NA
ASHIRU USMAN GABASAWA
ADM.NO:1110106129
SATUMBA, 2016
BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
2.0 Shimfiɗa
Hausawa kan ce “waiwaye adon tafiya, kuma daga na gaba ake
gane zurfin ruwa” saboda haka wannan aiki ya yi waiwaye da bitar ayyukan da
masana da manazarta da malamai suka yi masu alaƙa
ta kusa da ta nesa da wannan aiki ta fuskoki da dama komai kankantarsu domin
samun tudun dafawa.
2.1 Bita a Kan Aro da ƙirƙira
Imam (2009) ya wallafa littafi mai suna “Asalin Aro,
Ma’anarsa Da Ire-Irensa” ciki ya kawo asalin aro daga Larabci da yadda Hausa ta
mai da ita a yau sannan ya kawo rabe-raben aro da mahimmancin sa ga harshen aro
da ire-iren misalan aro daga Larabci da Turanci da Azbinanci da Fulatanci da
Nupanci da Barbanci da Faransanci da sauran su zuwa cikin harshen Hausa. Akwai
alaƙa ta kusa da littafin Imam wajen bayyana asalin
kalmar aro da ire-irensa da rabe-rabe tare da kawo misalan aro daga wasu
harsunan duniya zuwa Hausa. Sun bambanta da wannan aiki da zai kalli aro da ƙirƙira
a karin harshen ‘yan siyasa na Arewacin
Najeriya.
Giro (2012) ya yi bincike a kan ire-iren aron kalmomin da ke
cikin littafin Mace Mutum a kan harsunan Ingilishi da Larabci wanda
mawallafiyar tai amfani da su a ƙoƙarinta na isar da sakon
littafin, bayan kawo ma’anar aro da ire-irensa
daga masana da dama sai ya tsara kalmomin ta yin la’akari
da irin aron da Hausa ta yiwo a Larabci da kuma ɗaya ɓangaren wato Ingilishi sannan daga baya kuma ya
kawo kalmomin aron a littafin na Larabci da akai amfani da su da Ingilishi da
kuma tsofaffin kalmomin Hausa a ƙarshe
ya gama da kammalawa da manazarta. Akwai alaƙa
domin sun yi canjaras ta fuskar aron kalmomi duk da yake aikina zai kalli aro
da ƙirƙira
a cikin kalaman ‘yan siyasa na Arewacin
Najeriya.
Besse (2015) ya gudanar da bincike kan “Dangantakar Harshe Da
Siyasa A Sakkwato.” Bayan gabatarwa a sashi na farko a na biyun ne ya shiga
kawo ma’anar harshe daga masana da alaƙarsu
da siyasa da irin tagomashin da ya samu. Sai kuma ya ba da irin nasarar da ‘yan
siyasa a garin Sakkwato ke samu a dalilin harshe. Akwai dangantaka tsakanin
aikina da na Besse ta la’akari da yadda ya gudanar
da bincikensa ne a kan abin da ya shafi siyasa da harshe amma kuma sun sha
banban saboda aikina zai yi nazarin nau’in karin harshen ‘yan
siyasa na Arewacin Najeriya.
Aliyu (2007) ya gudanar da bincike mai taken “Kalmomin Aro Na
Zamani A Hausa”. Ya kawo yadda zamani ke sauyawa wanda hakan ke haifar da baƙin abubuwa a harshe wanda ba a san su ba. Daga
nan sai aikin ya mayar da hankali kan baƙin
kalmomi ɓangaren kimiyya da fasaha da suka ƙara yawan samuwar wadatattun kalmomi a Hausa da
ake amfani da su kai tsaye ko saɓanin
hakan. Tabbas akwai dangantaka makusanciya ta fuskoki mabanbanta, musamman idan
aka yi magana a kan aron kalmomin zamani a Hausa.
Yakasai (2005) Bayan gabatarwa da bayyana ra’ayin masana
dangane da aro a cikin harshe tare da kawo ma’anar da suka
bayar irin su Fishman (1972) da Trudgill (1974) da Hymes (1974) dangane da aro
cikin harshe. A kashi na biyu ya kawo amfanin da ƙirƙira ke kawo wa da cewa “dukkanin
kalmomin aro suna inganta kalmomin harshe da kuma ƙirƙira
na kawo hikima a harshen aro” sai ya yi ƙoƙarin fassara abubuwa
sababbi cikin faɗaɗa
ma’anar. Ya kuma bayyana samuwar sababbin kalmomi waɗanda
al’ummar wannan wurin ke amfani da su a jama’a.
Misali
• Wanki – mai nufin maguɗin jarabawa
• B.Z – mai nufin bazawara
• ƙwaro –
mai nufin mai ƙwazo
• Presido – mai nufin shugaba
Babu shakka akwai alaƙa
dangane da faɗaɗa ma’anar
kalmomin da ake da su a cikin harshe da ƙirƙirar sababbi domin sadarwa a cikin jami’a
da garin Sakkwato. Sun sha bamban da wannan aiki ne da ya kalli nau’in
karin harshen ‘yan siyasa na Arewacin Najeriya baki ɗaya
kan aro da ƙirƙira a cikin kalami ko kalmomi.
Bature (2002) ya gabatar da maƙala
mai taken “Nazari Kan ƙirƙirar Sababbin Kalmomi A Hausa”.
Da farko ya kalli hanyoyin ƙirƙirar kalmomi daban-daban da suka dace da kalmomin
Larabci zuwa Hausa da kuma Turanci. A nan ya kasa aikin zuwa gida biyu sashi na
ɗaya
ya yi bayanin mahimmancin binciken da dalili samuwar sababbin kalmomi, a ɓangare na biyu kuwa sai ya kalli hanyoyin ƙirƙirar
sabuwar kalma tare da amfani da kalmomin Hausa na asali ko na aro da yadda ake
hausance su a Hausa har su koma kamar sabuwar kalma, daga ƙarshe ya naɗe da yadda Hausa ke
sarrafa kalmomin aro zuwa azuzuwan kalmomi ya yin da aikatan Hausa yafi ɗaukar
kaso mai yawa na kalmomin aro. Binciken Bature na da alaƙa da wannan aiki ta ƙut-da- ƙut
sakamakon ɓangaroren da ya taɓo a cikin aikinsa ya yin da aikina ke kallon aro
da ƙirƙira
a cikin kalamai ko kalmomin fannu ko jimloli a Hausar ‘yan
siyasar Arewacin Najeriya.
Salihi (1998) ya gudanar da bincike mai taken “Baƙin Kalmomi Da
Gamin Gambiza Daga Turanci Zuwa Hausa A Cikin Rubutattun ƙagaggun Labarai”. Ya kawo ma’anar
baƙin kalmomi da samuwar su tare da ire-iren aro haɗi
da gamin gambiza da kalmomin ƙirƙirarru sannan a cikin aikin ya kawo misalansa
cikin ƙagaggun labarai da dama ƙarshe ya kammala da shawarwari tare da manazarta.
An samu alaƙa sosai tsakanin ayyukan,
sai dai sun banbanta ne ta fuskar keɓe
farfajiyar binciken sa a cikin ƙagaggun labarai sabanin
wannan aro da ƙirƙira a karin harshen ‘yan
siyasar Arewacin Najeriya.
'Dantumbishi (ba shekara) ya wallafa maƙala mai taken “Neologism
In Hausa: Its Relevence And Development”. Ta ƙunshi irin bunƙasar
da ƙirƙirar
kalmomi ke haifarwa a harshen Hausa musamman wanda aka samar sakamakon cuɗanya
da Larabawa da Turawa tun ƙarni na tara zuwa na sha
biyu (9th – 12th centuary) tare da faɗaɗa
ma’anar wannan kalmomi da muka aro a garesu. Ya duba ɓangaren ƙirƙira da samar da wata kalma daga cikin wata da
wanda muke canzawa ma’ana ta asali daga harshen
aro sai ya mayar da hankali kan ƙirƙirar sababbin kalmomi daga Turanci da Larabci
inda yake ganin an gaza a nazarin bangaren. Akwai dangantaka da aikin
[antunbishi dangane da ƙirƙira da mahimmancin ta a Hausa a lokacin cuɗanya
da Larabawa da Turawa sai dai mu aikin mu zai ba ƙarfi
ne kan abin da ya shafi Hausar Hausawa ‘yan siyasa.
Abba (2013) ya gababtar da maƙala
mai take “Coinage And Neologism In Kano Politics”
ya kawo kaɗan daga tarihin shahararrun ‘yan
siyasar Kano na farko har kawo wannan zamani kan yadda suke bunƙasa harshen Hausa wajan yin aro da ƙirƙira
a ƙoƙarin neman goyon bayan
jam’iyyun su dan sukai ga nasara a cikin yaƙin neman zaɓen
jahar Kano. Ya kawo kalmomin na nan kusa (2011) ƙadan
irin su wujuwuju da dawodawo tare da wanda aka faɗaɗa
ma’anar su zuwa wata daban, misali hannun jaririrai da goro ɗan
ujile da sauransu. Babu ko shakka akwai alaƙa
mai nauyi da aikin Abba kan yadda ya dubi aro da ƙirƙira tare da faɗaɗa
ma’anar wata jimla a cikin bayanan ‘yan
siyasar Kano, wannan aiki ya banbanta da na sa domin ya yi duba izuwa aro da ƙirƙirar
kalami ko kalmomin fannu a cikin bayanin ‘yan siyasar Arewacin
Najeriya ba jaha kaɗai ba.
Busa (2013) ya gudanar da bincike mai taken “Hausa Loans
Words In Gbagyi”. Bayan kawo taswirar wannan al’ummar cikin ƙasar nan sai ya ba da dalili cewa sakamakon cuɗanyar
su da Hausawa ya saka su aro na dole daga harshen Hausa ta ɓangarori irin su ilimin gundarin sauti
(phonetics) da ilimin tsarin sauti (phonology) da kuma wadatuwar kalmomi
(lexicology). Ya yi nazarin irin kalmomin da suka aro zuwa cikin harshen na su
na Gbagyi ya kawo kalmomin walwalar harshe cikin aron su da sunayen mutane da
kasuwanci da dabbobi da tsirrrai da sassan jikin mutum da launi da sutura da
sauransu. Misali:
GBAGYI HAUSA
Gbada Agwada
Kawa Akawu
Yira Inna
Batule Bature
Fali Fari
Ciloma Ciroma
Baluba Abarba
Bunsulu Bunsuru
Kamar yadda muka ambata a sama aikin Busa bincike ne kan
yadda harshen Gbagyi ya yi aro daga Hausa saɓanin
wannan da zai duba yadda Hausa ke amfani da aro wajen samar da Hausar ‘yan
siyasa.
Dambo (2013) ya gabatar da maƙala
mai taken “ƙirƙirarrun Kalmomin Hausa: Ina Makomarsu? Bayan
gabatarwa da waiwaye kan irin hanyoyii da ake bi wajan ƙirƙirar
kalmomi a harshe daga masana ya yi ƙoƙarin kawo shawarwari domin kafa wata hukuma ko
cibiya da za ta taskance wannan ƙirƙirarrun kalmomin a isar da su cikin al’umma
domin bunƙasa harshen Hausa da
inganta sadarwa a ƙarshe ya naɗe
da kawo manazarta. Tabbas hanyoyin da ya nuna da ke taimakawa wajan samar da
sababbin kalmomi za su ƙara wa aikinmu haske
sosai, musamman ta fuskar ƙirƙira da ta shafe mu kai tsaye.
Abbas da Umar (2016) Sun gabatar da maƙala mai taken “Harshe Da Siyasar Canji A
Arewacin Najeriya”. Bayan kawo mahimmancin
harshe da siyasa a rayuwar al’umma sai aikin ya yi duba
irin tasirin harshen Hausa cikin jama’a da jam’iyyar
adawa wajen kawo canjin gwamnati a yaƙin
neman zaɓen da bayan babban zaɓen shekara ta 2015 a Arewacin Najeriya, binciken
ya gudana kan ra’in nazarin kalami a
kimiyyar harshe. Akwai alaƙa da aikin Abbas da Umar
dangane da muhallin da aka gudanar da binciken Arewacin Najeriya da da rukunin
‘yan siyasa tare da mahimmancin harshe, sun sha banban da wannan aiki kan ra’in
nazarin kalami a kimiyyar harshe wajen yaƙin
neman zaɓe ya yin da wannan aikin ke kallon aro da ƙirƙira
a cikin zantukan ‘yan siyasa.
2.2 Bita a Kan Hausar Rukuni
Harshen Hausa yana da faɗi da yalwa ta yadda har
ya kai ga samar da kare-karensa masu damar gaske. Haka kuma, wannan yalwar tasa
ita ce ta kai ga haifar da nau’o’in Hausa daban-daban (Yakasai 2012:109). Shi
karin harshe na rukuni wani ɓangare ne na karin harshe
da ya danganci wasu mutane masu halayyar zamantakewa da kuma hanyoyin sarrafa
harshe iri guda, yanayin zamantakewar suke amfani da shi (Fagge, 1982).
Yakasai (2012) a cikin littafinsa ya kawo “Danagantakar
Harshe Da Rukunin Jama’a”. Wanda ya yi tsokaci kan yanayi da tsarin rukunin
jama’a tare da dangantakar harshe da rukunin jama’a sannan sai ya kawo nau’o’in
Hausar kasuwanci da Hausar sarakuna da Hausar mawaƙa da Hausar malamai da Hausar dattijai da Hausar
samari da ‘yan mata da Hausar matan aure da Hausar gidan magajiya da ta
wurin zaman makoki a ƙarshe ya kawo naɗewa
cikin babin. Yakasai bai kai ga taɓo
lamarin da muke son gudanar da bincike akai ba wato Hausar ‘yan siyasa.
Fagge (2004) ya bayyana yadda ake samun sauye-sauye ta hanyar
saye da ƙirƙira
a cikin harshe wanda ya haifar da ire-iren karin harshen Hausa na rukuni. Ya yi
bayani a kan rukunoni da dama waɗanda suka danganci masu
sana’o’i mabanbanta da sabgogin
rayuwa na yau da kullum. Da yake aikin Fagge ya kunshi Hausar rukuni
daban-daban duk da yake ayyukanmu suna da kama, saboda sun taɓo abin da ya danganci Hausar ‘yan
siyasa, amma sun yi hannun riga da juna musamman ganin nawa aikin ya shafi nau’in
karin harshen ‘yan siyasa na arewacin Najeriya a matsayin binciken neman
digiri wanda zai kasance mai yalwa fiye da gudunmawar marubuci da ya fi ba da ƙarfi a cikin garin Kano.
Zailani (2012) ya gudanar da bincike mai take “Hausar Kan
Titi”. Bayan gabatarwarsa sai ya kawo ma’anar kan titi da mutanen kan titi da
sana’o’in su daga nan kuma sai ya shiga cikin aikin gadan-gadan inda ya yi ta
kawo misalan nau’o’in Hausar kan titi kamar Hausar ‘yan tasi da Hausar ‘yan
giya da Hausar ‘yan kodin da ‘yan sholisho da ‘yan wiwi da irin yadda suke
sadarwa tsakanin su ya kuma faɗi mahimmanci harshe wajen
sadarwa har da Hausar masu maganin gargajiya da jami’an tsaro a kan titi.
Garba (2010) ya gudanar da bincike mai taken “Hausar Gidan
Rediyon BBC”. Bayan kawo tarihin kafuwar gidan rediyon na BBC da samun sashe na
watsa labaru cikin harshen Hausa, ya karkata akalar aikin na sa zuwa irin yadda
suke ya da labarai ta hanyar kawo irin jimlolin su cikin Hausa amma kuma a
tsinci Turanci nan da can da fassarar da sukewa labarai na Turanci zuwa Hausa
ya naɗe
aikin da kammalawa da manazarta.
Yakasai (2003) ya gabatar da maƙala
taken “Sadarwa Tsakani Maza Da Mata: Nazarin Dagantakar Harshe Da
Daidatuwar Jinsi”. Bayan gabatarwa ya duba
dalilin da ya sa mata ba sa magana kamar maza tare da kawo ma’anar
daidatuwar jinsi sannan ya yi ƙoƙarin fahimtar alaƙa
tsakanin harsuna daga nan sai ya kalli ayyukan masana domin nuna yadda suka
gudanar da bincike kan irin na sa aikin yanayin tsare-tsaren Harshe har ma
akwai inda akai magana akan harshe da jinsi a Hausa an kammala da shawarwari da
manazarta.
Yakasai (2013) ya gabatar da maƙala
mai taken “Adon Harshe A
Fagen Dimokaraɗiyya A Kano”. Ya kawo
ma’anar harshe da adon harshe tare da dimokaraɗiyya. Sai ya ya kawo
jerin kafafen ya ɗa labarun da ‘yan siyasa
ke amfani da su wajen sadarwa tsakanin su da juna. Daga nan, ya mayar da
hankali wajen misalai na daga kalmomi da bayanan ‘yan siyasar Kano domin fito
da abin da yake magana akai wato yadda suke adonta harshe cikin kalamansu ya kammala
aikin da manazarta. Akwai alaƙa ta ƙut-da-ƙut
da aikin Yakasai da ya yi magana a kan adon harshe a rukunin ‘yan
siyasar Kano. Ayyukanmu sun sha bamban saboda kamar yadda taken aikin ya nuna
zai fi mayar da hankali ne kan samuwar Hausar ‘yan siyasa na Areawcin Najeriya
ta amfani da dabarun aro da ƙirƙira.
Ayyukan da suka gabata da wannan nazari ya duba sun ƙara wa wannan aiki haske kasancewar akwai alaƙa da ke tsakani ta kusa da ta nesa. Don haka
dukkan ayyukan sun bayar da babbar gudunmawa ga wannan bincike.
2.3 Naɗewa
Aikace-aikace da aka yi bitarsu su ne waɗanda
wannan aikin ya ci karo da su yayin gudanar da binciken wanda suke da alaƙa ta kusa ko ta nesa. Kamar yadda bayanai suka
gabata akwai kare-karen harshe da dama kuma waɗansu suna kama da juna,
wannan alaƙa da ke tsakanin wadannan
kare-karen harshe ya sa waɗansu mutane kan ɗauka
cewa karin harshen waɗannan mutanen yana
dai-dai da na waɗancan. Amma abin da ya
kamata a fahimta a nan akwai ‘yan bambance-bambance a
tsakaninsu musamman wajen tsara alƙiblar
wannan aiki mai taken “Hausar ‘Yan Siyasa A
Arewacin Najeriya”.
1 Comments
[…] ci gaba da karatu […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.