Karin Magana Game Da Mutuwa

    1. Mace mai ciki ke tsoron mutuwa.

    2. Furfura manzon mutuwa.

    3. Abokin kuka ba a É“oye masa mutuwa.

    4. Abin da yawa, mutuwa ta shiga kasuwa.

    5. ƙurulla, mutuwa ranar salla

    6. Tonon asiri mutuwa gidan kwaraka

    7. Tsufa ya zo da gardama

    8. Lahira ba ta ƙin gawa

    9. Allah ya hutar da biki, É—an matsiyaci ya mutu ranar suna

    10. Sai ai kare ya mutu da haushin kura

    11. Tsattsaye sallar gawa

    12. Mutuwa ake fasawa, ko hisabi?

    13. ƙurulla, mutuwa ranar salla

    14. Ai giwa ta mutu ake É—ibar namanta

    15. Makashinka na gidanka

    16. Kowa ya mutu ya É—ebe takaicin kwana

    17. Abin da yawa, mutu ta shiga kasuwa

    18. Furfura manzon mutuwa

    19. Likkafani ba a son ka sai ran mutuwa

    20. Mutuwa ba aimiki layar zana

    21. Mutuwa ba ki raina ciwo

    22. Bita da ƙulli, bugun kabarin kishiya da mucciya

    23. Cakulkuli, ƙanwar mutuwa

    24. Wa albarkar gawa, tai tusa tana ga hannun Allah

    25. An kori mutuwa, ciwo sai ya yi yawo

    26. Fatalwa mai ta da hankali

    27. Tashinku, tashina, inji mai tsaron gawa

    28. Gata, ba ya hana mutuwa

    29. Wane, mutum inji mutuwa

    30. Bidiri, tusa cikin kabari

    31. Ba kukana ba, uwar kishiya ta mutu

    32. Wai Allah ya isa, an yi wa mai takaba ciki

    33. Sai dai a mutu har liman, a rasa mai ba da salla
    www.amsoshi.com

    1 comment:

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.