Kundin Binciken Kammala Karatun Digiri Na Farko (B.A. Hausa) A Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Na
SHEHU HIRABRI
08143533314
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 Shimfiɗa
Wannan babi zai yi bayanin kammalawa da yadda tsarin aikin ya kasance daga babi
na ɗaya zuwa babi na biyar, sannan za a kawo sakamakon bincike da naɗewa. Haka
kuma bayan naɗewa, manazarta da ratayen waƙoƙin makaɗa Alhaji Musa ‘Danba’u
Gidan Buwai za su biyo a ƙarshen aiki.
https://www.amsoshi.com/2017/06/17/jigogin-wakokin-madahu-cikin-wakokin-masu-jihadi/
5.1 Kammalawa
Wannan aikin bincike mai taken: “Zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji
Musa ‘Danba’u Gidan Buwai.” Na ɗauke da babi biyar. Babi na ɗaya shi ne
gabatarwa da ke ƙunshe da shimfiɗa da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci
gaba da bincike da hanyoyin gudanar da bincike da muhallin bincike da kuma
matsalolin bincike. A ƙarshe aka biyo da naɗewa.
A babi na biyu an kawo taƙaitaccen tarihin rayuwar Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan
Buwai mai ɗauke da haihuwarsa da iliminsa da iyayensa da matansa da yaransa da
fara waƙarsa. Haka kuma an kawo jerin sunayen yaransa makaɗa da maroƙa da
nau’o’in waƙoƙinsa da abubuwan da yake sha’awa. An kuma bayyana dangantakarsa
da sauran makaɗa da kuma dangantakarsa da sauran al’umma. A ƙarshe aka kawo naɗewa
da babin ke ɗauke da ita.
A babi na uku an kawo bayanin asalin kalmar zambo da ma’anarta da ire-irenta
tare da bayyana dalilin da ke sa a yi zambo. Haka kuma an kawo amfaninsa,
sannan aka yi sharhin zambo a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa ‘Danba’u da kuma bayanin
naɗewa a ƙarshen babin.
A babi na huɗu an tattauna habaici tun daga asalin kalmar da ma’anarta da
ire-iren habaici da dalilan da ke sa ana yin sa tare da bayyana amfaninsa.
Sannan aka yi sharhin habaicin tare da fito da shi a cikin wasu waƙoƙin Alhaji
Musa ‘Danba’u Gidan Buwai. A ƙarshe an kawo naɗewa.
Babi na biyar aka yi bayanin kammalawa tare da bayyana sakamakon bincike kamar
haka:
5.2 Sakamakon Bincike
Kamar yadda Bahaushe ke cewa: “Komai da ranarsa.” Wannan magana haka take, domin
al’ummomi da dama sun ɗauki zambo da habaici a matsayi hanya ta ɓatanci da cin
zarafi, a haka su ma masana da manazarta suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da
ma’anonin kalmomin biyu inda suka bayyana zambo a matsayin suka ta kai tsaye
shi kuma habaici suka a kaikaice. Amma tare da haka sashen wannan aiki ya gano
cewa zambo da habaici suna da matuƙar amfani ga jama’a a wurare daban-daban
kamar haka:
1. Zambo da habaici
dukkansu taska ce ta adana adabin Bahaushe.
2. Zambo da habaici na
hana yin shisshigi wato mutum ya shiga sha’anin da bai shafe shi ba.
3. Zambo da habaici
dukkansu ado ne da ke ƙawata harshe musamman a cikin waƙa da kuma zantukan yau
da kullum.
4. Zambo da habaici na
faɗakar da mutane ta hanyar sanin miyagun ɗabi’u ko ƙazafi ko wani abu na daban
da jama’a ke zargin sa da shi.
5. Zambo da habaici kan
taimaka wajen ƙara soke abokin hamayya.
6. Zambo da habaici na
bayyana miyagun ɗabi’un mutum cikin hikima domin a kauce masa.
7. Zambo da habaici na
samar da nishaɗi ga mai sauraro. Yakan iya kasancewa hannunka-mai-sanda ga
wanda ake wa.
8. Zambo da habaici kan
taimaka wajen mai da martani musamman ga sarakuna da masu mulki ta hanyar wani
zalunci da suke yi wa talakawansu.
9. Zambo da habaici a
cikin waƙoƙi ko maganganu yau da kullum na ƙara bunƙasa harshe.
10. Zambo da habaici na
taimakawa wajen huce haushin wanda ba a iya mayar wa raddi kai tsaye.
11. Ƙwarewa wajen yin
zambo da habaici a cikin waƙoƙin siyasa da na sarauta na ƙara wa makaɗi ɗaukaka
da farin jini ga wanda ba shi ake yi wa ba. Wanda aka yi wa kuwa, an tsira gaba
ta har abada.
12. Ƙwarewa wajen yin
zambo da habaici kan sa mawaƙi ko makaɗi ko maroƙi ya samu alheri.
13. Muhimmancin zambo da
habaici ga al’umma har ya kai ga samun gurbi a cikin adabi da ake nazarin su a ƙananan
makarantu da kwalejoji da kuma manya-manyan jami’o’i.
5.3 Naɗewa
Wannan babi an yi bayanin kammalawa ne tare da bayyana yadda tsarin aikin yake,
sannan an kawo sakamakon bincike inda aka gano muhimmancin zambo da habaici ga
al’ummar Hausawa.
1 Comments
[…] Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai (5) […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.