Maƙalar da aka gabatar a
taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa na farko a kan Nazarin Hausa a Ƙarni na
21 wanda Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano, ta shirya
daga ranar Litinin 10 zuwa Alhamis 12 ga Nuwanba, 2014.
IBRAHIM ABDULLAHI SARKIN SUDAN
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe
Jami’ar Jihar Kaduna, Kaduna, Nijeria
Gabatarwa
A yanayin tunani na ɗan’adam,
mace takan amsa sunanta ne idan ta fara mallakar hankalinta. Shi wannan mallaka
na hankali, yakan zo ne da yawan shekaru. Duk da yake kaifin tunani ko saurin
mallakar hankali sukan bambanta daga mutum zuwa mutum. Haka kuma yanayin
abincin da aka ɗabi’antu da ci da muhallin da al’umma take zaune, sukan yi
tasiri ga bayyanar alamonin shiga budurci ga mace. Duk da haka adadin shekarun
da ake ɗammahar mace ta fara ganin ɓullowar wasu siffofi a jikinta kamar nono
da gashin hammata da na gaba, suna kamawa daga shekara bakwai zuwa goma. Sannu
a hankali har ta fara jin sha’awa musamman ta ɗa namiji a ran ta. Wannan yanayi
yakan kai ƙarshe ne idan ta fara ganin al’ada (jinin haila).
Kowace al’umma takan yi
tanadi na musamman ga irin waɗannan yara mata na yadda za su tunkari wannan
sauyin da kuma yadda falsafar rayuwarsu za ta kasance. Daga cikin irin waɗannan
al’adu akan sami hani da aikata wasu al’amurra saboda munin da ke gare su ga
yanayin da ake ciki. Wasu al’adun kuma sun ƙunshi horo ne ga aikata wasu
abubuwa saboda ganin irin taimakon da za su ba rayuwar ta budurwa a wannan
yanayin.
Wannan nazari, zai mayar
da hankali ne wajen duban yadda al’ummar Maguzawa suka ɗauki lamarin Budurci da
kuma irin tanade-tanaden da al’adunsu suka yi mata. An keɓe wannan nazari ne ga
Maguzawa, bisa tunanin cewa, su ne Hausawan asali da al’adunsu na gargajiya
suka yi tasiri a kan su. Haka kuma nazartar waɗannan al’adu za su taimaka wajen
kwatanta halin da budurcin Hausawa ya sami kansa a ciki a yau ta la’akari da
talalaɓiyar zamani.
Maguzawa
Nazarce- nazarcen da
masana suka yi a baya a kan al’ummar Maguzawa, zai iya wadatar da masu nazari a
kan ko su wane ne waɗannan mutanen. Amma a ƙoƙarin tabbatar da dugadugan wannan
nazarin, akwai bukatar a yi ‘yar shimfiɗa don a waiwayi wasu ayyukan da suka
gabata wajen fayyace mutanen da ake kira Maguzawa. Misali, ayyuka irin na
Ibrahim (1982) da Last (1993) da Abdullahi (2008) sun tabbatar da cewa, ba wasu
mutane ne ake kira Maguzawa ba, illa Hausawan asali waɗanda ba musulmi ba, waɗanda
yanayin rayuwarsu ta dogara ne ga tunaninsu da al’adunsu da addininsu na
gargajiya. Maguzawa Hausawa ne waɗanda suka sami wannan suna daga ’yan’uwansu
da suka karɓi addinin musulunci. Su kuma da suka zaɓi zama cikin yanayin
addinin nasu da al’adunsu na gargajiya, aka kira su Maguzawa. Duk da yake
musulunci da kiristanci da yanayin zamantakewar Hausawa na zamani ya yi
tasiri matuƙa a rayuwar Maguzawa, har yanzu ana samun su a wasu sassa na
jihohin Katsina da Kano, da Zamfara a Nijeriya.
Budurci a Yanayin
Tunanin Maguzawa
Budurci a al’umar
Maguzawa wata rayuwa ce da ’yanmata suke shiga daga lokacin da suka fara ganin
alamar balaga zuwa lokacin da za su yi aure. A wannan lokacin ne ’yanmatan
Maguzawa suke gudanar da wasu al’adu da ke ba da dama namiji ya kusance su don
samun abokin zama a matsayin ma’aurata. Waɗannan al’adun sun ba da damar
budurwa ta saki jiki, ta darje, ta zaɓi saurayin da take ganin za su iya gina
dangantakar soyayya da shi, wadda ake ɗammahar ta kai ga aure. Bayan saurayi ya
ga budurwa a kasuwa ko a wurin wani buki, ya nuna yana son ta, akwai wata dama
da al’ada kan ƙara ba shi don ya tabbatar wa jama’a ko yarinyar ko wasu masu
sha’awar ta cewa, da gaske yake yi. Waɗannan al’adu sukan tabbatar wa iyayen
Budare cewa, ’yarsu tana da masoya. Wannan zai ba su haske su yi shawarar wanda
suka ga ya dace, ta yadda za a ba shi dama, a kuma sallami sauran da ba a so. A
tunanin Maguzawa, yanayin budurci wata ishara ce ga iyaye su san cewa, ’yarsu
ta fara fafutikar barin gida. Wasu daga cikin waɗannan al’adu, ba a
ɗammahar yarinya da fara aiwatar da su in ba ta kai wannan matsayi na budurci
ba.
Al’adun Maguzawa da Suka Shafi Bayyanar da
Budurci
A wannnan fasalin, za a
waiwayi al’adun tabbatar da budurcin Maguzawa tare da fayyace abin da aka
tanada na aiwatar da kowace al’ada.
Gaisuwar Makaɗi
A lokacin kaka akan sami
makaɗa daga cikin Maguzawa waɗanda sukan zagaya ƙauye-ƙauye don nishaɗantar da
jama’a da neman kuɗi. Idan makaɗi ya sauka a ƙauye zai nemi gidajen da ’yanmata
suke. Zai tafi wajen maigida ya ce, yana neman izinin ya zo rana kaza ya yi wa
Wance wasa. Idan maigida ya amince, to za a sa rana ta musamman. Kafin wannan
ranar, makaɗin zai tabbatar da labari ya kai ko’ina musamman ga samarin da ke
wannan ƙauyen da kewaye. Idan ranar ta zo, samari da ’yanmata za su haɗu. Makaɗi
da jama’arsa za su yi ta kiɗa, ’yanmata suna rawa. Su kuma samari za su yi ta
musu kari/liƙi. Wannan ya sa kuɗi, ya ce budurwa kaza ta fito ta yi rawa, wani
ya zo ya ɗora a kai. Ta haka ake gane masoyan budurwa da farin jininta. Idan
jama’a sun watse, makaɗi kan yi godiya wurin maigida, ya ƙara gaba. Duk karin
da samari suka yi wa ’yanmata na makaɗin ne. Su kuma samari sun sami damar da
za su nuna son su ga budurwa. Daga nan sai dangantaka ta ƙara ginuwa. Su kuma
’yanmata wata dama ce da za su ƙara tabbatar da masu son su ko farin jinin da
suke da shi. Abin murna ne ga budurwa da iyayen ta, a ga ana ta karakaina a
kanta. Wannan ya nuna tana da farin jini ke nan. Miji kuma sai ta
zaɓa.
Shasshawa/Jarfa
Shasshawa ko Jarfa tsaga
ce ƙanana da ake yi a jikin mata don ado. A lokacin kaka ‘yanmatan unguwa ko ƙauye
sukan keɓe wani lokaci su gayyaci wanzami don ya yi musu irin waɗannan
tsage-tsage a jiki. Wanzaman sukan zo ne tare da makaɗi. ’Yanmata za su zauna
bainar jama’a su bayar da ƙirjinsu da bayansu a yi musu Shasshawa. A wannan
lokacin ne samari za su ta yi wa makaɗin da wanzamin kari/liƙi. Saurayin da ya
yi fice wurin son yarinya shi zai yi wa wanzami kyauta mafi yawa da cika ido.
Haka kuma, shi zai kawo wa budurwarsa ɗan akuyan da za ta sallami wanzami da
shi. Ita ma uwar budurwa za ta ba wanzamin zani idan an watse taro a matsayin
sallama. Wasu Maguzawan sukan yanka kaji, a yi abinci a ci a wurin taron. A
wànnán gidan wanzamin da makaɗan za su kwana. Idan gari ya waye, za a sallame
su, su tafi, sai kuma an ƙara gayyatar su. Wannan shi ake kira jarfa, wasu kuma
su kira shi shasshawa. Duk saurayin da ya kasa ɗaukar ɗawainiyar wannan tsagar,
ko ya kasa taɓuka abin kirkin da zai tabbatar wa jama’a lallai shi masoyin ta
ne, to zai iya rasa ta a matsayin matarsa.
Wasannin da Bera Kan Shirya
A wasu ƙauyuka na
Maguzawa, akan zaɓi wani saurayi a matsayin shugaban ’yanmatan ƙauyen. Ana
kiran wannan saurayi bera (béerà). A lokacin kaka, Bera kan
karɓi ’yanmata daga hannun iyayensu su rinƙa zagayawa daga ƙauye zuwa ƙauye ko
daga unguwa zuwa unguwa suna yin wasa. Zai ba iyaye tabbacin ’yanmatan suna
hannunsa. Duk abin da ya same su shi ne. Za su yi kwanaki da yawa ba su gida.
Idan aka je fagen wasa, makaɗi zai nemi alfarma wurin Bera da ya ba shi
’yanmatan su yi masa rawa yana kiɗa. Su kuma samari za su yi ta nuna soyayyarsu
ga ’yanmatan nan ta hanyar yi musu kari/liƙi. Abin da aka samu za a raba
tsakanin makaɗi da Bera. Shi kuma Bera ya sami abin da ya ba ’yanmata.
Bera yana taƙama da makaɗi, shi kuma makaɗi yana taƙama da ’yanmata. Su kuma
’yanmata suna taƙama da samari. Ko da budurwa ta nuna tana son saurayi, ba za
ta yarda da shi ba, ko ta amince masa su yi zance, sai da yardar Bera. Shi kuma
Bera ganin cewa, ya ɗauko alƙawari tsakaninsa da iyayen ’yanmatan, to ba zai
yarda ya bar budurwa ta bi saurayin da bai amince da tarbiyarsa ba. Shi ke da
ikon ya ce budurwa ta tafi wurin Wane, kada ta je wurin Wane. Haka kuma shi ke
da ikon ya ce ga lokacin da za ta dawo, ko ya ba da sharaɗin kada a wuce lokaci
kaza. Shi kuma saurayi, Bera zai ja kunnensa cewa, idan ya saɓa masa, kowane
irin mataki soyayyar ta kai zai iya ruguza ta. Ko da suna son junansu, sai dai
su haƙura. A lokacin irin waɗannan wasanni, farin jini ’yanmata yakan fito a
fili. Haka su ma samari sukan sami damar nuna soyayyarsu da gane budurwar da ke
son su ta yadda za a ci gaba da gina dangantakar har a kai ga aure.
Gaɗa
A lokuta daban-dabam,
bayan an gama cin abincin dare, ’yanmata sukan haɗu a wani fili a unguwa ko a ƙauye
don yin wasanninsu na gaɗa. A nan ma akan sami makaɗan da sukan zo su taya su
cashewa. Su kuma samari suna amfani da wannan damar wurin sa kuɗi ko wani abu
ga wata budurwa don ta fito ta yi rawa. Idan tana da masoya da yawa a wannan
fili, lokacin za su fito su nuna, ta hanyar ajiye kuɗi su sa ta yin rawa. Ita
ma a irin wannan wuri takan nuna ra’ayi ko rashin son saurayi. Idan ta ƙi
fitowa ta yi rawa na kuɗin da saurayi ya sa, hakan ya nuna ba ta ra’ayinsa.
Wanda ta yi rawa a kan bukatarsa, to shi ake gane tana so. Daga nan sannu a
hankali wanda ta nuna tana son zai yi ta gina dangantakar har ta kai ga wani
mataki.
Hikimomin Al’adun Bayyana Budurcin Maguzawa
Da dama daga cikin
Hausawa za su kalli waɗannan al’adu da mummunar fuska musamman saboda ɓirɓishin
rashin wayewa ko kwamacalar da ke ciki. To amma idan da za a nazarce su da idon
basira, a kuma kwatanta su da yanayin wayewar Hausawa a yanzu, za a yaba
da hikimar Maguzawa da suka assasa waɗannan al’adu kuma suka jaddada su. A
wannan fasali, za a baje waɗannan al’adu a faifan nazari don zaƙulo alfanun da
suka yi wa rayuwar ta Maguzawa wanda ya samar musu da kariyar mutunci ta
fuskoki da dama.
Ba Samari da ’Yanmata
Damar Bayyana Soyayya
Kunya da rayuwar Hausawa kamar tsoka da jini
suke. Wannan al’ada ta kunya tana daga cikin ɗabi’un da suka ƙara bayyanar da
kimar Bahaushe a idon duniya tun fil-azal. Akwai kunya matuƙa ga saurayi ya
fito kai tsaye ya ce wa mace yana son ta. Babu laifi ya yi ta kiwon hankalinta
da sha’awar siffofin jikinta da kuma yaba nasabarta. Haɗuwar da ake yi a waɗannan
wurare tsakanin samari da ’yanmata, inda za su sa wa budurwa kuɗi ta fito ta yi
rawa, ko in tana rawa saurayi ya yi mata kari/liƙi, wata dama ce da saurayi ya
samu ta fitowa ya bayyana so. Wannan saɓani ne ga abin da ke faruwa a yanzu,
inda samarin Hausawa ke cire takunkumin kunya da al’ada ta ƙargama musu, su
tunkari budurwa kai tsaye don su bayyana mata ra’ayinsu na soyayya.
Wannan ba al’adar Hausawa ba ce, kuma ga dukkan alamu samo ta aka yi daga wani
tunani na daban. Su ma ‘yanmata ko budare a nasu ɓangaren, wata dama ce da za
su fito kai tsaye, su nuna amincewa ko rashin amincewa da saurayi ba tare da
munafunci ko yaudawa ba. Da zarar saurayi ya sa kuɗi aka ƙi fitowa a yi masa
rawa, ya ga alamar babu haske a wannan wurin. Ita kuma ta sami shedu da yawa da
za su tabbatar da cewa, tun farko ba ta amsa masa ba. Wannan saɓani ne ga abin
da ke faruwa a yanzu. Sai a yi shekara da shekaru ana yaudarar saurayi, alhalin
ba a da niyyar auren sa.
Ishara ga Iyaye da Dangi
Waɗannan al’adu wani
hannunka-mai-sanda ne ga iyayen ’yanmata da samari su san ra’ayin ’ya’yan nasu
a kan lamarin aure. Da zarar iyayen budurwa ko wakilansu kamar su Bera suka ga
alamar inda ra’ayin ta ya karkata a fagen aiwatar da waɗannan al’adu, an ba su
hasken fara gudanar da bincike tun kafin iyayen saurayi su fito. Wannan kai
tsaye ya saɓa wa irin rayuwar ƙarya da ake gudanarwa a yanzu. Budurwa sai ta yi
shekara da shekaru tana tare da saurayi ko ma samari da yawa, ba tare da
iyayenta sun sani ba. Wannan yanayi da ake ciki yanzu, ba ya ba iyaye damar
sanin halin da ’ya’yansu ke ciki ta fuskar mu’amala da ake sa ran ya kai ga
aure.
Kare Ɗiyaucin ’Ya’ya Mata
Al’adun bayyana budurcin
Maguzawa, sun yi tanadi na musamman wajen kare ɗiyaucin ‘ya mace. Wannan ya ƙara
tabbatar da wayewar Maguzawa. Dabarar da ake yi wajen damƙa amanar ’ya mace ga
Bera, wata katangar ƙarfe ce a gare su. Irin amanar da ke tsakanin wanda suka
ba ’ya’yansu, da kuma dagewar da yake yi na ganin bai ci amanarsu ba, ta hanyar
barin a yi abin da aka ga dama da su, haƙiƙa wani abin sha’awa ne. Wannan
dabara ta Maguzawa ta yi daidai da koyarwar musulunci na rashin bayar da dama
ga mace ta yi tafiya ita kaɗai ba tare da rakiyar muharraminta ba. Wannan ya ƙara
fito da wautar wayayyun Hausawa a yanzu da suke barin ’ya’yansu mata suna
tafiya su kaɗai na kwana da kwanaki ba tare da kulawar kowa ba. Ashe ba zai
zama abin ka-ce-na-ce ba idan aka ce Bamaguce ya fi wayayyen Bahaushen zamani
hankali da zurfin tunani musamman a irin wannan lamari.
Fayyace Kyauta Tsakanin Saurayi da Budurwa
Duk abin da aka yi a ƙudundune,
to ƙarshen ta a ji kunya. Waɗannan al’adu sun yi tanadin fayyace kyauta
musamman na farko-farkon gina soyayya daga saurayi zuwa ga budurwa a bayyane.
Idan saurayi na son budurwa, dole a irin wannan yanayi ya fito bainar jama’a ya
sa kuɗi a kan ta, kuma a bayyana wa jama’a. Haka kuma idan kari/liƙi zai yi
mata, a fili ake yin hakan. Shi ma Bera, haka yake kasa abin da aka tara a
wajen wasa, ya ba ’yanmata nasu. Wannan ya sa Maguzawa suka sami kariya daga
tarkon zargi ko ƙazafin cin kuɗin saurayi daga budurwa da iyayenta. A duniyar
Hausawa ta yau, Allah kaɗai ya san yawan rikice-rikicen da ke maƙale a kotuna
na zargin cin kuɗi ko dukiya daga budare da iyayen su. Wannan yana faruwa ne
saboda a duƙunƙune ake yin kyautar a lokacin da ake cikin shauƙin soyayya.
Samun Damar Zaɓe
Duk abin da aka bayyanar
da yawa, to mutum yana da damar darjewa ya zaɓa. Ga samari, waɗannan al’adu sun
ba su damar ganin ‘yanmata da yawa suna fitowa wajen rawa. Ta nan saurayi zai
zaɓa ya darje, kafin ya fara tunanin jawo ra’ayin budurwar da ya ji yake so.
Haka su ma ‘yanmatan, sukan yi amfani da damar karakainar samari a kan su, ta
yadda sai sun zaɓi wanda ya yi musu.
Dabarun Inganta Tattalin arziki
Ganin irin alherin da
wanzami da makaɗi da Bera suke samu a sakamakon aiwatar da waɗannan al’adu, ya
nuna a fili cewa, wasu hanyoyi ne na farfaɗo da tattalin arziki. Daga cikin
abin da suke samu na kari/liƙin da ake yi wa ’yanmata, za su warware matsalolin
rayuwa da suka yi musu dabaibayi musamman a wannan shekarar. Wannan ba ƙaramar
dama ba ce da hikima ta amfani da waɗannan al’adu a sami abin da ake so.
Al’adun sun ba su damar mallakar abin da zai ƙara wa noman da suka yi auki,
kuma su gudanar da hidimomin da suka sa a gaba cikin sauƙi. Haka kuma wannan
damar ta kare su daga wulaƙanta a hannun mutane ta hanyar roƙo ko neman
gudunmuwar dangi idan wata lalura ta taso.
Naɗewa
Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin
fito da wasu al’adun nuna budurcin Maguzawa tare da bayyana hikimomin da ke ƙumshe
a cikinsu. Waɗannan al’adu kamar yadda aka yi bayaninsu, sun haɗa da gaɗa da
wasannin da Bera kan shirya da shasshawa da ziyarar makaɗi. Iyaye suna amfani
da waɗannan al’adu ta hanyar sanin ra’ayin ’ya’yansu mata da kuma bayyanar da
su ga mabiɗa ta yadda za su gina dangantakar da ake tunanin ta ɗore har abada.
Ta fuskar manema aure kuma, su ma fitowar mata a irin waɗannan al’adun sukan sami
damar zaɓe. Su kuwa wanzamai da makaɗa da Bera, wata dama ce ta inganta yanayin
rayuwa, baya ga abin da suka samu na noma. Waɗannan al’adu sun taimaka wa
Maguzawa kasafta yanayin rayuwa da tsara ta, baya ga nishaɗantarwar da kowane
rukuni suka amfana da ita.
1 Comments
Mun gode. Allah ya taimaka.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.