Ticker

6/recent/ticker-posts

Yanayin Zuwan Mafayyaciya Da Lokatak Da Dirka Cikin Jumlolin Karin Harshen Sakkwatanci (2)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya

NA 

HARUNA ABDULLAHI UMAR

BABI NA DAYA: GABATARWA

1.0    SHIMFI’DA


An dad’e ana gudanar da bincike, musamman a kan abin da ya shafi lamarin Sakkwatanci, ko Katsinanci, ko Zamfaranci, ko Kabanci da dai sauran kare-karen harshen Hausa. Da farko dai kafin a ce komai, ya kamata a san k’unshiyar wannan babi da ke k’ok’arin bayyana abubuwan da suka shafi nazarin da ake son gudanarwa. A wannan babi na farko yana da bayanan abubuwa da suka had’a da, bitar ayyukan da suka gabata, da dalilin yin bincike, da hanyoyin gudanar da bincike, da kuma muhimmancin bincike. Don haka wad’annan abubuwa da aka ambata, su ne za a gabatarwa, a kaso na gaba in da za a fara da bitar ayyukan da suka gabata kamar haka:

1.1    BITAR AYUKKAN  DA SUKA GABATA


Ganin irin muhimmancin da ke akwai wajen duba ire-iren rubuce-rubucen da magabata suka rubuta da nufin yin bitar wad’ansu daga cikin su, musamman wad’anda suke da alak’a da wannan binciken, tun daga kundaye da muk’alu da mujallu da litattafai in har akwai.

Abubakar, B. (1990) ya yi k’ok’arin yin zuzzurfan bincike kan karin harshen Sakkwatanci, inda ya yi k’ok’arin gano bambancin sunaye tsakanin Sakkwatanci da daidaitacciyar Hausa. Kuma ya yi magana kan yadda karin harshen Sakkwatanci ke samar da suna na jinsin mace, wanda ya sa’ba wa na daidaitacciyar Hausa. Ya nuna cewa ana iya k’irk’iro suna ta hanya biyu, wato ta amfani da tushen kalma, da kuma d’afi. d’afin zai iya kasancewa d’afa-goshi da kuma d’afa-k’eya ko kuma d’afa-k’eya kawai. Misalin irin wad’annan Kalmomin su ne:

Tushen kalma                 d’afa-k’eya                     cikakkiyar kalma

kan-                                - o                                  - Kano

d’afa-goshi            tushen kalma         d’afa-k’eya  cikakkiyar kalma

ba-                        kan -                     - o               Bakano

ba-                        kan -                     - uwa           Bakaniya     D.H.

ba-                        kan -                     - a               Bakana   KH. SK.

Amfani, A. H. (1984) ya gabatar da mak’ala mai suna “Aspects' of Hausa Dialectology,” ya yi bayanin ke’ba’b’bun siffofin (idiosyncractic features) wasu kare-karen harshe Hausa. Ya yi bayani kan yadda wasu kare-karen harshen Hausa suka sha bamban da juna wajen amfani da lokatak’ (tense aspect).

Hamma'ali B.M. (1985) A cikin nasa aikin ya kwatanta Sakkwatanci da daidaitacciyar Hausa a fannin furuci da tsarin Kalmomi da kuma tsarin jimloli. Haka kuma, ya yi k’ok’arin kawo bayanai dangane da Sakkwatanci da kuma bambancinsa na Kalmomi da Ma'anoni duk a tak’aice.

Duk wad’annan ayyukan na wad’annan masanan suna magana ne a kan abin da ya shafi kare-karen harshen Hausa a ciki harda Sakkwatanci, inda suka banbanta da wannan aikin shi ne, wannan aikin ya ke’banta ne kan wasu muhimman kalmomi, na ajin kalmomi masu aiki irin na nahawu. Kalmomin sune mafayyaciya, lokatak’ da dirka don nuna yadda suke zuwa a cikin Karin harshen Sakkwatanci.

1.2 DALILIN BINCIKE


        Dalalin da ya haifar da wannan binciken shi ne, a lokacin gudanar da bitar ayyukan da magabata suka aiwatar ba a sami wani aiki da ya yi daidai da wannan nazarin ba ko da kuwa ta fuskar taken bincike ne. Wani dalilin kuma shi ne don cika k’a’idar da Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato ta shar’anta kan cewa duk dalibin da ya kawo shekarar k’arshe dole ne ya gudanar da bincike na nazari a fannin da yayi karatu don bada gudumuwa a sashen ta fuskar ilimi. Dalili na uku kuwa shi ne yin wannan bincike zai taimaka wajen warware matsalar da akan samu na fahimtar karin harshe Sakkwatanci ga sauran jama’a musamman ma mutanen da suka fito daga rukunin karuruwan Hausa na gabashi.

1.3 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE


        An gudanar da wannan bincike a kan matakai daban-daban. Da yake aiki irin wannan ya shafi cud’anya da jama’a da ziyartar wurare muhimmai da ake iya samar da shiga d’akunan karatu da kuma huld’a da mutane don samar da ingantattun bayanai. Don haka nazarin ya yi k’ok’arin shiga sak’o da lungu tare da ziyartar masana, da yin nazarin ayyukansu domin cimma burin ganin anyi aikin bincike mai inganci.

1.4 MUHIMMANCIN  BINCIKE


Wannan binciken ba zai rasa rawar da zai taka ba a gaban manazarta, wato ma'ana ba zai rasa kasancewa mai muhimmanci ba ga masu karatu ko nazarin abin da ya shafi karin harshe, musamman ma tsakanin Karin harshen Sakkwatanci da kuma daidaitacciyar Hausa, da sauran kare-karen harshe Hausa.

Wannan binciken zai kasance mai alfanu ga manazarta masu bincike kan abin da ya shafi karin harshen Sakkwatanci, musamman  kan abin da ya shafi lokatak’ a Sakkwatanci da kalmomin dirka da kuma kalmomin mafayyaciya. Haka kuma, zai taimaka ga masu son su san Sakkwatanci, da kuma masu nazarin bambance-bambancen da ake samu tsakanin Sakkwatanci da Daidaitacciyar Hausa.

Muhimmancin wannan binciken ga manazarta kuwa, bai wuce su yi amfani da shi wajen sanin bambancinsa da sauran karuruwan harshen Hausa ba, ta yadda za su iya tantance shi tsakanin sa da sauran karuruwan harshen Hausa. Haka kuma zai taimaka wa mai nazarin rubuce-rubucen mak’alu da kundayen digiri da litattafai musamman masu aiki kan tsarin ginin jumla, don sanin k’a’idar yin amfani da kalmomin.

A k’arshe wannan binciken zai kasance mai muhimmanci a gare ni. Domin shi ne zai kasance abin bugun gaba gare ni, da kuma makami, a duk inda na shiga ko na kasance ya rik’a nuna ni domin in kasance a cikin wad’anda suka d’an ce wani abu a cikin harshen Hausa. Kuma zai k’ara muhimmanci ga masu son cigaba ga harshen Sakkwatanci da su k’ara zurfafa bincike na wasu abubuwa makamantan wad’annan a cikin harshen Sakkwatanci, kuma, zai k’ara k’arfafa k’warin gwuiwa ga wasu masu nazari da zak’ulo hanyoyi domin bunk’asa harshen Sakkwatanci.

 

1.5 NA’DEWA


A wannan babin na d’aya an yi bayani kan bitar ayyukkan da suka gabata da kuma dalilin yin bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike tare da kuma muhimmancin bincike, haka kuma an nuna tsarin gabatar da aiki. Babban muhimancin wanannan binciken shi ne na kulawa wasu muhimman kalmomi da zantukan Karin harshen Sakkwatanci dan gudun salwantar su, saboda barazanar sauyawar zamani da ake samu kan harsunan duniya da harshen Ingilishi yake yi musu.

 

 

Post a Comment

0 Comments