Ticker

Gurbin Magani A Mahangar Karin Magana


Wannan muk’alar, an   gina ta ne da k’udurin duba gurbin magani a mahangar karin maganar Hausa. Magani a nan kan iya kasancewa domin kawar da ciwo ko cuta a jiki, ko zuciya, ko sinadarin had’in magani...

_____________________________________________
Daga
Dr. Abdullahi Sarkin Gulbi
Phone: 08089949294
Department of Nigerian Language
Usmanu ‘Danfodiyo University, Sokoto
 _____________________________________________

1.0 Gabatarwa

Wannan muk’alar, an   gina ta ne da k’udurin duba gurbin magani a mahangar karin maganar Hausa. Magani a nan kan iya kasancewa domin kawar da ciwo ko cuta a jiki, ko zuciya, ko sinadarin had’in magani, ko warkarwa, ko  jingar magani, ko kuma wata mafita daga wata matsalar rayuwa ta yau da kullum. Kafin a duk’ufa wajen walwawre zare da abawar takardar, zai kyautu mu hango ma’anar magani da karin maganar daga bakin masana da manazarta.

2.0  Ma’anar Magani


A duk lokacin da rayuwa ta fuskanci matsalar rashin lafiya ko wata damuwa da kan k’ange ta ga jin dad’i da samun sakewa wajen aiwatar da al’amurranta na yau da kullum a cikin annashawa, to abu na farko da zai fad’o a rai shi ne, fafafitukar neman sauk’i da mafita watau ta hanyar “magani” ke nan. Dangane da haka ne,  nake ganin cewa magani shi ne:

Duk wata hanya da za a yi amfani da ita domin

riga-kafin cuta, ko rage rad’ad’inta, ko ma a kawar

da ita gaba d’aya, ko warwale wata matsalar rayuwa.

Galibi, Bokaye da Malaman tsibbu, da wasu  da

suka yi fice a sana’o’in garagjiya, da kuma wasu

mutane na musamman suke bayarwa.

Wannan hanyar, tana iya kasancewa ta

kimiyyar zamani, ko kuma a gargajiyance

(watau hanyar tsafi da tsibbace-tsibbacen al’umma).[1]

3.0  Ma’anar Karin Magana

Karin magana gajeruwar jimla ce mai d’auke da ma’ana mai fad’in gaske idan aka yi fashin bak’insu.[2] Duk da haka, ina ganin karin magana  a matsayin wani zance ne da akan shirya cikin hikima da nak’altar harshe wanda kan zo da sigar tak’aita zance da ke k’unshe da hoton rayuwar al’umma ta gaba d’aya.

4.0  Karin Maganar Magani

Wad’annan karin maganganu ne da suke magana kacokan dangane da magani idan an yi nazarin k’unshiyar ma’anarsu.Wannan dalili ne ya sa aka kira su da suna “Karin maganar magani”. Kowane daga cikin wannan rukunin karin magana aka d’auka za a tarar da cewa yana magana ne a kan magani a Bahaushiyar al’ada.

Daga cikin irin wad’annan karin maganganu kuwa sun had’a da;

  1. Ba don ka na sha ba.

  2. Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa.


iii. Dabara na ga mai hawan kura, walau takunkumi ko lak’ani.

  1. Don bak’ar rana ake bak’ar tambaya.

  2. Hannu banza ba ya d’aukar wuta, in ba da magani ba da sharifta.

  3. Idan ka ci maganin k’arfe, ka ci na k’arfi?


vii. Idan kura na da maganin zawo, da ta yi wa kanta.

viii. In ka raina dagumi ka ga k’uk’umi.

  1. Kowa bi daren banza, ya sha kashin banza.

  2. Kowa ce babu magani garai a babu.

  3. Rubutu ba ya maganin yunwa, sai dai a warke cuta.


Wad’annan karin maganganu da aka kira “Karin maganar magani” babu shakka sun amsa sunansu. Dalili kuwa shi ne, idan aka d’auki kowane d’aya daga cikinsu aka aza shi a faifan nazari za a tarar da cewa babu wani abu da suke magana face “Magani”. Wannan ne ya tilasta samar masu gurbin zama a cikin rabe-raben karin maganar Hausa. Misali,

  1. Hannu banza ba ya d’aukar wuta, in ba magani da sharift

Wannan zance yana fayyace muna al’adar Bahaushe ta amfani da maganin  wuta, wanda galibi mak’era da sharifai suka shahara da yi a tsakanin al’ummar Hausawa. Domin  ba yadda za a yi mutum ya d’auki wuta a hannunsa, ko ya yi wasa da ita, idan bai ci maganin wutar ba. Su dai mak’era kamar yadda aka sani mutane ne da suke tu’ammali da wuta a wajen aiwatar da sana’arsu ta k’ira, su kuwa sharifai mutane ne da ke ikirarin cewa suna da maganin wuta, ko kuma a ce wuta ba ta k’ona su, kuma wannan ne dalilin da ya sa suke bayar da maganin wuta idan ta k’ona mutum. Mak’era sukan yi wasan wuta a lokacin bukukuwan al’ada musamman idan ana bukin suna, ko na aure domin nuna martabar sana’arsu.

  1. Ba don ka na sha ba


Akan ji mutane suna wannan karin magana domin su nuna irin yadda suka k’oshi da magani a jikinsu. Musamman idan an yi wani artabu ko karakkiya da abokan gaba.Wannan zance yana nuna irin yadda al’adar Bahaushe  take ta shan magungunan kare kai, don kauce wa ‘bacin rana. Yadda za a iya fahintar hakan shi ne, idan mutum ya had’u da farmakin ‘yan fashi suka da’ba masa wuk’a(yuk’a), ko wani makami, sai makamin ya darje ba tare da ya fasa shi ba, jikinsa zai d’auki rawa tare da nuna bajinta a wasu lokuta yakan ce “Ba don ka na sha ba.” Ma’ana ya sha maganin ne saboda irin wannan ranar. Mafarauta da ‘yan tauri su ne suka yi fice da fad’in irin wannan karin magana, domin da ma sukan sha maganin ne domin nuna bajinta a wurin farauta da kuma wasan tauri.      

iii. In ka raina dagumi ka ga k’uk’umi

Dagumi dai wani nau’in magani ne da Hausawa kan yi amfani da shi ta hanyar d’aurawa a hannu, ko k’afa, ko ma a kwankwaso domin shirya wa ‘bacin rana. Saboda haka, Bahaushe ke kallon cewa duk wanda ya raina dabarar yin amfani da dagumi, ko laya, ko d’amara wajen kariyar kai da kaya daga had’uwa da ‘bacin rana, to lallai wata safiya zai had’u da wulak’anci da k’uncin rayuwa daga mak’iya na mutane, da Iskoki, da  k’wari, da kuma dabbobi.

  1. Idan ka ci maganin k’arfe , ka ci na k’arfi?


Wannan zance yana tattare da bayanin d’abi’ar Bahaushe na cin maganin tauri(k’arfe), ma’ana idan har aka gwada mutum da wani makami na k’arfe, ba a fasa shi ba, musamman idan ana wani artabu, to akan gwada k’arfin tuwo a ga wanda zai yi nasara. Misali idan maza suka had’u a wajen farauta, ko wasan tauri, ko kuma farmakin ‘yan fashi a kan tituna da gidaje. Sau da yawa akan ji labarin had’uwar ‘yan fashi da wasu mutanen da maganin k’arfe ya kama.’Yan fashi kan yi amfani da dabarar k’arfin tuwo don su rinjayi mutumen da ya so ya kawo masu barazanar maganin tauri. Wannan karin maganar yana nuna muna amfanin cin magani k’arfe.

Don mu k’ara tabbatar da da’awarmu ta samar wa karin maganar magani gurbin zama a cikin karin maganar Hausa, sai mu dubi wannan karin magana mai taken:

Magani a sha ka ba don yunwa ba

Wannan karin maganar ya tabbatar muna da cewa ba domin yunwa ake shan magani ba, sai domin a kawar , ko a yi kariya, ko kwantar da rad’ad’in wata cuta da ke addabar jikin mutum ko dabba, domin kawo jin dad’i ga zuciya da sauk’ak’e duk wata wahala da damuwar da cutar ta haddasa.Wannan bayanin ya yi daidai da ra’ayin Ahmad(1984)[3] a fahintarsa game da magani.

3.2.2  Karin Maganar Sinadarin Had’in Magani


A k’ark’ashin wannan rukunin kuwa, za a yi tsokaci ne dangane da irin karin maganar da ke zance a kan sinadiran had’in magani a Bahaushiyar al’ada, wad’anda ake ji a bakunan mutane daban-daban a cikin zantukansu na yau da kullum. Kad’an daga cikin ire-iren wad’annan karin maganganu sun had’a da;

  1. Da tsohon zuma ake magani.

  2. Da tsohuwar zuma ake magani.


iii. Da haka ake yi a ce ba a so, an sa wa majinyaci zuma a magani.

  1. Karen da ya yi cizo da gashinsa ake magani.


A nan, idan an lura za a ga cewa karuruwan magana na d’aya zuwa na uku, suna fayyace muna muhimmancin zuma ne wajen had’a magani. Inda a karin magana na hud’u  yake bayyana muna irin yadda ake amfani da sassan jiki na dabbar da ta cutar wajen maganin cuta.

Misali,

Da tsohuwar zuma ake magani

Wannan karin magana yana nuna muna cewa zuma wani sinadari ne na had’a magungunan Bahaushe na cututtuka da dama da ke addabar jiki kamar yadda  al’adarsa da addininsa suka tabbatar. Kuma ba lallai sai tsohuwar zuma ce kad’ai ake amfani da ita ba wajen magani ba. Sabuwar ma, ana amfani da ita wajen had’a wasu magunguna. Misali akan nemi sabuwar zuma idan aka haifi yaro ko yarinya a saka masu tsokar nama a cikin zuman, sai a sanya masu a cikin baki suna tsutsa na tsawon kwanakki, kafin a fara ba su nonon mahaifiya (uwa). Wannan al’adar akan yi ta ne tun kafin a fahinci muhimmancin bayar da nonon uwa da zarar an haifi jinjiri. A al’adun wasu Hausawan kuwa, maimakon tsokar naman, sukan yi amfani da cibiyar da aka yanke wa yaron ne, a d’ebi wani sashe na cibiyar a saka cikin ruwan zuma a ba jinjirin ko jinjira suna tsutsa kafin a  fara basu nono.[4] Domin dad’a fitowa da muhimmancin zuma wajen kiwon lafiya Kibiya(babu shekara) ya ce: “Likitocin zamani sun yi kira da cewa ya kamata mutane su lizinci yin amfani da zuma a kodayaushe. Ba wai sai ba su da lafiya ba.Yin hakan zai hana su kamuwa da cuce-cucen da ke addabar mutane.” [5]

Karen da ya yi cizo da gashinsa ake magani.

Daga cikin tsarin magani da warkarwar Bahaushe akwai magungunan da akan had’a da wani sashe na halittun mutane da dabbobi. A irin wannan nau’in mahad’in magani ne ake amfani da wani sashe na jikin karen (musamman mahaukacin kare) da ya yi cizo domin a samu waraka daga cutar da yake iya haddasawa. Daga cikin abubuwan da ake amfani da su a matsayin mahad’in maganin kuwa akwai gashin jikinsa ko antarsa ko harshensa da sauransu.

Misalan da aka bayar a k’ark’ashin wannan rukuni sun isa su zamar muna wata hujja ko madogara da cewa akwai wasu karin maganganu da ke bayyana sinadaran had’in magani.Wannan ne ya tilasta yi wa irin wad’annan karin maganganu gurbin zama a cikin karin maganar Hausa a cikin wannan bincike.

3.2.3  Karin Maganar Mafitar Al’amari


A cikin wannan fasalin kuwa, za a yi nazarin wasu daga cikin karin maganar magani ne da suke fayyace muna samun wata mafita daga wani al’amari. Al’amarin kuwa kan kasance na wata cuta ne ko kuwa wasu buk’atun zuciya na musamman. Daga cikin karin maganganun da suka dace da wannan rukunin kuwa sun had’a da;

Aure maganin talauci

Araha maganin mai wayo

Babban zane maganin wawan zama

Babbar gona maganin awon bad’i

Bincike maganin kuskure

Gida biyu maganin gobara

Gangar baka maganin hasarar fata

Dukiya maganin k’ask’anci

Ganwo maganin kaya

Hak’uri maganin zaman duniya

Hadarin k’asa, maganin mai kabido

Haske maganin duhu

Haukan ba ni, maganin ta  ungo

Haihuwa da yawa maganin annoba

Hank’uri maganin zaman duniya

Harsashe maganinka a kwanta

Haihuwa maganin wulak’ancin duniya

Hannu da yawa maganin mai k’wange

Idan so cuta ne hak’uri magani ne

Jarabta maganin mak’aryaci

Kaya da yawa maganin ‘barawo

Karen bana, ke maganin zomon bana

Kira da hannu maganin mai nisa

Kira da hannu maganin mak’uyaci

Kud’i maganin talauci

Kud’i maganin tsufa ne

Maganar ciki maganin mai tsegumi

Maganin so aure, maganin k’iyayya rabuwa

Maganin kunama hak’uri

Maganin annoba sadaka

Maganin mantuwa waiwaya

Maganin bawa sanda

Maganin mak’i gudu ban kashi

Maganin tsoro barci

Maganin mace mijinta

Maganin zaman duniya, hak’uri

Maganin zaman lahira, tsoron Allah

Maganin wahala hak’uri

Maganin ka da a ji, ka da a fad’i

Masani maganin mak’aryaci

Maganin gari da nisa tafiya

Maganar ciki maganin mai kwarmato

Nisan rai maganin annoba

Ruwan dad’i maganin k’ishirwa

Rana tsaka maganin sanyi/d’ari

Sana’a goma, maganin kwanan rana

Suruki maganin kumallo

So mai son ka, maganin k’iyayya rabuwa

Sabo da manya maganin wata rana

Zuwa da kai maganin mak’aryaci .

Karin maganganun da ke a k’ark’ashin wannan rukunin idan an yi nazarin su, za a ga cewa karin maganganu ne da suke k’ok’arin samar da mafita ga al’amurran rayuwa daban-daban. Inda a wasu lokuta akan d’auko wasu abubuwa guda biyu wad’anda a kishiyoyin juna a zo  da su a cikin karin magana d’aya domin su samar da mafita ko magance wata matsala kai tsaye.

Misali;

Haihuwa da yawa maganin annoba

Annoba dai wata musiba ce da Allah (SWA) kan saukar wa mutane da dabbobi da sauransu. Rayukan mutane da dabbobi kan salwanta a dalilin yad’uwar cutar. Musamman a lokacin da ake cikin tsananin cutar da yad’uwarta. Bahaushe kuwa yake kallon wannan matsalar da cewa ba ta da wani magani illa wanda  Allah ya bai wa ‘ya’ya da yawa. Ma’ana wanda duk yake da yawan ‘ya’ya, to ko da wasu sun mutu,wasu za su rayu.Yawan ‘ya’yan ya magance ‘banar cutar.

Bari mu d’auko wani misali mai kama da wannan domin mu dad’a tabbatar da gaskiyar hasashenmu, misali;

Araha maganin mai wayo

Bahaushe yana da imanin a kan cewa ba sai abin da ake sha ko shafawa a jiki kad’ai ne magani ba, watau kalmar magani kan yi shige da fice a cikin zantukansa na yau da kullum. A wannan zance ana son a nuna cewa wayo idan ya yi wa mutum yawa, to zai zamar masa wata cuta a zuciya, kuma wannan kan haifar masa da zubar daraja da k’ima a idon jama’a, ganin cewa duk wata huld’a aka k’ulla da shi, to sai ya nuna wayo a ciki. Babbar hanyar warkar da wannan cutar ga irin wad’annan mutane musamman idan abu ya shafi hanyar saye da sayarwa, ita ce hanyar araha. Mutum mai wayo ba yakan so ya ‘batar da k’ud’i ba, to, amma idan ya ga wani abu mai araha, za a ga yana rawar jiki wajen sayen abin nan, ke nan araha ta yi maganin mak’wadancinsa.[6]

Gungurin turmi maganin mahaukaci

Wannan ya fito muna da hoton dabarun warkar da hauka a k’asar Hausa. Abin da aka saba gani ne cewa idan lalurar ta’bin hankali ya sami mutum, mataki na farko da za a fara d’auka a gargajiyance shi ne a d’aure(tsare) shi  a cikin d’aki na d’an lokaci ko hankalinsa zai dawo, idan ya sami sauk’i sai a sake shi, idan kuma bai sami sauk’i ba, akan d’aure sa da mari ko wani gungurin turmi ko ice, domin a k’ange sa daga samun walwalar da zai iya tafiya mai nisa ya bar bagiren da ake kula da shi. Saboda haka gungurin turmin ya yi maganin mahaukacin na rashin samun sakewa na aikata duk wani abu da yake son ya aikata na rashin hankali da kuma barin muhallin da ake yi masa magani, ko kula da shi.

Dukkan wad’annan karin maganganu da aka zo da su a wannan rukuni suna fayyace muna cewa karin maganganu ne masu nuna wata mafita ga al’amurra daban-daban kamar yadda aka gani a misalan da suka gabata.

3.2.4 Karin Maganar Allah Magani


A k’ark’ashin wannan rukunin kuwa, za a yi bayani ne dangane da wasu daga cikin sababbin karin maganar Hausa da aka samu bayan da addinin Musulunci ya yi tasirin gaske ga rayuwar Bahaushe. Domin an ce “Idan kid’a ya canja, rawa ma sai ta canja,”mutane na k’ago karin maganganu sababbi da suka dace da zamani. Daga cikin irin wad’annan karin maganganu akwai abin da wannan bincike ya yi wa lak’abi da “Karin maganar Allah magani.” Wad’anda suke bayani a kan cewa Allah(SWA) Shi ne maganin kowane irin al’amari a doron k’asa[7]. Kad’an daga cikin wad’annan rukunin karin maganganu sun had’a da;

Abin da Allah bai ba ka ba ko ka yi magani aikin banza ne

Bala’i maganinka rok’on Allah

Allah maganin komai

Allah maganin mai bore

Allah maganin munafuki da azuzi, idan bai mutu ba ya lalace

Gobara daga kogi maganin ta Allah

Hauka maganin ta Allah Sarki

Komi ya yi zafi maganin sa Allah

Maganin musifa Allah

Idan aka dubi wad’annan karin maganganun da aka tsara a sama, aka kuma yi masu kallon  nazari, za a ga cewa mak’asudin gina su ya ta’allak’a ne ga imani da cewa Allah (SWA) shi ne maganin kowace  irin matsala. Misali;

 Allah maganin komai

Wannan karin magana yana d’aya daga cikin karin maganar da aka samu bayan da Bahaushe ya sadu da addinin Musulunci. Ganin cewa zantukan hikima irin karin magana kan sauya a dalilin sauyawar zamani.[8] Dangane da haka, Bahaushe ya gano cewa duk wani abu da ke a doron k’asa, to lallai mallakar Allah (SWA) ne watau a halicce, da mulkance, da kuma bautance. Ta haka ne ya gano cewa duk wata musifa ta ciwo, da fatara, da fari, da yunwa, da dangoginsu,  Allah ne ke kawo sauk’i da mafita ga d’an Adam. Kuma hakan ya k’ara tabbatar muna da cewa Bahaushe tuni ya yi imani da Allah wajen magance matsalolinsa na yau da kullum.


Bala’i Maganinka Rok’on Allah

A cikin wannan zance kuwa, ana bayyana muna al’adar Bahaushe ta imani da cewa duk wata musifa ta sami mutum, to lallai babu wani magani da ya fi ga mutum face ya nace ga rok’on Allah ta hanyar addu’a domin samun ku’buta daga cikin wannan hali.Wannan ya yi daidai da fad’ar Manzon Allah (SAW)inda ya yi umurni da cewa addu’a ita ce takobin mumuni a kowane irin yanayi ya sami kansa.

A tak’aice wad’annan karin maganganu sun tabbatar muna da cewa karin maganar “Allah magani” yana d’aya daga cikin karin maganar Hausa da ke buk’atar samar wa da gurbi a cikin rabe-raben karin maganar Hausa kamar yadda wannan takarda ta tabbatar.

3.3   Karin Maganar Warkarwa


A k’ark’ashin wannan fasalin kuwa, za a yi nazarin karin magana ne mai alak’a da warkarwa, watau ko dai ya kasance an sami ‘bir’bishin waraka, ko a sami wata mafita ga samar da waraka a cikin zancen, ko kuma zancen ya kasance yana tattare da manufar waraka daga cuta.

Daga cikin ire-iren wad’annan karin maganganun kuwa sun had’a da;

Abincin wani gubar wani

An sha kanwa k’warnafi ya kwanta.

Ciwo ba mutuwa ba

Ciwon da kare ya yi shi ya warke, idan akuya ta yi shi sai yanka

Cituwar wani,warkewar wani

Hoho ba ta  warke ciwo, sai dai ta sa sanyin rai

In ka ga ana shan magani ana samun sauk’i, akwai sauran kwana gaba

Kurciya hauka ce, warkewar ta girma

Magani a sha ba don yunwa ba sai don a warke cuta

Rubutun sha ba ya maganin yunwa, sai dai ya warke cuta

Idan aka kalli wad’annan karin maganganu da idon basira, za a ga cewa dukkansu suna bayani ne a kan samar da waraka dangane da wasu matsalolin rayuwa iri daban-daban,wanda hakan ya sa aka kira su karin maganar warkarwa, saboda samun ‘bir’bishin waraka a cikinsu.

Misali,

      Ciwo ba mutuwa ba

Wannan zance yana magana ne a kan waraka , watau duk yadda ciwo ya yi tsanani a jikin mutum, idan dai har ba shi ne tafarkin barinsa a duniya ba, to lallai zai warke ya sami lafiya kamar ma bai yi fama da rashin lafiyar ba.Wannan al’amari haka yake, domin an danganta wannan zance ga wanda ya yi fama da matsanancin rashin lafiya, ya kwashe shekaru kwance har aka d’ebe zaton ya rayu, daga baya kuma ya warke ya sami lafiya, idan wani ya gan sa, sai ya ce “Kai lallai  ciwo ba mutuwa ba,” dubi wane ya warke, kamar ba shi ne sai an kwantar, sai an tayar ba”. A tak’aice  karin maganar ciwo ba mutuwa ba yana  d’aya daga cikin karin maganar waraka da ke nufin duk yadda ciwo ya yi tsanani, akan murmure a wasu lokuta.

K’urciya hauka ce, warkewar ta girma

K’urciya wani mataki ne na rayuwa wanda ya fara daga haihuwa zuwa a balaga,a wannan tsakanin ne ake rayuwar k’urciya, watau an wuce jinjiri ba a kai shekarun balaga ba.[9] Saboda haka wannan mataki, mataki ne mai had’arin gaske ga yaro da ma mahaifansa da mak’wabtansu gaba d’aya, domin irin yanayin haukar k’urciyar da yake a ciki. Maganin wannan hauka shi ne girma,ma’ana yaro ya kai mizanin balaga, inda zai iya rarrabe abu mai kyau da marar kyau.

Hoho ba ta warke ciwo, sai dai ta sa sanyin rai

Wasu kan ce sannu ba ta warke ciwo, a nan an fito muna da al’adar Bahaushe ta tausayi ga maras lafiya, ko idan wani ya sami rauni a jiki, irin dad’ad’un kalamai da ake yi wa maras lafiya su ne ake nufi a nan, da kuma rawar da suke takawa wajen samar da waraka. Bahaushe yana hangen cewa kalaman ne ke warkar da ciwon, domin sukan sanya masa wani sanyi ga rayuwa da rage  zogi da rad’ad’in cutar,da kuma kwantar masa da hankali, da k’ara sa rai ga samun sauk’i. Rawar da wad’annan kalamai ke takawa wajen dabarun warkarwa ba k’aramin muhimmanci suke haifarwa ba ta amfani da shawarwari domin samar da waraka ga maras lafiya wanda a Turance ake kira Psycho-therapy.[10]

 Idan aka d’auki kowane daga cikin wad’annan karin maganganu aka yi nazarinsa, za a ga cewa ba komai suke magana ba face lamarin warkarwa.Wanda hakan ya sa wannan bincike ya yi masu gurbin zama daga cikin rabe-raben karin maganar Hausa.

3.4  Jingar Magani


Sha’anin warkarwa a Bahaushiyar al’ada ba abu ne da aka bari kara zube ba. Akwai  tanade-tanaden da ake yi na biyan jingar magani da galibi masu hidimar bayar da magani kan shata kafin su bayar da maganin(jingar sa hannu), Misali ga abin da wani mawak’i ya fad’a a cikin wak’arsa lokacin da wata mata ta je neman magani ga wani boka:

                   Ki ba ni farin rago biyar,

                   Turmin alawayyo guda biyar,

                   Ki ba ni kud’inki sule d’ari,

                   Kin ga yanzu zan maki magani. [11]

Kuma  sukan shata abin da za a ba su bayan an ga amfanin maganin ta fuskar samun biyan buk’ata, ma’ana idan an warke(jingar magani).Wannan ne ya sanya lamarin ya bayyana a cikin karin maganganun Hausawa, kuma nake ganin ya kamata  a yi masu gurbin zama daga cikin karin maganar Hausa.

Wasu daga cikin masu bayar da magani sukan umurci majinyaci ko mabuk’aci da ya kawo kud’i, ko jinsin wasu dabbobi kamar  farar kaza,ko bak’ar kaza,ko wake-wake, ko k’uzugu, ko bak’ar akuya, ko bunsuru, ko rago, ko farin goro, ko goro k’war uku, ko kurman goro, da makamantansu, a matsayin jingar magani. [12] Misali wasu masu bayar da magani sukan buk’aci a kawo masu farar kaza da sukan had’a gashinta da garin ganyen biye rana a turara su wajen had’a maganin farin jinin ‘yan mata.Saboda haka, a wannan muhallin za a yi nazarin irin wad’annan zantukan hikima na Bahaushe domin tabbatar da hasashen nazarin. Daga cikin irin wad’annan karin maganganu kuwa sun had’a da;

Abun majinyaci na mai magani ne

Da wuyar sha magani da kud’i

Don ciwona, na saye bokana

Kayan majinyaci, duk na mai magani ne

Kayan mai cuta,  duk na mai magani ne

Kud’in marar lafiya, na mai magani ne

Kare da kud’i, sai ya sha rubutu

Magani da kud’i, akwai wuyar sha

Ranar tsafi bunsuru ke tsada    

Misali,

Abun majinyaci, na mai magani ne

Abin fahinta a  cikin wannan zance shi ne, duk wani abu na dukiya da marar lafiya ko mabuk’aci ya mallaka, bai wuce ya bayar da shi ba ga mai bayar da magani ba. Ganin irin muhimmancin da sha’anin warkarwa yake da shi ga wanda Allah Ya d’ora wa wata rashin lafiya, ko shiga wani hali na buk’atuwa da son samun wani abu da ya yi wa zuciyarsa shamaki.Wannan ya fito muna da hoton jingar magani da ke akwai a tsakanin masu neman magani da masu hidimar warkarwa a cikin al’umma.   

Hakan ya yi daidai da fad’ar wani da ke cewa:

Kayan mai cuta, na mai magani ne

Kud’in marar lafiya, na mai magani ne [13]

Wani misalin kuwa shi ne a cikin karin magana mai taken:  

Da wuyar sha, magani da kud’i

A nan, ana bayyana muna cewa akwai irin cutar da magungunan da Bahaushe ke bayarwa a cikin sauk’i da ‘yan kud’i kad’an  a matsayin jingar magani, akwai wad’anda ake kar’bar jinga mai tsoka. Musamman idan lalurar mai nauyi ce.

A bisa wannan dalili ne Bahaushe ke hangen cewa duk wani magani da ke da tsada wajen samar da shi ko sayensa, mai k’aramin k’arfi ba zai iya saye ba, ko amfani da shi ba.Wannan ya sa ake yi wa abin fassarar magani da kud’i, akwai wuyar sha.Watau magani ba dad’i, neman kud’i ba dad’i. Misali labarin cin dak’uwar Buza. Buzu ne ya shigo kasuwa sai aka ba shi dak’uwa ya ci ya ji dad’i. Shi ke nan wata rana sai ya ga ana sayar da tukar sha, sai ya saya ya ci, yana sanya ta a bakinsa sai kumfa ta fara fito masa a baki, sai ya ce “a dai ci kada kud’i su ‘baci.” Sai dai abin kula a nan shi ne ai dak’uwar tamkar magani take gare shi.

Ga wani misali mu gwada shi mu gani;

 Don ciwona, na saye bokana

A wannan zance, ana k’ok’arin fayyace muna al’adar Bahaushe ta neman warkarwa ta hanyar bokaye a kan wasu matsalolin da kan iya tasowa  na rashin lafiya da biyan buk’atar zuciya. Kazalika neman buk’ata ga boka ba banza ne ba,domin sai an yi jingar abin da za a ba shi kafin ya shiga aikinsa na warkarwa,wa imam a fara ba shi na sa hannu,ko kuma bayan buk’ata ta biya a biya shi.Mallakar boka da wasu mutane ke yi wajen jagorancin tafiyar da lamurransu na yau da kullum shi ake nufi da sayen boka a cikin zancen. Ga irin wad’annan mutane,duk wani abu da za su k’ulla a duniyar nan sai sun sa boka gaba,idan ya ce ka da su yi, ba za su yi ba.A kowace harka suna jiran umurninsa ne kawai.

Mu dubi wannan misalin da ke k’asa, mu ga yadda karin maganar jingar magani ke k’ara bayyana a cikin zancen mutane.

Kare da kud’i, sai ya sha rubutu

Rubutu dai wani nau’in magani ne da ake amfani da shi a k’asar Hausa,ta hanyar rubuta ayoyin Al-k’ur’ani da wasu harrufan Larabci a jikin allo da ake wankewa. Akan bai wa mutane domin su sha ko su yi wanka da zimmar samar da waraka daga cuta ko wata biyan buk’atar zuciya.

Galibi wad’anda suka shahara ga shan irin wannan rubutu, su ne manyan mutane kamar sarakuna, da malamai da alk’alai domin neman dauwama a cikin sha’anin mulki, da kuma almajirai da mata a bisa wasu dalilai mabambanta. Dangane da haka ne, Bahaushe yake ganin cewa baya ga jama’ar da aka lisafta a sama, to komai k’ank’ancin mutum a cikin al’umma, yakan iya amfani ko shan rubutu, muddin dai yana da kud’insa na biyan jingar maganin.

Wani misali mai jan hankali shi ne inda ake cewa:

  Ranar tsafi, bunsuru ke tsada

Hausawa kan ce tsafi gaskiyar mai shi, ashe ke nan lamarin tsafi wani babban kaso ne na addinin gargajiyar Bahaushe. A al’adar tsafin Hausawa kamar sauran al’ummun duniya irin su Indiyawa, da Girkawa, da Misrawa da sauransu, sukan aiwatar da ‘yan yanke-yanke na dabbobi k’anana da manya domin samun biyan buk’atunsu na magani. Buk’atar magani wani ginshik’i ne babba ga Bamaguje da ke samar da dangantaka a tsakaninsa da abin bautarsa. Maguzawa dai ba wani abu suke bauta wa ba illa Iskoki. Su wad’annan Iskokin ake neman biyan buk’atunsu na magani ta hanyar shugaban tsafi. Galibi akan yi ‘yan yanke-yanke a zubar wa tsafin jini don samun yardarsa ya biya buk’atarsu ta magani(Sarkin Sudan 2008:20).[14]  A irin wannan hali ne akan ji cewa jagoran tsafin ya umurci jama’a da  su yanka dabba iri kaza domin samun biyan buk’ata ko waraka daga wata cuta a matsayin jinga ko biyayya ga tsafin. Kasancewar wannan ibadar ta zama jiki a cikin al’ummar ya haifar da wannan karin maganar “Ranar tsafi bunsuru ke tsada.” A lokacin da addinin Musulunci ya yi tasiri ga rayuwar Bahaushe, sai wannan karin magana ya sauya zuwa “ranar Sallah rago ke tsada”

In Allah ya k’i addu’ar mai sakiya, sai k’urji ya fashe da kansa    

Sakiya ita ce huda k’urjin da ya d’uri ruwa, musamman kurkunu ko wani ciwo, da kibiyar da aka sa a wuta ta yi ja don a sami kafar da ruwan k’urjin zai fita.[15]A al’adar Bahaushe sakiya na d’aya daga cikin dabarun warkar da cutar da ta shafi ciwon daji da kan fito a hannu, ko k’afa, ko a kai, ko a fuska da sauran sassan jiki. Idan an yi sakiya ruwan da k’urjin ya ajiye za su sami  kafar fita daga cikin k’urjin, daga nan sai a sami sauk’in  fitinar ciwon. Galibi akwai wasu rukunin mutane  musamman mak’era da suka shahara da gudanar da irin wannan sana’ar ta sakiya, wanda yake su fatar su a kowane lokaci su sami masu irin wannan lalura domin su sami abin masarufi idan an sallame su. Idan Allah bai amshi du’a’insu ba kuwa, sai k’urjin ya fashe da kansa ba tare da  an tunkare su ba.

Idan an nazarci wad’annan rukunin karin maganganu, za a tarar da cewa dukkansu suna bayani ne a kan jingar magani.Wannan ne babban dalilin da ya sa aka samar masu da nasu kaso daga cikin karin maganar Hausa.

3.6   Nad’ewa


A tak’aice takardar ta yi tsokaci tare da yin nazari a kan magani, da warkarwa a gurabun karin maganar Hausa. An soma fayyace ma’anar karin magana daga bakin masana da manazarta adabi da al’ada. An kuma yi  nasarar gano  karin maganar da ke da ‘bir’bishin magani a cikin kunshiyar ma’anarsu. Inda aka nazarci yadda kalmar magani kan yi shige da fice a gurabun karin magana. Kazalika an dubi yadda lamarin warkarwa ke bayyana a cikin karin maganar tare da yin sharhi a kan sa. Daga bisani, binciken ya tsamo karin magana mai zance a kan jingar magani.

Manazarta

Post a Comment

0 Comments