DAGA
RABI YUSUF
FAUZIYYA ABUBAKAR WAZIRI
SAMIRA SHEHU AHMAD
SASHEN HAUSA TSANGAYAR HARSUNA, KWALEJIN ILIMI DA KERE-KERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU, JAHAR ZAMFARA.
SADAUKARWA
Mun sadaukar da wannan kundin bincike na samun takardar shaidar malanta ta ƙasa
(NCE) a Sashen Hausa na kwalejin Ilimi Da Ƙere-Ƙere da ke Gusau a jihar Zamfara
ga mahaimafanmu Alhaji Abubakar Waziri da Alhaji Yusuf ‘Dan Ƙane da Alhaji
Shehu Ahmad da kuma ‘yan ‘uwanmu. Allah ya saka masu da Alheri. Amin.
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai kowa mai komai da ya ba
mu rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.
Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi
Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun
farko har ya zuwa ranar ƙarshe.
Dunƙulalliyar godiya cikin girmamawa zuwa ga mahaifanmu: Alhaji Abubakar Waziri
da Alhaji Yusuf ‘Dan Ƙane da Alhaji Shehu Ahmad da kuma ‘yan uwanmu yayyenmu, ƙannenmu,
ƙawanyenmu da masoyanmu tareda da abokan arziki, domin su suka ba mu dukan
taimako da goyon baya da ya kamata musamman a wannan karatu namu.
Haka kuma muna miƙa kyakyawar godiyarmu ta musamman ga malamanmu Na
wannan sashe kamarsu; Malam Habibu Lauwali Ƙaura wanda ya ɗauki tsawon
lokacinsa yana kula da aikinmu har Allah ya sa aka kawo ƙarshe Allah ya saka
masa da mafificin alherinSa amin. sai Shugaban Sashen Hausa (H.O.D) Malam
Haruna Umar Bunguɗu, Shugaban Tsangayar Harsuna (Dean) Malam Surajo Guluba,
Mal. Ibrahim ‘Dan’amarya, Mal. Aminu Saleh, Mal. Husaaini Aliyu da sauran su.
Godiya ta musamman ga Malam Hamisu tare da ‘yan uwa da abokan arziki baki ɗaya,
dafatan Allah ya saka masu da mafificin alhrinSa. Amin.
JINJINA
Hausawa kan ce, “yabon gwani ya zama dole” wannan haka ne, don haka dole mu
jinjina ma malaman mu musamman Mal. Habibu Lauwali Ƙaura da ma wasu daga cikin
mutanen da suka taimake muna da wasu shawarwari da gudummuwa, da goyon baya da
suka bamu, wajen samun bayanai masu gamsarwa domin wayar da kan dalibai da ma
duk masu neman ƙarin haske dangane da nazari da muka gudanar a kan “Baƙo Ra’ba
‘Dan Gari Kaba: Nazari A Kan Tasirin Baƙo A Cikin Karin Maganar Hausawa” muna
masu roƙon Allah ya saka masu da maifificin alheri. Amin.
ƘUNSHIYA
Shaidantarwa -
-
-
-
- -
-
- ii
Sadaukarwa -
-
-
-
- -
-
- iii
Godiya
-
-
-
- -
-
-
- iv
Jinjina
-
-
-
- -
-
-
- vi
Ƙunshiya -
-
-
-
- -
-
- vii
BABI NA
‘DAYA
1.0 Gabatarwa
-
-
-
- -
- 1
1.0.2 Yanayin Bincike - -
-
-
-
- 2
1.0.3 Muhallin Bincike -
-
-
-
- 3
1.0.4 Hanyoyin Gudanar da Bincike
-
-
- 4
1.0.5 Manufar Bincike
-
-
-
-
- 5
1.0.6 Matsalolin Da Suka Taso -
-
-
- 6
1.0.7 Matsalolin Da Aka Fusakanta -
-
-
- 8
BABI NA
BIYU
2.0 Gabatarwa
-
-
-
- -
-
- 10
2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata
-
- 10
2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa -
-
-
-
- 16
2.0.3 Kammalawar Babi -
-
-
-
- -
17
Babi Na
Uku
3.0 Rubutun Zube
3.0.1 Ma’anar Rubutun Zube
3.0.2 Ire-Iren Rubutun Zube
3.0.3 Tarihin Rubutun Zube A Ƙasar Hausa
Babi Na
Huɗu
4.0 Jigo
4.0.1 Jigon Turmin Danya
4.0.2 Warwarar Jigo
4.0.3 Ma’anar Zubi Da Tsari
4.0.4 Ma’anar Salo
4.0.5 Ire-Iren Salo
4.0.6 Salon Littafin Turmin Danya
4.0.7 Ma’anar Taurari
4.0.8 Taurarin Littafin Turmin Danya
4.0.9 Manyan Taurarin Littafin Turmin Danya
4.0.10 Ƙananan Taurarin Littafin Turmin Danya
4.0.11 Muhimmanci Littafin Turmin Danya
Babi Na
Biyar
5.0 Jawabin Kammalawa
5.01 Shawarwari
5.0.2 Ta’arifin Wasu Kalmomi
Manazarta
Babi Na
‘Daya
Gabatarwa
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (SWT) da Ya ba mu damar gudanar da
wannan bincike a kan wannan littafi na “Turmin Danya”.
Mun yi wannan bincike ne domin mu bayar da tamu gudunmuwa wajen bunƙasa sashen
Hausa, don haka mun rututa wannan bincike ne mai taken “Nazari A Kan Littafin
Turmin Danya” don amfani ga masu nazarin harshen Hausa.
Maƙasudin yin wannan binciken shi ne, saboda kwaɗaitar da masu sha’awar harshen
Hausa, musamman saboda masu sha’awar gudanar da bincike a irin wannan fage na
nazarin Adabi wanda ya danganci zube.
Domin samu sauƙin gudanarwa mun kasa wannan aikin namu a kan tsarin babi-babi
har babi biyar.
Babi na farko za mu kawo bayani ne a kan Gabatarwa, Yanayin Bincike da Manufar
Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin Da
Suka Taso da kuma Matsalolin Da Aka Fuskanta.
A babi na biyu kuwa nan ne za mu yi tsokaci dangane da Waiwaye A Kan Ayyukan Da
Suka Gabata da kuma Salon Nazari Da Tsarinsa.
A babi na uku za mu yi bayani a kan Rubutun Zube da Ma’anar Rubutun Zube da
Ire-Iren Rubutun Zube da kuma Tarihin Rubutun Zube A Ƙasar Hausa.
Babi na uku nan ne za mu yi tsokaci a kan Ma’anar Jigo da Jogon Turmin Danya da
Warwarar Jigo da Zubi da Tsarin Littafin Turmin Danya da Ma’anar Salo da
Ire-Iren Salo da Salon da ke cikin Littafin Turmin Danya. Mun kuma yi bayanin
Ma’anar Taurari tare da yin bayanin Taurarin da Ke A Littafin Turmin Danya
Manya Da Ƙananansu, sannan za mu bayar da Muhimmancin Littafin Turmin Danya.
A babi na biyar kuwa nan ne za mu yi bayani a kan Jawabin Kammalawa da
Shawarwari sai Ta’arifin Wasu Kalmomi.
Yanayin
Bincike
Kamar yadda aka sani mun gano cewar akwai buƙatar mu yi nazari a kan wasu
bayyanai da marubuta suka yi a kan wannan binciken kuma mun gano cewa, mu
yi Nazarin wannan Littafi na “Turmin Danya” , don haka muka ga ya kamata mu
gudanar da wannan binciken domin zuwa gaba ko kuma mu ce domin masu
tasowa yanzu da su san cewa wannan lttafi yana rawar da yake takawa a cikin
adabin Hausa.
Haka kuma a yunƙurinmu na gudanar da wannan aikin Binciken mun sha wahala sosai
saboda rashin samun wasu litattafai da suka yi Magana a kan wannan aiki namu.
Haka kuma yawace-yawacen da muka yi wajen samun wasu bayanai ya sa mun wahala
matuƙa.
Muhallin
Bincike
Wannan bincike mun gudanar da shi ne a ‘bangaren adabin Hausawa, sai dai domin
samun sauƙin gudannarwa mun ke’bance aikin namu a kan littafin Turmin Danya
wanda Sulaiman Ibrahim Katsina ya rubuta
Hanyoyin
Gudanar da Bincike
Wannan ya rataya ne a kan wasu hanyoyin tattara bayanai daban –daban na
marubucin littafin ko mai aikin bincike na wasu ayyuka waɗanda suka gabata
domin yin nazari a kan binciken da ake gudanarwa domin samun ra’ayoyi
daban-daban.
Bayan wannan akwai wata hanya wadda mai bincike ke bi domin samun ra’ayoyi
daban-daban don ƙarin haske ga aikinsa na bincike da yake gudanarwa, wato ta
hanyar tambayoyi ga ma’abuta wannan ilimi.
Kamar yadda bayani ya gabata mun lura da cewa, dukkan mai aikin bincike
dole ne ya yi amfani da littafai daban-daban domin samun ingantu da kuma
cikakkun bayanai masu gamsarwa. Haka kuma mun mayar da hankali a wurin gudanar
da wannan bincike namu domin kuwa har ɗakunan karatun wasu manyan
makarantu mun leƙa. Mun kuma ziyarci ɗukunan karatu, don yin bincike ga kaɗan
daga cikinsu: Jami’ar Usman Danfodio inda muka shiga ɗakunan karatunsu wato
(library).
Haka ma binciken namu bai tsaya a Jami’ar Usman Danfodio kawai ba a’a har
Jami’ar Bayero da ke Kano mun leƙa a ɗakin karatun ɗalibai duk a wannan
Jami’ar.
Binciken namu bai tsaya a waɗannan Jami’o’in ba kurum. Domin kuwa ziyarar
binciken ta kai mu ga daɗaɗɗiyar Jami’ar Ahmadu Bello mai tarihi ita ma mun
shiga lunguna- lunguna domin gudanar da wannan bincike namu. Daga nan sai muka
cirata zuwa Jami’ar Katsina, inda a can muka samu ziyarar sauran makarantu kuma
yanayin binciken ɗaya ne.
Manufar
Bincike
Binciken yana da muhimmamcin gaske domin ta fuskar bincike ne a kan gano
cikakkiyar ƙwarewar ɗalibai da fahimtarsu da hazaƙarsu. Ta wannan hanyar
karance-karace za a ci karo da wani sabon al’amari domin ya ƙara tabbatar da
abin da aka riga aka sani a fagen ilimi.
Binciken yana fitar da bayanai domin amfani al’umma, wani babban muhimancin
bincike shi ne a duk lokacin da mai bincike ya tsunduma a fagen aikinsa yakan
yi karo da wasu ra’ayoyi daban-daban wanda yana iya zama sabon darasi gareshi.
Manufar wannan binciken shi ne mu fito da wasu abubuwa da wannan littafi na
Turmin Danya ya ƙunsa musamman Jogonsa da Salon da aka yi amfani da shi. Muna
kuma fatar wannan nazari namu ya zama abin dogaro ga masu nazarin harshen
Hausa.
Matsalolin
Da Suka Taso
Wannan bincike namu mun gudanar da shi ne a kan hanyoyin da suka dace, na irin
hanyoyin da ake bi wajen samun bayanan da suka dace ta hanyoyi da dama. Mun ci
karo da matsaloli da dama wajen binciken mu kamar haka.
Rashin isassun kuɗin mota, da matsalar iska waɗansu masana da muke tuntu’ba
wajen gudanar da wannan bincike namu, haka ma wani lokaci za mu kashe kuɗin
mota domin zuwa wajen waɗansu mutane da abin ya shafa, sai mu iske ba su
nan. Haka ma kowa ya san irin halin da ake ciki a ƙasar nan na rashin tsaro, a
inda ba ko ina za mu iya shiga ba dole sai da taka tsantsan.
Aikin bincike aiki ne mai wahalar gaske, musamman ma ga irin mu ɗalibai mata
masu rauni da kuma karancin ilimi. Saboda haka lokacin da muke gudanar da
wannan aiki na bincike wasu matsaloli da dama sun sha kanmu. Daga cikinsu
akwai
Matsalar kar’bar lacca da aikin aji da na jinga da kuma karatun jarabawar gwaji
da ta ƙarshen zangon karatu.
Akwai kuma matsalolin gida kasancewar mu mata da suka haɗa da girke-girken
abinci kula da tarbiyar yara, akwai rashin lafiyarmu da ta ‘ya’yanmu. Duk waɗannan
matsaloli ne da mu ka yi ta cin karo da su .
Akwai matsalar tuntu’bar magabata da masana, saboda wasu daga cikinsu suna
ganin kamar za mu ɗauki sirrinsu ne mu watsa wa duniya.
Haka ma akwai matsalar yawan ɗaukewar wutar lantarki, domin sai mun tattaro
bayanan mu na cikin aikin kwatsam sai wuta ta ɗauke. Kaɗan kenan daga
irin matsalolin da muka ci karo da su.
Matsalolin
da aka Fuskanta
Kamar yadda aka sani a dukkan bincike za a iya samun nasarori da akasin haka,
wato matsaloli a wajen gabatar da aikin. To don haka wajen bincike nan mun
fuskanci matsaloli da dama kamar rashin kuɗi da za mu buga wannan aiki namu.
Haka kuma akwai matsalar haɗuwarmu idan mun yi alƙawali, kuma idan za mu tafi
wajen ganawa da waɗanda za mu yi hira da su, saboda lokacin ba lallai ne
a same su ba.
Haka akwai sha’anin rashin lafiya yakan kama magidanci , ko kuma halin tafiya
wajen ƙaro ilimi wato a bangaren su masana.
Ba nan kaɗai muka samu matsala ba kuma mun fuskanci matsalar karamcin lokaci.
Domin wannan aiki na bincike aiki ne da ya kamata a ce an gudanar da shi a
cikin shekara ɗaya.
Babi Na
Biyu
Wannan babi zai ƙunshi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, tare da Salon
Nazari da tsarinsa.
2.0.1
Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.
Ayyuka da suka gabata fage na adabin Hausawa suna da yawa, saboda haka wannan
aiki namu ba shi ne na farko ba a wannan fage. Don haka ya zama wajibi a garemu
da mu waiwayi wasu ayyuka da suka gabata masu alaƙa da wannan aiki domin mu ga
inda suka zo daidai da kuma inda suka sha bambam, ko kuma suke da dangantaka da
namu.
Daga cikin ayyukan da suka gabata a wannan fage akwai; bugaggun littafai
daban-daban, da suka gabata a kan fannoni daban-daban na adabin Hausawa ga wasu
daga cikinsu;
‘Dangambo A (1984) a cikin littafinsa mai suna “Rabe-Raben Adabin Hausa Da
Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa” marubucin ya bayyana ma’anar adabi ya kuma
karkasa adabin Hausa, inda ya kawo zube da waƙa da wasan kwaikwayo. A ƙarƙashin
zube nan ne ya bayyana cewa akwai littafai waɗanda aka yi rubutun zube a
cikinsu.
Wannan aikin na shaihin Malami ‘Danganbo yana da alaƙa da namu aikin, saboda ya
ta’bo zube, yayin da mu ma a namu aikin zube ne wanda ya danganci nazarin
littafi. Inda muka samu bambanci da shi kuwa shi ne, shi marubucin littafin
yana magana ne a a kan zube gaba ɗayansa mu kuma mun taƙaice aikinmu ga littafi
ɗaya mai suna “Turmin Danya.”
Yahaya I.Y. (1988), ya rubuta littafi mai suna “Hausa A Rubuce” a cikin wannan
littafi masanin ya yi bayanin rubutu, tarihin samuwar rubutu yadda aka samu
rubutun zube, wasu daga cikin littafan da aka samu na zube, gasar da aka shirya
don samun littattafan zube tarihin wasu hukumomi na gudanar da ayyukan rubutu
musamman na boko da na Arabiyya.
Wannan aikin na shaihin malami Yahaya I. Y. Yana da alaƙa da aikinmu saboda ya
yi tsokaci a kan zube da littattafan zube da tarihin Rubutu da dai sauransu.
Aikin yana kuma da bambanci da namu saboda shi yana magana ne a kan adabi
dukkansa, mu kuma muna magana ne a kan wani sashe daga cikin adabi ko shi kuma
mun taƙaita akin manu a kan littafin “Turmin Danya”.
Sagiru A.G (1991) a nasa kundin bincike mai taken “Nazari Da Sharhi A Kan
Littafin Uwar Gulma” wannan manazarci ya gudanar da aikinsa ne a kan tsari na
babi- babi har zuwa babi baiyar. Bayan ya yi gbatarwa a babi na ɗaya ya kuma yi
waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, sai a babi na uku da na huɗu inda ya
ta’bo, jigo, warwararsa, taurari, manya da ƙanana da kuma salo duk a cikin
littafin “Uwar Gulma”.
Wannan aiki na wannan manazarci yana da alaƙa da namu aikin, musamman da ya yi
bayani a kan jigo da warwararsa, haka namu aikin zai yi tsokaci a kan
jigo da warwararsa da salo da taurari. Amma duk da haka mun sha bamban da shi
saboda shi ya gudanar da aikinsa ne a kan littafin “Uwar Gulma” mu kuma namu
aikin muna yin sa ne a kan littafin “Turmin Danya”.
Gobir, (1993), ya rubuta wani kundi mai suna “Malam Muhammadu Umar Kwaren Gamba
Da Waƙoƙinsa” manazarcin ya ta’bo jigo da salo da tarihin Mawaƙin. Mun bi sahun
wannan manazarci wajen nemo salo da jigo da tarihin marubuci, wannan ya sa
aikinmu yake da alaƙa da nasa. Inda kuma suka bambanta shi ne, shi Gobir yana
nazarinsa ne a kan waƙa mu kuma muna namu a kan zube.
Hadiza A. Da Wasu (1999), a kundin Bincikensu da suka gudanar mai taken “Nazari
A Kan Littafin Jatau Na Ƙyallu”. Marubutan sun fara ne da mayar da taƙaitaccen
tarihin marubucin wannan littafi, sun kuma yi tsokaci a kan ma’anar jigo,
babban jigo da ƙaramin jigo. Sun ci gaba da yin sharhi a kan littafi tare da
bayani a kan salo da zubi da tsarin wannan littafi tare da tsokaci a kan
taurari.
Wannan aiki na su Hadiza yana da alaƙa da namu aikin saboda dukan mu muna
nazarin Littafi ne, sai dai inda muka sha bamban shi ne su suna nazarin
Littafin “Jatau Na Ƙyallu” ne mu kuma muna nazarin littafin “Turmin Danya”.
Shafa’atu A. I. (2005), sun rubuta kundi mai taken “Nazari A Kan Littafin Iliya
‘Dan MaiƘarfi” a wannan kundin sun yi bayanin jigo, warwararsa da salo da
tarihin marubuci da sharhin littafin.
Wannan kundin nasu yana da alaƙa da namu saboda dukanmu muna nazari ne a kan
littattafan zube, sai da inda muka bambanta shi ne su suna nazarin littafin
“Jatau Na Ƙyallu” ne yayin da mu kuma muna nazarin littafin “Turmin Danya”
Hannatu A da Wasu (2008), a nasu kundi mai taken “Nazari A Kan Littafin Ai Ga
Irinta Nan” a wannan kundin sun yi bayanin jigo, salo tarihin marubuci da
sharhin littafin.
Wannan kundi nasu yana da alaƙa da namu kundin saboda dukkanmu muna nazarin
littattafan zube ne. Amma fa mun samu bambanci a yayin da su suke nazarin
littafin “Ai Ga Irinta Nan” mu kuma muna nazarin littafin “Turmin Danya”
Firdausi A. Da wasu (2010), sun rubuta wani kundi mai taken “Nazari Da Sharhi A
Kan Littafin Jiki Magayi” manazartan sun karkasa kundinsu a kan babi-babi
sannan suka gudanar da aikinsu a cikin babi na uku da na huɗu. Sun kuma yi
bayani a kan salo, jigo, da sharhin littafin, sun kuma yi bayanin taƙaitaccen
tarihin marubucin wannan littafin.
Wannan kundin yana da alaƙa da namu aikin saboda su sun gudanar da aikinsu a
kan littafin zube haka mu ma mun gudanar da namu aikin a kan zube. Amma inda
muka samu bambanci shi ne, su sun yi nazarin littafin Jiki Magayi ne mu kuma
muna nazarin littafin Turmin Danya.
2.0.2
Salon Nazari Da Tsarinsa
Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin
mutum.
Salon nazari wata hanya ce ta isar da saƙo da bayyana tunanin mutum. Haka kuma
salo ya na nufin hanyoyin da marubuci ko mawallafi kan bi domin yi wa harshe
kwalliya ko kuma yi wa rubutun sa ado, haka kuma wata dabara ce da marubuci kan
yi amfani da ita domin samun sauƙin isar da saƙonsa a cikin rubutunsa. A
dalilin haka ne mu ka yi amfani da hanyoyin guda uku na nazarin salo.
Na farko dai irin kalmomin da muka yi amfani da su, kalmomi masu sauƙi ne. Sai
kuma muka saka su a inda ya dace.
To anan za mu yi amfani da salo mai jan hankali, domin mu ja hankalin mai
karatu ya karanci wannan kundi, ba tare da wata wahala ba ko ya ƙagara da
karatun wannan bincike ba.
Idan mai karatun wannan aiki ya kwantar da hankalinsa ya biyo mu cikin natsuwa
to zai ga irin matakan salon da muka yi amfani da shi wajen rubata wannan kundi
saboda mun yi amfani da littatafai masu saukin fahimta.
An kuma yi amfani da nuna ƙwarewar harshe sosai a cikin wannan kundi saboda
anyi amfani da kalmomi masu burgewa da kuma armashi waɗanda ke sa mai karatu ya
ji daɗi a zuciyarsa, wannan shi zai sa binciken namu ya yi kwarjini da farin
jinni ga makaranta.
Babi Na
Uku
- Ma’anar Rubutu
Kamar yadda aka riga aka sani cewa, rubutu wasu alamomi ne da suke wakiltar
zance ko magana. Wannan ya sa masu ilimi na rubutu sukan samu lokaci su tsaya
su tsara waɗannan alamomi wato rubutu don su bayyanar da abin da ke cikin
zuciyarsu ko su isar da wani saƙo.
Wasu masana tuni sun tofa albarkacin bakinsu game da ma’anar rubutu. Kuma
dukkansu sun tafi kan cewa, alamomi ne masu wakiltar magana, kuma duk sun yarda
cewa, alamomin suna isar da wani saƙo.
3.0.1
Ma’anar Rubutun Zube
Masana da manazarta da dama sun baje kolinsu wajen bayyana ma’anar rubutun
zube, kuma ga wasu daga cikinsu:
Yahaya I. Y. (1988) ya ce, “Rubutun zebe, labari ne ƙagagge kuma shiryayye, a
cikin hikima da fasaha da aka gudanar don ƙwarewa.
Shi kuwa Ahmad Magaji (1982) ya bayyana rubutun zube da cewa, “Rubutun Zube
labari ne da mawallafa suke shiryawa da ka, sannan suka rattaba a zube.”
Rubutun zube dai shi ne duk wata wallafa da aka ƙago aka rubuta kara zube ba a
shirin waƙa ba ko wasan kwaikwayo
Wannan shi ne rubutun zube.
3.0.2
Gasar Ƙagaggun Labarai:
Irin wannan Gasa ta samo
asali ne tun lokaci mai tsawo, a kan sanya kyaututtuka ko lada ko wani abu a
matsayin goro ga wanda ya fi nuna bajinta ko ya zama gwani a cikin gwanaye.
Misali, a shekarun da suka gabata hukumar da aka kafa a ƙasar Ingila domin ta
kula da harsunan mutanen Afirka, ta tsara yadda zata rinƙa gudanar da gasa tare
da cin kyautar kuɗi duk shekara, tsakanin al’ummun Afirka ta hanyar shiga gasar
rubuta ƙagaggun Labarai cikin harsunansu. An fara shirya wannan gasar ta
harsunan mutanen Afirka, a shekarar 1930.
Jami’an da ke kula da harkokin ba da ilimin a ƙasashen Afirka, su ke wakilta waɗanda
suka shiga gasar ta hanyar taimaka masu da sanin dokokin da hukumar ta tsara
domin shiga gasar, tare da ɗaukar Labaran da ‘yan Afirkan suka rubuta na shiga
gasar, su kai wa jami’an hukumar da ke shirya gasar a can Ingila domin nazari
da bayar da shawarwari kan yadda za a inganta hanyar rubutun adabin harsunan da
suka shiga gasar.
Shiryawa da gudanar da irin wannan gasa na daga cikin hanyoyin da aka bi domin
samar da ingantaccen adabin harsunan Afirka. Har ila yau, bayan an gama nazarin
Labaran da aka aiko domin shiga gasar, ana aikawa da ladan kuɗi daga hannun
gwamnati da jami’an da suka wakilci masu shiga gasar, domin a raba wa waɗanda
suka shiga gasar, kusan muna iya cewa wannan shi ne kaɗan daga cikin abin da ya
assasa shirya gasa a rubutun ƙagaggen labari ƙarƙashin adabin Hausa. (Afrika,
1933:102-103 vol.vi No.1).
3.0.3
Tarihin Samuwar Ƙagaggun Labarai (Rubutun Zube)
Jami’an gwamnatin mulkin
mallaka musamman waɗanda ke aiki a ƙarƙashin Hukumar ilimi na ƙoƙarin bin
hanyoyi da matakan da za su dasa tare da samar da ingantaccen adabi ga mutanen
da suke yi wa aiki. Kan wannan tunanin ne, Hukumar makarantar Kwalejin Katsina,
ta shirya gasar rubuta ƙagaggun labarai cikin Hausa tsakanin ɗaliban kwalejin a
shekarar 1927. An shirya wannan gasar da manufar koya wa ɗalibai fasahar ƙirƙira
labarai a cikin harsunansu. Haka kuma, yin haka zai sa a sami labaran karantawa
masu sanya nishaɗi ga al’ummar Hausawa. Dakta East na ɗaya daga cikin jami’an
makarantar da suka shirya wannan gasa. A lokacin yana aikin malanta a wannan
Kwalejin. Abubakar Imam na ɗaya daga cikin ɗaliban da suka rubuta labarai domin
shiga gasar. Kuma shi ne ya samu nasarar lashe gasar ƙagaggun labaran da aka
shirya cikin harshen Hausa, har hukumar makarantar ta ba shi sule Goma a
matsayin lada na shiga tare da samun nasarar zama na ɗaya cikin waɗanda suka
shiga gasar. A littafin da aka wallafa kan rayuwa da tarihin Abubakar Imam
(Mora 1989:28), wanda Imam ɗin ne ya fara rubuta shi da kansa. Abubakar Imam ya
nuna cewa, ya rubuta ƙagaggun labari ne a Kwalejin Malamai ta Katsina, amma bai
iya tuna taken labarin da ya yi rubutu a kai, kuma ba a buga labarin a matsayin
littafi ba. Haka nan, ba wani kwafe na labarin a hannunsa. Saboda haka labarin
yana da wuyar a same shi a yanzu domin masu yin nazari. Wannan ita ce gasar
farko da aka ta’ba shiryawa kan ƙagaggun labaran zube cikin harshen Hausa
(Abdullahi, 1998:23). Wannan gasa ita ce ta fara share fage da nuna hanya
tsakanin ‘yan bokon ƙasar Hausa, na yadda za a yi amfani da basirar ƙirƙira/ƙagawa
a maimakon fassara domin a samar da littafan labarai cikin harshen Hausa.
A shekarar 1930 ne wasu
daga cikin malaman ƙasar Hausa, suka rubuta ƙagaggun labarai cikin harshen
Hausa suka aika Ingila domin shiga gasar shekara-shekara da Hukumar Nazarin
Al’adu da harsunan Mutanen Afirka ke shiryawa domin raya tare da inganta adabin
harsunan mutanen Afirka. Hukumar ta fara shirya wannan gasa a shekarar 1930.
Amma a wannan shekarar ba a sami waɗanda suka shiga gasar daga arewacin
Nijeriya ba. Sai a karo na biyu a shekarar 1931, inda wasu Hausawa ‘yan
arewacin Nijeriya suka shiga gasar kamar yadda za a ga sunayensu a nan gaba kaɗan.
Wanda ya wakilci waɗannan malamai da kuma kai labaran da suka rubuta a gaban
Hukumar da ke Ingila, shi ne Dakta East. A lokacin, yana aiki da Hukumar
Fassara wadda aka kafa domin samar da litattafan da za a yi amfani da su wajen
koyar da ilimi a makarantun gwamnati na Elementare da ke yankin arewacin
Nijeriya. Kamar yadda aka ambata jami’an da suka wakilci waɗanda suka shiga
gasar, na daga cikin kwamitin da ke nazarin labaran da aka aika da su domin ba
da matsayi da kuma kyaututtuka ga waɗanda suka sami nasara. Bayan an gama
nazarin dukkanin labarai da aka aika a wajen wannan gasa daga harsuna
daban-daban na Afirka, sai aka ba da sakamakon gasar tare da aika kyautar kuɗi
har sule Talatin ga duk wanda ya shiga gasar. Ga yadda Hukumar da ta shirya
gasar ta ba da sakamakon gasar kamar haka, ta 1931:
Nuhu H.G.B, “Hausa Stories”
Malam Dodo. “Hausa Stories”
Malam Ahmed Mettden, “Zaman Dara”
Malam Bello Kagara, “Littafin Karatu Na Hausa”
Malam Na Gwamatse da ‘Dan Malam Alƙali Sokoto “Takobin Gaskiya” “(Africa
1933:102-103, Vol. Vi).
Waɗannan Malamai daga ƙasar Hausa su ne suka shiga wannan gasa. Sauran mutanen
daga wasu harsuna ma sun shiga wannan gasar. Daga cikin harsunan da suka aika
da nasu labaran akwai harshen Suto da Ganda da Mandingo da Mende. Bayan an
kammala gasar, Hukumar ta yi shelar cewa ba za ata ɗauki nauyin buga waɗannan
labarai a matsayin littafai ba. Sai dai jami’an da suka je a matsayin wakilai,
su taimaka wa masu sha’awar buga labaransu a matsayin litattafai wajen yin
hakan. Kuma ba a dawo da su ga marubutansu ba. Haka kuma ba a yi masu wani
tanadin da za su kawo yanzu, har a saka su cikin jerin labaran da ake yin
nazari a kansu ba, kamar yadda ake yin nazarin sauran labaran da aka samar ta
hanyar yin gasa.
Wannan gasa ta zama ta biyu a jerin gasar ƙagaggun labarai da aka gudanar cikin
harshen Hausa. Kuma shirya ta ya yi tasiri ga samar da litattafan da aka rubuta
domin samun nasarar cin kyauta a gasar da ta biyo bayanta.
Dukkan jerin gasar da
aka shiya domin samar da ƙagaggun labarai cikin adabin Hausa, an shirya su ne a
ƙoƙarin da gwamnati, tare da taimakon jami’an ma’aikatar ilimi, ke yi na dasa
tsiron tare harsashin rubutacce adabin Hausa cikin rubutun boko. Haka kuma
domin koya wa ‘yan ƙasa yadda za su samar da labarai cikin harsunansu ta hanyar
amfani da basirar ƙagawa. Amma har zuwa shekarar 1933 Hukumar Fassara na ganin
ba ta sami litattafan adabin da take buƙata ba. Don haka ne Hukumar ta shirya
gasar da za ta taimaka wajen samar da litattafan adabin da take buƙata, waɗanda
kuma za buga a matsayin litattafan karantawa domin nishaɗi. Haka kuma domin a
sayar da litattafan, ba a raba kyauta ba, kamar yadda aka saba yi. Wannan gasa
ta samar da litattafai da suka inganta tare da kyautata adabin Hausa. Kafin a
fara gasar sai da Dakta East ya zagaya ƙasar Hausa kamar garuruwan
Katsina da Kano da Sakkwato da Birnin Kebbi da Bauchi da wasu garuruwan da
dama, ya haɗu da malamai da ɗalibai a makarantu ya bayyana musu abin da ake so
dangane da gasar, musamman abin da ya shafi tsari da fasalin yadda litattafan
za su kasance. Dakta East ya jaddada wa waɗanda suka shiga gasar cewa Hukumar
ba za ta amince da duk wani abu mai kama da haka ba. Hukumar Fassara ta sami
litattafai da dama da suka amsa shiga wannan gasa. Da yawa daga cikin
litattafai da aka aiko wa Hukumar sun dace da tsarin da ta shimfiɗa. Lokacin da
Hukumar ta zo buga litattafan waɗanda suka lashe gasar sai da ta yi musu taciya
sosai musamman ta tattace farkonsu da ƙarshensu, ta kuma sake tsarin wasu daga
cikin tabobinsu, sa’anann ta buga su (Abdullahi 1998:54). Byana da Hukumar
Talifi ta gama tsara da sake fasalinm waɗannan litattafai, sai ta fitar da
sakamakon gasar kamar haka: Ruwan Bagaja, Malam Abubakar Imam, Ganɗoki, Malam
Bello Kagara, Shaihu Umar, Malam Abubakar Bauchi, Idon Matambayi, Malam
Muhammadu Gwarzo, Jiki Magayi, East da Tafida (NAK/AND/1029/1934).
Duk da cewa waɗannan su ne aka za’ba a matsayin waɗanda suka ci gasa, amma ba a
sami buga su ba, su ne: Boka Buwaye, Malam Nagwamatse; da Yarima Abba, Malam
Jumare Zariya. Wannan gasa ita ce ta uku a jerin gasannin rubuta ƙagaggun
Labaran Hausa. Sai dai ba a sami damar buga sauran labaran da aka samar lokacin
gasa ta ɗaya da ta biyu ba. Sai dai a wannan karon Hukumar ta yi ƙoɗarin buga
litattafan kamar yadda aka gansu a kasuwa.
Tun daga shekarar 1933 ba a ƙara samun wata fitacciyar gasar ƙirƙira ba sai a
shekarar 1971, inda kamfanin Wallafa Littafai na Zariya wato NNPC ya fito da
wata gasar ta ƙirƘira rubutun zube, domin samar da sababbin litattafai na
karatu da nishaɗi. Kamar dai yadda waɗancan suka gabata, ita ma wannan gasar ta
jawo hankalin marubuta da dama. Da ƙarshe an tankaɗe kuma an rairaye daga cikin
litattafan da aka samu, an tace litattafai guda takwas waɗanda suka tsallake
siraɗin ƙa’idojin da aka shimfiɗa wa gasar, amma daga waɗannan litattafai guda
uku kawai kamfanin ya sami damar wallafawa.
Litattafan da suka yi dace suka yi nasara a ƙarshe aka wallafa litattafan su
ne:
‘So Aljannar Duniya; Na hafsat Abdulwahid wanda ita ce mace ta farko da ta fara
yin fice a rubuta littafin ƙirƙira a adabin Hausa, kuma ta zama na ɗaya a
gasar.
Amadi na Malam Ama; Na Magaji ‘Danbatta shi ya zo na biyu a gasar. A ƙarshe
sai, Mamallakin Zuciyata wanda wani ɗan jarida ya rubuta wato, Suleman Ibrahim
Katsina.
Wannan al’amari na gudanar da gasa fagen ƙirƙira yana bayar da gagarumar
gudunmuwa ta fanni da dama musamman samar da litattafan karantawa a makarantu
da nishaɗi.
Bayan kammala waccan
gasa, sai shekarar da ta gabata, sai a cikin shekarar 1982, aka sami wata
sabuwar gasar wadda hukumar yaɗa Labarai ta Tarayya da ke Ikko ta sanya gasar ƙirƙirar
rubutun zube cikin harsunan ƙasa wato Hausa, Yarbanci da kuma Ibo. A wannan
karon ma littatafai da dama sun shiga gasar wasu sun yi nasara wasu kuma
akashin hakan. A harshen Hausa littafin da ɗan jaridar nan Suleman Ibrahim
Katsina ya rubuta mai taken, ‘Turmin Danya’ shi ya zo na ɗaya. Sai waɗanda suka
rufa masa baya kamar haka:
‘Tsumingiyar kan Hanya’, na Musa M. Bello
Ƙarshen Alewa Ƙasa, na Bature Gagare
‘Za’bi Naka’, na Malam Mannir Katsina
‘Soyayya tafi kuɗi’ na Habib A. Alƙalanci
‘Dausayin Soyayya’ na Muh’d B. Yahuza.
Bayan kammala gasar an bayar da kyaututtuka, kuma kamfanin NNPC da ke Zariya ya
ɗauki nauyin buga waɗannan litattafai, kuma daga nan aka ci gaba da samun
gasanni nan da can amma ba su yi wani cikakken tasiri ba, saboda waɗanda suka ɗauki
nauyin shirya gasar suna da ƙarancin ƙarfin ɗaukar gasar, ta yadda za ta karae
ko’ina.
3.0.4
Tsokaci A Kan Marubucin Littafin Turmin Danya: Suleman Ibrahim Katsina.
Suleman Ibrahim Katsina shahararren ɗan jarida ne kuma haziƙi a fagen rubutu.
Kafin ya fara karatun boko sai da ya fara yin karatun ilimin addinin musulunci,
kuma shi masani ne a lamurran addini. Ya samu ilimin boko wanda ya zama mashi
sanadin shiga fagen gasar rubuce-rubuce a fannoni daban-daban, ciki har da gasar
rubutattun ƙagaggun Labarai.
Suleman Ibrahim Katsina ya rubuta, littattafai da dama ciki kuwa har da
littafin nan da muke nazari a kai wato “Turmin Danya” ya kuma rubuta wani
littafi mai suna, “Mallakin Zuciyata” wanda ya shiga gasa da shi har ya taka
muhimmiyar rawa sannan ya ɗora jigon wannan littafin bisa soyayya. Shiga wannan
gasar da ya yi ya zame masa alheri domin gasar ta fito da shi sarari, wanda a
dalilin ƙwazonsa ne ya zama ɗan jarida na farko, kuma a fage rubuta ƙagaggun
Labarai.
Babbi Na
Huɗu
4.0.
Jigo
‘Dangambo (2007:12) Abin da ake nufi da jigo shi ne saƙo, manufa ko abinda waƙa
ta ƙunsa, wato abinda take magana a kai.
Jigo a fagen adabi yana nufin manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka
dogara da ita. Saboda haka ana iya cewa Jigo shi ne irin saƙon da marubuci ke
son sadarwa ga jama’a kuma duk wani salo da tsari ko wata dabara da marubuci
zai yi amfani da su, zai yi hakan ne da nufin isar da saƙonsa ga jama’a.
Sar’bi, (2007:71).
Dangane da abin da muka gani game da jigo za mu iya cewa, jigo shi ne dukkan
wani saƙo da ko manufa ko ginshiƙin abin da ya sa aka rubuta labari, ko dalilan
da suka sa marubuci ya rubuta littafinsa. Don haka duk wani abu da za a faɗa a
cikin labari, ya kan danganci jigo wannan labari.
Da wannan muke gani Jigo a matsayin igiya maɗaura kayan kowane rubutu da aka yi
a fagen adabi ta kowane ‘bangare wato Zube da Waƙa da Wasan Kwaikwayo in ba da
shi ba to kayan za su kwance. A nan jigo na nufin burin zuciyar mawaƙi ko
marubuci wanda yake son jama’a su fahimta.
4.0.1
Kashe-Kashen Jigo
Kamar yadda aka riga aka sani cewa, da yawan masana da manazarta sun tofa
albarkacin bakinsu a fannin adabi kuma sun yi aiki da ya danganci wannan fage
da muke bayani a kai. Wato jigo. Mafi yawansu duk sun tafi a kan cewa, Jigo ya
kasu kashi biyu. Wato, Babban Jigo da Ƙaramin Jigo.
Masana sun bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, kamar dai yadda Bunza (2009)
da sar’bi (2007) suka bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, wato ‘Babban jigo’
da ‘ƙaramin jigo’. Yanzu bari mu zo da su ɗaya bayan ɗaya don ganin yadda abin
yake.
4.0.1.1
Babban Jigo
Babban jigo shi ne abin da mawaƙi ko marubuci ya sa gaba gadan- gadan domin ya
feɗe shi a gane shi sosai. Bunza (2009: 63).
Galibi shi babban jigo mawaƙi ko marubuci ya kan faɗa a cikin waƙarsa ko kuma
tun a sunan waƙar ya zan yana tafiya da saƙon wannan waƙar, idan kuma mawaƙi ko
marubuci bai faɗa a waƙarsa ba kuma ba a gane a sunan waƙar ba, to sai mai
nazari ya yi ƙoƙarin yin anfani da kalmomin fannu da aka gina waƙar da su waɗanda
za ka samu ƙananan jigogin.
4.0.1.2 Ƙaramin
Jigo.
Ƙaramin jigo ya sa’ba wa babban jigo ta kowace fuska. Na farko dai abin da ya
kyautu a kula shi ne, ƙarmin jigo ɗa ne ga babban jigo, domin babban jigo ke
haifar da shi. Haka kuma ba don ƙananan jigogi ba da babban jigo bai fito fili
sosai aka ganshi ba. Duk wata waƙa da aka gina wani babban jigo ɗaya, za a samu
wasu ƙananan da yawa da za su mara wa babban jigon baya, domin Ƙawata shi da ƙara
fayyace shi sosai. Bunza (2009:64)
Idan aka ce ƙananan jigogi dai, to ana nufin tuballan da suka gina babban jigo,
su waɗannan tuballan sun danganta daga waƙa zuwa waƙa, ma’ana dai kowace waƙa
da irin nata tuballai da suka samar da jigonta. Haka abin yake ga rubutun zube.
4.0.2 Ma’anar
Salo.
Malamai da masana sun bayar da ma’anar salo ta hanyoyi daban – daban duk da
yake abu ɗaya suka fuskanta.
Sa’idu Muh’d Gusau a tashi fahimtar ya ce:
“Salo shi ne hanyar da aka bi aka nuna gwaninta da dabaru a cikin furuci ko
rubutu. Kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa
da za’bar abubuwa da suka dace game da abin da yake son bayyanawa. Daga nan ne
za a fahimci salon mai sauƙi ne ko tsauri, mai tsauri ko mai daɗi ne da armashi
ko mai kashe jiki maras karsashi da sauransu” Gusau (1993).
Yahya kuwa ya ce:
“Salo dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya
bayyana” Yahya (1999)
Shi kuma ‘Dangambo cewa ya yi:
“Masana da manazarta suna ganin cewa Salo yana da wuyar a gane shi a bisa kansa
sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa” dangane da ma’anarsa.To amma muna iya
cewa salo shi ne hanyoyin isar da saƙo, ‘Dangambo, (2007).
A bisa ra’ayin Abdulƙadir ‘Dangambo yana cewa za a iya karkasa salo kamar
haka;
1.
Salo wani ƙari ne da ya ƙunshi za’bi cikin rubutu ko
furuci.
2.
Salo wani ƙari ne na daraja a cikin karatu ko furuci wanda
ba lalle ne a same shi cikin kowane rubutu ba.
3.
Salo ya shafi kauce wa wata daidaitacciyar ƙa’ida
4.
Salo harshen wani mutum ne, wato yadda salon wane ya
bambanta da na wane.
Haka kuma ya ci gaba da bayyana mana cewa salo yana da nau’oi har guda biyar,
1.
Miƙaƙƙen salo: Wato salo na kai tsaye mai sauƙin ganewa,
wannan salo yana iya zama kamili mai iya isar da saƙo ba tare da “ado” ko ƙaƙale
ba .
2.
Salo mai armashi ko mai karsashi: Shi ne salon da ya gamsar
ta hanyar karsashi ƙaƙale da burgewa
3.
Raggon salo: Shi ne salo mai kashe jiki kuma marar
gamsarwa.
4.
Tsohon salo/Sabon salo: Salon da ke yin amfani da tsofaffin
hanyoyi ko sababbi don isar da saƙo, yana iya zama mai gamsarwa ko akasin haka.
5.
Salo mai sarƙaƙiya ko mai tsauri. Shi ne salo mai wahalar
ganewa saboda tsaurin saƙar manufofi ko tsauraran kalmomi.
Wani manazarcin na ganin cewa: .
“Salo shi ne yadda mawaƙi ya zana tunaninsa a takarada, za a dube shi a gani
shin yana da manufa, kuma bayaninsa yana da ƙarfi ko raunanna ne ana fahimtarsa
cikin sauƙi ko kuma sai an yi lalabe kafin a gane manufarsa. (Bashir 2007).
Shi kuma Sar’bi cewa ya yi:
“Salo na nufin za’bi cikin gudanar da wani abu/aiki. Amma fagen nazarin waƙa
salo hanya ce da marubuta waƙoƙi ke bi wajen isar da saƙonsu ga jama’a”
(Sar’bi, 2007).
A tamu fahimtar, mun lura da dukan bayanan da waɗannan masana da manazarta suka
kawo suna nufin salo ya ƙunshi hanya ko hanyoyin da mawaƙi ko ke bi domin isar
da saƙonsa ga jama’a.
4.0.3
Ma’anar Taurari/Tauraro
Tauraro ko taurari dai a cikin rubutun zube yana nufin wani mutum da aka yi
amfani da sunansa wajen gina wannan labari da aka yi a rubuce, haka abin yake
ko a cikin wasan kwaikwayo wadda aka rubuta ko wadda aka gabatar a cikin faifan
bidiyo. Tauraro ya kasu kashi biyu. Wato babban tauraro da Ƙaramin/ Ƙananan
Taurari/tauraro.
4.0.3.1
Babban Tauraro.
Babban tauraro dai a cikin rubutun zube ko a faifan bidiyo shi ne mutumen da
aka fi yin amfani da shi wajen gudanar da wannan rubutu ko wasan da ake nunawa
a bidiyo domin isar da saƙon da ake son a isar ga jama’ar da ake son a sanar.
4.0.3.2 Ƙananan
Taurari/Ƙaramin Tauraro.
Ƙaramin Tauraro/Ƙananan Taurari dai su ne mutanen da aka yi amfani da su a
cikin rubutun zube ko a faifan bidiyo a yayin da ake gudanar da wata wasa ko
ake rubuta wani Ƙagaggen Labari don isar da wani saƙo.
4.0.4
Nazarin Littafin Turmin Danya
Wannan shi ne ainihin aikin da za mu yi a wahen gudanar da wannan bincike.
Sanin jama’a ne cewa, shi wannan littafi kamar yadda muka faɗa a baya cewa,
aikinmu zai mayar da hankali ne wajen yin Nazarin wannan littafi na “Turmin
Danya”.
4.0.4.1
Jigon Littafin Turmin Danya
Wannan littafi da muke nazari wato, “Turmin Danya” wanda Suleman Ibrahim
Katsina ya rubuta a Shekarar 1982, babban jigonsa dai shi ne “Horo A Kauce ma
rashin gaskiya”. A namu nazari da muka yi mun gano cewa, marubcin littafin bai
riga ya faɗi jigon littafinsa ba, amma kuma da yake ana dubin wasu Ƙananan
jigogi a kuma gano babban jigo shi ya sa muka yi wannan tunani cewa, mu kalli
littafin gabaɗayansa bayan mun karanta shi, sai mu yi amfani da abin da muka
karanta mu gano jigonsa.
Dalilinmu dai shi ne, Alhaji Gabatari ya yi bushasha a cikin wannan littafi
kuma ya ishi kowa, sannan babu yadda suka iya da shi ba wata hanya da za su iya
bi su hana shi. Saboda Alhaji Gabatari yana sayar da ƙwayoyin da aka haramta da
hodar ibilis, ko bayansu kuma Alhaji Gabatari yana yin abubuwan masha’a da yawa
saboda har gidan karuwai yana da, sai ga shi daga ƙarshe bai yi ƙarshe mai kyau
ba.
Idan muka duba a shafi na 129 a sakin layi na biyu da na uku za a gaskata abin
da muka faɗa cewa, “Horo A Kauce ma Rashin Gaskiya”. Ga dai abin da ke ciki:
“Alhaji bai daddara ba ya ɗaga. Mai shari’a na babbar kutu, ya sake karanta
abin da mai shari’a na farko ya yanke. Amma sai ya yanke don haka babu abin da
zai raba Alhaji Gabatari da igiyar mutuwa.”
“Ina wani wanda ya yi Turmin Danya? Wannan ya girbi abinda ya daɗe yana
shukawa.”
Wannan ɗai ya isa mu gane cewa, duk abin da mutum ya shuka shi ne zai girba.
4.0.4.1.0
Warwarar Jigon Littafin Turmin Danya
Anan za a yi sharhi ne kan Jigo gaba ɗayansa. Za a duba shi dangane da jawaban
jigo, da kuma abin da littafin ya faɗa a taƙaice. To amma muhimmin abin shi ne
za a duba lungu-lungu na dangane da jigo tare da ƙarin bayani daga
dukkannin abin da za a iya danganta waƙar da shi. Misali ana iya kawo ƙarin
bayani don kafa hujja da misalai daga Alƙur’ani, Hadisi, littattafai, muƙalu,
da ra’ayoyi iri daban-daban da dai sauran bayanai da za su taimaka wajen gane
abin da waƙar ta ƙunsa da inda aka dosa. ‘Dangambo, (2007:16)
A ɗan tunaninmu a nan mai nazari yake da babban aiki kuma ja! Domin ana son ya
tsattsafe bayanan da labarin ya ƙunsa ya fito da su daki-daki.
4.0.4.1.1
Harƙallar Alhaji Gabatari
A babi na biyar shafi na
56, sakin layi na ƙarshe, Alhaji Gabatari ya na cewa:
“Alhaji ya buga wa ‘yansanda waya cewa, yau ne fa ranar shigo da kaya, shi ma
ya ce ai bai manta ba, sai dai yana son sanin lokacin da kayan za su shigo
garin Karaini su wuce.”
Wannan bayani ya nuna cewa, Alhaji Gabatari yan da wani kasuwanci da yake yi
wanda yake haramtacce ne.
4.0.4.1.2
Mai Ƙin Jinin Alhaji Gabatari.
A babi na biyar shafi na 62, sakin layi na 5. wani mai suna Mukhtar yana ƙin
al’amurran Alhaji, duk da cewa, a wannan lokacin Alhaji alheri zai yi masu. Ga
dai abin da yake cewa:
“......Alhaji Ya ce, wato garin ya bushe,
Tanimu ya ce, I, Alhaji,
Alhaji ya ce, Ku nawa ne?
Mu shidda ne a halin yanzu, in ji Ishaya.
Mukhtar ya ce, kar ka ƙirga da ni!”
Da jin wannan bayani za a iya gane cewa, Mukhtari baya tare da Alhaji Gabatari.
4.0.4.1.3
Matsayin Alhaji Gabatari Ga Wasu Mutanen Gari
Wasu mutanen gari ba su ganin girman Alahji saboda irin harƙallar da yake yi
wadda ta sa’ba wa doka. Ga dai abin da wasu suka tattauna a cikin labarin:
“Af! To ba shi ya sa nake gaya maka ya dai zame mana “Turmin Danya” ba haka ma
na ji wani ,maroƙi yana yi masa kirari a ranar bukin Alhaji Adamu.....”
Wannan ya nuna cewa duk da yake wasu na goyon bayan Alhaji Gabatari bai hana
wasu suka dage wajen ƙin ayyukansa ba.
4.0.4.1.4
Sharholiyar Alhaji Gabatari
Tun farko an bayyan cewa, shi Alhaji Gabatari yana da dukiya da kuma hanyoyin
haramtattun kasuwanci, sannan kuma mun bayyana cewa, yana zuwa gidan Banza ida
yake neman mata. Ga dai yadda abin ke gudana a cikin littafin:
A babi na ɗaya shafi na biyar sakin layi na biyar, marubucin yana cewa:
“Bayan da Alhaji ya ƙare ya biya kuɗinsa, sai ya iske Alhaji Shanono a ɗakin
shaƙatawa, suka ƙara gaisawa”
Wannan ya nuna cewa, kenan shi Alhaji yana da inda yake zuwa don shaƙatawa.
4.0.4.2
Taurarin Littafin Turmin Danya
Turmin Danya dai kamar sauran littafai yana da taurarin da marubucin ya yi
amfani da su wajen gina saƙon wannan littafin. A wannan littafin akwai wasu da
suka taka muhimmyar rawa wajen isar da saƙo kuma su ne suka fi fitowa. Waɗannan
mutane su ne ake kira da Taurari. Don haka a wannan littafi za a samu manyan
taurari da kuma ƙanana. Misali.
4.0.4.2.1
Manyan Taurarin Littafin Turmin Danya
Littafin Turmin Danya ya ƙunshi manyan Taurari da suka fi yawan taka rawa wajen
isar da saƙon da littafin yake ɗauke da shi. Waɗannan taurarin sun haɗa da:
- Alhaji Gabatari
- Baby
- Bawale
- Mukhtar
- Alhaji Bushasha
- Bansuwai
- Mista Sammai Aciba.
4.0.4.2.2.
Ƙananan Taurari A Littafin Turmin Danya
Kamar yadda aka sani cewa, wannan littafi na Turmin Danya yana da Manyan
Taurari, to kuma yana da Ƙananan Taurari da suka taimaka wa manyan wajen fito
da saƙon da ake buƙata. Waɗannan Ƙananan Taurari sun haɗa da:
- Baushe
- Alhaji ‘Dan Faransi
- Kande Manzagi
- Mista Samai achiba
- Alhaji Atiku
- Dela
- ‘Yar Fillo
- Asha Banza
- Malam magaji
4.0.4.3
Salon Littafin Turmin Danya.
A tamu fahimta mun gano cewa, shi wannan littafi na “Turmin Danya” marubucinsa
ya yi amfani da miƙaƙƙen salo. Wannan ko shakka babu idan mutum ya karanta zai
ga cewa, babu kwan gaba kwan baya a cikin labarin, shi dai labarin a miƙe yake
kuma kowa ma yana iya fahimtar abin da ake son a gudanar a cikin saƙi.
Dalilinmu na cewa haka kuwa shi ne, marubucin ya yi amfani da babi-babi da inda
ya bi su ɗaya bayan ɗaya yana bayanin abin da yake son isarwa ga jama’a.
Haka kuma salon wannan littafin ba mai kashe jiki ba ne, wanda mutum zai ce ya
ajiye saboda ba ya jin daɗin karantawa. Da wannan ma muke ganin cewa wannan
salo mai Armashi ne.
Marubucin ya yi amfani da kalmomi masu sauƙi, babu rikitarwa a cikinsu. Sai dai
ya ari wasu kalmomi daga Ingilishi da Larabci kuma su waɗannan kalmomi ba masu
wahala ba ne. Kalmomi sun haɗa da: sumogal, Kwastam Direba, Lasin, Firij,
mista, sakatare, da dai sauransu.
4.0.4.4
Zubi Da Tsarin Littafin Turmin Danya
Zubi da Tsari sun ƙunshi yadda marubuci ya zuba ko tsara aikinsa a cikin
littafi. Marubucin littafin Turmin Danya ya zuba labarinsa a cikin sakin layi
masu kyau tare da amfani da salo mai burgewa. Ya kuma tsara littafinsa bisa ga
tsari na babi-babi har babi na tara.
4.0.5
Muhimmancin Littafin Turmin Danya
Wannan littafi yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar Al’umma. Wannan ko shakka
babu idan mutum mai nazari ne da ya karanta wannan littafi ba zai so ya yi
halin Alhaji Gabatari ba saboda ya san cewa, duk abin da ya shuka shi ne zai
girba.
Idan kuma muka dubi irin jigon da wannan littafi ke isarwa za mu ga cewa, ko
nan akwai muhimmanci saboda horo ne a kauce wa rashin gaskiya. Saboda kar mutum
ya yi da –na- sani.
Babi Na
Biyar
Jawabin
Kammalawa
Kamar yadda a ka gani a bayana, wannan bincike namu yana a matsayin share fage
ne kan muhimmin ‘bangaren adabi wanda ya shafi zube.
Kamar dai yadda aka saba mun kasa wannan kundin bisa ga tsarin babi-babi, kuma
kowane babi da abin da yaƙunsa daban tun farko har ya zuwa babi na ƙarshe.
A babi na ɗaya mun yi tsokaci a kan Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallin
Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike, Matsalolin Da Suka Taso da Matsalolin Da
Aka Fuskanta.
A babi na biyu kuwa, mun yi Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata kana muka biyo
da Salon Nazari da Tsarinsa.
Babi na uku ya ƙunshi, Ma’anar Rubutu, Ma’anar Rubutun Zube, Gasar Ƙagaggun
Labarai, Tarihin Samuwar Ƙagaggun Labarai, da kuma Tsokaci A Kan Marubucin
Littafin Turmin Danya.
A babi na huɗu nan ne muka yi magana a kan Jigo, Kashe-Kashensa inda muka ce ya
kasu kashi biyu wato, Babban Jigo da Ƙaramin Jigo. Mun kuma yi tsokaci a kan
Ma’anar Salo inda har muka ɗan faɗi wasu salailai da suke a cikin wannan
littafi na Turmin Danya. Mun yi magana a kan Taurari inda har muka ce, akwai
Babban Tauraro kuma a kwai Ƙananan Taurari kuma mun kawo taurarin da suke a
cikin littafin Turmin Danya. Mun kuma yi maganar zubi da tsarin wannan littafi,
kuma mun kawo muhimmancinsa ga al’umma. Mun yi nazarin wannan littafi inda kuma
muka yi warwarar jigon wannan littafi.
A babi na biyar nan ne muka naɗe tabarmar wannan Bincike da Jawabinmu na
Kammalawa tare da yin bayar da shawrori ga jama’a tare da yin Ta’aliƙin Wasu
Kalmomi.
5.0.1
Shawarwari
A nan muna kira ga masu sha’awar labaran zube da su hankalta da cewa yanzu fa
lokaci ya canza an kuma samu cigaba wajen karatun labarai da aka shirya su
domin isar da wani saƙo.
Idan aka duba ta furskar addinin Musulunci za a ga, ya kawo baban sauyi kan
yadda Hausawa suke tafiyar da al’amurransu na rayuwa, wanda wannan sauyi ya
shafi har yadda ake gudannar da wannan sha’ani na Ƙagaggun Labarai.
Dangane da shigowar turawan mulkin mallaka sun kawo wata hallayar rayuwa
sa’banin wadda mazauna ƙasar Hausa ke bi kafin zuwansu. A nan sun kawo tsarin
ilimin zamani da sabon tsarin kiwon lafiya na zamani wanda ya ƙunshi
rubuce-rubucen da suka isar da wani saƙo daban, sa’banin namu.
Bugu da ƙari, wasu Hausawa masu ilimin zamani na ƙyamar wannan wannan sashe na
nazarin Hausa. Saboda haka ya kamata iyayen su himmantu wajen sanya ‘ya’yansu
makarantun zamani da na addini domin samun ilimin wanda zai zamana domin samun
cigaba.
5.0.2
Ta’arifi Wasu Kalmomi
A cikin wannan kundin da yake yana da alaƙa da adabin Hausa kuma abin da ya
danganci Ƙagaggun Labarai na Zube mun yi amfani da wasu kalmomi da za su iya
shige ma mai nazari duhu, don haka za mu tsamo wasu daga cikinsu mu ɗan yi
fassara ga mai karatun wannan kundin don ya samu ƙarin fahimta.
Kwastam -
-
- Jami’in Fasa Ƙwauri
Alli -
-
-
- Ƙwaya
Magajiya -
-
- Shugabar Karuwai
Shamaki
-
-
- Abin da ya shiga tsakani
Ganuwa
-
-
- Katangar da ka zagaye gari
Hotel -
-
-
- Gidan Shaƙatawa
Ƙyaure
-
-
- Gambu/Ƙofa
Kalwani
-
-
- Jakadan mai neman karuwai
Okey -
-
-
- daidai
Dont forget -
-
- kar ka manta
Kafet -
-
-
- kilishi
Flacks
-
-
- ma’adanin ruwan zafi
Hegi -
-
-
- fili
Babur -
-
-
- mashin
Rosuman -
-
- sunan wata taba ce
Kushin
-
-
- kujerun zamani na ƙawata ɗaki
Albun
-
-
- wajen adana hoto
Television -
-
- na’ura mai hoto
Kabed
-
-
- wajen adana jika
Shafen ɗaki -
-
- da’ben ɗaki
Wiski -
-
-
- sunan wata giya ne
Tambulan -
-
- dogon kofi
Ƙosawa --
-
- gajiya
Rodi -
-
-
- ƙarfen gini
Tangarɗa -
-
- matsala
Razana
-
-
- tsoro
Barasa
-
-
- kayan maye
Sitirio -
-
-
- babban rediyo
Catred
-
-
- abin ɗaukar murya
Tuma ƙasa -
-
- abin rufe abinci
Tos -
-
-
- gasasshen biredi
Maƙasudi -
-
- manufa.
2 Comments
Assalamu alaikum,
ReplyDeleteDa fata ana lafiya.
Na ci karo jiya da shafinku na intanet, wato http://amsoshi.com, inda na ga wani aiki mai suna, “Nazari a Kan littafin Turmin Danya. Aikin da Rabi Yusuf, da Fauziyya Abubakar Waziri da da Samira Shehu Ahmad suka yi: Nazari A Kan Littafin Turmin Danya (amsoshi.com)
Sun yi ƙoƙari ƙwarai da gaske. Duk da haka, akwai ɗan kuskure game da sakamakon gasar da ta samar da Mallakin Zuciyata, da So Aljannar Duniya da kuma Amadi Na Malam Ama.
A sashe na:
3.0.3 Tarihin Samuwaar Ƙagaggun Labarai (Rubutun Zube)
Sakin layi mai suna:
Littattafan da suka yi dace suka yi nasara a ƙarshe aka wallafa litattafan su ne:
An ce “So Aljannar Duniya” ne ya zo na ɗaya. Na biyu kuma, “Amadi na Malam Ama”.
Wannan kuskure ne. Shi kuma kuskure, musamman ma na tarihi da zai ci gaba da wanzuwa, ya kamata a gyara shi. Ga yadda nasarar take:
Na ɗaya: Mallakin Zuciyata – na Sulaiman Ibrahim Katsina
Na biyu: So Aljannar Duniya – na Hafsatu Abdulwahid
Na uku: Amadi na Malam Ama – na Magaji ‘ɗambatta
Ina godiya,
Sulaiman Ibrahim Katsina
Mun gode sosai Malam Sulaiman.
ReplyDeleteMuna maraba da gyararraki da shawarwari a kowane lokaci.
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.