NA
NAZIRU MUHAMMAD ALKALI
BABI NA BIYU: JUMLA DA IRE-IRENTA A HARSHEN HAUSA
2.0 SHIMFI’DA
Wannan babin na biyu shi ne babin da yake k’unshe da jumlar Hausa tare da ire-irenta. Saboda haka shi ne, babin da za a kalli yadda ire-iren jumlolin Hausa suke. Kafin nan za a kawo ma'anar jumlar ta hanyar ra'ayoyin masana.
MA'ANAR JUMLA
Jumla kamar yadda masana suka bayyana ta ita ce, zance mafi tsari da cikakkiyar ma'ana, wadda ta k’unshi jerin kalmomi daban-daban bisa k’a'idar harshe. Kowace jumla tana k’unshe da muhimman ‘bangarori guda biyu, wato yankin suna, da yankin bayani. Don tabbatar da gaskiya ko me ake nufi da jumla an dubi wasu k’amusoshi Ingilishi. A cikin wani k’amus an bayyana jumla da cewa:
Runnie (1975). “Jumla rukunin kalmomi ne, wanda yake k’unshe da yankin aikatau da kuma suna aikau wanda ke bayyana wani bayani ko tambaya ko maganar motsin rai ko umurni. Za ta iya zama sark’ak’k’e da ganga dogarau ko hard’ad’d’e wanda yake da suna aikau fiye da d’aya ko kuma yankin aikatau d’ai-d’ai”.
Shi kuwa Rundell (1982), cewa ya yi: “jumla ta k’unshi wasu taron kalmomi wad’anda suka had’u, suka bayar da cikakken bayani”.
Robinson, (1978) Ya bayyana jumla da cewa: “Jumla wani babban ‘bangaren nahawu ne, wanda ya k’unshi yankuna da ganguna, wad’anda za a iya amfani da su don bayyana wani bayani ko tambaya ko kuma umurni”.
A nan ma'anonin da masana suka bayar ya nuna cewa, kalmomi su ne gimshik’an da ake harhad’awa a samu cikakkiyar jumla mai ma'ana. Tun da yake kalmomi ne ke had’uwa su gina jumla zai yi kyau a ba da tak’aitaccen bayani dangane da ire-iren jumlolin Hausa, ta hanyar lura da yanayin zubin kalmomin cikinsu.
IRE-IREN JUMLOLIN HAUSA
- Sassauk’ar Jumla
- Jumlar Tambaya
- Jumlar Umurni
- Jumlar Korewa
Yanzu za a d’auki kowace jumla domin a nuna yadda tsarinta yake:
2.2.1 SASSAUK’AR JUMLA
Sassauk’ar Jumla ta k’unshi yankin suna da kuma yankin abin da aka fad’i a game da suna. Wannan batu ana iya tak’aita shi da:
J Suna aikau + Abin da aka fad’i a game da suna. Wannan yanki na abin da aka fad’i a game da suna ya k’unshi kalmar aikatau da suna kar’bau (Aikatau + Suna kar’bau). Wannan tsarin shi zai ba da fasalin nan na S.A.K. a matsayin tsarin gudanar da sassan sassauk’ar jumla. Irin wannan gundarin tsarin na S.A.K. shi ne ake samu a harshen Ingilishi da wasu harsunan masu dimbin yawa. Masana da yawa sun kawo wannan tsarin na S.A.K. kuma sun yi bayaninsa. Akwai kuma wasu ayyukan wad’anda a kan tsarin S.A.K. na Hausa suke. Misalin Sassauk’ar jumlar Hausa shi ne:
(a1) Bala ci abinci
Sn aikau Aik Sn k’b
(b1) Musa sha ruwa
Sn aikau Aik Sn k’b
(c1) Musa kama Zaki
Sn aikau Aik Sn k’b
(d1) Ali kashe Kare
Sn aikau Aik Sn k’b
(a2) Bala ya a ci abinci
Sn aik maf lokt Aik Sn k’b
S A K
(b2) Musa ya a sha ruwa
Sn aik maf lokt Aik Sn k’b
S A K
(c2) Musa ya a kaama Zaki
Sn aik maf lokt Aik Sn k’b
S A K
(d2) Ali ya a kashe Kare
Sn aik maf lokt Aik Sn k’b
S A K
Abin lura a nan shi ne, a misalai na (a1) zuwa (d1) jumlolin suna d’auke ne da tsarin gundarin kalmomin S.A.K. ba tare da an tsarma kalmar mafayyaciya ba, tare da manunin lokaci da tak’I ba. Amma a misalai na (a2) zuwa (d2) an tsarma kalmomin na mafayyaciya da lokatak’, domin cika k’a’idar da jumlar Hausa ta k’unsa.
JUMLAR TAMBAYA
Jumlar tambaya ita ce jumlar da ake gina wa don a yi tambaya. Saboda haka Hausa tana da tsarin da take bi wajen ginin jumlar tambaya. Hanyar da Hausa take bi wajen ginin jumlar tambaya ita ce, dole ne 'kalmar tambaya', ta zo a farkon jumla. A Hausa ana da kalmomin tambaya kamar haka: Ina? waa? yaushe? k’ak’aa? yayaa? mee? Ga misalin su a cikin jumla:
a- Ina Audu ya a tafi ?
klm tmb almtmb
b- Waa zai sha ruwa?
klm tmb almtmb
c- Yaushe za a dawo hutu?
klm tmb almtmb
d- k’ak’aa za a yi da ‘barawon?
klm tmb almtmb
e- Yayaa Audu ya a fad’i jarabawaa?
klm tmb almtmb
f- Mee Ali ya a sayaa?
klm tmb almtmb
g- waa ya zo d’azu ?
klm tmb almtmb
Kalmomin da aka ja wa layi su ne suke nuna cewa wad’annan jumlolin na tambaya ne, kuma su suka bambanta jumlar tamabaya da sauran jumlolin harshen Hausa.
JUMLAR UMARNI
Jumlar umarni jumla ce wadda take d’auke da kalma d’aya tak, kuma cikakkiyar jumla ce. Haka kuma jumlar umarni a Hausa tana d’auke da wani tsari na musamman, inda jumlar takan zo da kalma d’aya rak tare da alamar motsin rai, a matsayin jumla cikakkiya, mai ma'ana. Kuma kalmar da take zuwa da ita, ita ce kalmar aikatau. Ga yadda abin yake:
- Tashi!
- Rubuta!
- Karanta!
Ga yadda ya kamata jumlar ta kasance, amma saboda wasu dokokin nahawu sai suka sa aka ajiye sauran kalmomin.
Misali
Kai/ke ka tashi!
Kai/ke rubuta!
Kai/ke karanta!
JUMLAR KOREWA
Jumlar Hausa ta korewa tana d’auke da wasu kalmomi na musamman da harshen Hausa ya aminta da su domin su zama sharad’i, kafin a gina jumlar korewa ta amsu. Sannan da wad’annan kalmomin ne za a iya nuna irin korewar zance da ake samu a cikin jumla. Kalmomin ana amfani da su ne, wajen nuna korewar zance a cikin jumla ta hanyar bin wasu k’a'idoji da aka shimfid’a. Ta amfani da su ne, za a iya fahimtar korewar da aka samu a cikin jumla. Kalmomin korewar su ne:
- Bá (báá ------- bà)
- Bà (bà --------- bá)
- Bá (báá………….)
- Bâ (bâ………….)
- Bà (báábù ----)
- Báí (báí----)
- Káádà/kár ----)
Ga misalin kad’an daga cikin jumlar korewa:
Ali ya a sayaa
- Bá (báá ------- bà) Báá Ali ya sayaa bà.
Rabi ta a tafi makaranta
- Bà (bà --------- bá) Rabi bà ta a tafi makaranta bá.
akwai kud’i a banki
- Bá (báá………….) Báá kud’i a banki
Agwagwa ta tashi sama sosai
- Bâ (bâ………….) Agwagwa bâ ta tashi sama
Akwai ruwa a randa
- Bá (báábú ----) Bààbú ruwa a
- Káádà/kár ----) Káádà/kár ka a tafi/kar kaa tafi.
NA’DEWA
Wannan babin na biyu ya bayyana ma'anar jumlar Hausa a bisa ra’ayoyin masana, tare da bayyana ire-iren jumlar Hausa da ake da su tare kuma da ba da wasu misalai daga cikin kowace jumla. Misali, a sassauk’ar jumla an nuna cewa, jumla ce da ta k’unshi yankin suna, da kuma yankin abin da aka fad’i game da suna. Haka kuma ita ce jumlar da ke bisa tsarin S.A.K. Jumlar tambaya kuma ita ce, jumlar da ake gina wa don yin tambaya. Jumlar umarni jumla ce da ta k’unshi kalma d’aya rak a matsayin cikakkiyar jumla. Jumlar korewa jumla ce da ke d’auke da wasu kalmomi na musamman da harshen Hausa ya amince da su, domin su zama sharad’i waje nuna irin korewar da aka sanu a cikin sassauk’ar jumla. Sannan su ne a matsayin dokokin da aka shimfid’a wajen samar da ita kafin ta zama jumlar korewa.
https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
1 Comments
[…] Bambanci Da Kamanci Tsakanin Karin Harshen Sakkwatanci Da Katsinanci (3) […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.