NA
ALIYU MUSTAPHA
BABI NA BIYU
TSAKANIN HARSHE DA RUKUNIN JAMA’A
2.0 Shimfid’a
Rukunin jama’a ya k’unshi d’aid’aikun mutane wad’anda suka yi tarayya ta fuskar zamantakewa ko tattalin arziki. A kowace al’umma ta duniya, d’aid’aikun mutane kan bambanta da juna ta hanayr magana. Wad’ansu daga cikin wad’annan bambance-bambance na d’abi’a ne kawai, amma kuma ana danganta wasu da kasancewa cikin wani rukuni na mutane. Ana danganta irin wad’anna da bambancin jinsi da kuma yanayin ci gaban mata na magana daban da na maza, kamar yadda yara ke magana daban da manya. Wad’annan bambance-bambance a harshe ta fuskoki biyu, a bu ne da halitta ta tanada. A wad’ansu al’ummu ana danganta wad’annan rukunai da alfarma ko arziki ko kuma mulki. Misali, ma’aikatan banki ba sa magana kamar yadda kwandastan motocin bas-bas ke yi. Haka shi ma mai ilimi ba ya magana kamar yadda wanda ba shi da ilmi ke magana (Yakasai, 2012).
Wannan babi zai yi bayani ne a kan tsarin rukunin jama’a, tare da bayanin nau’o’in Hausa, inda daga k’arshe za a fito da bayanin yadda Hausa take a kafafen yad’a labarai.
2.1 Tsarin Rukunin Jama’a
Ana samun rukunan jama’a a birni ko maraya. A birni ake samun manyan makarantu kamar jami’o’I da kwalejojin ilmi da sauransu. Haka kuma a nan ne ake samun filin jirgin sama, babbar tashar jirgin k’asa, wani lokaci ma har da tshar jirgin ruwa. Babbar kasuwa, manyan bankuna, manyan wuraren kwanan bak’i, gidajen sinima, gidanjen talabijin da na rediyo duk abubuwa ne da ake samu a birni. A birni ake samun gidan sarki da na gamna. Haka kuma nan ne babban alk’ali ke zaune, tare a sauran shugabanni na al’umma duk suna zaune a birni.
Su ma manyan masana’antu da kuma manyan ma’aikatun gwamnati a birni ake samunsu. Saboda haka mutane kan yo tururuwa zuwa birni domin neman aiki. Ta fuskar walwalar harshe, wannan ya nuna cewa ana samun cud’anya cikin mu’amala a birni fiye da karkara saboda yawan jama’a (Yakasai, 2012).
Gaskiyar magana ita ce, akwai mutane da yawa a birni, wato a birni ake samun mutane masu arziki, talakawa, k’ananan ma’aikata, matsakaita da kuma manya na zaune a birni. Saboda haka, duk inda aka samu al’umma to dole a samu bambancin ayyuka. Akwai masu mulki ko iko masu dukiya ko attajirai, masu ilimi da kuma sana’o’I iri-iri. Wannan dalili ne yake tabbatar da samun tafi da rayuwa iri daban-daban. A ra’ayin Trudgil (1974), bambancin tafi da rayuwa na bambanta al’umma fiye da bambancin shiyya.
Rukunin jama’a kamar k’ungiyoyi ne na al’umma. Dalilan samuwar k’ungiyoyi suna da yawa, amma kusan mafi yawa na son kare mambobinsu. Haka kuma suna k’ok’arin akre mutuncinsu daga k’untatawa ko muzantawa daga wasu ko daga hukuma. Don haka cigaban ‘yan k’ungiya muhimmin abu ne. tarihi ya nuna cewa wayewa na samuwa a dalilin samun ilimi. Wannan kuma shi ne yake haifar da kafa k’ungiyoyi domin neman ‘yanci ko hak’k’i. Yanayin rayuwa a wannan lokaci yana nuna cewa rukunin al’umma na samuwa a dalilin bambancin ilimi, muk’ami ko mallakar duniya (Fussel, 1983). Masu ilimi su ne suke kafa k’ungiya domin cimma wata manufa wadda suka yi imani da ita. Amma a yanzu har ma maras ilmi kan kafa k’ungiyoyi domin wad’annan daliliai da muka ambata. Wannan na samuwa ne saboda zaman birni ko maraya.
Don haka akwai k’ungiyoyi iri-iri, kamar na ‘yan kabu-kabu da makiyaya da manoma da masu shayi da guragu da makafi da sauransu. Ire-iren wad’annan na da k’arancin daraja ko martaba domin ba a cika samun masu ilmi ciki ba. masu ilmi ne suke kafawa da kuma gudanar da k’ungiyoyi musamman na k’wadago da ‘yan jarida da malaman jama’a da lauyoyi da likitoci da sauransu, domin haka sun fi samun daraja da martaba daga hukumomi.
Haka kuma ‘yan kasuwa da ‘yan makaranta, da malaman addini kamar na Musulunci da Kiristanci duk sukan kafa k’ungiya. K’ungiyoyin siyasa ne kawai suke fitowa domin neman son shugabancin k’asa. Duk ire-iren wad’annan k’ungiyoyi na da manufofi iri daban-daban. Saboda haka k’ungiyoyi taro ne na jama’a amma masu manufa. Irin wad’annan k’ungiyoyi sun bambanta da rukuninjama’a domin na farko kan yi taro su kira mambobinsu su tattauna matsalolinsu. Amma shi rukunin jama’a ya ta’allak’a kan halayyar d’aid’aikunsu, wato yana yin rayuwarsu ta yau da kullum. Hasali ma, ai wanann ya shafi dukkan rayuwa gaba d’aya. Ga misali, yanayin abinci, wurin zama, suturar sawa da lokacin aikatawa, motar hawa, ginin gida, magana, wasannin motsa jiki da sauransu. Haka kuma ya shafi sana’o’I yadda ake tafiya da sauransu.
Pugh (1996) ya amince cewa muk’ami ko iko a ko yaushe na da dangantaka da wani abu. Wato ba zai yiwu ba ga misali, ka iya cewa ga muk’ami kowa ya gan shi da ido. Ana ganinsa ne ta hanyar gudanar da wani abu da wani ko wasu sukan yi. Wannan shi ne mak’asudin smun rukunai cikin jama’a.
2.2 Nau’o’in Hausa
Harshen Hausa yana da fad’i da yalwa ta yadda har ya kai ga samar da kare-karensa ita ce ta kai ga haifar da nau’o’in Hausa daban-daban. A nan abinda ake nufi da nau’o’i Hausa daban-daban. A nan abin da ake nufi da nau’o’in Hausa shi en, irin yadda ake samun rukunonin jama’a a harshen Hausa. Amma kuma sai a iske kowanne rukuni yana da nasa nau’in kalmomin da yake amfani da su wajen tasa Hausar. Amma kuma sai a iske kowane rukuni yana da nasa nau’in kalmomin da yake amfani da su wajen tasa Hausar. Wannan shi ne ya sa ake jin irin kalmomin da ake furtawa a Hausar rukunin ‘yan tasha sun bambanta da kalmomin da ake amfani da su a Hausar rukunin malaman zaure. Haka kuma Hausar ‘yan kasuwa, kalmomin da za ka ji ana furtawa a cikinta, sun bambanta da kalmomin da za ka ji ana furtawa a rukunin Hausar fadar sarakuna. Domin kowane rukunin jama’a da nasa kalmomin fannu, da yake amfani da su a sadarwarsa ta yau da kullum (Yakasai, 2012)
Saboda haka, da zarar mutum ya ji ana magana da Hausa ko ya karanta Hausa ta kowace fuska, to kalmomin da aka yi amfani da su ne za su yi jagora a fahinci irin rukunin jama’ar da maganar ko rubutun ya shafa. Ga misali, da jin an ce: “Ranka ya dad’e” za ka ce wannan nau’in Hausar fadar sarakuna ce. Haka kuma, da zarar ka ji an ce: “muna arha, muna hana bashi” (ga araha ba bashi), kai tsaye za ka ce wannan nau’in Hausar ‘yan kasuwa ce.
To ashe kuwa idan haka ne, ana iya cea kowanne rukunin jama’a yana da nasa kalmomin fannu. Wad’anda suka ke’banta da shi kad’ai, a harshen Hausa. Kuma wani rukunin fannun su ne suke fayyacewa mai saurare ko mai karatu ruknin da magana yake ko wanda yake magana a kai.
A nan za a kawo wasu daga cikin rukunonin jama’a tare da yin nazarin irin Hausarsu, sannan a bayar da misalan kalmomin fannu da suka danganci kowanne fanni (Yakasai, 2012).
Hausar Kasuwanci
Sana’a hanya ce ta neman d’an abin dogaro da kai, kuma shi malam Bahaushe a al’adance ko kad’an bai amince da mutum ya zama cima-kwance ko d’an zaman kashe wando ba. rayuwar yau da kullum ta malam Bahaushe ita ta haifar a Hausar rukunin masu sana’a, wadda take cike da kalmominta irin na fannu. Haka kuma duk inda ka zagaya ba za ka ji ana aiwatar da su ba sai a Hasuar rukunin masu sana’a. ga wasu ‘yan kad’an daga cikin kalmomin kamar haka
Kalma | Ma’ana | |
1. | Saye | Ka bayar da kd’i ka kar’bi wani abu. |
2. | Sayarwa | Ka bayar da wani abu a ba ka kud’i. |
3. | Tayi | Ka fad’i abin da za ka biya abu ko a bar maka ko a hana maka ko kuma a nemi ka k’ara. |
4. | Albarka | Neman k’ari daga yadda mai saye ya saya |
5. | La’ada | Kud’i ne da mai sayen kaya yake bai wa dillali wanda yake sasantaw da kiyayewa tsakanin mai saye da mai sayarwa |
Yakasai, (2012).
https://www.amsoshi.com/2018/01/12/harshen-wasa-tsokaci-daga-shirin-labarin-wasanni-na-gidan-rediyon-bbc-2/
Hausar Sarakuna
Sarakuna su ne shuwagabannin jama’a. A idon Bahaushe su ne uwa su ne uba ga al’umma. Bugu da k’ari kuma, su ne wuk’a su ne nama a cikin ahrkokin jama’arsu a kan abin da ya shafi jagoranci.
Irin wannan matsayi da daraja da sarakuna suke da su a idon malam Bahaushe, shi ne ya harfar da Hausar sarakuna. Wato k’asaita, ko kuma lamuran tafiyar da fada. Ga misalin wasu daga cikin kalmomin:
Kalmomin Fada | Ma’ana | |
6. | Ranka ya dad’e | Girmamawa ga sarki (gaisuwa) |
7. | Mu muka ce | Magana ce ta k’asaita da sarki ke yi |
8. | Fadawa | Masu muk’ami a fadar sarki |
9. | Jakadiya | Mace ce mai sada huld’ar sarki da matansa |
10. | Hawan daba | Sarki ne ke hawan doki, tare da d’aruruwan jama’arsa zuwa d’an lokaci |
Yakasai, (2012)
Hausar Mawak’a
Mawak’a mutane ne da suke da matuk’ar muhimmanci a kowane harshe na duniya. Musmman idan aka yi la’akari da irin rawar da suke takawa wajen bunk’asa harshe, da kuma al’adun da suke k’unshe a cikin harshen. Wannan kuma shi ne, ya haifar da Hausar mawak’a wadda take k’unshe da kalmomin fannu masu gargad’i, daidaitattu, da ingantattu. Don haka Hausar mawak’a ta bambanta da Hausar kowane rukunin jama’a. a irin wanan Hausar ce za a iya jin ana amfani da kalmomi irin na kambawmawa da cicci’bawa da yabawa, da aibantawa, da kushewa da zuzzugawa da salontawa da dai sauranru. Ga misalan ‘yan wasu kalmomi daga Hausar kamar haka:
Kalmomin Wak’a | Ma’ana | |
1. | Gulbi- cicci’bawa | Mai yawan kyauta |
2. | Sadauki-kambamawa | Jarumin jarumai/ mai k’arfi |
3. | Ruwan fak’o - aibantawa | Marowaci |
4. | Bahagon zaki - zuzzugawa | Wanda ba a gitta ma, a sha da dad’i |
5. | Farin komo - kushewa | Maras amfani |
Hausar Malamai
Bahaushe yana kallon malamai ne a matsayin idanu ga al’ummarsa. Don haka ne ma akan ce: “Malamai magana annabawa.” Abin nufi a nan shi ne, yadda annabawa suka kasance idanun al’ummominsu, haka malamai suka kasance wurin mutanensu, kuma suke yin aikin shiryar da mutanensu. Wannan k’imar da matsayi da kuma mutunci da malam Bahaushe ya bai wa malamai, suna taka rawa sosai wajen samar da Hausar malamai.
Hausar malamai cike take da kalmomi irin na sakayawa, domin jin nauyi ko kunyar ambaton wasu kalmomi. Haka kuma Hausa ce da kalmomin aro suka cika ta, musmman daga harshen Larabci, sakamakon tasirin da addinin Musulunci ya yi a kan su malamai d’in. Har wa yau kuma, Hausa ce mai tsari da kuma kimtsi ainun, wadda yanayinta ya dace da yanayin ma’abotanta, wato malamai. Ga misalin kalmomin Hausar wannan rukuni:
Kalmomin Malamai | Ma’ana | |
1. | Toroso ko ga’idi | Kashi (tutu) |
2. | Dahuli ko jima’i | Saduwa da mace |
3. | Mahaifa | Iyaye |
4. | Mak’iri | Talaka |
5. | Muwafak’a | Dacewa da sa’a |
6. | Al’aura | Gindi, na maza ko mata/tsiraici |
7. | Nysabtawa | K’aryatawa |
8. | Alfasha | Batsa ko zina |
9. | Ladabtarwa | Azabtarwa/yin horo |
10. | Ma’barnaci | Mazinaci |
Yakasai (2012)
Hausar Samari Da ‘Yan Mata
Samari mutane ne da suke da matuk’ar muhimmanci a kowace al’umma. Har ma akan ce: “in al’umma ta gyaru samarinta ne, in kuma ta ‘baci su ne.” saboda haka lura da cewa, su ne suke da jini a jika, kuma su ne suke da kowane irin al’amari suka sa gaba (la’alla abin mai kyau ne ko marar kyau). Wata sananniyar d’abi’a da samari suka yi fice da ita, it ce hayak’in kai. Sannan kuma ga son nuna gadara, ga jayayya da kuma son nuna burgewa. Musamman a gaban ‘yan mata. Ana ma iya cewa, k’ok’arin nuna burgewa a gaban ‘yan mata shi ne ke d’ora asalin soayayyarsu da su.
Ta la’akari da irin wad’annan halaye da d’abi’u da aka bayyana ga samari, ana iya cewa, Hausarsu, Hausa ce da a ko yaushe takan sha kicibis da sabbin kalmomi. Ga misalin kalmomin Hausar samari:
Kalmomin Samari | Ma’ana | |
1. | Yaya dai? | Gaisuwa ce irin ta samari |
2. | Ji mana | Yadda samari ke neman bakin budurwa |
3. | Kai amma kin had’u | Wato kin burge/kin k’ayatar |
4. | Yaya wai? | Neman labari ne samai ke yi |
5. | Ba ka yi wallahi | Ba ka iya taka rawar da aka buk’ata ga lamari ke nan |
6. | Yawu ce | K’auyanci ne |
7. | Bula ce | K’arya ce |
8. | Tauraruwata | Masoyiyata |
9. | Kana haskawa | Wai kana burgewa |
10. | Mutumin | Abokin sharholiya kenan |
A d’aya ‘bangaren, Hausar ‘yan mata takwarorin samari a koyaushe ba za ka raba ta da kalmomi irin na soyayya ba. Da kuma kalmomin ya yi ko sara. Bugu da k’ari kuma, Hausar ‘yammata cakud’e take da kalmomi irin na nuna karsashi da shagwa’ba. Harwa yau, ta wani ‘bangare kuma, Hausar ‘yammata tana k’unshe da kalmomi da suka danganci arashi, da habaici da kuma zolaya. Ga dai wasu ‘yan misalai kad’an da za mu iya bayarwa da Hausar ‘yan mata kamar haka:
Kalmomin ‘Yan Mata | Ma’ana | |
1. | Rabin rayuwata | Saurayinta kenan masoyinta |
2. | In ba kai ba sai rijiya | Nuna shagwa’ba ga masoyi |
3. | Soyayya tsuntsuwa ce | In aka k’are da saurayi ake masa wannan habaicin |
4. | Haba mutumina | Nuna k’auna ne ga masoyi |
5. | Malam yi hak’uri | Cikin d’asa shi ake wannan zancen ga sabon had’uwa |
6. | Wai kai zalahoto | Zolaya ce ‘yan mata kan yi wa mai wahala inda ba a son sa |
Yakasai, (2012)
2.3 Hausa A Kafafen Yad’a Labarai
Harshen Hausa harshe ne mai kima da martaba da kwarjini da bunk’asa da d’aukaka a nan cikin gida da wajen k’asar Nijeriya. Harshen ya dad’e yana cin kasuwa ta fuskar ma’amala da cinikayya da yayatawa a wurare daban-daban. Daga cikin wuraren da ya mamaye har da kafofin yad’a labarai.
Kafofin yad’a labarai tun farkon kafuwarsu a k’asar nan da k’asashen waje suna taka muhimmiyar rawa ga ci gaban al’umma daban-daban. Kafofin yad’a labarai suna da nau’o’I da suka had’a da radiyo da talabijin da jaridu da muhallu. Akwai ma kafofin sadarwa masu nasaba da shafukan zumunta da shafukan zumunta na yanar gizo masu zaman kansu. Kamar yadda Magaji (2013) ya nun acewa ko’ina a duniya an san muhimmancin kafofin yad’a labarai a matsayin tushen ilmantar da al’umma, wannan kafar ce harshen Hausar ya samu ya ciri tuta a nan Arewacin Nijeriya da k’asashen k’etare. An d’auki radiyo a matsayin kafar yad’a laarai wadda ta fi muhimmanci da amfani dangane da harshen Hausa. Wanan kafa tana yin yunk’uri sosai da sosai wajen fad’akar da al’umma a ‘bangarori daban-daban na rayuwa.
Harshen Hausa yana taka muhimmiyar rawa a rediyo na cikin gida da ma k’asashen waje. Hasali ma dai ana da gidajen rediyo daban-daban a Arewacin k’asar nan wad’anda Hausa take da babban tasiri da muhimmanci dangane da yad’a shirye-shiryen rediyon. Tun farko ana iya cewa ahrshen Hausa ya samu ayd’uwa da bunk’sa a nan gida Nijeriya a dalilin tafiye-tafiye da Hasuawa suka yi zuwa fatauci a garuruwa da k’asashe daban-daban. A ra’ayin Yunusa (1993) cewa ya yi, harshen Hausa ya samu yad’uwa ne ta hanyar kasuwanci a Nijeriya fiye da kowace irin anya. A k’asashen k’etare kuwa, harshen Hausa ya shiga lunguna daan-daban. Kamar yadda Sar’bi (2011) ya bayana cewa tushen bunk’asa da yad’uwar harshe cikin duniya shi ne cud’anya. A ra’ayin malamin, ya nuna cewa harshen Hausa ya yi nasarar samun irin wannan dama ta cud’anya da harsuna daban-daban. Ya k’ara da cewa bayan Larabawa, Hausawa sun yi cud’anya da k’abilu da dama a cikin da wajen Nijeriya.
Saboda haka harshen Hausa a kafofin yad’a labarai, musamman rediyo na k’asashen waje suna bayar da gagaruwamar gudunmuwa dangane da cigaban k’asa. Wasu daga cikin gidajen rediyo da ake gudnar da shirye-shirye a cikin harshen Hasua sun ahd’a da:
- BBC
- Muryar Amurka
- Muryar Jamus
- Rediyo Faransa
- Muryar Sin
- Rediyo Ghana
- Rediyo Masko
- Muryar Alk’ahira, Masar
- Rediyon Garwa, Kamaru
- Rediyon Yamai da Damagaram (Muryar Sahel)
- Rediyon Jamhuriyar Musulunci ta Tehran (D’an mai goro)
Turk’ashi, wasu kaya sai amale, lallai harshen Hausa ya shiga duniya. Akamar yadda Garba (2013) ya bayyana cewa ahrshen Hausa na d’aya daga cikin harsunan Afirka da aka fara watsa shirye-shirye a gidajen rediyo na k’asashen waje. Ya k’ara da cewa akwai wasu harsuna biyu a k’asar Ghana, wato Ewe da Twi wad’anda suke tare da harshen Hasua da suka fara ‘bullowa a gidajen rediyo tun wajen shekara ta 1930. A ra’ayin malamin kamar yadda ya samo daga Ansa (1979) da Kugblenu (1974) a cikin Blankson (2005), ya ce, ‘yan mulkin mallaka na Ingila sun fara gabatarwa da watsa shirye-shirye a gidan rediyon Ghana a cikin ahrsunan Ewe, Twi da harshen Hausa a kafar yad’a labarai ya dad’e da samuwa da bunk’asa da taimakawa wajen ci gaban k’asa.
https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
2.4 Nad’ewa
Nazarin harshe cikin dangantaka da rukunin jama’a yaan taimakawa ta hanyoyi da yawa. Na farko yana taimakawa wajen sanin matsayin, harshe, ta hanyar tantance al’umma majiya wannan harshen, kare-karen ahrshen da kuma karoron sassa gaba d’aya. Misali a nan shi ne halayen rukunan jama’a cikin al’umma. Wato duk da cewa wad’annan rukunai sun bambanta da juna, to bambancin yana zuwa a tsare ta yadda duk suna amfana da dokoki na sarrafa harshen.
Daga abubuwan da suka gabata a cikin wannan babin, mun ga yadda tsarin rukunin jama’a yake, da kuma yadda fad’i da yalwar harshen Hausa ta haifar da nau’o’in Hausar harshen daban-daban. Daga k’arshe kuma, mun ga yadda Hausa ta kasance d’aya daga cikin manyan haarsuna da ke taka rawa ta fuskar sadarwa a kafafen yad’a labarai na gida da wajen Nijeriya. A yau, babu wata k’asa a doron duniya da take ji da kanta, face tana amfani da harshen a kafafen yad’a labaranta. Alal misali: Gidan rediyon BBC da ke London shi ne ya fara shiye-shiryen Hausa kafin daga baya gidan rediyon Jamus da Muryar Amurka su biyo baya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.