Ticker

    Loading......

Ruwa-Biyu: Sabon Zubin Wakokin Karni Na Ashirin Da Daya

A ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ21), wani sabon salon waƙoƙa ya bayyana. Sababbin waƙoƙin suna tattare da tasirin zamani. Tasirin zamanin ya shafi amfani da kayan kiɗan zamani wajen samar da su da tace sauti da makamantansu. Wannan takarda ta mayar da hankali wajen ƙoƙarin sama musu gurbi na musamman a cikin farfajiyar nazarin waƙoƙin Hausa.

Ruwa-Biyu: Sabon Zubin Waƙoƙin Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya

Dakta Bello Bala Usman
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Imel: bbusmanbk@yahoo.co.uk
080 27459617

 GABATARWA

Bisa ga bayanin masana irin su Muhammad (1978 da 1979 da 1980) da Ɗangambo (2007) da Sa’id (1981) da Yahya (1997) da Gusau (2014) waƙa ta kasu kashi biyu ne wato ta Baka da Rubutatta kuma kowace da irin nata sigogin da suka bambanta ta da ‘yar uwar tagwaicinta. Akwai sigogi na tarayya da suka wajaba a same su a kowace waƙar Hausa ta baka da wadda ake rubutawa. Sigogin sun haɗa da jigo da tsari da kari da reri da zaɓen kalmomi da hikima; waɗanda sai an same su kafin waƙa ta amsa sunanta na waƙa ga Bahaushe Yahya (2010).

  • Lallai ne ya kasance waƙa tana ɗauke da wani saƙo da ake son isarwa ga jama’a. Misali ko saƙo na siyasa ko na soyayya ko gargaɗi ko zambo da sauransu.
  • Haka ma tilas sai an zuba tunanin nan cikin irin siffar waƙa wanda ya bambanta da misalin zube ko wani saƙon da ba na waƙar ne ba.
  • Sannan sai an zaɓo kalmomin da za a yi amfani da su, an tace su domin su hau irin tsarin da yake na waƙar ne.
  • Haka ma dole kalaman nan da aka haɗa ya kasance ana iya rera su bisa ga wani sautin murya irin na waƙa ba wai a faɗe su kawai kamar yadda ake magana ko zance na yau da kullum ba.
  • Sai an samu kari ko baharin da za a gina waƙar a kan sa.
  • A ƙarshe lallai ne tsarin da za a yi na maganar nan ya kasance ya ƙunshi wata hikima ta rayuwa ko kuma hikimar harshe wadda da an ji ta an san cewa an yi wa kalaman wani tsari mai burgewa.

Nazarce-nazarcen da magabata suka yi ya tabbatar mana cewa tun can inda aka fito waƙoƙin Hausa na baka da ka ake yin su, su kuwa rubutattu da alkalami da takarda ake rubuta su. Wato su rubutattu na masu ilimi ne waɗanda ke da wata ƙwarewa ta rubutu da karatu akasin masu yin ta baka waɗanda su ba sai suna da wani ilimi na karatu da rubutu ba. Masu waƙar baka suna sarrafa wata baiwa ce da Allah ya ba su ta iya shirya magana mai daɗi da hikima. Su kuwa masu rubuta waƙa bayan baiwar da Allah ya yi musu na iya tsara waƙa, suna kuma da ilimin rubutu da karatu.

Tun can inda aka fito lokacin da Bahaushe ya fara tsara tunaninsa na waƙa a rubuce, aka zo ƙarni na goma sha bakwai inda muke da dahir na samfurin irin waƙoƙin da suka fi ko waɗanne tsufa a ƙasar Hausa, har aka zo ga ƙarni na goma sha takwas da na sha tara lokacin da aka samu tarin waƙoƙin da malaman jihadi suka rubuta, har aka zo ƙarni na ashirin inda aka kai ga samun rubutattun waƙoƙi na boko a bisa ga wannan fasali muke. Wato waƙar da ake rubutawa ta bambanta da ta baka.

RUWA-BIYU

Allah cikin ikonsa ya yi halittu jinsi-jinsi kuma iri-iri misali akwai mutane baƙaƙen fata da farare. A tsarin yaɗuwa baƙi kan haifi baƙi ne, haka shi ma farar fata ‘ya’yan da kan fito daga tsatsonsa farare ne. To amma idan fari da baƙi suka haɗu, sukan samar da ‘ya’yan da ba fari ba kuma ba baƙi ba. Irin waɗannan ne ake kira ruwa-biyu ko barbarar yanyawa. Ko a dabbobi ma idan aka haɗa misali rago da akuya suka yi barbara ko aka haɗa ruwan halittarsu, abin da za a haifa zai zama baina-baina ne; shi ba dangin awaki ba kuma ba na tumaki sak ba. Haka ma a duniyar kimiyyar ƙere-ƙere yanzu an kai ga ƙirar ababen hawan da suna iya aiki da fetur a matsayin makamashi, kuma ana iya amfani da makamashin lantarki ko hasken rana don sarrafa su. Waɗannan irin ababen sufuri su ne ake ce ma hybrid a Ingilishi, kalmar da kuma ake kiran abubuwan da aka ambata tun farko.

Irin wannan cigaba ne ya samu waƙoƙin Hausa a ƙarni na ashirin da ɗaya; domin a yanzu ana samun waƙoƙin da suka haɗa sigogin waƙar baka da na rubutatta. Idan aka nazarce su sai a iske suna da sigogi wasu daga cikin sigogi tara da Sa’id (1978) ya yi bayanin an san rubutattar waƙa ke zuwa da su kamar amsa-amo (ƙafiya) da mabuɗi, sannan kuma a ga suna da wasu sigogin da aka san na waƙar baka ne kamar karɓi da rashin daidaiton ɗangwaye. Aikin Chamo (2010) ma ya yi nuni da cewa an samu sauyi a zubin waƙoƙin ƙarni na ashirin da ɗaya. To irin wannan sauyi ne nake ganin ya ɗauki siffa ta haɗakar sigogi a waƙa ɗaya wanda a nan na kira ruwa-biyu.

IRE-IREN SIGOGIN WAƘOƘI RUWA-BIYU

Waƙoƙin nan na ƙarni na ashirin da ɗaya suna da sigogi daga dukan ɓangare biyu na waƙa. Duk da yake har yanzu ana samun waƙoƙi rubutattun da na baka kamar yadda aka san su tun can da amma mafi yawancin waɗanda ke tashe yanzu suna zuwa da wannan sabon zubi na ruwa-biyu. Wato a irin waɗannan waƙoƙin sai mai nazari ya ga yana da matsala wajen yanke shawara. Idan aka ce rubutatta ce to yaya aka samu sigogin ta baka kamar kiɗa da amshi da karɓi a cikinta. Kuma idan aka ce ta baka ce to yaya za a yi da sigogin rubutattar waƙa da suka fito fili ɓaro-ɓaro kamar mabuɗi da amsa-amo da ƙayyadadden zubin gaɓoɓin layuka da na baiti, duk da yake wannan zubin gaɓoɓi yakan wuce ƙa’idojin rubutattar waƙa? Sai dai ana iya lura da cewa ana iya samun mawaƙi/mawaƙiya ɗaya da za a iya kasa waƙoƙinsa/ta gida biyu. Kashi ɗaya na waƙoƙin baka kacokam, kashi ɗaya kuma na waƙoƙi ruwa-biyu.[1]

Daga cikin sigogin da ake samu a cikin waƙoƙin nan da ke nuna cewa su ruwa-biyu na akwai:

KIƊA

Amfani da kayan kiɗan gargajiya ko na zamani ya zama wata siga da ta karaɗe waƙoƙin da ake yi a zamanin nan. Yanzu kusan a ce dukkanin waƙoƙin suna ɗauke da wani nau’i na kiɗa, wato kiɗan ma shi ne za a fara ji kafin ma a soma waƙar. Kamar dai yadda yake a waƙoƙin baka inda sai mawaƙi shi kaɗai ko tare da makiɗansa sun tsayar da irin kiɗan da za su yi wa waƙar sannan a fara ambaton kalaman waƙar.To haka yake a yanzu amon kiɗan za a fara ji kafin a ji waƙar ɗauke da saƙon da aka yi niyyar isarwa.

AMSHI

Siga ta biyu da ake amfani da ita a waƙoƙin ita ce ta amshi. Yahya (1997) ya bayyana da cewa “Amshi ɗango ne ko ɗangogi da ake maimaitawa a-kai-a-kai cikin waƙa, ko da yake akan sami rubutacciyar waƙa mai amshi, amma waƙar baka ce ta fi shahara da wannan tsari.” Shi kuwa Gusau (2008) ya nuna cewa “akan raɓa ma waƙoƙin kiɗan fiyano wani amshi irin na waƙoƙin baka kai tsaye.” Ba waƙoƙin fiyano kaɗai ke da amshi a wannan zamani ba hatta waƙoƙin ruwa- biyu na madahu da na siyasa da na wa’azi duk suna ɗauke da wani nau’i na amshi. Yanzu ma yana da wuya a samu waƙar da ba ta da amshi. Misali a waƙarsa ta Baubawan Burmi Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) ya yi amfani da amshi kamar haka:

Baubawan burmi,
Kasassaɓarmu ce kan zaɓen jagora,
Iye-iye.
Shi kuwa Yakubu Muhammad a waƙarsa ta Zumunci an yi amfani da amshin:
Shi zumunci yana ƙara kusanci ƙwarai,
Ai zumunci yana harhaɗa kan ‘yan uwa

KARƁI

Waƙoƙin sun yi tarayya da waƙoƙin baka wajen amfani da karɓi; wani irin nau’i na amshi inda masu amshi ke yi wa jagora cikon wata magana da ya fara bayan kalamansu na amshi da suke maimaitawa King (1981). Misali Nazir ya samu karɓi a waƙarsa ta Sardaunan Ganye:

Jagora: In na ce Bismillahi

Karɓi: Shi Rabbana in ka kira shi
Ba zai bar ka ba sai ya dafa

Jagora: Ku taya ni da roƙonsa

Karɓi: Allah ka ɗaukaka waƙar tamu, sannan ka ɗaukaka mai waƙa
Ka ɗaukaka mai waƙa sannan ka kyautata ƙarshensa

A waƙarsa ta Sama Cibiyar Nisa Ado Gwanja an yi amfani da karɓi a wasu wurare misali kafin ya ƙarasa waƙar ya samu karɓi kamar haka a waƙar.

Jagora: Yara iye dutse, dutse ba rabon gara ba

Mai Amshi: Yara iye dutse, dutse ba rabon gara ba.

Jagora: Mata ku ringa takawa

Mai Amshi: Dushe ba rabon gara ba

Jagora: Ku yo rausaya, ku ringa juyawa

Mai Amshi: Dutse ba rabon gara ba

Jagora: Idan kun yo farin ciki ku nunawa

Mai Amshi: Dutse ba rabon gara ba.

KARɓEɓENIYA

Kamar yadda ake samu a waƙoƙin baka su ma waƙoƙin zamani suna cike da wani irin nau’i na amshi wanda ake kira karɓeɓeniya King (1981). A karɓeɓeniya tamkar hira ce za ta wanzu tsakanin jagora da masu amshi. Ko kuma jagora ya yi tambaya su amsa masa. An samu misalin irin wannan a waƙar Ajnabi ta Nagudu:

Jagora: Yau gari ya yi wayewa, baƙo a gidanmu ya sauka

Karɓeɓniya: Eh

Jagora: Shi nake ba ki labari, abokin da bai da tamka

Karɓeɓeniya: Eh

Karɓeɓeniya: Amini koko habibi mai tarin albarka

Karɓeɓeniya: Eh

Jagora: Yarinta har ma girma, da ni da shi a ce sambarka

: Mun ga ɗaukaka, so ya haɓɓaka

Karɓeɓeniya: A zaman juna, haƙuri ga tawakkali

Amshi: Ajnabi baƙo, zuciya na kai saƙo

So da shaƙuwa, bai misaltuwa

Soyayya, saƙo ne mai asali

A nan za a lura cewa baiti aka raba tsakanin jagora da mai amshin. Irin wannan salon karɓeɓeniya ce Kabiru Yahaya Classic yake amfani da shi tsakaninsa da wadda take yi masa amshi.

Ga misalin baitocin waƙar da Classic ya yi wa Garkuwan Kwatarkwashi Alhaji Mani Aliyu:

Jagora: Bunguɗu mun san Allah mun san Annabinmu,
Mun yi karatun ilimi kuma bai gagarar mu,
Gwargwadon hali mun san mai gudunmu,
Kamar wane mun jigata da shi ya butulce.

Karɓeɓeniya: Karankaɓau gona ban san mi za ka yo ba,
Hakin banza ba sa wa kuma ba hana ba,
Bunguɗu kowa bai ce ma Allab bari ba,
Ba ka kwana Bunguɗu sai dai kauce-kauce,

Jagora: Had da ni yai min ƙaryar banza ta rago,
Da za ni haihu ya ce shi zai ba da rago,
Yai yi mini ƙarya ya rufe kainai da bargo,
Kai wa maza ƙarya balle ni ta mace.

Karɓeɓeniya: Dama inda yaƙ ƙware wajjen ɗauke-ɗauke,
Wanda yaw wahala gunka ka bar shi tanke,
Ƙurungun Bunguɗu an saba da bugun fatake,
Ga shi Gwamnanai ya hana ‘yan sace-sace.

Wani fitaccen salon karɓeɓeniya shi ne wanda Aminu Ala da El Mu’az da Yahaya suka yi amfani da ita a waƙar Haka Allah Yas So.

AMSA-AMO

Daidaita gaɓoɓin kalmomi a baiti a farko ko tsakiya ko ƙarshe, wata fitacciyar siga ce a rubutattun waƙoƙi. Waƙoƙin nan na ƙarni na ashirin da ɗaya sun ɗauki wannan tsari inda suke ƙoƙarin daidaita irin gaɓoɓin da ke a ƙarshen baitocin waƙoƙinsu, wani lokaci har su yi amfani da sigar inda ba ta dace ba.

A waƙarsa ta Ƙurunƙus Dauda Kahutu Rarara ya yi amfani da amsa-amon ciki da waje, kodayake bai cika amfani da irin wannan tsari a fitattun waƙoƙinsa ba. Ga misalin:

Jagora: Biyan bashi dole ne ga dukkan mai hankali,

Halin kirki ya fi kyau, ga jagora adali,

Na tuba gurin Ilahu, na ce masa madali,

Ashe ba Malam ba ne, a boko ya sanar da su.

Amshi

Jagora: Sai wani Honorabul kwatsam, yaz zam malami,

Ashe wai zai takara ta Gwamna, ku ji tsegumi,

Sannan ni ban sani ba, sun sa ni cikin ɗumi,

A yau ta kai ta ɓare da shi, oho na ce da su.

Ado Gwanja ya bi irin wannan tsarin amsa-amon ciki da waje a waƙarsa ta Indosa:

Mai saurarona, bana sauti ya sauya,

Faɗa wa mai fafe gora, yau ce ranar tafiya,

Ado Gwanja ne, ga wani baiti na shirya,

Mai dukan sauti, buga ganga mu yi taken a sha ruwa-ruwa.

Ado Gwanja ne, na Aminun Dawayya,

A sauya salon tako, tun da kiɗana ya sauya,

Lokaci in har zai zo maka ba ya bari sai ka shirya.

Mai saurarona, don jin daɗin gangar, bi ni mu je fagen rawa.

Ayye, Wasu nij ji suna magana, wai mata muka wa waƙa,

Kuma in na kaɗo sautin, har da mazan sai sun taka,

Kai ya zama dole iri, za ya fito ranar shuka,

Sai doki ya kai doki, a kwalliyatai za ka jiyo ƙarar ƙararrawa

ZUBIN LAYUKAN BAITI

Ƙayyade layukan baiti fitacciyar siga ce a rubutattun waƙoƙi. Ɗangambo (2007) An saba da zubin gwauruwa (mai layi ɗaya) da ‘yar tagwai (mai layi biyu) da ƙwar uku (mai layi uku) da ƙwar huɗu ( mai layi huɗu) da ƙwar biyar (mai layi biyar) da tarbi’i (mai layi biyu ga asali wani ya ƙara mata biyu ta koma huɗu) da tashɗiri mai kama da tarbi’i, amma ita raba baitin asali biyu ake yi, kowane ɗangon asali ya sami ƙarin ɗango. Ta haka sai waƙar ta riɓanya baitoci; idan waƙar asali an san ta da baiti goma sai ta koma mai baiti ashirin saboda tashɗiri da aka yi mata da kuma tahamisi (mai layi biyu ga asali, wani ya ƙara mata uku ta koma biyar). A bisa ga wannan tsarin ake sai da aka zo wannan zamanin inda aka sake fasalin layukan baiti kamar yadda Chamo (2010) ke cewa: “Zubin waƙoƙin ƙarni na 21 ya sha bamban da na waƙoƙin ƙarni na 19, da na 20 ta fuskar yawan layuka a baitoci” Misali ana samun waƙa mai layi shida-shida a baiti ko ma fiye. Dubi yadda Fati Nijar ta yi a waƙar Ka Yi Mun Gani:

Jagora: Rabbi tutil mulki, kai kaɗai ne mai bayarwa,

Dukkan lamarina, ni da kai nake yin farawa,

Sallama ga Ma’aiki, Maƙurar kyau gatan kowa,

Alihi sahabai, mai nagarta nai gaidawa,

Duk wanda ya bi su, shi ne za yai dacewa,

Mu kama salati da hailala, a Jigawa ba za mu faɗi ba.

Amshi:

Jagora: Jama’a ta Jigawa, mata da maza duka kowa,

Ni Fati Nijar, sallama nai ƙarawa,

Ga ni ɗauke da saƙo, wanda na san zai burgewa,

……… Zannan adali yau nai ɗaukowa

Jigo kuma ango, mai kishi gun talakawa,

Sule Lamiɗo ɗan halaliya, namijin gaske, gamji jagaba.

Amshi.

Jagora: Addu’a talakawa, mun yi Allah yai amsawa,

Matsaloli sun kau, mun ga haske yau a Jigawa,

Samun managarci, zuciya tasa tsaf kyakkyawa,

Gwamna Sule ya zo, alkhairi yai kawowa,

Ba ma kokwanto, mun gani kuma mun shaidawa,

Zuciya hankali ta yi kewaya, a Jigawa yau babu fargaba.

A waƙar Dauda Kahutu Rarara “Masu Gudu Su Gudu” ya yi amfani da tsarin mabambantan layukan baiti domin an samu baiti guda ɗauke da layuka fiye da goma, wani baitin ya ƙunshi layi goma, wani tara a cikin wannan waƙa. Dubi wannan baiti:

Assalamu alaika salam jama’a na ƙasa barkanmu haka,

Ga Rararan waƙa na Kahutu gida kun shaida haka,

Jami’a gonar waƙa in ka mana adalci mu maka,

Ana maganar canji APC sai ta karɓi duka,

In kai maganar turmi kowa ya san aikinshi daka,

Shi injin Tahuna an fi yi masa lissafi da niƙa,

Ita PDP timɓir muka ce za ai kuma an yi haka,

Mun hallaka PDP a saman da ƙasan mu ne da ɗaka,

A kasa, a tsare, a raka in ji Baba Janar shi ne waraka,

Yau ga canji ya zo, APC kullum na haɓaka,

Yau dai mu ne da tuwo, mu ne da miya, mu ne da duka,

Janaral na talakawa ko Turawa sun shaida haka,

Buhari muke magana in ji Rarara Allah ya riƙa,

Talakawa sun ce addu’ar da sukai ta karɓu duka,

Janaral ya karɓi sama, Allah taya ka riƙo addu’ar talakawa.

Haka aka lura da irin wannan tsari a waƙoƙin Kamilu Gashuwa kamar “Gafara Koko” da ma sauran masu waƙoƙin zamanin nan.

SHARAR FAGE

Wani sabon zubi da aka lura da shi a waƙoƙin ƙarni na ashirin da ɗaya shi ne na sharar fage, inda mai waƙa zai buɗe waƙarsa da wani abu kafin ya koma ga zubinsa na rubutacciya mai ƙwar huɗu. Dubi yadda Dauda Kahutu Rarara ya share fage a farkon waƙar “Ƙurunƙus” da cewarsa:

Amshi: Ƙurunƙus, Kwankwaso ya firgita su,

Allah ya kawar da su,

Ƙurunƙus, a zaɓe an ka da su,

A kotun an ka da su,

Kwankwaso ya tarwatsa su,

Allah ya kawar da su.

Jagora: Tawassul ga Allah da yai wawa yai gwani,

Yai Dauda Kahutu Rarara tun tuni,

Yai Abdullahi Gwarzo bawan Allah da ni,

Yai Rabi’u Kwankwasonmu shi ne yai Ɗangwani,

Yai Sadiyya Lawal cikin Fagge mu yi zamani,

Yai Titi Ɗandamargu gemunsa daban da su.

Amshi:

Jagora: Salati marar addadi gun khairul anbiya,

Manzona Ɗan Amina haskenka ya zagaya,

Har ahali har Sahabu su duka zan bayyana,

Har Sharifai suna ciki ban manta da su.

Amshi:

Jagora: Biyan bashi dole ne ga dukkan mai hankali,

Halin kirki ya fi kyau da jagora adali,

Na tuba gurin Ilahu na ce masa madali,

Ashe ba Malam ba ne a boko ya sanar da su.

Amshi:

Sai wani Honorabul kwatsam yaz zam malami,

Ashe wai zai takara ta gwamna ku ji tsegumi,

Sannan ni ban sani ba sun sa ni cikin ɗumi,

A yau ta kai ta ɓare da shi koko na ce da su.

Amshi:

Jagora: Batun shari’a an gama ina wani mai tsegumi,

Da na ji gunaguni da sa jama’a zullumi,

Sun tattara dukkanin bayanansu na tsegumi,

Da ɗai ɗai aka ya da su.

MABUƊ

Wani abin lura a waƙoƙin ƙarni na ashirin da ɗaya shi ne sun riƙe al’adar nan ta rubutacciyar waƙa ta sanya mabuɗi a waƙoƙinsu. Misali Alan Waƙa ya buɗe waƙar “Baubawan Burmi” da cewarsa:

Jagora: Allah malikal mulki,

Tutal mulki man tasha’u a kan mulki.

‘Yan Amshi: Iye-iye

Jagora: Allah mun yi zaman dirshan

Tamkar fittila a lokon alkuki.

Mafi yawan waƙoƙinsa sukan fara da mabuɗI, wato ambaton sunan Allah, wani lokaci har da yin salati.

Dubi yadda Nura Oruma ya yi wa waƙarsa ta Umar Mai Akwai S/Tudu Turakin Jabo mabuɗi bayan ya ba mai yi masa amshi amshin waƙar kamar dai yadda aka san mawaƙan baka na yi a farkon waƙoƙinsu:

Jagora: Mai Akwai S/Tudu

‘yar Amshi: ‘Yan Jabo kun yi dace da Turaki

Jagora: Ga zama lafiya

‘Yar Amshi: Bajinin Atiku ne Gagara-gasa

Gidan Sarkin ɓurmi Jabo yau an yi naɗinsa

Jagora: Rabbana Allah Wahidun Gwani na yi kiranka

‘Yar Amshi: Saraki mai martaba

Jagora: Kai ne kaɗai guda ba ka da tamka

‘Yar Amshi: Mai Akwai S/Tudu

Jagora: Kai kay yi mai kuɗi kay yi talakka

‘Yar Amshi: Ku sha zama lafiya

Jagora: Ga abin da kan nufa wa ka hana ka?

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Jalla ka taimaka du’a’inmu ka amsai

Amshi:

Jagora: In Ilahi ya yarda duniya wa ka hanawa?

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Da ya furta KUN mutum zai ta ɗagawa

‘Yar Amshi: Mai Akwai S/Tudu

Jagora: Mai kushe da hassada ba ya iyawa

‘Yar Amshi: Ku sha zama lafiya

Jagora: Idan yai wa ɗan Adam tarin baiwa

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Bishiyarsa nan da nan za ta yi rassai

Amshi:

Jagora: Rabbana miƙa salati inda ɗan ɗa ga Amina

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Manzon da ke hanawa a yi ɓarna

‘Yar Amshi: Mai akwai S/Tudu

Jagora: Mahamudu duniya shi fittila na

‘Yar Amshi: Ku sha zama lafiya

Jagora: Alaye da Sahibai sun shiga raina

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Da Sheikh Ussumanu ma ba ni cire mai

Amshi:

Jagora: Babu tababa sallama ado ce ga musulmi

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Duw wanda yai yi zai so ya ji amin

‘Yar Amshi: Mai Akwai S/Tudu

Jagora: Jama’ar gari ku taso ku riƙa min

‘Yar Amshi: Ku sha zama lafiya

Jagora: Ƙasar Jabo, fada nis so a gwada min

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Gidan Sarkin ɓurmi Jabo, in gane kalarsa

AMFANI DA SANƘIRA

Yin amfani da Sanƙira siga ce sananniya da aka san waƙoƙin baka da ita kamar yadda binciken Tsoho (2010) ya tabbatar. Sai ga shi an samu shaiduddukan da ke tabbatar da ita a waƙoƙin nan na ƙarni na ashirin. Suna amfani da sanƙira kamar yadda aka san ana yi a waƙar baka. Misali Marigayi Umar Abdul’Aziz Baba Fadar Bege da aka sani da rubuta waƙoƙin ruwa-biyu na madahu ya yi amfani da sanƙira daga farkon waƙarsa Daɗin Duniya zuwa ƙarshe:

Jagora: Jalla Mafi girma, gyara Jalla mafi girma

Sanƙira: Kai! Fadar Bege

Jagora: Jalla mafi girma

Sanƙira: Allah ke nan, mafi girma

Jagora: Allah mai kowaaaaaaaaaa, mai kome

Sanƙira: La’ila ha illallahu, Ka ji Lillahi Wahidun Ƙahharu

Jagora: Jalla mafi girma

Sanƙira: Maƙagin Muhammadur Rasulullahi

Jagora: Sarkin daraja, Allah kai tsira ga Ma’aikina

Sanƙira: Allah da ya ƙagi mutum da aljan, yai mala’ika da Annabi

Jagora: Yara duniya daɗi

Sanƙira: Allah da yai dabba yai tsuntsu. Annabi Muhammadu

Jagora: Duk daɗin duniya, mun san bai yi zama da Ma’aiki ba

Sanƙira: Sarkin Muhammadur Rasulullahi, ke nan, A’a!

Jagora: Yara duniya daɗi, duk daɗin duniya, kun san bai yi zama da Ma’aiki ba

Sanƙira: Annabi Muhammadu, kai duk daɗin zama bai yi zama da muhammadur Rasulullahi ba

Jagora: Allah Rabbi nike sawa, mai mulki da abin mulka

Sanƙira: Mai mulki da abin mulka, Muhammadur Rasulullahi

Sanƙira: Kai! Duk daɗin duniya, bai yi daɗin zama da Muhammadur Rasulullahi ba

Jagora: Allah Rabbi ka dafa man, kullum kai nika wa kuka

Sanƙira: Annabi Muhammadu, Allah kai muke roƙo

Jagora: Zuljalali abin bauta, amsa min da abin roƙa

Baituka ne zan wa Annabi, ban tsaro su da wasa ba

Sanƙira: Eh! Baituka za mu yi wa Muhammadur Rasulullahi

Jagora: Allah mai kowaaaaaaaaaaaa mai kome, Jalla mafi girma

Sanƙira: Eh mana! Sha kira da baiwa

Jagora: Sarkin daraja, Allah kai tsira ga Ma’aikina

Sanƙira: Allah kai tsira ga Annabin da babu irinsa

Jagora: Yara duniya daɗi, duk daɗin duniya kun san bai yi zama da Ma’aiki ba

Sanƙira: Annabin da ba shi da farko ba shi da ƙarshe

Annabin da shi kaɗai ne a gaba, babu wani a bayansa.

Irin wannan salon amfani da sanƙira ne Ali Jita ya yi a wata waƙarsa da yake lissafo abokan sana’arsa ɗaya bayan ɗaya Baba Ari yana ƙarin bayani a kan duk wanda aka kira cikin mawaƙan nan.

KARI

A wajen zaɓen kari ko bahari ma za a lura da cewa waƙoƙin nan sun raba ƙafa domin akwai waɗanda aka gina su kan Karin Aruli da kuma waɗanda aka tsara su bisa ga Karin waƙoƙin baka. Fitaccen misali shi ne waƙar Daɗin Duniya ta Madahu da Fadar Bege ya ɗora a kan Karin waƙar Sani Sabulu mai wannan sunan. Haka ma waƙarsa ta Babba Ɗan Babba aron karin waƙar Sa’adu Bori na Nijar ya yi ya tsara tasa.

Jagora: Manzon Allah Babba ɗan Babba

‘Yan Amshi: Manzon Allah Babba ɗan Babba

Jagora: Kai nike kira Sarki

Ƙara ban dubun tsarki

Nai shirin shiga aiki

Zan yabon Ma’aiki

Babba ɗan Babba.

‘Yan Amshi: Manzon Allah Babba ɗan Babba

Jagora: Ƙara yo salatinka,

Gun cikon Ma’aika,

Mai idon ganinka,

Shi kaɗai ya gan ka,

Babba ɗan Babba.

‘Yan Amshi: Manzon Allah Babba ɗan Babba

Jagora: Alihi in sanya su,

Ham maza da matansu,

Na daɗe da ƙaunar su

Dole ne in gaishe su,

Su kaɗai nake duba.

‘Yan Amshi: Manzon Allah Babba ɗan Babba

TSARMIN ƊAN WAƘA

A cikin waƙoƙin nan na ƙarni na ashirin ana samun inda ana cikin zubin baitocin rubutattar waƙa sai a tsarma wani ɗan waƙar baka. An ga irin wannan misali a wasu waƙoƙin Siyasa. Misali a waƙar Aminu Isiyaku Rinji ɓagwai mai suna “PDP Tsumma Da Jini” wadda ya rubuta cikin zubin ƙwar huɗu a kowane baiti. Sai ga shi a baitin ƙarshe na waƙar ya sako ɗan waƙar baka ya rufe da shi haka:

In ba mu lafiya ba assibitin zuwanmu don kwantarwa,

Duka assibiti ba magunna da likkitan dubawa,

Mu ne muke zuwa mu tsumayi zuwa na mutuwar ɗaukewa,

In ka ga shugaba a garinku siyasa fa ta dawowa,

Da sun ci ƙurri’a shi ke nan mu da su fa sai gilmawa,

In ba su lafiya sai can a ƙasar waje ake dubawa,

Batu na ilimi mu dagur-dagur muke ‘yan uwa,

Don babu ilimi ba yalwatas su malaman koyarwa,

‘Ya’yanmu ne suke hoririya a cikin ajin koyarwa,

Su ko suna fitar da ɗiyansu ƙas ashen waje koyowa,

Haka ci gaban yake? Ko ci baya tambaya amsawa,

Tambaya amsawa,

Tambaya amsawa,

Ina da mai shirin amsawa?

Ko da mai amsawa?

Wani misali ya samu a waƙar ALA ta Baubawan Burmi inda daga tsakiya ne ya kawo wani ɗan waƙa wanda ya saɓa wa tsarin da yake a kansa na rubutattar waƙa tun farko. Ga yadda ya zuba ɗan tare mai amshinsa:

‘Yar Amshi: Ala mai faɗakarwa,

Da’in kukan kokawa,

Allah ne ke sakawa,

Sannan shi ke cirewa,

In ya so zai canzawa,

Ba mai ikon hanawa.

Jagora: Dole in koka da tsiwa,

Dubi ƙasar nan Arewa,

Ba ilimu talakawa,

Ba mu da aikin taɓawa

Mun zama jujin zubawa,

Tarkacen tarkatawa.

An ga irin wannan tsarmin ɗan waƙar baka a cikin rubutatta a waƙar Haruna Aliyu Ningi ta Shegiyar Uwa inda yana bisa ga tsarin ƙwar huɗu sai a tsakiya ya kawo wannan ɗan:

Jagora: Tumburun buƙun

‘Yan Amshi: Baba a sha maganin ƙaba,

Jagora: Ina ake jiƙon?

‘Yan Amshi: Sai Nassarawa can garin Wamba,

Jagora: Da me ake zuwa?

‘Yan Amshi: Baba ka je da ƙatuwar kwalba,

In ka nannaga, sai ka nufaci ƙatuwar salga.

GAZA

Ita gaza wata ‘yar tsawa ce da mawaƙan baka ke yi don su mayar da hankulan ‘yan amshi da makaɗansu ga aikin da ake yi na waƙar, musamman idan suka ga wani abu na neman janye mataimakan daga waƙa.

To hatta irin gazar nan ta shigo cikin zubin waƙoƙin zamanin nan, inda za a riƙa jin suna ambaton kalmomi irin su ‘haba!’ ko ‘sama!’ ko ‘hayya kai!’

KAMMALAWA

Wannan maƙalar ta yi bibiyar cewa lamarin nazarin waƙoƙin Hausa ya tabbatar da samuwar waƙa iri biyu ne; ta baka da rubutatta kuma kowace da irin sigoginta in ban da irin sigogin da kowacensu sai ta same su kafin ta amshi sunanta na waƙa.Amma sai ga shi a ƙarni na ashirin da ɗaya an samu waƙoƙin da ke da ruwa-biyu. Wato sun haɗa sigogin ta baka da na rubutatta yadda za su iya faɗawa kowane kashi. Ire-iren sigogin da ke haɗaka a waƙoƙin sun haɗa da kiɗa da amshi da karɓi da karɓeɓeniya da amsa-amo da zubin layukan baiti da sharar fage da mabuɗi da amfani da sanƙira da kari da tsarmin ɗan waƙa da gaza. To samun waɗannan a tare a waƙoƙin ne ya sanya aka yanken hukuncin cewa ruwa-biyu ne. Saboda suna da sigogin duka biyun yadda yana da wuya su tsaya a kashi ɗaya kamar yadda aka saba gani inda aka fito.

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takardar.

Kalangu

Post a Comment

2 Comments

  1. Sunana Usman Ahmed Mai ratata.
    Ba shakka mun gamsu da wannan bayani kuma mun kara ilimi .
    Allah yabamu lafiya da nisan kwana.
    Wata rana za'a buga Misali da wakokinmu.

    ReplyDelete
  2. Abu-Ubaida Sani10 June 2018 at 05:33

    Malam Mai Ra-ta-ta,

    Mun gode.

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.