Ticker

    Loading......

Adashen Ƙauna 3: A’isha Humaira



Allah Mahalicci maƙagin dukka tunanina,
A gare ka kaɗai nake miƙo dukka buƙatuna,
A har kullum kuwa kai ɗai ke cika burina.

Ilahu ka ƙara salati wurinsa macecina,
Ibnu Abdul, iyalai da sahabban manzona,
Ilahu Musulmai duk ka saka da Humairana.

Sanina na yi asusun dukka kalamaina,
Sannan na adana zuci da har ma gaɓɓaina,
Soyayyar da na tsara Ash’ab ce cafe ƙauna.

 
Halinta ya sa ta ta mallake dukkan ƙalbina,
Humaira a sura har ta zarci kwatancena,
Humaira guda ce ga matayen duka ƙarnina.

Allah ne ya dube ni ya amsa buƙatuna,
A nan ko ya ba ni Humaira ciko na muraduna,
A yau haɗuwarmu ta sa na zarce sa’o’ina.

Humaira ki zo na zo zauna ki ji zancena,
Haɗuwar da mu kai nai alƙawar kama amana,
Har abadan sam ba ki nadamar amsa kirana.

Ujila naka yi na a shafa du’a’in haɗa ƙauna,
Umumin zuci a nan ne za ta yiwo rana,
Ussin jin daɗi don zan sanya ki a lemana.

Mataye za sui gulman ki ƙwarai a hasashena,
Matsayinki zai sa musu kishi har ma da tsana,
Mance su mu zauna lau lambun soyayyana.

Alƙawarin nai na riƙe ki tafarkin manzona,
A’isha kin zama NI a gare NI tunanina,
A kullum in zama KE a gare KI shi ne fatana.

Idan na yi aibu ki nusance ni cikin ƙauna,
Idan kika kauce nai magana ki bi zancena,
In mun riƙe wannan za mu ci riba kan ƙauna.

Ranki ya zambo ba ya baƙi sam-sam kaina,
Rabi na jikina ya za ai na saka rana?
Rashi na fahimta sam kada mui wa juna.

Allah naka roƙo mai sa in cim ma mafarkaina,
Allah sa bayan shekaru ashirin daga aurena,
A ce ni da ke su wuce muna mararin juna.



Post a Comment

0 Comments