Ticker

    Loading......

Laifi Tudu Ne



Waƙar ƙwar uku ce, babban amsa amonta “na”. Yawan baitocinta saba’in da shida (76). An kammala ta ranar 10/06/2013 a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina. Mai yawo lisafin laifukan mutane da leƙen kasawarsu da ƙoƙarin ci musu zarafi da muzanta su bai tsaya da kyau ya karanci nasa hali ba. Don haka, waƙAr take hararar abubuwan da mahasada da magabta da ‘yan sa ido da ‘yan sai-mun-gani ke ƙoƙarin kai hari ga marubucinta. A ganin Bahaushe, mutum duk ɗan tara ne. Da akwai ɗan goma, da shi ya kamata ya yi wa ‘yan tara kallon kifi na ganin ka mai jar koma (homa). Kama kanka! Wanda ke cikin ta tsaka mai wuya, ina ya ga bakin kirari?
-----------------------------
------------------------------

1.        Allah na roƙi taimako ga rubutuna,
Na nemi dubun tsari ga dukkan lafazina,
Kar in cutar da masu son saurare na.

2.           Taso haba ɗan'uwa ka zo in maka hira,
Na ji ana tsegumi shiru ba mai gyara,
Lungu-lungu ana ƙidayan laifina.

3.           Laifin farko rashin zamana ɗibgagge,
In koma baya in kasance jibgagge,
In bi wanin Jalla kun ji farkon laifina.

4.           Ni da na yo sassabe da turbe nai maimai,
Ga taki ya yi kyau ga shuka ba ƙamfai,
In tsiri yin ƙwadago ga gonan maƙiyina.

5.       Wai don na gamsu gun rabon mahaliccina,
Na ƙi aminta ga galihun mai tsince na,
Girman kai an ka fassara shi ga laifina.

6.       Laifin ga na ukku shi kaɗai ke ban haushi,
Gurgu ke arashi da zunɗen tarkoshi,
Na ce a yi hattara a shashace batuna.

7.       An ce rowa gare ni wai ban sake hannu,
Ban kwaso kuɗin haramiya in saye shanu,
In kai su kiyo gidan waɗanda ka zargina.

8.       In dai kauce wa ɗan hali ne laifina,
In zama Nazaƙi ko'ina aji sunana,
Na yahe zama da ku abokan hirana.

9.       Laifi na biyar gare su wai na cika sabko,
          Don me koyaushe ni ka kwashe kashin farko?
Kamin su iso su iske na kwashe rabona.

10.     Laifin ga na shidda wai Alu yai musu rata,
Don me koyaushe Rabbana nai mini gata,
Me zan cewa a nan na kare laifina?

11.     Laifi na bakwai gare su na ƙi zama wawa,
Na ƙi aminta a sa zuma ga kunun kunwa,
          In an ka taɓe ni take in hau bakina.

12.     Laifi na takwas da Audu yallabarta min,
Wai na cika hasadar su, nan sun ka diran min,
Me sun ka aje da babu ninkinsa gidansa?

13.     An so a haɗa ni yin faɗa da abokaina,
An ka gaza an ka lallaɓo ga maƙwabtana,
Na' ahumo nat tsaya da kyau da ƙafafuna.

14.     Laifina ƙin bari a ɓata mini suna,
Bayan ƙazafi da tsegumin cin zarafina,
Ya zama tilas a yanzu in hau bakina.

15.     An ce wayo gare ni ba a yi min burtu,
Rami duk an ka yo ina mai sai guntu,
Take in tsallake haƙon ga ƙafafuna.

16.          Laifina kin bari a kaɗa ni akulki,
Na ki sako kai a danƙarai bahagon kulki,
     Bayan na gangara a aure matana.

17.                        An ce rigima garan kaman mai kashe kura,
Don na hana doli-doli ɓata muna shara,
Na kwakkwashe shi na zuba shi a kwandona.

18.                        Laifina gyangyadi idan na gaza kwana,
In ya fizge ni ba a j in hansarina,
Ɗan motsi ɗan kaɗan na buɗe idanuna.

19.                       Na kai musu ko'ina saboda zuwa gona,
Hannu biyu kowane wata ga adashina,
Bakin ƙarfin talakka na ima gidana.

20.                         Mamakin duniya Alu na gaza barci,
Ɗan bokona ya tsunduma su cikin ƙunci,
Hab bisa karaga ana ta kamun sunana.

21.                         Na rantse har ga wanda yay yo'ni Ta'ala,
Ban taɓa jin kai ba ko kirarin sa mala,
An ka sawo an ka sakaɗa bisa laifina.

22.                        Laifina ba ni gaisuwa, ban kai kaiwa,
Na ki tumulli da jewaɗi garkar kowa,
In bi dare jijjihi ina kai kukana.

23.                         An ce ni nah hana ma jam'iyya girma,
   Don na ƙi bari a mai da al'umma kurma,
             Na ce a yi hattara da wasan Afajaana.

24.                        Kwat tuba da yin kidin duma ba ya na kurya,
Ɗan Babule ya tuba bai kama garaya,
Kun ji misalin da nay yi an ka ga laifina.

25.                         Ban taɓa jin kai ba ba ni ƙaunar son girma,
Je tambayi 'yan ajinmu had da abokai ma,
In ka yi musun su tambayo malammaina.

26.                 Laifin Ali yai yawa rashin ƙyale azazza,
    In bar maƙiya su hau cikina su yi murza,
      Har in yi kururuwa a ruga cetona.

27.                         Laifina ƙin hawa kujera mai lauɗi,
In yi ta doro a kewaye ni ana kauɗi,
In ba da haramiya a ƙara mini suna.

28.                         Ban taɓa ƙaryar hadin jini da sarakai ba,
Ban taɓa cewa gidanmu an gaji kuɗi ba,
    Koyaushe faɗa ake haɗa ni da Sardauna. 

29.                         Faufau ban gaji sanƙiranci ga uwa ba,
Ban gaji zama a fada faufau ga uba ba,
Koyaushe a Kanwuri ake kai ƙara na.

30.         Don na ƙi zama a fada tallan gilɓoshi,
   Kigama Malam Naƙoƙi mai 'yan ƙissoshi,
   Hannu ga gaba da ya ji an kiri sunana.

31.                         Wai laifina da nag ga an matsa sara na,
Nag gangame nau-ya-nau na jaye jiragena,
                   Naƙ ƙetara lafiya da ni da iyalaina.

32.     An ce sauri garan ga fid do ra'ayina,
Ga kuma tsaurin tsiya ga kare tunannina,
Na ƙi zama raƙumi a ja da akalana.

33.     An ce suna Alu faɗa ne da hasumi,
Mis sa doki ka zabura in ya ji ƙaimi?
Ai ta kilisa ana gumi ko ba rana?

34.     Kowa yas san halinmu mun fi zuma zaƙi,
Wa za a haye da caccaka a ji mai sauƙi?
In wannan ne faɗa iina ne sunana.

35.     Dan samuna da bai wuce ɗebi haɗe ba,
Shi ne laifin Alu zaman ban taɓare ba,
In zama kekenmaƙa ga ɗakin maƙiyana.

36.          Laifina babba sun ka ce neman kuɗɗi,
Kaunarsu na zo wurinsu rance su ji daɗi,
In kasa biya a hau duron a ci sunana.

37.     Sun ce yawo garan kamar naira birni,
Take a gane ni na wuce ka ce zunni,
Na ƙi zaman dandali na cin naman juna.

38.     To kai Mannanu mai ɗuwawun kashe wundi,
Tun Ikko a ƙunso tsegumi sai Mungadi,
Kai ka musu tsintar rubutunmu Kaduna?

39.     Laifin ɗaya nai zaton kaman sun manta shi,
Nat tar da uban gidansu na nanata shi,
Wai na ƙi shiri da masu ɓata mini suna.

40.     Assha maganar ga ko kaɗan ba ta taso ba,
          Mai bin Sunna daɗai shari’a yaka duba,
                   Don ita ke canjaras a gane kuren juna.

41.     Ban taɓa jin muminin da an ka ƙuƙunta ba,
          An ka kwarare shi an ka so a sabatta ba,
                   Yaƙ ƙi ya ruga kwatankwacin ƙyasta ashana.

42.     Ban ji sahabin da ya aminta a cuta ba,
          Ban mu ga nassin da sun ka rungumi maƙiya ba,
                   Mai yawo ko’ina shi ɓata musu suna.

43.     Ba mu da ƙimar da taw wuce darajar suna,
          Ba mu da girman da yaw wuce kyawon suna,
                   Mai cin zarafinsa ba shiri ku ji zancena.

44.     Kowane buzu da raƙuminai shika gata,
          Malam bai ɗaukaka idan ba makaranta,
                   Wa zai zama kamili idan ya rasa suna?

45.     In Dakka Na’umme na rawan gwalmo a gona,
          Roggo da makunyaci da ɗan gugar zana,
                   Ba ai musu take don gudun ɓanna suna.

46.     Zargi ya kasa cin Alu an biɗo yuƙa,
          Had da itace da sanduna igiyar tunƙa,
                   Bayan an rataye a bizne kabarina.

47.     In nim miƙo wuya a damƙe sai yanka,
          Barho na sha-da-yanzu mai mugun yanka,
                   Fatarsu guda shi samu kai ga maƙoshina.

48.     Babu faragar gudu zaman rami an nan,
          Suna nai yunƙura ka sake direwa nan,
                   Ga zarto an aje na yanke ƙafafuna.

49.     Ko na yi gaba-gaba da taro wane ni!
          Don na ga barandami da kaifi kaico ni!
                   Alƙawali sun ka yo na zazzage tumbina.

50.     Manta da batun zama bala’i yai nisa,
          An sa ni cikin rutsin da ba ɗaukar fansa,
                   An sa sarƙa ga hannuwa da ƙafafuna.

51.     Ɗan dama na guda abin yai mini sauƙi,
          Tuya an manta albasa ba ta masƙi,
                   An manta abin da za shi liƙe bakina.

52.     Laifina ba ni rena duk mai ra’ayina,
          Zan sake fuska da murmushi gun baƙina,
                   Ka ce mun shekare ɗari da sanin juna.

53.     Na ƙi zama dabba’una mai fuskar shanu,
          In sha toka da ɓata rai in riƙe hannu,
                   Wai ni ƙato a daina wasa a wajena.

54.     Ban ce a ƙi shugaba ba ban kuma zargai ba,
          Shi ko shi sani fa ba kaman Annabi ne ba,
                   Bai kwaso taɓasgara ya ɓata muna suna.

55.     Ni dai ban ce rabon kashin bai gamsan ba,
          Ban ce a raba da ni a ƙyale kowa ba,
                   Cewa a raba da kyau ya sa aka zargi na.

56.     Koyaushe uban kashi ya kwashe kashin farko!
          In an luro shi ce gidanai aka aiko,
                   Wai ‘yammuna yay yi yaudara safe da rana.

57.     Laifina yin tsayin daka in bi abina,
          Don na hana zurmuguɗɗu faufau ga kasona,
                   An ka yi banga da ‘yan rawa a ƙi takena.

58.     Ban ga dalili na maƙurar ɗan aike ba,
          Ga mai aiken ana gani ba a dokai ba,
                   Ƙarya filin wuri a sake mata suna.

59.     Babban naƙali ka san halin masu kula ma,
          Kai ko ka tsaya da kyau ka bar ba su makama,
                   An ce raggo ya sha hura ya saɓa gona.

60.     Babban magana a kanka kowa ya gaya ma,  
          Kar ka yi aikin da za a rena maka girma,
                   In ta ruɓa Kamba sunsune ta a Banganna.

61.     Kyawon ɗa har ya kwanta dama ga sarkinai,
          Bai muzantar da malami magabacinai,
                   Balle a haɗa da shi a ɓata musu suna.

62.     In ga wayo da hankali da sanin girma,
          Ɗan tsako zai gwada wa giwa ya girma,
                   Don ta kula mai ya je ya ɓata mata suna.

63.     Wautan Jigji hawan kirari ga kura,
          Ya ji awaki suna faɗin: “Ka wuce tsara”,
                   Wai don bokansa ya yi mai layar zana.

64.    In kag ga mutum shina kirarin ya girma
Tambas shi wurin da yas sayo shi, shi nuna ma,
          Kowac ci tumu shi gai da mai shukan gona.

65.     Jin kai na mai da malami bawan gona,
Girman kai bai barin matashi ya yi suna,
Rowa na ƙaddaro wa ɗa mugun suna.

66.     Son kai ka kashe mutum da sauran sheɗanai,
Rena mutane ka sa mutum a ƙi ƙaunatai,
Cin fuska ke mayar da ƙarshe mummuna.

67.     Mun dai san yau da gobe ba ta barin komi,
Shi ne hujjan hura da ta kwan ta yi tsami,
Komi ƙarshe garai ka saurari batuna.

68.     Ba mamaki miloniya ya zama gyartai,
Mai mulkin duniya ya ƙare ɗan kwantai,
          Malam ya yi sanƙira wurin taron suna.

69.     Kowa Allah Yana biya tai da halinai,
 Bayinai kowanensu Ya san matsayinai,
Can ga hukunta su tabbata bai yin sauna.

70.     Komi muka yi mu san ana nanata shi,
Can ga hisabinmu Rabbu za Ya hukunta shi,
          Ga zantukkanmu ga sikeli, kaicona!

71.     Ban dai taɓa arashi ba ban san zambo ba,
Ba zan yi ƙire ba lura ba waƙa ce ba,
Tarihi ne nake zubawa a fagena.

72.                        Komi nisan dare ana dakon rana,
Wane mutuwa ta ɗauki mai sauran kwana,
Na shedi hakan ga tun ga Salihu kakana.

73.                         Matarsa Gadaje san da taj ji kalamaina,
Tac ce: "Tafi sa ido ka kwanta ka yi kwana,
Sai ka ji karakkiyar damuttsansu da rana."

74.                         Na yarda Waliyiya Waliyi taka aure
Ba su tunani a iske ya zamto gajere,
Ba su barin zuriya a ce ba ta da rana.

75.                         Tammat na kammale muradin ƙudurina,
Waƙar da na hangi masu son su ga laifina,
Don ɗai hasada da kushe dukkan lamarina.

76.                         Na roƙi rabo ga Rabbana mahaliccina,
Ranar da Ka ƙaddaro da ƙarin kwanana,
In shiga ceton Nabiyu in tsallake ƙuna.

Aliyu Muhanunadu Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua, Katsina.
10/06/2013

Post a Comment

0 Comments