Karin Magana Game Da Aure

1. Ƙarya ba ta sa amarya lalle.
2. Faɗi ke matar aure ni saɗaka in na faɗi gida nika kwana.
3. Mai son ɗan Ƙwarai, ya auri isassa.
4. Barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarrafe.
5. Larura auren namiji da ‘ya’ya
6. Arahar banza auren bashi, in an haihu a biya
7. Aure ba ka da malam
8. Ƙoshin takaba aure da mai ƙararren kwana
9. Larura, auren namiji da ‘ya’ya
10. Abin da ke ga amarya shi take ba ango
11. Komai wayon amarya sai an sha manta
12. Kurum baka, amarya ta ci ɗan masu gida
13. Kwana nawa ne? maye ya yi amarya
14. Jin dadin aure, har da ce wa miji baba
15. Izgili, angaye bakin rijiya
16. Na gaji, mai hana wa mata lada
17. Abin ya ci matar lifidda
18. Matar in tashi, ba ta ƙosar da mijinta
19. Dace da masoyi, riba
20. Son maso wani ƙoshin wahala
21. Ba haka aka so ba, ƙanin miji ya fi miji kyau
22. Matar na-gode, ba ta rasa mijin aure
23. Mai zanin gamin baki, ba ta wa miji yanga
24. Ban faye musu ba, an ce da bazaura ta hau gado
25. Daki-bari turmin gidan miji
26. Ƙarya ba ta sa amarya lalle
27. Kilin kiso da balanƙwalma, kiran miji da akaifa
28. Faɗi ke matar aure, ni saɗaka in na faɗi gida naka kwana

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.