Nahawun Magana (Jereken Biyar Diddigin Ma’anar Magana da Rabe-Rabentaa Bahaushen Tunani)

Daga

Aliyu Muhammadu Bunza
Faculty of Humanities and Education
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau.

Takardar da aka gabatar a Sashen Nazarin Hausa Adamu Augi College of Education Argungu, Kebbi State, a bukukuwan Makon Hausa, 28 ga Maris, 2017 da k’arfe 10:00am na safe a dakin taron na Sashen Hausa
www.amsoshi.com

Gabatarwa:


Magana ita ce mutum, da ita ake rarrabe shi da sauran halittun dabbobi, k’wari da tsuntsaye. Kowace iri martaba da d’aukaka d’an Adam yake da ita idan ya rasa magana ba su da wani tasiri a rayuwarsa. Magana ita ce cigaban d’an Adam ta farko gabanin ya iya sarrafata a rubuce wani ya karanta ta a fahince shi. Tunanina na gabatar da wannan muk’ala shi ne, a fayyace nahawun magana gwargwadon yadda d’alibin harshe zai gano cewa, lallai nazarin harshe ba k’aramin d’aukaka gare shi ba ga rayuwar d’an Adam. A fahintarmu, mu d’aliban Hausa, sirrin sanin magana da iya ta yana cikin sanin nahawunta. Matuk’ar ba a san nahawunta ba, ba a gane bakin zarenta. To, mene ne nahawun magana?

Nahawun Magana:


A iya d’an bincikena, Farfesa Isa Mukhtar ne manazarci na farko da ya yi zuzzurfan bincike kan “nahawun Wak’a” a digirin MA Jami’ar Bayero, Kano. A tak’aice, nahawu kalmar Larabci ce. A Larabci tana nufin “ma’ana” ko a ce “kamar” ko “misali” ko “daidai”. An ce, Sayyidina Aliyu (RA) ya fara fito da ita ga ajamawan da ba su iya Larabci ba, in sun karanta ko fad’a a kan kuskure, ya ce “nahwi haazaa” ko “nahwu kazaa”. A fagen karatu, “nahawu” ya fara cin gashin kansa da sunan daidaita magana da biyar k’a’ida ga ma’abotanta bisa ga tsarin yadda suke fad’arta, furtata, jeranta kalmominta su gina jimlar da za ta fito da ma’anar da za a gane abin muradi ba da mamare ba. Ashe ke nan, nahawu shi ne fasalta abu dalla-dalla yadda za a kakka’be masa kowace irin k’urar da za ta hana a fahimce shi. Burina a wannan d’an bincike shi ne, fayyace ma’anar abin da ake cewa “magana” wadda d’aliban nazarin Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa za su yi madogara babba a kai. Haka kuma, ma’anar ta fito da sigogin da kowane Bahaushe d’an asali zai kama ma’anar abubuwan da aka k’walailaice kai tsaye.

 

 

Sunayen Magana:


A nawa tunani, ina ganin zai fi dacewa mu fara bijiro da ire-iren sunayen da Bahaushe ke yi wa “magana” domin da an ji su, an san magana yake nufi. Bahaushe na yi wa magana suna da: magana, batu, zance, shirme, shi’ba, batutuwa, d’umi, maganganu, sabbatu da sauransu. Bari mu k’walailaice su mu gani:

Magana: wadda ake furtawa a baki ko a yi nuni da wani abu da za a fahinci abin kai tsaye. Ga wata wak’a ta Tashe da yara suka fassara magana:

Jagora:        Ke magana ke!

Wata magana ta wuce baki

Yara  :         Da d’uwawu aka yin ta.

 

Batu  :         Yana d’aukar wata magana ta musamman kamar zancen sharholiya in ji Narambad’a.

Gindi:        Gwarzon shamaki na malam toron giwa

:         Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Zance:        Magana ce musamman a fagen yin hira da wani ko wasu a fad’ar Ak’ilu Aliyu

Hana mata lek’a wajen matanka

Don kar tai musu zancen banza.

(Wak’ar ‘Yar gagara).

 

Shirme: Maganar da ba ta da ga’bar kamawa. Ma’anarta ta k’i fita

sarari.

Ban gane abin da yake fad’a ba. Shirme kawai yake yi, ba ya da hankali.

 

Shi’ba: Maganar da ba ta kama hankalin kowa. A fassarar Kaftin

Umaru ‘Da Suru ita ce.

Bakunansu sai warin taba

Me suke fad’a in ban da shi’ba.

 

 

Batutuwa: Jam’in “batu” ke nan, amma ana amfani da ita ga

maganar fitar hankali irin kirari kamar yadda Sambo Wali Gid’ad’awa ke cewa a wak’ar Janborodo:

 

Da sunanka Alla za ni fara batutuwa

Tunawa da manya masu yak’i  da garkuwa,

Fito-na-fito ka yi ta ba ta k’idayuwa,

Yabon bajini ad dole don ba ya gasuwa,

Zaman ba a giwa da raskwana ba ya faruwa.

 

Jagora:        Ya watse batutuwa na Jekada ya taho gida

Yara  :         Kunya ga ta nan gare ku mutanen banza

Gindi :         Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:         Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Jagora:        Batutuwan da nikai don mahassada su ji haushi

Yara:           Wad’anga yanga da kara, wa ka rufa ma baki?

Gindi: Koma shirin daga gwarzon bahago d’an Iro.

 

Dumi: A Sakkwatance idan an ce d’umi ko d’umumuwa ana danganta su da magana maras tushe ko ta banza.

Magangannu: Magana tilo ce jam’inta maganganu. Maganganu su ne zantukan fitan hankali na rud’ewa da raki da jin tsoro.

Sabbatu: Magana ce da ake yi cikin ‘batar hankali. Ga yadda Sambo Wali ya ruwaito ta:

 

Idan an ka ce ga Bube duk sai su raurawa,

Maza sai su zan mata suna ‘yan batutuwa

Na sai’bi da sabbatu k’afafunsu na rawa.

(Wak’ar Janborodo).

 

Nauyin Magana:


A tunanin Bahaushe, cikin fashin bak’in nahawun magana akwai nauyin magana. A awon nauyinta, a wajen Bahaushe, akwai babba, akwai k’aramar magana. Babbar magana ita ce ke buk’atar kulawar gaggawa da fuskanta gadan-gadan. Gaskiyar Bahaushe da yake da karin maganar: babbar magana d’an sanda da ya ga gawar soja. Ita kuwa k’aramar magana, ma’anarta na kai tsaye shi ne tsegumi ko tsince ko an-yi-an-ce. Ita k’aramar magana tana da harshen damo. Takan kasance doguwar magana wadda sai an yi tonon silili da taliyo. Tana kuma zama gajeruwar magana kamar a ce, wanda ake bi bashi ya tabbatar da ana bin sa, kuma yana da abin biya, sai biya kawai, maganar ta zama gajera.

Sifofin Magana:


Duk da yake magana ba a ganin ta, jin ta ake yi, a wajen Bahaushe tana da sifa ko sifofi. A tunain Bahaushe akwai, Bak’ar magana da maganar arziki. Duk wata magana da ba ta arziki ba, bak’ar magana ce don haka idan aka yi masa ita yakan ce: “Barka da ta fito bakin mai ita ba ta kashe shi ba”. Bakar magana maganar jin haushi ce da takaici da jiyewa mai mugun zafi ga rayuwar wanda aka yi wa ita. Malamin kid’i Narambad’a na cewa:

 

Jagora:        Bak’ar magana ba ‘baci ce ba

Yara  :         Amma ta d’ara, ‘baci zahi

Gindi :         Gogarman Tudu jikan Sanda

:         Maza su ji tsoron d’an mai Hausa.

 

Maganar arziki sananniya ce, irinta ce wadda Garugaru ya yi wa Kassu Zurmi yana cewa:

Jagora:        Maganar garugaru tai mani dad’i,

:         Tamkar na dama zuma na sha.

 

A ganin Bahaushe, kowace magana mai dad’i maganar arziki ce, wadda duk ba ta da dad’i bakar magana ce.

Hukuncin Magana:


A al’adance, ana hukunta magana ta fuskar nahawun ma’anarta. Kai tsaye za a ce: Wannan maganar daidai ce, kure ce, gaskiya ce, k’arya ce, ba’a ce, raki ce, sai’bi ce, ga su nan dai. A nahawun wad’annan zantukan za mu yi musu turke da wad’annan sassan adabi:

 

 

Daidai: ‘Dan’anace na cewa:

 

Jagora:        Mai son miya ya auri tsohuwa

:         Mai son shimfid’a ya auri budurwa

:         Mai son d’an k’warai ya auri isassa.

(Wak’ar Shago)

 

Wa zai ji wannan ya ce ba daidai ba ne.

 

Kure:          “Muna cikin tuwo muna cin zaure ko da an ka yi kura ga

walk’iya tsugunne”. Babu ga’bar da babu kure a wannan maganar.

 

Gaskiya:    Narambad’a ya kawo bayaninta da yake cewa:

 

Jagora:        Na hore ki gaskiya bari tsoron k’arya

Yara  :         Mai k’arya munafuki Allah su yak’ k’i

:         Har yau ba mu ga in da an ka yi mai k’arya ba.

Jagora/Yara :         Amma ita gaskiya gari da mutane tay yi

Gindi :         Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa,

:         Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Ba’a: Magana da za a yi don raha da nishad’i, kowa ya ji ta ya san ba’a ce, ba da gaske ake ba. Tsawon hancin Bazaurar da Sani ‘Danbold’o ya so ya aura ya ce:

Jagora: Ya kai mil goma misalin dogon hanci.

(Wak’ar Zaura: Sani ‘Danbold’o).

 

Idan hancin ya yi mil goma, yaya misalin tsawon k’afa da hannu da fad’in kai da tsawon wuya? Wa zai gan ta ya tsaya zancen aure? Tun da cikin wak’a maganar ta fito Bahaushe zai ce: “Kai wannan mutum da ba’a yake”.

Raki: Magana ce da ake yi cikin tsananin sumalin zafin rauni ko wani bone da aka fad’a a ciki. Dubi yadda Bakwai ya yi da kunama ta harbe shi in ji Garba Maitandu Shinkafi:

Jagora:        Yay yi kwance yac ce: “Yo, na mace”

:         Ku ba ni ruwa in mace ga sanyi ga mak’oshi

:         Danginai sun ka ce: “Mun d’aukai mu aza shi

:         Nan ga jakinmu mu kai gida”

:         Yac ce: “In kun aza ni, to ita wannan k’afar

:         Ina mai d’auka muku”?

:         Ni kun san ba ni son tana reto

:         Ba ni son ta sha hantsi

:         Na hi son ku ruga ku bid’o gado

:         To kuma in na mace

:         Ku kad’a ni cikin haki

:         Da kaina da k’afafu da baina ciwo sukai

:         Kunama ta sa ni dumdumi Ala ebe mata,

:         Ni ko nac ce: Bakwai ka bar zagi

:         Tun da in kana zagi ba ta fad’uwa sai ciwo take

:         Bakwai yac ce: “Nai shiru rufa kat ta jiya

:         Tana cikin d’aki ban kashe ba

:         Ka san in taj jiya kare in kai ma kid’i.

Gindi :         Kunama zan wa kid’i

:         Zaman ciwo ag gare ta

:         Ta halban na jiya

 

Wad’annan kalamai masu kama da na fitar hankali da aka yi saboda rad’ad’i da zagin ciwo su ake cewa “raki”. Duk wata magana irinta sunanta raki.

Sai’bi/Santi: Magana ce wadda ke fita a bakin wanda matsananciyar

yunwa ta kama, yana cikin juyayi aka gabato masa da abinci mai kyau mai dad’i irin wanda ransa ke so. An ce, wani Bafulatani ya sha furar shinkafa mai zuma a garin Maradun, yana cikin sha sai ya tuno da wani d’an wak’a cikin wak’ok’in Shata ya d’ora hannu a kunne ya rera.

 

‘Danfulani   : Kaka ta yi uban zimma

: Gyara ta fara zar fata!

Zamfarawa  : Haji Garban Bici yai damu.

 

Azancin Magana:


Fagen k’ididdige azancin magana nan sirrin nahawunta yake. Cikin azancinta za a ci karo da: Kairn Magana, Salon Magana, Kirari, Dad’in Baki, Wak’a, Zantukan hikima, da sauransu. A nan ce zuciyar nahawun magana yake, domin nan ne za a fito da nahawun azancinta duka.

 

Karin Magana:


Zantukan hikima ne da aka gada kaka da kakanni. Jimla ce gajeruwa mai d’auke da ma’ana mai fad’i:

Magana zarar bunu

Maganar duniya iyawa ce,

Magana ba taka ba bi ta da ihm!

Wata magana sarakuwa baki ce

Baki abin magana

Magana daga bakin wawa.

 

Salon Magana:


Maganganu ne na nuna k’warewa ga harshe da iya sarrafa shi.  Ga d’an misali:

Da Kalla da abokin Kalla sun tafi kallon kalangu, sai aka kalle Kalla mari wajen kallon kalangu, sai aka ce wa abokin Kalla maza kalla gida da gudu ka gaya wa matar Kalla ga Kalla can an kalle da mari wajen kallon kalangu. Ya kalla da gudu, ya kalla wa matar Kalla kira cewa, ga Kalla can an kalle da mari wajen kallon kalangu. Ta kallo kara, da gudu domin ta kalla wa wanda ya kalla wa Kalla mari wajen kallon kalangu. Da ganin ta da kallallen kara ya kalla da gudu don kat ta kalla masa shi da ya kalla wa Kalla mari wajen kallon kalangu.

Kirari: Magana ce da aka tsara cikin tsayayyun kalmomi masu shiga zuci da kururuta wanda ake yi wa shi ko babu kid’a ya tsimu. Ga yadda makad’a ‘Dan’anace ya kod’a Shago:

 

:         Kutu’bi abin aza wa ruhewa

:         Samji irin hakin da ka ramno

:         Burundumi abin zuba shara

:         Yaro hattaraka ga sababi nan

:         Ka da aradu ta farma

:         Halan dai ba ka san halin k’anen ajali ba?

:         Laapirwaa! Akai miki gawwa!

:         Sanu da d’ibas shed’a

:         Mutuwa ke dad’e kina kashe bayi

:         To, to, to!------

 

Duk Bahaushe ya ji saukan amon wad’annan kalmomi zai ce, an zuga Shago ko ya ce: “Wannan kirari ya yi”. Hawa da saukan kalmomin kirari ba irin na yabo ne ba ko rok’o ko wak’a. A ko’ina aka ji zugugutawa da cicci’bawa ta yi yawa za a ce kirari ne aka yi.

Zantuka Hikimomi/Wak’a/Dad’in Baki: Wad’annan duk nau’o’i ne na magana kuma duk sai sun bayyana a cikin wak’a za a ce, ta wak’u, ko ta yi dad’i. Azanci da hikima da dad’in baki su ne wak’a. wani mawak’in tashe na cewa:

 

Jagora:        Sai dai a fi mu kalangu da kurkutu

Yara  :         Amma ba a fin mu dad’in baki,

Gindi :         Yau da borin goje,

:         Kana da borin tashe.

(Ayya Mai Wak’ar Tashe Tak’aji).

 

Maganar Zuci da Nahawunta:


Maganar zuci ita ce maganar da ke cikin k’irjin mai ita, amma ta kasa ta bayyana saboda wani hali da aka shiga ciki ko wani yanayi da aka samu kai a ciki. Garba ‘Danwasa Gummi ya hikayo maganar zuci wurin da yake nuna bala’i ya kai ga sarki ya fito ba nad’i, a bar gari ba shiri, ba a san ina aka dosa ba. A cikin wannan hali ya ce:

 

Jagora:        Maigida bai kula mata ba

:         Rannan ko da ana d’umi sai maganar zuci.

Gindi :         Ya san ‘yan maza gudu ba da la’bewa ba…

 

Idan ana cikin wannan hali wasulan da ke sa a daidaita nahawun maganar zuci su ne: tsaki, nishi, kuwwa, ajiyar zuciya, kuka, dariya….

Sakamakon Nazari:


A tunanin Bahaushe ma’anar magana ya fi zare tsawo. Duk abin da baki ke furtawa a fahimce shi, ya zama magana. Hanyoyin da ake bi na nuna duk suna cikin nahawun magana amma maganar da ake furci da baki ita ce maganar da nahawunta ba ‘boye yake ba ga manazarta. A fagen nazari, matuk’ar ana son a fayayce magana, kalmomin da ke cikinta, da yanayin da aka furta ta, da mai furucinta, ba su ne nahawunta ba. Nahawunta na nan cikin sunanta daga cikin ire-iren sunayenta da za ta d’auka, da nauyinta a sikelin nahawun al’adar magana, da sifarta ga yadda ma’anar ta zai d’auka, tilas a fayayce hukunce-hukuncen da za ta hau in ana son a yanke mata hukunci. Magana tana k’unshe da azanci mai yawa, a nan za a yanke mata hukunci kasancewarta wak’a ko wata taska daga cikin taskokin adabin baka. Duk wad’annan abubuwa suna rataye ga maganar da aka furta, maganar da ba a furta ba, ita ce maganar zuci ‘yan rakiyata su ne tsaki, k’yaci, nishi, kuka da sauransu. Yana da kyau kowace magana aka tunkara a bincike a san ina gurbinta.

 

Nad’ewa:


Da gangan na yi wa takardata taken: “Nahawun Magana” domin na san kowace magana da muhallinta shi ne nahawunta kuma da shi za a yi mata hukunci. Ba a d’auko zancen wak’a a salon kambamar zulak’e a ce, k’arya ce aka shara domin muhallin wak’a muhallin ba’a ne da raha. Da jin maganar Santi ba irin ta raki ba ce. Idan d’alibin bincike zai ci karo da kowane irin magana a fagen nazari ya tabbata ya aza ta a kan gurbinta wanda shi ne nahawunta gabanin ya fed’e ta biri har wutsiya. Sanin nahawun magana shi zai sa mai magana ya lura da maganar da ake so da wadda ba a so. Kasawar sanin nahawun magana alamun ta’buwar hankali ce, in ji Malamin wak’a Narambad’a, domin ya ce:

Jagora:        Kai magana an ce maka tsaya

:         Ka sake an ce maka bari

Yara:           Kai magana ka san ba a son ta

J/Y    :         Ka k’i bari waz zan mahaukaci?

Gindi: Ya ci maza ya kwan yana shire

:         Gamda’anan sarkin Tudu Alu.

 

MANAZARTA


 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

1 Comments

  1. mun code hashakin malami a fagen Mazarin harshen Hausa Allah ya karawa rayuwa albarka

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.