Burin wannan tattaunawa fito da
irin gurbin da ke ga Katsina da Katsinawa a farfajiyar karatun Hausa, a duniyar
ilimin Hausa jiya da yau. An waiwayi gurbin ƙasar Katsina cikin ƙasar Hausa da dangantakarta da sauran ƙasashen da Hausawa ke bugun gaba da su. An ƙyallaro haihuwar boko, da yadda Katsina ta agaza
wa naƙudarsa, da karɓar biƙinsa da yayensa. Gudunmuwar fitattun marubutan
adabi irin su Alhaji Abubakar Imam da takwarorinsa, da addibbai irin su Shata,
an kakkaɓe mata ƙura. An harari manyan makarantu
bakwai da ke agaza wa karatun Hausa a Katsina. Takardar ta yi nazarin yadda
Katsina ta ƙwace kambun karatun Hausa daga
shekarar 1967-2014...
----------------------------------------
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
-------------------------------------------
Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na maraba da ɗaliban Hausa sababbi na
shekarar, 2014, a sashen Hausa na Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina a
babban ɗakin taro na Tsangayar Fasaha, na Jami’ar ranar Alhamis 14/08/2014 da ƙarfe goma na safe (10:00am)
TSAKURE
Burin wannan tattaunawa fito da
irin gurbin da ke ga Katsina da Katsinawa a farfajiyar karatun Hausa, a duniyar
ilimin Hausa jiya da yau. An waiwayi gurbin ƙasar Katsina cikin ƙasar Hausa da dangantakarta da sauran ƙasashen da Hausawa ke bugun gaba da su. An ƙyallaro haihuwar boko, da yadda Katsina ta agaza
wa naƙudarsa, da karɓar biƙinsa da yayensa. Gudunmuwar fitattun marubutan
adabi irin su Alhaji Abubakar Imam da takwarorinsa, da addibbai irin su Shata,
an kakkaɓe mata ƙura. An harari manyan makarantu
bakwai da ke agaza wa karatun Hausa a Katsina. Takardar ta yi nazarin yadda
Katsina ta ƙwace kambun karatun Hausa daga
shekarar 1967-2014, a cikin shekarar 1983 da 2010. A duniyar karatun Hausa,
Katsina na da jigajigai (12) da muryoyinsu ke yin zara a wannan ƙarni. An kakkaɓe buzun karatun da waigo irin
gudunmuwar Jami’ar UMYUK ga ƙara wa Borno dawaki. An naɗe tunanin takardar da kakkaɓar gara da waiwayen tarihin
tabbatar da kasancewar “Katsina Rumfar Hausa, Gamji matattarar Tsuntsaye”. Fatar
takardar ka da Katsina da Katsinawa su bari tutar karatun Hausa ta sha ƙura a hannunsu.
Gabatarwa:
Ga al’adar karatu, ɗalibinsa ya yi adalci wajen
nuna wurin da ya karɓo shi, da wurin da ake samun sa, shi ne rabin ilmi ga ma’ilmanta, da masu
neman ilmi. Na sha tunanin, yadda zan fuskanci Katsina ga ɗan karatuna na ɗalibi, a kowane gehe na leƙo, sai in ga babu masoka haki. A fagen tsarin
shugabanci Katsina, M.G. Smith bai rage abin da ɗalibi zai tsinta ba, a
ayyukansa biyu, Government in Katsina da The two Katsina. Idan
aka hangi Katsina da sauye-sauyenta a zangon tarihi, me Yusuf Bala Usman ya
rage da wani ɗalibi irina zai hango? Aikinsa Transformation of Katsina dogon
kogi ne mai faɗi. Da na tsura wa birnin Katsina ido a ma’aunin al’ada, sai na ga Malam
Munnir Mamman ya riga ya share wa Katsinawa hawaye a ayyukansa biyu masu taken:
The Emergence of words in Katsina metropolis da Tarihin Unguwanin
Birnin Katsina, 2011. Da na laɓaɓo ga irin karamci da na samu ga Katsinawa na
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, na fara kakkaɓe teburin rubutu sai na yi kiciɓis da littafin malam Ingawa, Katsina
gidan Kara. Da dai na ga babu wata babbar ƙofa sai na ce, ana wata haka, in ji gwanin rawa
da ya faɗi. Kai tsaye na yi wa wannan takarda take: Katsina Rumfar Hausa Gamji
Matattarar Tsuntsaye.
Kwance Ƙullin Fitilun Kalmomi:
Na san ɗalibai ‘yan’uwana za su so su
ji, don me aka yi amfani da kalmomin “rumfa” da “Gamji” da “ Matattara” da
“Tsuntsaye”? Rumfa dai ita ce mahuta bayan an motsar da jiki an wahala domin a
samu. Rumfa ba domin mutum ɗaya aka yi ta ba don kowa da kowa. Katsina wata
mahuta ce ga Hausawa da maƙwabtansu da baƙinsu na nesa da na kusa. Da
gangan na kawo kalmar “Gamji” domin idan ba a samu sukunin yin rumfa ba, gamji
na ɗauke mata ɗawainiyar. Dalilin Bahaushe ke nan da ke cewa: “Gamji babbar inuwa” wanda
duk ya ratsi ayyukan da aka yi na tarihi da adabi da walwala da al’ada a kan
Katsina, ba zai yi musun kasancewarta “mattatara” ba. A ganin Nufawa, Katsinawa
tsuntsaye ne masu wayo “Kenci” ba su taɓa tabbata a ice/bishiya ɗaya. Don haka, suka barbazu uwa
duniya, suka bar ƙofofin birninsu a buɗe baƙin arzikin na ta kwarara su amfana a amfana da
su. Da fatar an yi wa matambayi susa gurbin ƙaiƙayi.
Maƙasudi:
Babban maƙasudin wannan bincike shi ne, ya lalubo irin
rawar da Katsina da Katsinawanta suka taka a fagen raya ilmin karatun Hausa.
Wace rawa suka taka tun daga haihuwar boko zuwa yau da muke ciki a ɓangaren karatun Hausa da
harshen Hausa da Hausawa da ya sa aka koɗa birninsu. Rumfar Hausa? Shin gabanin rumfar
akwai wata rumfa ko ita ce ta farko? Gagabanin rumfar akwai gamji, ko ita ta ba
da damar shuka itacen gamji karatun Hausa a duniyar ilmin Bahaushe? Ban ce na
san komai a kan Katsina ba, domin baƙo ɗan shekara huɗu a gari bai isa a ce ya tantance komai sarai a garin ba, sai dai dole baƙo ya gane mai masaukinsa a riwayar Ɗankadi mai zari da ke cewa:
Jigo :
Mata ta san mijinta
:
Ko daji tag gane shi
:
Komai taron maza
Yara : Tana
bambanta shi.
Ka da in cika ku da gafara sa,
ba ku ga ƙaho ba, ga yadda na hangi Katsina
a fagen ilmi karatun Hausa.
Gurbin Ƙasar Katsina:
Allah Ya zaɓa wa ƙasar Katsina wani irin gurbi wanda ya dace da
ita. Tana maƙwabtaka da Kano da ake yi wa
kirarin Jalla Babbar Hausa. Ta haɗa iyaka da ƙasar Adar/Maraɗi da ake jin daga nan Hausawa suka ɓullo. Tana da danga da ƙasar Zamfara da ake yi wa kirari dandin Hausa. Maƙwabciyar ƙasar Zazzau ce a tsohon tarihi. Idan ban yi son kai ba, zan ce daga cikin
ƙasashen Hausa babu mai irin
wannan gurbi a farfajiyar daularsa. Ashe ban yi washi ba idan na kira ta;
“rumfar Hausa”.
Abin ban sha’awa, Kano da ta yi
ficen bunƙasa a tarihi Katsina ta ba ta
tsaro ku binciki tarihin Ɗanwaire. Ƙasar Kabi da ke bugun gaba da
sarki Kanta Kotal, a Katsina aka auro mahaifiyarsa. Gobirawa da ke ganin da su
da mutuwa uwa ɗaya, Katsina ta koyar da su sanin dabarun yaƙi, ko kun manta da, “A mazaya...”.
Ƙasar Nufe da ke garkuwar ƙasar Hausa a fagen fatauci dole su durƙusa wa Katsinawa. Dakarkari da ke da karin
maganar shiga sojan Badakkare, Katsina ce babbar cibiyarsu. Idan za a yi wa
tarihi adalci, ba za a musanta cewa, babu ƙasa daga cikin ƙasashen Hausa da ke da wannan babban gaba irin na
Katsina don haka iƙirarina na kiran Katsina
“Babban Gamji” ba washi ba ne, karatu ne.
Bincike ya tabbatar da har gobe
sarautar Maraɗi ana ce da ita “Sarkin Katsina” sarautar cibiyar Zamfara ‘Gusau’ sunanta
Sarkin Katsinan Gusau. A taƙaice, kudancin Katsina daga Katsina zuwa Karaɗuwa da Zamfara ƙasar Kwatarkwashi da Tsafe suna cikin Katsinar
Laka. Dukkanin daulolin da muke da su ƙasar Hausa, Gobir, Kebbi, Kano, Zazzau, da sauransu babu mai irin wannan
babban baki na laso zango uku bayan cibiyar a masarautarsa sai Katsina. Da na
harari wannan leshi na ƙasar Katsina ban ga na yi cika
baki ba da na kira ta “Gamji Matattarar Tsuntsaye”.
Haihuwar Boko:
Bature ba da girma da arziki ya
kai boko ƙasashen da ya mallaka ba. Boko
cikin fitina ya zo, tsaitsaye aka karɓe shi, tsaitsaye aka bayar da shi. Manufarsa cusa
harshe da al’adu da addinin Yahudu da Nasara a ƙasashen da suka mallaka. Duk da haka, Hausawa kan
ce, da ɗan gari akan ci gari. Da ‘Hausa’ aka fara boko a Nijeriya ta arewa
musamman ƙasar Hausa. Makarantun boko da
suka yi fice a ƙasar Hausa su ne: Makarantar
Nasarawa, Kano da makarantar Sakkwato 1905 da ta Katsina Middle School, 1922.
Da karatu ya fara shiga ran ‘yan makaranta babu littattafan karatu, dole aka
shirya gasar neman littattafai. A gasar, 1933 Katsina ta limanci bokon Nijeriya
da littafin Ruwan Bagaja na Malam
Abubakar Imam. Wannan littafin shi ya kai Katsina da Katsinanci wurin da
dugadugan Katsina bai taka ba. Bugu da ƙari littattafan Abubakar Imam Magana
Jari Ce 1-3 da Ƙaramin sani Ƙuƙumi da Kayi ta Karatu da Ka Ƙara Karatu,
su suka fara fitar da karatun Hausa a duniyar ilmi. Da waɗannan karatun Hausa ya samu karɓuwa a ilmin boko, duk wani
masani da malamin Hausa da bazarsu yake taka rawa. A iya sanina ya zuwa yau, ba
a yi kwatankwacin su ba. Na yarda da Ɗan’anace da ya ce:
Jagora : Mai son miya ya auri tsohuwa
:
Mai son shimfiɗa ya auri budurwa
:
Mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa.
Takwaransa a fagen rubutun waƙoƙi ya ce:
A nemo manya al’amarin da yai tsawo
Zaman babban yatsa ko ba ta cin tuwo
Ta
iya ɓare malmala.
(Waƙar Siyasa, A.M. Bunza 1997).
Har gobe, masana adabin Hausa
suna bugun gaba da Iliya Ɗan Mai Ƙarfi na Amadu Ingawa. Zaɓi Naka na Munir Mamman ba ƙaramar rawa ya taka ba. Turmin Ɗanya da Tura Ta Kai Bango, na Suleman Ibrahim Katsina sun cancanci yabo.
Ibrahim Sheme, ba ƙaramar gudumuwa ya bayar ba a
cikin littafin ‘Yar Tsana ba. Bilkisu
Funtuwa, ta fito da ‘Ya’yan Hutu da Mugun Zuma da Duniya Rawar ‘Yanmata. Waɗannan rubuce-rubuce a ko’ina ake nazarin Hausa a
binciken Hausa da koyar da Hausa za a ga a kan gaba suke. Don haka suka zama
wata azara ko ginshiƙi ga rumfar da Abubakar Imam ya
haƙa. Idan Katsina ta kasance haka
a nazarin Hausa, to a yi wa Narambaɗa ɗa’a:
Jagora : Shigifa in babu azara
: Kuma babu ginshiƙi
: Ai kun san sai ta tuɗe
: Mi
aƙ ƙarfin shigifa
: Ba
su ba?
Gindi : Na
yaba ka da girma Abdu ƙanen Maidaga
: Kan
da mu san kowa
: Kai
mun ka sani Sardauna.
Adabin Baka:
Da aka fara karatun Hausa da Adabin Baka aka fara share fage domin
shi ya haifar da rubutacce. A tunanin ɗaliban tarke adabi sun ce, waƙa tafi amo da shahara da shiga zuciyar ma’abuta
adabi. A nan, Katsina ta yi tsayin daka na ganin ta zama rumfar Hausa. Da an ce
waƙa in an kawo sunnan Alhaji
Muhammadu Shata Katsina dole a yi shiru maƙoƙo ya fito a bakin zabiya. Abin ban sha’awa, mafi yawan mawaƙan baka irin su Kurna, Narambaɗa, Alu Ɗandawo, Salihu Jankiɗi, Sarkin Taushin Sarkin
Katsina, Ɗanƙwairo, Gero Zarto, Sa’idu Faru, da suka yi fice a
waƙoƙin fada, duk a gidajen suka rasu a nan aka rufe
su. Alhaji Muhammadu Shata kawai aka kai
gidan uban gidansa (Mai daura) aka rufe shi. Wannan wani tarihi ne na karatun
Hausa da babu wanda ya gabaci Katsinawa da shi. A gai da Narambaɗa da cewa:
Jagora : Ɗan bajimi shi ka zama bajimi,
:
Yai bobakali yai tozo
:
Ɗan akuya na kallo.
Gindi :
Na yaba ka da girma
:
Audu ƙanen Maidaga
:
Kan da mu san kowa kai mun ka sani Sardauna.
Karatun Hausa A Katsina:
Sanin asalin rumfar da Katsina
ta yi wa karatun Hausa a arewa, ya sa na ga ya kyautu a ƙyallaro wannan bagiren. Bayan makarantun Firamare
da na gaba da su da ake karatun Hausa akwai makarantun ilmi mai zurfi da Hausa
ta baje kolinta a ciki irin su:
i.
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Katsina
ii.
Jami’ar Musulunci ta Katsina
iii.
Federal College of Education, Katsina
iv.
College of Education Dutsin-ma
v.
Bala Usman College of Legal Studies, Daura
vi.
Katsina Polytechnic
vii.
Federal University, Katsina (Muna Fata)
Jami’ar (UMYUK) da FCE, Katsina
suna ba da digirin Hausa. Jami’ar Musulunci an saka Hausa cikin darussanta.
Sauran kuwa suna ba da shaidar NCE, Federal University, muke fatan a buɗe sashen domin ɓarin waina/ masa cikin zuma ba ɓanna ba ne. A nan kaɗai za mu ga cewa, Katsina ta ɗaure wa Hausa gindi har da wuya
domin yanzu haka, ma’aikatar kulawa da ilmin Jami’a ta ba da izinin a fara
babban digiri M.A. da M. Phil da Ph.D a Jami’armu. Wannan ya sa Katsina ta zama
ta (4) a Jami’o’in duniya da ake koyar da Hausa.
Muryar Katsina a Duniyar Karatun Hausa:
Idan an ce duniyar karatu, da
an kai Jami’a an kai sin-waw-raa-taakuri in ji Bagarden allo. A tsarin ilmin
Jami’a da alƙalami da littafi da kujera da
allo da allin karatu ba su kai ƙima da darajar digirin First Class
ba. A ɗan nawa tunanin ya kyautu a kira ta “Fintinkau” domin ita ce kan takardar
kowa baya yake. A irin tsarinmu na Jami’a, ba a bayar da ita sai ga ɗalibin da aka tabbatar da cewa,
ko an daka cikin turmi da su cikin masu fita. Ka ce, Shata a fagen waƙa ko Shago a fagen dambe, ko Daƙƙwale a wasan Tauri, ko Ɗantagaro a filin sata, ko Muhammadu Duguru a
sana’ar gini, ko Ɗantata a zancen kuɗi, ko ka ce Fir’auna a fagen
mulki, ko Manzo Muhammadu (SAW) a gurbin Annabawa. Mai digirin “Fintinkau” haka
haskensa ke bayyana a cikin tsara.
A tarihin karatun Hausa na
duniyar Hausawa, Bakatsine ya fara karɓar wannan digiri a birnin Kanawa, Jalla Babbar
Hausa, a Jami’ar Bayero Kano, 1983. Sunan Shagon, Malam Aminu Lawal Auta
Katsina. Ya yi digirin M.A 1986, PhD, 2008. Abu Kaman ƙaddara in ji Buzu da ya sha kayen raƙumi, sai ga shi, an buɗe Jami’ar Umaru Musa Yar’adua,
2006. A shekarar 2010 ta yaye ɗalibanta na farko. A sashen Hausa wani Ɗandunawa ya sake bayyana mai suna Abdurrahman
Faruk ya yi wa digirin “Fintinkau” zama ɗaya kamar yadda baƙauye ke yi wa busasshen biredi. A kula da waɗannan jawabai:
i.
An fara karatun Hausa a Nijeriya a 1967
ii.
Yau shekaru Arba’in da bakwai 47 ana karatun Hausa a Nijeriya
iii.
Jami’o’in da suka yi fice da karatun Hausa, ABU, BUK, UDUS da Maiduguri
iv.
Daga 1967-2014 digirin Fintinkau biyu (2) kwai aka samu a duniyar bokon
arewa kuma waɗannan buwayayyin duk Katsinawa ne.
Idan dai aka ɗebe ƙyashi da hassada. Da Hausa addini ne, to, Katsina
annabinsa yake. Idan kuwa wata ƙasa ce, Katsina shugaban ƙasa yake. Idan kuwa mun ce, harshe ne, kuma ilmi ne, dole mu aminta da
cewa, Katsina ce rumfar da za a je a baje kolin litattafan karanta shi domin
can kanbum yake har yanzu babu wanda ya ƙwato shi. Wayyo! Na so Katsinawa ku ba ni dama mu yi bitar karatun nan na
Narambaɗa:
Jagora :
Amadu dubi mazan gaba
:
Dubi na baya
Yara :
Ka duba dama ka duba hauni
:
Ka san jama’ar ga da an nan
Yara :
Ƙyauye da birni ba su da jigo
sai kai,
Jagora :
Maɗi bai kai ga zuma ba
Yara :
Kowal lasa shi ka hwaɗi
Yara :
Kwandon wake
:
Bai kai ga damen gero ba
Jagora :
Ɗan akuya ko ya yi ƙahoni
Yara :
Ya san bai yi kamar rago ba
Jagora :
Duk wada ɗan sarki
:
Yak ƙasara
Yara :
Kak ka raba shi
:
Da bawan sarki
Gindi :
Gogarman Tudu jikan Sanda
:
Maza su ji tsoron ɗan maihausa
Jigajigan Katsina A Duniyar Karatun Hausa:
A fagen karatun Hausa a
Jami’o’inmu za mu ga Katsina ba wai ba ce. Abin ban sha’awa, masana Hausa na
Katsina ka ce zaɓa mata aka yi a fannonin da suka shahara. A ɓangarorin karatun Hausa uku ga
yadda Katsina ta yi rumfa Hausa ta zauna ta huta:
Harshe:
Farfesa Isma’il Junaidu (Abuja)
Farfesa Munir Mamman ABU, Zaria
(Marigayi) Dr. Wurma ABU, Zaria
Dr. Aminu Galadima Ɓatagarawa, UMYUK
Dr. Tanimu ‘Yar’adua (BUK)
Adabi:
Dr. Aminu Lawal Auta (Fintinkau) BUK
Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi, KASU, Kaduna
Dr. Mustapha Safana, UMYUK
Al’ada:
Dr. Ahmad Magaji, BUK
Dr. Bashir Sallau Sarkin Aska, UMYUK
Wasan Kwaikwayo:
Malam Adamu Ibrahim Malumfashi,
Dr. Ahmed Ɗanmaigoro FCT Katsina,
Farfesa Isma’il Junaidu shi ne
garkuwansu. Duk da haka, a cikin masana
ilmin harsuna na Hausa Farfesa Munir na ɗaya daga cikin masananmu masu hannu duka dama. Ya
san harshen Larabci, ya san Turanci, ya san Hausa kuma ga shi da shahadar koyar
da ilmin (education). Bugu da ƙari, marubuci ne sosai, yanzu haka litattafansa uku suna shawagi hannun
makaranta. Idan dai za a yi bayanin adalci daga cikin farfesoshinmu na adabi. A
fannin rubuce-rubucen ƙagaggun labaru, dole a cire
hula idan an ambaci Ibrahim Aliyu Malumfashi. A fagen, a yanzu, ba ya da
takwara, babu ƙani, babu abokin wasa. Don
tsananin wayon Bakatsine, sai ya dafa kafaɗar barden Hausa Alhaji Abubakar
Imam, ya yi PhD a kan ayyukansa. Dole a girgiza wa Limamin makarantar Malam
Bambadiya a duniyar yanar gizo. A fagen al’ada Dr. Ahmad Magaji Malamin
Malammai ne. Su dukkansu, Malam Adamu Ibrahim Malumfashi shi ya shayar da su
mama. Wanda duk ya karɓi shahaɗar Hausa Jami’ar ABU, ya ce bai san Malam Adamu ba, ban ga dalilin rashin
ƙaryata shi ba. A iya sanina a
yau, a duniyar karatun Hausa, babu malami ƙwararre a wasan kwaikwayo kamar sa. Idan aka
harari ɗan li’irabina da kyau za a tabbatar da cewa a fagen karatun Hausa Katsina
da Katsinawa suna hawan doron tunanin Ɗan’anace ga Shago:
Jagora :
Wanda bai ga damben Shago ba
:
Na da sauran kallo
:
Ya za ka duniya kamar bai zo ba,
:
Kamar zuwan kare ga aboki
:
Ko ya ƙaura ba a gafarta mai
(Waƙar shago).
Rawar Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua:
Wannan Jami’ar ta taimaka wa
karatun Hausa ba ga bunƙasa kawai ba, ta ba shi
martabar da ba a taɓa ba shi ba a tsawon shekara 47 da ake koyar da Hausa. Da farko dai, da
aka buɗa ta da Hausa aka buɗa tattare da sanin ana maƙwabtaka da Jami’o’i uku da suka yi fice a Hausa.
Na biyu, shugabannin Jami’ar tun kafa ta ya zuwa yau, sun bai wa Hausa damar
bunƙasa da mamaye duk sassan da ake
karatun Hausa a duniyar zamaninmu.
Za a tabbata haka idan aka dubi jerin masana da malaman da suka yada zango a
Jami’ar da sunan koyarwa kamar haka:
Farfesa Lawal Ɗanladi Yalwa
Farfesa Isa Mukhtar
Farfesa Sa’idu Gusau
Farfesa Ahmad Baba Tela
Faefesa Muhammad Lawal Aminu
Farfesa Haruna Abdullahi Birniwa
Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi
Farfesa Munir Mamman
Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
Farfesa Atiku Dunfawa
Farfesa Aliyu, Muhammad Bunza,
Malam Adamu Mulumfashi
Dr. Aminu Lawal Auta
Dr. U.U. Fage
Dr. Ummu Ado Abbas
Dr. Ahmad Magaji
Dr. Ahmad Ɗanmaigoro
Dr. Magaji Tsoho Yakawada
Dr. Ibrahim Tsoho Yakawada
Dr. Ibrahim S.S
D. Wurma
Tattare da kasancewar Jami’ar Umaru ‘yar Jinjira idan aka auna nauyin
malamanta na Hausa za a ga abin ba da wasa aka assasa shi ba. Malaman Hausa na
sangaron daban-dabn na koyon Hausa a Jami’ar su ne:
1.
Dr. Bashir
Aliyu Sallau (Sarkin Aska) BA,MA,PHD (BUK) - Culture
2.
Dr. Aminu
Galadima Ɓatagarawa BA, (ABU) MA(UDUS)phd(ABU) - Language
3.
Dr. Almustapha
Shu’aibu Safana. BA, MA, (UDUS) phd (DUK) - Literature
4.
Malam Sirajo
Ibrahim, BA, MA (UDUS) - Language
5.
Bashir Abu Sabe
BA, MA, (UDUS) (Ph.D in progress Cairo) - Literature
6.
Ado
Abdulrahaman BA,(BUK) MA (UDUS) (Ph.D in progress Cairo) - Culture
7.
Malama Zainab
Isa BA, MA, (ABU) - Literature
8.
Malama Salima
Sulaiman, BA, (ABU) - Language
9.
Malam Abdulƙadir Ɗan Alhaji BA,MA
- Language
10.
Malam
Abdulrahman Faruk BA, (UMAR) 1st class – Literature
11.
Malam Aminu
Ibrahim, BA,MA - Culture
12. Malam
Murtala Adamu, BA, (BUK) MA (ABU) - Literature
Daga cikin malaman goma sha biyu da muke da su, uku suna
da digirin Ph.D, takwas na da digirin MA, ɗaya yana da Fintinkau kuma yanzu haka yana MA a UDUS. Haka kuma, uku ne
fannin al’ada, huɗu a harshe, huɗu a adabi. Haƙiƙa tsarin
malaman da fannoninsu ya yi tangam mai zuwa Haji ya gamu da Annabi (SAW). Tirƙashi! Lallai
Katsina rumfar Hausa ce.
MALAMAI MASU
ZIYARA
1.
Farfesa Manir
Mamman
2.
Farfesa Ibrahim
Aliyu Malumfashi
3.
Farfesa Lawal Ɗanladi Yalwa
4.
Farfesa Aliyu
M. Bunza.
5.
Dr. Aminu Lawal
Auta
6.
Dr. Ummu Ado
Abbas
Ina tabbata muku, babu Jami’ar da ake karatun Hausa a duniya da ta samu
albarkar malamai masu ziyarar koyarwa irin tamu. Wannan Wani ƙarin armashi ne
ga karatumu da takardun shaidar da ake bayarwa a nan. A ganina, yana ɗaya daga cikin dalilan da su ka sa yaron da ya ci digirin “Fintinkau” aka
ce, a tabbatar da ita, domin ya sha nonon Farfesa goma sha ɗaya da daktoci goma. Don haka, babu sauran kukurunkudu Inyamiri ya harbe
kurciya. Jerin tsarin masanan da suka yada zango Jami’ar Umaru ya cancanci a
kira Katsina da Jami’ar “Rumfar Hausa”. Na tabbata Katsina gamji ce matatarar
tsuntsaye, domin duk wani masani ya yi ƙoto, a nan zai zo ya yi tuƙe.
Rumfar Katsina
ga Hausawa:
Ban ce, ina yarda da dukkanin abubuwan da masana tarihi
da al’ada da walwala suka ce game da asalin Hausawa ba. Rashin yardata ba hujja
ba ce, amma kuma hankalin karatu na alalin Bahaushe dole ya taɓo:
(i)
Daura, wadda
Hausawa ke yi wa kirari, tushen Hausa. Komai raunin tarihin Daurama yana nan a
kundace, da duk aka lalubo asalin Bahaushe sai an kakkaɓo shi. Da an kakkaɓo shi dole a ambaci katsina.
(ii)
Ba ni cikin waɗanda suka yi imani da zuwan Bayajida shi ne asalin Hausawa. Duk da haka,
ban musanta kayan tarihin da ke rijiyar kusugu ba, kuma ban ƙaryatar da
ziyarar Bayajida a ƙasar Katsina ba.
Sarautar Daurama
tana da alaƙa da sarautar Sarauniya Amina ta Zazzau da Inna ta Gobir da Magajiya da ake
naɗa wa ƙasashen Hausa daban-daban, wanda ya haifar da Karin
magana, aikin Magaji ba ya hana na Magajiya. Wannan duk, wata rumfa ce Katsina
ta yi na zaunawa a huta, a sake bitar asalin Bahaushe da harshensa.
A kowace fuska aka ɗauko tarihin
Bahaushe, a kan kowane irin rai za a ɗora shi Katsina
ba ta ƙyalle.
Rumfar Katsina
ga Addinin Bahaushe:
A tarihin addinan gargajiya Katina ta
agaza wajen adana al’adu na Bahaushe a da, da suka zama wani furen kallon
hasashen addinan da suka ratsa ƙasar Hausa. A gargajiyance, ƙasar Mulumfashi da
Kainafara Arnan Birci da Matsafar Jino ta Ƙasar Ƙanƙara wasu taskoki ne ga ƙasar Hausa da
masu karatun Hausa. Matsafar Jino matattarar Kabawa da Gobirawa da Katsinawa da
sauran maƙwabta ce. An ce, ita ce tushen kafa garin “Acida” na cikin jihar Sakkwato.
A fagen saukakkin addinai, idan aka dubi tarihin hulɗar Katsina da ƙasashen waje, tun gabanin ƙarni na sha tara akwai abin
cewa. Ga alama, hulɗar kasuwanci Katsina da ƙasashen Larabawa ya yi
sanadiyyar shigowar addinin Nasara da Yahudu.
Binciken da Babajo ya yi (2012) da na Shobhana Shaukar,
Christian Origins in Muslim Northern Nigeria, (c. 1890-1975) da aka wallafa
(2014) sun tabbatar da haka. Ke nan, rubutun boko da Hausar boko sun riga
karatun boko shigowa birnin Katsina. Tarihin Musa Aya da ke Liverpool, a
Ingila, ya tabbatar da wanzuwar rubutun boko a Katsina tun gabanin ƙarni na sha
tara. Musa Aya madugun cinikin bayi ne da ya makara a liverpool, Ingila. Na
shaidi kayayyakinsa da na je can.
Babu wani masani da zai tantance lokacin da aka fara
rubutun ajami a Katsina. A duniyar Bahaushe, da an ambaci Bahaushe a kan Ilmin
addini dole a gabatar da Wali Ɗanmasani da Wali Ɗanmarina. Waɗannan Katsinawa ne, kuma su
suka mamaye ƙasar Hausa. Duk da yake ba a taskace tarihinsu da kyau ba, kamar yadda aka
yi wa na Kano Tarikh Man bi Kano Min
Auliya’il Laahi na Hausai Baukar Adakawa, ba. Husmiyyar Masallacin Gobarau
ya isa zama cewa Katsina rumfa ce ga ƙasar Hausa da Hausawa.
Babu abin da ke hana wa harshen salwanta kamar rubuta.
Katsinawa suka fara yi wa Hausa agaji da rubutu da harufan boko. Gare su aka
fara adana ajami ta fuskar fatauci. Abin ban sha’awa, a Katsina aka fara fito
da wani sabon salon rubutun Hausa, wai shi Rubutun
Tafi. Wataƙila, wanda ya jahilci abin zai ga wata rigima ce aka jawo ta mayar da gaba
baya. Da na sa natsuwa na karanta aikin sosai, na ga wata lamba ce aka ƙara wa Bahaushe
daga cikin lambobin daraja ga harshensa da mutuncinsa. Ala tilas mu girgiza wa
Injiniya ga wannan ƙoƙarin.
Sake Kafa Tutar
Katsina a Duniyar Karatun Hausa
Idan muka yi la’akari da ‘yan abubuwan da aka tattauna za
a ga Katsina na buƙatar Katsinawa su sake zama su kare ta. Ta da harshen da
ya fi Hausa amo. Karin harshenka aka fara rubutun Hausa da shi duniyar ilmi ta
Hausawa. Karin harshen Katsina ya fara wanzuwa a karatun Hausa, don haka babu
yadda za a salwantar da shi komai kishin mai kishi. Lokaci ya yi ga Katsinawa
su kafa wata babbar gidauniya ta:
(i)
Fassaro dukkan
ayyukan da aka yi a kan Katsina daga wasu harsuna (Turanci da Faransanci da
Larabci) zuwa Hausa. Manyan ‘yan boko Katsina da suka yi kundayen digirinsu na
uku PhD a kowane fanni, a zauna a fassara su zuwa Hausa yadda Bahaushen Katsina
zai amfana da su.
(ii)
A yi tunanin
sake taron masana na musamman a yi bitar asalin Hausa da harshensu.
(iii)
A tabbata
Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma ta buɗa Sashen Hausa domin
Katsina ce cibiyarta, ya kyauta a ce ta amfani cibiyarta fiye da yadda za a
amfanar da ‘yan ci rani.
(iv) Ɗaliban Hausa na
NCE da BA da MA da MPh da phD a riƙa yi musu tallar Katsina a ƙudurin kundayen bincikensu.
Yin haka zai ƙara amfanar da Katsina da Katsinawa ga cibiyoyin karatu da aka girke
farfajiyar ƙasarsu.
Kashedi
Ɗaliban nazari da karatu da Hausa, mai t5unanin Hausa ta takkwallai ce, don
haka ya zo a ba shi takkwalin digiri, ya sake shawara zomo ba ya kamuwa daga
kwance. Mai ganin ya zo sashen Hausa ya kwashi ɓagas ya yi tattara, kowa ya ci zomo ya ci gudu. Mai ganin ya rasa abin da
zai yi, ya zo ya yi Hausa, ya yi ɓatan ɓakatantan ba ya ga tsuntsu ba ya ga tarko. Mai zaton ba sai ya yi karatun
harshen iyayensa zai ci jarabawa ba me ya raba shi da gidansu? Ya zauna can
mahaifansa su ba shi shahada ya kai gwamnati ta ba shi aiki. Fatarmu samun ɗalibai da ke sha’awar karatun harshenmu haziƙai da za mu yaye su ba
duniya mamaki. Ba mu ce, mun fo kowa ba, amma babu shakka, ba mu ga karatun da
ya fi namu ba, a bokon da ake yi duniya.
Naɗewa
An takura ni ƙwarai da ba ni ƙurarren lokaci daga jiya Laraba zuwa yau Alhamis
13/03/2014 na gabatar da bincike mai ma’ana. A ɗan rangadin da wannan takarda ta yi, a duniyar karatun Hausa Katsina ce
gamji. Irin gudummuwar da ta bayar ya sa na kira ta “Rumfar Hausa” A yau 2014,
Gwamnan Jihar Katsina, kaɗai ake kira da Sarkin Yaƙin Hausa. Haka
kuma, shi ne Sarkin Fulanin Zamfara domin asalinsa Bajagwade ne daga garin
Shema Ƙaramar hukumar Suru, Jihar Kabi, Muhammadu Shata kuwa, daga Sanyinna ta
Sakkwato. Janar Buhari daga Borno. Fitattun gidaje irin su gidan Malam Sallau
Kumasi sun yi fice a wajen Katsina, su suka wayar da Asante, garin Gamaiji da
sarautun gargajiya na Ghana Katsinawa suka assasa su.
Larabawa na Alwajad irin su Abu Algais jikokinsu suka
haskaka katsina. Fitattun Unguwanni irin su Farin Ɗadi da Albaba da Tanatinke
da ‘Yansiliyu Larabawan Gat da Gadamus da Insala suka share musu wurin zama.
Fitattun ƙwararru a Katsina sun kai suna Katsina wajen ƙasar Hausa. ƙwararru daga
wajen Hausa sun yada zango a Birnin Katsina. Wannan shi ya ɗaukaka Katsina da Katsinawa da harshen Hausa, Hausa ta samu babbar Rumfa a
Katsina.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.