Ticker

    Loading......

Wakar Jam’iyyar PDP (Alhaji Musa Danba’u Gigan Buwai)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

www.amsoshi.com

Rubutawa: Shehu Hirabri 
08143533314


Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: In mutum zai shiga fati,

Ya zauna ya yi lassafi×2

Ya duba shi da kyau,

Yara:    Ya gane wa naɗ ɗauko shi.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ga ɗan asali,

Da shi da Ɗanmasanin Sakkwato,

Ga Azzika Tambuwal da Tambari na Tafida,

Ga Modi na Yabo Maigida babban jigo,

Wanda yac ce bai son ku babu shakka wawa ne,

Yara:    Ko a Sakkwato birni waɗanga su ne am manya.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

 

 

Jagora: Na yi mamakin wane,

Don siyasa ta hurce,

Shi muddin yag ga nan,

Ya canza man huska,

Ga siyasa ta dawo,

Ga mu mu ku mun dawo,

An ce a haɗe,

Ba mu buƙata ‘Danba’u,

kowa ya tsaya wutinsa

A buga a gani,

Yara:    A gane wa zai rinjaye.

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: ‘Yan siyasa ku yi hanƙuri da Musa ‘Danba’u,

Kun san ku nawa ne,

Sannan ni naku ne,

Ko da kun ƙi ni mai kamata kuka so,

In kuka ƙi ni da ɗa,

Yara:     Kun ganan da jika na goya.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Dubara batutuki dubara banza ce,

Yara:    Ya kiraye ruwa kuma mun ga alamar sun ci shi.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ko cikin mata,

Wance ‘yar jidalin mata ce,

Kullun habshi takai,

Kamar karya zango,

Yara:   An yi an ƙare ke bakin jidali ya hwarma,

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ku ‘yan mata,

Akwai jawabi wajanku,

Dud da macce ka kwakwa,

Ba za ta samun aure ba,

Yara:   Sai a gan ta ga titi tana ta yawon iskanci.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Wanda duk ke kwakwa,

Ba mutumen kirki ne ba,

Yara:    Daga ɗan ƙwaya sai ɗan dara sai ko ɗan daga.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Wanda duk ke APP,

Ba mutumen kirki ne ba,

Yara:    Daga ɗan ƙwaya sai ɗan dara sai ko ɗan daga.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Babu mai cin bashi,

Cikin siyasar PDP,

In kana son ka shigo,

Cikin siyasar PDP,

Ka biya bashin banki,

Ka je mu je tare da kai,

Kar tafiya ta yi nisa,

Yara:    Ka je ka goga man laɓo.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ga ɗan’asali,

Uban su Nasiru Dattijo,

Harsashe kai ka maganin,

Mai taurin kai,

Yara:   Baba alƙawali na,

Da ni da kai kyautar mota.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Alhaji Hadi ciyaman,

Hadi Ɗanmalan,

Yara:   Na sarkin baƙi,

Ka kashe kwakwa wajenmu.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ashe wane barazanarka,

Aikin banza ce,

Ba ya da kowa,

Garinsu ko ran shi ɗai ne,

Yara:   Mun ji labarin ko gidansu,

An ce ya sai da.
 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Raƙumi na tafiya,

Ɗauke da kayanai,

Ya isko kunama yat taka,

Naj ji ya buga rura,

Ƙasa akwai shaggu,

‘Yar abig ga ‘yar tcito,

Ga shi yanzu ta halban,

Yara:    Har na gaza ɗaukar kayan nan.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi ƙoƙari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ga wani ɗan takara da doro,

Abu dai zuƙwi-zuƙwi,

Ke kuma bushiya ki ɓoye doronki,

Yara:    Ba ki bakin komai,

Wurin hwarauta banza ce.

 

Jagora: Na ga baki bakin komai,

Yara:   Wurin gwarauta banza ce.

 

Jagora: Maigida Modi na Yabo,

Maikiɗa ya gode ma,

Yara:   Ban rena mai ba,

Tun da hairan yab ba mu.

 

Jagora: Bana Duna baƙin kare Dubara ta ƙare,

Kai dare ɗauke ƙafarka,

Na ga gungun ‘yan yara,

Yara/Jagora:   Kar su ɓata ma tsari.

 

Jagora: Mutane na tcegumi,

Suna mamakin shigar da ni yi a PDP,

Yanzu ba mamaki tunda akwai babba huja,

Yara:    Wanda bai ra’ayi na ba ni buƙatar kayansa.

Post a Comment

0 Comments