Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Sakkwato, NijeriyaNA
KUDU MUHAMMAD SALIHU
BABI NA BIYU
TAK’AITACCEN TARIHIN HULD’AR NUFAWA DA AL’UMMAR HAUSAWA
2.0 Shimfid’a
Babi na biyu, babi ne da zai nuna cikakken bitar aiki game da wad’anda za a yi magana ko bayani a kansu na abin da ya shafi tarihinsu da huld’arsu da wad’anda suka yi rayuwa na tsawon lokaci a ban k’asa kuma tarihinsu ya bazu ciki da waje, ba wasu bane face Hausawa da Nufawa.
Wad’annan al’umma kuwa, tarihinsu ya ke’banta da na sauran mutane da suke rayuwa a wad’annan yankuna guda biyu wato yankin k’asar Nufe da kuma na Hausa irin kayan tarihin da suka fara musamman idan muka tuno zuwa lokacin Turawa mulkin mallaka irin k’alubalantar da Turawa suka gani a gefen sarakuna wanda muka sami hasken lamarin a cikin littafin mani wato zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa a shafi na 48-50 yadda gwamna Lugga ya yi k’ok’arin shawo kan Sarki Abubakar kuma bai cimma manufa ba.
A tak’aice dai, wannan babi zai nuna mana tak’aitaccen tarihin k’abilun nan guda biyu Nufawa da Hausawa da muhallin zamansu da kuma yanayin zamantakewarsu da juna.
2.1 Tak’aitaccen Tarihin Hausawa
Jinju (1990) a littafinsa garkuwan Hausa da tafarkin ci gaba ya na cewa zaurancen ra’ayin Hausawa ne cewa babu wani harshe a duniya ban da Larabci wanda ya fi Hausa daraja ko dad’in ji ba shi ma Larabcin saboda addinin musulunci ne kawai. Ko da yake Turanci ya yi kaka gida a k’asar Hausa musamman birane wannan ra’ayin Hausawa bai sauya ba.
A farkon wannan k’arni (1903) ne Turawa suka zo wa Hausawa da harsunansu (Ingilishi a Nijeriya, Faransanci a Nijar), suka tilasta musu su koye su daga (1903) zuwa (1960).
A tsawon wannan lokaci Hausa ta zama marainiya marashiya gata. Mak’iyanta, Turawa da tsirarrun Afirkawa a zamanin mulkin mallaka suna yi mata dariya wai ba ta iya baza ilimin fasaha da kimiyya ba, amma a yau masu muguwar suka a da sun yi shiru sai dai k’ulle-k’ullen banza da makirci da ba za su fasa yi ba sai ran da dole ta zo musu kai-tsaye. Turawa sun shammaci Hausawa, amma duk da matsayin da harsunan ‘yan Ingilishi da Faransanci musamman daga k’arnonin tsakiya (Middle Ages) na Turai zuwa k’arni na (20).
Ba mu ta’ba samun shaidar cewa Hausa, kafin k’arni na (7), ta sami rubutu ba, amma mun san cewa sahabban Manzon Allah sun fito daga tsibirin Larabawa (Arabic Peninsula) sun bi ta Afirka ta Arewa sai Tumbutu. Lokacin da wad’ansu kamar su Ukba Ibn Nafi’i da jama’arsu, suka tunkaro zuwa gabas sun biyo t k’asar da yau ake k’ira Jamhuriyar Nijar a (666) inda suka soma yad’a addinin musulunci. Bayan k’arni na bakwai Abdulkarim Al-Maghil wanda ya rasu a 1504 ya ziyarci Nijar da Kano da Katsina yana ta yin wa’azi kuma yana ta karantar da ‘yan k’asa. A Katsina an yi waliyai biyu da ake girmamawa har kwanan gobe. Su ne Shehu D’an Marina (da Larabci Ibn Alsabbagh) wanda ya rasu a 1655 da D’an Masani wanda ainihin sunansa shi ne Muhammad Albarnawi.
Ya sake fad’a (Jinju) cewa musulunci ya shigo Nijeriya a k’arni na 14. Daga wannan lokacin su waliyyi D’an Marina aka sami tabbacin yin amfani da ajami saboda rubutattun wak’ok’in Hausa an fara samunsu daga wad’annan magabata ne. A kusan gaban kowanne gida, kafin zuwan mulkin mallaka, akwai makaranta. Wannan tsarin ilimi ya lalace sarai tun 1903, lokacin isowar Turawa k’asar Hausa. Hausa tana da kalmomi nata na asali wad’anda yawancinsu suna cikin masaranci, harshen su fir’auna. Ta kuma aro kalmomi da yawa daga wad’ansu harsunan Afirka ta yamma kamar sanwayanci da zabarmanci da barbarci da azbinanci da fulatanci da nufanci da kuma Yarbanci.
Birnin Tudu (2013: 25-26) tarihi ya nuna cewa, gabanin shigowar musulunci k’asar Hausa, Hausawa ba su san wani addini ba face na gargajiya. Addinin gargajiya shi ne tsafe-tsafe ta hanyar bautar iskoki da tsafin gari kamar su tsunburbura da Dodo da sauran abubuwan da ake bauta wa domin an yarda da cewa, suna iya ba da wani amfani ko suna iya cutarwa idan an sa’ba musu. Har bayan da addinin musulunci ya shigi k’asar Hausa, wasu daga cikin Hausawa, ba su daina tsafi ba. Kodayake bayyanar musulunci ya dushe su, musamman lokacin jihadin Shehu Usmanu ‘DANFODIYO. Daga cikin tsafe-tsafen akwai tsafin gari da na gida da na d’ai-d’ai kun mutane. Tsafin gari shi ne, wanda kowa ya yarda da shi kuma yana bauta masa kamar shan kabewa a kabi (can da) “wato al’adar tsafi da ake yi shekara-shekara” da bautar macijiya mai suna “sarki” a Daura, da tsafi mai Duro a kwatarkwashi, da tsumburburar Kano da makamantansu.
Ya sake cewa (Birnin Tudu), masana tarihi da al’adun Hausawa sun had’u a kan cewa ba Bayajidda ne asalin Hausawa. Don haka, suke k’iran hikayar Bayajidda da sunan “Tarihihin Bayajida”, a cewarsa, an ce Bayajida dai d’an Sarkin Bagadaza ne, (wato babban birnin Irak’i ta yanzu). Ya sami sa’bani da ubansa ya yo hijira zuwa Borno inda ya yada zango ya kuma auri d’iyar Sarkin Borno mai suna Waira Bagira. A wata riwayar ya auri d’iyar bawan Sarkin da yakan ziyarci k’asar Hausa, kamar dai yadda ya fito a littafan Muhammadu Bello da Abdul-K’adir B. Al-Mustafa masu sunaye “Infak’ Al-Maysur da Raudat Al-Afkar”. Bayan wannan ne ya isa Daura ya kuma samu nasar kashe wata macijiya da ke hana wa mutane d’iban ruwan rijiya. Wannan jarumtaka ta sa ya auri sarauniyar garin mai suna Daurama. Auren ya yi albarka domin an haifi d’a Bawo wanda shi haifi sarakunan k’asar Hausa na wancan lokaci.
Har ila yau ya na cewa (Birnin Tudu p.32), a halin yanzu k’asar Hausa ita ce ta mamaye jihar Kano da arewacin Jihar Kaduna da jihar Katsina da kuma wani d’an bangare na jihar Bauchi da kudancin jamhuriyar Nijar. A mik’e daga Arewa zuwa Kudu k’asar Hausa ta fara daga Azben har ya zuwa kasuwar Arewa maso gabas ta tsaunukan k’asar Jos. Daga nan ta kwaso ta yi yamma har zuwa wurin da kogin Kaduna ya yi wani babban doro. Daga nan kuma sai ta buga ta yi arewa maso yamma ta yi mahad’a da k’aton rafi na kogin kabi. Daga nan wurin sai ta karkata ta nufi arewa maso gabas har Azben. A tak’aice, k’asar Hausa tana cikin shiyarsu dan ta tsakiya kuma ta had’a da k’asar Sarkin Zazzau ta yanzu idan aka d’ebe kudancin Zazzau da k’asar Sarkin Kano da Katsina da ta Sarkin Musulmi da k’asar Sarkin Kabin Argungu da Sarkin Gwandu da Sarkin Daura da k’asar Had’ejiya. A cikin Jamhuriyar Nijar kuwa, k’asar Hausa ta fara tun daga Birnin Kanni, ta yi Arewa gaba da Agadas da nisa duk k’asar Hausa ce amma banda yamma ga gilinge da kuma Gabas ga Damagaram. Har wa yau ga garuruwan ko kuma k’asashen da k’asar Hausa ta yi iyaka da su: daga gabas ta yi iyaka da k’asar Borno, daga yamma kuwa da k’asar Dahomey (wanda yanzu ake k’ira Jamhuriyar Benin) daga arewa ga hamadar sahara daga kudu kuma ga k’asashen Nufe da kuma yankin Middle Belt.
2.2 Tak’aitaccen Tarihin Nufawa
Haske manihinci, al’ummar Nufawa al’ummu ne da suka yi rayuwa mai tsawo cikin shekaru aru-aru kuma tarihinsu ya na da yalwa matuk’a domin masana da marubuta daban-daban sun yi rubuce-rubuce a kansu kamar Isma’il (2002) da Elizabeth (1983) da Isah (2003) da Ndagi (2008) da wasunsu duk sun yi bayanai game da wad’annan al’umma na abin da ya shafi addininsu da yanayin gudanar da sarautunsu irin na gargajiya da dai makamantansu.
Isma’il (2002) cewa ya yi kalmar Nufe ya sami asali ne daga harshen “NUBIA” wanda asalin kalmar mawuyacin abu ne wajen ganewa. Amma kuma ana iya kallon kalma da cewa mutane da ke zaune a ga’bar kogin Neja da kogin Kaduna.
Harsuna daban-daban su kan k’ira wannan k’abila da suna dai-dai yadda ya dace da harshensu da suke magana da shi, wasu su kan ce ‘NEGEU’ wasu kuma ‘NUFFE’ a wasu wuraren kuma cewa kalmar ta samu asali ne a Larabci kuma kalmar ita ce ‘NEFIN’.
Malaman Larabci kamar Ibn Battuta da El-Idris ‘yan kasuwan Afirika ta arewa suna kallon kalmar ‘NUFE’ da ‘NUFFE’ da ‘NEFU’. Nufawa sun yi shahara a tsawon zamani da bin addini da son yin liyafa da himma wajen aiki ko sana’a tare da fasaha ko dabara har ma da tserewa cikin kasuwanci.
Kasancewar harshen Nufe gama-gari ne wajen furuci, akwai kuma kare-kare da ke tattare cikin harshen. Wad’annan k’are-k’aren sun ke’banta daga shiyya zuwa shiyya kuma suna da daidaito wajen aikin ibada da kuma ra’ayi iri d’aya. Amma kuma akwai zartarwar k’aurace-k’aurace da ta abku cikin harshen kuma ta na ci gaba da abkuwa tsakanin shiyyoyin ko kuma daga wannan shiyya zuwa wancan.
ELIZABETH EZIKIEL (1983) cewa ta yi:
“Tarihin Nufawa a asalce ya ta allak’a ne wajen bada haske game da al’adunsu domin kuwa, tushen jihohin da jaruman suka kafa daga waje na tsawon lokaci wajen tabbatar da hark’ok’in siyasa cikin kalamin da NADEL ya gabatar a kan Nufawa cikin shekara (1930) ta samu ne daga Etsu Patigi (Sarkin Fatigi) daga cikin jikokin TSOEDE na baya-bayan nan”.
Ya sake cewa (Ezekiel) tushen gwamnatin Nufawa ta k’unshi wasu k’ananan sarakunan Birni wad’anda ke tsakanin ga’bar kogin Neja da kogin Kaduna da kuma na Cibako da aka ke’be a wurare daban-daban suka amince da shugaba d’aya wanda ke da zama a wani gari mai suna Nku kusa da kogin Neja da kogin Kaduna, sai dai sarakunan sun yi mubayi’a ga sarakunan Igala.
Ya sake jaddada cewa an nad’a Yariman Nku a kujerar masarautar Igala (wato Tsoede kenan), wanda a k’arshe ya sake komawa k’asarsu inda ya gaji kujeran sarauta. Duk da girman Tsoede an tura shi garin Idah a maimakon bayi. Ubansa ya yi hakan ne ganin irin jarumta da ya ke da shi da Attah (wato Sarkin Igala), da ya ga tsufa ta yi masa tsiya, sai ya mayar da Tsoede k’asar Nufe tare da yi masa kyautar wasu abubuwan sarauta kamar su jan k’arfe da jiragen ruwa da kakaki da ganguna irin su tambari har ma da k’arfen sihiri da makamantansu.
Haka zalika, Tsoede ya shirya nan take ya d’au farmaki zuwa ga wad’annan k’abilu Yagba, da Bunu, da Kakanda, da Kambari da kuma Kamuku. Ka’ana ya mayar da babban jiharsa Nupeko kusa da garin Nku ya kuma kafa d’ayan masarauta a garin Gbara da ke ga’ban kogin Kaduna. Haka kuma ya kafa musu sana’o’in hannu iri-iri kamar su mak’eran bak’in k’arfe da na farin k’arfe da masu k’era jiragen ruwa (wato masassak’a) har ma da sadaukar da ran ‘yan adam.
Masana tarihi irin su C.R Ni’ben da S.E Nadel sun tabbatar da cewa, akwai matsaloli guda biyu da ke tattare ga hikayar da aka zayyana a kan rayuwar Tsoede na abin da ya shafi shekarun da ya yi sarauta d kuma yak’e-yak’en da ya yi.
Wannan lamarin kuwa (Mascon) ya yi bayanin cewa yak’ininsa a kan daidaiton tarihin Tsoede inda ya ce a cewar marubucin nan wato (Obayemi) cewa:
“Madogaran hikayar Tsoede wata alama ce ta tarayya mai tabbatar da shakke game a game da lamarin”.
Awwal (2003:25) cewa ya yi Tsoede shi ne asalin Nufawa inda ya bayyana shekarun haihuwarsa cikin shekara (1463 A.D) a cikin shekara (1493-1523 A.D) kuma aka yi cinikin bayi zuwa Idah. Daga shekara (1531-1591 A.D) ne ya kafa daular masarautar Nufe inda shi ne Sarki a wannan lokaci a garin Nupeko.
Bayan rasuwar Tsoede, sai aka nad’a sabon sarki mai suna Sha’aba (Etsu Sha’aba) cikin shekara (1591-1600), sarki na gaba shi ne Zu’bunla (Etsu Zu’bunla) a shekara (1600-1625), bayan wannan sarki, sai Jiegbo (Etsu Jiegbo), ya yi sarauta cikin shekara (1625-1670) daga nan sai Mamman Wari (Etsu Mamman Wari) shi ma ya yi sarauta cikin shekara (1670-1679), bayan rasuwar Mamman Wari aka mayar da masarautar zuwa (Zhima) inda Abdulwaliyi (Etsu Abdulwaliyi) da ya d’au ragamar sarautar a cikin shekara (1679-1700), sai kuma Aliyu (Etsu Aliyu) a shekara (1700-1709), bayan wannan shekara sai kuma ga namace (Etsu ganamace) a cikin shekara (1710-1713) bayan wannan sarki sai kuma Ibrahim (Etsu Ibrahim) a shekara (1713-1717) sai kuma sarki Idrisu (Etsu Idrisu) a shekara (1717-1721) daga shi sai Abubakar Kolo Tankari (Etsu Kolo Tankari) wanda ya yi sarauta a shekara (1742-1746), sai kuma Jibrilu (Etsu Jibrilu) a shekara (1746-1759), marub in ya bayyana cewa an tsige wannan sarki daga kujerarsa aka kuma mayar da shi kutigi har ranar mutuwarsa a shekara (1759), sai kuma aka nad’a Mu’azu (Etsu Mu’azu) a kwana a tashi sarkin ya ‘bace ya koma Yawuri da zama duk da hakan ya faru a cikin shekara (1759-1767) inda kuma aka nad’a Majiya (Etsu Majiya) wanda ya yi mulkinsa a shekara (1767-1777) daga nan sai Iliyasu ya hau kujerar sarauta a shekara (1777-1778) wato bayan shekara d’aya aka nemi Iliyasu aka rasa, nan ne kuma aka nad’a Mu’azu (Etsu Mu’azu) II (1773-1795), nan ne Malam Dendo wanda Nufawa suka yi wa lak’abi da (Manko) ya shigo k’asar Nufe da tutar jihadin Shehu Usmanu ‘DANFODIYO. Dendo ya sami wannan lak’abin ne saboda iliminsa. Manko kuwa na nufin babban malami. Haka kuma Dendo ya samo asali ne da wasu kalmomin Nufe inda ake nuni da ‘MAN DAN YANDONDO’ ma’ana malamin da ya zo da tarkace wad’anda suka had’a da Buzu, da Gora da Buta da makamantansu. Wannan ya faru ne a shekara (1773-1795), bayan haka sai kuma Mamma (Etsu Mamma) wanda ya yi sarauta a masarautar Rabo wato reshe ne cikin masarautar Nufe a shekara (1796-1805) daga nan kuma sai Majiya II (Etsu Majiya) inda yak’i ya ‘barke tsakanin shi da Jimada (Etsu Jimada) da ke masarautar Jima wanda ya yi sanadiyar mutuwar Jimada a wani wuri mai suna Jengi (Ragada) a shekara (1796-1805) shi kuwa Majiya II ya sake d’au farmaki da Fulani a can k’asar Ilori inda aka yi gidan jiya da sojojin Nufe a shekara (1806-1810), a cikin wannan yak’i, Fulani sun sami goyon bayan Idrisu d’an Jimada (Etsu Jimada) suka sami galaba a kan Majiya inda suka amshi masarautar Raba Majiya ya gudu zuwa Zugum (Zugurma).
Daga nan kuma aka rantsar da Idrisu (Etsu Idrisu) yana kan sarautar a Adama Lellu kusa da Egga.
Ya sake cewa (Awwal p. 27) Idrisu yisa (Etsu Idrisu) yana kan sarautar a Adama Lellu tsakanin shekara (1810-1813), wanda kuma aka kashe shi a cikin shekarar (1830). Kwatsam Dendo ya tuna da Majiya, sai aka d’auko shi daga Zugurma aka rantsar da shi kuma ya yi sarautar cikin wata hud’u.
Wad’annan sune sarakunan Nufawa da suka yi mulki gabanin zuwan sarakunan Fulani, haka kuma mun sami haske a cikin littafin (Awwal p. 21) cewa Al-Ilori da Ajayi sun yi bayani cewa kafin zuwan Fulani, Nufawa suna addini kuma akwai masu yad’a addinin nan kamar su Abdulrahman Bajichi da Sulaiman da sauransu.
Ya jaddada da cewa (Awwal), bayan shud’ewar Dendo, sai aka kafa daular masarautar Bida a k’ark’ashin sarakunan Fulani inda Usman Zaki ya zamo Sarki na farko bayan rasuwarsa sai kuma Umaru Majigi bayan wucewar Majigi sai kuma Sarki Abubakar Masaba inda a lokacin ne tarihi ya nuna cewa Turawa suka shigo Nijeriya ta Arewa inda aka nemi Sarki Abubakar ya zo su shirya cikin aminci a wuri mai suna Egbaji shi Sarkin kuma yak’i zuwa.
Mani (1956:48-50) ya sake ba da haske cewa, a farkon karon sai da Turawa suka nad’a wani sabon sarki a sabilin had’in kai da ba su samu da Sarki Abubakar ba. Sunan wannan sarki kuwa shi ne Muhammadu Maku Kai, hasali ma dai a cikin shekara 1900, kusan a ce sarakuna guda biyu ne a Bida. D’ayan shi ne Sarki Abubakar d’ayan sarkin kuma Muhammadu Maku wanda Turawa suka nad’a.
Ana cikin wannan hali, sai Gwamna Lugga ya sake aikawa Sarki Abubakar da takarda ya ce masa, ya dai yi k’ok’ari ya zo ya same shi dab da kogin Kaduna kuma kada sarki ya ji tsoron komai shi Gwamna Lugga kuma ya yi masa alk’awarin cewa ba abin da za a yi masa inda ya tabbatar masa da cewa lallai zai zo lafiya ya kuma koma gida lafiya.
A wannan karon ma, sarki Abubakar yak’i zuwa sai dai Muhammadu Maku da ‘yan rakiyarsa suka amsa k’ira suka je wajen Gwamna Lugga daga nan, Turawa suka d’aura aniyar zuwa Bida suka shaidawa jama’a muddin dai ba ta’ba su ba, babu fad’a kuma duk mutumin da ya ga don ganinsu ya yi haramar gudu, za su d’auke shi tamkar mak’iyinsu. Har ma Gwamna Lugga ya aikawa sarki kuma da cewa, ko da ma Muhammadu Maku ne suka d’auka tamkar sarki, amma duk da haka, idan sarki Abubakar zai yarda su had’a ido da shi ko da a Bida ne, ya yi masa alk’awari ba zai wulak’anta ba, kuma zai sa ya yi zamansa cikin jin dad’i har abada. Duk dai a banza, sai sarkin ya gudu ya tasamma wajen Lapai fitar-kutsu sarki ya yi, daga shi sai fadawa kamar shida ya fita daga Bida. Aka yi irin abin nan wuji-wuji ina gabas, ake karkashe manyan sarakunansa aka yi wa wad’ansu rauni aka kama na kamawa. Wad’anda aka kama bayan sun wartsake sarai sai aka sake su.
Mani (p. 49) ya jaddada da cewa, sojoji suka duru cikin garin Bida suka jera suna maci, suna ta rera wak’a har suka isa k’ofar gidan Muhammadu Maku. A nan suka yi irin tsayuwar nan tasu, wadda suke tsayawa gaba d’aya karaf-karaf suka yi da’ira a nan ne Gwamna Lugga ya nad’a Muhammadu Maku shi zama sarkin Nufe a Bida. Jama’a masu yawan gaske suka taru sai Gwamna Lugga ya sa aka yi shela, don jama’a su ji irin k’a’idojin da aka nad’a musu sabon sarki a kai. Bayan Lugga ya mik’a wa Makun takardar tabbatar da shi sarautar sarki, sai ya cewa Muhammadu Makun ya rik’e mutanensa da adalci, sannan kuma ya bi duk abin da ya ke cikin odojin da yankin k’asa ta Nijeriya ta Arewa ta yarda da su. Ya kuma yi biyayya a shugaban Turawan mulki, ya kuma rik’a yarda da shawarwari masu amfani da Razdan zai rik’a ba shi. Kuma duk irin ma’adanai da za a samu a cikin k’asar da sauran wurare wad’anda babu kowa a kansu, duk na hukuma ne.
Bayan gamawa da karon nan na Bida, inda aka nad’a Muhammadu Makun sarkin Bida, sai Gwamna Lugga ya sake rubuta wata takarda ya za’bi mutum takwas ya aike su zuwa wajen sarkin Musulmi a Sakkwato, a cikin takardar, Gwamna Lugga ya bai wa sarkin Musulmi labarin irin abin da ya aikata ya kuma nemi sarkin Musulmi da ya aiko wanda za a nad’a a Kwantagora, sannan kuma ya bada dalilin da ya sa wancan sarkin ya fito daga sarautan. Dalili kuwa shi ne, idan aka bar sarkin Kwantagora da na Bida, to ba za a sami ragowar kowa ba saboda yawan yak’e-yak’ensu na kamun bayi da rushe-rushen garuruwan da suka yi.
2.3 Tarihin Huld’ar Hausawa da Nufawa
Tarihin huld’ar wannan al’ummun guda biyu wato Hausawa da Nufawa, ana ganin ta fara ne tun wajen k’arni na sha hud’u (14 century).
Muhdi (1978:49-50), tarihi ya nuna cewa a k’arni na sha hud’u zamanin sarkin Katsina Muhammadu Korau ne Nufawa suka fara samun huld’a lokacin da yak’i ya ‘barke tsakanin wasu sassa na Nufawa da Katsinawa a wajen shekara (1320) dai-dai inda k’asar Nufe ya yi iyaka da masarautar Katsina. A lokacin ne Hausawan Katsina suka fara sassauyawar abubuwan amfani da Nufawa a wajen rafin da ta raba masarautar. Sannu a hankali cikin k’arni na sha biyar ne wannan wannan huld’a ta samu kar’buwa sosai da sosai. A cikin wannan lokaci ne kuma aka nuna cewa, sarkin Kano na wancan lokaci; wato Sarkin Kano Yakubu kenan wanda ya yi rayuwa a wajen shekara (1452 zuwa 1463) ya aikawa sarkin Nufe na wancan lokaci da dawakai guda goma (10) don ya saya. Alanda kuma a cewarsa, babbar masarautar Nufe yana wani gari mai suna ‘Nupeko’. Bayan shekara d’ari kuma, sarkin Kabi Muhammadu Kanta ya d’ullawa masarautar Nufe tare da had’in gwuiwar Sarauniya Amina ta Zazzau inda ya shaida da cewa, a cikin tsakiyar k’arni na sha shida bayan mutuwar Muhammadu Kanta a shekara (1561) ne kayayyakin amfani suke ta shigowa k’asar Hausa daga k’asar Nufe. Bayan ya nuna cewa Sarauniya Amina ta koma Zazzau wato masarautarta da dubban kwandunan goro da wasu abubuwan amfani. Saboda haka, huld’ar Hausawa na Nufawa ya k’ara jaddada sosai inda kowannensu basu jin tsoron abkuwar wani abu har ma suke yad’a da cewa, wanda ya je bid’ar neman wani abu, zai tarar da su can.
Ya k’ara da cewa (Mahdi 1978), rafin da ya yi iyaka tsakanin Katsina da k’asar Nufe an yi masa lak’abi da ‘Rafin Wanke Tsiya’. Da zarar Hausawa suka k’etare rafin zuwa k’asar Nufe, sukan dawo ne da arzik’i masu yawa, da jin haka, wasu daga cikin Larabawa suka shirya fatakensu domin su yi ziyarar huld’a na kasuwanci da al’ummar Nufawa wanda a k’arshen k’arni na sha takwas ne ya faru kuma su kan haura Katsina da Zariya sai kuma k’asar Nufe. Masanin wannan tarihi bai bayyana wad’annan abubuwan da suke fitowa daga k’asar Nufe zuwa Hausa ba, sai dai wad’anda ke fitowa daga k’asar Hausa zuwa na Nufe wad’anda suka had’a da dawakai da gishiri da ledoji da zannuwa da takardu har ma da abubuwan amfani iri daban-daban wad’anda ake kwasowa ta hanyar masarautar Yawuri.
2.4 Mazaunin Al’ummar Nufawa
Marubuta da manazarta daban-daban sun yi rubuce-rubuce masu d’imbin yawa a kan ina ne mazaunin Nufawa? Tabbas a hak’ik’anin gaskiya, akwai amincewar marubuta da yawa inda suka ce Nufawa suna da mazauni ne a jihohi da suka had’a da jihar Neja da jihar Kwara da jihar Kogi har ma da wasu sassan jihar Kaduna.
Bayan doguwar tafiya a cikin tsawon lokaci, an yi wannan al’umma ta bak’in marubuta kamar su S.F Nadel cewa sun yi k’aura ne daga k’asar Egypt (wato wurin zaman wannan al’umma kenan na asali), suka bazu cikin Nijeriya musamman a jihohin nan da aka ambata a sama. Akwai kuma harsashen masana da marubuta kamar su J.E.G Sutton da Sultan Bello da H.R Palmer da C.R Ni’ben da Leo-frobenius da W.K.R Hallam da J.D Fage da wasunsu da yawa duk sun amince cewa yawancin k’abilun Nijeriya kamar Hausa da Yoruba da makamantansu sun samo asali ne daga k’asashen Nufe a cikin littafinnan mai suna “Nupe the Origin”. Haka kuma Leo-Africanus ya jaddada da cewa, kimanin shekaru dubu d’aya (1000) da suka wuce, duk harsunan da ake amfani da su a k’asar Hausa sun sami asali ne daga harshen Nufe a k’ark’ashin gara.
Awwal a littafinsa cewa, a shekaru aru-aru da suka wuce, an yi sarakuna masu yawa tun kafin jaddada addinin musulunci da Shehu Usmanu ‘DANFODIYO ya jagoranta tare da wasu muk’arrabensa. Wad’annan sarakunan Nufawa kamar su Tsoede, da Majiya da Aliyu Kolo Tankari da makamantansu, sun yi zama ne a garuruwan Nku da Gbara da Lelu da Jima (Zhima) da Zugurma da makamantansu.
Masana tarihi irin su na Nadel da wasu, suna cewa, Tsoede jarumi cikin sarakunan Nufawa wanda kuma hakan yasa ake kallonsa tamkar asalin Nufawa saboda jarumtarsa. Daga cikin wuraren da za a samu Nufawa har wa yau sun had’a da Lafiyagi da Tsaragi, da Patigi da Idah da Bida da Lapai da Agaie da Mokwa da Kutigi da Enagi da Kacha da Lemu da makamantansu da yawa.
Ta la’akari da wad’annan al’umma, tarihi ya nuna da cewa tun lokacin da suka bar k’asarsu na asali (wato Egypt), ba su da wani wuri da za a iya cewa nan ne mazauninsu da din-din-din kuma inda tushen karkasuwarsu yake da suka wuce wad’annan jihohin Kaduna da Kogi ba, sai a jihar Neja da kuma jihar Kwara wad’anda suke cikin Arewa ta tsakiya.
2.5 Nad’ewa
Wannan babi, ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da shimfid’a da tarihin al’ummar Hausawa da na Nufawa da kuma tarihin huld’arsu har ma da mazauninsu wato inda za a iya samun wannan al’umma a wannan k’asa ta Nijeriya daga k’arshe kuma muka nad’e wannan babi.
https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.