Abdullahi Sarkin Gulbi
asgulbi@yahoo.com
(08089949294)
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.
asgulbi@yahoo.com
(08089949294)
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.
Tsakure
‘Dabi’ar tsafe-tsafen magani dad’ad’d’iyar al’ada ce da ke faruwa a fad’in duniya. Tasirin addinin Musulunci ya sanya al’adar tsafe-tsafe ta ja da baya ainun, amma a wannan lokaci na dimokurad’iya sha’anin ya yi waiwayen baya. Dangane da haka ne wannan muk’alar , za ta tattauna dangane da irin yadda wannan d’abi’a take faruwa a wannan k’asar na aiwatar da tsafe-tsafe musamman a cikin harakokin da suka shafi neman shugabanci irin na dimokurad’iya.
1.0 Gabatarwa
Muk’asudin aiwatar da wannan takarda ba komi ba ne illa yin waiwaye tare da yin nazarin irin yadda aka koma gidan jiya dangane da tsafin magani da dangoginsa, musamman a lokacin da iskar guguwar siyasa ke kad’awa. Ba manufar binciken ba ne na k’ok’arin fayyace yadda ake harhad’a magungunan tsafi ba, a’a, nazarin zai karkata ne wajen lalubo irin ta’asar da jama’a kan yi domin cimma biyan buk’atunsu na samun muk’amai daban-daban irin na siyasa ta amfani da k’arfin maganin da aka danganta da tsafi, ko tsibbace-tsibbace. Kad’an daga cikin ire-iren ta’asar da ake yi kuwa sun had’a da ;yawaitar sace-sacen mutane, da salwantar sassan gawa a asibitoci ko bayan aukuwar had’ari, da d’ibar idanu da al’aurar mutane, da zubar da jini na dabbobi da tsutsaye, da turbud’ar makafi da kutare a raye, da turbud’ar dabbobi kamar karnauka da jakai da sauransu a raye, da salwantar mazakutar d’an takara, da mutuwar rik’is ta d’an takara, da kuma yawaitar luwad’i da aukawa k’ananan yara. Sai dai kafin nan, zai kyautu mu hangi ma’anar kalmar tsafi da magani da kuma dimokurad’iya, domin su ne fitillun kalmomin da suka haskaka taken bayanin da za a yi.
1.1 Ma’anar Tsafi
Wannan babban kandami ne da ya ta’ba d’aukar wani kaso na addinin gargajiyar Bahaushe tun tsawon zamunna. Kuma hanya ce da ta jagoranci imanin Bahaushe da ma sauran al’ummun da ke a doron k’asa.[i]Dangane da haka, idan ana magana a kan tsafi ba komai ake magana ba illa abu ne da ya k’unshi sadaukar da kai da camfi da zubar da jini da ba da rai da kafirce wa tafarkin kowane saukakken addini cikin yi wa Shaid’an hidima domin biyan wata buk’ata ta rayuwa.
1.2 Ma’anar Magani
A k’ark’ashin kiwon lafiya, kalmar magani sananniya ce ga kowane Bahaushe. Duk da haka, Masana da manazarta kamar: Alhassan da wasu (1982), Ahmad (1984), da Zulai (1984), da Tukur (1988), da Bunza (1990, da1995), da Gobir (2012) duk sun yi k’ok’arin fito da nasu ra’ayi a kan ma’anar magani. Wannan ya nuna cewa, ‘magani’ kalma ce mai iya d’aukar ma’ana mai fad’i, wadda kan sa dole a yi taka-tsantsan wajen bayar da bakandamiyar ma’anarsa[ii]. Duk da haka, da yake ‘kowa da ha’barsa yake tagumi’, ana iya fito da k’warya-k’waryar ma’ana da za ta fito da kalmar a fili, musamman a ‘bangaren kiyon lafiya da biyan buk’atun zuciya. Bisa ga haka, a fahintata, ana iya tak’aita ma’anar magani da cewa:
Magani shi ne duk wata hanya da za a yi amfani da ita domin
riga-kafin cuta ko rage rad’ad’inta ko ma a kawar da ita gaba
d’aya ko warwale wata matsalar rayuwa.Wannan hanyar tana
iya kasancewa ta kimiyar zamani ko a gargajiyance,
watau hanyar tsafi da tsibbace-tsibbacen al’umma.
1.3 Ma’anar Dimokurad’iya
Wannan bak’uwar kalmar ce da ta shigo harshen Hausa daga harshen Turancin Ingilishi da kuma Girkanci wadda take nufin wani k’e’ba’b’ben tsari da jama’a kan bi domin su za’bi shugabannin da za su wak’ilce su a fanni tafiyar da mulki domin su jagorance su a kan al’amurran rayuwarsu na yau da kullum.[iii] Idan haka abin yake, ke nan tsarin dimokurad’iya ya sha bamban da tsarin mulkin mulukiyya na sarautun gargajiya, wanda yake shi tsari ne da ake gado. Dangane da haka ne wasu ke fassara abin da cewa tsarin tafiyar da mulki ne da jama’a kan taru su kafa domin a jagorance su[iv].
1.4 Samuwar Tsafin Magani a Cikin Al’ummar Hausawa
Samuwar tsafi a cikin al’umma mahadi ne mai dogon zamani, domin ba wanda zai bugi k’irji ya ce ga lokaci, ko wata al’umma da suka fara aiwatar da tsafi. Hasali ma abu ne da ake iya samu a kowace al’umma da ke a doron k’asa tun a zamani mai nisa. Sannan kowace al’umma da tsafin da take bugun gaba da shi wajen bautarsu da biyan buk’atun rayuwarsu. Misali abin da aka sani ne cewa akwai tsafin Uwar gona da na kan gida da tsafin magiro da sauran tsafe-tsafe da maguzawan Hausawa kan yi a ‘bangarori da dama a k’asar Hausa. Duk da haka, domin duba a kan samuwa da tabbatuwar tsafe-tsafe a cikin al’ummar Hausawa zai yi kyau mu dubi irin yadda Mujaddadi Shehu Usmanu ‘Danfodiyo ya bayyana cikin littafinsa mai suna Nurur Albabi inda yake cewa: Hausawa na yi wa Jinnu hidima ta fuskar ajiye auduga a mararrabar hanya ko k’ark’ashin wasu manyan itace.[v] Saboda haka, idan aka yi la’akari da cewa bautar tsafi ita ce hanya ta farko da ta jagoranci imanin Bahaushe da ma sauran al’ummun da ke a doron k’asa, wanda zuwan addinin musulunci, da kuma irin tasirin da ya yi, na raunata tsafi da matsafa ya sa akasarin al’ummar Hausawa suka bar wannan bautar a dalilin kar’bar addinin musulunci da bin dokokinsa. Sai dai duk da haka, akwai Maguzawan Hausawa a Kano da Katsina(Kainafara) da sauran garuruwan k’asar Hausa da ba su daina yin tsafi da bautar Iskoki ba kamar bori da tsafi da dangoginsu.[vi]
Wannan tasirin ne ya sanya ake samun mutane da suke raja’a ga neman biyan buk’atu irin na kud’i, da aure, da mulki irin na sarauta da muk’aman siyasa da sauransu shiga gadan-gadan a cikin harkar tsafi domin biyan buk’atunsu.
1.5 Dalilan Tsafe-tsafen Magani a Cikin Al’umma
Hausawa sun ce “komai yana da dalili” dalilan da ke haifar da tsafe-tsafen magani suna da yawan gaske, wannan muk’alar za ta zak’ulo kad’an daga cikin dalilan wad’anda suka had’a da;
1.5 .1 Neman Waraka
Wad’annan magunguna ne da ake yi domin a kawar da cututtukan da ake gani a jikin mutum da ma wad’anda ba a iya gani. Irin wad’annan magunguna ne wani masani ya kira da suna “magungunan cuce-cucen jiki”.Inda ya bayyana su kamar haka:
Cuce-cucen jiki suna da yawa akwai wad’anda ido
ke iya gani, a ta’ba aji su, a kuma ga alamunsu. Kamar irin
su k’urji, da gwaiwa, da mak’ok’o, dankakkarai, da ciwon daji
da sauransu. Akwai wad’anda a cikin jiki suke, ko dai a
cikin ciki, ko cikin k’assa. Ire-iren wad’annan sun had’a da sanyin
k’ashi, da sanyin mata, da k’urjin hanji, da gwaiwar ciki, da sauransu.
Wad’annan cutuka sukan shafi jiki ne, kuma da zarar an yak’e
su da magani ana iya gano hak’ik’anin ci gaban da ake samu
wajen yi musu magani. [vii]
Sarkin Sudan (2000) cewa ya yi:
Magungunan warkarwa su ne magungunan da ake yi na
warkar da cututtukan da ake iya gani a jikin mutum dangin
k’urji ko gyambo,ko kumburi da kuma raunin da akan
samu a jiki,….da kuma wad’anda ba a iya gani sai dai
a ji rad’ad’insu ko a ga alamun kamuwarsu ta hanyar
kumburi ko rama ko hana gudanar da al’amurra
yadda ya kamata .[viii]
A ganina, magungunan warkarwa/waraka su ne magunguna da za a yi amfani da su domin a warkar da cutar da ta addabi mutum, ko dabba, ko tsiro, da nufin samar da walwala, da jin dad’i, da kuma annashawar rayuwa ta hanyar sha, ko shafawa, ko wanka, da turaren hayak’i, ko ratayawa, ko turbid’ewa da makamantansu wanda galibi akan yi su ta hanyar bokaye da malaman tsibbu.
1.5.2 Neman Cutarwa
Wad’annan magunguna ne da ake yi domin a cutar da wani ko wata ko ma wasu a bisa dalilan mu’amular yau da kullum. Irin wad’annan magunguna ne wani masani ya yi wa lak’abi da “Magungunan sharri”.Wad’anda suka had’a da kurciya, da sammu, da jifa, da kashe azzakarin namiji, da mallake wani ko wata da kashe wani ko wata, da nakasa wata ga’ba ta wani ko wata da sauransu. Hanyar samar da irin wad’annan magungunan sun fi ta’allak’a da tsafi da kuma tsibbace-tsibbace. Hakan ya sa ya zama d’aya daga cikin dalilan da ke sanya al’umma aiwatar da tsafin magani domin su cutar da wanda suke son cutarwa.
A fad’ar Bunza(1995) cewa ya yi:
Ga alama wad’anna rukunan magunguna suna da alak’a
da magungunan sihiri da shiddabaru. Dalili kuwa shi ne,
su dai magungunan sharri ba wai na maganin ciwo ne ba,
ba kuma riga kafin ba, domin ba wani ciwo da ke yi wa mutum
barazana a wannan lokaci. Ana neman wad’annan magunguna
ne kawai don sharri na karya abokan hamayya da razana su
da dubulbuta su. Magungunan sharri sun had’a da kashe
wa mutum zakari ,da yin kurciya, da sammu, da sake wa mace jini
a kowace rana, hana wa wani/wata aure, haukata wani/wata,
nakasa wani/wata, sa gobara a gidan wani/wata, tsorata wani/wata,
kunyata wani/wata, tsiyata/talauta wani/wata, fitar
da kishiya daga gida da sauransu. [ix]
Dangane da haka,wad’annan dalilan da suka bayyana daga ra’ayoyin masana da ya gabata su ne suka zama wata hujja ga masu jefa kansu ga aiwatar da tsafin magani su cutar.
1.5.3 Neman Kariyar Kai Da Kaya
Wad’annan magunguna ne da al’ummar Hausawa sukan tanada domin kare kai da kaya daga wata cuta gabanin ta auku, ko banza ma Hausawa sun ce “riga kafi ya fi magani”. Amfani da hanyar kare kai da kaya daga aukuwar cuta wani babban dalili ne ya ke sanya yin tsafin magani. Mu dubi abin da Ahmad(2011) ta hango dangane da magungunan kare kai da cewa:
shi ne duk wani magani da za a nema gabanin aukuwar
wata cuta ko wani had’ari ko bala’in da ake zaton
zai auku wanda hakan zai iya kawo wata illa ga rayuwar
mutum ko dabba ko dukiya ana kiransa kariya. [x]
A nawa hange kuwa, ina ganin magungunan kariyar kai da cewa, magunguna ne da Bahaushe ya tanada domin kariyar kowace irin cuta a kansa da iyalinsa ko zuri’arsa, da gidansa, ko garinsu ko k’auyensu, da gonarsa, ko kuma dukiyarsa gabanin ta auku. Irin wad’annan magungunan sun had’a da na baduhu, da sagau, da na kariyar had’arin mota, da maganin gobara, da na cizon kunama, da na sarar maciji, da na k’arfe, da kahin gida ko gona( hana sata) da d’aurin baki da sauransu. Dalili kuwa shi ne, ba domin kariya ga faruwar cuta ba, da Bahaushe bai tanadi wad’annan magunguna da aka lisafta ba. Wanda galibi akan had’a da dabarun tsafi ne wajen had’a magungunan.
1.5.4 Neman Biyan Buk’atun Zuciya
Zuciya ita ce ke d’auke da tunanin mutum a kowane lokaci, haka kuma duk wani imani da k’udurce-k’udurce na k’aunar wani abu ko rashin k’aunar abin, zuciya ce ke jagorancin abin.Wannan ne ya sa Hausawa kan ce “Zuciya babbar tsoka, idan kin yi kyau jiki kan shaida! Saboda haka ne Bahaushe ya tanadi magungunan biyan buk’atar zuciya domin cim ma muradun zuciyarsa masu kyau da marar sa kyawo.Wannan kuma ya zama dalili na aiwatar da mafi yawan tsafe-tsafen magani a Bahaushiyar al’ada.
Bunza (1995) ya kawo misalai na daga cikin ire-iren magungunan biyan buk’atun zuciya, wad’anda suka had’a da; magungunan had’a soyayya da raba ta, magungunan samun dukiya, ko mulki, ko aure ko cin nasarar wani abu, ko farin jini da sauransu.Ya k’ara da cewa ire-iren wad’annan buk’atu na d’an Adam ba ciwo ne ya shafi zuciyar mutum ba, kuma ba wani zogi ko zafi yake ji ba, illa abubuwa suna cin zarafin tunaninsa har su ta’ba birnin hankalinsa idan ba a tashi tsaye aka warkar da su ba.[xi] Irin neman biyan buk’atun zuciyar nan ne ke sanya ‘yan siyasa da sauran masu neman kujerun mulki kan fantsama cikin harkokin da suka shafi tsafe-tsafen magani domin biyan buk’atun rayuwarsu.
1.6 Nau’o’in Tsafe-tsafen Magani
A fagen nazari ana iya karkasa tsafi gida hud’u kamar yadda Bunza (2006:39) ya raba su,kamar tsafin bauta, da tsafin na buwaya, da tsafin na kare martabar gado, da kuma tsafin magani. A wannan bagiren, takardar za ta kalli rabe-raben tsafin magani da irin yadda ‘yan siyasa da sauran masu mulki ke amfani da magungunan tsafi domin kare muradun zuciyarsu.Yanayin da muka samu kanmu na siyasar zamani ya k’ara ruruta lamarin tsafi da dangoginsa, idan muka duba tun daga lokacin jumhuriya ta farko har ya zuwa yanzu, za a tarar da cewa akwai abubuwa da dama da suka zamar muna misalai na faruwar abubuwan tsafi a dalilin siyasa. Sau nawa ana kama ‘yan siyasa da wasu sassan jiki na mutum, ko su aika ‘yan bangarsu na siyasa su aikata, ko su yanka dabba su turbud’e ko a sha jininta ko a yayyanka namanta a rataye a bisa bishiya ko ice a cikin daji da sauran makamantansu? Mutum nawa ke jiran hukunci a gaban kotuna daban-daban, wad’anda aka kama da hannu wajen k’walk’wale idanuwa ko wani sashen na jikin d’an Adam a dalilin had’a maganin tsafi? Dangane da haka wannan bincike ya kalli magungunan tsafi ta fuskoki kamar haka;
1.6.1 Tsafin Neman Kud’i (Lukudi)
Wad’annan magunguna ne da ake amfani da su wajen biyan buk’atar mutum ta samun kud’i ido rufe ba tare da kula da had’urran da ke cikin lamarin ba.Yanayin da muka samu kanmu na ta’bar’barewar tattalin arziki yana d’aya daga cikin dalilan da suka sanya mutane shiga wannan halin. Bunza (2006:55-56) ya nuna cewa lukudi tsafi ne da ake yi domin a yi kud’i masu yawa.Wad’anda suka yi fice wajen amfani da wad’annan magunguna kuwa, su ne ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa. Ganin cewa siyasar yau ta zama sai mai kud’i a hannu ke iya shiga yak’in neman jama’a, ya sa ake samun wad’anda ke d’aukar kowane irin mataki na samun kud’i domin su zama wasu fitattun mutane a yankin da suke, wanda hakan zai ba su damar gwagwarmayar neman muk’amai daban-daban a matakai daban-daban na muk’aman siyasa.Wanda nake ganin hanyar samar da wad’annan magungunan dole sai an gama da ratse hanya(tsafi).
1.6.2 Tauri
Wannan yana d’aya daga cikin kashe-kashen tsafin magani a k’asar Hausa. Maganin tauri yana hana kowane irin k’arfe huda jikin mutum. Hanyoyin samun irin wad’annan magungunan kuwa, ba za su yiyu ba sai an had’a da ‘yan tsafe-tsafe[xii]. Galibi wand’anda aka fi sani da wannan magani su ne ‘yan tauri. Amma saboda yanayin da muka sami kanmu na siyasar k’asar nan da ta’bar’barewar tsaro shi ya sanya mutane masu neman kujerun mulki irin na siyasa amfani da tsafin maganin tauri domin kare kansu daga farmakin abokan adawar siyasarsu da kuma ‘yan fashi.
1.6.3 Tsafin Kwarjini (Neman Fice)
Kwarjini shi ne cika fuska ko haiba[xiii].’Yan siyasar wannan zamani sukan nemi irin wad’annan magungunan domin su sami kar’buwa ga jama’ar da suke neman goyon bayansu.Wad’anda suka shahara wajen bayar da ire-iren wad’annan magungunan kuwa su ne bokaye da malaman tsibbu.
1.6.4 Baduhu
Wannan magani ne na tsafi da ake amfani da wasu sassan dabbobi da kyanwar da ba ta bud’e ido ba, da suturar makaho ko makauniya wajen had’a shi.[xiv] Wanda duk yake cikin sihirin baduhu, to Bahaushe ya yi imanin cewa ba a ganinsa. A wancan lokaci da ya shud’e wad’anda suka shahara a fagen amfani da maganin baduhu akwai; mafarauta da mayak’a da fatake da kuma masu mulki irin sarakuna.A wannan lokaci kuwa, akan sami masu kud’i ko ‘yan siyasa tsamo-tsamo wajen amfani da wannan dabarar ta tsafin baduhu.Sukan tanadi irin wad’annan magunguna ne domin su kare kansu daga shairin mak’iya da farmakin ‘yan fashi da sauransu.
1.6.5 Rikid’a
Wannan magani ne da ake samu ta hanyar tsafi. Rikid’a kuwa nan nufin samun dama da iko na canza kama zuwa wani abu daban da ba ainihin halitar mutum ba. Misali rikid’ar mutum zuwa dabba, ko k’waro da sauransu[xv].Tsafin rikid’a tsafi ne da ake amfani da shi domin kare kai daga farmakin abokan adawa da kuma ‘yan fashi ko a gida ko a hanya. Bahaushe ya yi imani da samuwar irin wad’annan magunguna. A can da, mafarauta da sarakuna su ne suka yi fice wajen amfani da magungunan rikid’a. Amma a halin yanzu ana samun mutane musamman masu kud’i da ‘yan siyasa da suka shahara da yin amfani da irin wad’annan tsafe-tsafen magani.
1.6.6 Tsafin Nasara Da Samun Rinjaye
Wannan babban kandami ne na daga cikin tsafe-tsafen magani da ake aiwatarwa a lokacin mulkin dimokurad’iya a k’asar nan. Akasarin masu neman muk’aman siyasa sukan aikata hakan ko dai a kaikaice, ko kuma a kai tsaye ta hanyar malaman tsibbu (duba) da kuma bokaye. Da yawa akan sami mutane da suka fasa takara saboda kawai malaman dubansu ko bokayensu sun hango masu rashin samun galaba gabanin a yi za’ben. Za’ben kuwa kan kasance na share fage ne ko gaba d’aya. Wannan dalilin ne ya sa ake samun wasu mutane na shiga gadan-gadan ga harkar tsafin magani domin samun rinjayen kuri’u a kan abokan takararsu. Ire-iren wad’annan mutane sun d’auki cewa samun nasararsu ya dogara ne a kan abin da malamansu ko bokayensu suka fad’a.
https://www.amsoshi.com/2017/11/08/tabarbarewar-zamantakewar-hausawa-yau/
1.7 Shawarwari
- Kamata ya yi al’umma su rik’e karantarwar da addinin musulunci ya yi na hani ga aikata shirka da dangoginta, wanda hakan zai dad’a rage kaifin tsafe-tsafe a cikin al’umma.
- Kamata ya yi mu zafafa imaninmu wajen kad’aita Allah(SW) ga dukkan al’amurran da muka sanya a gaba na neman buk’ata. Domin shi kad’ai ya cancanci a nemi biyan buk’ata a wajenSa, ba wani boka ko malami ba. Dalili kuwa, shi ne mafi akasari masu tsunduma a harkar tsafin magani, miyagun malamai da bokaye ne ke kai su ga hakan.
iii. Ya kamata Malamai da sauran shugubannin addini su shiga gadan-gadan wajen wayar wa da mutane kai dangane da abin da shari’ar musulunci ta ce dangane da shirka da illolin yin ta. Wanda hakan zai k’ara cusa wa mutane jin tsoron Allah (SW) da kuma kaucewa aikata tsafe-tsafen magani.
- Kamata ya yi hukuma ta tsananta doka dangane da yadda za a hukuntar da dukkan wanda aka kama da hannu ga aikata wata ta’asa da ta shafi tsafe-tsafen magani. Ba wai idan aka kai mutum kotu ba, a ce ya yi amfani da kud’i ko wani gatanci a murd’e shari’ar ba.
- Akwai buk’atar tsalkake tsarin za’be a k’asar nan, kama daga za’ben share fage da kuma za’ben gaba d’aya. Yanayin tsarin siyasar k’asar nan, ya yi tasirin gaske wajen haddasa tsafe-tsafen magani. Dalili kuwa shi ne, wasu kan yi tsafe-tsafen ne domin su nemi kud’in shiga takara, wasu kuwa domin neman cin nasarar zaben, yayin da wasu kan yi tsafin ne domin kare kansu daga farmakin ‘yan bangar adawar siyasarsu.
1.8 Nad’ewa
Lokacin dimokurad’iya wani zango ne da wutar tsafe-tsafen magani ke hurawa a k’asar Hausa da ma sauran sassa na k’asar nan. Musamman idan aka yi la’akari da irin yadda ‘yan siyasa ke fad’i-tashi zuwa wajen malamai da bokaye domin neman taimakonsu a kan abin da suka kware na magani da warkarwa. Wannan muk’alar, kamar yadda aka gani, ta hangi lamarin a tsanake tare da gano wasu daga cikin dalilan da ke haifar da buk’atun tsafin magani a cikin al’ummar Hausawa da ma a wasu sassan k’asar nan. Muk’alar ta gano wasu daga cikin nau’o’in tsafe-tsafen magani da ake aiwatarwa a cikin al’ummar Hausawa musamman domin biyan buk’atun ‘yan siyasar wannan zamani. A k’arshe muk’alar ta bayar da wasu shawarwari ingantattu dangane da yadda za a rage wannan d’abi’ar a cikin al’umma.
Manazarta
Adamu, S.A. (2011), “Gurbin K’wari a Magungunan Gargajiya na Hausawa”. Kundin digiri na biyu (M.A), Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.
Alhassan, H. da Wasu (1982), Zaman Hausawa. Institute of Education Press, ABU Zaria.
Bargery, G.P. (1934) A Hausa-English and English-Hausa Vocabulary. Oxford University Press, London.
Bunza, A.M.(1990), “Hayaki Fid Da Na Kogo”. Kundin digri na biyu (M.A.), Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.
Bunza, A.M. (1995), “Magungunan Hausa A Rubuce.” Kundin digiri na uku (PhD) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza, A.M. (1999), “Rad’ad’i Da Zogin Cuta A Ma’aunin Bahaushe.” Muk’alar da taron K’arawa juna sani, Sashen Koyar da Hasrsunan Nijeriya, Jami’ar Usman Danfodiyo, Sakkwato.
Bunza, A.M. (2004) “Mahad’in Mugungunan Gargajiya”. Muk’alar da aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu’Danfodiyo, Sakkwato.
Bunza, A.M. (2006) Gadon Fed’e Al’ada . IBRASH LTD. Lagos
C.N.H.N (2006) K’amusun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Gobir, Y.A (2002) “Mahad’in Maganin Iska”. Muk’alar da aka gabatar a Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.
Gummi, A. M. (1997) Alk’ur’ani Maigirma Da Kuma Tarjamar ma’noninsa Zuwa Ga
Harshen Hausa. Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci, da Wak’afai, da kuma Wa’azi da Shiryarwa, ta K’asar Saudi Arabiya.
Hamza, M.W. (1977) “Magungunan Hausawa”. Kundin digirin farko, Jami’ar Bayero, Kano.
Ingawa, Z.S (1984) “Magungunan Hausawa Don Mata”. Kundin digirin farko, Jami’ar Bayero, Kano.
Oxford Advanced Learner’s Dictionary of Current English. New Eight Edition. Oxford
University Press. London.
Sarkin SudanI.A. (2000), “Magani da Siddabaru Cikin Rubutattun K’agaggun Labaran Hausa”. Kudin digri na biyu, Jami’ar Usman Danfodiyo, Sakkwato.
Sarkin Sudan I.A.(2008) “Jiya ba Yau Ba:Waiwaye A Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa Na Aure Da Haihuwa Da Mutuwa”. Kundin digirin PhD Jami’ar Danfodiyo,Sakkwato.
Shehu Usmanu ‘Danfodiyo, Nurul Albabi
The New World Encyclopedia Vol.5 . The Caxton Publishing Company Limited. Printed
in U.S.A
Tukur,A. (1988) “Nazari a Kan Cututtukan da Suka Shafi Fatar Jiki da Magungunansu a
Bahaushiyar Al’ada”. Kundi digirin Farko. Jami’ar Bayero. Kano
Wak’ar Muhammadu ‘Dantudun Doki ta Ilaje Mafarauci.
[i] Don k’arin bayani dubi Bunza,A.M (2006:35) inda yake cewa:Tsafi shi ne wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi wa Iskoki hidima, da yanka, da bauta, domin biyan wata buk’ata ko samun wani amfani, ko tunkud’e wata cuta. A cikin K’amusun Hausa(2006:449) an bayyana tsafi a matsayin hanyar ba da gaskiya da wani abu daban da ba Allah ba.
[ii] Gobir Y.A.Mahadin Maganin Iska. Muk’alar da aka gabatar a sashen Nazarin Harusanan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo.sakkwato.Ranar 6-11-2012.
[iii] A dubi K’amusun Hausa(2006:104) tafarkin mulki da mutanen k’asa ke za’bar shugabanninsu ta hanyar jefa kuri’a.
[iv] A dubi The New World Encyclopedia Vol.5,1973:1503. Democracy:From the Greek, meaning the rule of the people, as opposed to monarchy and aristocracy, an ancient Greek conception of government where by the people direct the activities of the the state, either directly or through representatives………Today, democracy represents “government of the people, by the people, for the people.”Da kuma, Oxford Advanced Learner’s Dictionary of Current English:Eight Edition page 388. Democracy :A system of government in which all the people of a country can vote to elect their representatives.
[v] Nurur Albabi Littafin Shehu Usmanu ‘Danfodiyo.
[vi] Dubi Sarkin Sudan I.A. “Jiya ba Yau Ba:Waiwaye A Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa Na Aure Da Haihuwa Da Mutuwa. Kundin digirin PhD Jami’ar ‘Danfodiyo,Sakkwato.2008, shafi na 189,270,315. Da Kuma fatawar kwamitin fatawa na duniya, mujalladi na 11 shafi na 414-415.
[vii] Dubi Bunza A.M .Hayak’i Fid da Na Kogo.Kundin digiri na biyu Jami’ar Bayero,Karno 1990,3 shafi na 101.
[viii] Dubi Sarkin Sudan I.A, “Magani da Siddabaru Cikin Rubutattun K’agaggun Labaran Hausa”, Kudin digri na biyu, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.2000, shafi na 19.
[ix] Dubi Bunza, A.M Magani A Rubuce:Nazarin Ayyukan Malaman Tsibbu A Kasar Hausa.kundin digiri na uku, BUK. 1995 shafi na 102-103.
[x]Ahmad,S.A.Gurbin Kwari a Magungunan gargajiya na Hausawa. Kundin M.A.Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo,Sakkwato,2011,shafi na 27.
[xi] Dubi lamba ta 8 shafi na 102
[xii] Shehu Usmanu ‘Danfodiyo ya yi maganar maganin tauri a cikin littafinsa mai suna Surajul Ikhwani inda ya nuna cewa tsafi ne.
[xiii]K’amusun Hausa 2006,shafi na 266.
[xiv] Bunza A.M. Gadon Fed’e Al’ada Tiwal publishers, Lagos 2006,shafi na 41
[xv] Wak’ar Muhammadu Dantudun Doki ta Ilaje inda yake cewa:Ilaje ya zama ragga
Shi ko zaki me ya koma
Zaki ya zama k’eya kwance tsakanin ragga
Ya ce matabbatata annan, sai na ga mai shisshe ni
Ana shirin wadda a kai
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.