Kundin Binciken Kammala Karatun Digiri Na Farko (B.A. Hausa) A Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Na
SHEHU HIRABRI
08143533314
BABI NA BIYU
TAƘAITACCEN TARIHIN RAYUWAR ALHAJI MUSA ‘DANBA’U
GIDAN BUWAI
2.0 Shimfiɗa
A
babin da ya gaba an yi bitar ayyukan da suka gabata tare da bayyana ƙudurin
bincike. Shi kuma wannan babin za a yi bayanin tarihin rayuwar Alhaji Musa
‘Danba’u Gidan Buwai. Tarihin zai ƙunshi haihuwarsa da iliminsa da matansa da
‘ya’yansa da fara waƙarsa da makaɗansa da maroƙansa da nau’in waoƙoƙinsa da
nasarorin da ya samu a cikin waƙa da yawace-yawacensa har zuwa rasuwarsa. Haka
kuma za a bayyana dangantakarsa da sauran mawaƙa da kuma sauran al’umma baki ɗaya.
2.1 Taƙaitaccen Tarihin
Alhaji Musa ‘Danba’ub Gidan Buwai
2.1.1 Haihuwarsa
An haifi Alhaji Musa ‘Danba’u a shekarar 1958 a shekarar da aka yi wata
yunwa a ƙasar Hausa wadda ake kira muɗa. An haife shi ne a garin Gidan Buwai da
ke cikin ƙaramar hukumar Mulkin Rabah ta jahar Sakkwato. Duk da yake wasu
manazarta da suka yi rubutu a kan Alhaji Musa ‘Danba’u sun sha bamban dangane
da shekarar da aka haife shi, Bala da wasu (1993) sun bayyana cewa, an haife
shi a shekarar 1955. Shi kuma Shagari, (2011) ya bayyana an haifi ‘Danba’u a
shekarar 1962.
Ganin irin wannan bambanci ya sa na zage dantse domin samun tabbacin shekara da
aka haife shi inda na yi tafiya har zuwa garin Illela inda wazirinsa mai suna
Shehu waziri wanda a yanzu shi ne halifan ‘Danba’u domin shi ke waƙa tare da
duk makaɗa da maroƙa da kuma kayan kiɗan da Alhaji Musa ya bari inda ni yi hira
da shi da kuma wani makaɗin ‘Danba’u Adamu Tozai inda suka bayyana mini wannan
shekara. Mun tattauna da su ne a ranar Lahadi 19-03-2017 a garin Illela inda
ranar 20-03-2017 na ga littafin Sa’idu Muhammad Gusau mai suna Makaɗa
da Mawaƙan Hausa na Biyu wanda aka buga a shekarar 2016 a ɗakin karatu
na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo inda a shafi na
goma sha ɗaya (11) ya tabbatar da an haifi Alhaji Musa ‘Danba’u a shekarar
1958, wanda wannan hujja ta tabbatar mana cewa an haifi Alhaji Musa ‘Danba’u a
shekarar 1958.
2.1.2 Iliminsa
A
wajen ilimi, Alhaji Musa ‘Danba’u ya yi karatunsa na addini tun yana ƙaramin
yaro a wajen kakansa, inda ya sauke Alƙur’ani mai girma kuma ya karanci
littafai da dama kamar Ahalari da Ishmawi da Iziyya da Risala da Hadisai haka
kuma kamar yadda Waziri Shehu da Adamu Tozai suka faɗa mini cewa ya hardace
ishiriniya gaba ɗaya.
A ilimin zamani kuwa, Alhaji Musa ‘Danba’u bai yi zurfi ba domin mahaifinsa ya
sa shi firamare yana aji uku kakansa ya fitar da shi domin ya yi zurfi ga
iliminsa na addini domin kakansa liman ne da ma ba su cika son boko ba.
2.1.3 Iyayensa
Sunan
mahaifin Musa ‘Danba’u Abdullahi Maiɗanjaki, wasu kuma na kiran sa Audu jikan
Liman. Asalin kakan ‘Danba’u daga wani gari ne mai suna Kurgaba a ƙaramar
hukumar Mulki ta Wurno ya taso ya komo Gidan Buwai.
Abdullahi makaɗin goge ne amma haye ya yi domin bai gaji kiɗa daga iyayensa ba.
Hasali ma, mahaifin Abdullahi, Liman Muhammadu, malami ne wanda ya kafa
makarantar ilimi sannan ga shi liman. Shi kansa Abdullahi mahaifin Musa malami
ne har kuma ya fara limanci sai ya daina ya ci gaba da kiɗan goge.
Sunan mahaifiyarsa Aminatu (Amo ko Umma). Ita ma haifaffiyar Gidan Buwai ce,
ita ma mahaifinta malam Musa malami ne. ‘Danba’u ya yi karatu wurinsa a nan ya
hardace ishiriniya kamar yadda wazirinsa Shehu da makaɗinsa Adamu Tozai suka
sheda mini.
2.1.4 Matansa
Alhaji
Musa ‘Danba’u ya yi aure a ranar 11 ga watan 10 na shekarar 1979 yana da mata
uku kafin rasuwarsa waɗanda suka haɗa da:
1.
Hajiya Asabe
2.
Hajiya Sadiya
3.
Hajiya Aminatu
Bayan waɗannan matan uku, ya auri wasu uku amma sun rabu kafin rasuwarsa. Daga
cikinsu akwai:
1.
Jumma
2.
Ta’Allah
3.
Asabe ƙarama
Jumma ita ce matarsa ta farko wadda ita ce mahaifiyar babbar ɗiyarsa
Hauwa’u (Kulu).
Ta’Allah ita ce matarsa ta biyu. Ita ma sun haihu sun samu ɗa mai suna Zayyanu.
2.1.5 Yaransa
Wazirin Alhaji Musa ‘Danba’u ya sheda min cewa, Alhaji Musa na da ‘ya’ya goma
sha tara (19) da jikoki bakwai (7). Daga cikinsu akwai maza da mata.
Jumma Gidan Buwai
1.
Hauwa’u Kulu
Ta’Allah Gwaddodi
2.
Zayyanu
Hajiya Asabe Illela
3.
Ubaida
4.
Abdullahi
5.
Bashari
6.
Aminu
7.
Mas’udu
8.
Mustapha
Hajiya Sadiya Wurno
9.
Zara’u
10. Amina (Uwani)
11. Mas’uda
12. A’isha
13. Aliyu
14. Abubakar
15. Nana Firdausi
16. Maryam
Hajiya Aminatu Ƙauran Namoda
17. Hadizatu
18. Kabiru
Asabe Ƙarama Illela
19. Murjanatu
2.1.6 Fara Waƙarsa
Wazirin Alhaji Musa ‘Danba’u Shehu Waziri ya sheda min cewa, ‘Danba’u ya fara
waƙa shekara bakwai kafin kafuwar jam’iyoyin NPN da GNPP da UPN da kuma NPP. An
kafa waɗannan jam’iyyun ne a shekarar 1978 (Birniwa, 1987) da Funtua (2003:
37). Kenan ya fara waƙa ne a shekarar 1972. Kuma ya fara ne da waƙoƙin kokawa.
Daga ciki akwai waƙar Isiya Zakinsu ‘Danba’u ga yadda waƙar take:
Amshi: Isiya zakinsu ‘Danba’u
Kowaj ja da kai bai ji daɗi ba,
Jagora: Wahabu Allah ka kiyaye bayinka,
Yara: Wahabu Allah gyara gyararre
Isya zakinsu ‘Danba’u
Kowaj ja da kai bai ji daɗi ba.
(Shagari, 2011; Gusau, 2014).
Haka kuma akwai wata waƙar kokawa wadda wazirin ‘Danba’u ya rera min ya ce tana
daga cikin waƙarsa ta farko waƙar ita ce:
Ya ci maza giyen ‘Danba’u,
Kadi maza suna saunatai.
Wannan ɗan bara ya kaka,
Ya ci tsakin miya yai ƙarhi.
To irin yanda ya taho maka Buba,
Buba ka faɗi rwahin gulbi,
Ga ‘yan yara na dwaga tai.
Daga waƙar kokawa wazirinsa ya ce ya fara haɗawa da waƙar noma. Inda ya yi wata
waƙa ta Abba na Ɗanladi. Ga yadda waƙar take:
Kana da noma,
Ɗan Aba na Ɗanladi.
Na ɗanguje,
Na Ɗanladi,
Na Akki mai aiki,
In dai ina da raina,
Sai kowa ya ji sunanmu.
Haka ko ya tabbata domin dun inda ake jin harshen Hausa an san ‘Danba’u daga
nan ya ci gaba da waƙoƙinsa har zuwa shekara ta 1978 lokacin da siyasar
jamhuriya ta biyu, inda aka samu jam’iyyun NPN da GNPP da UPN da kuma NPP inda
wasu ‘yan jam’iyyar NPN suka buƙaci ya yi musu waƙar jam’iyyarsu ta NPN sai ya
fara tunanin, shi da ke waƙar kokawa yaya zai yi waƙar siyasa? Daga ƙarshe ya
yanke shawarar ya waƙe jam’iyyar. Daga cikin mutanen da suka buƙaci ya yi wa
NPN waƙa sun haɗa da:
1.
Umaru Jikan Macca
2.
Arzika Maikujera Ciyan Party
3.
Wakili Buhari
Ga yadda waƙar take:
Amshi: Aminci ya fi kuɗi,
Mu yarda da NPN
Jagora: in kag ga mutum kajin-kajin
Kag ga mutum maƙal-maƙal,
Ba rigar dala garai,
Yara: Alhaji haske ne,
Alhaji mai zamani,
Allah magaba,
Allah raba mu da ɗan kwakwa.
Amshi: Aminci ya fi kuɗi,
Mu yarda da NPN.
Wannan waƙa da ya yi ta burge jama’a ƙwari da gaske. Daga nan sai ya kama
harkar waƙar siyasa gadan-gadan har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
2.1.7 Yaransa Makaɗa da
Maroƙa
Lokacin
da na yi hira da wazirin ‘Danba’u ya tabbatar min da cewa yana da yara goma sha
ɗaya da maroƙa huɗu. Su goma sha biyar (15) kenan. Amma Mande direba ya riga
shi rasuwa.
Yaransa
1.
Shehu Waziri Gidan Buwai
2.
Garba Ƙyamashi Gidan Buwai
3.
Muhammadu Bello Gidan Buwai
4.
Adamu Tozai Illela
5.
Muhammadu Ɗanmafara Gidan Buwai
6.
Muhammadu Nasiru Acida
7.
Baba Garba Tsaumawa/Jangebe
8.
Abdu Bagobir, Kadagiwa/Wurno
9.
Muhammadu Wandon Ƙarfe Gidan Buwai
10. Mande Direba Acida
11. Ɗanladi Dogo Illela
Maroƙansa
1.
Abdu Wakili Huci/Gwadabawa
2.
Muhammad Ɗanmaraya Kalmalo/Illela
3.
Zakari Ya’u Darma/Illela
4.
Muhammadu Nakogo Gidan Buwai
Waɗannan mutanen Wazirin ‘Danba’u da Adamu Tozai su sheda min cewa duk inda
‘Danba’u yake yana tare da su. Kuma shi ne cinsu da shansu, da suturarsu da su
da iyalansu gaba ɗaya. Kuma daga cikinsu akwai masu mata biyu akwai masu mata
uku. Kuma shi ke yi musu kowace lalura.
Yanzu haka Wazirin ‘Danba’u ne halifan waƙa kuma duk yaransa da maroƙansa da
kayan kiɗansa duk da su yake amfani wurin gudanar da waƙoƙinsa kamar yadda
maigidansu ke yi. Yanzu haka suna nan suna waƙoƙinsu daga cikin waƙoƙin da
waziri ya yi akwai waƙar Aminu Waziri Gwamnan Jihar Sakkwato da Waƙar Madawakin
Daura Sanata Mustapha.
Waƙar Aminu Waziri
Amshi: Riƙa ƙwarai ka hi su sa’a,
Sabon gwabna ɗan waziri,
Aminu mai halin bajinta.
Jagora: Yara ku shirya za mu Sakkwato,
Yara: Don in iske Aminu gwamna.
Jagora: Yara ku kimtsa za mu Sakwkato,
Yar: Don in iske Aminu gwamna.
Amshi: Riƙa ƙwarai ka hi su sa’a,
Sabon gwabna ɗan Waziri,
Aminu mai halin bajinta.
Jagora: Mun san Allah ad da mulki,
Sannan shi ke ba da mulki,
Inda ya so zai ba da mulki,
Yau kai ne matawalle Sakkwato,
Kai ne gwamnan Sakkwato
Ɗauki halin da Aliyu ya yi.
Yara: Riƙe talakawanka da kyawo,
Ka riƙe amana ɗan waziri.
A cikin wani ɗan waƙar yake cewa:
Jagora: Ga gwamna da mataimaki nai,
Ga Ahmad Ali ga Aminu,
Akwai wani ɗan saƙo gare ni,
Kun san ‘Danba’u ya hurce,
To ku riƙe mu amana Allah,
In kun riƙe mu kun yi daidai,
In kun aje mu babu komai
Yara: Mu mun tsaya ga sarki Allah,
Mun san Allah shi ka baiwa.
Waƙar Madawakin Daura
Sanata Mustapha
Amshi: Maganin maza,
Yaro ba ya hwaɗa ka wargi,
Ɗan Abubakar,
Sanata Mustafa madawaki.
A wani ɗan waƙa yake cewa:
Jagora: Ka ga halinta duniya,
Wata rana a sha zuma,
Wata rana a sha maɗaci,
In yau anai da kai,
Wata ran ba a yi da kai.
Yara: Ai ta bi ɗa mutum,
Ba a ganai ba.
Amshi: Maganin maza,
Yaro ba ya hwaɗa ka wargi,
Ɗan Abubakar,
Sanata Mustafa Madawaki
Jagora: ‘Danba’u ya wuce,
Ga yaran da ya bari,
Baba riƙe mu amana.
Yara: Sanata Mustafa Maigidana.
Jagora: Ɗan Audu riƙe mu da ƙima,
Yara: Sanata Mustafa maigidana
Jagora: Ɗan Garba riƙe mu amana,
Yara: Sanata Mustafa maigidana.
Haka wazirin ‘Danba’u yake gudanar da waƙoƙinsa yana biyar zubi da tsarin waƙoƙin
‘Danba’u da kuma amfani da irin salailansa.
2.1.8 Nau’in Waƙoƙinsa
Alhaji
Musa ‘Danba’u ya shahara a fagen waƙa saboda haka ya zama hantsi leƙa gidan
kowa. Don haka yana da waƙoƙi iri-iri kamar haka:
1.
Waƙoƙin kokawa
2.
Waƙoƙin noma
3.
Waƙoƙin siyasa
4.
Waƙoƙin sarauta
5.
Waƙoƙin masu mulki
6.
Waƙoƙin sauran jama’a
7.
Waƙoƙin yekuwa/faɗakarwa/gargaɗi
Haka kuma duk wata waƙa da aka buƙata a yi, ‘Danba’u na yin ta.
2.1.9 Yawace-yawacensa
Shagari (2011) cewa ya yi, ya yi hira da ‘Danba’u inda yake cewa: “mawaƙin ya
tabbatamin cewa ba ya iyakance wurare da ya tafi amma nan gida Nijeriya babu
jihar da bai tafi ba. Haka kuma Nijar ma ya shige ta kamar Nijeriya. Wato babu
jihar da bai shiga ba a cikin jamhuriyar Nijar. Sana’arsa ta waƙa da kiɗa ita
ce ta kai shi jamhuriyar Nijar. Sannan kuma ya je Makka wajen aikinhajji da
Umra ba sau ɗaya ba.
Ni kuma hira da na yi da wazirin ‘Danba’u ya sheda min cewa, a Nijeriya jihar
Barno (Maiduguri) can ne kaɗai ba su je ba. Domin sukan je cin rani a shekara ƙasashen
kudu kamar Anaca da Benin da Okene da Wari da Legas da sauransu. A Nijar sun
zagayi ciki da wajenta sunje Difa da Agadas da Zandar da Maraɗi da Tawa da Doso
da Birni Bayero da Niamey da Tiliberi da sauransu.
2.1.10 Nasarorin da Ya
Samu a Cikin Waƙa
Waziri
‘Danba’u a hira da muka yi da shi ya sheda mini cewa duk wata nasara da ake
samu a rayuwa Ɗana’u ya samu a cikin waƙa domin a cikinta yake ci, cikinta yake
sha, a cikinta yake sutura, iyalansa da makaɗansa da maroƙansa da duk wani
wanda ke ci ƙarƙashinsa duk waƙa ce. Haka kuma a cikin waƙa ya yi gida, ya yi
wa yarana, motoci da kujerun Makka duk a dalilin waƙa ne.
Wazirin ‘Danba’u Shehu da Adamu Tozai sun sheda min cewa, ko ‘Danba’u bai iya
bayyana adadin motar da suka samu a dalilin waƙa wanda ya fara ba shi mota shi
ne Abu Zahara ƙaura lokacin jam’iyar NPN a shekara ta 1978. Sannan sanata Ila
Gada ya ba su Bus mai rubutun NPN, kuma ya samu mota ta ƙarshe bayan an bayyana
sakamakon zaɓen gwamna na 2015 inda aka bayyana Aminu Waziri ya lashe zaɓe, sai
gwamnan ya ba shi mota ƙirar honda mai suna Anaconda.
Wanda ya fara ba shi kujerar Makka shi ne sanata Ɗanmalam Ila a Legas. Amma
asalinsa ɗan jihar Kebbi ne. Haka kuma waziri Shehu ya faɗa min cewa ya samu
lambar girmamawa a wurare kamar haka:
1.
Rima Rediyo Sakkwato
2.
Ƙungiyar ‘Yanjarida ta Jihar Sakkwato
3.
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
Haka kuma shis ne Ambasadon mawaƙan Hausa na Nijeriya da Nijar.
2.1.11 Sha’awarsa
Alhaji
Musa ‘Danba’u mutum ne mai sha’awar wasanni. Hasali ma sha’awar wasanni shi ya
sa ya fara waƙar kokawa kuma yana sha’awar wasar ƙwallon ƙafa kusan duk wanda
ya san ‘Danba’u a Illela ya san yana sha’awar ƙwallon ƙafa musamman ta ƙasashen
Turawa domin yana cikin riƙaƙƙun masu goyon bayan ƙungiyar Barcelona ta ƙasar
Spain. Haka kuma yana sha’awar tafiye-tafiye. Ta ɓangaren abinci kuma ‘Danba’u
bai da kamar tuwon dawa da hurar gero.
2.1.12 Rasuwarsa
Kullu nafsin za’iƙatil mauti, duk mai rai mai ɗanɗana mutuwa ne. Allah ya yi wa
Alhaji Musa ‘Danba’u rasuwa ranar talata 7-4-2015, jim kaɗan bayan bayyana
sakamakon zaɓen 2015.
Babangida Kaka Dawa a cikin waƙarsa yana cewa:
Mutuwa mai yanke ƙauna,
Da duk kake son mutum,
Bai tsayawa in ta zaka.
Mutuwa mai ɗauke sheɗa,
Da duk kake ƙin mutum,
Ya mutu sai kai ka mutu.
Gindi: Murna mukai,
Ka yi sarkin Musulmi,
Muhammad Sa’adu,
Ya gadi halifan Bubakar.
Allah ya jiƙan Alhaji Musa ‘Danba’u amin.
2.2 Dangantakarsa Da
Sauran Mawaƙa
Alhaji Musa ‘Danba’u kamar yadda na tattauna da mutane sun sheda min da cewa
yana da kyakkyawar hulɗa tsakaninsa da sauran mawaƙa domin mutum ne da bai da
hasada kuma duk inda haƙen mawaƙi ya kai zai bi don amsar masa haƙinsa. Haka
kuma idan wani mutum ya yi wa wani mawaƙi alƙawali bai cika ba, ‘Danba’u yakan
bi wannan mutumin har sai ya karɓo wa mawaƙin alƙawalin. Shi ya sa mawaƙa ke
kiran sa Ambasadan mawaƙan Hausa Nijeriya da Nijar. Haka kuma sun faɗa min
cewa, yana kyautata wa mawaƙa har ta kai karnan makaɗan Nijeriya da Nijar da
sauran mawaƙa ke zuwa har gidan ‘Danba’u suna yi masa waƙa. Daga cikin mawaƙan
akwai:
1.
Sani karen makaɗa Gwadabawa
2.
Shehu karen makaɗa kurya
3.
Makaɗa Dauro da dai sauransu.
Akwai lokacin da mawaƙa suke ƙorafi cewa idan aka je taro da an gabatar da
‘Danba’u to ba za a sake gabatar da wani mawaƙi ba, ko kuma duk wanda aka
gabatar hikimar ‘Danba’u za ta dushe tashi ba a ganin ƙoƙarinsa. Da ‘Danba’u ya
ji haka duk inda aka je taro yakan ce a bar shi ƙarshe.
Game da kyautata wa mawaƙa ni kaina na sheda a lokacin da aka yi taron siyasa
lokacin da shugban ƙasa Obasanjo ya zo Sakkwato a filin sukuwa, da idona na ga
‘Danba’u yana wa Gambo mai waƙar ɓarayi karin kuɗi naira ɗari-ɗari.
2.3 Dangantakarsa da
Sauran Jama’a
Dole
makaɗi ya yi hulɗa da mutane musamman waɗanda yake shirya wa waƙa da kuma
masoya masu ra’ayin waƙoƙinsa. Kuma yana waƙoƙin siyasa yana zuwa kamfe kuma
yana hulɗa da saurakuna da masu mulki da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da sauran
jama’a daban-daban.
Wannan ya ba ni damar tattaunawa da wasu mutane da nake jin yana yawan ambaton
su a cikin waƙoƙinsa da kuma wasu waɗanda ya yi wa waƙa da kuma sauran mutane
da ke zaune wuri ɗaya da shi. Daga cikinsu akwai Alhaji Bala Musa Yabo da
Sardaunan Hamma’ali Malami Maigandi da Muhammadu Galadima Horo (Ɗan’ige Horo)
da Yusuf Bello Ɗancaɗi da Alhaji Audu na ƙofa (Sarkin baƙi) da Alhaji Hadi Ɗanmalam
da Musa Damo da Alhaji Sanusi Ɗanwali da Alhaji Mani Sardaunan Illela da wasu
daga cikin yaransa kamar waziri Shehu da Adamu Tozai da sauran mutane da dama.
Sun faɗa min cewa Alhaji Musa ‘Danba’u mutum ne mai kyakkyawar hulɗa tsakaninsa
da jama’a. Kuma mutum ne wanda ba shi da girman kai. Yana da yawan son wasa da
mutane manya da yara kuma yana girmama mutane manya da yara.
Wannan ni ma sheda ne domin mun haɗu da shi a gidan mai martaba Sarkin Musulmi
Muhammdu Macciɗo a ranar da aka yi naɗin sarautun sarkin yamma da sarkin Arewa
da Jarma da Katuka da Durumbun Sakkwato. Na je wurin ‘Danba’u muka gaisa kuma
ya karɓe ni hannu bibiyu.
2.4 Naɗewa
A taƙaice a cikin wannan babin an kawo bayanai kan taƙaitaccen tarihin makaɗin
da ake nazari a kansa watau Alhaji Musa ‘Danba’u tun daga haihuwarsa da
iliminsa da iyayensa da aurensa da matansa da ‘ya’yansa da yaransa makaɗa da
maroƙa da nasarorin da ya samu da nau’o’in waƙarsa da yawace-yawacensa da
abubuwan da yake sha’awa da dangantakarsa da ‘yan uwansa makaɗa da mawaƙa da
kuma sauran jama’a. Kai! Har rasuwarsa.
1 Comments
Allah gafartama musa dan ba'u da sauran al'ummar musulmi.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.