Fahimtar
irin farin jini da kwarjinin da ke ga ƙagaggun
labaran Hausa, musamman iri su Ruwan Bagaja da Ganɗoki da
Shaihu Umar da Jiki Magaya da makamantansu a idon malamai da ɗalibai, tun
a makarantun firamare da sakandare da na gaba da sakandare, har zuwa jami’o’in
Arewacin ƙasar nan, har ma da waɗanda suka yi
yaƙi
da jahilci, da kuma ganin irin yadda masana da manazarta fannonin al’ada da
adabi da harshen Hausa suka yi rubuce-rubuce da dama a kan abubuwa da dama a
fagen ilimi. Misali a dubi yadda manya-manyan Farfesoshi da Doktoci na jami’o’i
daban daban na ilimi kamar su hamsin da ɗaya (51) suka yi rubuce rubuce a kan
littafin Ruwan Bagaja mai suna...
-----------------------------------
DAGA
GARBA UMAR
GUSAU
--------------------------------------
TSAKURE
Fahimtar
irin farin jini da kwarjinin da ke ga ƙagaggun
labaran Hausa, musamman iri su Ruwan Bagaja da Ganɗoki da
Shaihu Umar da Jiki Magaya da makamantansu a idon malamai da ɗalibai, tun
a makarantun firamare da sakandare da na gaba da sakandare, har zuwa jami’o’in
Arewacin ƙasar nan, har ma da waɗanda suka yi
yaƙi
da jahilci, da kuma ganin irin yadda masana da manazarta fannonin al’ada da
adabi da harshen Hausa suka yi rubuce-rubuce da dama a kan abubuwa da dama a
fagen ilimi. Misali a dubi yadda manya-manyan Farfesoshi da Doktoci na jami’o’i
daban daban na ilimi kamar su hamsin da ɗaya (51) suka yi rubuce rubuce a kan
littafin Ruwan Bagaja mai suna: Ruwan
Bagaja In Perspectives: Eight Decades Of Hausa Masterpieces In Prose
(1933—2013). Wannan shi ya ba ni sha’awa da in yi wani nazari a kan littafi
Shaihu Umar. Don haka, wannan nazari zai yi bayani a kan abubuwan da suka shafi
taƙaitaccen
tarihin marubucin littafin. Sannan a dubi littafin cikinsa da wajensa, musamman
ta la’akari da al’adu da ɗabi’un
Hausawa da nazarin ya hango sun yi naso a cikin littafin. Haka kuma, nazarin
zai dubi jigon littafin a matsayin ƙashin bayan
rubuta littafin.
1:1 GABATARWA
Littafin
Shaihu Umar, wanda Abubakar Tafawa Ɓalewa ya
rubuta a shekara ta 1933 aka kuma wallafa shi a shekara ta 1934, shi ne littafi
na uku a jerin littattafan da hukumar buga littattafai da sayar wa ta Arewacin
Nijeriya da ke Zariya (NNPC) ta buga. Baya ga littafin Ruwan Bagaja na Abubakar Imam da littafin Ganɗoki na Bello
Kagara, idan aka yi la’akari da tsarin gasar da ta samar da littafan ƙagaggun
labarai ta shekarar 1933, a ƙarƙashin
jagorancin Dokta R.M.East. A cewar, Malunfashi, (2004:5).
“A cikin
shekarar 1933 ne hukumar Fassara da Talifi
Ta ga ba a sami littattafan
adabi da take buƙata ba.
Don haka, ta shirya gasar
farko da ta taimaka wajen
Samar da littattafan ƙagaggun
labaran Hausa na farko
Ta
fuskar zube.”
A nan ana
iya cewa, Hukumar Talifi ta samu littattafai da dama a matsayin karɓa kiran
wannan gasar. Da yawa daga cikin littattafan da aka rubuto wa Hukumar sun dace
da tsarin buƙatun gasar. Lokacin da Hukumar ta zo buga
littattafan waɗanda suka
lashe gasar, sai da ta tace su sosai, sannan ta fitar da sakamakon gasar kamar
haka:
1.
Ruwan
Bagaja na Abubaka Imam.
2.
Ganɗoki na Bello
Kagara
3.
Shaihu
Umar na Abubakar Bauci
4.
Idon
matanbayi na Muhammadu Gwarzo
5.
Jiki
magayi na R.M.East da Tafida.
Da ma wasu
waɗanda Hukumar
ba ta sami damar buga wa ba, saboda wasu dalilai kamar littafin Boka Bowaye na
Muhammadu Nagwamatse da littafin Yarima Abba na Muhammadu Jumare Zariya da dai
sauransu. Shi dai wannan littafi na
Shaihu Umar ya ƙumshi abubuwa na fagen ilimi waɗanda suka haɗa da al’adun
Bahaushe da ɗabi’o’insa
da harshensa.
1:2 TAƘAITACCEN
TARIN MARUBUCIN LITTAFIN SHAIHU UMAR
Sunan
marubucin littafin Shaihu Umar shi ne, Sir. Abubakar Tafawa. An haife shi a wata
unguwa da ake kira Ɓalewa da ke cikin garin Bauchi a yau, 23 ga
watan huɗu (Afirilu)
a shekara ta 1912. Sunan mahaifinsa Bageri (hakimin Lere). Sunan mahaifiyarsa
Amina. Ya fara karatunsa na allo a garin Bauchi. Ya fara karatunsa na zamani
(makarantar boko) a Elimantare a nan garin Bauchi daga nan ya wuce makarantar
Katsina kwaleji. Bayan ya kammala karatunsa a wannan makarantar, sai ya dawo
gida Bauchi ya kama aikin malanta a makarantar Midil Sukul ta Bauchi a shekarar
1944. Yana a cikin wannan aikin ne aka zabe shi tare da wasu malamai ‘yan Arewa
zuwa Jami’ar London, inda suka yi wani kwas na sanin makamar aikin malanta na
shekara ɗaya.
Dawowarsa ke
da wuya, sai aka naɗa shi mai
kula da malamai a makarantun Elimantare (wato Inspector). Daga nan ne ya shiga
siyasar NPC (Northern People Congress) ta su Sir. Amadu Bello (Sardaunan Sakkwato)
Firimiyyan jihar Arewa a shekarar 1946. Marigayi Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa,
Firayim Ministan Nijeriya na farko ya rasu a shekarar 1966, yana da shekara 53.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya maza shida da mata biyar da jikoki da matansa na aure 4.
Allah ya jiƙansa da rahamarSA. Allah ya gafar ta mana da mu
da uwayenmu da malamanmu da duk kan musulmai.
1.3 AL’ADUN HAUSAWA A CIKIN LITTAFIN SHAIHU
UMAR
Abin da ake
nufi da al’ada shi ne, hanyoyin gudanar da rayuwar ɗan Adam ta
yau da kullun. Al’ada abu ce, da ta shafi rayuwa tun ranar gini, tun ranar
zane. A cewar Bunza, M. A. (2006:7) ‘’Al’ada tana nufin duk kanin rayuwar ɗan’Adam ce
tun daga haifuwarsa har zuwa kabarinsa.” Shi kuwa Ɗangambo, A.
(1987:5) cewa ya yi, “ Al’ada ita ce, sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa,
wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.” A taƙaice, al’ada
wata abu ce wadda ta shafi abin da rai ya riga ya saba da aiwatar da shi har ya
zamar masa jiki.
Littafin
Shaihu Umar, littafi ne da ya ƙumshi al’adu da ɗabi’un
Hausawa tsintsarsu. Kama da zaman iyali na namiji ya auri macce fiye da ɗaya, da
zaman fada a masarauta, da sana’ar noma, da sana’ar farauta, da yin hijira, da
fita neman arziƙi, da almajiranci da tawakkali ga Allah, da
yarda da ƙaddara mai kyau ko mummuna da sauransu. A
falsafar dangantakar iyali tsakanin magidanci da iyalinsa, idan aka ce iyali, a
iya cewa kawai ma’ana iri biyu a nan. Ma’ana ta fako ita ce, wadda wasu suka ɗauka cewa,
iyali sun haɗa mutum da
matarsa ko matansa da ‘ya’yansa kurun. Ma’ana ta biyu kuwa, wasu sun ɗaukai cewa,
abin da ake cewa iyali shi ne, magidanci da matarsa ko matansa da ‘ya’yansa da
duk wanda yake ƙarƙashin
kulawar wannan mai gidan. Wannan yana iya haɗa mahaifiyarsa da mahaifinsa da ƙannansa da
barori, in dai shi ke kulawa da cin su da tufafinsu da wurin kwanciyarsu.
Ga al’ada a ƙasar Hausa,
tsarin zamantakewar iyali a gidan Bahaushe miji ko maigida shi ne shugaba a
gidansa. Matarsa ko matansa da ‘ya’yansa, har ma da yaran gida masu yi masu
hidima suna a ƙarƙashinsa a
matsayin mabiya. Mai gida ne zai ɗauki nauyin ciyar da mazauna a
gidan. Shi ne kuma zai yi wa kowa tufafiin saka wa, ya kuma ba su makwanci.
Haka kuma shi ne, wanda zai shirya masu irin ayyukan da kowane za yi, ya kuma
tabbatar da kowa ya yi aikin da aka ba shi. wannan shi ne,tsarin zama na
Bahaushe na asali, inda yake zaune a cikin babban gida tare da magidanta fiye
da goma kowane magidanci da nasa yanki a gidan, inda yake tare da nasa iyalin,
duk dai a ƙarƙashin
“Uban-gandu”.
Uban gandu shi ne, dattijon gida da ya haifi
magidantan wannan gidan nasa da yake da shiya-shiya, inda kowane magidanci yake
da tashi shiyar, duk a ƙarƙashi
kulawarsa. Ga al’ada, kowane magidanci zai zo shiyar wannan mai gidan nasu
(Uban-gandu) da safe, don ya yi masa “ina kwana?” har matansu da jikokinsa,
suma zasu zo, domin yi masa ‘ina kwana?’tare da nasa iyalin. Haka irin wannan
tsari na iyali ya gada a wajen Bahaushe a ƙasar Hausa.
Abu na farko
da wannan nazari ya duba shi ne, tsarin iyali da zamantakewar Bahaushe a cikin
iyalinsa. A lokacin da Makau ya ji Sarki ya ce, na koreka daga wannan gari. ‘Ka
tafi can wani wuri da ba a hannu na ba.’ Sai Makau ya yi godiya ga Sarki ya
taso, ya zo gida, ya tara iyalinsa babba da yaro, maza da mata, ya ce da mu,
“To,
kun ga yadda Allah ya ƙaddara wannan al’amari
bisa
gare ni.---Duk iyali sai muka fashe da kuka gaba
ɗaya, muna cewa, wallahi tallahi ba
wata ƙasa da zaka
tafi ko da lahira ce, in ana
rakiya, lalle ba shakka, ma raka ka.”[1]
Wannan
bayani ya nuna yadda Bahaushe yake zaune da iyalinsa, da kuma yadda al’amurra
suke gudana na shawara tsakaninsa da iyalinsa.
Abu na biyu
da wannan nazari zai yi tsokaci a kansa shi ne, al’adar zaman fada ga fadawan
sarki a nan ƙasar Hausa. Alal-misali a cikin littafin an nuna
cewa:
“mahaifiyar
Umar ta so ta yi aure, domin masoya
da
yawa sun fito nemanta aure, a cikinsu har da
wani Bafade na kusa da Sarki ainun
wai shi Makau.”[2]
Shi aure
wajibi ne ga ɗiya macce,
muddin dai ta kai minzalin shekarun aure, ta kuma samu masoyi mai nufin ya aure
ta. Don haka, shawarar da uwar Umar ta yanke na ta yi aure ya yi. Duk da cewa,
ita Bajawura ce, tana da wata dama irin wadda Budurwa ba ta da ita, ta yin
gaban kanta ga sha’anin aurenta, saboda haka ne ta nemi shawarar kakarta bisa
al’adar Hausawa.
Abu na uku
shi ne, al’adar yaye, wadda ake yi wa yaro ko yarinya, idan kowanensu ya kai
shekara ɗaya da wata
bakwai bayan haifuwa a al’adance. Al’adar yaye yaro ko yarinya a ƙasar Hausa
ita ce, uwaye ba su kan yaye yaransu da kansu ba, musamman ‘ya’yansu na farin.
Sai dai su miƙa su ga danginsu na wajen uwa ko uba, can nesa
da su. Abin da ake nufi da yaye shi ne, cire yaro ko yarinya daga ba su nonon
uwa. Amam kuma ga al’ada ba laifi ba ne a bar yaro ko yarinya su wuce shekara ɗaya da wata
bakwai, idan uwaye sun lura da wata matsala da zata iya faruwa ga yaronsu ko ɗiyarsu.
matsala kamar ta rashin girma ko ƙiba ko
rashin miƙewa tsaye da wuri. Misali a cikin littafin an
nuna cewa:
‘’Da
aka yaye Umar, sai aka bar shi a wajen kakarsa”[3]
Wannan
bayani kuwa haka abin yake dangane da al’adun Hausawa wajen yaye. Wato, kakanni
suna da hannu a wajen hora da tarbiyya yaran da suka raina
Abu na huɗu shi ne,
al’adar munafunci da aka san wasu fadawan fada da yi wa juna, domin neman shiga
ga Sarki. Ga abin da fadawa suka cewa Sarki game da Makau:
‘’Bari
dai mu feɗe maka biri
har wutsiya. A garin nan ba
ka
taɓa samun
wanda yake cin amanarka kamarsa ba
(wato,
Makau ke nan). Ai Makau ne yake fallasa ka
a wajen talakkawanka da
kake ganin suna girman kan nan yanzu.”[4]
Kamar dai
yadda labarin ya nuna Makau, wanda yake da fada a wajen Sarki ya haɗu da makirci
da ƙiyayya
daga fadawa ‘yan’uwansa, har suka ɓata shi ga sarki. Wannan makirci ya
zama sanadiyar korarsa daga garin baki ɗaya. Wannan shi ne tarihi, wanda ya
nuna mana halayyar fada da kuma fadawa ta fuskar Sarauta a da, da kuma yanzu.
Nason wata
al’ada ta biyar ta Bahaushe da zamu iya gani a cikin littafin Shaihu Umar ita
ce, ta ɗaura laya ko
karhu ko guru ko daga, don kariyar kai da kaya (dukiya) daga harin ‘yan fashi (ɓaraayi).
Dubi dai yadda ya zo a cikin littafin;
“Sai
Maharbin ya kawo wata ‘yar laya
mai sasari
ya ba shi, y ace masa, wannan
ita ce abar
da na taimake ka da ita.
A ƙarƙashin wannan
labara akwai al’adun Hausawa masu yawa, kyawawa abin koyi ga matasan yanzu. Waɗannan al’adu
kowa sune, an taimako da aka san Hausawa da su ta hanyar aikin gayya. Ba
shakka, taimaka wa juna da shawara, wannan aikin Hausawa ne ba tun yau ba.
Domin Musulunci ma ya ƙarfafa aikata haka. Wato, a taimaka wa mutum baƙo da masauki
(gida ko ɗaki) har ma
da gona ko mata ya aura duk yana da ga cikin aikin Bahaushe a wancan zamani. A
dalilin haka, ga al’adarsa ya samar da gidan baƙi, yanzu
kuwa sai jefi-jefi.
Nason wata
al’adar ta Hausawa ta shida a cikin littafin Shaihu Umar ita ce, ta sana’ar
noma. Ga abin da marubucin littafin yake cewa:
‘’Domin
buƙatata
yayin da na sami matsugunni sosai,
sana’ar da zan yi ita ce, noma.’’
Sana’ar noma ga Bahaushe, al’adarsa
ce, gadaddiya tun kakanni da uwaye. A cikin wannan shafi na 12 mai kan labarin
‘Ka Zauna A Maƙarfi’’. Maharbin da suka gamu da Makau a cikin
daji yana ba shi shawara cewa, ‘ya tafi Maƙarfi domin
mutane garin sanannu ne wajen aikin gonaki, noma a can yana da riba, amfaninsu
kuwa kullun mai albarka ne.’’[6]
Ga hoton
wata al’adar ta Hausawa ta bakwai, duk a cikin wannan littafi na Shaihu Umar.
Wannan al’ada kuwa ita ce, ta neman ilimin addininsa na Musulunci musamman
karatun allo. Al’adar Bahaushe ce a nan dai ƙasar Hausa,
idan yaro zai fara karatun Allah, to a makarantar allo za a kai shi, kuma da
allo zai fara da zarar ya isa ya riƙe allon. Zai
kuma fara da ƙidan baƙi ne. Dubi
abin da marubucin littafin ya ce:
‘’Na
yi ta karatu, har wajen shekara biyu na sauke.
Na
sauke Alƙur’ani ranar laraba sha tara ga wata
Muharran’’[7]
Baya ga
wannan al’adar ta yin karatu da allo a makarantar allo, akwai al’adar bara,
wadda Bahaushe ya tsinta daga baya, kuma ta zama jiki ga wasu daga cikin
Hausawa, musamman a nan Arewacin Nijeriya. A inda Bahaushe yake ƙetarewa har ƙasashen waje
domin ya yi bara. Kuma wannan ƙirƙirar al’ada
tana janyo wa Hausawa faɗuwar daraja
ga masu kishin Hausa da Hausawa.
Al’adar
bara, ɗabi’a ce
wadda ba ga Bahaushe kai ta tsaya ba, har Larabawa da sauran ƙabilu ma
wasu daga cikin su suna aiwatar da ita. Amma kowa ya san cewa, bara da mola
suna zubar da mutuncin mai yinsu. Addinin Musulunci bai yarda da yin bara ba,
in ba ya zama dole ba. In kuma irin wannan lalora ta sami mutum to, sai ya nemi
taimakon jama’a dai-dai buƙatarsa ta hanyar yin baran.
Haka kuma shari’ar Musulunci ta yi hani da mai bara ya mayar da ita
sana’a. Ga dukkan tsammani na ire-iren
waɗannan
lalorori suka shigo da wasu gwamnonin wasu jihohi su hana gudanar da bara a
nasu jihohin. Al-misali jihohin Kano da Jigawa da Abuja da Legas. Sun yi haka
ne kuwa, don kare mutunci addinin Musulunci da Musulmai Hausawa da ma Arewa
baki ɗaya.
Illolin yin
bara suna da yawa, amma wasu daga cikin su sun haɗa da:
1.
Faɗuwar
mutunci, musamman ga masu yin mola.
2.
‘Yan
ɗauke-ɗauke na
kayan mutane, musamman a cikin gidajen mutane, wanda ake zargin almajirai da
aikatawa.
3.
Yawon
talla da yawon banza a gidajen karuwai da wanke-wanke a gidajen abinci da tasha
mota.
4.
Da
fama da raga (tsumma a jiki), da dauɗa. Ga kirci da ƙaswa da ƙeya.
5.
Ga
fama da yunwa, saboda ƙarancin abinci, da sauransu.
Ire-iren
waɗannan
matsaloli suna da wuyar magancewa ko ga gwamnoni jihohin da suka nemi hana
bara. Saboda manyan almajiran ba su son su bari, haka ma malaman nasu.
Gwamnonin ma ba da gaske suke yi ba.
1.4 AL’ADAR HAUSAWA TA YAKE-YAKE DA KAI WA JUNA
HARI
Al’adar Hausawa ta kai wa juna yaƙi da kai
hari a ƙauyukka da garurwa, har ma da birane a duk
lokacin da aka tsara al’ada ce, domin a faɗaɗa ƙasar mulki
da mallakar bayi, domin a sayar a sayi makamai. Don haka, akwai irin wannan
al’adar da yi tasiri a cikin zuciyar marubucin littafin Shaihu Umar, waɗanda zamu ga
hotonsu a cikin littafinsa. Alal-misali a cikin littafin an nuna cewa, Sarki ya
sa an tara masa fadawansa a nan fada yana gaya masu cewa:
‘’Ba
wani abu ne ya sa na kira ku ba, abin da nake so
Game da ku shi ne, ku yi shiri, ku tafi,
ku yi hari a can
Wannan
al’ada ce ta galibin manyan sarakunan ƙasar Hausa,
wadda ko a wancan zamani ba kowa ke yin wannan ba, sai da wani babban dalili.
Wannan ya nuna yadda Sarakunan ƙasar Hausa ke dogaro a kan
bayi wajen biya masu wasu buƙatu na yau da kullun.
Wata al’adar
ta Hausawa ta nuni ga daidaituwar tasirin Musulunci a cikin su ita ce, ta yin
tawakkali ga Allah a kan duk wani abu mai kyau ko marassa kyau ne ya faro a
kansu. Kasancewa galibi Hausawa Musulmai ne, sukan yi tawakkali su bar duk wani
abu da ya faro a garesu mai sosa rai ga Allah mahalaccen kowa. To, irin haka ne
ya faro ga mahaifiyar Umar da Makau da ma wasu masoya Makau da suka ji labarin
cewa, Sarki ya sa a fidda makau daga garinsa. Sai suka yi baƙin ciki,
wasu suna kuka saboda baƙin ciki, waɗansu ma suna ba shi ‘yan kuɗi waɗanda zai riƙe a hannu ko
ruwa ya sha a hanya. Wannan al’amari ya kai gaya, domin ya tarar da mahaifiyar
Umar tana kuka, sai ya ce:
‘’Wannan abu ba na kuka ba ne, ya wuce kuka.
Ko
ba haka ba, tun da yake musulma ce ke, ya kama ta
Ki
tuna cewa, dukan abubuwa daga Ubangiji (Allah)
Suke
samun mutum. Saboda haka, abin da ya fi kyau
A
gare mu duka, sai mu yi tawakkali ga Allah, wanda
Ke aikata komai yadda ya so.’’[9]
Baya ga
wannan al’ada ta yin tawakkali ga Allah da aka san Bahaushe da ita, duk da
cewa, ba kowane musulmi Bahaushe ke da tawakkali ba da yin amanna da ƙaddara mai
kyau ko mummuna ba, amma ba a rasa na Allah ko yaushe. Dangane da wannan labari
akwai nuni a kan haka a shafi na 9 a cikin wannan littafin kamar haka:
‘’
To, kun ga yadda Allah ya ƙaddara, wannan al’amari
Bisa
gare ni. Sarki ya ce, sai in bar masa ƙasarsa”
Jaddada
wannan bayani ya fito fili a lokacin da Makau ya haɗu da
Maharbi. Makau ya yi masa bayanin halin da yake ciki. Sai Maharbin ya ce, ‘Haƙiƙa, yadda
Allah ya ƙaddaro abu haka yake faruwa.” Mai gaskiya
har abada bai taɓa taɓewa.
1.5 TASIRIN RAYUWAR HAUSAWA A CIKIN LITTAFIN SHAIHU
UMAR
Tasirin rayuwar Hausawa game da imani a kan ƙaddara mai
kyau ne ko akasin haka, Hausawa musumai sun yarda abu ne daga Allah yake. Kuma
Allah ne ke da cikakken ikon ƙaddara komai a kan ɗanAdam.
Wannan tasirin rayuwar Hausawa na yarda da ƙaddara shi
ne ya gina wannan littafi na Shaihu Umar. Wannan shi ne jigon littafin Shaihu
Umar. Don mu tabbatar da abin da muka faɗa, muna iya kawo misalai biyu ko uku
a cikin littafi:
Da farko dai
an haifi Umar bayan rasuwar mahaifinsa, wanda hakan ya mayar da shi maraya. A
mafiyawan lokuta, idan yaro maraye ne ba kasafai yakan ji daɗin rayuwarsa
ba. To, amma a wannan halin kamar yadda Allah ya ƙaddara. Sai
ita mahaifiyar Umar ta auri Makau (wani babban bawan Sarki). Wani mutunen kirki
da sanin ya kamata, wanda ya nuna wa Umar (agolansa) so da ƙauna ta
kowane hali. Babu shakka, Makau ya nuna hali na gari, kamar dai yadda Hauswa
suka aminta suka yarda mutunen kirki ya kasance kuma ya yi.
Abu na biyu
shi ne, irin baƙin ciki da iyalin Makau suka samu kansu a ciki a
wani ɗan ƙanƘanen lokaci
aka raba mai gidansu (Makau) da muƙaminsa da
gidansa da garin baki ɗaya. A nan
mun ga abin da Allah ya ƙaddara a kan Makau. Kamar dai yadda shi ma ya
ce, a lokacin da ya isko matarsa tana kuka dangane da abin da ya sami mai
gidanta kamar haka:
‘’Tunda
yake ke musulma ce, ya kamata ki nuna
cewa, dai dukkan abubuwa daga Ubangiji suke
samun mutum. Haka Allah
yake aikata komai yadda ya so’’[10]
Ƙarin bayani
a kan irin wannan ɗabi’a ta yarda
da ƙaddara
muna iya ganin ta a cikin wannan littafin kamar haka;’ a lokacin da Makau ya
sauka a Maƙarfi, ya zauna, sai Allah ya yi masa baiwar
samun arziki, har ya aika wa Sarkin Kagara da Sarkin Zagi da Shantali wasu
kyaututtuka. Wannan ma wani abu ne da Allah ya ƙaddara.
Bayan waɗannan
misalai ana iya samun wasu misalan da dama. Ga misali, dubi dai ƙaddarar sace
Umar bayan da mahaifiyarsa ta tafi Fatika, da kuma kuɓutar da yi
lokacin da kura ta cinye wanda ya sace shi.
1.6 NAƊEWA
Dangane da darussan koyo a cikin
wannan littafi, akwai halaye da al’adu masu kyau da kowane Musulmi ya kamata ya
koya, ya kuma aiwatar. Na farko dai riƙo da haƙuri. Haƙuri yana kai
mutum ga nasara. Domin mun ga yadda Shehu Umar ya yi haƙuri da
wahalhalu da ya sha tun haifuwarsa har zuwa ƙas ashen
Larabawa, a inda ya yi karatu mai zurfi na muhammadiyya. Sakamako ya zama wani
babban malami, masani a fannunin ilimi a idon jama’a. Don haka, wannan ya nuna
mana cewa, kafin mutum ya ci nasara, har jama’a su san shi dole sai ya sha
wahala matuƙa. Saboda haka, tare da wahala, akwai nasara.
Kuma idan dai har muna son mu cimma burinmu na duniya da na lahira, dole ne mu
yi aiki tuƙuru. Haƙiɗa idan muka
yi haka zamau samu duk irin nasarar da muke su.
Abu na biyu shi ne, kyautatawa. Idan
mutum ya yi maka sharri, to kai kyautata masa. Kamar yadda tarihi ya nuna mana ɗabi’un
manzonmu Annabi Muhammadu (SAW). Idan an zalunce shi, yakan mayar da alheri,
muddun ba haƙin Allah aka taɓa ba. A cikin wannan littafi
na Shaihu Umar, mun ga yadda aka zalunci Makau. Shi kuma ya mayar da alheri.
Wani abin lura shi ne taimako. Taimako
wajibi ne ga wanda ya cancanta a yi masa. Mun ga yadda Maharbi ya taimaki Makau
da irin gudummuwa da Makau ya samu a wajen iyalinsa da abokanan zama, waɗanda suka riƙa ba shi
kyautar kuɗi da ban-
hanƙuri
a lokacin da Sarki ya kore shi garinsa.
Da ƙarshe, ya
kamata mu lura da abubuwan assha da yin tir da suka faro a wancan zamani. Waɗanda
marubucin wannan littafi ya zo da su a cikin littafinsa. Waɗanda suka
jawo tashin hankali, kamar bauta da kuma cinikin bayi. Waɗannan
abubuwa sun jawo halakar ɗuruwan
mutane a banza, ba gaira-ba-dalili.
MANAZARTA
[1]
Don }arin bayani
duba shafi na 9 na littafin.1
[2]
A duba shafi na 3 na wannan littafin.
[3]
A duba shafi na 2 a cikin littafin.
[4]
Don }arin bayani
duba shafi na 5 na wannan littafi.
[5]
Don }arin bayani
duba shafi na 12 na shi wannan littafin.
[6]
Duba shafi na 12 na wannan littafin Shaihu Umar.
[7]
A nan ma kana iya duba shafi na 37 domin }arin
bayani.
[8]
A duba shafi na 8 don }arin
bayani.
[9]
Don }arin bayani
duba shafi na 9 da na 11 da na 25.
[10]
Sake duba shafi na 9 na wannan littafin don }arin
bayani.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.