Ticker

Saƙon Yau Domin Gobe: Mawaƙi A Rigar Malanta Cikin Waƙar KUSHEWA Ta Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Maƙalar da aka gabatar a Taron Ranar Mawaƙa ta Duniya, da ƙungiyar Mawaƙa ta ƙasa ta shirya, a babban birnin Dutse da ke Jihar Jigawa, daga ranar Juma’a 30 ga watan Disamba 2016 zuwa Lahadi 01 ga watan Janairu 2017, da ƙarfe 10 na safe.

Daga

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
profyakasai@gmail.com
(+234) 08035073537

1.0 Shimfiɗa


A tarihance, mawaƙa sune a sahun gaba wajen adana martabar harshe da kuma aladun alumma. Wato ke nan tun zamani mai tsawo da ya gabata, ana amfani da waƙa wajen faɗakarwa da kuma wayar da kai. A matsayinsa na wanda ya naƙalci harshe, mawaƙi yana amfani da basirarsa wajen isar da saƙonninsa a waƙe domin faɗakarwa da ilimantarwa dangane da alamuran da suke ɗamfare da zubi da tsarin rayuwar alumma. Saboda haka, mawaƙi mutum ne wanda ya naƙalci harshe kuma waƙoƙinsa suka zamo hoto na rayuwar duniyar da yake tasarrufi a cikinta (Woolger, 1978).

A ɗaya ɓangaren kuma, waƙa wata kafa ce ta hikima da take ɗokantarwa domin sanya nutsuwa da kuma nishaɗantarwa ga zuciya. Wato tasirinta shi ne ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa. Hasali ma, ai kowane batu na ilimantarwa yana faidantarwa tamkar dai yadda masanin ilimin falsafa yake shayar da alumma ilimi mai inganci. Ita waƙa tana ilimantarwa fiye da wannan masanin falsafa, saboda tana ba da gudummawa wajen gina alumma. Wato dai gwargwadon ƙarfi da saƙon da waƙa take ɗauke da shi, to gwargwadon tasirin da za ta yi ke nan ga al’umma (Dennis, 1704).

Tun lokacin da rubutattun waƙoƙi suka bunƙasa a ƙarni na sha-takwas zuwa na sha-tara, sun kasance masu ɗauke da jigon Musulunci. Wannan jigo ya haɗa da fiƙihu da tauhidi da kuma madahu. Shehu Usmanu da jamaarsa sun yi amfani da rubutattun waƙoƙi wajen jawo hankalin alumma tare da faɗakarwa da kuma tsoratarwa. Haƙiƙa waƙoƙin sun taka muhimmiyar rawa wajen ɗabbaƙa jihadin ɗaukaka addinin Musulunci. Ko bayan jihadi ma, waɗannan waƙoƙi sun ci gaba da yin tasiri a zukata da rayuwar mutane. Rawar da rubutattun waƙoƙi suka taka a fili take wajen isar da saƙonni daban-daban ga alumma.

A ɗaya haujin kuma, waƙoƙin baka sun kasance masu matuƙar tasiri a kan alumma. Samuwar waƙoƙin zamani da ake gabatarwa a situdiyo sun samar wa waƙoƙin baka sabuwar duniya. Kayayyakin kiɗa na zamani da ake amfani da su yayin samar da irin waɗannan waƙoƙin sun zamo linzami na jawo hankalin mutane da yawa. Abin nufi shi ne, jamaa da yawa sun karkata zuwa ga waɗannan waƙoƙi. Hasali ma, ai tasirin waɗannan waƙoƙi a fili yake, musamman ma idan aka yi laakari da cewa, yan siyasa na amfani da su wajen neman magoya baya. Ta wannan hanya sun shiga zukatan mutane da dama. Haka kuma, gwamnati na amfani da su wajen yaɗa farfaganda, tare da isar da saƙonnin da take son isarwa ga jamaa. Ana kuma yi wa sarakuna tare da manyan mutane irin waɗannan waƙoƙi domin fito da matsayi da martabarsu a idanun duniya, tare da cusawa mutane soyayyarsu. Ana sanya waƙoƙin baka na zamani a cikin fina-finan Hausa domin ƙara masu armashi. Za a iya cewa kusan yanzu irin waɗannan waƙoƙi sun zama tilas a cikin fina-finan Hausa, saboda rashinsu tamkar miya ce babu gishiri.

Masoya na amfani da irin waɗannan waƙoƙi domin ƙara danƙon zumuncin da ke tsakaninsu. A ɗaya ɓangaren kuma, ana amfani da waɗannan waƙoƙi wajen barar soyayya. Ba shakka waƙoƙin baka na zamani sun kasance wata hanya ta samun masarufi ga masu yin su. Bugu da ƙari, kamfanoni da maaikatu da yan kasuwa suna amfani da irin waɗannan waƙoƙi domin tallata hajarsu. Idan aka yi laakati da irin wannan rawa da waƙoƙin baka na zamani suke takawa, lallai za a ga cewa sun samu karɓuwa matuƙa, sannan suna da tasiri ga rayuwar al’umma. Wannan ya nuna cewa, da za a yi amfani da su ta hanyoyi mafiya dacewa, da lallai sun zama masu amfani wajen gyara tsarin zamantakewa da tarbiyya da rage miyagun ayyuka da cin hanci da rasahawa domin samar da al’umma tagari, tare da zaman lafiya mai ɗorewa.

Sai dai kash, mafi yawan irin waɗannan waƙoƙi an gina su ne a kan duniyanci kawai. Sai dai kuma duk da haka, akan samu waɗanda aka gina su a kan jigon addini domin faɗakarwa da kuma shiryarwa. Da wannan yar shimfiɗa ce, wannan maƙala za ta nazarci gudummawar mawaƙi a cikin rigar malanta, wato yin tsokaci a saƙon yau domin gobe a waƙar KUSHEWA ta Aminu Ladan Abubakar (ALA). Domin cimma wannan manufa, an karkasa maƙalar zuwa kashi biyar. A kashi na farko da na ƙarshe, shimfiɗa ce da kuma jawabin kammalawa. A tsakanin waɗannan kuma, akwai taƙaitaccen bayani game da mawaƙin a kashi na biyu. Daga nan kuma sai cikakken sharhi dangane da jigo da salon waƙar a kashi na uku da na huɗu.

2.0 A San Mutum A San Cinikinsa


Na yarda da maganar hikimar malam Bahaushe da yakan ce a san mutum a san cinikinsa, kuma domin haka ne ma waƙa (ta baka ko rubutacciya) take ɗauke da wasu siffofi da suka sa ta bambanta da sauran sassan adabin harshen Hausa. Hasali ma, ai ta waɗannan siffofi ne ake samun bayanai dangane da rayuwar mawaƙi da daraja ko ƙimarsa a cikin alumma, da yanayin da ya samar da yin waƙar da mutanen da aka yi waƙar dominsu da kuma matasyinsa na mawaƙi (Halliday, 1964).

Daga binciken da masana magabata suka gudanar a kan Aminu Ladan Abubakar da waƙoƙinsa (duba ayyukan Gusau, 2003; da Hamza, 2011; da Barista, 2011; da Yakasai, 2014; Abubakar, 2015; Yakasai, 2015), mun samu haske dangane da kowane ne shi cikin tarihin rayuwa da kuma matsayin waƙoƙinsa a idon alumma. Bugu da ƙari, manazarta suna kuma laakari da abin da mawaƙi ya faɗa game da kansa a matsayin wata kafa ta samun ƙarin bayani dangane da mawaƙi da kuma saƙon da waƙarsa ta ƙunsa domin amfanin alumma. A waƙoƙinsa da yawa ya yi bayani game da kansa da kuma sana’arsa ta waƙa. Ga abin da ya ce game da kansa a waƙar Kwamishinan Yansanda Umar Usman Ambursa:

Kura ma bi almuru
Baban Amina baban Zara
Mai tambarinai waƙa
Alan mutan Kano wan Zara
Miskilin mai waƙa
Idan na yi ta sai an lura

A cikin wannan baiti, mawaƙin ya bayyana kowane ne shi da irin nasabarsa ta iyali da kuma tushe ko asalinsa na mutumin Kano. Wani abin shaawa game da mawaƙin shi ne yadda kowa ya san shi, to da tambarin waƙa ya san shi. A wata waƙar kuma, wadda ya yi wa Nasiru Bawa wanda ya yi wa laƙani da AGAJERE, mawaƙin ya jaddada kowane ne shi. Ya ce:

Ga mai tambura ƙanin Kalma
Yayan Zara ne uban Zara
Kura walwala da almuru
Kafin Zakara yawo cara
Alan inkiya da mai waƙa
Mai waƙa da hankali lura

Dangane da sana’ar tasa kuma ta waƙa, lamarin ya dace babu ko tantama da maganar hikimar nan ta a san mutum a san cinikinsa. A waƙar Kwamishinan Yansanda, ya nuna cewa ita kanta waƙa ana samun mai sauƙi da kuma mai tsauri (kuma duk yadda ta kasance, sune suke tsara ta) wadda ya kira da TAƙADARA. Da yake hannu ya iya kuma jikin ya saba, mawaƙin ya bayyana cewa Ubangiji Allah ne ya hore masa. Ga abin da ya ce:

Taƙadarin ɗan waƙa nakan ji mai nazar ya furta
Ko gagaren ɗan waƙa mai sa makwaikwaya yin mita
Taƙadarar kuma waƙa mukan taɓa har da gwaninta
Ubangiji ya hore ya tallafe ni ya zan kasa in biya

Gaskiya ne cewa, duk mutumin da Allah (SWT) ya horewa wani al’amari a rayuwa, to ba shakka za a samu ya naƙalci wannan fage nasa kuma yana sarrafa shi yadda yake so. A waƙar Nasiru Agajere, mawaƙin ya bayyana yadda waƙa take a wajensa. Ya ce:

Waƙa in ina wa mai sona
Ba ta da ƙaida ta jerowa
Ko kuma ƙaida ta ƙirgawa
Ko adadin ɗiya na saƙawa
Ko zaɓe na yan ɗiyan jigo
Ko kalma abin yabon bawa
Samma ta ka take sauka
Kai ka ce ruwan saman shawa

Tun kafin wannan, sai da mawaƙin ya bayyana wasu maaunai da yake laakari da su kafin ya shiga aikin nasa na waƙa. Ga abin da ya ce a waƙar Tukur Abba Zaga:

Sanadin da ka sa mai yabo ya ƙara ya kuma
Sanadi uku ne in ka ji su sai kai azama
Sanadin farko mahabubu so ne a sama
Sai fa cancantar asali ka sa a yi a kuma
Rukuni na uku martaba bukatar hikima
Ka da kul ka daɗa ko ka rage a aikin hikima

3.0 Mawaƙi a Rigar Malanta


Manazarta adabin baka tun daga tsakiyar ƙarni na goma sha tara, sun bayyana muhimmancin harshe wajen adanawa da kuma yaɗawar ayyukan adabin. Wato yadda ake yaɗa adabin baka, lamari ne mai ban shaawa a idanun masu ilimi da manazarta. Saboda haka, waƙoƙi da labarai ana adana su ne ta hanyar haddacewa ba tare da an rubuta ba tun a zamani mai tsawo, wato a lokacin da mai karatu yake ta ƙoƙarin tuna abin da ya faru a jiya (Rubin, 1995).

Duk da kasacewar waƙoƙin ALA da dama suna ƙunshe da ɓurɓushin jigon addini, abin burgewa ne da yabawa a samu waƙar da ya gina a kan addini zalla. Mawaƙin ya shirya wannan waƙa cikin jan hankali da nusantarwa, wato ya tsara ta yadda za ta kasance mai ratsa jiki da tsokar mai sauraro. Hakan zai sanya mai sauraro ya shiga taitayinsa, idan aka yi dace ma, ya yi karatun-ta-nutsu. Ya buɗe waƙar da amshi yana cewa:

Ranar da ba tsimi da dabara,
Ranar da za mu kwanta kushewa.

A nan mai sauraro zai ji ne kamar an buge shi ya farka daga bacci. Wato yana cikin harkokin duniya sai ga shi an tuna masa wata rana da ya zama dole ya fuskance ta. Sannan ga shi an sanar da shi cewa ‘ba tsimi da dabara’, ke nan ka da ma mutum ya yi tunanin wata hanyar tsira da ta wuce bin dokokin Ubangiji. Sannan ya ambaci ‘kwanta kushewa’, wanda yana ɗaya daga cikin manyan tashin hankali da ke gaban kowane ɗan’Adam.

A baitin farko na waƙar ya yi wani abu mai kama da tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro. Wato ya ɗauko misalan manyan kafirai da fanɗararru da masu girman kai da suka kasance masu izza da ƙarfin mulki da kuma yawan dukiya. Sannan daga ƙarshe ya nuna cewa Allah (SWT) ya yi maganinsu kuma har ya bar wasunsu a matsayin waazantarwa cikin tarihi. Ya fara buga misali ne da Abu-Lahabi, inda ya ambace shi da Uba a gun duka wawa. Daga nan sai ya ambaci Abdul-Sululu inda kuma ya kira shi da Uban maƙaryata. Sai kuma ya rufe da Abu-Jahala da kuma Fir’auna, kamar yadda ya ce:
Uban maƙaryata mai kwarwa,
Abdul-Sululu ya sheƙewa
Uba ga jahilai mai tsiwa,
Abu-Jahala ya taɓewa,
Ga mutakabbirin Misirawa,
Fir’auna ya yi ya kwantawa.

Lallai ambaton waɗannan mutane ya isa ya sanya zukata girgiza. A nan mai sauraro zai fara tunanin mutuwa tare da samar da hoton yadda su Fir’auna suka kasance a rayuwarsu, da kuma lokacin mutuwar tasu. Kwatsam kuma sai mawaƙin ya faɗa a shaɗarar ƙarshe ta baitin cewa: Komai gudu tana iskewa. Wannan magana da ma saura da suke sama, duka suna da tushe a ƙurani da kuma Hadisan Manzon Allah (SAW). A baiti na biyu kuwa, mawaƙin ya yi amfani da mutane mafiya daraja da kusanci wurin Ubangiji domin bayar da misali. Kamar yadda a baitin farko ya nuna manyan kafirai da yadda tasu ta ƙare, a baitin na biyu kuma sai ya nuna salihan bayi ma sun koma zuwa ga Allah (SWT). Wannan ke nan na nuna mana cewa, idan mutum tinƙahonsa bauta ne da tsarkake niyya, to ga waɗanda suka sha gabansa sun wuce, ballantana shi! A wasu shaɗarori biyu na baitin yana cewa:
Nabiyi mursalai ba kowa,
Tun daga Adamu na Hauwa.

Wato dai a gaba ɗaya, annabawa da mursalan da aka yi a waɗannan ƙarnuka ga shi sun koma zuwa ga Allah (SWT). A gaba ma har ya yi nuni da cewa, har mafificin halitta wanda aka ba wa ceto ranar gobe-ƙiyama, shi ma ya koma ga Allah (SWT), kamar yadda ya ce:

Cikamakon Nabiyi ɗan baiwa,
Wanda da kansa an ƙarewa,
Man la Nabiyi badahu kowa,
Mai izni na ceton kowa,
Wa ya rage abin dubawa?

Haƙiƙa yanzu kam mai sauraro dole ya fahimci cewa, babu wani matsayi da zai hana mutum barin duniya. A ƙarshen wannan baiti, mawaƙin ya yi ta fatan samun dacewa bayan mutuwar ta iske bayi, kamar yadda ya ce:

Allah ka sa mu zan dacewa,
Mu yo gamon katar ran tsaiwa.

A baitin waƙar na uku, mawaƙin ya yi amfani da kansa a wajen buga misali inda yake cewa: A kwan a tashi na zama gawa, koko zaran ya zam tsinkewa. Maana dai wata rana dole ya mutu, ko kuma yana raye amma a daina jin ɗuriyarsa saboda juyi na rayuwa. Amma kuma ba yana nufin kansa ne kawai ba, yana magana ne da duk wani mai sauraro. A cikin wannan baitin kuma sai ya nuna cewa, ya zo ne domin tallar magani. Kuma wani abu ma shi ne, maganin na nan a gonar kowa. Ke nan nuna maka shi zai yi kawai. Ga abin da ya ce:
Talla na ke ba hargowa,
Mai hankali kaɗai ka tayawa,
Ga magani a gonar kowa,
Mai izgili ka yin hargowa,
Allah wadan ido gululu,
Idan da babu tsinkayowa.

Haƙiƙa lamarin ya ci masa tuwo a ƙwarya, yadda ga magani a gonar kowa kuma suna da ido amma sun kasa gani. Wato dai hanyoyin kare kai daga azabar Allah (SWT) amma alumma ta bijire. A baiti na gaba, mawaƙin ya nuna cewa, ba kasa kallon gaskiya ba ne kawai matsalar alumma, akwai wasu matsalolin na daban. Dukkanin gaɓoɓi masu amfani, alumma ta kasa sarrafa su yadda za su amfanar. Kunnuwa ba sa jin gaskiya sai dai surutun banza da wofi. Sawu ba sa zuwa ga alheri sai sharri, haka kuma harshe ba ya furta abin amfani sai na banza. Ga abin da ya ce:

Da kunnuwa da ke jin sowa,
Fage na gargaɗi doɗewa,
Da sau da ke zuwa ga fasadi,
Ba sa zuwa ga amfanarwa,
Da sautuka da kan furtawa,
Ba furucin da zai shiryarwa.

A baiti na gaba mawaƙin ya nuna cewa, waɗannan gaɓɓai da Allah (SWT) ya ba wa ɗanAdam, ba domin ya yi shiririta ba ne, sai domin ya bauta masa. A cikin baitin kuma sai ya ja hankali kan yadda duk wani abu mai farko yake da ƙarshe, sannan ya nuna cewa:

Dukkansu mai halittar kowa,
Ya yi su don mu zan ganewa,
Mu zan rabe kaloli tsanwa,
Mu bautace shi ba ƙosawa.
Wannan kaɗai fa ya ishi bawa,
Taho da waiwayen dubawa.

A baiti na gaba, mawaƙin ya nuna cewa wawa ne kaɗai yake ruɗuwa da duniya, kuma duk wanda ya riƙi duniya a matsayin gida, to ya tabbata ba shi da gida, musamman ranar gobe ƙiyama. Sannan ya nuna cewa wawa ne kawai yake ruɗuwa da kuɗi har ya yi zaton a duniya ana ɗorewa. Ga abin da ya faɗa:
Duniya budurwar wawa,
Matar mahaukaci ko wawa,
Gidan maras gida mai ƙwawa,
Gidan marar rabo ran tsaiwa,
Wa ke biɗar ganin ruɗewa?
Yana ga mai sahun miƙewa,
Mai tara dukiya don ƙwawa
Zato yake ana ɗorewa
Ruɗi na dukiyar tarawa
Ta sa sahi ya zamanto wawa
Bawan ciki da bai ƙosawa
Kullum a ba shi bai turewa

A baitin waƙar na ƙarshe, mawaƙin ya koɗa kansa ne, kuma ya yi hakan ne cikin wani irin salo ta yadda sai an lura za a gane cewa da kansa yake. Ga yadda kirarin ya zo:
Kainuwa dashen mai kowa
Saman ruwa take tohowa
Gamji sassaƙa da sarewa
Ba ta hana ka kai tohowa
Rashin jinni rashin tsagawa
Ana zuwa ake iskewa
Sarari mai wuyar a ƙurewa
Mai sa matafiya sarewa
A kwan a tashi mai gillewa

Bayan wannan dogon kirari, shaɗarorin ƙarshe guda biyu sun nuna a kansa ne ya yi wannan kirari, kamar dai yadda ya ce:
A yau da ni ake damawa
Ina ta jan zaren saƙawa

A cikin kirarinsa ya nuna shi gamji ne sha sassaƙa, wato duk yawan abokan hamayya da cece-ku-ce ba komai ba ne gare shi. Sannan ya nuna idan dai fasaha ce to sai dai ba a tarar da shi ba, wato da zarar an sadu da shi to za a isko ta, kamar yadda ya ce:
Rashin jini rashin tsagawa
Ana zuwa ake iskewa
Sai dai kuma bayan ya yi wannan kirari gaba ɗaya, sai ya nuna wa mai sauraro cewa, wannan rayuwa ba komai ba ce. Dalili kuwa shi ne:
A kwan a tashi mai gillewa
A kwana wata ran ba kowa

4.0 Salo Asirin Waƙa


Mawaƙin wannan waƙa ya yi amfani da salailai da dama domin ƙarawa waƙar armashi. Waɗannan salailai sun haɗa da salon kinaya da aron harshe da salon sarrafa harshe da kuma salon mutuntawa. Ga su ɗaya bayan ɗaya:
Kinaya: Kinaya wata dabara ce ta sakaya zance wadda take juyar da abu daga asalinsa, wato ma’anarsa ta farko zuwa ga wata ma’ana ta biyu ta sakayawa (Gusau, 2003). A baitin farko na waƙar, mawaƙin ya yi amfani da salon kinaya. A baitin ya kawo mutuwa a matsayin karya mai tsananin gudu, wadda saboda tsabagen gudunta, babu wani mai rai da zai iya tsere mata. Ya ce:

Karyar Ubangiji mai kowa
Komai gudu tana tserewa

A baiti na uku ma akwai misalan kinaya. Na farko shi ne wurin da ya ambaci zare a maimakon harƙalla da kuma rayuwar yau-da-kullum na mawaƙin kansa. Ya ce:
A kwan a tashi na zama gawa
Ko ko zaren ya zam tsinkewa

A gaba kuma sai ya ambaci wa’azi da yake yi a matsayin ‘talla’, sannan waɗanda suka karɓa su ne suka taya wannan hajar. Ya ce:

Talla nake fa ba hargowa
Mai hankali kaɗai ka tayawa

A gaba kuma ya kwatanta shiriyar da ɗan’Adam zai yi domin neman tsira da ‘magani’, sannan maganin da ake samu a gonar kowa. Ma’ana kowa yana da damar da zai tsira daga azabar Allah (SWT) ta hanyar ayyuka nagari. Ya ce: Ga magani a gonar kowa.

Aron Harshe: Harshe shi ne babban tubalin da ake amfani da shi wajen gina saƙo, sannan a yi amfani da dabaru na nuna gwaninta a isar da saƙon ga jamaa (Gusau, 2003). Wannan ne ya sa wasu manazarta suke ganin akwai dangantaka ta kusa a tsakanin harshe da salo, har ma ake kwatanta matsayin nasu tamkar jini ne da tsoka. A wannan waƙa akwai wuraren da mawaƙin ya yi amfani da salon aron harshe (baƙin kalmomi) a cikin waƙar. Waɗannan wurare sun haɗa da baiti na huɗu in da ya yi amfani da kalmar fasadi wadda daga Larabci take. Ya ce:

Da sau da ke zuwa ga fasadi

Ba a harshen Larabci kawai irin wannan aron harshe yake ba, har ma da Ingilishi. Wannan ya nuna cewa mawaƙin yana ji da kuma fahimtar harsuna da yawa, kuma wannan damar ce ta haifar da samuwar irin wannan salon. A baituka na gaba kuma ya yi aro daga Ingilishi in da yake cewa:

Five sensory organs dubawa

Haka kuma a baiti na biyar ma ya yi aro daga harshen Larabci yana cewa:

Da ka ji Alhudusu ta zowa
Sai ka ji Alfana’u ƙirewa

Salon Sarrafa Harshe: Sarrafa harshe hanya ce ta amfani da harshe a cikin waƙa. Wannan hanya ta ƙunshi yadda mawaƙi ke zaɓar kalmomi da jumloli da kuma irin yadda yake amfani da su wajen isar da saƙonsa ga jamaa (Sarɓi, 2007). Mawaƙin ya yi amfani da salon sarrafa harshe a wasu baitoci na waƙar. Irin waɗannan wurare sun haɗa da baiti na shida, in da yake cewa:
Duniya budurwar wawa

A baiti na bakwai ma akwai irin waɗannan misalai, kuma sun haɗa da:

Kainuwa dashen mai kowa
Rashin jini rashin tsagawa

Salon Mutuntawa: Mutuntawa dabara ce ta jawo hankali, inda mawaƙi zai ɗauki halayya ta mutum ya ɗora wa dabba ko wani abu (Sarɓi, 2007). A wannan waƙa ta KUSHEWA, mawaƙin ya yi amfani da salon mutuntawa a baiti na shida. A cikin baitin ya mutunta duniya ta hanyar ba ta matsayin matar aure. Wata matar da wawa ko mahaukaci ke aura. Ga misali:
Duniya budurwar wawa
Matar mahaukaci ko wawa


5.0 Kammalawa


Daga abin da ya bijiro, mun ga ƙoƙari na nuna ko bayyana irin rawar da mawaƙa suke takawa cikin amfani da waƙoƙi da hikimominsu tamkar yadda aladar Hausawa ta tanada. Wannan ya nuna cewa waƙoƙi a matsayinsu na kafa ta bayyana ko isar da saƙonni da ke ɗamfare da harshen Hausa da ake amfani da su a sadarwa ta yau da kullum tsakanin alumma. Waƙoƙin faɗakarwa su ne waɗanda akan rubuta domin a wayar da kan jamaa game da wani abu da mawaƙi ke ganin akwai bukatar yi masa bayani sosai.

Wato waƙoƙi ne da ke ƙoƙarin faɗakar da jamaa dangane da wata matsala wadda ta shige duhu ko kuma mawaƙi ke ganin cewa mutane ba su hankalta da ita ba (Yahya, 1997). Ɗan abin da ya gabata tsokaci ne dangane da yadda mawaƙi ya sanya rigar malanta ya yi waazi game da KUSHEWA ta hanyar tunatarwa da faɗakarwa, domin ya fahimci cewa a yanzu jamaa sun shagala. Wato a nan mawaƙin ya yi amfani ne da rigar malanta ya ja hankalin jamaa a kan su riƙa tuna mutuwa a koyaushe.

A irin tasa hazaƙa da ƙoƙarin gyara alumma, mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya yi amfani da baiwa da kuma fasahar da Allah ya ba shi wajen tsara wannan waƙa domin faɗakar da alumma. Ta irin wannan siga ce mawaƙa kan nazarci wasu abubuwan da suke ganin ba su daidaita da ci gaba da makomar alumma ba. Ta hakan ne kuma suke wayar wa alumma kai kan wasu alamura da suke ganin suna da faida a rayuwarsu. Saboda haka, sai su yi ƙoƙarin jawo hankalin alumma da su rungumi irin waɗannan shawarwari domin su samu kyautatuwar rayuwar duniya da lahira.

MANAZARTA


Abubakar, A. L. (2015): Shahara: Alfiyar Alan Waƙa (Shahara Sanadin Sanina), Kano: TASKAR ALA GLOBAL LTD.

Barista, M. L. (2011): Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), Vol. 1, Kano: Iya Ruwa Publishers

Dennis, J. (1704): Available at Literature of the 20th Century to the Present (2008) “English Literature”. Microsoft R. Encarta R (DVD), Redmond WA, Microsoft Corporation.

Gusau, M. S. (2003): Jagoran Nazarin Waƙar Baka, Kano: Benchmark Publishers Limited.

Halilu, S. (2015): Jigon Faɗakarwa a Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar, Unpublished M.A. Thesis, Nigerian Languages Department, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Halliday, M. A. K. (1964): The Linguistic Science and Language Teaching, London: Longman

Rubin, D. C. (1995): Memory in Oral Tradition: The Cognitive Pschology of Epic, Ballads and Counting Out Rhymes, New York: OUP.

Sarɓi, S. A. (2007): Nazarin Waƙen Hausa, Kano: Samarib Publishers.

Woolger, D. & Ogungbeson, K. (1978): Images and Impressions: An Oxford Senior Poetry Course, Oxford University Press.

Yahya, A. B. (1997): Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: FISBAS Media Services.

Yakasai, S. A. (2014): “Some Major Themes in Hausa Responsorial Songs in Aminu ALA’s Performance”, in Current Perspectives on African Folklore: A Festschrift for Professor Ɗandatti Abdulkadir, Zaria: ABU Press

--------------- (2012): Jagoran Ilimin Walwalar Harshe, Sokoto: GARKUWA Media Services

RATAYEN WAƙAR KUSHEWA

Ranar da ba tsimi da dabara
Ranar da za mu kwanta kushewa

Mai izgili shira shi shirawa
Ba ya zuwa ga ɓarin dubawa
Ina uba a gun duka wawa
Abu-Lahabi ya ƙarewa
Uban maƙaryata mai kwarwa
Abdul-Sululu ya sheƙewa
Uba ga Jahilai mai tsiwa
Abu-Jahala ya taɓewa
Ga mutakabbirin Misirawa
Fir’auna ya yi ya kwantawa
Karyar Ubangiji mai kowa
Komai gudu tana iskewa

Gata ka ke da shi ko kuwa
Nabiyi Mursalai ba kowa
Tun daga Adamu na Hauwa
Uba na talikai har kowa
Cikamakon Nabiyi ɗan baiwa
Wanda da kansa an ƙarewa
Man La Nabiyi badahu kowa
Mai izini na ceton kowa
Wa ya rage abin dubawa
Wa ke da matsayin zartarwa
Allah ka sa mu zan dacewa
Mu yo gamon katar ran tsaiwa

A kwan a tashi na zama gawa
Ko ko zaren ya zam tsinkewa
Duniya fa ba ɗorewa
Babu wanda zai ɗorewa
Aminu Ɗankano ta Kanawa
Saƙo na zo na ke idawa
Talla na ke fa ba hargowa
Mai hankali kaɗai ka tayawa
Ga magani a gonar kowa
Mai izgili ka yin hargowa
Allah wadan ido gululu
Idon da babu tsinkayowa

Da kunnuwa da ke jin sowa
Fage na gargaɗi doɗewa
Da sau da ke zuwa ga fasadi
Ba sa zuwa ga amfanarwa
Da sautuka da kan furtawa
Ba furucin da zai shiryarwa
Da baituka da kan tsarawa
Bisa hululu don sheƙewa
Five sensory organs dubawa
Gani da ji da saurarawa
Shaƙa da ɗanɗanon ganewa
Da ji na zahirin ganewa

Dukkansu mai halittar kowa
Ya yi su don mu zan ganewa
Mu zan rabe kaloli tsanwa
Mu bautace shi ba ƙosawa
Abin bugun gaba gun bawa
Tsoron mamallaki mai kowa
Dukkan abin da yai farawa
Tabbas gare shi kwai ƙarewa
Da ka ji Alhudusi ta zowa
Sai ka ji Alfana’u ƙirewa
Wannan kaɗai fa ya ishi bawa
Taho da waiwayen dubawa

Duniya budurwar wawa
Matar mahaukaci ko wawa
Gidan maras gida mai ƙwawa
Gidan maras rabo ran tsayuwa
Wa ke biɗar ganin ruɗewa
Yana ga mai sahun miƙewa
Mai tara dukiya don ƙwawa
Zato yake ana ɗorewa
Ruɗi na dukiyar Tarawa
Ta sa shi ya zamanto wawa
Bawan ciki da bai ƙosawa
Kullum a bashi bai turewa

Kainuwa dashen mai kowa
Saman ruwa take tohowa
Gamji sassaƙa da sarewa
Ba ta hana ka kai tohowa
Rashin jinni rashin tsagawa
Ana zuwa ake iskewa
Sarari mai wuyar a ƙurewa
Mai sa matafiya sarewa
A kwan a tashi mai gillewa
A kwana wataran ba kowa
A yau da ni ake damawa
Ina ta jan zaren saƙawa

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments