Ticker

    Loading......

Nazarin Zaman Gandu A Garin Zazzau (2)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

SHEHU MUHAMMAD TAFIDA

BABI NA DAYA: Bitar Ayyukan Da suka Gabata Da Dalilin Bincike

1.0 SHIMFI’DA


A cikin wannan babin an yi k’ok’arin waiwayar baya domin bitar ayyukan da suka gabaci wannan aikin. Sannan an bayyana dalilin da ya sa aka gudanar da shi. An fito da bayanin iyakar farfajiyar binciken. An kuma bayyana mahimmancin binciken ga al’umma. Daga k’arshe kuma kamar kowace tafiya akwai hanyar da ake bi domin cimma manufarta, don haka sai aka nuna inda aka bi don samun nasarar kammala aikin. Inda aka fito da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan binciken. Sannan aka nad’e babin da tak’aita abin da aka bayyana a cikinsa.

1.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


A wannan kaso an yi bitar ayyukan da suka gabaci wannan aikin, masu nasaba da shi kai tsaye ko a kaikaice. Musamman wad’anda aka gudanar a fagen bincike na kundayen digiri da littafan da aka wallafa. Ga yadda aikin ya gudana.

Umar M.B. (1987). A nasa ra’ayin dangane da zamantakewar iyali musamman a al’ummar Hausawa ya ce; “ Ba kurum ya k’unshi matarsa da ‘ya’yansa ba ne, har da duk wani wanda ke k’ark’ashin ikonsa, ya-alla  suna da dangantaka ta jini ko babu. Wannan ya tabbata ne sakamakon wasu sharud’d’a ko yarjeniyoyi tsakanin jama’a wad’anda ke da ra’ayin zama na tarayya. Wad’annan yarjeniyoyin na iya kasancewa maigida shi ne wuk’a da nama ga duk harkokin da suka shafi jama’a wad’anda ke zaune k’ark’ashin ikonsa”.

Bisa ga bayanin da Umar ya bayar ana iya fahintar, sakamakon yarjeniyoyin da al’ummar Hausawa suka k’aga wa kansu ita ta haifar da zamantakewar iyali. Sakamakon wannan bayanin da ya gabata an maganta ne dangane da zamantakewar iyali na yau da kullum, wanda shi kuwa wannan aikin zai karkata ne ya zuwa zaman gandu.

Alhassan, H. da Musa, I.V. (1982) sun nuna cewa “ Ko da addinin musulunci ya iso k’asar Hausa ya tarar da Hausawa na zaune cikin tsari da ingantattun al’adunsu na auratayya da kuma zumunta da sauran nau’o’in zaman tare;” Wannan bayanin ya k’ara tabbatar da cewa al’umar Hausawa tun kafin zuwan addinin musulunci suna zaune ne cikin tsari da kyawawan al’adunsu, musamman wad’anda suka shafi auratayya da zumunta da zaman tare.

Bisa ga wannan bayanin na sama masanan sun maganta ne dangane da zamantakewa irin ta aure, wanda wannan aikin ba a kansa ya maganta ba, shi ya karkata ne ya zuwa ga zamantakewar zuriya gaba d’aya k’ark’ashin maigida wadda ake kira da zaman gandu.

Adamu,  M. (1976), ya nuna cewa; “ A irin wannan zamantakewa ta gandu mutun zai tarar da dukkan mazaunan gandu, iyalansu na zaune ne a gida guda wanda aka gada kaka da kakanni, hatta gonaki tare ake aikinsu. Wannan aikin ya so ya yi kama da wannan binciken, amma shi an gudanar da shi ne a yankin k’asar Hausa baki d’aya ba tare da an yi cikakken bayaninyadda zaman gandu yake a kowane yanki na k’asar Hausa ba. Sai dai wannan aikin zai ke’banta ne kawai a garin Zariya wanda wani yanki ne na k’asar Hausa.

Ogundokoro,  L.M.D. (1994), ta ce; “ Tsarin zaman gandu an fi samun shi ne a nahiyar afirka ta yamma, musamman a Nijeriya. Ta k’ara da cewa mazauna gidan gandu sun had’a da ‘ya’ya da k’annen uba da  ‘yan-uwa, da jikoki da agola k’ark’ashin jagorancin maigida d’aya da suke zaune a gida guda. Wannan bayanin ya ba da misali ne na inda ake aiwatar da irin wannan zamantakewar gandu. Amma wannan aikin ya kawo fasali ne da tsari na yadda ake gudanar da shi a garin Zazzau.

Makindi, D. (1983), ya nuna cewa; “ Iyali rukuni ne na jama’a mazauna gida, wanda kan taru a sakamakon auratayya. Wato dai akan sami rukunin iyali ne sakamakon namijin ya auri mace su zauna gida guda har su hayayyafa”

Wannan masanin ya yi bayani ne dangane da samuwar iyali, sakamakon auratayya. Amma wannan aiki ya yi bayani ne na zamantakewar gandu wanda rukuni ne na zamantakewar iyali. Sakamakon bitar da aka gudanar dangane da wannan aikin, magabata sun yi bayani ne dangane da ra’ayoyin da suka nuna yanayin  zamantakewar iyali a k’asar Hausa. Idan aka duba za a ga yana da nasaba da wannan aikin, sai dai wannan aikin zai ke’banta ne a cikin garin Zazzau, domin duba yadda Zagezagi ke aiwatar da zaman gandu  yanayin zamantakewa.

 

 


  • DALILIN BINCIKE




Bincike a kan gudanar da shi ne bisa ga wani muhimmin dalili ko dalilai, da aka d’ora wannan binciken a kansa, don ya zama ginshik’in ginin abin da aka binciko. Haka wannan  binciken an yi shi ne domin zak’ulo wasu abubuwa da ta yiwu ba a kai gare su ba, ta yadda masu bincike ko nazari game da al’adun Hausawa  za su same su cikin sauran taskokin da ake da su musamman ma na al’ada.

A nan ana  son a bayyana cewa wannan binciken ya samu dalilin wanzuwa, ne saboda kusan duk nazarce-nazarcen da masana suka gabatar sun ta’allak’a ne kan yanayin zamantakewar al’ummar Hausawa gaba d’aya. Wato ba wani wanda ya ke’bance zaman gandu na garin Zazzau don ya nuna mahimmancinsa wajen gina zumunci.


  • FARFAJIYAR BINCIKE




Zaman gandu wani nau’i ne na kulawa da tsarin rayuwar iyali da tattalin arzik’insu. Mutanen k’asar Zazzau sun fara aiwatar da irin wannan al’ada ce ta zaman gandu tun kaka – da – kakanni, wato a hasashe tun kafuwar al’ummar zagezagi. Ganin haka shi ya sa aka ga ya dace da a d’auko wannan al’adar domin a fito da ita fili. Ganin mahinmancin zaman gandu na Zagezagi ya sa wannan aikin zai ke’banta a garin birnin Zariya ba tare da ya k’etara wani sashi na lardin ba. Don gudun samun bak’uwar al’ada. Don ba da gudunmawa ga duk wata al’umma da ba ta da irin wannan fasali da tsari na kula da zuriya saboda su sami damar aron wannan al’adar.


  • MUHIMMANCIN BINCIKE




Muhimmancin wannan binciken shi ne, don a fito da yanayin tsaro da kula da tsarin rayuwar iyalin Zazzagawa a fili. Don ya taimaka wa masu sha’awar aro ko yin amfani da tsarin rayuwar  iyali irin ta Zagezagi. Saboda k’arfafa ko k’ulla zumunci da kare zuriya daga gur’bata daga wata mummunar al’ada da za ta ‘bata tsarin rayuwarsu.


  • HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE




Aikin ya bi diddigin ayyukan da aka riga aka gudanar a fagen nazari musamman wad’anda suka shafi al’adar zamantakewa ta al’umma. Aikin ya dubi litattafan da aka riga aka wallafa dangane da zamantakewar al’umma, da kuma d’akunan  karatu na manyan makarantu, tare da ziyartar wasu muhimman mutane da suka ga jiya suka ga yau. Domin tattaro muhimmnan bayanai daga gare su.


  • NA’DEWA




A cikin tak’aitattun bayanan da aka kawo cikin wannan babi an gudanar da bitar ayyukan da suka gabata, wad’anda magabata suka yi bisa zamantakewar Hausawa da iyalinsu. Inda binciken ya nuna ba wanda ya ta’ba gudanar da nazarin al’adar zaman gandu a garin Zazzau. Sai dalilin bincike inda aka nuna binciken an yi shi ne, domin zak’ulo wasu abubuwa da ta yiwu ba a kai gare su ba, ta yadda masu bincike ko nazari za su aiwatar da wani abu a kansu.

Cikin farfajiyar binciken an nuna iyakacin da binciken zai ke’banta. sabo da muhimmancinsa aka ce zai ke’banta a birnin Zazzau ba tare da ya k’etara wani sashi na lardin ba. A hanyoyin gudanar da bincike ne aka nuna  an bi diddigin ayyukan da aka riga aka gudanar a fagen nazari, musamman wad’anda suka shafi al’adar zamantakewa ta al’umma domin tattaro bayanan da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan aikin. Daga k’arshe sai aka nad’e babin da abin da aka tattauna a cikinsa.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments