Umar Aliyu Bunza
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
aliyubunzaumar@yahoo.com
07063532532, 08095750999
1.0 GABATARWA
Fad’akarwa aba ce da ake samu a cikin kowane nau’i na adabin Hausa. Wannan ya sa lamarin fad’akarwa ya kasance ruwan dare cikin adabin Hausa na baka da rubutacce.
K’agaggen labari wani nau’i ne na rubutaccen adabi da aka fara samarwa cikin Hausa bayan wanzuwar mulkin mallaka da kafa hukumomin inganta adabin Hausa. A zamanin rayuwar Hukumar Talifi ne aka fara samar da wannan nau’in adabi dalilin gasar da hukumar ta shirya a dukkanin fad’in Arewacin Nijeriya. Tun daga wannan lokaci zuwa yau, k’agaggen labarin ya ci gaba da samun kar’buwa ga hukumomi da d’aid’aikun mutane har zuwa yau da ake jin akwai littattafan k’agaggun labaran Hausa sama da 3, 500 (Malumfashi, 2010). Littattafan da aka samar sun kasance wata hanya muhimmiya don samar da nishad’i da gargad’i da fad’akarwa da koyar da al’umma dabarun rayuwa da sauransu. Ganin wannan matsayi da k’agaggen labari ya samu na zamansa komai da ruwanka a al’amurran yau da kullum na rayuwar al’umma, ya sa na shiga cikin wasu littattafai domin kalato darussan fad’akarwa da marubutan suka gina a cikin rubuce –rubucensu. Duk da yake k’agaggen labari ne ginshik’in mak’alar, na kauce wa duba tarihin k’agaggen labarin da nau’o’insa ba don komai ba sai don ganin masana da manazarta (Yahaya, 1988 da Mukhtar, 2004 da Malumfashi, 2006, 2009, 2010, 2011 da Bakura, 2011 da Adamu, 2013 da Aminu, 2013 da sauransu) sun yi rubuce-rubuce kan wannan.
2.0 MA’ANAR FA’DAKARWA
Kalmar fad’akarwa kalma ce da ke nufin jan hankali da wayar da kan jama’a kan wani abu mai alfanu gare su. A cewar, Usman (2008), fad’akarwa hanya ce ta waye wa mutane kai kan wasu al’amurra da yake ganin suna da alfanu gare su. Shi kuma Gusau (2008), a bayaninsa kan turk’en fad’akarwa ya nuna cewa, a kodayaushe wannan jigo na fad’akarwa yakan yi k’ok’ari ne ya sanar da mutane wasu abubuwa sababbi da suke aukuwa a rayuwar yau da gobe. A tak’aice, fad’akarwa hanya ce ta ilmantar da mutane ko yi musu nasiha da tunatar da su don jan hankalinsu kan wani abu muhimmi na rayuwarsu.
3.0 FA’DAKARWA A WASU K’AGAGGUN LABARAN HAUSA
K’agaggen labarin Hausa wata hanya ce da mutanen da Allah ya ba hikimar rubutu suke amfani da ita don isar da sak’onni daban-daban na rayuwar yau da kullum a cikinta. Marubuta litattafan suna shigowa da fad’akarwar ce wasu lokuta a matsayin k’aramin jigo ta fuskar nasiha ko ilmantarwa ko tunatarwa don kyautata wani abu na rayuwar al’umma da kuma nasarar warware babban jigon littafinsu. Kodayake, marubutan ba a fili suke nuna fad’akarwa suke yi ba, to sai dai ga wanda ya karanta ga’bar fad’akarwar zai ji wani abu na tunatarwa ko nasiha ko ilmantarwa ya shiga rayuwarsa. Akwai littattafan k’agaggun labaran Hausa masu yawa da aka rubuta kan jigogi mabambanta, amma kuma ta k’ok’arin warwarar jigo, sai marubuci ya shigo da wani batu na fad’akar da al’umma kan d’aya daga cikin fuskokin fad’akarwa guda uku.
3.1 FA’DAKARWA TA FUSKAR NASIHA
Nasiha na nufin kyakkyawar shawara (K’amusun Hausa, 2006: 357). Shi kuma Yahaya (2004), ya nuna kalmar nasiha na nufin luraswa ko shawara. Idan aka dubi wad’annan ma’anonin ana iya cewa, kalmar na iya d’aukar ma’anar shawarar da aka ba mutum ta amfani da kalmomin rarrashi don jan hankalinsa zuwa ga wani abu da ake son ya kula don amfanin rayuwarsa. Akwai wasu litattafan k’agaggun labaran Hausa da ke d’auke da irin wannan fad’akarwa ta nasiha a cikinsu. Ga misali, a littafin Shaihu Umar wanda Abubakar Tafawa ‘Balewa ya rubuta marubucin ya yi amfani da wasu kalamai da suke zama fad’akarwa ga al’umma ta bakin wata tauraruwar littafin a lokacin da ta kai Shaihu Umar rik’o a wajen wata mata. Ga yadda ya kawo bayanin;
‘Amina, ina so mu yi ban kwana da ke yanzu domin ina so zan tashi tun kafin a kira sallah. To, sai fa ki d’auki hank’uri, kin san halin yaron, kullum abin da ya ke so ya yi in ba a bar shi ba sai ya yi kuka, amma idan ana barinsa ya yi abin da ya so a gaba ba zai ji dad’i ba. Ya kamata ki rik’a kwa’bonsa ko yaushe, kada kuwa ki kula da cewa ai wannan yaro ba nawa ba ne, wallahi da ni da ke duk d’aya ne, tun da yake Allah ya had’a mu, kuma a kan amana mu ke zaune’ (shafi na 18).
Idan aka yi nazarin wannan zance da idon basira, za a ga cewa nasiha ce uwar Shaihu Umar ke yi wa Amina, amma yana k’unshe da abin da yake fad’akar da mutane dangane da halin yara da kuma yadda ya kamata a kula da tarbiyyarsu. Kowane yaro ba ya son a hana shi abin da ya sa a gabansa, to sai dai kuma hana shi, shi ne alheri gare shi da al’umma. Dalili kuwa shi ne, yaro bai san abin da yake daidai da wanda ba daidai ba a lokacin yarintarsa. Idan aka ce a bar yaro kan abin da yake so, to bayan girmansa zai iya zama fitina ga al’umma domin zai tashi ba shi da tarbiyya tagari musamman ta fuskar tarbiyyar jiki kan ayyukan wahala. Ke nan wannan ga’bar littafin fad’akarwa ce ga mai karatu kan yadda ya kamata a yi tattalin yara da renon su don su tashi nagari cikin al’umma. Wannan kuwa hak’k’i ne na kowa da kowa, ba wai sai iyayen yaro kawai ba kamar yadda uwar Shaihu Umar ta nuna wa Amina.
Shi ma littafin Tura Ta Kai Bango wanda Sulaiman Ibrahim Katsina ya rubuta an yi amfani da wasu bayanai da suke kasancewa fad’akarwa ga mai karanta littafin. Marubuci littafin ya shigo da irin wannan fad’akarwa ta bakin wani tauraronsa mai suna malam Maigafaka inda ya kawo cewa,
‘A yau malam Maigafaka yana karanta wa almajiransa wani hadisi na manzon Allah ne yana cewa, ‘Alamar munafiki uku ce: Idan ya yi magana sai ya fad’i k’arya, in an ba shi amana sai ya ci, in kuma ya yi alk’awari ba zai cika ba. Amma mu a yau mutane ba su d’auki k’arya a bakin komai ba. Sai ka iske babban mutum, ko ma malami yana ta zuba k’arya. Ko ya yi alk’awarin yin abu, ya k’i yi.’ (shafi na 25)
A nan marubucin na k’ok’ari ne ya fad’akar da jama’a hadisin Annabi (S A W) da ya yi magana kan alamomi ko siffofin munafiki. Ya kawo alamomi uku; k’arya da cin amana da kuma sa’ba alkawari. Shigo da wannan batu wani k’ok’ari ne na fad’akar da duk wanda ya karanta littafin don ya kiyaye daga fad’awa cikin wad’annan alamomin.
A wani wurin marubucin ya k’ara fad’akarwa ta bakin malamin da wani hadisi da ya kawo kamar haka;
‘Wani bai ta’ba cin wani abu mai amfani ba, da ya zarce abin da ya yi aiki da hannunsa ya samu.’ Malamin ya ce, ‘Wannan hadisai ya nuna muna cewa, kowanne mutum, abin da ke tabbata mafi amfani gare shi shi ne abin da shi ya yi aiki da hannunsa ya samu, ba wai wani ya je ya nemo, kai kuwa kana kwance ka amsa ka ci ba.’ (shafi na 25-26)
A wannan wuri fad’akarwa ce marubucin ke yi wa wanda ya karanta littafin don ya san irin abin da ya fi alheri ga rayuwarsa. A nan ya kawo bayanin abin da zai kasance mai kishin kai da tashi ya nemi abin kansa ba wai ya zama ci-ma-kwance ba, sai wani ya samo ya ba shi.
A wata ga’ba ta littafin marubucin ya ja hankalin mai karatu kan wani hadisi da ya kawo wasu abubuwa da ke nisantar da mai aikata su daga rahamar Allah da sa shi cikin azabarSa. Ga yadda ya kawo wannan bayani ta bakin malam Maigafaka,
‘....Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ranar k’iyama ba, ba zai yi musu duban rahama ba, kuma ba zai tsarkake su ba balle ya sa su a aljanna, kuma suna da azaba mai tsanani. Su ne mutumin da ke da ruwa mai yawa bak’o ya zo mai wucewa ya hana shi. Sai wanda ya yi mubaya’a don a ba shi kud’i ba don tsare hak’k’in Allah ba, in ba shi ba kuma ba zai jefa k’uri’arsa ba a inda ba a ba shi kud’in ba. Sai na uku shi ne wanda ya yi wa wani mutum k’arya ga kayansa don ya cuce shi.’ (shafi na 26).
Idan aka yi la’akari da wannan bayani za a ga cewa, fad’akarwa ce ga mai karatu kan abubuwa uku da za su kai shi ga halaka; su ne hana bak’o ruwa tare da halin ba shi da sayar da mubayi’a sai kuma k’arya don yin cuta. A nan marubucin fad’akarwa ce ya yi don wanda ya karanta ya hankalta ya tsare wad’annan abubuwa domin ya ku’butar da kansa daga shiga cikin mutanen da za su dauwama cikin azabar Allah.
Shi ma littafin Turmin Danya na Sulaiman Ibrahim Katsina marubucinsa ya yi amfani da wasu zantukan nasiha da ke zaman fad’akarwa ga duk wanda ya karanta littafin. Ga misali, a shafi na 62, a lokacin da wani tauraron littafin mai suna Mukhtar yake tattaunawa da wasu jami’an kwastan abokan aikinsa, marubucin ya yi amfani da yawun bakinsa ya kawo wannan fad’akarwar kamar haka,
‘Ai bai wuce cewa kowane rai mai d’and’anar mutuwa ne. Domin an ce, tun ran gini, tun ran zane. Hanyar da duk Allah ya k’addara za ka mutu, to babu dabarar da za ta iya kare ka. Ko haka nan, ko rashin lafiya, ko had’ari, tarnatsa, ko zubar d’aki, fad’owa daga jirgin sama, ko doki, ko tuntu’be ko a kai maka hari. Duk dai ta hanyar da Allah ya k’addara, baka da magani. Saboda haka, ka ga da ka yi mutuwar matacce, gara ka yi ta mai rai. Da ka mutu a banza, tunda mutuwar za ka yi, to gara ka mutu a kan tsaron gaskiya. Ka ga in ka yi nasara, jama’a ta ji dad’i, kuma Allah ya saka maka. In kuma ba ka yi nasara ba, wanda da wuya a ce baka samu nasarar ba, domin ko ba komi za ka wayarwa jama’a kai, to a lahira, ana sa ran Allah shi baka babban rabo-watak’il ma irin ta wad’anda suka yi shahada, don saboda kyakkyawar niyar da ka mutu da ita.
Idan aka yi la’akari da wannan ga’bar za a ga cewa, akwai fad’akarwa ga duk wanda ya karanta wannan wurin. Abu na farko dai shi ne, mai karatu na k’aruwa da sanin mutuwa dole ce kan kowa, kuma kowane mutum yana mutuwa ne bisa ga sanadin da Allah ya tsara masa. Abu na biyu kuma shi ne, kowane mutum ya yi burin ya tsaya kan gaskiya, ya kuma mutu kan hanyar gaskiya domin ta hanyar gaskiya ce kad’ai ake k’aruwa da mutum, kuma bayan mutuwa ya samu sakayya ta gari a wajen Ubangiji. Ke nan a nan marubucin na so ne mai karatu ya kasance mai tsoron Allah da kiyaye gaskiya a kan kowane lamari, kuma koyaushe.
Ita ma Habiba Muhammad a littafinta mai suna Rashin Rabo marubuciyar ta fad’akar da al’umma ta fuskar nasiha kan wasu mata da suke ‘yan wuta tun a nan duniya. Ta yi wannan fad’akarwa da wani hadisin Annabi (S A W) kamar haka;
‘....Annabi (S A W) ya ce akwai ’yan wuta iri biyu wad’anda har yanzu ban gan su ba. Mata ma su sanye da tufafi amma kuma tsirara suke karkatattu ne da kuma masu karkatar da kawunansu. Kamar tozon rakumi, su ne ba za su shiga Aljanna ba, kuma ba za su ji kamshinta ba.’ (shafi na 6).
A wannan ga’ba nasiha ce ga jama’a, musamman mata kan had’arin da ke tattare da sa suturar da ba ta kare tsiraicinsu. Idan aka yi la’akari da kawo wannan hadisi marubuciyar na fad’akar da mai karatu ne dangane da yadda ya dace mata su yi sutura mai kauri da ‘boye sassan jikinsu. Rashin yin haka da sa sutura mai bayyana jikinsu alama ce ta ‘yan wuta.
3.2 FA’DAKARWA TA FUSKAR TUNATARWA
Tunatarwa kalma ce da tushenta shi ne kalmar ‘Tuna.’ A K’amusun Hausa (2006: 444), an nuna kalmar ‘Tuna’ na nufin komowar abin da aka mance a zuciya. Daga wannan ana iya cewa, kalmar tunatarwa a nan na nufin a fad’akar da mutum don tunatar da shi kan wani abin da ya sani, amma ake ganin ya yi sakaci kansa ko kuma ya manta da shi don ya koma zuwa gare shi don alherinsa ko ya nisance shi don sharrin da ke tattare da shi. Akwai wasu litattafan k’agaggun labarai da ke d’auke da fad’akarwa ta fuskar tunatarwa don masu karatu su amfana da abin da marubuta suke son su lurar da su kansa.
Littafin K’waryar K’ira wanda Yusuf Adamu da Ado Ahmad Gidan Dabino suka shirya a cikinsa an yi amfani da dabarar fad’akar da mai karatu ta hanyar tunatar da shi kan wasu abubuwa muhimmai na rayuwa. Ga yadda aka kawo ga’bar labarin;
‘Wata daga cikin k’awayen amarya mai suna Zurfa’u ta kada baki ta ce. ‘To amarsu mu ma za mu tafi, amma kafin mu tafi, mu na da wata tsaraba da muka zo da ita za mu baki. ...Sulaiha ga wasu muhimman abubuwa da za su taimakawa rayuwar aurenku kamar haka: Na farko biyayya. Mace na samun mallakar mijinta ta hanyar biyayya. Kuma biyayya shi ne mace ta bi umurnin mijinta a cikin komai matuk’ar bai yi umurni da sa’bon Allah ba. Sai abu na biyu, watau hak’uri, domin shi hak’uri babban sinadari ne ga zamantakewar aure. Hak’uri nau’i uku ne, akwai tsakaninki da mijinki, hak’uri bisa biyayya ga umurnin mijinki, sai hak’uri bisa hanawa ga abin da yake yi. Sai abu na uku, sanin ya kamata, k’ok’arin yadda za ki kyautata mijinki da faranta masa shi ne sanin makama. Sai abu na gaba kuma nah ud’u watau zumunci. Kyautatawarki ga iyayen mijinki da ‘yan uwansa da danginsa shi ne ake kira zumunci.’ (shafi na 100-101).
Bayanan da ke wannan ga’ba suna kasancewa fad’akarwa ta hanyar tunatarwa ga duk wanda ya karanta kan matakan kyautata zaman aure, musamman ga ‘ya’ya mata. A bayanin an kawo biyayya da hak’uri da zumunci wad’anda dukkaninsu muhimmai ne kuma sanannu ga mata wajen kyautata zaman aurensu. A nan marubucin na fad’akar da mata ne kan su rik’e wad’annan abubuwan, su yi aiki da su domin kyautata zaman aurensu da kuma mallakar mazajensu.
A cikin littafin In Da So Da K’auna na Ado Ahmad Gidan Dabino nan ma marubucin ya fad’akar da mai karatu kan wasu al’amurran da yake son a kula da su domin samun dacewa, musamman a halin zamantakewar aure. Ga yadda ya kawo fad’akarwar tashi;
‘To ma’abota soyayya, kun ga yadda ake rik’e alk’awarin soyayya da hannu biyu, ba irin yadda kuke yi ba, idan yarinya ce ta sami wani mai hannu da shuni sai ta watsar da talaka, haka idan saurayi ne ya sami wata kyakkyawa sai ya watsar da ta farko, ‘yan’uwana matasa a bar neman kyau ko kud’i a nemi na gari.’(shafi na 80).
A wannan wurin marubuci littafin ya yi fad’akarwa ta hanyar tunatar da mutane kan yadda masoya ya kamata su rik’e alk’awarin soyayyar aure a tsakaninsu. Haka kuma ya fad’akar da mai karatu kan ya kiyaye ga za’ben matar aure kan cancanta ba don kallon kud’i ko kyau ba. Da wannan mai karatu ya amfana dangane da yadda soyayyar aure tsakanin namiji da mace ya kamata ta kasance.
A wani shafi marubucin ya k’ara fad’akar da mai karatu kan illar aurar da yarinya kan tilas da irin abin da auren tilas ke kawo wa al’umma. Ga yadda ya kawo batun nasa;
‘Ka ga auren tilas ba k’aramar illa ba ce, domin yawancin ‘yan matan da suka shiga bariki, suke kuma iskanci, auran dole ne sanadiyyarsa. Su kuma iyayenmu saboda rashin tunanin abin da zai je ya zo sai su k’ek’asa k’asa su ce sai wanda suke so za a bai wa. Ai yanzu zamani ya canja, wanda yarinya take so a ba ta shi kawai ka sami zaman lafiya....’(shafi na 81).
Idan aka yi la’akari da wannan bayanin za a ga kasancewarsa fad’akarwa ta fuskar tunatarwa ga duk wanda ya karanta shi kan illar auren tilas ga yarinya. Auren tilas ke sa wasu mata shiga bariki da yawon iskanci. Ke nan marubucin na fad’akar da mai karatu ne kan a rik’a aurar da yarinya ga wanda take so tun da zamani ya kawo haka. Yin wannan zai sa a sami zaman lafiya cikin al’umma da kuma rage yawan lalacewar yara mata da ake fama da shi a yau.
Shi ma littafi Zama Da Kishiya Riba Ce na Isah Rasco Dangoma marubucin ya yi amfani da hikimarsa ya fad’akar da mai karatu wasu abubuwa da yake son ya kiyaye don kyautata zaman iyalinsa a koyaushe. Ya yi wannan fad’akarwa ta bakin jarumar littafin mai suna Hajaru inda mijinta Dr. Haliru ya tambaye ta abubuwan da ya dace mutum ya kiyaye idan ya yi amarya. Ita kuma Hajaru ta zayyana wasu abubuwa da suke zaman fad’akarwa ga wanda ya karanta littafin kamar haka:
‘Ya kira amarya da uwargida a falonsa ko kuma idan bashidafalo, to ya kira su a dakin uwargida domin yayi musu huduba. Ya nuna musu duk matsayinsu daya don haka duk wadda ke son ta zauna tare dashi to ta zauna da abukiyarta lafiya. Amma kada ka kirasu dakin amarya saboda uwargida na ganin kamar ka walakantata, kada ka yarda ka nunawa Amarya cewa uwargida banza ce gareka, idan kayi haka to ka haddasa fitina tsakaninsu. Saboda ita amarya ba zata sake ganin uwargida da darajja ba. (shafi 49).
Idan aka dubi wannan bayani za a ga cewa, wata muhimmiyar fad’akarwa ce ta hanyar tunatarwa ga mai karatu kan yadda ya dace ya shirya iyalinsa don samun zaman lafiya. Wad’annan abubuwa sun had’a da bayyana wa matansa matsayinsu d’aya da kare mutuncin uwar gida da ba ta girma ta hanyar kiran matan a d’akinta don hud’uba. Ke nan kula da wad’annan abubuwa da aiki da su zai iya zama wata kafa ta samun zaman lafiya a cikin iyalin mutum. Wannan tunatarwa ce marubucin ya yi a kaikaice ga mai karatu. A wani wuri a cikin littafin marubucin ya k’ara yin fad’akarwar inda ya kawo cewa;
‘Kada ka nuna banbanci ga ‘ya’yansu ma’ana ka nuna ga wanda kakeso fiye da wani. Ta wajen sutura duk kayi musu kala daya. Bawai ina nufin ka sayawa wadansu yadi dan Madina suko wadancan ka saya musu gisna ko miro wannan yana daya daga cikin abinda ke hadda fitina.’ (shafi na 49).
A nan marubucin ya fad’akar da mai karatu ta hanyar tunatarwa kan yadda ya kamata ya daidaita iyalinsa musamman ta gefen ‘ya’ya. Ya nuna rashin daidaita soyayya ga d’iyan kishiyoyi wata babbar matsala ce da ke haddasa fitina a cikin iyalin mutum. Wannan fad’akarwa ce ga mai karatu don ya san yadda zai yi mu’amala da yaransa, musamman idan ya zan yaran ba uwa d’aya suke ba.
Ya k’ara fad’akar da mai karatu kan abin da ya rataya a wuyansa na yin adalci a tsakanin matansa ta bakin Hajaru. Ya ce,
‘‘Babbar magana a wajen kwana ka raba daidai, kada ka rinka doguwar hira ga kwanan wata idan kwanan waccan yazo ka dawo da wuri ka tuna da Allah da ya halicceka kayi adalci.’’ (shafi na 50).
A wannan bayani za a ga cewa fad’akarwa ce ta hanyar tunatarwa ga mai karatu dangane da yadda ya kamata mai gida wanda ke da fiye da mata d’aya zai yi dangane da rabon kwana a tsakanin matansa inda aka nuna ya raba daidai. Haka kuma an fad’akar da mai karatu yin adalci da ya kamata ya yi dangane da lokacin kowace mace. Wannan zai sa mai karatu, musamman mai mata fiye da d’aya ya samu haske dangane da wani abu da zai kawo zaman lafiya a gidansa.
Har ila yau, marubucin ya k’ara kawo wani abu da zai fad’akar da mai karatu dangane da zamantakewarsa da iyalinsa don samun zama na gari mai lumana. Misali,
‘‘...Ka karantar da su ilimin jin tsoron Allah, kuma ka umurcesu da suji tsoron Allah ba wai suji tsoronkaba. Saboda idan sukaji tsoron Allah to tsoronka tilas ne garesu.’’ (shafi na 50).
A wannan wuri marubucin ya tunatar da mai karatu ne kan alhakin da ya rataya ga wuyansa na karantar da matansa ilimin addini da horon su da jin tsoron Allah. Karantar da mata addini shi ne mataki na farko na cusa musu tsoron Allah wanda kuma idan ya samu zai sa su yi biyayya ga miji don biyayya gare shi a inda ba sa’bon Allah ba tilas ce domin biyayya ce ga Allah. A nan marubucin na son mai karatu ya hankalta da wannan ne, ya kuma yi aiki da shi don samun zaman lafiya cikin iyalinsa.
A cikin littafin Turmin Danya, marubucin ya shigo da wani bayani da ke zaman fad’akarwa ga mai karatu ta bakin tauraronsa Mukhtar lokacin da yake lurar da wani abokinsa Kirista mai suna Ishaya. Ga yadda ya kawo batun;
‘Ji nan Ishaya, ko da yake addininmu ya banbanta, amma ni cikin nawa addinin akwai rashin jin tsoron kowa banda Allah. Wanda duk kake zaton zai iya yi maka wani abu, shi ma bai iya yi ma kansa maganin kome. Yadda bai iya kare kansa daga talauci, to haka baya iya kare kansa daga rashin lafiya ko mutuwa.’ ‘Ai muma addininmu, haka ya ce.’ (shafi na 64).
A nan marubucin na k’ok’ari ne ya tunatar da mai karatu cewa, a tsarin addini, ba a jin tsoron kowa sai Allah kad’ai. Haka kuma ba wani mutum da ke da iko na cutar da wani domin shi kansa bai mallaki iya yi wa kansa maganin komai a rayuwa ba. Ga wanda ya karanta wannan littafi a daidai wannan wurin musamman mai k’arancin ilimin addini zai amfana da sanin Allah ne kad’ai abin tsoro da neman biyan buk’ata a koyaushe.
3.3 FA’DAKARWA TA FUSKAR ILMANTARWA
Ilmantarwa hanya ce ta karantar da mutane da fahimtar da su wani abu muhimmi da zai taimaki rayuwarsa ta hanyoyi masu yawa. Marubuta littattafan k’agaggun labaran Hausa na amfani da hikimarsu ta rubutu don karantar da mutane abubuwa daban-daban na rayuwa ta hanyar shigo da wata ga’bar labari da za ta fad’akar da mai karatu lokacin karatunsa.
A littafin Za’bi Naka na Munir Muhammad Katsina an yi amfani da wasu kalmomi da suke zaman fad’akarwa don ilmantarwa ga al’umma inda marubucin ya yi amfani da yawun wani shaihin malamin addini da ya bud’a layar da aka sa wa wata mata a k’ark’ashin filo, bayan ya karanta layar sai ya ce,
‘To, ni a kan matsayina na malamin addini ba d’a d’ibbu ba, ban san wani batu ba na cewa ana iya rubuta ayoyin Alk’ur’ani a sha ko a yi laya da su ba, saboda a kashe ko a haukatar da mutum ba.’ (shafi na 20).
Idan aka yi la’akari da wannan wuri za a ga cewa, bayanan da ke ciki na fad’akar da wanda ya karanta da ilmantar da shi dalilin saukar da Alk’ur’ani mai tsarki shi ne karanta shi ake yi, ba wai amfani da shi don halakar da wani mutum ba ta hanyar laya ko sha ba. Haka kuma an fad’akar da mai karatu cewa, amfani da Alk’ur’ani don halakarwa aiki ne na malaman tsibbu, ba na malaman addini ba. Ke nan a kaikaice marubucin na jan hankalin mutane ne da ilmantar da su don su nisanci amfani da ayoyin Alk’ur’ani don cutar da kowane mutum don ba kan haka Allah ya saukar da shi ba.
A wani wuri marubucin ya k’ara fad’akar da al’umma ta hanyar ilmantar das u matsayin Alk’ur’ani ta bakin shaihin malami inda ya ce,
‘Ni dai iyakar abin da na sani game da K’ur’ani shi ne Allah ya aiko da shi ga jama’a don ya zamo jagora ga rayuwar ‘Dan adam a nan duniya. An hore mu, mu rik’a karanta shi a kullum, mu san fassararsa da manufarsa, kuma mu yi aiki da abin da muka fahinta. Amma ban ji an ce a yi magani da surorinsa ko ayoyinsa ba wajen hallaka wani ba. Saboda haka, ki tashi ki tafi gida. Ki dogara ga Allah, kada ki ji tsoron komai don ba abin da zai same ki matuk’ar kina da gaskiya.’ (shafi na 20).
Bayanan da ke wannan wuri na ilmantar da duk wanda ya karanta game da dalilin saukar da Alk’ur’ani mai girma a duniya da kuma horon da Allah Mad’aukakin Sarki ya yi game da amfani da Alk’ur’ani. Wannan dalilin kuwa shi ne Alk’ur’ani ya kasance jagora ga dukkan rayuwar d’an Adam. Daga cikin horo da aka yi wa ‘yan Adam ga lamarin K’ur’ani shi ne su karanta shi, su san ma’anoninsa, sannan su yi aiki da abin da suka fahimta. A nan marubucin na fad’akar da mutane ne su tsaya ga Alk’ur’ani inda Allah ya umurta, kada su wuce wuri suna sarrafa ayoyinsa da sunan halaka wani mutum. Haka kuma ya nuna duk wanda ya dogara ga Allah, ya tsaya ga gaskiya ba wani abu da zai same shi.
A cikin littafin K’waryar K’ira marubucin ya kawo wani bayani na ilmantar da mai karatu kan abin da ya kamata duk wanda aka kawo wa amarya ya aikata a darenta na farko don dacewa da sunnar Annabi (S A W) da samun albarka da kariya daga sharrin shaid’an a cikin aurensa. Ga yadda aka kawo wannan batu kamar haka;
‘Shi kuwa ango Muzaffar bayan da suka yi sallama da k’awayen amarya sai abokansa suka raka shi har k’ofar gida. Har sun yi sallama sai wani daga cikin abokansa da ake kira da Shamsu Ashago ya ce. ‘Ango Kar ka manta da sallah raka’a biyu da za ku yi kai da amarya. Sai kuma ka dafa kanta ka ce, ya Allah ina rok’onka alherinta da alherin da ka halicceta da shi. Sannan ina neman tsari daga sharrinta da sharrin da ka halicceta da shi....’ (shafi na 101).
A nan akwai abubuwa biyu muhimmai da ake fad’akar da mai karatu kansu a kaikaice. Na farko shi ne, ilmantar da ango da amarya su yi sallah raka’a biyu a daren farko. Na biyu, ango ya dafa kan amarya ya yi addu’a ga Allah don neman albarkarta da neman kariya ga sharrinta. Ke nan marubucin a wannan wuri yana fad’akarwa ne kan abu na farko da ya kamata ma’aurata su aikata a daren farko na aurensu.
Ita ma marubuciyar littafin Rashin Rabo, a nata k’ok’ari na fad’akar da al’umma ta yi amfani da yawun bakin wata tauraruwar littafin mai suna Yusra don ilmantar da mutane dangane da abin da Allah ya ce game da suturar mace Musulma da kuma yadda ya kamata mata Musulmi su fita. Misali;
‘Hijab shi ne mace ta suturce jikinta daga maza da ba muharramanta ba kamar yadda Allah mad’aukakin sarki ya ce: ‘Kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi kuma su yi lullubi da mayafinsu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su bayyana adonsu sai ga mazan su, ko iyayensu, ko iyayen mazan su, ko ‘ya’yansu, ko ‘yan uwanku na jini muharramanku.’ (shafi na 5).
Kawo wannan bayani wani k’ok’ari ne na fad’akar da al’umma ta fuskar ilmantar da su bisa ga abin da wannan aya ta tabbatar kan suturar mace Musulma. A nan marubuciyar ta fad’akar da mai karatu kan abin da ake nufi da hijabi a addinin Musulunci da kuma irin mutane da shari’a ta yarje wa mace Musulma ta kawar da hijabinta da bayyana adonta gare su kamar iyaye, da kakanni, da mazajen aure, da d’iya da kuma ‘yan uwa muharramai.
Shi Sulaiman Ibrahim Katsina a littafinsa na Turmin Danya ya yi irin wannan fad’akarwa don ilmantar da mutane matsayin Alk’ur’ani mai tsarki da tasirin addu’a ga wanda ya dogara ga Allah. Misali;
‘‘Alhaji ‘Dantalle baka ganin shi yasin yake yi ma yanka kamar yadda ka ce. Bayan kuwa Allah yana cewa Alk’ur’ani rahama ne, ya ya mutum zai yi anfani da wata aya ko sura wajen mugun abu. Har y ace, bata biyan bukata sai an yi mata yanka. Ka ga wannan nau’i ne na shirka. Saboda haka, ka ga in mun rok’i Allah, to zai fi taimakon mu fiye da shi. Tunda shi ya kauce hanya.’’ (shafi na 75).
Idan aka dubi wannan bayani za a ga cewa, wani abu ne na ilmantar da al’umma ta hanyar fad’akar da su kan matsayin Alk’ur’ani mai girma na kasancewarsa rahama ba abin da ake amfani da ayoyinsa ba don wani mugun aiki, balle dogara ga cewa, akwai aya ko surar Alk’ur’ani da biyan buk’atarta ya dogara ga sadaukar da wani abu gare ta. Haka kuma ya tabbatar da yarda da haka shirka ne zahiri. Marubucin ya k’ara fad’akar da jama’a cewa, Ba abin da ya fi ga Musulmi illa addu’a kan kowace matsala da ke barazana ga rayuwarsa.
Shi ma littafin Mallakin Zuciyata marubincinsa ya kawo irin wannan ilmantarwa ta bakin Malam Kalla da ya yi wa kakarsa kan fa’idar kowane nau’in ilimi na Arabiyya da boko. Misali;
‘‘Kakar ta ce, ‘‘Ai ilmin karatun Allah ake nufi ba na bokon banza ba.’’ ‘‘Lura, ai kowane iri amfani gare shi, in dai zai yi ma mutum amfani
cikin rayuwarsa. Kuma a makarantar bokon ma ana koya musu salla,
wanka, da alwalla da kuma tauhidi. Har ma da Larabci’’ (shafi na 20)
A daidai wannan sakin layi akwai ilmantar da mai karatu fa’idar neman kowane irin ilimi da kuma makarantar boko. Mai karatu idan ya karanta wannan wuri zai san irin abubuwan da ake koyar da yara a makarantun boko wad’anda ke da alak’a da addinin Musulunci irin Sallah da wankan sunnah da Alwalla da tauhidi da harshen Larabci. Ke nan wannan fad’akarwa ce ta fuskar ilimi ga mai karatu, musamman wanda bai san abubuwan da ake koyar da yara na addinin Musulunci a makarantun boko ba.
Balkisu Ahmad Funtuwa a littafinta mai suna Duniya Rawar ‘Yan Mata 1 ta kawo irin wannan fad’akarwa ta fuskar ilmi kan abubuwan da suka kamata a kula da su wajen amincewa da mutumin da za a ba wata mata aure. Misali;
.....Idan ba ta manta ba malaminsu na islamiyya yace
masu wanda ya halatta a baiwa aure sune baligin da ya
malaki addininsa, kyawawan d’abi’u, sana’ar da zai iya
rik’e iyali sai mahalli, to me kuma zata nema wajen halifa? (shafi na 5-6)
Bayanan da ke wannan wuri suna ilmantarwa ne cewa, mutum wanda ya fi dacewa a ba mace aure shi ne baligi mai addini, mai halaye na gari, kuma wanda ke da wata sana’a da zai kula da iyalinsa. Ke nan marubuciyar a wannan wuri ta fad’akar da jama’a ne kan mataki na farko muhimmi da ya dace a kula da shi wajen ba namiji mata aure. Wannan kuwa bai shafi tarin dukiya ko muk’ami ba.
4.0 KAMMALAWA
Idan aka kalli bayanan da suka gabata da misalan da aka tsakuro daga littattafan da aka yi amfani da su, sun nuna lamarin k’agaggen labarin Hausa ya wuce abin da aka fi zato gare shi na nishad’antarwa kawai. Misalan sun tabbatar da ana tsintar dami a kala ta inda ake samun wasu bayanai masu fad’akar da mai karatu ta hanyar nasiha ko tunatarwa ko kuma ilmantarwa kan abin da zai taimaki rayuwarsa duniya da lahira.
Wani abu da binciken ya ci karo da shi cikin littattafan shi ne yadda aka karkasa fad’akarwa gida uku wanda marubutan suka yi amfani da shi don jan hankalin masu karatu da wayar musu da kai kan abubuwa daban-daban. Wannan na nuna cewa, bincike a littattafan k’agaggun labaran Hausa zai ba da dama ga hango k’arin wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar Hausawa ta kowane gafe.
Daga k’arshe, binciken na fatan wannan ya zama dalilin bud’e wata kafa muhimmiya ta ci gaba da bincike don gano wasu muhimman abubuwan ilmantarwa da ke k’unshe cikin k’agaggun littattafan.
5.1 MANAZARTA
https://www.amsoshi.com/contact-us/
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.