. Shi kuma yabo masana sun faɗi cewa ya kasu zuwa
gidaje da dama, kamar yadda za a gani cikin bayanan da ke tafe kamar haka:
3.1.2 ILIMI SUTURAR ALLAH
Ilimi na ɗaya daga cikin abubuwan
da ke ɗaga
darajar mutum a san shi kuma a ji shi ko’ina. Dokta Bukar Usman Biu na ɗaya
daga cikin waɗanda Allah Ya ɗaga darajarsu a fannin
ilimi. Za a zo da ɗiyan waƙan da suka tabbatar da haka nan gaba kaɗan.
Abu na farko da ke tabbatar da Bukar Usman ya sami ɗaukaka
a fannin ilimi shi ne matsayin (Dr.) da yake karɓawa
a halin yanzu. Ba mamaki a kira shi shehin malami nan gaba domin rabo daga
Allah ne.
Dr. Bukar Usman Biu ba kanwar lasa ba ne idan aka yi zancen
ilimi, kamar yadda wasu ɗiyan waƙa suka tabbatar. Bayan wannan ma mutane sun
tabbatar da haka domin abin a fili yake ba a fake ba, abin da Hausawa ke kira
filin wuri dabon ɗan kama. A taƙaice Dr. Bukar Usman ya rubuta littattafai sama
da ashirin. Daga cikin waɗanda suka bayyana akwai,
Taskar Tatsuniyoyi da na Turanci mai suna My Literary Journey da sauransu. Ga
waɗansu
ɗiyan
waƙa da ke tabbatar da Dr. Bukar Usman ma’ilmanci
ne kamar haka:
Gabar da yamma dama da hauni,
Nijeriya, ƙasashen Turai,
Sun san halinka ka san nasu,
Dokta Bukar Usman Biu,
Sun san ka ne dalilin ilimi.
Yau ga Ɗanƙwairon Biu,
Umar Idrisa a zahiri,
Dokta Bukar Usman Biu,
Umar ni na san da kai,
A zahiri fa kai ba ka san ni ba,
Ya zan dole na san da kai,
Tunda kai ka rubuta a san da kai.
Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu kuma babanmu ne,
Dokta mutunci naka ne,
Kuma kana da ilimin zamani.
Ina marubutan zamani?
Ku zo mu taru don ga malami,
Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu kuma babanmu ne,
Rimi mai faɗin gari,
Dokta Bukar Usman Biu,
Ka zama teku a fannin ilimi,
Dokta Bukar Usman Biu,
Ka riga su ka ce Allah,
Mai ilimin da babu iyaka,
Turawan duka duniya,
Su jinjina maka dole ne,
Giwa ba ta gudu don harbi,
Ka san Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu ne fa ta ko’ina,
Shi Dokta Bukar Usman Biu,
Yana aikinsa da ilimi,
Kuma yana aikinsa da hankali,
Wanda ya wuce a yi da lokaci.
Idan aka kula da ɗiyan waƙar da ke sama za a tabbatar da cewa Allah Ya yi
wa Bukar Usman suturar ilimi. A ɗan waƙa na farko da aka kawo, mawaƙin ya tabbatar wa jama’a
da cewa, duk kusuruwowi huɗu na duniya (Gabas,
Yamma, Kudu da Arewa) da gida Nijeriya da kuma ƙasashen
waje tattare da sanin halinsa da suka yi da kuma nasu da ya sani, ba abin da ya
haddasa hakan face ilimin da yake da shi. A hankalin tuwo ma, me ya dami Turawa
da baƙar fata in ba sha’anin ilimi ba? Ta yaya za
su san wani har a ce hulɗa ta shiga tsakani in ba
saboda ɗaukakar
ilimi ba? Sanin muhimmancin ilimi ne ya sanya Allah Ya yi umurni da a neme shi,
kuma Manzon Allah ya tabbatar da hakan a inda ya ce “Neman ilimi farilla ne ko
da ya kai birnin Sin”. Daga cikin hulɗar da aka samu tsakanin
Bukar Usman da mutanen ƙasashen waje akwai ta
ilimi. Ke nan, ilimi na cikin abubuwan da ke ɗaukaka darajar mutum har
a ji shi kuma a san shi nesa ba kusa ba, kamar yadda Allah Ya yi wa Bukar Usman
sutura da shi.
A ɗan waƙa na biyu da aka gabatar, makaɗin
na faɗar
cewa, shi ya san Dokta Bukar Usman, sai dai Bukar bai san shi ba. Ya ƙara da cewa ba dole ne Bukar ya san shi ba sai
dai shi ya san shi ne a tilas. Dalilinsa na faɗar haka kuwa shi ne cewar
da ya yi a ƙarshen ɗan
waƙar,
Tunda kai ka rubuta a san da kai.
Sanin kowa ne jahili ba ya rubutawa bale ya karanta. Sha’anin
rubutu da karatu na mai ilimi ne don haka, Allah Ya tufatar da Bukar Usman da
wannan tufa na ilimi har aka ji shi kuwa aka san shi ciki da wajen Nijeriya.
Ɗan waƙar da ke biye ma ya nuna
cewa bayan ilimin addini da Bukar ya tashi da shi an ƙara ɗaukaka darajarsa ta ba
shi ilimin zamani. Abin da ke ƙara tabbatar da wannan
shi ne rubuce-rubucen da ya yi. Ilimin rubutu babbar ɗaukaka
ce ga ɗan
Adam. Tabbacin haka kuwa shi ne, akwai masu buƙatar
su iya karatu da rubutu amma, kuma ba su sami hakan ba. Ashe duk wanda aka yi
wa baiwar iya karatu da rubutu, an ɗaukaka darajarsa ta
wannan fanni. A kan haka ba abin da ya rage wa Dokta Bukar Usman sai ƙara godiya ga Allah kan ni’imomin da aka yi masa.
maganar na cikin ɗan waƙar wurin da aka ce:
Dokta mutunci naka ne,
Kuma kana da ilimin zamani,
Kuma riƙon amana naka ne.
A ɗan waƙan da ke biye da na sama kuma, ya ƙara fitowa da darajar ilimi a fili inda makaɗin
ya nuna cewa:
Ku zo mu taru don ga malami,
Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu kuma babanmu ne.
A fahimtata wannan ɗan waƙa na iya fassara taron da aka yi don girmama
Dokta Bukar Usman sanadiyar littafin da ya rubuta na Taskar Tatsuniyoyi. Haka
kuma an sami marubuta da yawa da suka rubuta maƙalu
daban-daban kuma duk domin karrama Bukar Usman. An gudanar da wannan taro a
mazaunin Jami’ar Bayero ta Kano na dindindin. Haka kuma, duk wanda ya jiɓinci mai ilimi, zai amfana da iliminsa kamar
yadda ɗimbin
jama’a suka amfana da Bukar a cikin rubuce-rubucensa na ilimi.
A ƙarshen kuma, akwai ɗan
waƙan da makaɗin ya yabi Bukar Usman
inda ya nuna taska ne na ilimi da kowa ke amfana da shi dare da rana. Wannan ɗan
waƙar shi ne kamar haka:
Rimi mai faɗin gari,
Dokta Bukar Usman Biu,
Ka zama teku a fannin ilimi,
A gaishe ka na Dokta Shema,
Dokta Shema na fannin magani.
Idan aka yi zancen ilimi Dokta Bukar Usman rumbu ne sha ɗiba.
Za a fahimci haka tare da aminta idan aka yi la’akari da taron karramawar da
aka yi masa a Kano. Da wuyar gaske ake samun wanda ya rubuta takarda a wannan
taro da bai sanya littafin Taskar Tatsuniyoyi a manazartarsa ba. Ke nan kowa ya
amfana da ilimin Dokta Bukar . Wannan ne dalilin makaɗin
a kan cewa Bukar Usman Biu ya zama teku a fannin ilimi.
3.1.3 NAGARI NA KOWA, MUGU SAI UWAR DA TA HAIFE
SHI
Ba shakka Hausawa sun faɗi gaskiya a kan faɗar
wannan magana. Duk mutumin da ke da kirki za a ga koyaushe yana tare da jama’a.
Shi kuma maras kirki koyaushe neman jama’a yake yi suna nisantar sa. Dokta
Bukar Usman Biu mutum ne mai son jama’a tare da taimaka musu iya gwargwado. A
halin yanzu shi kansa bai san iya jama’an da yake hulɗa
da su ba kuma ba wanda zai gaya ma adadinsu. A ƙarƙashin wannan za a dubi abubuwan da suka haɗa
da:
3.1.3.1 Halayen Kirki
Bukar Usman Biu mutum ne mai kirki matuƙa. An ga haka tsakaninsa da mutane daban-daban na
gida da waje. Halayen kirkin da Bukar Usman ya mallaka masu yawa ne. Daga cikin
halayen kirkin da makaɗin ya kawo na Dr. Bukar
Usman akwai, mutunci da riƙon amana da taimakon al’umma
da kyauta da aiki da ilimi kuma ga hankali da sauran kyawawan halayen da wannan
takarda ba za ta iya ƙunsa ba, domin ba dukkan
halayensa na kirki makaɗin ya sani ba. Ya dai faɗi
waɗanda
suka sami shiga cikin waƙar domin ba a zube komi a
lokaci ɗaya.
Ga yadda makaɗin ya kawo halayen Bukar Usman a cikin ɗiyan
waƙar:
3.1.3.2 MUTUNCI
A lokacin da Ɗanƙwairon Biu ke lissafo halayen Dr. Bukar Usman Biu
na ƙwarai ga abin da ya ce dangane da mutunci:
Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu kuma babbanmu ne,
Dokta mutunci naka ne,
Kuma kana da ilimin zamani.
Dangane da wannan hali na mutunci ana ji daga masu hulɗa
da shi cewa, mutum ne mai karimci ƙwarai
da gaske. Yana girmama jama’a yadda ya kamata, har ma
idan ba ka san shi ba, aka nuna maka shi, za ka ji mamakin yadda yake karrama
mutane su ma suna girmama shi.
3.1.3.3 RIƙON AMANA
Hausawa sun ce; “Riƙon
amana sai ɗa”. A nan, ba kowane ɗa
ne ake nufi ba. An san duk wanda aka haifa namiji, ɗa
ne. Haka kuma ba irin kasancewa ɗa kamar shayi ɗan
gidan Labbo ba wanda Kassu Zurmi ya kawo a cikin waƙarsa. Abin da ake nufi a nan shi ne ɗan
da ya kasance son kowa, ƙin wanda ya rasa. Idan
aka ce son kowa ƙin wanda ya rasa, ana
nufin mutumin da ke da alheri a cikin rayuwarsa zuwa ga mutane tare da nisantar
su da sharri komin ƙanƙantar sa. Dokta Bukar Usman Biu ya kasance son
kowa ƙin wanda ya rasa musamman idan aka yi la’akari da
hulɗar
da ke tsakaninsa da jama’a. Za a tabbatar da haka idan aka yi la’akari da abin
da makaɗinsa
ya faɗa
a wani ɗan
waƙarsa. Ba shakka duk wanda aka samu da riƙon amana ne halinsa, to tabbas ya zama ɗa
irin wanda Hausawa ke nufi a wannan hauji. Ga abin da Ɗanƙwairon
Biu ya ce:
Dakta mutunci naka ne,
Kuma kana da ilimin zamani,
Kuma riƙon amana naka ne,
Hadari kashe kaifin rana,
Birni da ƙauye ba ka da zallumi.
Layin da aka ja wa layi ƙarƙashinsa ne abin yin la’akari
dangane da riƙon amanar da ake bayani
na Dokta Bukar Usman Biu. A nan za a iya cewa, Bukar Usman ya san amana, ya san
muhimmancinta, ya san munin rashin yin ta, shi ya sa ya zaɓi ya kasance mai riƙon
ta tsakaninsa da Allah da kuma kiyaye wadda ke tsakaninsa da jama’a.
A nan, makaɗin na sanar da jama’a cewa Dokta Bukar Usman
dattijo ne a ɓangaren amana, riƙon ta da kuma bayar da ita, musamman waɗanda
ba su san shi ba.
3.1.3.4 TAIMAKON JAMA’A
Taimakon al’umma na cikin kyawawan halayen Dokta Bukar Usman
Biu da aka shede shi da su tun kafin makaɗin ya faɗa.
Sai dai ba abu ne da za a fito a faɗa a rubuce ba kurum, har
sai wani sanadi ya faru irin wannan waƙar
da aka yi masa, sai kuwa idan an sami yin hira da wani mutum a cikin kafafen yaɗa
labarai kan halayensa. Da yake abin da waƙar
Ɗanƙwairon
Biu ta ƙunsa aka magana ga abin da ya sami faɗa
dangane da taimakon al’umma:
Dokta Bukar Usman Biu,
Kana da taimako fa ta ko’ina,
A ƙasar nan duk an san da
kai,
Baba da ku aka damawa gida,
Kuma da ku aka damawa waje.
Ba shakka ga maganar da aka faɗa ta cewa Bukar Usman na
da halin taimaka wa al’umma, domin ga shi nan a fili makaɗin
ya kawo a cikin ɗan waƙa na sama. A layuka biyu da aka ja wa layi makaɗin
ya tabbatar da Dokta Bukar Usman Biu na da taimakon jama’a
kuma ta ko’ina. Kalmar ko’ina da makaɗin
ya yi amfani da ita na nuna duk inda mutum ke tunanin taimakon da yake yi ya
kai, to ya hurce nan. Saboda yawan taimakon da Bukar ke yi wa jama’a
ya sa makaɗin ya ƙara
fayyace ma jama’a da cewa, an san da haka
a ƙasa baki ɗaya a cikin layi na biyu
da aka ja wa layi. Halin da ake ciki ni ma ina matsayin sheda a kan wannan
maganar cewa yana da taimato ta ko’ina. A taron da aka yi a ƙasar Nijar na karrama Marigayi Farfesa Muhammadu
Hambali Jinju a ranar 19th – 21st February, 2014 a
garin Niamey a ɗakin taro na Salle Sani
Baƙo, ministere des Affaires etrangeres Niamey, ya
taimaka ya biya wa duk mai gabatar da takarda kuɗin rajista naira dubi
biyar. Saboda wannan taimako da ya yi ya sa wani ya nemi a gwada wa jama’a
Dokta Bukar Usman Biu, a inda aka nemi ya tashi tsaye domin kowa ya gan shi,
kuma haka aka yi. Ba wannan taro kaɗai ba, a taron da aka yi
na Nigerian Folklore Society a Jami’ar Bayero Kano, taro na 11 da aka yi a
ranar 2-4 ga Afrilu, 2014, Bukar Usman Biu ya ba da kyautar littafinsa mai suna
‘Taskar Tatsuniyoyi” ga kowane mahalarcin taro day a gabatar da takarda. Ba da
kyautar littafin taimako ne babba ga kowane mutum domin na tabbatar ba ni kaɗai
na ji daɗin
wannan taimako da ya yi ba. Idan aka yi la’akari da waɗannan
abubuwa da aka kawo a sama zancen taimakon jama’a ba sai an nanata ba da Dokta
Bukar Usman Biu ke yi. Allah Ya saka da alheri.
3.1.3.5 KYAUTA
Yin kyauta na daga cikin halayen kirki da aka yi bayani, har
a addinin Musulunci. Abin da duk ya dace a faɗa dangane da halin Bukar
Usman da ya shafi kyauta an faɗa a sama, sai dai a ƙara. Ba dogon bayani za a yi ba na abin da ya
shafi kyautar da Dr. Bukar ke yi. Akwai daga cikin wani ɗan
waƙa da makaɗin ke cewa:
Hadari kashe kaifin rana,
Birni da ƙauye ba ka da zallumi,
Balbela ki bi saniya,
In kin bi kare me za ki ci?
Hausawa sun ce, “Nuni ya ishi mai hankali”. Ita dai balbela
sanannar tsuntsuwa ce da ke kiwo cikin shanu domin samun abinci. Haka kuma ba
ta da wata alaƙa da kare bale ta bi shi
don neman abinci. Idan ma ta bi shi, wahalar banza ce take yi ba samu za ta yi
ba. Hasali ma idan ba ta ci sa’a ba, ita za ta zama
abinci ga wani kare ba maganar ta samu abincin ba. A taƙaice wannan nuni ne na cewa, Bukar Usman mai
kyauta ne ga na bayansa da na tare da shi,wanda ya sani da ma wanda bai sani
ba.Jama’a na amfana da wannan bawan Allah matuƙa, kamar yadda balbela ke kama fari da ƙwari a lokacin da take tare da shanu a daji wurin
kiwo.
4.0 SALO A CIKIN WAƙAR BUKAR USMAN BIU TA UMAR
IDRIS (ƊANƙWAIRON BIU)
Masana sun bayyana ma’anar salo a cikin rubuce-rubucensu da
suka yi. Za a kawo ma’anar da Abdullahi Bayero Yahya ya bayar kamar haka:
“Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar
zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar”.
Daga bayanin ma’anar da ke sama za a fahinci salo hanya ce ko
dabara ko wayo da marubuci ke bi domin isar da saƙon
da ke cikin rubutunsa, ko maganarsa ko waƙarsa
ta baka. Akwai wasu salailai da suka fito a cikin waƙar Dokta Bukar Usman Biu wadda Umar Idris ya yi
masa kamar haka:
4.1 SALON KAMANCE
Salon kamance ɓangare
ne na babban salon siffantawa. Salo ne wanda ke bayyana sifar wani abu ta
fuskar kwatanta shi da wani abu daban tare da amfani da kalmomin da za mu ba
suna mizani. Salon kamance zai siffanta mutum da cewa ya yi kama da wani abu
amma ba shi ne abin ba. Salon kamance kamar wada muka ambata yakan yi amfani da
kalmomin da muka kira mizani. Kalmomin kuwa sun kasu gida uku akwai na
daidaito, akwai na fifiko sannan akwai na kasawa. Kalmomin mizani su ke yi mana
jagora wajen gane salon kamance a cikin waƙa.
Saboda haka bari mu kawo misalai na kowane rukunin mizani:
1. Mizanin daidaito: Awa, kamar, wa, i, ƙoƙa, ya, ce kake da kuma
daidai da.
2. Mizanin fifiko: Wuce, zarce, fi, take, gota, furce, tsere,
da kuma ɗara.
3. Mizanin kasawa: Kasa, gaza, wane da kuma kalmomin masu
soke samuwa kamar bai..... ba.
4.1.1 KAMANCEN FIFIKO
Ɗanƙwairon Biu ya yi amfani
da salon kamancen fifiko a cikin waƙar
da ya yi wa Bukar Usman Biu. Ya yi amfani da wannan salo domin nuna irin ratar
da ke tsakanin Bukar Usman a matsayinsa na malami da kuma waɗanda
ke a matakin jahilai a inda ya ce:
Dokta Bukar Usman Biu,
Umar na zo domin in gai da kai,
Malami fa ka wuce jahili,
Wajen hali kana da tawakkali,
Allah Ya yi ma sutura,
Ga ƙarfi da arziki babban
rabo.
A layi na uku da ke cikin ɗan waƙan da aka kawo a sama inda makaɗin
ya gwama malami da jahili ta fuskar kamance, a inda kowa ya tabbatar da malami
ya fi jahili amfani ga jama’a ta kowace fuska. A
wannan wuri makaɗin ya kawo cewa akwai
bambanci mai yawa tsakanin masani da wanda bai san komi ba. An tabbatar da cewa
malami na a matsayin haske jahili kuma na a matsayin duhu kamar yadda aka
kamanta tsakanin shiriya da ɓata. Wannan ya yi daidai
da maganar masu tallar hajojinsu a kafafen yaɗa labarai inda suke gwama
nasu kaya da na wasu inda suke cewa: “The difference is clear” domin nuna nasu
kaya ya fi na saura, wato da gani ba tambaya. Irin wannan ne makaɗin
ke nunawa, har aka sami wannan salon kamancen fifiko.
4.1.2 SALON KINAYA
Kamar yadda aka sami kamancen fifiko a cikin wannan waƙa, haka ma akwai na kinaya a ciki. Kinaya na
nufin kiran abu, musamman mutum da sunan da ba shi ne nasa da aka san shi da
shi ba, domin wannan suna ya bayar da ma’anarsa da kuma tunanin da
wannan suna. Salo ne wanda ake yin amfani da kalma ko kalmomi domin tunanin da
suke sa mutum ya yi game da ma’anoninsu ya nashe ko ya
lulluɓe wani abu ko mutumin da aka danganta kalmomin
gare shi. A kan wannan bayani ne aka fahimci akwai wannan salo a cikin waƙar Dokta Bukar Usman Biu wadda Ɗanƙwairon
Biu ya yi masa. Za a ga hakan a cikin ɗiyan waƙar kamar haka:
Rimi mai faɗin gari,
Dokta Bukar Usman Biu,
Ka zama teku a fannin ilimi,
A gaishe ka na Doctor Shema,
Doctor Shema na fannin magani.
Ina Bukar Usman Biu?
Karo da kai maza suka shan wuya,
Gwanki sha bara na mai Umai,
Allahu Ya yi ma sutura,
Da ƙarfi da arziki babban
rabo.
Ina kada hana wanka?
Dokta Bukar Usman Biu,
Malami a fannin Adabi,
Alfijir Bukar Usman Biu,
Ka fito gari ya waye,
Mujaddadi ina masaninmu ne?
Hadari kashe kaifin rana.
Duk kalmomin da aka ja wa layi ƙarƙashi kinaya ce aka yi zuwa ga Dokta Bukar Usman
Biu. Haka kuma kowace kalma na ɗauke da wata ma’anar
da makaɗin
ke nufi. Akwai kalmar Rimi da Teku da Gwanki da Kada da Alfijir da kuma
Mujaddadi da kuma hadari.
Rimi sunan gari ne da makaɗin ya kira Bukar Usman da
shi saboda yawan garin. A nan yana nufin yadda garin Rimi ke da yawa haka
ilimin Bukar Usman ya yawaita. Ya ƙara
bayyana ilimin Bukar Usman da cewa ai Bukar Usman ya zama teku a fannin ilimi.
Yadda ba a san iyakar teku ba haka ma ba a san iyakar ilimin Dr. Bukar ba. A
wani ɗan
waƙar kuma makaɗin ya kira Bukar Usman da
sunan gwanki. Gwanki a nan dabba ne kuma sananne a cikin dawa. Ko a bayanin
masana kaɗai aka tsaya na ma’anar kinaya, cewa kiran
wani mutum da sunan da ba nasa ba, ya isa ya zama hujjar cewa kinaya ce.
A wurin da aka kira Bukar Usman kada kuwa, makaɗin
na nufin yadda kada yake babba a ruwa haka Bukar yake a lamurran da suka shafi
jama’a a matsayin babba wanda Allah Ya ɗaukaka sosai. Kalmar
alfijir kuma a nan an yi amfani da ita domin a nuna duk wurin da Dr. Bukar yake
yana tare da jama’a domin da safiya ta waye mutane fitowa suke yi domin
hidimominsu na rana. Kalmar mujaddadi a nan na nufin mai ƙarfafa wani abu. A fahimtar manazarta Bukar Usman
mujaddadi ne a fannin adabi kuma ba za a musanta haka ba. Haka ma kiran da ya
yi wa Bukar Usman da sunan hadari a wani wuri. Ko ba komi wannan kirarin hadari
ne da ake yi masa da cewa: “Hadari mai kashe hasken rana”. A nan makaɗin
na nufin Dr. Bukar Usman Biu na da ficen day a kai idan yana cikin jama’a ya fi
fice idan aka yi zancen halayen kirki da ƙwarjini
ga jama’a.
4.1.3 SALON KAMBAMAWA
Masana sun ce, idan mawaƙi
ya yi zuƙu cikin magana, wato ya ƙara mata gishiri, a taƙaice ya bayyana abu fiye da yadda yake a haƙiƙani, za mu ce wannan mawaƙi ya yi amfani da salon kambamawa. Akwai irin
wannan salo a cikin waƙar da Ɗanƙwairon
Biu ya yi wa Dokta Bukar Usman Biu a wurin da ya kawo kamar haka:
Dokta Bukar Usman Biu,
Kai ka riga su ka ce Allah,
Mai ilimin da babu iyaka,
Turawan duka duniya,
Su jinjina maka dole ne.
- - - -
- - - -
A sha’anin nazari da sharhin waƙa
wannan ɗan
waƙa da aka kawo duk layukan da aka ja wa layi
kambamawa ce makaɗin ke yi wa Bukar Usman.
Ga alama, idan abin a yi wa makaɗi gyara ne, ko Bukar
Usman na iya faɗa wa makaɗin
cewa ya yi ƙarin gishiri ga abin da
ya faɗa.
Duk da yake shi makaɗi ya dai sami buƙatarsa ta biya, wanda ana kyautata zaton ta ma
biyan.
5.0 KAMMALAWA
Waƙa ce ƙololuwar tunanin ɗan Adam kuma a cikin ta
ne mawaƙa ke ɓarje
guminsu domin su yabi wanda suke ra’ayi kuma su kushe abokan
gwada tsawo da masu gidajensu ko su kansu. A cikin wannan takarda, makaɗa
Umar Idris (Ɗanƙwairon Biu) ne ya yi yabo da gaisuwar ban girma
ga maigidansa Dokta Bukar Usman Biu. Na ce maigidansa saboda a bakinsa na
tsinta a wurin da yake cewa:
Dokta Bukar Usman Biu,
Baba ni kai ne fa gwanina,
Gwanin wani ba gwanina ba ne,
Amma nawa gwani kuma,
Shi ne Dokta Bukar Usman Biu,
Dokta ga Umar Ɗanƙwairo,
ƙwairon Biu na wannan zamani.
Umar Idris ya ɗaga Dokta Bukar Usman Biu
da hannu biyu a sama ya nuna wa jama’a tare da bayyana ɗaukakar
da Allah Ya yi masa a ɓangarorin rayuwa
daban-daban. Ya yaba shi a fagen ilimi a inda ya kira shi malami kuma marubucin
da ya yi fice a fannin Adabi. Haka ya bayyana halayensa na kirki masu yawa.
Kai! Umar ya faɗi alkhairori masu yawa da
Bukar Usman ke yi sai abin da mantuwa ta hana a faɗa.
Da yake baƙin ciki ba baƙon uwar ɓarawo
ba ne, an sami wasu salailai kaɗan a cikin waƙar kuma aka nazarce su, domin ba yadda za a yi waƙa ba tare da an tsinci wani salo a ciki ba. Idan
ma aka rasa salo a cikin waƙa, to ba waƙa ba ce. Ai maganar da Hausawa suka yi ce cewa ‘Gaskiyar
biki jariri’. Idan babu jariri, babu buki. Don haka idan babu salo an
rasa waƙa.
Dokta Bukar Usman Biu jarumi ne kamar yadda Ɗanƙwairon
Biu ya faɗa. A ra’ayina na ɗalibin
nazarin waƙa na ga ya fi dacewa Umar
Idris ya mayar da laƙabinsa Ɗanƙwairon
Dokta Bukar Usman Biu, mamakon Ɗanƙwairon Biu. Dalilina a nan shi ne, da wuyar gaske
ya yi wa wani waƙar da ta kai ta Dokta
Bukar Usman bale ma ta hurce ta. Shi kuma Dr. Ya riƙi makaɗinsa matsayin yaro kamar
yadda ya riƙe shi maigida. Hausawa
sun ce “Soyayya ta fi kuɗi”.
Shi kuma Sani Sabulu na kanoma cewa ya yi “ƙauna ba ta ganin wahala Sani”.
Wannan ya faru ne a inda yake nuna hulɗarsa da mutanen ƙauye. Haka kuma kowane birni da zama ƙauye ya fara. Kowa ke ganin tausayi ya kasance
lokacin da ake tausan sa.
Karanta wannan
MANAZARTA
Alƙur’ani
Mai girma da Hadisin Manzon Allah S.A.W. da suka yi bayani kan neman ilimi
Abba & Zulyadaini (2000), Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Gaskiya
Corporation Ltd, Zaria.
Aminu N. (2012), “Nazarin Kirarin Madugan Raƙuna na Ilon Gezo” In
Dunɗaye Journal of Hausa
Studies, Department of Nigerian Languages, UDU, Sokoto vol.1 No. 4 pg 154-174.
Bargery, G.P. (1933), A Hausa-English Dictionary and
English-Hausa
Vocabulary, A.B.U. Press Ltd Zaria-Nigeria.
D. Muhammed (1990), Hausa Metalanguage (ƙamus na keɓaɓɓun
Kalmomi). Volume 1, University Press Limited, Ibadan.
Dangambo A. (2007), Ɗaurayar
Gadon Feɗe
Waƙa (Sabon Tsari) Amana
Publishers Ltd New Kano Road. P.O. Box 1265, Zaria, Kaduna-
Nigeria.
Gusau S.M. (1996), Makaɗa da Mawaƙan Hausa Benchmark Publishers
Limited, Kano-Nigeria.
Gusau S.M. (2008), Waƙoƙin Baka A ƙasar
Hausa: Yanayi-Yanayensu da
Sigoginsu. Benchmark Publishers Limited, Kano-Nigeria.
Gusau S.M. (2009), Diwanin Waƙoƙin Baka (Zaɓaɓɓun Matanoni na
waƙoƙin Baka na Hausa), Century Research and
Publishing Limited, Kano-Nigeria.
Jami’ar Bayero Kano, (2007), ƙamusun
Hausa, Cibiyar Nazarin Harzunan
Nijeriya, B.U.K.
Sarɓi S.A. (2007), Nazarin Waƙen Hausa, Samarib Publishers, A Division
of Samarib Ventures Ltd.
Yahya A.B. (2001), Salo Asirin Waƙa, Sisbas Media Services Kaduna.
Yahya A.B. (1997), Jagoran Nazarin Waƙa. Fisbas Media Service, Kaduna.
Yakasai, S. A. (2012), Jagoran Ilimin Walwalar Harshe,
GARKUWA Media Services, Kaduna.
WAƊABDA AKA YI HIRA DA SU
Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, 2014.
Farfesa sAlisu Ahmaed Yakasai na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, 2014.
ABIN DA AKA SAURARA
Kaset na rakoda mai ɗauke da waƙar Dr. Bukar Usman Biu ta Umar Idris Ɗanƙwairon
Biu, 2014
3 Comments
Ina son abani email ne ɗalibi daga A.b.u zaria
ReplyDeleteZa ka iya yin amfani da d'aya daga cikin wad'annan:
ReplyDeleteabuubaidasani5@gmail.com
amsoshi2017@gmail.com
Mun gode.
[…] Ka/kin taba karanta wannan? […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.