Wakar Kudi Ta Gambo Hawaja

    Sauraro Da Rubutawa

    Shu’aibu Murtala Abdullahi

    Mu koma jawabin kudi tara dangi
    Akwai gargadi masu neman kudi,

    Ina ‘yan uwanna ku zo ga jawabi,
    Muna yin wa’azi ga neman kudi.


    A yau ba hari ba samame da yaki,
    A yau babu sauran batu sai kudi.
     
    Ku sa hankuri ki kawai ku fahimta,
    A yau zan gaya muku ranar kudi.

    Zama da duhun kai yana damuwarmu,
    Mu bar yin sa yau gara neman kudi.

    Gama wajibi ne kudi a bide su,
    Musulmi da arne mu nemo kudi.
     
    Ku zo gargadi zan yi duk mai fahimta,
    Idan dai ya gane ya nemo kudi.
     
    Jama’a mu daure, mu cije, mu jure,
    Mu tayar wa aiki da neman kudi.
     
    A je Ikko kar mu sake, don fatauci,
    Mu je har Junaina mu nemo kudi.
     
    A dimanci jaki da jirgi da mota,
    Kaza rakumi mui ta neman kudi.
     
    Mu sa musu kaya mu hau su mu kora,
    Mu keta dawa mui ta neman kudi.
     
    A jirgi mu sami abinci mu kumshe,
    Su ba mu ticket don su kar’be kudi.
     
    Mu zauna kujera mu kinkintsa kaya,
    Mu dunga kula don ‘barayin kudi.
     
    Idan za mu sauka tasha sai mu shirya,
    Mu daure tufafi da kayan kudi.
     
    Mu bar ribibin nan na jirgi ya fada,
    Saboda da ‘barayi mayanka kudi.
     
    Ka lura da bai dan dako sai ka bi shi,
    Idan kai sake babu kayan kudi.
     
    Ka sauka ka nemi wuri mai mutunci,
    Gama ba sakewa a neman kudi.

     
    Idan kai sake, sakiya sai ta hauka,
    Su bar ka da kuwwa sun dauke kudi.
     
    Idan kuwa a mota ka zauna a benci,
    Da kayammu ba ya na neman kudi.
     
    Direba, “I” ja mu sannu don kar ta kwace,
    Mu tai tafiya mui ta neman kudi.
     
    Ku bar son a zauna a talbodi mota,
    Gama lafiya ta fi taron kudi.
     
    Fatauci, giya, caca, neman kilaki,
    A bar yinsu in dai ana son kudi.
     
    Idan ko akan rakumi ne amale,
    Ku gyara cukurfai na neman kudi.
     
    A kai rakumi gun dawa ya yi kiwo,
    A kamo shi kan za a neman kudi.
     
    A sa mai akala a ce, “Ish” ya duka,
    A sa tarkace don fataucin kudi.
     
    A bar son a lauta amali ya kasa,
    Ga babu kyawo manema kudi.
     
    Idan kau a jaki kake yin fatauci,
    Ka sai aura ka jaba mai judi.
     
    Ka sai mangala wanga aikata taiki,
    Ka nemo tayakai na neman kudi.
     
    Ka sai akumari abin lauta taki,
    A gyara shi don lauta kayan kudi.
     
    Ka nemo kwari da baka har da mashi,
    Akwai ‘yam fashi masu kwata kudi.
     
    A je nan kwana tashi a zarce,
    Da dari da ra’ba a neman kudi.
     
    Ka je wani dajin ka kwan a ciyawa,
    Ka kwan babu barci a neman kudi.
     
    Ka je gun tayi sai a zage ka malam,
    Ba za kai fushi ba a neman kudi.
     
    Gama mai bida ba a son yai husuma,
    Ida ya yi sai yai asarar kudi.
     
    Idan kai fada ba kudi ka ci dauri,
    Kamar ya yi satar akwatin kudi.
     
    Ina mai fatauci da zamba da rinto,
    A bar yin su in dai ana son kudi.
     
    Ka bar ‘bata kai don fura bando rinto,
    Idan ka yi sai kai asarar kudi.
     
    Kudi in da dadi mutunci da dadi,
    A bar ‘bata ‘yanci manema kudi.
     
    Kdi na sani ba a samun kamassu,
    Samari mu daure mu nemo kudi.
     
    Gama lafiya dai da rai sun fi komai,
    Akan ba da su don a samo kudi.
     
    Idan kai musu sai ka dubo ‘barawo,
    Dare zai bi don ya sato kudi.
     
    Akan aje mashi dalilin ‘barawo,
    Yakan je a soke shi domin kudi.
     
    Ilori su ce “Olie,” Hausa, “‘barawo,”
    Fulani su ce, “Gujju” kayan kudi.
     
    Kasar Larabawa da “Sarrak” na san shi,
    Sukan yanke hannun ‘barawon kudi.
     
    Da ingalilo, gatari har da mashi,
    Ana yin su domin ‘barawon kudi.
     
    Ana daure mugu da jifa da sowa,
    A faffasa kayin ‘barawon kudi.
     
    Wadansu a harba su fada a rami,
    Suna kan shiga don su sato kudi.
     
    Ku bar ma ta wannan ku zo ga misali,
    Da zam ba ku domin sharar kudi.
     
    Ku dubo akan soja masu yaki,
    Suna sai da rayinsu domin kudi.
     
    Ana kashe wasssu, dubu su lahanta,
    Ana kan shiga don a samo kudi.
     
    Ku sai ya da a daji jama’a,
    Kudi “cede belde” mu nemo kudi.
     
    Fulani mutan Yola – cede belde,
    Jede hirma har sula neman kudi.
     
    Ku ji kuguna wuri dadi jama’a,
    Abin burge yaro da mata kudi.
     
    Maras lafiya na ta nishi a daki,
    Da ka girgiza sai ya dubo kudi.
     
    Idan ban da rayi kudi ya fi komai,
    Abokin zaman lafiya rai kudi.
     
    Abincin da duk ka sani yau a duniya,
    Kana so shi ka gan shi in kai kudi.
     
    Fatauci yakan karya karfin talauci,
    A yau babu damar zama ba kudi.
     
    Akan bar iyaye, abokai da dangi,
    A je wani lardi a nemo kudi.
     
    Akan bar iyali da mata da ‘ya’ya,
    A watsar a ruga a nemo kudi.
     
    Wasu a neman su samo su dawo,
    Wadansu su watse a neman kudi.
     
    Wadansu ko ba kudi ba mutunci,
    Da dama akan ‘badda su don kudi.
     
    A zo babu karfin jki ba mutunci,
    A je babu ilmi, a zo ba kudi.
     
    A je babu tsuntsu, a zan babu tarko,
    Ta’ala ka fisshe mu sharrin kudi.
     
    Kudi za mu neme shi Allah ka ba mu,
    Ka sa kar mu ta’be a neman kudi.
     
    Ku bar gajiya ga batu dan kalilan,
    Ina son ishara a neman kudi.
     
    Kamar da ubanka ina yin sarauta,
    Idan babu shi ba ka hanayr kudi.
     
    Kana duba bawanka ba ka ikon,
    Ka ce masa kala idan ba kudi.
     
    Idan ba ka komai kan yi talauci,
    Da kai gara bawan da ya san kudi.
     
    Idan shi ya samo kudi shi fa bawan,
    Ya ce dan ya ji sai ya je don kudi.
     
    Ya aike shi tilas ya je ba shi ikon,
    Ya ce ya ki in dai yana son kudi.
     
    Diya sai su bauta wa bawansu dole,
    Idan sun ga bawansu ya san kudi.
     
    Idan kai kudi babu sauran lalura,
    Gama zamani ne na neman kudi.
     
    Idan kai kudi mai kasa sai I so ka,
    Ka je shawara fada domin kudi. 

    Ka je fada manyan gidan sai su tashi,
    Ku gana da sarki a dadin kudi.
     
    Abin da I dame ka duk sai ka buda,
    Tsakaninku sai kai da shi don kudi.
     
    Ka shisshirya zancenka ko kwai da babu,
    A kar’ba a zauna a kai don kudi.
     
    Idan ka yi zancenka sarki ya dauka,
    Bare di’o gwamna mutanen kudi.
     
    Idan mai kudi yai fada babu shaida,
    Da shedunsa ‘fefa’, takardar kudi.
     
    Shi kumsa, shi kai fada in anka gane,
    Ba a ta da tadin ba domin kudi.
     

    Idan ba ka komai ina za ku gana,

    Da sarki bare di’o mai son kudi.

     

    Da ka doshi kofar akwai masu gadi,

    Bafade ya turo ka don ba kudi.

     

    Idan ka ga sarki akwai dan  dalili,

    Idan ba fada, ka yi satar kudi.

     

    Dalilinsa shi ne isa za ku gana,

    Da sarka a hannun ‘bayaryin kudi.

     

    Irin wagga ba ma bukatar ganinsa,

    Ta’ala ka fisshe mu satar kudi.

     

    Kudi kan na ce zan fa dura in kunsa,

    Gari sai ya waye ga zancen kudi.

     

    Mu tashi mu bar gyangyadi mui ta niyya,

    Mu zage damtsu mu nemo kudi.

     

    Kudi shi ya kan sa a saba da aren,

    Musulmi akan ki shi im ba kudi.

     

    Akan tashi malam a zaunad da arne,

    Idan an ga arnen da halin kudi.

     

    Idan malami ya yi zance a murda,

    A gaskata kasge a dadin kudi.

     

    A bai jahili gun zama mai mutunci,

    A zaunad da malam a kar don kudi.

     

    Kudi shi ya kan hana ilmi hakikan,

    Mu zan Ingilshi na neman kudi.

     

    Kudi shi ya kan sa zumunta ta watse,

    Ana kashe juna a neman kudi.

     

    Kudi shi yakan sa a watsad da dangi,

    A kore diya masu ‘barnar kudi.

     

    Rashin mai yawa sai ya ‘bata ibada,

    Yana tauye ilmi idan ba kudi.

     

    Tilawa izu arba’in sai ta rushe,

    Ta dawo bakwai ko biyar don kudi.

     

    Idan kun ga gardi yana yin sikola,

    Jimawa kadan za shi neman kudi.

     

    Kudi ya riga ya ciyo zuciyarmu,

    Ana bin ta gangar jiki don kudi.

     

    A neme shi, amma idan anka samu,

    A bar yin butulci manema kudi.

     

    Idan anka samu a bar ratse hanya,

    Mu kare da hairan idan mun kudi.

     

    Ashe shi kudi ba shi gimsar jama’a,

    Ka ce ya isan ba ka neman kudi.

     

    Ku dubo kudin Larabawa jamu’a,

    Ku dubo ga U.A.C. sun san kudi.

     

    Da mota da jirgi da bubur na aiki,

    Da dayyar na jirgi na neman kudi.

     

    A kan ahu sisin kwabo in ka dauka,

    Sukan daure yaronsu domin kudi.

     

    Idan da kudi na isan ‘yan jamu’a,

    Kano Alhasan ba shi neman kudi.

     

    Na-Goda, Na-Malam a Jos sai su zauna,

    Su ce ya isan, ba su neman kudi.

     

    Idan nai kure malamaina ku gyara,

    Wa almaji Gamba mai son kudi.

     

    Da zai yi baiti dari shidda,

    Da sittin da shidda na wakar kudi.

     

    Ku ji ni ku bar jin wuta jui kawaita,

    Batun malamin masu neman kudi.

     

    Ku bar tsuguno, zaune za kui ku huta,

    Da sauran kirari ga zancen kudi.

     

    Kudi dai ana sonsa ba mu kadai ba,

    Musulmi da arne ana son kudi.

     

    Kudi ya fi kowa masoya a duniya,

    Gama ga ishara masoya kudi.

     

    Kwara, Larabawa, Bature, Bahaushe,

    A yau ko Majusu suna son kudi.

     

    Da mata, mazansu, da ‘ya’ya da bawa,

    Tsaya ko na turu yana son kudi.

     

    Masuki, kaza kuturu duk da gurgu,

    Makaho, laifi yana son kudi.

     

    Da malam da almajiri du da gardi,

    Da kotso, da kuri suna son kudi.

     

    Mutum ya ki salla da zakka da hajji,

    Da tauhidi amma yana son kudi.

     

    Da arna da matansu sun huda le’be,

    Mazan ga kororo suna son kudi.

     

    Da sarki kaza hakimai dagatansu,

    Tsaya ko bafada ina son kudi.

     

    Sarauta da kanta idan babu samu,

    Ina kwarjinin nata kan ba kudi?

     

    Abin tsere tsara a yau ba ya cede,

    Ina wanda ba ya bukatar kudi?

     

    Tsaya zan yi zance da Fulfulde malam,

    Mu shaida wa ‘yan Ful’be ranar kudi.

     

    Da da liyari da cede,

    Wuri da cambe sunansa babba kudi.

     

    Da sisi, sulalla, aninai da fefa,

    Abin yai yawa na takaice: kudi.

     

    Kudi kurdabi na kudi ‘boye muni,

    Ka dandana dadinsu zaki kudi.

     

    Da dadi da tabshi da kamshi da zaki,

    Da haske da rayin da yas san kudi.

     

    Idan kai kamar alade don kazamta,

    Ba sa gane munin ba in kai kudi.

     

    Idan ka yi kaushi kamar na dabino,

    Ba sa gane kircim ba in kai kudi.

     

    Miyangu idan yai kudi sai a bi shi,

    A ce masa malam na dadin kudi.

     

    A ce masa gafarta malam ya amsa,

    Ina dan dalili? Dalili kudi.

     

    Ya dubo Musulmi ya ce masa arne,

    A ce haka ne mai gida, don kudi.

     

    Idan kai kamar Larabawa a kyawo,

    Ba sa gane kyawon ba in ba kudi.

     

    Ka zauna, su ce tashi, tilas ka tashi,

    Kazami ya zuna a dadin kudi.

     

    Idan ba su, komai farinka da kyawonka,

    Da kai gara kunkuru mai kudi.

     

    Idan kai kudi, dole kowa I so ka,

    Ana bin ka in sun ga ka san kudi.

     

    Idan ko kudi yai karancin gareka,

    Su wa za su zo gunka in ba kudi?

     

    Ka bai wa diyarka miji sai ta ki shi,

    Ta ce ta ki tadinka im ba kudi.

     

    Idan ko ka dame ta zagi da duka,

    Ta ce za ta karuwa neman kudi.

     

    Ta je can a rude ta ko babu ahu,

    A dibganta ciyyo a domomin kudi.

     

    Idan danka ya girma ya kai misali,

    Ya je can ya bauta wa wasu kudi.

     

    Ka kamo ka kawo, ya kwace ya ruga,

    Ina za ku zauna da shi ba kudi.

     

    Idan ko ka daure sarauta ta kwace,

    Su ce bar shi zai je I nemo kudi.

     

    Ka yayo diyan ‘yan uwa in ya data,

    Su kwace shi in sun gani ba kudi.

     

    Ka roke shi wai don shi huce shi ba ka,

    Su ce za ka ‘bata shi don ba kudi.

     

    Da karni da daci da gautsi da zafi,

    Da haushi ga rayin mutum ba kudi.

     

    Idan kai kudi ko na bare ka kama,

    Ina za a kar’be a gun mai kudi.

     

    Idan ba ka da sai su ce kar’bi karo,

    Kana ki suna ba ka domin kudi.

     

    A ce ga budurwa ka aura ka aihu,

    Iyayenta sun hangi zaton kudi.

     

    Ka dubo mutum shekaru ba misali,

    A kai mai budurwa a dadin kudi.

     

    Ta zauna cikin ba ta ko kara yaji,

    A kayi, a kayi, mijin ba kudi.

     

    Idan ka ji mata tana shirga yaji,

    A kayi, a kayi, mijin ba kudi.

     

    Idan kai kudi sai ka tattara shirgin,

    Ka watsar su mai da a dadin kudi.

     

    Iyayen diya sai su zo gunka biko,

    Su sasanta zancenku domin kudi.

     

    Suna ba ka baki su komad da ‘yarsu,

    Ka san ba abin so a yau sai kudi.

     

    Da girman gwani wanda ya yo Alhassan,

    A birni, Na-Malam a Jos yai kudi.

     

    Ka sa in yi karshen irin na dabino,

    Ba za sai na kifi ba, sai na kudi.

     

    A ce ga ka katonka kai saurayi ne,

    Ina za ka san ‘ya idan ba kudi.

     

    Su ce ga budurwa ka nema mu ba ka,

    Su cuce ka san nan su ba mai kudi.

     

    Idan ka yi wa mai kudi dan jawabi,

    A doke ka nan yanzu gun mai kudi.

     

    A je nan da nan gun saraki a gana,

    Ina za ka san gaskiya ba kudi.

     

    Ya ce za ya kotu ya rungumi lauya,

    A mummurde zancenku domin kudi.

     

    A bar gaskiyar taka don ba ka afu,

    A sa masu shaidar riya don kudi.

     

    A yau babu girma ina mai mutunci,

    Idan ba sarauta ba sai mai kudi.

     

    Da matan kwarai har da doki da tufafi,

    Ina za ka same su? Gun mai kudi.

     

    Hatsi maganin kwarjini har ibada,

    Ina za a same su? Gun mai kudi.

     

    Da malam bafade ina za ka gan su,

    Idan ba wuce fada, gun mai kudi.

     

    Mu tsoraci Allah, mu kuanaci ilmi,

    A bayan wadannan mu nemo kudi.

     

    Kana zaune suddan a kai ka Madina,

    Ka je kai ziyara a dadin kudi.

     

    Wadansu idan sun kudi su yi London,

    Musulmi su je Makka domin kudi.

     

    A nemo kudi jama’a kar ku zauna,

    Ku bar ce bida ba ta kawo kudi.

     

    Abin dunya sai da nema ka samu,

    Idan ka ki ka shirga zambar kudi.

     

    Ka kamo dako yara katti su kama,

    Su fizge su ture ka don ba kudi.

     

    Ku bar wasani babu shauran a huta,

    Ina gun zama rai idan ba kudi.

     

    Idan ka yi gemunka ko yai na taure,

    Da yara kake kokawa don kudi.

     

    Mutane su doke ka sarki ya daure,

    Anai maka gorin ‘barawon kudi.

     

    Su dosa fadin baba ka cika zanga,

    Suna shafa gemunka don ba kudi.

     

    Idan ka ji kai baba mai saje ya kam

    Ku tabbata sajensa babu kudi.

     

    Idan an jima ka ji tsohon tsiyan nan,

    Ana tashi mai saje, to ba kudi.

     

    Kudi in ka same shi, to ka zarce reni,

    Idan ka rasa ka ji haushi kudi.

     

    Idan ba ka sisin kwabo ba ka ikon,

    Fadar gaskiya tun da dai ba kudi.

     

    Musu danaka zai maka don ba ka ahu,

    Ya gaskata karya a gun mai kudi.

     

    Idan kai dibararka kowa ya rena,

    A ce bai yi daidai ba don ba kudi.

     

    Maras ahu kar kai batu ya yawaita,

    Ka kaskanta kayinka don ba kudi.

     

    Ka bar cira kanka idan ba kudi,

    A yau ba mutunci idan ba kudi.

     

    Idan ba ka komai cikin masu komai,

    Baka kulla komai ba im ba kudi.

     

    A cuce ka karfinka kai za ka gode,

    Zatonka dalilinka kai za kai kudi.

     

    Ka shekara noma a kiyyo a daci,

    Ka tara ka kawo wa masu kudi.

     

    Su fanshi arha su tara a daki,

    A ce ba hatsi sai wajen mai kudi.

     

    A yau babu girma idan mai mtutunci,

    Idan ba sarauta ba sai mai kudi.

     

    Ka bar son fadar gaskiya ba ka ahu,

    Idan ka fada an ki sai mai kudi.

     

    Maras ahu kar kai batu ya yawaita,

    Ka kaskanta kayinka kan ba kudi.

     

    Ya ce ma ruwan shi ya ke fid da dauda,

    A a ce ka yi karya idan ba kudi.

     

    Ka ce rakumi ya fi jaki jamu’a su ce,

    Wane yamma za ai idan ba kudi.

     

    Ka ce na ga nono fari, sai su murda,

    Su ce baki ne idan ba kudi.

     

    Idan ba kudi babu sauran jawabi,

    Zukata sukan damu im ba kudi.

     

    Idan kau kana da kudi babu shakka,

    Maza sa bi shayinka domin kudi.

     

    Karatunka bai kai izu ko guda ba,

    Su ce maka malam na dadin kudi.

     

    Kana baya can nesa ga Sabbi,

    Ka dusa wa Ali na neman kudi.

     

    Akan je a tashishi ko wace sa’a,

    Ana doka dakin marasa kudi.

     

    A ce tashi ga mai gida na bidarka,

    Ka je yanzu tilas shi ce don kudi.

     

    Ka je da zuwarka ka duka gabansa,
    A watsad da kai ai ta kirgan kudi.

     

    A manta da kai kai zamar har ka kosa,

    Idan sun ga malam yana son kudi.

     

    Ya zauna awa uku san nan ya juya,

    Ya ce wane, to ka ji ranar kudi.

     

    Ya ce dazu wai na ji ka zo gare ni,

    Yana hura hanci wai na dadin kudi.

     

    Kana ladabi sai ka ce mai ibada,

    Kana jin jawabin ogan kudi.

     

    Idan ya yi karya ka ce gaskiya ne,

    Kana gyara tadinsa domin kudi.

     

    Idam ma kana so ka samu ka tashi,

    Ka ce maigida ka fi kowa kudi.

     

    Mutane su ce haka ne wane,

    To ba a minti guda sai ya miko kudi.

     

    Ina gargadi kun ki ji, to ku zuna,

    A ranar biki a yi zambar kudi.

     

    A shekara arba anai maka gori,

    Ina kwarjinin gun ‘barayin kudi.

     

    Ku farka ku bar gyangyadi mui ta niya,

    Idan kun ki mu za mu neman kudi.

    Anai mana gori yana ‘bata rayi,
    Ga mai zuciya sai ya nemo kudi.
     
    Maras ahu wai su ce mar kwatogo,
    Su ce masa tika idan ba kudi.
     
    Kaho sai a busa, bida bashi aski,
    Tike tuntu’be, tun’bare ba kudi.

    Fito, na fito, gatari tugga, waji,
    Idan ka ji gyanderu rai ba kudi.

    Tsakin tsakuwa, tsagawaro, tsaga dutse,
    Tsagera kirarin masara kudi.

    Maras ahu karfinsa ya zarce dutse,
    Da kunci ga rayin mutum ba kudi.

    Maras ahu ko shawara kar ku ba shi,
    Ba zai gane komai ba don ba kudi.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.