Hanyoyin Nazarin Jumla A Nahawun Hausa (2)

KUNDIN NEMAN DIGIRIN FARKO (B.A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA TSANGAYAR FASAHA DA ILIMIN ADDININ MUSULUNCIN JAMI’AR USMANU ƊANFODIYO, SAKKWATO


NA

IBRAHIM HAMISU YUSUF

 

                                         BABI NA ƊAYA

                                            GABATARWA

1.0 Shimfiɗa


Nahawu harshen Hausa fage ne da manazarta suka gudanar da zuzzurfan bincike a kansa. Duk da cewa harshen Hausa ya na da wadatattun kalmomi da kowane harshen duniya yake da su. Nahawun harshen Hausa ya na da rassan nazari guda biyar manya Akwai fanni nazarin gundarin sauti da na nazarin tsarin sauti, har-ila-yau akwai fannoni ginin kalma da na ginin jumla da kuma na ilimin ma’ana. Masana da mazarta ba fannin da ba su gudanar da nazari a kansa ba, sai dai idan aka yi la’akari da karin maganar harshen Hausa da ake cewa “ilimi gulbi ne mai zurfi wanda ba a kure shi”. Kenan duk da irin gudummawar da aka bayar, har yanzu akwai sauran abin dubawa. Sanin haka shi ya sa nazarin ya fara da bitar ayyukan da suka gabata a babi na ɗaya, sannan a ciki an bayyana dalilin da ya sa ake son gudanar  da wannan nazarin .

Bayan bitar ayyukan da masana da manazarta, suka gudanar, da shi an ƙebe wa nazarin hujjar gudanuwa. Don haka aka ƙebe wa nazarin farfajiya a fannin ilimin ginin jumla. Aikin zai sanmi nasarar gudunuwa ne ta bin hanyoyin gudanar da bincike kamar yadda aka bayyana a nan gaba. Da irin muhimmancin da binciken yake da shi in an kammala, naɗewa ita ce marfin babin.

A babi na biyu mai suna “Azuzzuwan kalmomi a taskar masana nahawu”. Sauran fannonin nazari na ilimi shi ne ake ganin ya dace a gudunar da bincike a fannin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Da fatar Allah ya sa a sami nasarar gudanar da binciken bisa ƙa’ida domin amfanin masu bincike da manazarta harshen Hausa.

 
1.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


Masana da dama sun gudanar da ayyuka a kan nahawun Hausa, tun daga Turawan mulkin mallaka da suka yi aikin rarraba ɓangarorin nazarin nahawun Hausa, bisa tsarin harshe Ingilishi har zuwa ga masana ‘yan gida da suka gaji Turawan, duk abun guda ne. Ire-iren waɗannan ayyukan masanan zamani musamman waɗanda suka gudunar da aikinsu kan yankin suna da ajin sifa da kuma ajin kalmomi masu aikin irin na nahawun harshen Hausa. Inda wannan aikin zai baje hajarsa a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Da farko kafin a shiga ka’in-da-na’in cikin aikin za a yi waiwayen  ayyukan da aka gudanar waɗanda suka shafi nazarin ginin jumla a nahawun Hausa.

Galadanci, 1976. Ya rubuta littafin mai suna “An introduction to Hausa Grammar”. A cikin wannan littafin an yi zancen kan nahawun ginin jumla, inda aka nazarci wasu mahimman abubuwa ɗangane da ginin jumlar Hausa. Amma a cikin wannan nazarin za a  fito da hanyoyin nazarin jumla ne a nahawun Hausa, ba tare da keɓe wasu ɓangarori ba wannan nazarin za a fito da Hanyoyin nazarin jumla  ne a nahawun Hausa.

Galadanci da Wasu, 1980. Sun wallafa wani littafi mai suna “Hausa a Textbook of Methodology.” Littafin ya yi bayanin jumloli masu ƙunshe da fi’ili a cikin nahawun Hausa. Bayaninsu ya taƙaita ne kan jumla mai ɗauke da fi’ili da lokaci a cikinsa, a nan bayaninsu ya taƙaita. Wannan binciken zai zayyano ire-iren Hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, kamar  yadda suke a sauran harsunan duniya.

Skinner da Wasu, 1976. Sun wallafa littafi mai suna “Hausa a sauƙaƙe: jagoran nahawun Hausa”. A cikin wannan littafin an kawo bayani akan azuzuwan kalmomin Hausa ƙa’idojin rubutun Hausa. Sai dai wannan aikin zai bi sawun hanyoyin nazarin jumla ne a nahawaun Hausa.

Calvin, Y.G. 1985.  Ya rubuta wanni littafinsa mai suna “Nazarin Hausa a ƙananan makarantun sakandare na ɗaya’’. A nan ya yi bayani kan Sasauƙar jumlar Hausa sai dai ya tsaya ne kan cike gurabe, ba tare da an gudanar da gamsashen bayani game da jumlar Hausa ba. Amma wannan aikin zai yi tsokaci ne a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Ahmadu, B.Z. 1981. Ya rubuta littafin mai suna “Nahawun Hausa”. A cikin wannan littafin ya takaita bayanin wasu matakan nazarin jumla irinsu; suna, aikatau, lokaci, amsa-kama, tare da misalan jumloli nahawun Hausa a nan aikin ya tsaya. Bai ci karo ba da wannan nazarin ba, hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Umar, 1985. Ya gudanar da aikinsa na kundinn digiri na farko a sashenn harsunan Nijeriya, jamia’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, kan “Bishiyar li’irabi a cikin nahawunn Hausa”. Cike suke da matsaloli dangane da rabo ko bayanan wasu a zuzuwan kalmomin harshen Hausa. Ya dubi ƙwayoyin ta fuskar ajin nasaba da mallaka, amma a daidailiyar Hausa. Don haka ba zai ci karo da wannan aikin ba, saboda shi wannan aikin zai yi tsokaci da bibiyar hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Lawal, 1985. ya gudanar da nasa bincike a kan ajin Sifa, mai taken “Gurbin Sifa a cikin jumlolin Hausa” a sashen harsunan Nijeriya na jami’ar Usmanu Danfodiyo sasakkwato. Inda ya dubi yanayin zuwan ajin sifa tare da suna. Sannan ya dubi yadda kwayoyin ma’anar –n da -r ta fuskar zaman takewar sifa da suna, tsarin daidaiciyyar Hausa. Sai dai wannan aikin zai yi bayani ne game da hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, tare da waiwayar azuzuwan kalmomin nahawun Hausa.

Umar, S. 2012. Ya gudanar da aikinsa na kundinn digiri na biyu a sashenn harsunan Nijeriya, jami’ar Usmanu Danfodiyo sakkwato, kan “Matsayin ’yan Rakiya a Yankin Suna: Tsokaci a kan ƙirgau”. Inda aikinsa ya dubi wasu sassa na nahawu. Don haka ba zai ci karo da wannan aikin ba, saboda shi wannan aikin zai yi bayanin hanyoyin nazarin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Amfani, A.H. 1995. Ya yi zuzzufar nazari a kan “giredin aikatau na Hausa” domin ya sama masa matsuguni sosai a rabe-raben kalmomin Hausa, shi giredi kwayar ma’ana ce mai aiki irin na nahawu (functional categoriy) a cikin jumla. A nan ya yi bayani aikatau Hausa da aka nazarce su bisa tsarin nazarin na ci gaba zamani. Nazarin zai tsaya ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Amfani, A.H. 1996. Ya gudanar da nazari a kan ”Aspect of Agreement Relations in Hausa Clause Structure”. A nan ya yi bayanin Mafayyaciya wato (agreement element (AGR) ) da lokataƙ (tense aspect) da ajin sifa kuma ya bayyani gamsashe bisa tsarin nazari na  zamani. Amma wannan aikin zai yi bayani daki-daki a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Amfani, 2004. Ya gabatar da mukala mai suna “waiwaye adon tafiya”. A nan ya yi bayanin wasu ƙwayoyin ma’anar tare da kawo rabe-rabensu a fannin nahawun Hausa, bisa tsarin nazari. Wannan nazarin zai tsaya ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Rabi’u, da wasu, 1988. Sun gudanar da wani aiki a kan nahawun Hausa, cikin wanin littafi da suka buga mai sunan “sabuwar hanyar nazarin Hausa: ɗon kananan makarantun sakadare”. A nan ma sun yi bayani kan azuzuwan kalmomin da tsarin jumlar Hausa, ba tare da an gudanar da bayani kan zamantakewan azuzuwan kalmomi a cikin jumlar ba. Amma wannan aikin zai yi tsokaci ne daki-daki a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Sani, 1981. ya rubuta littafi mai suna “Nahawun Hausa”. A ciki ya bayyana ƙwayoyin ma’ana ta fuskar ajin sifa da adadi a jinsi. Shi ma ya yi aikin nasa ne ta la’akarin da matsayinsu a daidaitaciyyar Hausa. Wannan nazarin ya tsaya ne a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Safiyanu, B. K. 2013. Ya gudanar da aikinsa na kundinn digiri na biyu a sashenn harsunan Afirika da al’adu Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, kan “Kwatancin Wasun Bayanau (Rukunan Nahawu Dangin

Suna) A Hausa Da Fulfulde” binciken a nan ya tsaya, kuma bai cikaro da wannan nazarin ba, na hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

 

Bagari, D.M. 1987. A cikin littafin sa mai suna “Hausa Subordinate, Adverbial Clauses, Syntax and Semantics” ya kawo mahimman sassan nazarin jumlar Hausa, irinsu; aikatau (Adverb) lokaci (Tense Aspect) yankin Suna wato (Noun Phrase). Ya yi bayani gamsasshe game da wasu sassan jumlar Hausa. Wannan binciken ya tsaya ne a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Jinju, 1988. A cikin littafin sa mai suna “Rayayen Nahawun Hausa”. Ya yi Magana a kan azuzuwan kalmomi nahawun Hausa tare da nau’o’in jumlar harshen Hausa. Amma bai fito da hanyoyin nazarin jumla ba, wannan nazarin zai yi bayanin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa ta yadda mai nazari zai fahimce su daki-daki, domin kwalliya ta bi ya kudin sabulu.

Hassan, 1999. Ya yi magana ne kan suna a cikin littafinsa mai suna “Hausa Language”. Wanda aikin nasa ya danaganci tsarin yakin suna a cikin jumlolin Hausa. An buga aikin da ingantattun bayanai. Wannan aikin zai tsaya ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Sani, M.Z.1999. Ya kawo a cikin littafinsa mai suna “Tsarin sauti da na nahawun Hausa”. Inda ya kawo kasha-kashen azuzuwan kalmomi tare da bayani kan suna. Binciken zai tsaya ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

‘Yar’aduwa, T.M. 2007. Ya wallafa littafi mai suna “harshe da adabin Hausa a kammale don Manyan makarantun sakandare”. A cikin littafin ya kawo suna da sifa da bayanau da nasaba da adadi da jinsi. Ya bayana yadda suke daki-daki tare da misalansu a cikin jumla. Wannan nazarin ya tsaya ne a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Ibrahim, da Wasu, 1989. Ya bayyana wasu kalmomin da jumloli da sassan jumloli da karin sauti da kuma irinsu, Suna da wakilin suna da aikatau da sifa da mahadi da kuma harafi a cikin littafin sa mai taken “Darussan Hausa na ɗaya”. Waɗannan duk bayanan da suka gabata cikin wannan nazarin, mai ɗauke da hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa zai tsaya.
 

1.2 DALILIN BINCIKE


Komai na da dalili idan har za a gudanar da shi, don haka wannan nazarin ya na da nasa dalili. Wasu daga cikin dalilan sun hada. Cika ƙa’idojin da jamia’a ta shimfiɗa kan duk wani ɗalibi da ya zo shekarar ƙarshe ta karatu don ya ba da ta shi guɗunmawa a fagen da ya ke karatu saboda ya taimakawa ɗalibai masu zuwa. Dalili na shi ne, na kuma ciyar da harshen Hausa gaba ta fuskar nazari, don haka wannan aikin ake sa rai zai taimka sosai wajen bunƙasa harshen Hausa ta fannin samin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Wato nazariin zai taimakawa ɗalibai masu sha’awar yin bincike a fannin ginin jumla sanin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Wani dalilin daya haifar da wanzuwar wannan bincike da yawa ɗalibai ke bukatar sanin wani abu dangane da hanyoyin nazarin jumla a harshen Hausa, amma abin ya shige musu duhu wannan nazarin, a na burin nazarin shi ne ganin  cewa, ba  duk ɗalibai suka cika son gudanar da bincike a fannin ilimin ginin jumla ba. Shi ya sa aka zabi wannan fannin don ba da guɗunmawar ilimin.

Dalili na gaba kuwa shi ne, ganin cewa ya dace da a gudanar da wannan nazarin don samun ƙarin abin dubawa a fagen nazarin ginin jumla yin haka zai ba ‘yan’uwan ɗalibai masu sha’awar yin nazarin nahawun Hausa, sanin yadda tsarin nazarin jumla yake a harshen Hausa waɗannan dalilan su suka haifar da guɗunmawar wannan bincikem.

 
1.3 HUJJAR Ci GABA DA BINCIKE


Bisa la’akari da zuzzzurfan nazari da bincike da ka yi a kan bitar ayyukan da suka gabata a kaso na 1.1 ba a samin wanda ya yi nazari a kan  hanyoyin nazarin jumla a nahawun harshen Hausa ba, sai dai wasu sun taba ne kan wasu rassa kuma zai ba da guɗunmmawa wajen nazarin jumlolin a harshen Hausa kuma ya zame masu hasken da zai haska masu hanyar samin yadda a ke nazarin jumla ne ko gefe wannan shi ne ya ba da damar ci gaba da yin aikin ko bincike da a ke yin a hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Binciken bai ci karo da wani aiki ba da ya gabata wannan shi ya sa a ka ci gaba da wannan binciken don a samin abin dubawa ga ɗalibai ‘yan’uwan masu neman ilimi.

 
1.4 MUHIMMANCIN BINCIKE


Bincike kowane iri ne ya na da muhimmanci ga rayuwar al’umma, da yake zai iya ilmantarwa akan wani abu da ba a sani ba, ko ya fito da muhimmancin wani abu don mutane su yi koyi don su amfana, ko kuma ya fito da illar wani abu don mutane su gaju masa. Saboda haka shi ma wannan bincike ya na da nasa muhimmancin.

Wannan binciken ya shafi hanyoyin nazarin jumla  a nahawun Hausa. Saboda haka zai zama a matsayin cike gurbi a kan abinda aka bari a baya wajen bayyana jerin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Wannan nazarin zai taimakawa ɗalibai ta fuskar samun dammar sanin irin yadda ake gudunarar da nazari jumlolin harshen Hausa ta yadda zai zamo abin sauƙin karatu kuma ya taimakawa wajen masu nazari,  musamman ma ɗalibai ‘yan’uwana.

Kamala wannan bincike zai fito da  tsarin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Kundin zai taimakawa sauran ɗalibai su ma, su mayar da hankali wurin bincike a kan irin waɗannan nazace-nazarcen domin su sami abin karantawa musamman irin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, da suke taimkawa wajen bayar da ingantacciyar hanya da masu son nazarin jumlolin harshen Hausa.

 
1.5 FARFAJIYAR BINCIKE


Wannan binciken ya shafi nahawun harshen Hausa. Nahawun Hausa ya karkasu zuwa gida biyar,  kamar yadda masana fannin suka  nuna. Watau akwai abin daya shafi ilimin gundarin sauti (Phonetics) da ilimin tsarin furuci (Phonology) da ilimin ginin kalma (morphology) da ilimin ginin jumla (syntax) da kuma ilimin ma’ana (semantics). A ya yin da shi wannan bincinken za a gudanar da shi a fannin ilimin ginin jumla, inda za a yi tsokaci kan ɗaya daga cikin hanyoyin nazarin jumla. Don haka faɗin wannan aikin zai tsaya kan hanyoyin nazarin nahawun Hausa.

1.6 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE


Wananan bincike za a gudanar da shi, ɓangarorin da dama. Hanya ta farko ita ce duba ayyukkan da masana suka yi ta fuskar rubutu da wallafa mujallu da littafai da kuma kundaye da maƙalu a fagen ilimi. Hanya ta biyu ita ce binciken cibiyoyin nazarin harsunan Nijeriya da daƙunan karatu da shi ga yanar gizo, (internet), domin fito da ayyukan da za su taimaka wajen kammalar  wannan nazarin.

Wata hanya kuma ita ce neman shawarwarin daga manyan malaman nahawun harshen Hausa, musamman waɗanda suke ƙware a fagen ilimin ginin jumlar Hausa, da nahawun Hausa gaba ɗaya. Hanya ta ƙarshe ita ce, ziyartar  ɗaƙunan karatu na manyan makarantun da jami’o’i domin samin nasarar kammalawar nazarin.

 
1.7 Naɗewa


A ƙarshe wannan babi, babi na dake ɗauke da shimfiɗa a farkonsa, sai kuma a ka yi bayani a kan abubwan da suka shafi wannan nazarin, kamar dalilan yin bincike da hujjar ci gaba da bincike da mahimmancin bincike tare da matakan da aka bi domin  gudanar da binciken. Har-wa-yau an yi bitar ayyukkan da suka gabata, akan wani fage na ilimin nahawun harshe Hausa, domin samun ƙarin bayani game da aikin. Farfajiya bincike da hanyoyin gudanar da bincike tare da duba iyakar binciken su suka biyo bayan ƙunshiyar babin. Daga ƙarshe sai aka rufe babin da jawabin kammalawa, watau naɗewa a taƙaice.

Post a Comment

0 Comments