Ticker

Matsayin /N/ Da /R/ A Karin Harshen Sakkwatanci (3)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya

NA 

SHAMSUDEEN BELLO HAMMA’ALI

BABI NA BIYU: K’WAYAR MA’ANA


2.0 SHIMFI’DA


A cikin wannan babin za a kawo irin gudummawar da masana da manazarta suka bayar, game da bayyana yadda ma’anar k’warayar ma’ana take da kuma yadda kashe-kashenta yake kasancewa. Sannan a bayar da misalai da za su fito da nazarin a fili, daga k’arshe sai a nad’e babin.

 

2.1 MA’ANAR K’WAYAR MA’ANA


Masana sun tofa albarkacin bakinsu wajen ba da ma’anar k’wayar ma’ana a fagen nazarin ginin kalma ta hanyar da suka dube ta da idon basira. Misalin irin wad’annan masana sun had’a da:-

Skinner N. (1977) ya bayyana k’wayar ma’ana da cewa:-

K’wayar ma’ana ita ce sashen magana mafi k’ank’anta ga harshe wadda ke d’auke da ma’ana”.

 

 

 

 

Crystal (1980). Inda yake cewa: “K’wayar ma’ana furuci ne mafi k’ank’anta a cikin nahawun harshe wadda ita ce zuciyar ilimin ginin kalma”.

Ta la’akari da ire-iren wad’annan bayanan da masana suka yi dangane da k’wayar ma’ana ana iya cewa, k’wayar ma’ana ita ce furuci ko kalamin da aka k’ara wa kalma domin samar da sabuwar ma’ana wadda ta bambanta da ma’ana ta asali.

 

2.2 RABE-RABEN K’WAYAR MA’ANA


Bisa tsarin nazarin harsunan duniya, ana iya cewa samun rabe-rabe a ajin kalmomin na hausa ba sabon abu ba ne, domin akwai azuzuwan kalmomin da dama wad’anda ake iya samun sun zo da rabe-rabe a cikinsu. Daga cikin ire-iren azuzuwan nahawun da suka samu irin wannan rabe-rabe akwai k’wayar ma’ana. K’wayar ma’ana ta samu kulawa na a nazarce ta, don haka ita ma ta samu rukunonin da aka kasa ta domin a sami sauk’in fahimtar ta kamar yadda za a gani nan gaba.

 

2.2.1 TURK’AK’K’IYAR K’WAYAR MA’ANA


Turk’ak’k’iyar k’wayar ma’ana, k’wayar ma’ana ce da take da wasu dalilai da ya sa aka kira ta da wannan suna na Turk’ak’k’iya, sabo da tana da wasu ‘yan tsare-tsare guda biyu da suka kasance hujja na a kira ta da wannan suna. Dalilan kuwa su ne:-

  1. Dalili na farko shi ne ba a iya yi ma ta k’ari a gabanta ko a bayanta. Hasali ma irin wannan k’wayar ma’anar tana zuwa ne a madadin haruffa ne kawai, wato su ba ga’ba ba kuma ba saiwar kalma ba.

  2. Dalili na biyu kuwa ba ta iya tsayuwa da kanta domin ta ba da ma’ana cikakkiya.


Misali:

Kwayar ma’ana               Tilo             Muhallinta

una                                 Jaki             Jakuna

oyi                                 Taya            Tayoyi

uwa                                Shiri            Shiraruwa

Abin lura a nan shi ne, wannan k’wayar ma’ana tafi amfani ta ‘bangaren jam’in abubuwa.

 

2.2.2 NINKAKKIYAR K’WAYAR MA’ANA


Ninkakkiyar k’wayar ma’ana ana amfani da ita ne a lokacin da ake k’ok’arin samar da wata kalma daga kalma mai ma’ana ta asali. Inda ake amfani da ninka wani bak’i daga cikin kalmar ta asali domin a samar da wata kalmar mai sabuwar ma’ana.

Misalin wannan shi ne:-

Kalma                      Tushe          Sabuwa       Kasancewa

  1. i) Zaga Zag Zag-zaga               Zazzaga

  2. ii) Kare Kar Kak-kare               Kakkare


iii) Share                  Shar            Shas-share             Sasshare

Haka kuma ana nunka bak’i sau biyu a cikin kalma domin samar da wata sabuwar kalma mai d’auke da ma’ana cikakkiya ta daban. Misali:

Kalma                   Sabuwa

  1. i) Buga Bugagge

  2. ii) K’ona K’onanne


iii) Ajiya               Ajiyayye

  1. iv) Yanka Yankakke


 

22.3 K’WAYAR MA’ANA TA GURGUZU


Ana samun irin wannan k’wayar ma’ana ne a lokacin da turk’ak’k’iya k’wayar ma’ana guda biyu ko fiye da biyu suka had’e wuri guda domin samar da wata kalmar da take d’auke da ma’ana ta daban.

Misali-nta, d.s

  1. i) K’aho (k’ahon dabba) k’aho nta     k’ahonta

  2. ii) Wuri (Wurin zama) Wuri  nta     Wurinta


 

2.2.4 K’WAYAR MA’ANA MAI MAIMAICI


Ana samun irin wannan k’wayar ma’anar ne a lokacin da ake k’ok’arin samar da wata sabuwar kalma daga kalma mai d’auke da ma’ana ta asali, a yayin da ake maimaita ita kalmar ta asali domin fito da sabuwa daga gareta, mai d’auke da ma’ana ta daban.

Misali:

Kalma                   Maimaici

Bak’i                    Bak’i-bak’i

Fari                       Fari-fari

K’arami                K’arami-k’arami

Duhu                    Duhu-duhu

 

2.2.5 BAMBANTACCIYAR K’WAYAR MA’ANA


Ita irin wannan k’wayar ma’anar ta bambanta da sauran k’wayoyin ma’ana, saboda ita ba a amfani da kalmar asali ko saiwarta wurin samar da ita. A maimakon haka sai a samar da wata da ta sha bamban da ita, amma kuma suna da kusanci da juna wurin amfani da su illa iyaka ma’anar tasu ce ba d’aya ba.

Misali:

Kalma                   Bambantaciya

  1. i) Miji Mata

  2. ii) Sa Nagge


iii) Saurayi            Budurwa

 

2.2.6 SAKAKKIYAR K’WAYAR MA’ANA


Sakakkiyar k’wayar ma’anar ana iya yi ma ta k’ari na d’afin harafi a gabanta ko a bayanta ta samar da ma’ana cikakkiya. Wad’annan k’wayoyin ma’anar ana iya yi mata k’ari ta samar da wata sabuwar kalmar wadda ma’anarta ta bambanta da ta kalma mai ma’ana ta asali. Misali -n da -r.

  1. Rigar Bala

  2. Wandon Audu



  • Gidan K’asa



  1. Farin Gida


Wad’annan k’wayoyin ma’anar suna kasancewa a gurabe da dama a cikin kalmomi.

 

2.3 NA’DEWA


A wannan babi an ga yadda aka kawo ma’anar k’wayar ma’ana, daga ra’ayoyin masana, da yadda aka raba nau’o’in k’wayar ma’anar da kuma yadda kowane nau’i yake kasancewa wajen samar da sabuwar kalma daga saiwa ko kuma k’irk’irar wata kalmar ba tare da an yi amfani da wani sashe na kalmar asali ba. Sannan an nuna yadda ake samar da wata sabuwar kalmar. Haka kuma an ga yadda aka gabatar da k’wayoyin ma’ana na -n da -r a fagen nazarin k’wayar ma’ana.

 

 

 

 

Post a Comment

0 Comments