Abdullahi, I. S. S. (2008) “Fitattun Ɗabi’un Maguzawa” Maiduguri Journal of Linguistics and Literary Studies (MAJOLLS) Vol. X Department of Languages and Linguistics, University of Maiduguri, Page 77–82 ISSN: 1595-6873
Fitattun Ɗabi’un Maguzawa
Daga,
Ibrahim
Abdullahi Sarkin Sudan Ph. D
Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
e-mail: ibrasskg@gmail.com
GSM: 0803 6153
050
1.0 GABATARWA
Kowace al’umma ta duniya akwai irin kallon da
wasu mutane na daban suke yi mata. Wannan kallo yakan bayyana ra’ayi a
MaƘasudin
wannan maƘala
shi ne, nazarin fitattun ɗabi’un Maguzawa da ninyar a yi
musu adalci duk da saɓanin addini da ke tsakaninsu da
’yan’uwansu Hausawa. A ƘoƘarin cimma wananan
manufa, za a so sanin ko su wa ake kira Maguzawa, kuma me ya bambanta su da
mutanen da ake kira Hausawa? Sanin wannan zai taimaka wa tsokacin da za a yi a
2.0 MAGUZAWA
Masana da yawa sun yi rubuce-rubuce a
Ta fuskar tarihi kuwa, wannan suna da ake yi
musu a ganin masanan, ya samo asali ne bayan da wasu daga cikin Hausawan suka
karɓi
addinin musulunci a matsayin addininsu. Wannan ya sa suka yi ƘoƘarin bambanta kansu
da waɗanda
ba su kaɓi
addinin ba ta hanyar kiransu da suna Maguzawa. Bayan wannan kuma,
musulmin sun bambanta kansu da Maguzawa ta hanyar ɗaukar
kansu su ne Hausawan. A taƘaice,
Hausawa su ne musulmin da Hausa ita ce harshensu. Su kuma Maguzawa su ne Hausawan
da ba musulmi ba kuma addininsu shi ne addinin gargajiya wanda suka gada daga
iyaye da kakanni. To ko dai yaya lamarin ya kasance, Maguzawa Hausawa ne. Ba
su da wani harshe illa Hausa, kuma Ƙasar
Hausa ita ce Ƙasarsu.
3.0 ƊABI’UN MAGUZAWA
Sakamakon bincike-binciken da masana suka yi da irin
kallon da mutane suke yi musu, da mu’amalar da ake yi da Maguzawa sun tabbatar
da cewa, Maguzawa mutane ne da ke da kyawawan halaye da ɗabi’u masu ban sha’awa da Ƙayatarwa in ban da ɗan abin da ba a rasa ba da ya saɓa wa rayuwar mutane musamman ‘yan’uwansu Musulmi. A
wannan fasalin za a kalli yadda halaye ko ɗabi’un Maguzawa suke a idon manazarta.
3.1 Tsare Gaskiya
Hausawa suna yi wa gaskiya kirari da “dokin Ƙarfe” Maguzawa mutane ne da aka sani da faɗar gaskiya. Duk wanda ya yi hulɗa da Maguzawa ta kasuwanci ko a wata mu’amala zai
tabbatar da haka. Abu ne mai wuya dattijon Bamaguje ya buɗe baki ya yi Ƙarya don
kawai ya kare mutuncinsa ko don ya sami wani abin duniya. Wannan ba abin mamaki
ba ne domin tun a tarbiyyarsu ta tsafi akan ladabtar da su daga illar yin Ƙarya. Misali, Maguzawa suna da tsafin gida. Kusan kowane
gida akan ajiye wani jan dutse, ko tama ko dutsen ƘanƘara a Ƙofar gida ko a wani wuri na musamman a cikin gidan, a
matsayin tsafin gidan. Wannan tsafin da shi akan dogara wurin gudanar da
al’amurra a gidan. Idan ana gardama a kan wani abu ko aka zargi wani da aikata
wani abu ya musanta, akan zo wajen tsafin gida a rantse.[1]
Duk Bamagujen da ya yi imani da tsafin gidansu, ya kuskura ya rantse da shi a
kan Ƙarya to babu shakka ranar zai baƘunci lahira.
A wani misalin kuma, a al’adar Maguzawa, kafin a kai
amarya ɗakinta
(gidan miji), akan kai ta wurin tsafin da suke bauta wa ta rantse a kan ba ta
taɓa sanin ɗa namiji ba. Idan ta rantse kan Ƙarya to takan tozarta kai tsaye ko ma ta rasa rayuwarta
gwargwadon irin tanadin da tsafin ya yi.[2]
Ire-iren waɗannan
tsafe-tsafe su suka yi wa Maguzawa jagoranci tun fil azal dangane da hana su
yin Ƙarya. Bamagujen asali, yakan gwammace a kashe shi da ya
yi Ƙarya a kan abin da bai faru ba.
3.2 Taimakon Juna
Maguzawa mutane ne masu ɗabi’ar taimakon junansu. Babu mai raba Bamaguje da ɗan’uwansa. Irin zaman da Maguzawa ke yi na gandu shi ya
tabbatar da haka. Idan Bamaguje yana da ɗan da ya isa aure, shi zai yi masa komai na hidimar
auren, kuma ya ci gaba da ciyar da shi. Shi kuma ɗan don nuna godiyarsa, yakan ci gaba da aiki a gonar uban
(gandu) har da matarsa. Kuma duk amfanin gonar da aka samu na uban ne. Idan
bukin Bamaguje ya tashi na aure ko haihuwa ko mutuwa, komai nisan inda dangi
suke za su zo muddin dai suka sami labari. Kuma zuwan da za su yi ba hannu sake
ba. Hatta da karen gidan Bamaguje sai ya san ana buki a gidansu. ‘Yan’uwa sukan
kawo gudummawa fiye da yadda ake tsammani. Rashin abin yin buki bai sa Bamaguje
ya ɗaga bukin gidansa, domin ya
san dangi za su taimaka.
3.3 Ɗiyauci na Ƙyamar Ɗan Hali
Sata ga Bamaguje mummunar ɗabi’a ce. A al’adar Maguzawa, abin kunya ne a kama mutum
ya yi sata. Laifin sata a tunanin Maguzawa yakan shafi ’ya’ya da jikoki da ma
zuri’a gaba ɗaya ta
hanyar hana masu samun aure ko Ƙyamar
auren mata daga wannan zuri’ar. Maguzawa Sata takan sa Bamaguuje barin gari har
abada. Don kare al’umar Maguzawa daga wannan mummunar ɗabi’a an yi tanadi na musamman ta hanyar tsafin da suke
bauta wa. Misali, ga masu bauta wa tsafin Uwar gona,[3]
ba yadda za a yi su yi sata su kwana lafiya. Kuma kayansu, musamman amfanin
gona bai satuwa ga kowane mahaluki. In kuwa har mutum ya kuskura ya yi satar,
to cikinsa zai kumbura ya mutu. Wanda ya yi satar da wanda ya sayi kayan satar
da wanda ya ci kayan satar duk za su baƘunci
lahira a wannan ranar. Haka kuma dole ne a ja gawar wanda Uwar gona ta kashe (a
sakamakon satar da ya yi) da igiya, ana barbaɗa toka har wurin da za a bizne shi. Ba a yi masa shagali
ko wani bukin mutuwa. In ba haka ba to duk ‘yan’uwansa maza za su rinƘa mutuwa ɗaya bayan ɗaya cikin
‘yan kwanaki.[4]
Gudun irin wannan abin kunya shi kan sa sai dai Bamaguje ya ga an kamo ɓarawo amma ba a zarge shi da yin sata ba. Hatsin Bamaguje
yakan shekara cikin gona ba tare da tsoron wani ya kwashe ba.
3.4 Kare Ɗiyaucin Zuriya
Yin lalata (tarawa tsakanin mace da namiji ba tare da
aure ba) yana daga cikin munanan ɗabi’u da Bamaguje ya nisanta. Don haka suke alfahari da tsarkakakkiyar
zuri’a. Kamar yadda bayani ya gabata, dole ne kafin a kai mace ɗakin mijinta sai an tabbatar da ta kai budurcinta. In ba
haka ba ya zama abin kunya gare ta, da iyayenta da ma danginta. Irin al’adun da
ake gudanarwa na tsafi don tabbatar da ɗiyaucin mace sun bambanta daga wuri zuwa wuri, duk da
yake akwai Maguzawan da ba su gudanar da wannan al’adar. Ta ɓangaren namiji shi ma tun a wurin tsarance,[5]
da zarar ya yi ƘoƘarin lalata yarinyar da yake nema aure asirinsa zai tonu,
ya tozarta a al’uma, ya ma rasa mata. Dole ya bar gari. A wurin Maguzawan Kainafara[6]
ma har bayan an haihu sai sun yi tsafin tabbatar da ɗan nasu ne ko ɗan zina ne. Don haka maza da mata a al’umar Maguzawa da wannan takunkumi
ake haihuwarsu, su kuma girma da shi, su kiyaye shi don kare mutuncinsu da mutuncin
zuri’arsu.
3.5 Ladabi Da Biyayya
Maguzawa mutane ne masu ladabi da biyayya ga na gaba.
Suna yi wa ’ya’yansu tarbiya a gargajiyance ta yadda yaran su ma za su tashi
suna girmama mutane, ba lalle sai iyayensu kaɗai ba. Bamaguje ba ya walaƘanta iyayensa. WataƘila ɗaukar nauyi da biya musu bukatun rayuwa har bayan sun yi
aure shi ya sa ’ya’yan suke tausayawa, suna yi wa iyayen duk abin da ya kamata
su yi waɗanda
al’ada ta tanada a matsayinsu na iyaye. A lokacin da uba ya tsufa, ya fara
rauni wurin noma, ’ya’ya manya su ke da alhakin ɗauke masa ci da sha. A al’adar Maguzawa, komai tsufan
mutum, in ya yi magana ta zauna. Ba mai musawa ko sauya masa magana. Wani abin
sha’awa ga rayuwar Maguzawa dangane da tarbiyya ita ce, sukan matsa nesa da
’ya’yansu idan manya za su yi hirarsu wadda ba su son ’ya’yansu su koya. Haka
su ma mata suke yi a cikin gida.
3.6 RiƘon Amana Da AlƘawali
Bamagujen mutum yana da riƘon amana. Duk abin da za ka ba shi don ya ci amanar wani,
gara ya rasa abin da yake nema na rayuwa. Haka ma lamarin alkawari yake gare
shi. Misali, idan aka ajiye magana da Bamaguje cewa, a haɗu rana kaza ko lokaci kaza, to sai dai ka tarar da shi
yana jira. Suna da riƘon amana musammam dangane
da wani abu da aka ba su su kula da shi kamar gona ko amfanin gona ko ’ya’yan
dangin da suka mutu ko dukiya da dai sauransu.
3.7 Wayo da Daɗin Baki
Masu mu’amala da Maguzawa sun shaide su da wayo wurin
gudanar da al’amurra. Sukan ce abu ne mai wuya ka yaudari Bamaguje ko ka
zalunce shi. Idan kuwa ka ci nasarar yin haka to ka tabbata in ya gane wata
rana sai ya rama, ko da ga ‘ya’yanka ne in ba ka da rai. Wannan ya sa na tuna
da labarin “Dan hakin da ka raina”
na cikin littafin Magana Jari Ce
juzu’i uku. A cikin labarin, Anunu mahaucin birni ya yi wa Bamaguje wayo ya karɓe masa saniya a kan ’yan kuɗi kaɗan. Da Bamaguje ya zo rama cutar da aka yi masa sai da Anunu
ya yi da-na-sani a kan cutar Bamaguje da ya yi. Ta fuskar iya magana kuma, ta
bakin Bamaguje ake jin gangariyar Hausa. WataƘila wannan na faruwa ne saboda zamansu cikin daji da
rashin son gurɓata zuri’a
ta hanyar auren waɗanda ba Maguzawa ba. An haife su a cikin Hausar, da ita suka tashi, da ita
suke magana.
3.8 Son Mutane
Maguzawa mutane ne da ba su da Ƙyamar mutane. Ba su da ɗabi’ar rashin son mu’amala ko sakin jiki da mutane. Ba su
da Ƙyamar cin abinci a kwano ɗaya da wanda ba Bamaguje ba sai dai su a Ƙyamace su.[7]
Ta fuskar auratayya ma, idan ’yarsu ta nace a kan Musulmi take so, sai su bar
ta ta aure shi. Haka ma ba su Ƙyamar
ibadar da Hausawa Musulmi suke yi, kamar salla da azumi. A sakamakon kyakkyawar
mu’amalarsu da mutane, wasunsu har sukan aiwatar da ladubba na addinin
Musulunci kamar faɗar Allah Sarki, Insha Allah, Masha Allah, Bisimilla, Alhamdu Lillahi,
ka ce dai Musulmi ne. Sukan tanadar wa Musulmin da ke hulɗa da su tabarma da buta don yin alwalla da salla idan sun
ziyarce su. Suna gamawa za su naɗe su ajiye a wuri na musamman sai in wani ya zo. Idan suka yi baƘo, galibi sukan ba shi tabarma su koma Ƙasa su zauna. Maguzawa mutane ne masu son raha. Kusan duk
wanda yake kusa da su sukan mayar da shi kamar abokin wasa. Suna sha’awar yin
ba’a da wasa da dariya da mutane.
3.9 Yawan Kyauta da HaƘuri
Maguzawa mutane ne masu kyauta. Abin su ba ya tsone musu
ido. Abin kunya ne su yi baƘo su rasa
abin da za su ba shi na tsaraba. Haka kuma, a wurin mu’amalarsu, mutane ne masu
haƘuri. Ba Ƙaramin saɓani ke sa Bamaguje zare dantse ba, duk da yake ba ya son
a rena shi. Haka sukan yi banza da mutanen da suke tsarguwar su musamman abokan
wasa a kan ɗabi’unsu
da suka saɓa wa
Musulunci. Ba cikin sauƘi akan ga ɓacin ran Bamaguje ko a ga yana buga-in-buga ba.
3.10 Son
Sharholiya
Bamaguje mutum ne mai sha’awar shan giya. Tana daga cikin
abin da ya fi ba muhimmanci dangin shaƘatawa.
Haka kuma suna da sha’awar tara mata da yawa. Ɗaukakar Bamaguje, da matsayinsa, da darajarsa a al’umma
sun dogara ne ga yawan iyalan da ya tara. Haka ma suna sha’awar yin bukukuwa.
Suna kashe dukiyarsu wurin gudanar da buki. Suna ba wasannin dara da gaɗa a dandali muhimmanci. Haka kuma, mutane ne masu
sha’awar doki. Duk Bamagujen da ya Ƙasaita
dole ne ya nemi doki ko dawaki ya ajiye. Akan gane girma ko matsayin mutum ta
la’akari da yawan dawakin da ya zo da su wurin bukin hawan sadaka (Bukin Mutuwa
na Shekara). A irin wannan buki ba abin da Bamaguje yake taƘama da shi, daga doki sai tsafi.
3.11 Taka-Tsantsan Da BaƘon Abu
Maguzawa musamman a wannan zamani sukan guji karɓar baƘo ko baƘon abu sai fa in ya biyo ta hannun shugabanninsu ko kuma
wanda ya san su ya tabbatar musu da cewa, abin nan ba zai cuta musu ba.
Maguzawa mutane ne masu taka-tsantsan da wani baƘo wanda ba su sani ba, ba su san manufarsa ba.
3.12 Yarda da Gabaci
Ƙwarewa kan tsafi da yawan shekaru da yawan dukiya ko
yawan zuri’a su ake la’akari da su wurin ba da shugabanci a al’umar Maguzawa. Ƙwarewa a tsafi ya danganci bayar da magungunan cuta ko
biyan bukatun rayuwa da buwaya da kuma sihirce-sihircen da suka shafi noma da
yin fice a kan sa. Yawan shekaru kuma abu ne da suke girmamawa saboda ladabi da
biyayyarsu. Sun yarda da cewa, “babban yatsa ko ba ta cin tuwo ta iya ɓare malmala. Yawan zuriya kuma abu ne da suke ganin yake
jawo musu martaba a idon jama’a har a yanke shawara kai tsaye ta buƘatar shugaba a gida ya jagoranci unguwa ko Ƙauye. Suna ba shugabanni girma da aiwatar da bukatunsu
kai tsaye. In suka gitta kara ba mai tsallakewa. Irin waɗannan shugabanni su ke yi musu jagoranci a rayuwarsu ta
yau da kullum. Maguzawa sun fi sha’awar su saurari dattijo mai shekaru irin
nasu, ba yaro ba. A kowane lokaci sukan rena sauraron yara, saboda ganin cewa
sun fi su shekaru, ba abin da za su gaya musu na hikima ko burgewa. Sun fi son
su saurari magana mai ma’ana daga dattijo. Wannan shi ya sa ko da wurin buki
aka je, kowane rukunin jama’a sukan zauna ne ta la’akari da shekarunsu.
Maguzawa ba su zama tare da ’ya’yansu suna hira ko shan giya.
3.13 Kiyaye Al’adu
Maguzawa mutane ne masu sha’awar riƘe da kiyaye al’adunsu. Ba su so mutane su yi musu
shisshigi a kan al’adun nasu. Haka kuma ba su kan yi karambani a kan lamarin
wasu Ƙabilu. Duk abin da suka sani dangane da al’adar mutanen
da sukan ziyarce su, suna kiyayewa. Haka su ma suna la’akari da abin da suka
tarar na al’adun mutane idan suna baƘunci.
4.0 NAƊEWA
Wannan maƘala ta yi ƘoƘarin yin adalci ne wajen
kallon Bamaguje kamar yadda aka fahimci yake a zahiri kuma ba tare da amfani da
wani mizani na tarihi ko wata dangantaka wurin auna shi a idon mutane ba. Mu’amala
a cikin wannan al’uma ta Maguzawa na shekaru fiye da biyar don nazartar wasu
al’adu nasu shi ya haifar da wannan nazari. Duk da yake ba a nazarci kallon da
abokan hamayyar su suke yi musu ba don kwatantawa a tabbatar da sahihancin
wannan nazari, a fili yake cewa, Maguzawa mutane ne da ke da kyawawan ɗabi’u
na zahiri kamar yadda rubuce- rubucen magabata suka nuna, kuma wannan nazari ya
tabbatar. Wannan nazari tamkar matashiya ce ga manazarta da su ƘoƘarta kallon kowace
al’uma ta duniya bisa tafarkin da suka ginu a kai.
5.0 MANAZARTA
Adamu, M. T. (1997) Asalin Hausawa da Harshensu. Ɗan Sarkin Kura
Publishers,
Adamu, M. (1976),
“The Spread of Hausa Culture in
Adamu, M. (1977)
“The Economics of Culture Among The Hausa during the Present Millenium A. D.”
Akodu, A.
(2001), Arts and Crafts of the Maguzawa and some Educational Implications.
Gaskiya Corporation Limited. Zaria – Nigeria.
Alhassan, H. da Sauransu (1982), Zaman Hausawa
Aliyu, A. Y. (1973) “Asalin Hausawa” a cikin littafin Bukin Makon
Hausa Jami’ar Bayero Kano,
Bunza, A. M. (1995) “Magungunan Hausa a Rubuce: (Nanzari Ayyukan Malaman
Tsibbu),” Kundin digiri na uku, Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza, A. M.
(2006) Gadon Feɗe
Al’ada Tiwal
Nig. Ltd:
Bunza, A.M. (1990), “HayaƘi Fid Da Na Kogo: (Nazarin Siddabaru Da Sihirin
Hausawa)”, Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano.
Charanchi,
R. (1999), Katsina Dakin Kara: Tarihin Katsina Da Garuruwanta, Northern
Nigerian Publishing Company Limited, Zariya.
Fletcher, D. C. (1929) “The Kai-na-Fara.”
Extract from Re-assessment Report on ’Yanɗaka District, Katsina Emirate,
Furniss, G.
(1999), Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa,
Greenberg, J. (1946) The Influence of Islam on a Sudanese Religion:
Monographs of the American Ethnological Society. J. J. Augustin Publisher,
Ibrahim, M. S.
(1982), “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”,
Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero,
Kado, A. A.
(1987), “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar
Sakkwato.
Krusius, P.
(1915), “Maguzawa” Archiu, Anthropologies, NF Vol. XIV.
Lawal, A. T.
(1986), “Al’adun Hausawa Jiya da Yau”, Kundin Digirin farko Jami’ar Sakkwato.
Madauci
I. da wasu (1968) Hausa Customs Northern Nigerian Publishing Company,
Magaji, A.
(2002) “Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye- yanayensu a Ƙasar
Katsina.” Kundin digiri na uku, Ja’mi’ar Bayero,
Malumfashi,
A. A. (1987) “Hausa Language Speech Usage Norms: A Case Study of Maguzawa
Society in Malumfashi Area”, Bayero University, Kano.
Marriage.
Malumfashi,
A. I. (1988) ‘Wauta A Rayuwar Bafullace: Gaskiya Ko Shaci Faɗi?’ MaƘalar da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani, a Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijerya, Jami’ar Bayero, Kano.
Morel, E.D.
(1968),
Ottenberg,
P. and Simon (Ed.) (1960), Cultures and Ethics of Africa, H. Wolff Book
Mfg.Co., Inc. U.S.A.
Safana, Y.B.
(2001), “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar Safana”, Kundin Digiri na
farko, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Sufi, A. H.
(2001) “Hanyar Kiran Maguzawa Zuwa Ga Addinin Musulunci.” MaƘalar
da aka gabatar a taron Kwamitin Yaɗa
Addinin Musulunci na Jihar Kano.
Tremearne,
A. J. N. (1913) Hausa Superstitions And Customs. John Bale, Sons and
Danielsson, LTD
Yahaya,
Yusuf, A. B.
(1986), “Wasannin Maguzawan Ƙasar
Katsina”, Kundin Digirin farko, Jami’ar Sakkwato.
[1] Muhammadu Sani Ibrahim,
“Dangantakar Al’ada Da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar
Hausawa.” Kundin
digiri na biyu, Jami’ar Bayero Kano, 1982, shafi na 33.
[2] Dubi lamba ta 1, shafi na
171.
[3] Uwar gona aljana ce da Maguwa ke bauta wa. Dubi lamba ta 1, shafi na 32
don Ƙarin bayani
[4] Hirarmu da da wani Bamaguje
mai suna Tukunya Jikan ƘwanƘi (ɗan shekara 82) a Ƙauyen ƘwanƘi cikin
Ƙaramar hukumar Bakori Jihar Katsina, a ranar 22-02-06.
[5] Tsarance wata al’ada ce ta
Maguzawa inda saurayi zai tafi gidan budurwar da yake so ya aura, su kwana
tare kan shimfiɗa ɗaya ba tare da wani abu ya faru ba.
[6] Maguzawan
Kainafara wasu Maguzawa ne da ke zaune a Birchi a da cikin Ƙasar Kurfi ta
jihan Katsina ta
yanzu.
[7] Na tabbatar da haka a
lokacin da nake zagaya Ƙauyukan
Maguzawa don tattara bayanai a kan wasu al’adu
nasu. Ga misali,
na sha hura a Ƙwarya ɗaya da Babban Kada
(shugaban Maguzawan Lezumawa), a Ƙasar
Safana cikin Jihar
Katsina, a lokacin da na ziyarce shi a ranar lahadi 26-02- 06.
1 Comments
[…] Fitattun ‘Dabi’un Maguzawa […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.