NA
MUSA SHEHU
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
msyauri@yahoo.com
07031319454
TSAKURE
Masu iya magana na cewa, “zaman lafiya ya fi zama d’an sarki”. Yunk’urin da ake ta famar yi na ganin zaman lafiya ya samu inuwar hutawa a k’asar Hausa da ma Nijeriya baki d’aya bai bar sha’iran Hausa a bayan fage ba. Akwai rubutattun wak’ok’in Hausa da dama da wasu sha’irai suka rubuta domin ba da tasu gudunmuwa ga samar da zaman lafiya da sasantawa. Manufar wannan takarda dai shi ne fed’e wak’ar zaman lafiya ta Bashir Musa Liman domin fito da hikimomi ko falsafar da ke cikin wak’ar, wanda suka had’a da bayanin amfanin zaman lafiya, hanyoyin samar da zaman lafiya, dalilan da ke haddasa rashin zaman lafiya, da illolin rashin zaman lafiya da sauransu.1.0 Gabatarwa
‘Dangambo (1981) cewa ya yi “Wak’a wani sak’o ne da aka gina shi kan tsararriyar k’a’ida ta baiti, d’ango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (k’afiya), da sauran k’a’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, za’bensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”. Gid’ad’awa (2006:174) cewa ya yi: “Wak’a dai magana ce tsararriya wadda ake shiryawa a bisa wasu muryoyi na musamman, wadda kuma ta bambanta da maganar yau da kullum. Tsara wak’a baiwa ce ta Ubangiji sai wanda Allah ya hore wa ita zai iya. Hausawa sun fara rubuta wak’a ne ta dalilin isar da sak’on Allah, wato domin yin wa’azi ga jama’a domin su koma tafarkin Allah makad’aici. Ladan (1975) ya bayyana cewa, marubucin wak’ok’in Hausa yana nazarin abin da aka fi shagalta da shi, idan na zarafin duniya ne, ya fad’i ra’ayinsa a kansa, idan kuma na addini ne ya yi wa mutane wa’azi.[i] Misali, a cikin k’arni na 18 da na 19 lokacin da aka himmatu kan jaddada addini, wak’ok’in Hausa na wannan zamani duk sun k’unshi wa’azi ne. A wajen tsakiyar k’arni na 20 kuwa, lokacin da aka shagalta da yak’in duniya na biyu, da ilimin zamani da siyasa da tafiye-tafiye zuwa k’asashen Turai, an sami hazik’an marubuta wak’ok’i da suka wak’e wad’annan al’amurra, kamar Malam Sa’adu Zungur, Malam Mu’azu Had’eja, Alhaji Mudin Sipikin da makamantansu.
To sai dai kuma, wannan zamani na k’arni 21 ya zo ne da rikice-rikice da tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na k’asar Hausa da ma Nijeriya baki d’aya. Zaman lafiya ya kasa samun gindin zama, don haka aka sami wasu marubuta wak’ok’in Hausa wad’anda suka himmatu wajen wak’e sha’anin zaman lafiya, kama daga alfanun zaman lafiya, da hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, da hanyoyin kariya daga aukuwan rikici, da illolin da ke tattare da rashin zaman lafiya, da makamantansu. Wad’annan abubuwa ne wannan takarda za ta mayar da hankali wajen nazarinsu kamar yadda marubuta wak’ok’in Hausa suka kalle su.
https://www.amsoshi.com/2017/11/08/makamin-dimokradiyya-a-falsafar-alada/
2.0 Ma’anar Zama Lafiya
Zaman lafiya a Bahaushen tunani shi ne, zama cikin natsuwa, da sakewa da rashin fargaba da tashin-tashina ta kowace fuska. Zama ne da ba ka cuta ba, ba a cuce ka ba. Zama ne na aminci ga k’asa da wad’anda ke cikin ta, da wad’anda za su ziyarce ta, da wad’anda za su fice daga cikin ta, da wad’anda ke mak’wabtaka da ita. Zama ne da zai bai wa duk wanda ke cikin k’asa d’an asalin ta, da bak’nita na arziki, da ‘yan gudun hijirarta, da masu zaman mafakar siyasa a ciki, natsuwa da kuranye firgita a zukatansu. Zaman lafiya zama ne na d’ebe d’ammaha ga duk wata hayagaga da ru’bushi da ta da zaune tsaye da wata halitta za ta haddasa ga wanda ke cikin ta, face abubuwan da babu makawa aka k’addaro gare ta daga mai k’addarawa (Allah)[ii].
A K’amusun Hausa (2006) ba a kawo ma’ana d’aya da ta shafi kalmomin biyu ba, wato ‘zama da lafiya’, sai aka kawo ma’anonin kalmomin daban-daban kowane yana cin gashin kansa. Don haka aka bayyana ma’anar zama da “kasancewa zaune”, wato kishiyar tsayuwa, lafiya kuma aka bayyana ta da “rashin tashin hankali da hargitsi a wuri.” Saboda haka, idan aka dubi ma’anonin kalmomin biyu za a ga suna bayyana ma’anar zaman lafiya da kwanciyar hankali da rashin rigingimu da fitina a cikin jama’a.
Ibeanu (2006) ya kawo ma’anoni kamar guda biyar da suka shafi fannoni daban-daban na ilimi a kan zaman lafiya, ga su kamar haka:
Zaman lafiya na nufin rashin wanzuwar yak’i; yak’i kuma na nufin rashin wanzuwar zaman lafiya. Don haka, a koyaushe kalmomin biyu ba sa had’uwa wuri d’aya, dole a kiyaye su da yadda suke wakana a rayuwa.
A ma’ana ta ilimin falsafa kuwa (Philosophical definition), zaman lafiya na nufin rashin wanzuwar cin hanci ko rashawa a cikin al’umma kamar yadda Allah Ya tsara. Haka ma, ana iya cewa, zaman lafiya yanayi ne na kyakkyawar rayuwar al’umma a doron k’asa da bai riga ya gur’bata ba.
A fannin ilimin walwalar rayuwa (Sociological definition), zaman lafiya na nufin yanayin had’in kan al’umma na rashin tashin-tashina a tsakaninsu. A wata fad’ar kuma, zama lafiya na nufin wani yanayi ne na rashin wanzuwar rikice-rikice a tsakanin d’aid’aikun mutane ko k’ungiyoyi ta yadda za su iya samun damar biyan buk’atun rayuwarsu cikin lumana.
A fannin siyasa kuma (Political definition), kamar yadda Jami’ar zaman lafiya ta bayyana, zaman lafiya shi ne tsarin siyasa da ke tabbatar da wanzuwar adalci ga al’umma. Daga nan kuma marubucin ya bayyana ra’ayinsa kan ma’anar zaman lafiya yana cewa, zaman lafiya al’amari ne da ya shafi al’amurran da suka shafi bunk’asa da ci gaba kai tsaye ko a fakaice, da rage rikici a cikin wata al’umma da ma al’ummomin duniya baki d’aya.[iii]
Francis (2006) yana cewa, zaman lafiya na nufin rashin wanzuwar yak’i, tsoro, rikici, fargaba, wahala, da ta’addanci, da kuma wanzuwar lumana. Wato abu ne da ya shafi samuwa da d’orewar adalci a cikin al’umma da kuma sasanta rikici ta hanyar ruwan sanyi.[iv]
3.0 SASANTAWA
Sasantawa (Conflict Resolution) wani al’amari ne mai muhimmancin gaske a rayuwar kowace al’umma. A duk lokacin da wasu rikice-rikice ko yak’e-yak’e ko tashin-tashina suka wanzu a tsakanin al’umma, hanya mafi dacewa da ya kamata a yi amfani da ita domin warware su cikin ruwan sanyi da kuma dawo da zaman lafiya mai d’orewa ita ce hanyar sasantawa ko yin sulhu a tsakanin masu husuma.
A k’amusun Hausa (2006) an bayyana ma’anar sasantawa da shiga tsakanin masu husuma biyu, ko kuma sulhu.[v] A cikin K’amusun Oxford an kawo ma’anar sasantawa da cewa, yanayi ne na warware ko daidaita matsala, jayayya, da sauransu.[vi]
4.0 Musabbabin Rikice-Rikice
Duk wata matsala ko rikici da ya auku a rayuwa akwai musabbabin aukuwarsa, ko dai kai tsaye ko a fakaice. Marubuta wak’ok’in Hausa daban-daban sun bayyana wasu dalilai da ke haddasa rashin zaman lafiya a wak’ok’insu na “zaman lafiya” wad’anda suka had’a da:
Rashin Adalcin Shugabanni: Ba shakka, rashin adalcin shugabanni na taushe hak’k’in talaka, da tursasa shi, da yin ko-oho da muradun rayuwarsa, sun taka muhimmiyar rawa wajen rashin samuwar zaman lafiya da ake fama da shi a yau a k’asar Hausa. Shugabanni sun kasance marasa gaskiya, da rashin amana, da rashin cika alkawali musamman ga ‘yan siyasar wannan zamani, da uwa-uba barazanar da ake yi wa rayuwarsu a kullu yaumin. Bashir Musa Liman a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 10 da 11 da 12 da 17, yana cewa:
Baiti na 10 Masu iko sun yi k’i-mudu-gus
Wajen bai wa talaka hatsin gus-gus
Su kuwa suna ta tauna gurus-gus
Hakan ya haifar da zaman k’iyayya
Baiti na 11 ‘Yan siyasa suna alkawartawa
Idan sun ci za’be za ai morewa
Suna ci sai su zam ‘bacewa
Hakan ma na jawo hatsaniya
Baiti na 12 Masu mulki suna shek’a mulki
Wanda ya sa wasu ke take hakki
Almundahana, danniya da zulak’i
Wanda ta sa talaka yin gogayya
Baiti na 17 Masu iko na fashi da muk’ami
An bar talakawa cikin jimami
Da warin jiki mai tsabar hamami
Ga ruwan hawaye na zuba a idaniya
Talauci da Rashin Aikin Yi: Talauci da rashin aikin yi na daga cikin abubuwan da ke kassara rayuwar al’umma, wanda a mafi yawan lokuta idan ba a kai zuciya nesa ba, sai a fad’a ga aikata miyagun ayyuka wad’anda za su iya haddasa fitina da rashin zaman lafiya. Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a wak’arsa ta gasar wak’ok’in zaman lafiya a baiti na 57 da 58, ya bayyana rashin aikin yi na haddasa rashin zaman lafiya a cikin al’umma, yana cewa:
Baiti na 57 Rashin aikin yi shi ka kawo
Zaman banza a yi gardama
Baiti na 58 Da sannu abin ya game gari
Har ya watsu k’asa ya k’udan zuma
Bashir Musa Liman a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 18 da na 19, ya bayyana talauci da rashin aikin yi daga cikin musabbabin hana zaman lafiya a cikin al’umma, yana cewa:
Baiti na 18 Talauci ya sanya fashi da makami
Kana gida ka ga ‘barayi da makami
A kan hanyar tafiya ma da makami
Ka bayar da kud’i ka zauna lafiya
Baiti na 19 Matasa ba aikin yi sai zaga gari
Ba su da ko sule, balle zancen d’ari
Hakan kuwa ya sa su cikin garari
Wanda ya sa suke ta hatsaniya
5.0 Illolin Rashin Zama Lafiya
Rashin zaman lafiya babbar musiba ce a rayuwar al’umma, domin yakan haddasa talauci da fargaba da ta’bar’barewar tattalin arziki, da hasarar dukiyoyi da ma rayuwa baki d’aya. Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 81 da na 82 da na 99 da na 100, ya bayyana irin illolin da ke tattare da rashin zaman lafiya a cikin al’umma, wanda ya had’a da ta’bar’barewar ilimi da tattalin arzikin k’asa, yana cewa:
Baiti na 81 Kashe ilmi fitina ka yi
Duk ta k’are manyan maluma
Baiti na 82 Takan k’are jama’ar k’asa
Duk su tsere ba mai sallama
Baiti na 99 Jidali na tauye darajar k’asa
Ga idanun al’uma
Baiti na 100 Ya toshe tafarkin arziki
Ba zama na lumana an gama
Shi ma Bashir Musa Liman a wak’arsa ta zaman lafiya a baiti na 5 da na 7 da na 15, yana bayyana irin illolin da rikicin Arewaci da Kudancin Nijeriya suka haifar, wanda suka had’a da hasaran rayuka da dukiya, yana cewa:
Baiti na 5 A Kudu maso gabas ana ta hatsaniya
Suna fasa bututun mai da hauragiya
Tattalin arziki ya zama koma baya
Muna cikin talauci ba zaman lafiya
Baiti na 7 A Arewacin k’asata har da Maiduguri
Ana ta rikici na addini babu tsari
Rayuka da dukiyoyi sun ‘bata ba ik’irari
Wanda hakan ya haifar da k’iyayya
Baiti na 15 Rayuwa ta zam ta’bar’barewa
Al’amurra sun zam rikirkicewa
Komai da komai yai k’azancewa
Sai lahaula a k’asata Nijeriya
6.0 Matsayin Mai Hana Zama Lafiya
Babu wata al’umma da ta aminta da mai tayar da k’ayar baya, balle ma ta yi masa tarbon arziki. Wannan ya sa duniya take kiran masu tayar da zaune tsaye da suna ‘yan ta’adda. Don haka ma Hausawa ke da karin maganar da ke cewa: “Maso fad’a wawa” da kuma “Fitina kwance take, Allah ya la’ani mai tayar da ita”. Malam Sambo Wali ya bayyana irin wannan matsayi na mai tayar da zaune tsaye a wak’arsa ta “Ku bar fad’a ku bar son yaya” a baiti na 13 da na 19, yana cewa:
Baiti na 13 Fad’a halin matsiyaci ne don ba shi da komi
Bak’in cikin mutan kirki sun tattara komi
Shi bai aje ba ‘banna ba ta cin shi da komi
Mai arziki ka tsoron fitina ko bisa komi
Don ba ya son abin da duk ka lalata bid’atai
Baiti na 19 Dut ‘yan k’asarmu Afirka ban d’ebe guda ba
A bar fad’a a bar son yaya ba falo na ba
Mai hankali tunani yaka yi ba sababi ba
Fad’a halin matsiyaci na hauka shika wo ba
Ko mace na iza shi ga ‘bannatai ya ga daidai
Shi ma Hamisu Lamid’o wanda aka fi sani da Hamisu Iyantama, ya bayyana matsayin mai ta da fitina a cikin mutane a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na farko kamar yadda Malam Sambo Wali ya bayyana, yana cewa:
Baiti na 1 Fitina kwance take hankali kwance ne
Duk wanda ya tashe ta shaid’ani ne
Tsinuwar Allah yai la’anta ne
Ga wanda duk ya ta da hankalin juna
7.0 Hanyoyin Zama Lafiya da Sasantawa
Rubutattun wak’ok’in Hausa ba a bar su baya ba wajen k’ok’arin bayyana hanyoyin da suka dace mutane su rik’a amfani da su domin d’orewar zaman lafiya da sasantawa. Daga cikin wad’annan hanyoyi da marubuta wak’ok’in Hausa sukan bayyana a wak’ok’insu akwai: Hak’uri da taimakon juna da son juna da kauce wa rud’in duniya da neman ilimin addini da ilimin kimiyya da sauransu.
Hak’uri: Hak’uri muhimmin sinadari ne da za a yi amfani da shi wajen samar da zaman lafiya da d’orewarsa a rayuwar al’umma. Da mutane za su rik’a sa hak’uri a dukkan al’amurran rayuwarsu, da wasu fitintinu ba su addabe su ba. A wak’arsa ta “zaman lafiya”, Bashir Musa Liman ya kawo bayanin hak’uri a baiti na 25 a matsayin hanyar zaman lafiya musamman dangane da rikice-rikicen siyasa da ya mamaye Hausawa a yau, yana cewa:
Baiti na 25 ‘Yan siyasa su san cewa
A za’be akwai ci da fad’uwa
In sun fad’i su zan hak’urewa
Haka zai haifar da zaman lafiya
Wannan baiti yana kira ne musamman ga ‘yan siyasa da ‘yan bangarsu da ke tayar da k’ayar baya idan ba su samu nasara ba. Kamata ya yi su bar wa Allah su d’auki k’addarar fad’uwa, wata rana za su iya samun nasara.
Adalci ga Shugabanni: Duk al’ummar da ta ribantu da samun adilan shugabanni masu k’ok’arin kyatata wa mabiya da kare martabarsu da ba su kariya ga duk wani abu da ka iya barazana ga zamantakewar rayuwarsu. Yin hakan zai sa zaman lafiya ya sami sukunin walwala, yayin da tashe-tashen hankula da rikice-rikice za su k’aranta. Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a wak’arsa ta gasar wak’ok’in zaman lafiya a baiti na 13 da 27, yana cewa:
Baiti na 13 A tabbata duk sha’anin k’asa,
‘Yan k’asa kowa ya tsunduma.
Baiti na 27 Hukuma ya zama wajibi gun ki,
Dole ki tashi ki d’au tsuma.
Bashir Musa Liman a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 26, kira ya yi ga shugabannin siyasa da su sauke nauyin da aka aza musu na kare martaba da hak’k’ok’in talakawan da suke wakilta, domin yin hakan ne zai kawo d’orewar zaman lafiyar al’umma. Ga abin da yake cewa:
Baiti na 26 Su kuma wad’anda suka kai ga d’arewa
Ga muk’ami, kujera suna masu lilawa
To, su sauke nauyi da hak’k’in talakawa
Don a samu kyakkyawan zaman lafiya
Taimakon Juna: A duk lokacin da al’umma suka had’a kansu wuri d’aya wajen taimaka wa junansu domin warware wasu matsaloli na rayuwa, ba shakka rayuwarsu za ta kyautata, kuma zaman lafiya zai sami filin baje kolinsa a tsakaninsu. Ga abin da Bashir Musa Liman ke cewa dangane da taimakon juna a baiti na 28 da na 30:
Baiti na 28 Masu kud’i ku zan taimakawa
Kayan masarufi ku zam bayarwa
Taimakon talaka ku ci gaba da yowa
Wannan zai sa a samu zaman lafiya
Baiti na 30 Mu so juna, mu k’aunaci juna
Mu ji tausayi, mu taimaki juna
Mu agaza, mu kyautata wa juna
Yin haka zai sa a zauna lafiya
Kawar da Bambancin Addini da K’abilanci: Nuna bambancin addini da k’abilanci na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rikice-rikice da rud’ani a k’asar Hausa, wad’anda suka jima suna ci wa mazauna k’asar tuwo a k’warya. Sha’iri Farfesa Aliyu Muhammada Bunza a wak’arsa ta gasa mai suna “mu zauna lafiya” a baiti na 35 da 36 da 44 da baiti na 45, kira ya yi da a kauce wa tashin-tashinar addini da k’abilanci domin jama’a su zauna lafiya, yana cewa:
Baiti na 35 Dukkan masana a cikin ‘Darik’a
Izala Shi’a na gama
Baiti na 36 Ku daina jidalin k’ungiyoyi
Da jayayya don mai sama
Baiti na 44 K’abilanci cutarsa ya k’aik’ayi
Tsami wane rama
Baiti na 45 Yana kawo yak’i k’asa sai,
Ta tarwatsa babu wurin zama
Shi ma, Muhammadu Sambo Wali a wak’arsa mai suna “ku bar fad’a ku bar son yaya..” a baiti na 8 da na 11, kira ya yi da a guji nuna bambancin addini da k’abilanci musamman tsakanin Musulmi da Kirista. Ya nuna cewa, tun da Allah ya riga ya halitto mu wuri d’aya, kamata ya yi mu hak’ura mu zauna tare don mu amfana da juna. Ga abin da yake cewa:
Baiti na 8 A bar fad’an k’abilanci ban yarda da shi ba
Fad’an a tsarkake jinsi bai sahi da mu ba
Ubangijinmu yay yo mu k’asa d’ai fa ki duba
Da yai nufin mu watse da bai yo haka nan ba
Nufin yakai mu amfana da junanmu gaba d’ai
Baiti na 11 Nan da d’ai Musulmi muke mun tsere tsara
Bisa dole an ka mulke mu ga mulki na Nasara
Ku rik’e fad’in Lakum Dinukum ba ta da gyara
A nan akwai Kiristoci na bayyana saura
Ga zamantakewa kowa tashi ta fissai
Bashir Musa Liman a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 31, ya bayyana kawar da nuna bambancin wad’annan abubuwa biyu (addini da k’abilanci) a zukatan al’umma, wani mataki ne na zaman lafiya da kawar da rikice-rikice, yana cewa:
Baiti na 31 Idan muna so mu zam walawa
‘Bangaranci ya zamto mun wullarwa
Yarenci da k’abilanci, mu zam kaucewa
Hakan zai sa a yi daddad’ar dariya
Kauce wa Rud’in Duniya: Ko shakka babu, duk wanda ke biye wa rud’in duniya zai iya fad’awa cikin halaka ko da-na-sani. Wannan ya sa da yawa daga cikin rikice-rikicen da ke addabar mutane akwai rud’in duniya na biye wa son zuciya suna aikata masha’a ba tare da tunanin abin da zai biyo baya ba, mai kyau ko akasinsa. Wannan ya sa Bashir Musa Liman a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 33 da 34 da 35, yake gargad’in mutane da su guji irin wannan rud’i na duniya don a samu zaman lafiya mai d’orewa:
Baiti na 33 Jama’a mu guji rud’in budurwar duniya
K’azamiya, mamugunciya, makauniya
Asharariya, ibilishiya, mayaudariya
Mak’aryaciya, mahillaciya, mazambaciya
Baiti na 34 Rud’inta ke haifar da k’iyayya
Har ya zamto ana ta bugayya
Yaudararta ta wuce sanayya
Ta wani, bare a yi zancen dubayya
Baiti na 35 Ya kamata mu yo tunani
Don tantance yanayin zamani
Don guje wa sharrin shaid’ani
Wanda ba ya son zaman lafiya
Ilimi: Samuwar ilimin addini had’i da na zamani yana taimakawa k’warai wajen wanzar da zaman lafiya da sasantawa. Haka ma, rashinsa a cikin al’umma yana haifar da rud’anin tashe-tashen hankula da wanzar da k’iyayya. Haka kuma, samuwar tarbiyya tagari ga al’umma wani sinadari ne na dauwamar da zama lafiya a cikinsu. Wannan ya sa duk al’ummar da ta rasa kyakkyawar tarbiyya musamman ga matasa, tilas ayyukan ta’addanci da rashin zama lafiya su addabe ta. Har wa yau, Bashir Musa Liman a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 37, yana gargad’in al’umma da su tashi tsaye wajen neman ilimi da kuma samar da tarbiyya domin rayuwa ta sami walwala da sakewa, yana cewa:
Baiti na 37 A yi ilimin addini da na kimiyya
Kuma a k’asa idan aka samu tarbiyya
Mu lura k’asa za ta zauna lami lafiya
Da rayuwa ba kwan gaba, kwan baya
Dakta Aliyu Tilde ya yi irin wannan gargad’i a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 35 ya ce a nemi ilimin addini da na zamani domin a sami zama lafiya da ci gaban tattalin arziki:
Baiti na 35 Mu rungumi ilmu na dini da duniya
Ci gaba rizk’u don zaman lafiya
Had’in Kai: A yayin da kawunan al’umma ya rarraba, kowa ya kama gabansa, tilas fitintinu da rashin zaman lafiya su wanzu a tsakaninsu. Had’in kansu wuri d’aya kuma, shi zai kawar da duk wata gaba da zogin zuci da kuma duk wani tashin-tashina da kawo zaman lafiya. Da ma Hausawa na cewa: “Hannu d’aya ba ya d’aukar jinka” Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a wak’arsa ta gasa mai suna “mu zauna lafiya” a baiti na 9 da na 10, ya bayyana had’in kan al’umma daga cikin abubuwan da ke zaunar da su lafiya, yana cewa:
Baiti na 9 Ku zamto k’asa d’ai zuriya d’aya
Zaman dad’i tamkar zuma
Baiti na 10 Irin haka shi ke sa k’asa
Ha’baka ya zamo ta kankama
Hamisu Iyantama a wak’arsa ta “zaman lafiya” ya fito da wannan jigo na had’in kai domin samun zaman lafiyar al’umma a baiti na 4 da na 10, yana cewa:
Baiti na 4 Mu dena raba junanmu babu ci gaba
Ta kowace siga mu bar yin gaba
Idan Allah ya so ba zai bambanta mu ba
Halittarmu sai ya yo kamannin juna
Baiti na 10 Mu had’a kai al’umma d’aya kar mu rarraba
Muna kira mu jure wa halin juna
Mu zauna lafiya, mu zauna lafiya
Mu zauna lafiya tsakanin juna
Addu’a: A duk lokacin da wani al’amari ya zama tarnak’i ga rayuwar Hausawa, ya k’i ci ya k’i cinyewa, za ka iske an mayar da lamarin ga hannun Ubangiji ana yawaita addu’ar samun mafita domin ku’butar da rayuwa ga irin barazanar da ake yi mata. Wannan ya sa marubuta wak’ok’in Hausa bayan sun bayyana irin hanyoyin zaman lafiya, sai kuma su biyo da addu’a ga mahalicci domin ya sa hannu cikin lamarin. Wannan shi ya haifar da yawaitar amfani da karin maganar Hausawa da ke cewa: “Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya”. Bashir Musa Liman a wak’arsa ta “zaman Lafiya” a baiti na 39 yana cewa:
Baiti na 39 Rok’ona ga Ubangiji Makad’aici
Mai halitta har da iccen mad’acci
Wanda ya sa har abinci nakan ci
Ya sa k’asata a yi zaman lafiya
Baiti na 40 Tammat a wak’e na zo k’arshe
Don alfarmar Annabin k’arshe
Dace da ganinsa shi ne k’arshe
Allah ya sa a samu zaman lafiya
Shi ma Aliyu Tilde ya yi makamancin wannan addu’a na samun zaman lafiya mai d’orewa a cikin al’umma, a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 30 da 31 da 34 da 87, yana cewa:
Baiti na 30 Ta’ala mashiryi ga ni gare ka
Ina zan ka rok’on zaman lafiya
Baiti na 31 Gare ni da ‘ya’ya da mata dukkanmu
Da dangi abokai ga baki d’aya
Baiti na 34 Fitintinu na baya kaza na zamanu
Ka kare mu Jalla mu zam lafiya
Baiti na 87 In yi sujuda in gode Allah
Ta’ala ka zaunar da mu lafiya
8.0 Amfanin Zama Lafiya
Hak’ik’a babu wani abu d’aya mafi alfanu a rayuwar al’umma da ya kama k’afar zaman lafiya. Sai da zaman lafiya basarake zai gudanar da mulkinsa a tsanake. Mai arziki ba ya more wa dukiyarsa idan babu zaman lafiya. Walwala ba ta samuwa ga talaka idan ba a zaune lafiya. Wannan ya sa Hausawa ke cewa: “Zama lafiya ya fi zama d’an sarki, ko ma ya fi zama sarkin.” A kan haka ne marubuta wak’ok’in Hausa suke bayyana alfanun zama lafiya domin al’umma su rungume shi ta yadda za su ribanci rayuwarsu. Sha’iri Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a wak’arsa ta zaman lafiya, ya yi bayanin amfanonin zaman lafiya a cikin al’umma a baiti na 61 da na 62 da na 63, yana cewa:
Baiti na 61 Ku bi ni da kyau in lisafo
Fa’ida ga zama bisa lalama
Baiti na 62 Yana bunk’asar da ‘ya’yanta
Al’amurranta su kankama
Baiti na 63 Sana’o’i su yawaita don arzikinmu
Ya zan ya dauwama
Idan aka yi nazarin wad’annan baituka za a ga suna nuni da cewa, idan aka samu zaman lafiya a k’asa, komai zai ha’baka a samu ci gaba, kama daga tattalin arziki da abubuwan more rayuwa da sauran al’amurra.
Shi ma Dakta Aliyu Tilde a wak’arsa ta “zaman lafiya” ya fito da amfanin zaman lafiya a matsayin arzikin da babu kamarsa a fad’in duniya a baiti na 32 da baiti na 33, yana cewa:
Baiti na 32 Musulmi, Kirista Ta’ala Karimu
Had’a mu zumuncin zaman lafiya
Baiti na 33 Dad’e mu fahimta ta juna mu gane
Cikin arziki ba kamar zaman lafiya
Auwalu Anwar a wak’arsa ta “zaman lafiya” a baiti na 4 da baiti na 8 da ke cikin littafin Gadar Zare, shi ma yana bayyana cewa, dukkan wani ci gaban k’asashen duniya da za a iya samu ya ta’allak’a ne ga zaman lafiya. Ga abin da sha’irin ke cewa:
Baiti na 4 Batun ci gaban duk k’asashe hak’ik’a
Yana nan ga samun zaman lafiya
Baiti na 8 Ku gane batun tattalin arzikinmu
Gudan ginshik’insa zaman lafiya
https://www.amsoshi.com/2017/11/06/lokacin-abu-yi-shi/
Nad’ewa
Babu shakka, zaman lafiya wani al’amari ne da ke da matuk’ar muhimmanci da amfani a tarihin rayuwar d’an Adam. Babu wani mutum d’aya mai arziki ko moro, basarake ko talaka ko mai mulki da zai sami ingantaccen rayuwa mai d’orewa da sakewa ba tare da zaman lafiya ba. Babu wata al’umma da za ta sami d’aukaka ko bunk’asa da ci gaban tattalin arziki da siyasa da zamantakewa da walwala face tana gudanar da rayuwarta cikin k’oshin zaman lafiya. Saboda haka ne za a iske duk wata al’umma da ta sami ci gaban rayuwa, hak’ik’a tana bisa turba ta zaman lafiya. Haka ma, duk wata al’umma ko k’abila ko k’asa da rikice-rikice da yak’e-yak’e da tashin-tashina suka mamaye ta, za a tarar al’amurranta sun ta’bar’bare ko ma sun durk’ushe baki d’aya.
MANAZARTA
Bunza, A.M. (2015) “Labarin Zuciya a Tambayi Fuska: Sak’on Dariya ga Sasanta Tsaro a
Farfajiyar Karatun Hausa”. Takardar da aka gabatar a Makarantar Harsuna, Sashen
Hausa na Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie, Argungu.
Bunza, A.M. (2015) “Zama Lafiya Ya Fi Zama ‘Dan Sarki: Shirin Tunkarar Za’ben 2015
2015 a Nijeriya” Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani kan kyautata zama
lafiya a za’ben da za a gudanar a shekarar 2015 wanda k’ungiyar Orphans and Huffaz
Educational Foudation Birnin Kebbi ya shirya.
Bunza, A.M. (2015) “Zaman Lafiya da Tsaro a Daular Musulunci ta Sakkwato: Abin Koyi ga
Shugabannin Zamaninmu”. Takardar da aka gabatar a taron yini d’aya da Centre for Intellectual Services on Sokoto Caliphate ta shirya na fad’akarwa a kan muhimmancin tsaro da zaman lafiya.
Ezirim, G.E. (2009) “The Role of Civil Society in Conflict Management” in Peace Studies
and Conflict Resolution in Nigeria: A Reader, Edited by Ikejiani-Clark M. Spectrum
Books Limited, Ibadan.
Francis, D.J. (2006) “Peace and Conflict Studies: An African Overview of Basic Concepts” in
Introduction to Peace and Conflict Studies in West Africa, Edited by Shedrack Gaya
Best Published by Spectrum Books Limited, Ibadan.
Sani, S. (2007) The Killing Fields: Religious Violence in Northern Nigeria. Ibadan: Spectrum
Books limited, Spectrum House.
[i] Alhaji Abubakar Ladan 1975:ix, Wak’ar Had’a kan Al’ummar Afirka. Ibadan: University Press Limited.
[ii] Aliyu Muhammad Bunza 2015. “Zaman Lafiya da Tsaro a Daular Musulunci ta Sakkwato: Abin Koyi ga Shugabannin Zamaninmu.” Takardar da aka gabatar a taron yini d’aya da Centre for Intellectual Services on Sokoto Caliphate ta shirya na fad’akarwa a kan muhimmancin tsaro da zaman lafiya a k’ark’ashin koyarwar shugabannin Daular Musulunci ta Sakkwato ranar Asabar 31 ga Janairu, 2015 da k’arfe goma na safe.
[iii] Oke Ibeanu 2006 “Conceptualising Peace” a cikin Introduction to peace and conflict studies in West Africa,
[iv] David J. Francis, “Peace and conflict studies: An African overview of basic concepts” a cikin Introduction to peace and conflict studies in West Africa, 2006.
[v] K’amusun Hausa Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano, shafi na 393.
[vi] Oxford Advanced Leaners’ Dictionary Seventh Edition, shafi na 1244.
1 Comments
[…] Yunk’urin Samar Da Zaman Lafiya Da Sasantawa: Bincike Kan Wak’ar Zaman Lafiya Ta Bashir Musa Lim… […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.