Takardar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa domin karrama marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Junju mai taken “The Challenges of Teaching African Languages” da ƙungiyar des Auteurs Nigeriens en Langues Nationales (ASAUNIL) due da Nigerian Indigenous Languages Writers Association (NILWA) suka shirya a ranar 19-21 ga Fabrairu, 2014 a Emir Sultan, Niger Republic haɗe da bukin ranar International Mother Language Day (IMLD) da UNESCO ta shirya.
MUSA SHEHU
Department
of Nigerian Languages
Usmanu
Danfodiyo University, Sokoto
0703 131 9454
msyauri@yahoo.com
Gabatarwa
Zamantakewa
a kowace irin al’umma gona ce mai faɗin gaske, sai dai a yau ana iya cewa, haki
na ƙoƙarin yi mata barazana na hana yabanya walwala. Haƙiƙa al’ummar Hausawa sun
kasance masu kyakkyawar zamantakewa a tsakanin junansu. Gaskiya da riƙon amana
da shi suke kwana suke tashi. Haƙuri da taimakon juna ya zama musu ruwan sha a
ji sanyin rayuwa. Biyayya ga magabata da tausaya wa talakawa ga shugabanni ya
zama ruwan dare game duniya. Sai dai kuma wannan kyakkyawar zama yana neman taɓarɓarewa
a wannan zamani. Manufata da wannan maƙala ita ce, fito da tsarin zamantakewar
Hausawa a jiya, da kuma yadda zamantakewar ke ƙoƙarin sukurkucewa a yau na
rashin gaskiya da riƙon amana. A yau, taimakon juna da biyayya ga magabata, da
tausaya wa talakawa daga shugabanni, da haƙuri da juna yana neman ya zama
tarihi. Ga dai al’amurran nan suna ƙoƙarin taɓarɓarewa a rayuwar Hausawa a yau.
Yanayin Zamantakewar Hausawa a Jiya
Tarihi ya nuna al’umma takan kafu ne a sakamakon wata yarjejeniya tsakanin wasu
mutane waɗanda suka taru suka amince da kare kansu daga wasu abubuwan ban
tsoro, ko hare-haren abokan gaba, ko namun daji, ko kuma su sauƙaƙa wa kansu
wasu wahalolin duniya (Mar, 1980 a cikin Gusau 1999). Irin wannan zama na
yarjejeniya yakan kawo sahihin haɗin kai da yarda da juna, sannan da taimakon
juna. A irin wannan yarjejeniyar zama aka sami wasu mutane daga ƙabilu
daban-daban suka haɗa ƙarfi suka samar da al’ummar Hausawa, masu ma’amala da
harshe ɗaya wato harshen Hausa, tare da samun daidatuwa ta wajen fannin ɗabi’unsu
da al’adunsu da muhallinsu da sauran kayayyakin ayyukansu duk sun zama fanni ɗaya
(Gusau, 1999).
Hausawa tun farko mutane ne da suka tashi da taimako da son juna, da ladabi da
biyayya, da tsare gaskiya da riƙon amana, da aikata ɗa’a da tsare haƙƙin
shugabanci da maƙwabtaka da sadar da zumunci, da tausayi da sanin ya kamata, da
sauran ayyukan alheri iri daban-daban. Kuma su mutane ne masu matuƙar karimci
da saurin amincewa da wasu mutane, wato baƙi. Sannan ga sakin fuska da shimfiɗar
fuska wadda ake cewa ta fi shimfiɗar tabarma. Mutane ne masu kyakkyawan
zamantakewa tsakaninsu da ma sauran baƙi masu shigowa. Duk da yake cewa, mun
san akwai wasu halaye da ɗabi’u munana da ake aikatawa tun wancan lokaci na
farkon rayuwar Hausawa, domin Hausawa na cewa, mutum duka ɗan tara ne bai cika
goma ba. A kan haka, za a iya kallon zamantakewar Hausawa zuwa waɗannan
rukunnai:
Zamantakewa Tsakanin Maƙwabta
Maƙwabtaka
ita ce zama wuri guda da mutum dangane da sana’a ko wurin zama (Gusau, 1999).
Ba shakka, akwai kyakkyawan zama da ƙaunar juna tsakanin maƙwabci da maƙwabci.
Idan wani abin farin ciki ya sami maƙwabci kamar harkar aure ko suna, yakan
shaida wa maƙwabcinsa don a taru a yi murna. Hakazalika, idan abin baƙin ciki
ne ya samu akan haɗu a jajanta wa juna. Sukan kuma taimaka wa junansu idan wata
hidima ta samu domin a rufa wa juna asiri. Maƙwabcin Bahaushe tamkar ɗan’uwansa
ne, ya san samu ko rashin maƙwabcinsa. Haka ma ya san farin ciki ko baƙin cikin
maƙwabcinsa. Bugu da ƙari, zamantakewar ba ta tsaya a nan ba, galibi idan dare
ya yi magidanta sun dawo gida, maƙwabta sukan fito da abincin dare daga
gidajensu a zauna a ci tare ana tattauna lamurran da suka shafi rayuwar duniya.
Ziyarar mara lafiya, da zuwa jaje ga wanda wani abu na baƙin ciki ya sama, da
saƙonnin taya murna, duk Hausawa na gudanar da su ga maƙwabtansu na jini da na
zaman unguwa ko gari ko sana’a, saboda ba da haƙuri da nuna tausayawa da taya
murna. Idan wani rikici ya ɓarke tsakanin maƙwabta, akan haɗu a tattauna a yi
sulhu don samun masalaha.
Zamantakewa Tsakanin ‘Yan’uwa
Zamantakewa tsakanin
‘yan’uwa na jini kamar ta maƙwabci da maƙwabci ce. Babu nuna bambanci tsakanin
‘yan’uba. Iyaye mata ko kishiyoyi ba sa nuna bambanci tsakanin ‘ya’yansu. A
wani lokaci ma yaro bai gane mahaifiyarsa sai idan ya girma. ‘Yan’uwa kan
yawaita sadar da zumunci tsakaninsu ta hanyar ziyartar juna daga lokaci zuwa
lokaci. Kamar maƙwabta, su ma ‘ya’uwa kan taru domin taya juna murna ko farin
ciki idan wani buki ya samu. ‘Yan’uwa kan yi iya ƙoƙarinsu don ganin ɗan’uwa
bai ji kunya ba. Babu yaudara ko cin amana tsakanin ‘yan’uwa. Idan iyayen yara
suka rasu, ‘yan’uwa kan ɗauke su suna kulawa da su tamkar su suka haife su ta
yadda rayuwarsu za ta inganta ba tare da sun tagayyara ba. Idan wata rashin
lafiya ta sami ɗan’uwa, babu maganar ƙyama, ‘yan’uwansa na kusa da ma na nesa
kowa yakan kawo tasa gudummuwa domin ganin wannan ɗan’uwa ya sami cikakkiyar
lafiya.
Zamantakewa Tsakanin Masu Mulki da Talakawa
Haƙiƙa akwai kyakkyawar zamantakewa ta fahimtar juna a tsakanin masu mulki ko
sarakuna da talakawansu. Abin da aka sani tun can azal a rayuwar Hausawa, sarki
ko shugaba mutum ne wanda a koyaushe yake ƙoƙarin tsare mutuncin sarautarsa ko
shugabancinsa ta hanyar riƙe talakawansa da kyawo, ya ɗora su kan tafarki
madaidaici wanda zai amfani rayuwarsu. Haka ma shugaba kan sa ido ya ga cewa,
zalunci da cin amana da rashin gaskiya ko yaudara bai wanzu tsakanin
talakawansa ba. Yakan kare mutuncinsu ga dukkan wani abu da zai kawo tarnaƙi ga
rayuwarsu. Shugabanni kan sa ido ga baƙi masu shigowa cikin gari don gudun
saukar da ɓara-gurbi. Haka ma a ɓangaren talakawa, akwai ɗa’a da ladabi da
biyayya zuwa ga shugabanni. Sukan kuma taimake su wajen tabbatar da zaman
lafiya mai ɗorewa da kawo arziki da wadata a cikin ƙasa. Haka kuma sarakuna
sukan nemi shawarar talakawansu a cikin al’amurra daban-daban domin tabbatar da
adalci ga jama’arsu.
Zamantakewa Tsakanin Malamai da Ɗalibai
Malamai dai a cikin kowace al’umma su ne masu ilmantar da jama’a maza da mata,
yara da manya sanin hanyoyin rayuwa tagari, da koya musu halaye masu nagarta,
da nuna musu munanan halaye don su kauce wa faɗawa a ciki. Sannan su ilmantar
da mutane ilimin addini da na zamani wanda zai shiryar da su zuwa ga rayuwar
duniya da na gobe. Malami shi ne mai koya wa yara ƙima da girmama iyayensu, da
yadda za su yi musu ɗa’a da biyayya, da kuma yadda za su yi kyakkyawar hulɗa da
sauran jama’a. Su kuwa ɗalibai suna matuƙar girmama malamansu da yi musu ɗa’a
da biyayya da kauce wa duk wani abu da zai sosa rayuwarsu. Sukan kuma ƙudurta
kyakkyawar niyya game da malamansu. Ba su cin zarafin malamai ko yi da su,
balle ma a gabansu. Haka dai wannan kyakkyawar zamantakewa take gudana tsakanin
malamai da ɗalibansu. Bugu da ƙari, ko da ilimin zamani ya shigo ƙasar Hausa
aka fara samun malamai da ɗalibai ‘yan ƙasa, wannan kyakkyawan tsarin
zamantakewa tsakanin malaman zamani da ɗalibansu bai sauya ba. Malaman sukan ɗauki
ɗaliban kamar ‘ya’yansu na cikinsu. Haka su ma ɗaliban sukan yi wa malaman
ladabi tamakar iyayen da suka haife su. Akwai girmamawa da tsare haƙƙin juna
tsakaninsu.
Zamantakewa Tsakanin Masu Arziki da Talakawa
Masu iya magana na cewa, kowa am mutum mutane ash shi. Zamantakewa tsakanin mai
shi da mara shi abu ne gwanin ban sha’awa a ƙasar Hausa. Masu arziki ba su walaƙanta
talakawa, hasali ma sukan jawo su ga jiki domin su ma su sami albarkar dukiyar.
A wasu lokuta, masu arziki sukan rarraba wa talakawa jarin da za su gudanar da
kasuwanci domin kowanensu ya amfana. Idan wata lalura ta sami talaka wanda ya
shafi aure ko suna da makamantansu, talaka yakan kai kukarsa ga masu shi kuma a
share masa hawaye gwargwadon iko. Su kuwa talakawa sukan kasance masu ɗa’a da
biyayya da gaskiya da riƙon amanar dukiyar da masu shi suka damƙa masu. Idan
wata hidima ta samu mai shi, za ka tarar talakawa sun taru a ƙofar gidan mai
shi don su taya shi murna idan abin farin ciki ne. Idan kuma akasin farin ciki
ne ya auku, nan ma talakawan sukan taru domin taya shi juyayi da jajanta masa.
Haka dai wannan kyakkyawar zamantakewa take tsakanin masu arziki da talakawa a ƙasar
Hausa, sai dai ɗan abin da ba a rasa ba na saɓani na yau da gobe. Da ma Hausawa
na cewa, mutum duka ɗan tara ne bai cika goma ba.
Zamantakewa Tsakanin Ma’aurata
Haƙiƙa akwai kyakkyawar
yanayin zamantakewa tsakanin miji da matarsa a ƙasar Hausa. Miji yakan yi iya ƙoƙarinsa
na ganin ya tsare haƙƙin matarsa da ke bisa kansa. Yakan kula da ci da sha da
lafiyar matarsa da sauran lalurorin yau da kullum gwargwadon hali. Yakan kauce
ma wasu munanan halaye na cin zarafi ga matarsa ko waɗanda al’ada ba ta amince
da su ba. Bugu da ƙari, miji kan sa hannu wajen tarbiyyantar da yaran da suka
haifa don ganin sun rayu bisa turba tagari da yanayin zamantakewar duniya. Ita
ma matar takan yi ƙoƙarin tsare haƙƙin mijinta da ya rataya a wuyanta. Takan
kasance mai ɗa’a da biyayya ga miji da rashin ƙetare iyakokinsa. Ita ce mai
kula da harkokin gida na yau da gobe, da tsaftar yara da ba su tarbiyya tagari.
Mace kan yi haƙuri da mijinta da tausaya masa game da harkokin rayuwa. Idan
wata matsala ta shiga a tsakaninsu, sukan taushe zuciyarsu ga hana aikata ɗanyen
hukunci. Wannan ne ya sa yawaitar sakin aure bai samu gindin zama a tsakanin
Hausawa ba. Haƙuri kusan shi ne jigon zamantakewar mata da miji, tare da bai wa
juna shawara don samun mafita a rayuwa.
Zamantakewa Tsakanin Iyaye da ‘Ya’yansu
A koyaushe burin mahaifa
ko uwaye bai wuce ganin ‘ya’yansu sun tashi cikin halaye masu kyau da nagarta.
Saboda haka suke koya musu ɗa’a da ladabi da biyayya da bin kyakkyawar turba
don su ribanci rayuwarsu, al’umma ma ta amfana da su. Uwaye sukan sanya yaransu
makaranta irin ta addinin musulunci da ta zamani. Sukan nuna musu muhimmancin
gaskiya da riƙon amana domin aiki da su. Sa’annan kuma da illar ƙarya da cin
amana domin su kauce musu. Sukan kuma nuna musu amfanin zumunci da ‘yan
uwantaka ta hanyar yawaita aikensu a gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki. Akan
koya musu sanin darajar mutane da girmama su, ba wai sai iyayensu kawai ba.
Saboda haka ne ‘ya’ya sukan kasance masu biyayya da jinƙan iyayensu tun suna
yara har zuwa girmansu.
A taƙaice, ana iya kallon yanayin zamantakewar Hausawa a jiya da wasu kyawawan
abubuwa da al’ada da addini suka amince da su da kuma masu aikata su.
- Gaskiya da riƙon amana
- Zumunci da ziyartar ‘yan’uwa
- Tsare haƙƙin maƙwabtaka
- Taimako da tausaya wa juna
- Ladabi da biyayya ga shugabanni
- Girmama na gaba
- Adalcin shugabanni ga talakawa
- Tsare haƙƙin talakawa ga masu mulki
- Haƙuri da yafe wa juna
Taɓarɓarewar Zamantakewar Hausawa a Yau
Sanin kowa ne cewa,
matsayin zamantakewar Hausawa ya kai inda ya kai a yau. Kyakkyawar tsarin
zamantakewa da aka sani ga Hausawa a da, a yanzu ya ɗauki sabon salo na koma
baya. Kusan kowane rukunin tsarin zamantakewar Hausawa da aka ambata a baya, an
sami taɓarwarewarsa a yau.
Kyakkyawar zamantakewa da ke tsakanin maƙwabta a da, ya fara yin nisa a yau.
Sau da yawa za ka iske ba a ga-maciji tsakanin maƙwabci da maƙwabci, kowa ya
kama mai fisshe shi. Maganar maƙwabta su haɗu kowa ya fito da abinci a ci tare
ya zama tarihi a yau, kowa ya yi gabansa. Sai maƙwabta su share mako ɗaya ba su
yi ido huɗu da juna ba balle a yi maganar gaisawa, sai dai idan an yi kiciɓis
da juna a bisa hanya. Hatta ‘ya’yan maƙwabtan da suke haɗuwa musamman da
dare domin gudanar da wasanni, ya sha ruwa a yau, kowane maigida ya ja babbar ƙofa
ya rufe ‘ya’yansa a cikin gida. Maƙwabci bai san halin da maƙwabcinsa yake ciki
ba, na farin ciki ko akasinsa, balle su taimaka wa juna da shawara wajen samun
maslaha a rayuwa. Sau da yawa za ka iske maƙwabta na ta husuma a kan
iyakokin gida ko haraba har zuwa wajen masu shari’a. Ga dai al’amurra nan sun
cakuɗe sai dai Allah ya gyara.
Shi kuwa harkar zamantakewa tsakanin ‘yan’uwa a yau ya zama abin da ya zama.
Babu zumunci da taimakon juna, balle riƙon aman. Kowa ya kama gabansa, kansa
kawai ya sani sai ‘ya’yansa. A yau, idan iyaye suka mutu suka bar marayu sai
‘yan’uwa su sa musu ido suna taggayara, babu ilimin addini balle na zamani, ba
su samun tarbiyya balle su amfani kansu da al’umma baki ɗaya. A yau idan ba ka
da abin hannunka, babu ɗan’uwa mai kusantarka domin ba a samun komai wurinka.
Hatta shawara a kan wasu al’amurra na rayuwa ba a yi da kai balle ka san halin
da ‘yan’uwa suke. Su kuwa ‘yan’uwa masu abin hannunsu sun keɓe kansu ba su buƙatar
kowa ya ziyarce su don gudun a aza musu lalura.
Zamantakewa tsakanin masu mulki da talakawa kuwa ya sauya fasali a yau. A
maimakon kare haƙƙin talakawa da mutuncinsu, masu mulki sun sanya ƙafa sun
shure wannan ɗawainiya da ya ratayu a kansu. Sun kasa tsare mutuncin talakawa,
sai cin amana da danne haƙƙoƙinsu da ma barazana ga rayukansu. Masu mulki
sun ƙi su jawo talakawansu ga jiki domin sanin halin da suke ciki. A dalilin
haka, su kuwa talakawa sun bijire ba su ganin mutunci da darajar masu mulki
balle su yi musu biyayya. Talakawa sai muguwar addu’a suke yi wa masu mulki
saboda danne haƙƙoƙinsu da ake yi. Zamantakewa ya taɓarɓare ta yadda sai an
kashe haki kafin yabanya ya sami walwala.
Dalilan Taɓarɓarewar Zamantakewar Hausawa a Yau
A bayanin da ya gabata, an bayyana cewa, kyakkyawar yanayin zamantakewar
Hausawa a jiya ya samu gindin zama ne saboda riƙo da wasu ɗabi’u da al’ada da
addini suka amince da su, kamar gaskiya da riƙon amana, zumunci, haƙuri,
taimakon juna, da makamantansu. A duk lokacin da al’umma suka rasa ire-iren waɗannan
al’adu, ko suka yi rauni a rayuwarsu, tilas halin zamantakewar wannan al’umma
ya taɓarɓare. Wasu daga cikin abubuwan da nake ganin sun taimaka wajen haifar
da wannan taɓarɓarewa na zamantakewar Hausawa a yau sun haɗa da:
Yawaitar Zalunci: Saɓanin inda aka fito, a yau galibin al’ummar
Hausawa burinsu bai wuce tara abin duniya ko ta halin-ƙaƙa (halat ko haram).
Masu kuɗi sun daina taimakon na ƙasa gare su wai don gudun ƙarewar dukiyar ko
raguwarta. Su kuwa masu mulki sai danne haƙƙin talakawa idan sun shigo
hannunsu. Shugabannin yanzu sun daina wakiltar talakawansu, babban burin
akasarinsu shi ne su wawari dukiyar talakawa da suka shigo hannunsu a matsayin
amana ta yadda ko bayan sun sauka ba za su talauce ba daga su har jikokinsu. A
kan haka, a yau matsananciyar adawa ta wanzu tsakanin shugabanni da waɗanda ake
shugabanta, sai kallon-kallo ake yi wa juna. A yau, a gida guda ma idan wani
abin amfani ya shigo hannun wani daga cikin gidan wanda za a raba kowa ya
amfana, sai ka iske wannan da kayan ya shigo hannunsa ya wawari wanda ya fi na
saura.
Rashin Haƙuri da Juriya: A yau rashin haƙuri da juriya ya yi tasiri
ainun a tsakanin al’ummar Hausawa. Tashin hankula ya yawaita a tsakanin
ma’aurata, koyaushe sai an yi sulhu saboda yawan faɗace-faɗace. Ƙarin tabbatar
da wannan zance shi ne, a leƙa kotunan alƙalai za a ga yawan ƙararrakin da ake
shigarwa a kowane yini waɗanda suka shafi ma’aurata ne (Gusau 1991). Zawarawa
sun yawaita a kowane sashe na gari. A unguwa ɗaya sai ka sami zawarawa
bila’adadin an sako su, wanda galibi saboda rashin haƙuri da juriya ne.
Rashin Gaskiya da Amana: ‘Yan kasuwa sun bijire wa gaskiya, sai son
cin amana da yaudara da cin ɓatacciyar riba da ɓoye abubuwan sayarwa sai sun yi
tsada. A yau, idan mai dukiya ya jawo talaka cikin arzikinsa domin kowa ya
amfana, sai talakan ya sa rashin gaskiya da cuta, ko kuma shi mai arzikin ya riƙa
danne haƙƙin yaron nasa. A yau idan ka ba wani saƙon kaya ko kuɗi ya kai ma
wani wuri ko ya adana maka har na tsawon wani lokaci, sai ya ci amanarka ya ƙi
kai saƙon ko ya salwantar da ajiyar da ka ba shi. A yau mai gaskiya bai cika
tasiri a mafi yawan kotunan shari’ummu ba, sai dai wanda ya fi ƙarfin ba da
abin hannunsa. Mata ta ci amanar mijinta, miji ya ci amanar matarsa. Masu mulki
da shugabanni sun murje ido sun yi babakere da handamar dukiyar talakawa da aka
ba su amana. Babu gaskiya da amana tsakanin abokai da ‘yan uwa, ga abubuwa nan
dai duk sun taɓarɓare. Ba manufata ba ne da wannan bayanai cewa, babu
kyakkyawar zamantakewa baki ɗaya a ƙasar Hausa a yau ba, sai dai don yin
hannunka-mai-sanda ga al’ummarmu domin a farga ta yadda za a shawo kan matsalar
tun abin bai yi muni sosai ba.
Hanyoyin Farfaɗo da Zamantakewar Hausawa
A tunanina, taɓarɓarewar
da zamantakewar Hausawa ta yi a yau bai yi munin da za a kasa samar da hanyoyin
da za a warware matsalar ba muddin an himmatu da gaskiya. Dole iyaye su farga
wajen cusa kyakkyawar tarbiyya tagari a zukatan ‘ya’yansu ta yadda za su rayu
bisa turba madaidaiciya da za ta amfani al’umma, kamar gaskiya da mana, ladabi
da biyayya ga na gaba, sai kuma uwa-uba haƙuri wanda aka ce shi ne gishirin
zaman duniya.
Su kuwa malamai tilas su taka irin nasu rawa wajen gargaɗi a kan hani da horo
na koyarwar addini da al’ada a kan irin zalunce-zaluncen da ya yi katutu a
rayuwarmu ta yau. Haka zalika su ci gaba da bayyana wa jama’a irin mummunar
sakamakon da ke tattare da aikata miyagun ɗabi’u da al’adau ga masu aikata su.
Har wa yau, dole gwamnati ta sanya ido ga harkokin shari’a ta yadda za a
daidaita adalci ga kowa, da kuma hukunta duk wanda ya aikata ba daidai ba. Su
kuwa sauran mutane kowa ya tsaya ya tsarkake zuciyarsa da halayyanrsa ta yadda
rayuwarmu za ta sake komawa ga turba mai tsarki da muka gada daga magabatan da
suka wuce.
Kammalawa
Zamantakewa abu ne da ya
shafi illahirin rayuwar mutane, idan ya inganta, rayuwar al’umma ce za ta
kyautatu, idan kuma ya lalace, rayuwar al’umma ce za ta taɓarɓare baki ɗaya. A
taƙaice ana iya cewa, tun asali al’ummar Hausawa suna da ingantaccen tsari na
zamantakewa a tsakaninsu da kuma sauran jama’a masu maƙwabtaka da su. Sai dai
kuma, babban abin takaici a yau shi ne, wannan kyakkyawar halayya tana
fuskantar gagarumar barazana na taɓarɓarewa. Wannan kuwa yana faruwa ne saboda
son kai da kwaɗayin tara abin duniya, da rashin gaskiya da amana da haƙuri da
ya mamaye al’ummarmu ta wannan zamani. Sai dai ana cewa, ruwa na ƙasa sai ga
wanda bai tona ba, ma’ana za a iya bin wasu hanyoyi da aka ambata a baya wataƙila
a shawon kan matsalar ta yadda al’ummarmu za ta sake ginuwa kamar inda aka
fito.
MANAZARTA
Tuntuɓi
mai takardar.
1 Comments
[…] Ta’bar’barewar Zamantakewar Hausawa A Yau […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.