Ticker

    Loading......

Wane Ne Farfesa A Farfesance? (Hannunka Mai Sanda Ga Magabata, Hayya!Ga Mabuk’ata, Kashedi Ga ‘Yan Kallo)


Buk’atar ko wace rayuwa ta kai matuk’a ga muradin sha’awarta. Labudda kowane mutum akwai abin da ya gada, ko abin da ya yi haye, ko abin da ya koya. Gurin d’alibin Alk’ur’ani ya kai ga dogon alif, mak’arar basin. 

________________________________________
Daga
 Aliyu Muhammadu Bunza.
Faculty Of Humanities And Education, 
Department Of Languages And Cultures, 
Federal University Gusau
_________________________________________

Gabatarwa

Buk’atar ko wace rayuwa ta kai matuk’a ga muradin sha’awarta. Labudda kowane mutum akwai abin da ya gada, ko abin da ya yi haye, ko abin da ya koya. Gurin d’alibin Alk’ur’ani ya kai ga dogon alif, mak’arar basin. Kowane uba fatarsa d’ansa ya gaje shi. Matuk’ar ba a ce wa d’an galadima sarki ba, buk’ata ba ta biya ba. Babu wani d’an sana’a da ba ya burin ya yi wa tsara fintinkau ya sarauce su. Lallai yin nasarar kai buri ke sa a tattaro ‘yan uwa da abokan arziki a yi bukin mun gode. Shekarar da Narambad’a ya samu muk’amin malamin wak’a ya k’ago bakamdamiyarsa ga yadda ya yi walimarsa:

Jagora: Ko waz zaka kallo ya karkad’e kunnenai,

Yara:   Ga makandamiya za ni yi cikin manyan wak’ok’i

Jagora: Na jiya Jankid’i

Yara:   Ya yi tai uwar wak’a sai nai tau

Jagora: Na jiya Zaman

Yara:  Ya yi tai uwar wak’a sai nai tau

Jagora: Na jiya Gurso

Yara:   Ya yi tai uwar wak’a sai nai tau

Jagora: Na jiya Akwara

Yara:   Ya yi tai uwar wak’a sai nai tau

Jagora: Na jiya ‘Dandawo

Yara:   Ya yi tai uwar wak’a sai nai tau

Jagora: Na jiya Nagaya

Yara:   Ya yi tai uwar wak’a sai nai tau

Jagora: Dodo malamin wak’a kundumin magajin ‘Dan’baidu

Yara:   Ya yi tai uwar wak’a sai nai tau

Jagora: Kullum ji nikai azanci na hudo min

Yara:   In wani ya hi ni martaba ni kau na hi wani

Jagora: Ai kyan mafarauci

Yara:   Ya d’au kare ya kiyaye yah hi

Jagora: Shi dillali

Yara:   Da an saya ya hwad’o ad daidai

Jagora: Shi ko arne

Yara:   Ya kama noma daidai an nan

Jagora: A sai mai kwando

Yara:   Ya barbad’e taki ad daidai

Jagora: Shi makad’i kau

Yara:   Shi gyara turu daidai an nan

Jagora: Ni kan kun gane ni

Yara:   Na gyare turuna

Jagora: Sai zuba wak’a nikai

Yara:   Kama da ta Alfa Zaazi

Gindin Wak’a: Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

: Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

A ma’aunin malaman addinin musulunci na Afirka ta Yamma, duk wani yabo baya ga na Annabi Muhammadu (SAW) yake. A fagen yabon Annabi (SAW) Ishiriniyar Alfa Zaazi ta cancanci kujerar Farfesa. Don haka, kowane mawak’in Hausa ke burin zama Alfa Zaazi.

Zubin Allo Da Boko A K’asar Haua


Karatun boko a k’asar Hausa cikon sunna ne makaho da waiwaya, domin ko da iska ya zo ya tarar da kaba na rawa. Boko ya tarar da mu da iliminmu na addini a duniya da littattafai da fasahar karatu da rubutu da bincike cikin harsunanmu. A tsarin karatun addininmu, idan yaro ya iya Fatiha zuwa “Alam Tara” a baki da k’idan bak’i sai a dafa wake a yi walima. Idan ya turza ya kai “Sabbi” sai a yi masa walima da tuwo. Idan yana fara wa kansa rubutu kowane hizo za a yi masa walima da tuwo. Da ya kai K’uluhiya sai a yanka bunsuru. Idan likkafa ta ci gaba ya kai “K’aala” rabin Alk’ur’ani sai a yi babbar walima ta cikin gida. Da ya soma dafa “Bara’atu” sai babban bunsuru na a zo a gani. Idan ya kai dogon “Alif” sai zayyana da gangamin bukin babbar sauka muradi ya samu, ya samu lasisi karatun Alk’ur’ani sai a nad’a masa babban rawani, digiri ya samu. In ya hardace ya zama “Alaramma”. In ya rubuta da hannusa ya zama “Gwani”. In ya goge ya kai matsayin gyara wa Gwani rubutu ya kai Gangaram, kwatankwacin Farfesa ke nan a karatun bid’ar tuwo.

Da gaba ta koma baya, boko ya yi wa karatun addini idon marurugiya, e-bi-ci-di ta yi wa a-ba-ja-da wayo da sunan gurgusa in zauna abu ya koma gurguza ba ni wuri. Da yaro ya kai shekara bakwai za a kai shi aji d’aya har shekara bakwai. A yi bukin ba shi takardar iya karatu da rubutu. Daga nan sai makaranta ta gaba, a shekara biyar, a ba shi takardar shaidar sanin gari da k’ara karatu. Daga sanin gari yana da za’bi uku: in dai ya je Jami’a, ko kwalejin koyan koyarwa, ko kwalejin kimiyya da k’ere-k’ere. ‘Dayan biyun k’arshe duk ya je zai share shekara uku gabanin a yaye shi. Idan Jami’a ya je kai tsaye tsakanin shekara (4-5) a ba shi digirin farko. Komai saurinsa sai ya shekara (1-2) ya je digirin k’warewa (Masters). A al’adance za a yi shekara (1-3) a samu digirin. Daga nan in a yi zagege (ta ‘Danfulani) in ko a tsaya a huta. Duk yadda aka yi sai an shekara (3-5) za a samu digiri na uku (PhD). Da samun digirin PhD komai k’wazo ana share shekara (6-10) gabanin a hau kujerar Farfesa. Matuk’ar kowace tasha ana tsayi a huta, sai an share shekara (40-45) ana wasan kura da takardun boko gabanin a hau kujerar Farfesa.

Ma’anar Farfesa


Malamanmu sun yi kai da kawo wajen fassara wannan kalma cikin Hausa. Na tabbata d’an share fagen da ya gabata ya d’an ba mu haske yadda wahalan noma gandun yake. Wasu masana suna fassara kalmar da “Shaihin Malami”. Masu taka tsan-tsan ga shiga cikin kadadar addini su fassara ta da “Shehin Masani” . Da baya-bayan nan wasu masana suka hausantar da ita zuwa “Farfesa” kawai. Rashin kalmar a k’amusoshinnmu na Hausa ba zai rasa alak’a da cewa bak’uwa ce ba.

A Turanci asalin kalmar daga “Profess” yake wadda ke da harshen damo a fassara. Tana d’aukar ma’anar bayyanar da wani abu (da ya shafi mai bayyanarwa) shi kansa, ko ik’irarin samun wani horo ko koyo ga wata sana’a ko abin sha’awar mutum. A fassarar fannu sun ce:

Ingilish:      “A teacher of the higher grade in a University or College, or in an                                   institution where professionals or technical studies are persued;                     usually an officer holding a chair in some particuler branch of higher                      institution”. (The New International Webster’s Comprehensive                               Dictionary of the English Language)

Hausa:       “Malami mai gawurtaccen matsayi a Jami’a ko kwaleji ko wata

Cibiya (-r karatu) da ake horar da k’wararru ko karatun fasahohin        hannu; musamman (ana fassara shi) ma’aikaci mai rik’e da wata kujerar alfarma a wani sashe na musamman a manyan cibiyoyin     zurfafa karatu”.

A bisa bayanin masu abu Farfesa shi ne, “fitaccen malami, sananne, gawurtacce wanda ke saman kujerar shakundum a farfajiyar da ya yi artabon karatu da bincike. In ya kai babin murabus ba ya da abokin gwada tsawo daga d’a sai jika sai kama kunne bai fasa ba, bai kasa ba, sai a k’ara wa kujerarsa k’wari zuwa “Emeritus”. Masu abu cewa suka yi:

Ingilishi: Emeritus: Retired from active service (as an account of age), but retain in                    an honorary position, postor Emeritus. (Webster’s Comprehensive                          Dictionary of the English Language)

Hausa: Kartagi shi ne wanda ya yi murabus don rage nauyin aiki (musamman idan           shekaru sun fara kar’bar shara) amma aka ci gaba da rik’e shi bisa ga martaba                   shi, kartagin Pasto.

Ga alama kujerar Farfesa ba a son gara ya ci ta, matuk’ar yana raye, ko da idanu da k’afafu sun yi masa tawaye, muddin yana ji ana jinsa, da shi da hankali ba su fara hararar juna ba, kujerarsa na nan daram! Mannanu k’uda ya fad’a k’waryar alewa.

Farfesa A Farfesance


Hausawa na cewa kowa ya ci zomo ya ci gudu. Don haka wasu ke k’ara wa batun gishiri da fad’ar zomo ba ya kamuwa daga kwance. Duk Bahaushen da ya ji irin shekarun da ake sharewa ana kokuwa da boko kafin a zama farfesa, dole ya ce ba a wane bakin banza. Matuk’ar k’wazon ya dace da sunan to za mu ce Farfesa: Soja ne tsakanin mazaje namiji ne a ko’ina ake zancen maza su ma mazan da kan su za ka ji sun ce: “Soja maza”. Ga yadda wani soja ya fassara batun:

Sannun ku soja maza tsakanin mazaje,

Sannunku masu kashi da wawan gidaje,

Ku d’ai ka kwanci kan k’asa ba gadaje,

Sauro shi ciza ga kiyashi, k’udaje,

Manya wajen ladabi, wajen bin umurni.

(Kaftin U.D. Suru: Nijeriya Ina Muka Dosa (1986) b+24)

A fagen suna da fice, Farfesa kwatancin Shago ne a fagen fama. Da an gilma sunan Shago babu namijin da za ya sake kirari. Yadda duk Shago ya zama:

Jagora: Samji irin hakin da ka ramno,

: Burundumi abin zuba shara,

: Kutu’bi abin aza ma ruhewa,

:  Lahira a kai maki gawa.

(‘Dan’anace: wak’ar Shago)

A fassara Bahaushe haka farfesa yake, kuma haka yake son ya ga ya kasance. Da ya zo a wuri gardama ta k’are.

(iii) A fassarar Bahaushe farfesa uban ‘yan boko ne, da ya zo al’amari ya kai k’arshe, kamar yadda ‘Dank’wairo yake ce wa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato:

Jagora: Namiji uban ‘yan boko,

: Amadun Amadu mai tawakkali gun Allah,

: Baban mai saje,

Gindi : In ba ka nan maza suka k’arya su ce, “maza ne”,

: In ka taho uban Ajiya kowa bai motsawa,

Gindi : Mai dubun nasara tarnak’ak’i Sardauna,

: Ba a kai maka wargi....

(Musa ‘Dank’wairo; wak’ar sardauna)

(iv) Na tabbata Bahaushe abin da yake kallo farfesa a farfesance shi ne, wata aya ta k’arshe ga boko. Haka kuma, yana kallon ta wata irin kadada ga ilimin boko da an kai gare shi an tuk’e, idan gand’on ya fashe kuwa sai kowa ya yi ta kansa. Na kwatanta shi da irin hangen da Narambad’a ke yi wa sarkin Gobir Amadu yana cewa:

Jagora: Gand’o kake ran da kaf fashe,

: Rannan sai ka iske kowa na dawara,

: Ruwa sun cika karkara,

Gindi: Na rabu da ganin amali yau na zaka in ganai

: Dad’in Tudu ya kamata dad’in Tudu hank’uri.

Babu wai, irin yadda Bahaushe ke kallon farfesa kamar yadda ya ke kallon limamin garinsu ne ko unguwarsu. A boko, yana ganin farfesa liman ne domin shi ne k’arshen a-bi-ci-di. Na tuna wata shekara mun je garin K’aurar Namoda d’aurin aure, ‘ya’yan Khalifa Maahi Liman na zuwa tare da jama’arsa kowa na a bayansa sai maba/sank’ira ya hau baki da yi wa liman kirari:

“Dudduk’e Maguzawan Allah,

Azumi babbar gayya,

Komi girman mutum guda yaka d’auka,

Allahu akbar! Haka muk’amin Farfesa yake, komi tsufan mutum guda aka ba shi.



https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

A Ji Farfesa A Ga Farfesa


A wajenmu d’alibai koyaushe muna son mu ga mai suna irin na karatu da d’alibta ya kar’bi sunansa da muk’amin da aka ba shi. Ba dole ne sai ya gamsar da kowa ba, amma ko da ba a samu gamsuwa daga gare shi ba, ba za a yi wa maganarsa turbud’ar mushen jaki ba. An so Farfesa ya d’an siffantu da wad’annan siffofi da ake zaton a samu a wajensa.

Ya san da cewa, muk’amin Farfesa fara karatu ne aka yi, yanzu aka sa k’afa ka ce dai manomi ne ya had’a babban gona ga taki da iri da sungumi na shuka yana jiran a samu ruwa a yi shuka. An ce, wani malami ya ce, ya zama farfesan sani halin mata, ya kwashe shekara (40) yana bincike ga sakamakon da ya samu:

Bayana ya kwashe shekaru arba’ain yana binciken sharrin mata ya rubuta kundaye manya-manya, ya zo wani k’auye ya je rijiya ya sha ruwa, ya tarar da wata ‘yar yarinya ko budurci ba ta fara ba. Ya nemi ta ba shi ruwa, ta yi masa kallon raini. Malam ya husata ya ce, “Ke tun ba a haifi uwarki ba nake binciken makircin mata, kar’bi kundayen nan ki kai wa kakanki ya fassara miki”. Ta ce: “In gani baba!” Ya mik’o mata gafakar tana gefe d’aya na rijiyar. Yana sakar mata ta jaye hannu kundayen suka yi alkafura cikin rijiya tsundum! Ta ce, wayyo! Baba ka iya wannan? To, Farfesa a lura.

Yarda da cewa, ga kowa ana koyo. Kana koyo ga d’anka da abokinka da yayanka da k’anenka da d’alibinka da d’alibin d’alibinka. Samun kujerar ba hujja ba ce ta rufe karatu ba da cewa an fi kowa. Dubi ka-ce na-ce tsakanin yaran Firamare da k’wararrun injiniyoyin hanya:

An ce, wasu injiniyoyi suka je wani gari da motar cire itace. K’ofar ganuwar garin ta hana su shiga domin motar ta yi tsawo. Suka share wuni suna tunanin yadda za su yi, can suka yanke shawarar a fashe k’ofar ganuwar motar ta wuce, in an k’are aiki a gyara. Lebarori na batun fara aiki sai ga yara ‘yan Firamare sun taso k’wallo, suka ce: “Ah! Ga mota ba wurin wucewa”, sai wani ya ce: “In ni ne, zan fasa k’ofar”, wani ya ce: “Ni d’aga motar zan sa a yi” can sai wani ya dube ta da kyau ya ce, “In ni ne zan sace tayoyinta ta wuce, a nemo mai faci ya sa iska”. K’wararrun injiniyoyin na jin haka suka bi shawarar yaro suka ci nasara. Farfesa a kula.

Farfesa ya sani cewa, saninsa ba hujja ce ta k’aryata wani ko wasu ko da a kan kuskure suke. Abin sani ga Farfesa shi ne, amfani da saninsa ya gyara kuren wani cikin nishad’i da annashawa da tawali’u. Dubi yadda Sarkin Wawan Sarkin Katsina ya yi da telansa:

Wawan Sarkin ya ba tela d’inki an sha yi masa k’arya, ya zo ya kar’ba in ya zo ba a k’are ba. Da aka yi masa alk’awalin k’arshe ya dako sabko, tela na hangesa sai ya shige cikin kayan da ake kawo d’unki aka jibga masa su aka lullu’be shi. Ashe an manta ba rufe yatsun k’afarsa ba. Da Wawa Sarki ya shiga d’akin d’inki suka ce: “Baba tela ya je kasuwa ya nemo zaren da zai yi maka aiki ka je an jima ka dawo”. Ya tsaya ya dubi kayan d’inki ya ga k’afar tela a waje ya ce: “To babu laifi, a dai cika alk’awali, kuma in ya dawo ku gaya masa baya da kyau dattijo na tafiya da k’afa d’aya a kasuwa, ya dinga zuwa da k’afafunsa biyu mana”. A gai da Farfesa Wawan Sarki.

Dole Farfesa ya san ana dafa kafad’arsa a fi shi tsawo. Wanda ka koyar ya zo da wata basira cikin basirar da ka koyar da shi, kai Allah bai ba ka ba. Godiya ya kamata ka yi ba ‘bata rai da kuka za ka yi ba. Dubi k’issar malami da matarsa da almajirinsa ka k’ara karatu:

Malami ne ya fita zuwa zauren karatu bai ci abinci ba. Ya bayar a gasa masa zakara. Zakara ya gasu, ga jama’a sun taru, ga malam na jin yunwa. Matarsa ta ce ma d’alibansa: Wa zai yi dabarar gaya wa maigida zakara ya nuna? ‘Daya daga ciki ya ce, zai yi. Ya je zaure ya tarar jama’a tinjim, kuma duk irinmu ne jahilai masu tambaya. Sai yaro ya durk’usa ya aje allo a gaban malam ya ce:



Yaro: Malam Zakarutu ya nun naam!

Malam: To, a sarkafe shi ga tankallazii,

: Hatta jama’atu Watseem!

Farfesa a nan wane ne malam? Wane ne d’alibi? Haka ake son mu kasance, ba mu dinga hawaye idan d’alibi ya zo da hazak’a ba.

Zuga da kirari da yabo ba su sa Farfesa ya wuce saninsa. Duk abin da ba ya iyawa zai yi tsaye ya zama d’alibi sai ya san shi. Da yabo da kushewa duk ba su sa ya ci mutunci martabar ilimi. Karatun malam Gambo da Farfesa Manu Dahin Gumbire abin lura ne. Manu ya shahara ga sata. Ga abin da suka yi da Gambo:

Jagora         : ‘Dan Dahi Manu,

: Wanga da ag Gumbire zaune,

: Ko bataliyas soja tas shiga daji,

: In gaya maka Manu Dahi na d’an taya ta,

: Yac ce min: “Mis samu Gambo?”

: Nac ce, “Tudu Tsoho yat ta’ba ni,

: yac ce: “Maganar banza da yohi”,

: In akwai ta da dad’i ka je da kanka

: Ai ba mu tsar ma tambaya ba”.

Farfesa Manu ya yarda gaba da gabanta ya rufa wa kansa asiri, yau ga mu muna amfana da fatawarsu. Haba Farfesa! Duk mai ganin iliminsa ya kai yana gwada tsawo da kowa ba Farfesa ba ne farfesu ne. Hattara da kayan Allah!

Kasance mai hankalin amfani da ilimi wajen gyaran matsalar ilimi, ba da cin fuska da cin zarafi da muk’abala da bugun gaban wa mutum nan. Ya kyautu Farfesa ya san tunatar da d’alibi da mai ilimi cikin ilimi, wani haske ne na karatu da ke amfanar mai gyara d mai kuskure.

An ce, wani cikakken malami a Masar ya je aikin Hajji da d’alibansa. Ba sa ta’ba ganin Ka’aba ba. Da ganin ta sai suka rungume ta suna kuka. Suna shafar ta suna sumbata. Abin ya koma bautar d’akin ba bautar Allah ba. Da wani k’wararren shaihin malamin tauhidi ya gan su sai ya d’auki Alk’ur’ani, ya ce gun shaihin neman a koya masa karatu da fassara; ya ce: Akarama kallahu a taimake ni da fassara wannan aya”: “Fal ya’abuduu Rabbu haazal baiti.” Shehi ya fassara masa da cewa: “Ku Bautawa Ubangijin wannan d’aki”. Sai shehin ya ahumo ya kira d’alibansa ya ce, “Ku zo mu gyara, “Rabbu haazal baiti” aka ce, ba “haazal baiti ba”. Daga nan suka daina abin da suke suka ci gaba da d’awafi yadda shari’a ta tanada. Tabbas! Muna da aiki baya.

K’wararren Farfesa shi ne mai yarda da fassararsa da ta waninsa, matuk’ar ba su ci karo da sawaba ba. Wanda ya yarda duk abin da ya sani wani ya san sa’baninsa ya huta da d’irkaniya, mota cikin randa. Wani shehi ya yi wa jama’a nasiha da su rik’a kyauta da sadaka. Ya gaya masu cewa: “Ku sani rubuce yake, in ka ci ya k’are, in ka ba wani ya k’are, in ba ka ba wani ba ya k’are”. Jama’a kowa ya gamsu sai ‘Dankama ya ce: “Akwai gyara ga hadisin malam, fassarar nan ba ta lugudu ba. Malam ya so ya yarda sai jama’a suka yi caa kamar su cinye ‘Dankama. Sarkin gari ya ce: “To, kai kawo taka fassara mu jiya” ‘Dankama ya ce: “In ka ci ya k’are, in ka ba wani ya k’are, in ba ka ba kowa ba ka dad’e kana cin abinka”. Me za ka ce da wannan Farfesa?

An so Farfesa ya kasance mai cikakken wayo da k’oshin ilimin tunkarar kowane ilimi ya bijiro masa. Da iliminsa zai yi amfani ya ku’butar da kansa da wani ya ceci al’umma. Labarin ‘barawon mak’ullin mota da direba abin lura ne:

Wani fitaccen ‘barawo ne ya dami mutanen Arkilla Federal low coast. Ya sha sace wa direbobi mak’ullan mata da dare ya je ya bud’e ya sace abin da ke ciki. Wata rana ya d’auki mak’ulli wani yaron Alwasa. Yaron mai wayo ne, da ya tabbata yaron ne ya sace mak’ulli, kuma ya gan shi cikin aljihunsa. Idan aka ta da rigima zai iya jefa shi wani wuri ya ‘bace, ya kira ‘barawon gefe d’aya. Ya zaro naira hamsi ya ba ‘barawon ya nuna masa wata kwana ta unguwar mai nisa ya ce: “Ga yaron da ya sace min mak’ullin motata can ya shiga kwanar can, je ka k’wato min abina ka ci goron naira hamsin”. Da jin haka sai ‘barawon ya ruga da gudu ya shiga kwanar ya dawo ya ciro mak’ullai a aljihunsa ya ce: “Ga su, su ne wad’annan? Abdullahi Alwasa ya ce: “Su ne na gode”

Da k’asar Turai ne aka yi haka, ba abin mamaki ba ne a kira direban a ba shi kyauta ko wata jami’a ta ba shi digirin girmamawa. Madalla! Ashe a tasha ma akwai masana da manyan Farfesoshi.

Ko yaushe a dinga tsantseni wajen yanke hukuncin ilimi. Wannan wata dama ce ta nuna wa mutane su daina nuna sun iya ko da sun sani. A al’adance gwani ko ya san abu yana so ya ji ta bakin abokin tattaunawa. Domin Hausawa cewa, suka yi, “ko ‘bata k’ara sanin daji ne”. K’issar wani malami da ya bugi k’irjin cewa, in yana raye ba a k’ara musun kwanan wata wani babban darasi ne:

Musu ya kaure a masallaci kan kwanan wata domin a tantance tsayuwar Ramalana. Da musu ya tsananta sai wani malami ya tashi ya gaya wa jama’a cewa, in yana raye ya d’auke wa kowa ganin wata da tantance kwanakinsa. Bayan an yi ittifak’in yau d’aya ga wata, ya je gida ya d’auko burgamensa ya rataya shi a rumfar k’ofar d’akinsa. Kowace rana ta Allah sai ya d’auko tsakuwa d’aya ya jefa a ciki. Ashe d’iyarsa ta lura da cewa, kowace asuba malam in ya dawo da salla sai ya jefa tsakuwa d’aya burgame. Halinka da yaro, sai ta dinga taya shi, a koyaushe ta lura ya jefa sai ta la’ba’bo da nata cike da d’an hannunta ta jefa. A kwana a tashi gardama ta sake tashi kan tsayuwar wata. Malam ya ce, “Ku bari in zo an gama”. Ya je gida ya sauke burgami ya k’yarga ya ga wajen (80-100), ya sake rairayewa ya tsame (50-60) ya sake d’ebe wasu ya fitar da (30-40) ya zo masallaci ya ce wa jama’a: “Yau kwanan wata (35), “aka bushe da dariya. Ya ce: “Da na gaya maku abin da burgamina ya fad’a ai za ku sha mamaki.

Dank’ari! Ashe gaskiyar Bahaushe da ya ce, “Kowa ya ce, ya ce, sai ya ce, bai ce ba”. Idan haka karatu da bincike yake, don me ba za mu rage doro da tak’ama ba?

Farfesa ilimi amana ce ka daina ‘boye wa mai koyo, shi ka da ka yaudare shi da shi, duk abin da za a koyar ga d’alibai ka tabbatar da gaskiya ce, a gaban kowa ya ambace shi ba za a muzanta shi ba balle a yi masa dariya. Na tuna da labarin wani Resdan Bature da yaronsa mai kula masa da dokinsa:

A kowace rana Resdan na cire kud’i ya bayar domin a kula masa da dokin da yake hawa. Yaro yakan je ya ce: “A kawo kud’in ciyawa, a kawo na gyaran linzami, ko k’aimi ko na gyaran turke da na tur!” Duk Bature ya bayar. Da Bature ya ji Hausa sosai sai ya je fadar sarki ana cikin tad’i ya ce yana son a gaya masa abin da ake ce wa tur!” Kowa ya kasa, ya gaya wa sarki cewa, a kira masa yaron da ke kula da dokinsa ya san kalmar, aka kira shi a fada. Ya fad’i ma’anr kalmar “tur!” Sai turu-turu da idanu. Da aka gano yaudara ce sai aka dinga yi masa kirari, “Adad’e ana yi” sai ya ce: “Sai gaskiya”.

Farfesa masani ne mai ilimin hangen nesa tare da kiyaye karatun yau a tunkari na gobe. Wannan ce ta sa a koyaushe ba a girshinsa a fagen karatu, domin da tambaya yake tunkarar mai tambaya, har sai tambaya ta fito da amsar wata tambaya a kasa wata tambaya ta gaba. Sak’on Yakubu Gawon zuwa ga Sarkin Musulmi Abubakar  III da tambayar sarkin Gwandu Haruna wani babban kundin karatu ne.

A zamanin mulkin Yakubu Gawon ya samu labarin ana son a yi masa tashintashina a ham’bare gwamnatinsa. Ya aika wa Sarkin Musulmi Abubakar III cewa a tara sarakuna su shirya talakawa a yi zanga-zangar goyon bayan gwamnati domin a samu damar kama masu son su yi ba-mu-soa hukunta su. Sarkin Musulmi ya kira taron sarakuna, wakilan gwamnatin tarayya suka hallara a taron, da sarki ya karanto sak’on shugaban k’asa, sai ya ce: “Abdullahin Gwandu (cewa da sarkin Gwandu Haruna) me kuka gani?” Sarkin Gwandu Haruna ya ce: “A gaya wa shugaban k’asa cewa, Mai Martaba Sarkin Musulmi ya ce: “In suka sa talakawa zanga-zangar ‘muna so’ idan wata rana talakawa suka yi masu zanga-zangar ‘bamu-so’,. Wa zai kwantar da tarzomar?”

Wannan tambaya har yau gwamnatin Yakubu Gawon ba ta ba da amsar ta ba. Haka malamanmu suka ce, a koyaushe Farfesa ya yi magana a ji ta a yi tangam, mai zuwa hajji ya gamu da Annabi (SAW).

Ba Fankam – Fankam ne Kilishi ba, Tsomi


Hausawa suka ce, “Maza tamkar gyad’a ne sai an ‘bare, za a san mai k’waya”. A al’adance ba kowane mutum ke cin sunansa ba. Babbar buk’ata ga kowane mutum ita ce, “idan aka ga mutum sunansa na d’aukaka, a ga ayyukansa da halayensa na d’aukaka”. Ba abin mamaki ba ne a irin k’arshen zamaninmu a tarar da Farfesa bai cika mudun da ya kamata a ce ya cika ba a fannin karatu. Wanda duk Allah ya nufi aka nad’a wa wannan rawani, ya sani cewa:

Rawanin karatu ne na har abada babu ranar hutu har sai an kwanta kushewa. Sunanka da rawanin da aka ba ka ba su yi wa jahili barazana sai dai a yi taho- mu gama. Ba a wa ilimi kwalo-kwalo da dabarar da wayon sanin gari na shekaru. In an san abu, an san shi, in ba a san shi ba, ba a san shi ba. A zage dantsen neman a san shi. Na yarda da hangen Marigayi ‘Dantalata Maiduma Bunza, makad’in tauri da yake cewa:

Jagora: Ba wayo aka wa yuk’a ba,

:Ba ta da ban magana sai tauri.

Gindi: Gara da kaz zaka baban Idi,

: Dajin namu da zabbin gumbi.

Wane wayo za a yi wa kujerar Farfesa in babu karatu kuma ba a yi shi ba? Ai sai dai karatun Baru uwa uba ga maraye. Wa in bari bari, wa in kasada kasada.

Kama da Wane ba Wane ba ne


Kujerar Farfesa ba ita ce ilimi ba, sannan kuma Farfesa ba shi ne ilimi ba. Zama Farfesa ba ita ce hujjar gogewa da k’warewa ba. Babbar hujjar da babu makawa a kan ta ita ce, “Karatu” a tabbata an yi shi, an san shi, an saba da shi, karatun ya zama tobashin zuciya abokin baki. Ina amfani a ce wane ya kai, a zo da d’an ma’auni a tarar bai kai ba. A sake bitar tunanin Narambad’a:

Jagora: Ai An wa wani Alk’alin k’asa,

Yara  : Da babu sani taw walwale,

Jagora: Bai san amma ba, bai san sabbi ba,

Yara  : Shi dai shi tsare “Min nun guda,

Jagora: Can gaba ko “ra baguje”,

; Iya kas sanin an nan.

Gindi: Ya san girma ya san yabo,

: Mu zo mu ga Alk’ali Abu.


Ba Sunan Ba Aikin


Malaman k’asar Hausa idan aka ce wane ya sauke Alk’ur’ani sukan ce, “ Allah ya ba da karatun tsoron Allah”. Abin da suke nufi shi ne, ba karatun za a yi wa hisabi ranar Alk’iyama ba, mai karatun za a yi wa. Idan an hau kujerar Farfesa ana son a ga ayyuka na d’a’a da biyayya ga gabaci da rahama a magana da rubutu da k’auna da soyayya ga wanda aka sani da wanda ba a sani ba. Da makamin da sunan Farfesa ke d’aukaka mutum ba za a ji suna wani a bangon k’asa ba face Farfesa. Aiki mai sunan shi ke d’agar da sunan da aiki a ji su a duniyar zamaninsa. Wani mawak’in mashaya giya ya yi wa wani shaihin malami wa’azi lokacin da shaihi ya ce masu ‘yan wuta masu sa’bo. Shi kuwa ya mayar da raddi da cewa:

Jagora: Dan nan sai nak kada baki,

: Nac ce malam ka yi sa’bo,

: ‘Dan laifinmu na shan giya na,

: Wansu da sata, wansu maita,

: Wansu had da bid’ar matan mak’wabta,

: Ba allo ka ganin ma’aiki ba,

: In allo ka ganin Ma’aki?

: Shekarar bana danya ba ta toho,

: Dud da ni sai na yi bakwai ba.

(Kwara Mairuwa: wak’ar ‘yan Birni ku yi tamataila, 1975)

Wai in don ta alluna ne kawai ke sa a ga Annabi (SAW) ba a yi aiki nagartacce ba, to shi zai sassare itatuwan danya gaba d’aya, (da ita ake yin allo) ya yi wa kansa bakwai ya ga mai hana masa ganin Manzon rahama (SAW).

Farfesanci


Farfesanci wata babbar daraja ce da d’aukaka wadda ke tabbata wa duniya cewa, lallai kujerar da jami’a ta ba mutum bisa cancanta aka ba shi da lokacin da aka saka k’afa a jami’a, har lokacin da aka samu hawa kujerar Farfesa, duk nema ake yi. Duk wani aiki da ake yi don a kai ga kujerar nan ne. Hausawa cewa suka yi, “Ba a san maci tuwo ba sai miya ta k’are”. Idan an hau kujerar ana buk’atar a ga :

Wani sabon k’wazonka na bincike da rubuce-rubuce da za su tabbatar da cewa, lallai k’wazonka ne ba kirarin matsoraci ba. Duk wata takarda ko littafi ko bincike ya fito daga gare ka a tabbata k’wazon ka ne sabo ba d’aurayar baya ba ce, ba damben wada ba ne.

Farfesanci shi ne a samu fannin da aka ce ka cancanta, hatta da mala’iku su shaida Allah ya hore maka shi. Jami’arka ba ta fargaban sa ka gaba, ka wakilce ta domin ta san ko an daka cikin turmi da ku cikin masu fita. K’asarku da jiharku ba su fargaba wajen neman taimakonka a fanninka saboda an san zancenka, nashin k’asa ne babu kure.

Duk yadda zamani ya juya, indai kana raye, ba a tababan tura ku gaba wajen saka wa jahilci takumkumi da yi wa ilimi talala na sai baba ta gani. Kuna zaune gida a nemo wasu k’wararru waje kunya ne a kanku. Ku yi tsari ya kasa kar’buwa zance ne. Ku yi nuni a kasa ganin haske labari ne. Ku sa hannu a ce a dakata shirme ne. Ai ku ne igiya mad’aura kaya, kowa ya yi ba da ku ba ta tsinke.

Hankali ba zai yarda da a ba ka tsani/kwaranga ga hau rumbu ka d’ebo abinci ka ci, kai da iyalanka, da ‘yan uwanka, da masoyanka, sai kun k’oshi ka d’auke tsanin ka ‘boye wai kar a sake amfani da shi. ‘Dalibbai nawa ka yaye kuna tare ana fafatawa? Nawa ka yi wa mafarin samun kujera irin taka? Nawa an nan kana raino da kake son su hau munzalinka gabanin ka yi murabus ko duniya ta kore ka da aiki? Me ka rubuta ka ajiye wa na baya domin su karanta su shahara kamar yadda ka yi? A d’an namu gani na d’alibbai, Furofesanci ya fi Farfesan wuya, domin Farfesa nawa aka fesa wa turare har suka kai ga kujerar sai sun haye su fesa wa d’alibai barkonon tsohuwa?

Hankali ka Gani ba Ido ba


Amfani ilimi ya saka wa mai shi hankalin da zai iya zama da kowa, a yi huld’ar arziki da mutunci.  Da yawa, hankali na koya wa ilimi karatu, sai dai idan ilimi ya yi tambaya a raba ‘yan kallo. Da magabatnmu da mabuk’atanmu da mu d’alibbai da ‘yan kallo mu kiyaye sosai da sanin:

Kujerar Farfesa ba ta tsira hasada ba ce da abokan gwagwarmaya. Tir! Da hassadar ka akai ana harin kai gare ta?

Ba ta girman kai ba ce, na ganin dole sai an duk’a maka

Ba ta sauke karatu ba ce a dangane allo, wai an kai walawaladaina, walam malam na k’iya.

Ba ta soke k’wazon magabata ba ce, ka fito da naka salo da sanin gari.

Ba kujerar neman muk’amai ba ce, kujera ce ta nema wa masu neman kujerun girma, mai ita sai gyashin Alhamdulillah.

Ba kujerar kafa wata sabuwar mazhaba ba ce, don duniya ta ji kai ma ka kai. Assha! Babu k’ira me ya ci gawai?

Ba kujerar kirari ba ce, wai girma ya kawo tsoro ya d’ebe. Kash! Da wa ka yi kukuwa ka k’wato ta.

Sakamakon Bincike da Shawara


Kowane ilimi na duniya yana da tsarin da aka hau aka same shi. Muk’amin Farfesa da a Arewacin k’asarmu sai k’wara-k’wara. A yau, saboda yawaitar jami’o’i a yankinmu sun fara yawaita. Ina d’an hasashen ta’bar’barewar ilimi a k’asarmu da mummunar ak’idar nan ta cin hanci da rashawa da magud’i babu fannin da ya tsira ciki a k’asarmu. Babu laifi a samo wani tsanin da zai rik’a zaburar da Farfesoshi su k’ara amfanin k’asa da jama’a. A fafutukar rubuta wannan takarda na gano cewa:

Mafi yawan farfesoshin k’asar nan sun manyanta shekaru na yi masu barazana. Wane lokaci ne suka samu na kulawa da lafiyar jikinsu da farfesanci?

Jingar da aka biya ba ta taka kara ta karya ba, kud’ad’en bincike da ake bayarwa ko kud’in rangadin bincike ba su biya, balle a tsaya a yi aiki a wallafa shi.

Yawan d’alibban da ake bai wa masanan digirin B.A da M.A da PhD sun yi yawa. Abin takaici an daina biyan tallafi ga masu duba d’alibai da yawa. Wannan kisan mummuk’e ta’addanci ne ga ilimi.

Siyasa ta shiga jami’o’i haik’an musamman jami’o’in jihohi da sababbi, in ba a kula ba za su ragaita kujerar farfesa ta koma k’ark’ashin ofishin gwamna. Ko ofishin Pati

A fito da wasu gawurtattun mujallu na k’asa da za su rik’a wallafa ayyukan farfesoshi kawai. A yi tsaye ganin dole kowane farfesa sai an ji muryarsa a ciki.

Bayan laccar shimfid’a Buzun karatu (Inaugural lacca) a fito da laccar shekara-shekara ta manyan masana da kowane masani zai baje kolin wani sabon abu da ya hango a shekara.

Hukuma ta sa ahnnu ga wallafa ayyukan farfesoshi da tallafa musu da biyansu na goro in ana ta ciki da wane hankali za a yi bincike.

Nad’ewa


Hak’ik’a ba a san maci tuwo ba sai miya ta k’are. Ga kowane d’alibin sani mai k’wazo da naci da kishin kai, samun kujerar farfesa gare shi da al’ummarsa babbar nasara ce. Hawan kujera da rashin cancanta wani tonon silili ne, da zubar da mutunci ga d’an k’uk’e-na-k’uk’e. Ilimin da ladabi da biyayya da hankali mak’wabtan juna ne, amfanin sani aiki da shi. Daga cikin sirrin ilmi akwai rik’on gaskiya da fake amana da godewa ga wanda ya azurta ka da shi. Narambad’a ya ce a gaya muna:

Jagora: Duk d’an malamin,

: Da yak’ k’i biyan Allah,

: yak kid’e bak’i,

Yara  : To, Allah yana watse kayanai.

Jagora: Ya kama yawo,

Yara  : Yannan gidan har ya zan kango.

Gindi : Gagarau mai buge kangara Ali ‘Yandoto,

: Ba shi son wargi ba a kai mai batun banza.

Manazarta

Post a Comment

0 Comments