HAUSAR ‘YAN SIYASA A AREWACIN NIJERIYA (BABI NA ‘DAYA)

KUNDIN BINCIKEN NEMAN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) WANDA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO.

ASHIRU USMAN GABASAWA
ADM.NO:1110106129

SATUMBA, 2016

BABI NA ‘DAYA
1.0 Gabatarwa

Akan ce harshe shi ne mutum haka yake, domin kuwa sai da magana mutum ke kammala. Sadarwa muhimmiyar aba ce ga rayuwar ‘yan Adam domin kuwa ta shafi dukkanin mu’amular al’umma na duniya. Musamman da yake ana samun hulɗa tsakanin wasu harsuna daban-daban masana kimiyyar harshe sun tabbatar da cewa, harshe ba ya ci gaba sai da aron kalmomi daga wasu harsuna tare da ƙirƙirar sababbin kalmomi waɗanda za su bunƙasa rumbun kalmominsa.
Don haka, duk wani harshe mai son ci gaba ko wata al’umma masu son harshenta ya bunƙasa, to dole ta riƙa aron da ƙirƙirar sababbin kalmomi da za su cike giƂin da harshen ke fuskanta ta fuskar kayyayakin da zamani ya shigo da su. Ta haka ne waɗannan harsuna, ko kuma duk wata alummar da suke hulɗa za su bunƙasa. Da wannan gabatarwar ce binciken zai yi nazari a kan Hausar yan siyasa a Arewacin Najeriya, wato irin aron da ƙirƙirrarrun kalmomin da wannan rukuni na yan siyasa ke amfani da su a cikin alummar arewacin ƙasar nan cikin harshen Hausa. Domin fito da wannan karin harshen fili musamman saboda ganin yadda yake tashe a wannan lokacin siyasa. Don cimma wannan ƙuduri, binciken har ila yau zai yi ƙoƙarin tattaro zantukan yan siyasa domin fashin baƙin maanonin su ta yadda duk wanda ba ɗan wannan rukuni ba zai fahimci irin wainar da ake tonawa.

1.1 Manufar Bincike


Tabbas duk abin da mutum zai yi lallai dole ya kasance yana da manufar yin sa. Wato duk wani abu da mutum zai ƙudirci yin sa, kafin ya gudanar sa shi sai an sami manufarsa kan hakan tare da wannan ƙudiri. Manufar wannan bincike nawa shi ne fito ko gano ararrun kalmomi da ƙirƙirarrun su daga Hausar rukuni yan siyasa na arewacin Najeriya. A nan babbar manufar wannan aiki ƙoƙarin zaƙulo tare da tattaro ire-iren kalmomin aro da ƙirƙira daga wannan rukunin alummar ta yan siyasa a harshen Hausa wato daga bakin masu goyon bayan jam’iyyunsu tare da sojojin baka da suke amfani da aron da ƙirƙirar kalmomi a harshe domin samun magoya baya tare da yaɗa manufofin jamiyyunsu, ko tsokana da habaici har ma da mai da martani ga abokan adawa ko jamiyyun hamayya wanda hakan yana faruwa ne domin ƙara samun amincewa da goyon baya ko kuma mayar da martani kawai. Wannan shi ne babbar manufar shi wannan aiki ko binciken.

1.2 Farfajiyar Bincike


Wannan bincike zai yi nazarin Hausar da ta dangance wani rukunin jama’a. Wato Hausar ‘yan siyasa a Arewacin Najeriya, musamman abin da ya shafi aro da ƙirƙira da ake samu a cikin kalmomin fannu ko yanki jimloli da suka danganci wannan rukunin jamaa. An iyakance aikin ne a Ƃangaren Arewacin ƙasar nan. Saboda haka duk wasu bayanai da misalai an iyakance su ne a waɗannan Ƃangarori da aka ambata a baya. Binciken ya duba Arewacin Najeriya ne ta fuskar Karin harshen yan siyasa daga 1999 zuwa 2016 (1999-2016) na jahohin arewacin ƙasar nan kadai wanda aka iya ziyarta domin gudanar da binciken.

1.3 Mahimmancin Bincike


Ana fatan wannan bincike ya kasance mai matuƙar mahimmanci, musamman ga harshen Hausa wajen magana da inganta sadarwa ta fuskar muamula da kuma bunƙasa shi wajan bayyana ararrun kalmomi da ƙirƙirarrun na wannan rukunin jamaa. Yana da kyau a taskance irin
Hausar domin nazarin su ne zai sa ba za a manta da su ba, haka kuma dai binciken zai bai wa waɗanda ba su san su ba damar fahimtar su, waɗanda suka fahimce su za su ƙara tunawa da su.
Ci gaban ayyukan da suka gabata ne ko kuma faɗaɗa su . Don a ƙara haskaka wannan rukunin jamaar wajen irin gudunmawar da suke kawo wa a cikin harshen Hausa musamman abin da ya shafi aro da ƙirƙira cikin yankin jimloli ko kalmomin fannu da suka danganci wannan rukuni.
Binciken zai rage matsalolin rashin kalmomin fannu da suka keƂanci yan siyasa ko siyasar. Domin a san su a kuma san yadda ake amfani da su a wannan rukunin jamaar na yan siyasa a kuma ƙara fahimtar abubuwan da suke gudana a tsakaninsu ko ba a cikin rukuni kake ba.
Binciken idan ya kammala zai zama makama ga masu nazari. Wajen sanin makamar aiki ta inda za su tashi da inda aka kwana a wannan
Ƃangaren.

1.4 Matsalolin Bincike


Tazara tsakanin jahohin da binciken ya shafa, na daga cikin matsalolin da wannan binciken ya ci karo da su sakamakon ya haɗa da garuruwa da dama na arewacin Najeriya wajan tattaro bayanan da suka
shafi aikin.
An fuskanci matsala wajan ganawa da shahararrun sojojin baka na wannan jahohi domin rashin zaman su a garuruwansu da kuma kai kawo irin na harkokin siyasar, hakan ne ya haifar da dole da hanyoyin tattara bayanai da akai binciken da su maimakon ganawa da kai tsaye don tambayoyi gare su.
Binciken ya fuskanci matsalar saƂawar alƙawari na wasu yan siyasa a arewacin ƙasar nan domin ganawa da su dangane da harkokin mulki sun sha masu kai ta sa aka mai da hankali wajan sauraronsu ta kafafen ya ɗa labarai irin hirarrakin da ake da su a gidajen rediyo da jaridu da talabajin, hakan shima aka haɗu da matsalar rashin wutar lantarki ko ɗauke ta a lokacin gudanar da wani shiri a ɗaya daga kafafen da aka ambata na sama.
Matsalar rashin yarda daga wasu ‘yan siyasa da aka fuskanta wajan ƙoƙorin ganawa da su a dalilin rashin tsaro na wannan ƙasar da muke fama da shi a lokacin rikicin boko haram ya haifar da rashin yarda ga duk wata baƙuwar fuska ta matso kusa da shi ko gidansa dama garin su baki ɗaya. ƙarancin kuɗi wajen gudanar da wannan bincike, musamman a harkokin sufuri da katin waya don kiran waɗanda aikin ya shafa da ma sauran kayan gudanarwa da suka danganci binciken.
ƙarancin karatun boko na wasu daga cikin sojojin baka ya sa sun kasa ba da ma’anar abin da suka faɗa a ilmance.

1.5 Naɗewa

A wannan babi mai taken gabatarwa an fara ne da kawo manufar bincike da farfajiyar sa da mahimmnaci tare da matsaloli kamar yadda aka tsara su daki-daki.

Post a Comment

3 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.