Bahaushe yana da hanyoyin
da yake bayyana sha'awarsa ko damuwarsa ga duk wani abu da ya shafe shi. Saboda
haka, kiɗa da waƙa na daga cikin hanyoyin
da Hauwasa ke amfani da su domin bayyana ra'ayinsu ko sha'awarsu ko kuma
damuwarsu. Rubutattun waƙoƙi, waƙoƙi ne da aka tsara su a
rubuce, aka kuma aiwatar da su a rubuce,ta hanyar rerawa cikin daɗaɗɗan sauti. Wannan bincike
,ya ginu a kan adabin Hausa, musamman rubutacciyar waƙa. Binciken ya karkata
akala ne wajen zaƙulo
waƙoƙi masu salon hira na
Kabiru Yahya Classic...
__________________________
NA
ABUBAKAR MACCIƊO
______________________
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan kundin digirin nawa
ga mahaifiya ta Hajiya Hauwa’u da mahaifi na Alhaji Macciɗo
da kuma dukkan iyalan gidanmu ga baki ɗaya.
Sannan da dukkan waɗanda suka tallafa min a
lokacin da nike wannan karatu, tun daga farkonsa har zuwa wannan mataki. Ina
rokon Allah ya tallafi rayuwarsu kamar yadda suka tallafamin, ya kuma sa
albarka a cikin rayuwarsu duniya da lahira.
GODIYA
Tsarki ya tabbata ga
Allah, tare da godiya a gare shi, dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin
talikkai wanda ya halicce mu, ba don komai ba, sai don mu bauta mishi. Ya
Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi salati
ga Ibrahim da alayen Ibrahimu, lallai kai abin godewa ne, mai girma. Ya Allah!
Ka yi albarka ga Muhammadu, da Alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga
Ibrahimu, da alayen Ibrahimu lallai, kai abin godewa ne, Mai girma.
Bayan
godiya ga Allah, wanda ya ba ni ikon kammala wannan bincike nawa. Ina matukar
godiya ta musamman maras adadi ga malami na, Mal. Dano Balarabe Bunza wanda ya
sadaukar da lokacinsa a kai na, tare da haƙuri
da ya yi da ni domin ganin wannan aiki ya kammala. Haƙiƙa
Mal. Dano Balarabe Bunza ya taimakamin matuƙa
da kayayyakin aiki da nuni da kuma shawarwari, wanda hakan ne ya sa wannan
bincike ya kammala cikin nasara. Domin haka ban da abin d azan iya saka mashi
da shi, sai addu’a. Da wannan nike roƙon
Allah ya sa albarka a cikin rayuwarsa da
zuri’arsa baki ɗaya.
Ina godiya ta musamman ga Mal. Naziru Ibrahim Abbas da ya taimaka min da
shawarwari a wajen gudanar da wannan aiki da dukkan malamai na Sashen Nazarin
Harsunan Nijeria, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato, bisa irin yadda suka jajirce, wajen ƙoƙarin koyar da ni da sukai tun daga
shekarar karatu na ta farko har zuwa ƙarshe.
Ina godiya ga iyaye na
Alhaji Macciɗo da Hajiya Hauwa’u, waɗanda
suka tarbiyantar da ni, kuma suka ɗora
ni a kan hanya madaidaiciya, musamman ta neman ilmin addini da na zamani
(boko). Ina rokon Allah ya tsare su da talauci da kuma azabar ƙabari, sannan ya kyautata rayuwarsu
duniya da lahira, ya sa Aljanna fiddausi ce makomarsu, Amin.
Haka
kuma ina miƙa godiya ta ga
‘yan’uwa da abokan arziki maza da mata waɗanda
suka taimaka min da ƙarfinsu
da dukiyarsu da kuma addu’o’i domin ganin wannan karatu nawa ya kammala.
Haƙiƙa
ba zan manta da abokai na ba waɗanda suka taimakamin
sosai a lokacin da na gudanar da wannan karatu na wato, Nafi’u Abubakar Binji
da Salim Muhammad Sani da Ahmad Abdullahi da Aminu Sanusi Sani da Ibrahim A
Ibrahim da Gaddafi Labaran da Nasiru Abdullahi da sauran abokai na ga baki ɗaya.
Ina roƙon Allah ya saka musu da alhairi.
Ba
zan manta da abokan karatu na ba wato, Mubarak Murtala da Zubairu Lawal Ibrahim
da Husaini Abubakar da Bello Aleru da Imrana Sulaiman da Lukman Abubakar da
Murtala Guiwa da sauran abokan karatu na, su ma ina godiya a gare su da, irin
taimakon da suka ba ni don ganin wannan bincike ya kammala.
Daga ƙarshe
ina miƙa godiya ta musamman ga dukkan dangi
na, da kuma duk wanda ya taimakamin wajen karatu na, da kuma wajen gudanar da
wannan bincike nawa. Allah ya sakawa kowa da mafificin alkhairi, Amin.
BABI NA ƊAYA: SHIMFIƊA
1.0
GABATARWA
Bahaushe yana da hanyoyin
da yake bayyana sha'awarsa ko damuwarsa ga duk wani abu da ya shafe shi. Saboda
haka, kiɗa da waƙa na daga cikin hanyoyin
da Hauwasa ke amfani da su domin bayyana ra'ayinsu ko sha'awarsu ko kuma
damuwarsu. Rubutattun waƙoƙi, waƙoƙi ne da aka tsara su a
rubuce, aka kuma aiwatar da su a rubuce,ta hanyar rerawa cikin daɗaɗɗan sauti. Wannan bincike
,ya ginu a kan adabin Hausa, musamman rubutacciyar waƙa. Binciken ya karkata
akala ne wajen zaƙulo
waƙoƙi masu salon hira na
Kabiru Yahya Classic.
Wannan babin namu zai ƙunshi
abubuwa kamar haka: Gabatarwa, Manufar bincike, Muhimmancin bincike, Bitar
ayyukan da suka gabata, Hujjar ci gaba da bincike, Farfajiyar bincike, Hanyoyin
gudanar da bincike, Dalilan bincike da kuma Kammalawa.
1.1
Manufar Bincike
Manufar wannan bincike
ita ce samar da kundi wanda zai fito da salon hira a cikin waƙoƙin Kabiru Yahya Clasicc
domin zai taimaka ga masu nazari su sami wani abu da zai taimaka musu,su
fahimci salon hira da ke cikin waƙoƙinsa.
1.2 Muhimmancin Bincike
Salon hira abu ne mai muhimmanci a cikin waƙoƙin Kabiru Yahya Classic,
musamman da yake mawaƙin
siyasa ne. Saboda haka, binciken ya dangana ne a kan salon hira a waƙoƙin Kabiru Yahya Classic.
Idan wannan bincike ya kammala zai taimaka ga wasu manazarta da ke da
sha'awa ga irin wannan bincike su sami makamar gina nasu.
1.3 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata
A
nan an duba ayyukan da suka gabata ne waɗanda suka haɗa da littafai da kuma kundaye.
Abdullahi
(1993) Sun yi bayani a kan ma'anar waƙa da nauo'in waƙoƙin
baka da tarihin mawaƙin
da jigo da salon waƙar
da kayan ƙidansa.
Wannan aiki yana da alaƙa
da nawa sai dai akwai bambance-bambance. Zan amfana da wannan aikin ƙwarai da gaske.
Aliyu
da wasu (1995) aiki ne mai taken "Kwazo Bagage da waƙoƙinsa" marubucin ya
yi bayani a kan tarihin mawaƙin
da kayan kiɗansa
da jigogin waƙarsa,
kamar zambo da yabo da habaici da zuga,sai kuma salailan waƙar. Wannan aiki yana da
alaƙa da nawa haka yana da bambanci da
nawa. Haƙiƙa zan amfana da wannan
aikin.
Ɗanƙal G.L (2000) "Gero
Zartu da waƙoƙinsa" marubucin ya yi bayani ne a kan tarihin mawaƙin da kayan kiɗansa da ma'anar waƙa da asalin waƙa da jigogin waƙoƙinsa kamar yabo, zuga da
habaici da zambo. Amman bai yi bayanin
muhimman salailan mawaƙin
ba. Wannan aiki yana da alaƙa
da nawa sai dai akwai bambance-bambance da nawa aikin. Zan amfana da wannan
aikin.
Akwai
kuma littafin "Salo Asirin Waƙa (2001)" wanda Abdullahi Bayaro Yahya ya rubuta.
Wannan littafin an shirya shi cikin manyan babuka uku waɗanda suka haɗa da ma'anar salo da
ire-irensa da muhimman abubuwa da suka shafi tubalan salo a waƙa. Sai kuma fito da wasu
hanyoyi da suke tabbatar da muhimmancin salo a waƙa. Har wa yau marubucin ya yi tsokaci a kan wasu
salailai da yadda suke ƙulluwa
a waƙoƙin Hausa.
Kasancewar
wannan aiki babban fanni na waƙa
zai taimaka ainun wajen gudanar da wannan aikin da yake wannan littafi ya yi
bayani a kan salailai da yawa.
Abubakar
(2004) "Muhammadu Ango Rabo Yabo da Waƙoƙinsa".
Aikinsa ya ƙunshi
tarihin mawaƙin
da kayan kiɗansa
da yawace-yawacensa da dangantakarsa da sauran mawaƙa da turakun da ma'anar
turke da salo da ma'anarsa. Wannan aikin na da alaƙa da nawa aiki haka kuma akwai
bambanci a tsakaninsu. Zan amfana da wannan aikin matuƙa.
Takware(2005)
ya gudanar da aikin bincike mai taken "Nazarin Waƙoƙin Abdullahi Fircin
Koko". A cikin aikin bincikensa na neman kundin digirinsa na farko da ya
yi a Sashen Harshen Nijeriya da ke Jami'ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato, a inda ya yi bayanin zubi da tsari
da jigogin waƙar
da salailai da ke cikin waƙoƙin Abdullahi Fircin
Koko.Idan aka lura wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin bincike, duk da yana magana a kan
"Rayuwa da Waƙoƙin Abdullahi Fircin
Koko”. Amma nawa aikin binciken yana
magana ne a kan " Nazarin Salon Hira a cikin waƙoƙin Kabiru Classic".
Wannan aikin na da alaƙa da nawa kuma akwai
bambance-bambance da nawa aiki.
Bafarawa(2006)
ya gabatar da aikin bincike a kan "Nazarin Rayuwa da Waƙoƙin Dr. Waziri
Junaidu". A cikin aikinsa na neman kundin digiri na farko a Jami'ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato. Wannan
aikin yana magana ne a kan "Nazarin Rayuwa da waƙoƙin Dr. Waziri
Junaidu". Amma nawa aikin binciken yana magana ne a kan "Nazarin
Salon Hira A Cikin Waƙoƙin Kabiru Classic".
Akwai alaƙa da kuma bambanci
a tsakanin wannan aiki da nawa.
Bunza(2009)
“Narambaɗa”, dangantakar wannan
littafin da bincike na ita ce ya yi bayanin waɗansu salailai masu muhimmanci a nazarin waƙa,kamar yadda za a yi
la'akari wajen bambanta habaici da zambo.
Mustapha Umar (2009) ya rubuta wata maƙala a kan ‘Waƙoƙin
Muhammadu Gambo Fagada’ da ya gabatar a
taron ƙara wa juna ilmi na Sashen koyar da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato. Wannan maƙalar
ta ƙunshi ma’anar kalmomi da Bayanau da
Amsa-kama. Wato ta ƙunshi
kalmomi ne masu Amsa-kama a cikin wasu waƙoƙin Gambo Fagada. Wannan maƙala za ta taimaka min matuƙa a wajen gudanar da nawa aiki.
Shehu M. (2009) ya rubuta
wata maƙala da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato. Mai suna ‘Gambo
mawaƙin Maza ne ba mai cin gashin kansa
ba’. Wannan maƙalar ta ƙunshi mawaƙan maza ,dangantakar waƙoƙin
maza da waƙoƙin Gambo da kuma Jigon ta’addanci.
Wannan maƙala za ta taimaka
min matuƙa a wajen gudanar da nawa aiki.
Shafa'atu
I.B (2010) mai taken "Nazarin Rayuwa da waƙoƙin
Isya Mafara". Wannan aikin yana da dangantaka da nawa saboda an kawo taƙaitaccen tarihin mawaƙin. Haka an kawo ma'anar
salo da ire-irensa. Zan amfana da wannan aikin matuƙa.
Shehu
(2010) ya gudanar da aikin bincike mai taken "Waƙoƙin Abdu Kurna" a
inda ya yi ƙoƙarin bayyana zubi da
tsari da kuma fito da salailan da ke
cikin waƙoƙin na Abdu Kurna. Wannan
aikin zai taimaka min a wajen gudanar da nawa aikin. Saboda dama a aiki na zan
yi nazarin salon hira ne a waƙoƙin Kabiru Classic.
Sai
Bunza (2011) da ya rubuta wata maƙala
a kan ‘Sakkwato ce tushen ‘Hausa’ in ji Narambaɗa‘.
Wannan maƙalar ta ƙunshi taƙaitaccen tarihin Narambaɗa
da farfajiyar ƙasar Hausa da Ɗaurayar zantukan Narambaɗa
da kuma wasu waƙoƙin Narambaɗa
da aka yi nazari a kansu. Wannan maƙala
za ta taimaka min matuƙa
a wajen gudanar da aiki na.
Umar.M
(2011) mai taken "Rayuwa da Waƙoƙin
Ɗanbaba Birnin Tudu"
a wannan aikin an kawo taƙaitaccen
tarihin mawaƙin
haka kuma an kawo ire-iren salo,don haka akwai dangantaka a tsakanin aiki na da
wannan aiki.
Yahya
H (2012) mai taken "Nazarin waƙar Ta'aziyyar Malam Jafar Mahmud Adam". A cikin
aikinsa na neman kundin digiri na farko a Jami'ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato,a inda
ya kawo taƙaitaccen
tarihin marubucin waƙar
Aliyu Muhammad Bunza. Haka kuma an yi nazarin zubi da tsari na waƙar da kuma ma'anar salo
da ire-irensa. Wannan aiki yana da dangantaka da nawa aiki. Zan amfana da
wannan aiki matuƙa.
1.4 Hujjar Ci Gaba Da Bincike
Duk da bitar wasu daga
cikin ayyukan da suka gabata tare da yin tsokaci a kansu, amma har yanzu ba a
ga wani aiki da ya leƙo
gurbin da ake ƙoƙarin lalubowa ba, saboda
haka ganin irin muhimmancin Salon hira a cikin waƙoƙin
Kabiru Classic, aka ga ya dace a fitar da wannan hikima a fili domin amfanin
masu nazari
1.5 Farfajiyar Bincike
Wannan aiki ya keɓanta
ne a kan Nazarin salon hira a waƙoƙin
Kabiru Yahya Classic saboda haka ba za a wuce amfani da waƙoƙinsa ba.
Wannan bincike ya rabu ne a ƙarƙashin
inuwar rubutaccen adabin Hausa da ya shafi rubutacciyar waƙa.
1.6
Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Domin gudanar da wannan bincike an bi hanyoyi
da dama domin cimma abin da ake buƙata dangane da wannan bincike da aka yi.
Da
farko na sadu da shi kansa Kabiru Yahya Classic domin samun taƙaitaccen tarihinsa.
Hanya
ta biyu ita ce an nemi kayan aikin kamar littafai a cikin ɗakunan karatu da kundaye
da maƙalu domin karantawa tare da zaƙulo wasu muhimman
abubuwan da ke taimakawa a wannan fagen nazari.
Hanya
ta uku ita ce sauraren waƙoƙin Kabiru Yahya Classic
domin a fito da wannan salo a fili gwargwado.
1.7 Dalilan Bincike
Babu shakka wannan aiki kamar sauran ayyukan
bincike ne, dukkan wanda ya karanta zai ƙaru da wasu abubuwa masu amfani. Haka kuma domin cike
giɓin da ake da shi a wannan
fanni na salon hira a waƙoƙin Kabiru Yahya Classic.
Sannan kuma yana iya zama wani abin amfani, musamman ga manazarta masu sha'awar
adabin Hausa, tare da taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa adabin da kuma ƙara wa mutane fahimta.
Haka
kuma masu iya magana na cewa ' banza ba ta kai zomo kasuwa ' don haka, duk abin
da za a yi yana da wata manufa ta musamman, don haka wannan bincike na ɗauke da fasali biyu. Na
farko cike giɓi
domin samun takardar kammala karatun digiri na farko a Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya (Hausa Studies). Na biyu kuma domin ɗaliban da ke tafe su samu ƙarin haske kan nazarin waƙa da ya shafi salon hira
da abin karantawa ko nazari ga masu neman ilmi.
1.8
Kammalawa
Sanin kowa ne cewa, gabatar da kundin bincike ga kowane ɗalibi wajibi ne.
Kasancewar waƙa
wata muhimmiyar aba ce a al'adun Hausawa, haka ya sanya aka samu masana da kuma
ɗalibai suka duƙufa kanta domin gano
sirrin da ke ciki.
A cikin wannan babi an yi bayanin gabatarwa, kuma an kawo manufar
bincike. Haka kuma an kawo muhimmancin bincike tare da kawo bitar ayyukan da
suka gabata da kuma hujjar ci gaba da bincike da kawo farfajiyar bincike. Haka
an kawo hanyoyin da aka gudanar da bincike da dalilan da suka sa aka gudanar da
binciken.
BABI
NA BIYU
TAƘAITACCEN
TARIHIN KABIRU YAHAYA CLASSIC.
2.0 GABATARWA
Wannan babi na ɗauke
da taƙaitaccen
tarihin Alhaji Kabiru Yahaya Classic. Haka kuma yana ɗauke da lokacin da ya fara waƙa
da kuma ficensa. Sai kuma waƙoƙin da yake yi da kuma yanayin rera su.
2.1 HAIHUWARSA
An haifi Alhaji Kabiru Yahaya
Classic a shekarar 1978 a Unguwar Tashar Kali
da ke ƙaramar hukumar Talatan Mafara da ke cikin Jahar Zamfara.
Sunan mahaifinsa shi ne Malam Yahaya Ibrahim.
2.2 ILMINSA
Ta ɓangaren ilimi Alhaji Kabiru Yahaya
Classic ya yi karatunsa na firamari a makarantar Abubakar Model Primary School
da ke cikin ƙaramar hukumar Mafara da ke
jahar Zamfara.
Bayan ƙare karatunsa na firamari sai ya shiga
makarantar sakandare a makarantar Sheik Abubakar Gummi da ke Sakkwato.
Bayan Alhaji Kabiru Yahaya Classic
ya kammala karatunsa na Sakandare a 1996, sai ya shiga makaranta ta gaba da
sakandare mai suna Ahmadu Gusau inda ya yi Satifiket daga 2000 zuwa 2002.
2.3 IYALINSA
Ta
ɓangaren iyali Alhaji Kabiru Yahaya
Classic yana da mata uku,
akwai:
- Hajiya Lubabatu.
- Hajiya Shafa’atu.
- Hajiya Hauwa’u.
Ta
ɓangearen 'ya’yansa, Alhaji Kabiru
Classic yana da 'ya’ya tara ga sunayensu kamar haka:
- Yahaya.
- Khadija.
- Ibrahim.
- Zainab.
- Muhammad.
- Fatima.
- Hauwa’u.
- Safiya.
- Mahmud.
2.
4 LAƘABINSA
DA DALILINSA
Laƙabin Alhaji Kabiru Yahaya kuwa ya samo
asali ne dalilin wani shago da suka yi bayar da aron kaset-kaset, da wannan
shagon ke da taken Classic a matsayin sunansa. Daga wannan shagon ne Alhaji
Kabiru Yahaya ya samo laƙabinsa na Classic, a sakamakon haka ne
aka fara kiransa da sunan Classic.
2.5 FARA WAƘARSA
DA FICENSA
Alhaji Kabiru Yahaya Classic ya fara
waƙa
a shekarar 1996. Dalilin fara waƙarsa kuwa shi ne a dalilin waƙokin
Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai da yake sauraro. Sauraron waɗannan waƙoƙin Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai ya
sa Kabiru Classic fara waƙa.
Maganar ficensa kuwa, Kabiru Classic
ya daɗe yana waƙoƙin amma bai samu yin fice ba sai a
2007-2008 wato lokacin da Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi ke matsayin gwamnan
jahar Zamfara a dalilin waƙoƙin da ya rera masa a wannan lokacin.
2.6 WAƘOƘIN DA YAKE YI DA KUMA YANAYIN RERA
SU.
Kabiru Classic mafi yawancin waƙokinsa
na siyasa ne, saboda da ma da su ne ya yi fice.
Ta
ɓangaren yanayin waƙoƙin
Kabiru Classic kuwa, a cikin waƙoƙinsa ana samun ɗan jagora fiye da ɗaya wato su biyu suke jagorancin, wato
wani lokacin sukan yi jagorancin a waƙarsa wato shi da Zuwaira ko kuma tare
da Naja’atu. Haka kuma akwai amshi a cikin waƙoƙinsa.
2.7 KAMMALAWA
A cikin wannan babin an kawo taƙaitaccen
tarihin Kabiru Yahaya Classic sannan kuma wannan babin ya taɓo irin waƙoƙin da Kabiru Classic yake yi da kuma
yanayin rera su.
BABI
NA UKU
SALON
HIRA A CIKIN WAƘOƘIN KABIRU CLASSIC
3.0 GABATARWA
A
cikin wannan babin, an kawo ma’anar salo da yadda masana suka yi bayani tare
kuma da kawo salon hira a cikin waƙoƙin Kabiru Classic. An yi haka ta hanyar
kawo hirar da suka yi, wato Kabiru da abokan hirarsa Zuwaira da Naja’atu. An yi
haka ta hanyar tsamo salon hirar, daga waƙoƙinsa da ke ɗauke da shi.
3.1 MA’ANAR SALO
Masana
da dama sun bayyana ma’anar salo acikin rubutunsu. Misali:
Sa’id
(1981:35) ya bayyana salo da cewa ‘’Salo shi ne yadda mawaƙi
ya zana tunaninsa a takarda".
Ɗangambo (19812.3) yana ganin cewa
‘’Salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da Saƙo”. Ya daɗa faɗaɗa tunaninsa da cewa lallai ne Salo ya
danganta ga yadda kowane mutum ya zaɓi abubuwan da ya yi amfani da su cikin
rubutunsa ko furucinsa don isar da saƙonsa kuma salo yakan ta’allaƙa
ne dangane da yadda mutum yake tunani cikin dacewa.
Guban (1993:54) ya bayyana salo a waƙoƙin
Hausa da cewa ‘’Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce wadda makaɗi yake kyautata zaren tunaninsa ya
sarrafa shi cikin azanci don ya cimma burinsa na isar da saƙo
ko waƙa”.
Salo a waƙoƙin baka abu ne wanda yake daɗa fito da ainihin kyansu ko muninsu ta
haka za a iya gane waƙoƙi masu karsashi, masu hikima da balaga
da kuma waƙoƙi marasa ma’ana marasa inganci.
Yahya (2001) a cikin littafinsa mai
suna ‘Salo Asirin Waƙa’’ yana cewa “Salo yana nufin duk wata
dabara ko hanyar yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon
waƙar
zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar”.
Gusau (2002:54) cewa ya yi “Salo
wata hanya ce da ake bi a nuna gwaninta a cikin furuci ko rubutu, kuma yana
nuna yadda mutum ya shirya wani ta bin yanayin harshensa da zaɓar abubuwan da suka dace da abin da
yake son bayyanawa’’.
La’akari da waɗannan ma’anoni da masana adabin Hausa
suka bayar ina iya cewa ba wani abu ba ne Salo illa hikima ce ko kuma gwaninta
da ake sauyawa cikin magana ko rubutun da ake yi na yau da kullum.
Haka kuma Salo wasu dabaru ne da mai
harshe ke amfani da su domin ƙara wa furucin da aka bayyana ta fatar
baki, ko ta hanyar ƙara ma rubutu armashi kuma ya inganta
shi ya zama yana ɗauke
da wasu kalmomi zaɓaɓɓu. Salo ya danganta ne ga irin kalmomi
da jimloli da aka yi amfani dasu, ta la’akari da saƙon
da yake ɗauke da shi.
3.2
HIRA DA YADDA AKE GANE TA A CIKIN WAƘOƘINSA
Yahya (2001:108-112) Salon hira ko
labari, Salo ne mai ban sha’awa mai kuma sa ƙarsashi ga masu sauraren waƙa.
Ana iya gane Salon a cikin waƙa a yayin da mawaƙi
ke sarrafa harshe cikin muryoyi mabanbanta ya ƙaddarta tamkar yana magana da wani ko
kuwa wasu ne daban suke maganar ba shi ba. Idan kuwa Salon labari ne, mawaƙi
na ƙoƙarin
bayyana abin da ya gudana ne a tsakanin mutane biyu ko fiye.
Yahya (2016) a cikin littafansa na
‘Salo Asirin Waƙa’ ya bayyana Salon hira da cewa
"Idan baitocin waƙa
suka ƙunshi
muryar mai magana fiye da ɗaya,
wato mawaƙi ya ƙaddarta da shi da wani ne ke magana ko
kuwa wasu masu magana biyu ko fiye ne ke wa juna magana to a fagen nazarin waƙa
sai a ce mawaƙi ya yi amfani da Salon hira a cikin waƙarsa”.
Mai karatu ko sauraren waƙa zai ji muryoyi na masu magana a cikin
waƙar.
Salon
hira yakan taimaka wa mawaƙi a ƙoƙarinsa na isar da saƙonsa
ta hanyar sa mai saurare ko karatu ya zamo ya ƙara kusantar mawaƙin.
Wato sai mai saurare ya ji daga bakin waɗannan mutane ne mawaƙin
ke magana, ba wai daga bakinsa shi mawaƙin ba
Akwai
hanyoyi da dama da ake gane Salon hira a cikin waƙoƙin Kabiru Classic za ka ji ana musanyar
magana a tsakanin Kabiru Classic da kuma abokan waƙarsa
waton su ne abokan hirarsa, wato ko dai ya yi hirarsa da Zuwaira ko kuma
Naja’atu. Wannan dai ya danganta da wadda ya yi waƙarsa
da ita.
Ana
gane Salon hirar a waƙoƙinsa, misali ta hanyar tambaya ko kuma
musu a tsakaninsa da abokiyar hirarsa ko kuma su kama wa juna don a yi wa wani
kirari ko habaici, ko zambo ko kuma bayar da labarin abin da ya faru da dai
sauransu.
Ga
kaɗan daga cikin waɗannan hanyoyin da suke yin hirar a
cikin baitocin wasu waƙoƙi.
3.2.1
TA
HANYAR TAMBAYA
An samu hira ta
hanyar tambaya a tsakanin Kabiru da Naja'atu a cikin wani baiti na waƙar
‘Sarkin Gobir’ Misali:
Kabiru: Wane ba ya da haure guda cikin baki
nai dasashi ne
na yi tambaya ko kuma hira?
Naja’atu: Ko ni na so in leƙa
kwabacciyar bakina ina gadara
Wallahi da sai na dara,
Kabiru: Margamar gandutse halor ne gaggado a
bar ka ko tilas
kun jiyo ko kun tura,
Naja’atu : Yanzu ‘yan sarki sun hanƙura
kowa ya bi kad da ka
yarda da su na sani sun dai lwaye.
3.2.2 TA HABYAR MUSU
An
samu hira ta hanyar musu a tsakanin Kabiru da Zuwaira a cikin wasu baituka waƙar ta’ Ciroman Wamakko’. Misali:
Kabiru: Ciroma ya ce kar na yi zambo don haka
na ƙyale,
Zuwaira: Ko ka ƙyale ni kam sai na kwance buhun lalle,
Kabiru: Ko ke kwance tun da an hana dole ki
ma ƙulle,
Zuwaira: Abun ne yai
mini zafi Kabiru angulu wai ni za ya
ƙyama.
Kabiru: Kabir
Classic cizon bobo yai mani baibaici,
Zuwaira: Kabiru ai kyawon hutsu a gwada ma shi
hutsanci,
Kabiru: Da ni da zambo mun raba hanya gara ki
bar naci,
Zuwaira:To in ba ka taɓi ka faɗa mini ko ni ɗai in taɓa ma.
Kabiru: Ki bar ni in na tashi da kai na in yi zubar kurna,
Zuwaira: Ai ni har na katse adalcin ga da kan
nuna,
Kabiru: Ni kuma ke ban haushi batun ga nawa
da kir raina,
Zuwaira:To
ka faɗa
mini jigon Aliyu ba ni shirarra in taɓa ma.
3.2.3 TA HANYAR ROƘO
An
samu hira ta hanyar roƙo a cikin wani baitin waƙar
‘Sarkin Ɓurmin
Jabo’ a tsakanin Kabiru da Naja'atu. Misali:
Kabiru: Kabiru rai na ya ɓaci har gobe abin yanai man ciwo,
Naja’atu: Ina da hauya ta mai ƙwari
in na riƙa
ta nai man kyawo,
Kabiru: Sai dai ba ni da gonar noma na rasa
ko laɓi sai yawo,
Naja’atu: Sarkin ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.
3.2.4 TA HANYAR KIRARI
An
samu hira a tsakanin Kabiru da Naja'atu ta hanyar kirari
a
cikin waƙar
‘Sarkin Gobir ’. Misali:
Kabiru: Wanda Amadu yah haihi ubanai a duniya
Kabir Classic ai
ba shi yin kalan dangi,
Naja’atu: Sannu ɗan Sarki kuma jikan Sarki kuna gani mai
gina
shi na ɓallar shingi,
Kabiru: Tun da tsuntsu kukan gidansu yas so
ya riƙe
ga mai buhu
yar rai na ka mai lelen bagi,
Naja’atu: Yanzu Allah yai Nasiru a gidan Ibrahim
Kabiru Wallahi
baƙin
ciki na ya yaye.
3.2.5 TA HANYAR HABAICI
An
samu hira ta hanyar habaici a tsakanin Kabiru da Zuwaira a cikin waƙar
‘Ciroman Wamakko’. Misali:
Kabiru: Ƙarya ba baƙuwar
Classic ce ba ku dai duba,
Zuwaira: Wanda ka hulɗa da ‘yan siyasa bai wuce ƙarya
ba,
Kabiru: Kullun sai an man ƙarya
sai in ba mu ɓullo
ba,
Zuwaira: Allah waddanka mai baƙar
ƙarya
makashi ɗan tashi
rama.
3.2.6 TA HANYAR ZAMBO
An
samu hira ta hanyar zambo a cikin waƙar
‘Gaskiya Takobin Yaro’ a tsakanin Kabiru da Naja'atu a cikin wani baitin wannan
waƙar.
Misali:
Kabiru: Ni Mafara ni ke iccen mangwaro Kabiru
ya watsa mani shadda,
Naja’atu: Allah mai hana bawa kuka sai wani yam
miƙa
mini kaɗa,
Kabiru: Nar rufe kunne nar rufe hanci sannan
yam miƙa
mini adda,
Naja’atu: Yac ce anshi Kabiru Classic faskari
saƙon
mai maka zamba.
3.2.7 TA HANYAR LABARI
An samu hira/labari daga cikin wani
baiti a cikin waƙar ‘Rayuwa Dukiyar Ɓoye’ tsakanin Kabiru da Zuwaira.
Misali:
Kabiru: Wani Kwamishina da nig gani har ya
ban tausai,
Zuwaira: Ya ɗau fasinja Naija nib bi in fansai,
Kabiru: Nig gane ya ji kunya na kwana jin
tausai,
Zuwaira: Lallai kwamishina kan mulkinku na da
wuya.
3.3 ABOKAN HIRAR KABIRU CLASSIC
Abokan hirar Kabiru Classic ba su wuce Zuwaira Isma’il da
kuma Naja’atu Musa ba, wato ko dai ya yi waƙa tare da Zuwaira ko kuma tare da
Naja’atu.Amma mafi yawancin waƙoƙinsa ya fi yin su ne tare da Naja’atu
Musa.
3.4 SALON
HIRA A CIKIN WAƘOƘIN KABIRU CLASSIC
Yahya
(2016) a cikin littafansa na ‘Salo Asirin Waƙa’ ya bayyana Salon hira da cewa ‘’Idan
baitocin waƙa suka ƙunshi muryar mai magana fiye da ɗaya, wato mawaƙi
ya ƙaddarta
da shi da wani ne ke magana ko kuwa wasu masu magana biyu ko fiye ne ke wa juna
magana, to a fagen nazarin waƙa sai a ce mawaƙi
ya yi amfani da Salon hira a cikin waƙarsa".
3.4.1 WAƘAR CIROMAN WAMAKKO
A cikin wannan waƙar
ta Ciroman Wamakko an samu hira da dama daga cikin wasu baitocin waƙar
a tsakanin Kabiru da Zuwaira. Misali:
Kabiru: Kabiru Allah ya yi mani sa’a Aliyu ya
koma,
Zuwaira: Ashe bikin balbela kaza gobe da
didima,
Kabiru: Kabiru ai ka san mai gona shi ka
batun damma,
Zuwaira: Kai ko marar gona ko ka yi batun
damma ba a riƙa ma.
Kabiru: Ai sabo da maza jari ne tuntuni na
gane,
Zuwaira: Kaza matuniya nike sirrin Kabiru na
tone,
Kabiru: Kowa dai ya tsaya matsayi nai yin
haka dai dai ne,
Zuwaira: Ni ta ruwan sanyi zan biyarka ƙarshenta
ƙasa
zan tuna ma.
Kabiru: Ciroma ya ce kar na yi zambo don haka
na ƙyale,
Zuwaira: Ko ka ƙyale ni kan sai na kwanci buhun lalle,
Kabiru: Ko ke kwance tun da an hana dole ki
ma ƙulle,
Zuwaira: Abun ne yai mini zafi Kabiru angulu
wai ni za ya ƙyama.
Kabiru: Ba ka hayo ƙarfi
kai ƙarfi
dole kunun dawa,
Zuwaira: In kuma an ƙi
biyar magana ta dole a sha yunwa,
Kabiru: Ashe da sauran hankalinki don Allah
ki bar tsiwa,
Zuwaira: In ka tashi ɓaramɓaramarka Classic kowa bai hana ma.
Kabiru: Kabiru Classic cizon bobo yai mani
habaici,
Zuwaira: Kabiru ai kyawon hustu a gwada mashi
hutsanci,
Kabiru: Da ni da zambo mun raba hanya gara ki
bar naci,
Zuwaira: To in ba ka taɓi ka faɗa mini ko ni ɗai in taɓa ma.
Kabiru: Ki barni in na tashi da kai na in yi
zuba kurna
Zuwaira: Ai ni har na katse adalcin ga da kan
nuna,
Kabiru: Ni kuma kin ban haushi batun ga nawa
da kir raina,
Zuwaira: To ka faɗa mini jigon Aliyu ba ni shirarra in
taya ma.
Kabiru: Tunku ya san jibar da zai ba kashi
yarinya,
Zuwaira: Tafiyar kura gefe-gefe ita ba ta
biyar hanya,
Kabiru: In ta ce za ta bi hanya ina haɗa ta da zakanya,
Zuwaira: Na san faɗa kana ba da gari har dai in ba mai
tare ma.
Kabiru: Rubin garden Biba ya yi nauyi ta bani
ta ƙara,
Zuwaira: Ka san Biba da son duniya biɗa da kwaɗan biɗan nera,
Kabiru:Akuya guda da kura tara tag gangama
tatatura,
Zuwaira: Wayyo ita am bat ta da turke da gudu
ta shaida ma gwamma.
Kabiru: Jikan Jeɗo mai hana ƙarya
mai tsoron Allah,
Zuwaira: Kowaj
ja ma bar ni da shi na buge shi da bulala,
Kabiru: Ina ya Allah Kabiru Classic babu
kamar Allah,
Zuwaira: Kowa nas san labarin Jeɗo ya kwatanta ga ciroma.
Kabiru: Zamani ya kai mu ga hairi Arɗo ga shi ya haifi Ali,
Zuwaira: Kwalliya ta yi kubebewa Kabiru babu
ga ɗan ƙoli,
Kabiru: Arɗo du’a’inka ya yi rana tamu kamar leli,
Zuwara: Da rarrafe aka tashi Aliyu ja mu gani
zaki Ciroma.
Kabiru: Aliyu hazo kashe kaifin rana dole na
gaishe ka,
Zuwaira: Gwani gare ni cikin Wamakko Kabiru
ina naka,
Kabiru: Agola an sa ka gida daɗa sai yag gwada ya hi ka,
Zuwaira: Ba ka raba mu da Aliyu Jeɗo ido maƙiyi kowa nat tsaya ma.
Kabiru: Rana kani kuɗi na na ɓoye in yi bukin dangi,
Zuwaira: Da ka ga mai nama ya gitta dole ka
sai tsagi,
Kabiru: Dama ka san shi mai waƙa
dole ya yo gogi,
Zuwaira: Makamakale ko ka koma ko ƙauyenci
zai gwada ma.
Kabiru: Ga wani makama ya gayyato ni ya ga ni
ya ɓoye,
Zuwaira: Mai rayuwa ta birni wane jikinka jikin ƙauye,
Kabiru: Na yini na kwan ina jira nai jikin
saye,
Zuwaira: Kowaɗ ɗauko tuwo nai shi ɗai za ya ci nai ba ya taya ma.
Kabiru: Yunwa tai yunwa ga Kabiru zaune kamar
shege,
Zuwaira: Mutan gari sun sa ka kaɗaici su kuma sun gunge,
Kabiru: Kala ina hammata ga ni na gagara
Kabiru na tsige,
Zuwaira: Ga rogo kuma ba ka da kuɗɗi sannan kowa bai kira ma.
Kabiru: Bakin kura buɗe Kabir in tana biɗar nama,
Zuwaira: Ka sha baƙar
wuya kai Kabiru am maka ka rama,
Kabiru: Azabar yunwa ta fi ta zambo ba wani
na rama,
Zuwaira: Yunwar ta hurce yanzu ga waƙar
na kaiwa da koma.
Kabiru: Ga wani ya zo yai mani ƙarya
ya aza na ɗauka,
Zuwaira: Ashe sara ka ka kallo nai ka ɓoye asirinka,
Kabiru: Muna ta wayon-wayon da wane ka ga ni
na ganka,
Zuwaira: In ba don ba don ba Classic kai ka
san ba ya raga ma.
Kabiru: Ƙarya ba baƙuwar
Classci ce ba ku dai duba,
Zuwaira: Wanda ka hulɗa da 'yan siyasa bai wuce ƙarya
ba,
Kabiru: Kullun sai am man ƙarya
sai im ba mu ɓullo
ba,
Zuwaira: Allah waddanka mai baƙar
ƙarya
makashi ɗan tashi rama.
Kabiru: Wani in yallema ma ƙarya
dole ka ma ruga,
Zuwaira: Dole ka ruga ka rufe ɗaki kad da ka bar taga,
Kabiru: Tagar ma in tana da hanya ka sanya
'yan raga,
Zuwaira: Don ƙarya in ta shigo ɗakin mine ne ribar gudum ma.
Kabiru: Aliyu ɗan Sarkin Musulmi Macciɗo gwarzo ne,
Zuwaira: Ciroma ka yi tsayayye wane kunun wake
ne,
Kabioru: In dai ga Aliyu Orojo Kabiru Sarki
ne,
Zuwaira: Na san ba ni rashin komai ma Kabiru
in dai ga Ciroma.
3.4.2 WAƘAR SARKIN GOBIR
A
cikin wannan waƙar ta Sarkin Gobir an samu hira daga
cikin wasu baitocin wannan waƙar a tsakanin Kabiru da Naja'atu.
Misali:
Naja’atu: Ubangiji na ni ban gaza da roƙo
nai ba saboda Allah
kullum ya nai man gatanci,
: Na riƙe Allah shi ya ke tsaya man kullun baƙin
mutum ya yi kaɗan ya ga rai na ya ɓaci,
: Wanda yaɗ ɗauki mutum yanai mai illoli Kabiru ya
ya ma
za ya jin daɗin kwanci?
: Ni ga Allah
nad dogara ban sanyo wani ba da ka yi
wannan Allah yanai ma rinjaye.
Kabiru: Wanda Ahmadu yah haihi ubanai a
duniya Kabir Classic
ai ba shi yin kalan dangi,
Naja’atu: Sannu ɗan Sarki kuma jikan Sarki kuna gani mai
gina
shi na ɓallar shingi,
Kabiru: Tun da tsuntsu kukan gidansu yas so
ya rike ga mai buhu
yar raina ka mai lelen bagi,
Naja’atu: Yanzu Allah yai Nasiru a gidan
Ibrahim Kabiru Wallahi
baƙin ciki na ya yaye.
Kabiru: Zuga ka tada maƙera
bari in tada ubana Sarkin Gobir mai
martaba Sarkin Isa,
Naja’atu: Sannu-sannu na ke tafiya ta babu
garaje cikin iyawar
Allah ina kwana nesa,
Kabiru: In ga Sarkin Gobir Nasiru mai ƙauna
ta mu yo ido huɗu
lallai Kabir har na ƙosa,
Naja’atu: Mu muna ƙaunar
Sarki Sarki yanai da mu Kabiru amma
sirrin zukata mun ɓoye.
Kabiru: Wane ɗan Sarki don ba ya da kuɗɗin rogo na ga shi bakin
titi yana lasar yaji,
Naja’atu: Ka ga 'yan Sarki sun haɗa kai sun bi gaskiya shi kuma
mahaukaci ya koma yana kwasar
daji,
Kabiru: Na yi hira da shi sai yana faɗa man ƙarya yana bari amma
so yake sai yai turji,
Naja’atu: Da ɗan Sarkin yaz zo yana yi min ɓaɓatu saboda
mamaki sai da kai na yab
banye.
Kabiru: Kai ci zabo Malam ka gane ka sha daɗi ko da ganin burgu
ba shi yin daɗin nama,
Naja’atu: Lallai mai waƙa
ko wana ne ya san daɗi
ga mai gidan
Hajiya Rabi yau can nak koma,
Kabiru: Uwar gida Hajiya Rabi Sarauniya da
kin amince man mai
bugu na nar rama,
Naja’atu: Idan Hajiya Rabi’atu ta yi min gata
to ashe Naja’atu wa
zai kira na‘yar ƙauye.
Kabiru: Duk ɗiyan Sarki ne mutane in kun gane uba na
kirki ne ga
shi ga’ya’yan kirki,
Naja’atu: Ja mu je baƙon
dole jinin Ummaru Sanda mahassada
sun gane a yau ta zan taki,
Kabiru: Tela bai san da cikin gari akwai kuɗɗi ba Kabiru sai dai
har in yana kwana ɗunki,
Naja’atu: Za ya nemo kaji a kai gida mata nai
saboda murna am
fige kaji an soye.
Kabiru: Nemi Kwano Malam rufawa kanka asiri
karankaɓau ba
rango yake tun farko ba,
Naja’atu: Ina ‘yan Sarki sai ku ɗauki horo na ka ga wanda bai
zama Sarki ba bai sha daɗi ba,
Kabiru: Ka ga kowa bai san shi cikin duniyar
ga ba Kabri Classic
na yarda bai san kowa ba,
Naja’atu: Ban da Sarki na taimakonsu da sai
rugga duk da hakan
amma wane kai ya jaye.
Kabiru: Mai saran kaba idonka kar ya kauce ga
rina gadar zare ta
katse da mai man labako,
Naja’atu: Ga sanyi ɗan sarki ana kwanan sanyi saboda ba
sisi
gane ba sauran iko,
Kabiru: Ashe ɗan Sarki sai dai ya yi rantsar idi
rashin wadata ta sa
yana haushin maiƙo,
Naja’atu: Na ga ɗan Sarki sai yana ta ɓoyon hannu ashe wajen ga
tuyar maƙwabta yat toye.
Kabiru: Wane ya ban tausai ƙarfi
bai fi jiki ba wani ɗan
Sarki
shaddar rama tai yaɗ ɗunka,
Naja’atu: Ga shi ya bi rariya shaddarsa miyan
goro ku ji ƙwarin
wake sun hana mai shan iska,
Kabiru: Tunkiya ta cizo nan akuya ta jawo
shige gida don shanu
suna nan bayanka,
Naja’atu: Na ga ‘yan yara suna kuwa sun bi
kwarkwaɗa suna
faɗin mai waƙa muna neman maye.
Kabiru: Wance kura mis sa ki ke shiga harka
ta Kabiru ni ko can
ba ni son wargin cizo,
Naja’atu: Ga ruhewa ta nan ina kurin gero da
nit hato nab buɗa
a
yau ya zam ɓarzo,
Kabiru: Tun da wargin haka ne a yau ni na yi
hushi mu je ga
Sarkin Gobir ina samo zozo,
Naja’atu: Mun taho da hushi za mu na wajjen
noma da mun ka
duƙa sai ga shi hauya ta karye.
Kabiru: Ranan fa Classic ni na kwana dariya
da nig ga mai
gilɓoshi yana tamnar goro,
Naja’atu: Rinƙa alheri sai muna ta kallon kallo ashe
dai mawaƙi
ba ya son kallon mauro,
Kabiru: Duk abin da na ce wanda ba na alheri
ba gare ka ko ni ma
na sani sai nai ɓauro,
Naja’atu: Mai halin banza wani mai ɗabi’un banza da zuciya ta
ƙarya mutum ai ya karye.
Kabiru: Wane ba ya da haure guda cikin baki
nai dasashi ne na yi
tambaya ko kuma hira,
Naja’atu: Ko ni na so in leƙa
kwacciyar baki na ina gadara wallahi
da sai na dara,
Kabiru: Marganar gandutse halo ne gaggado a
bar ka ko tilas kun
jiyo ko kun tura,
Naja’atu: Yanzu ‘yan Sarki sun hanƙura
kowa ya bi kad da ka
yarda da su na sani sun dai
lwaye.
Kabiru: Wanda yan nemi tuwo yag gaji bai samo
ba Kabiru
yunwa na sa shi yin kwanan
dole,
Naja’atu: Ka ga ‘yan Sarki an ga ba wuri an ɓoye suna ta fatar su
ga ko ƙawa nan ta sulle,
Kabiru: Tun da ɗan Sarki bai da amana na gano sun kau
da kai in
ka lura tamkar sun ƙyale,
Naja’atu: Ce yana nan na san da bai barin
jayayya ɗan Sarki ko da
ya gwada mai ya jaye.
Kabiru: Yau ko al’ummata daɗa ga kallon-kallo da nig ga mai
tarƙonshi yana kallon gwame,
Naja’atu: Mai dahwahen Sarki yana ganin ya
tisra a zuciya tai sai
ya yi mummunan hwame,
Kabiru: Ku dakata ba fankan-fankan ne kilishi
ba Kabiru sai in ya
samu kyakkyawan tsome,
Naja’atu: Ni da mai laifi babu shiri ba
shiryawa abun da ke damu
na dukan sai na juye.
3.4.3 WAƘAR SARKIN ƁURMIN
JABO
An
samu hira daga cikin baitocin wannan waƙar ta Sarkin Burmin Jabo a tsakanin
Kabiru da Naja'atu. Misali:
Kabiru: Kabiru rai na ya ɓaci har gobe abin yanai man ciwo,
Naja’atu: Ina da hauyata mai ƙwari
in na riƙa
ta nai man kyawo,
Kabiru: Sai dai ba ni da gonar noma na rasa
ko laɓi sai yawo,
Naja'atu: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki,
Kabiru: Don Allah Jama’a ku riƙa
mani za ni fari mutanen Jabo,
Naja’atu: In kuma kun ka bari nif faɗi kun ga jikinmu zan yo
tambo,
Kabiru: In kuma kun ka riƙa
min za ku ga na wuce sai ƙwambo,
Naja’atu: Sarkin ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.
Kabiru: Im ma har wani bai gane ba shi wani
na sani ya gane,
Naja’atu: Ashe mawaƙi
ɗan wayo ne duk wada yaf faɗi daidai ne,
Kabiru Da nig ga leda sai naɗ dauka ka ga ashe tulin kashi ne,
Naja'atu: Ka aza ko bantamin zuma ne don ka
wuce ka sha zaƙi.
Kabiru: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu farin cikin duk Jabo,
Naja’atu: Ko ‘yan yara suna ƙauna
tai tun da jikinsu kan ɗau
bobo,
Kabiru: Kabiru na tanya ku da murna sannu da
ku mutanen Jabo,
Naja’atu: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.
Kabiru: Ka je ya Allah yana bayanka Aliyu kaɗa ni in sha dada,
Naja’atu: Ka riƙe dangi ka riƙe
sabga tufansa babu mai ko dauɗa,
Kabiru: Kai masu aure kai masu suna ko ni nan
Kabir na shaida,
Naja’atu: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.
Kabiru: Kabir Classic ga ni a Jabo inda farin
watan Sarkinsu,
Naja’atu: Mai albarka ɗan albarka Jabo farin cikin an ba su.
Kabiru: Don samun Sarki Aliyu zai wahala
hakan an san su,
Naja’atu: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.
3.4.4 WAKAR GANIN IDO
An samu hira daga cikin wasu baitoci na
wannan waƙar ta Ganin Ido a tsakanin
Kabiru da Zuwaira. Misali:
Kabiru: Aliyu ai ko gobe da shi don Shehi
hali nai yaka yi,
Zuwaira: Zan yi yaƙe-yaƙen
takobuna shi gwamna da jan biro
yaka yi,
Kabiru Ka sanya hannu yanzu a basu Kabiru ni
na yarda a yi,
Zuwaira: Ɓakin ciki na yanzu Kabiru ga dokunan
nan ba mahaya.
Kabiru Saboda Baba ba ni aminta ana ta cin haƙƙin
marini,
Zuwaira: Ina masaƙi
yay yi Classic Kabiru bai zauna ba tuni,
Kabiru: Da sunɗe-sunɗe akan daɗa miƙi mu raina mai mugun
katani,
Zuwaira: Idan da dama dawo a dama a sha da
dama ai ta riya.
Kabiru: Gwamna yi man kashedi inda Jarma ya
dai sani gaba,
Zuwaira: Masha Allahu mun yi dace Oranti bai
kasa muna ba,
Kabiru: Ke ba ki san komi ba gaba ɗai ki dakata man in ci gaba,
Zuwaira: Kabiru ga ni ina sauraro ina biyar
hujjar ka biya.
Kabiru: Oranti hauka za na yi nan gaba in ba
ka sassauta mani ba,
Zuwaira: Gwamna yi mai magana ya bari don ba a san wada za ta
tsaya mana ba,
Kabiru: Ubangiji gatan marar shi ko ba a so
yannab ba’a ba,
Zauwaira: Oranti sannu da ƙirgi
daloli ka bai wa ɗanɗa gun
Safiya.
Kabiru: Da Sallama ni za ni shiga garinmu nai
waƙa
na fita,
Zuwaira: A gaida jikan Abdullahi ɗan Yari in zo in rabata,
Kabiru: Da safe niz zo ba ni barin Mafara sai
rana ta yi fita,
Zuwaira: Ni sai naje gun Asma’u Zuwairatu in
gaido Hajiya.
Kabirou: Na sai man shanu da kuɗina wajen rabo an bani tsaki,
Zuwaira: Kar ka ji komai Kabir Classic an yi
wa mai rama ma
buki,
Kabiru: Lallai turmi ba ya riƙa
ta Kabiru in dai ga madaki,
Zuwaira: Mutum ya lura da Allah yay yi ni ba
wani mai sa in ci
wuya.
Kabiru: Tumbin yaƙi
mai gudun Hisabi ba ya shakkar sababi,
Zuwaira: Kabiru rabin jin daɗin duniya mura ma ta mai ladabi,
Kabiru: In dai ba ka da mugun aiki ba ka jin
shakkar laƙabi,
Zuwaira: Idan miya ta riga abinci a nan ake
gane maciya.
Kabiru: Idan duma gero taka ci ku ƙyale
goge gun kabuwa,
Zuwaira: Da an ka maran na ƙi
na rama saboda albarkar taƙawa,
Kabiru: Kabiru ko ni na koyi tuma kar da a ce
na koyi nawa,
Zuwaira: Ba na jin haushin dillali na tutu in
dai ga masaya.
Kabiru: Wasu da sun ga na yi wa Shehi waƙa
za su ga APP ni ka
yi,
Zuwaira: Bara na Ƙara
faɗa wa mutane Kabiru PDP ya ka yi,
Kabiru: Mai ganewa ya ƙi
ya gane kasan komai na yanayi,
Zuwaira: Ba kai ɗai ba Kabiru PDP ko ni ma na yi biya.
Kabiru: Da tunkiya ta kamu da ciwo na lura
domin ba ta tuƙe,
Zuwaira: Shi ko manomi cikon gadara na gan shi
kunkurin shi
rike,
Kabiru: Na saki kowa na riƙe
Jarma Oranti albashinmu da ke,
Zuwaira: Da ka riƙe
Allah ka ci gaba za ka watsa alkaryar maƙiya.
Kabiru: Bugun ku bai kai gare ni ba Kabiru
balle in ji jiki,
Zuwaira: Kabiru ka more rijiya matsalar ka guda
na rashin wasaki,
Kabiru: Ai ina da guga aru-aru igiyar ɗaurawa naj ji jiki,
Zuwaira: Ka sai da guda ka sawo tsawo don
Allah rage sauga ta
tsiya.
Kabiru: Shigo-Shigo ba zurfi banza Kabiru ban
yarda fa da shi,
Zuwaira: Ya wuce reza baki na Kabiru ya wuce
almakashi,
Kabiru: Bakina jari na Kabiru shi nika kwana
tare da shi,
Zuwaira: Saboda Allah shi yay yo mani kowa bai
sa in ci wuya.
3.4.5 WAƘAR HANA KISHIYA WAƘAR
MIJI
An
samu hira a cikin wasu baitocin wannan waƙa ta Hana Kishiya Waƙar
Miji a tsakanin Kabiru da Naja'atu. Misali:
Kabiru: Maciji mai sarar gayya sai mun bugi
mai mugun nuhi,
Naja’atu: Idan tsafi ne kai wa jaha sai mun tuɓuke wannan kahi,
Kabiru: Azabar da kay yi wa jama’a za ka ɗanɗano wannan dahi,
Naja’atu: Domin Sallar bana na shaida jama’a da
yawa ba sa
kawa.
Kabiru: Mu yi ma wankan babban bargo mu gwada
maka ƙarfin
addu’a,
Naja’atu: Don yanzu matasa sun shirya fatansu
mu dai zarce sa’a,
Kabiru: Har Ƙuru har bokan ƙuru
banke su muke yi ba ba’a,
Naja’atu: Akuri da magarya duk ɗai ne bambanci ba wani mai
yawa.
Kabiru: Wani ya hau kuka ya faɗo kuma ga shi a cikin shingi
ƙaya,
Naja’atu: Da ya tambaye ni tun farko da na
gwada mashi ɗan
ɗibar miya,
Kabiru: Ku ji yarinya mai gandarƙi
kuma ta iya babbar zolaya,
Naja’atu: Ni da wane ba sauran ƙauna sannan kuma ba wata
jituwa.
Kabiru: Yau mai ƙarfi
ga talakkawa Zamfara duk mun koma awo.
Naja’atu: Sai an yi takarda a rubuce sannan ka ka cin bashin
dawo,
Kabiru: Babu tallafi mun lalace daɗa yau ba noma ba kiwo,
Naja’atu: Ya mai
da mutane shanu nai fuskarsa kamar naman
dawa.
Kabiru: Ni Kabiru na dai kai ƙarshe
ɗunkin afatati ba ni yi,
Naja’atu: Masu yi muna kallon ‘yan wahala ku ci ku ɗai babu
taɓin tayi,
Kabiru: Wasu sun kashe al’umma
da Jaha ko jin shakka ma
ba su
yi,
Naja’atu: In Allah ya kai ƙarshensu za mu kai su ko a rabin awa.
3.4.6 WAƘAR RAYUWA DUKIYAR ƁOYE
A
cikin wannan waƙar
ta Rayuwa Dukiyar Ɓoye
an samu hira daga cikin wasu baitocin waƙar a tsakanin Kabiru da Naja'atu.
Misali:
Kabiru: Bello Matawalle waƙa
ce zan yi saurara,
Naja’atu: Daɗa
yau da mu da guntaye za a yin tsera,
Kabiru: In an tsere ma a bubbuge ka ba kara,
Naja’atu: Duk inda
kag ga guntu wajjen faɗa
za ya.
Kabiru: Ni da ‘yan siyasa
na ɗau anniyar daru,
Naja’atu: Kabiru faɗa
mani ni ma in ji in ƙaru,
Kabiru: To mun yi wa junanmu sani damu sau
wauru,
Naja’atu:
Sai ka je ka koyo ni gunka in koya.
Kabiru: Komai za a man PDP nake ƙauna,
Naja’atu: Babbar Jam’iyya ta ita ma tana so na,
Kabiru: Kai ko tana guda na ita za ni sa kai
na,
Naja’atu: Balle
da amana ɓota
ba ta ƙin
hauya.
Kabiru: Kashin baƙi
sai taron garke na gardawa,
Naja’atu: Don waƙar da nay yi fashin baƙi sai an nemi Hausawa,
Kabiru: Da ma ɗaurin giwa wa za ya sa tsauwa,
Naja’atu: Kar ku ɗauki
giwa tamkar barkata karya.
Kabiru: Na ƙyale rijiya tun da ruwa su na rafi,
Naja’atu: Kafin
na tuba sai na san wa na wa laifi,
Kabiru: Sai babbar murna ke shi gini tafi,
Naja’atu: Kuma sai ya yi shi ɗai don kaucewa ingwayya.
Kabiru: Kabiru Classic wai mi nir rasa yanzu,
Naja’atu: Balle ka canja Jam’iyya na faɗi ɗanzu,
Kabiru: Zafin biɗa ka samu kuma na faɗi yanzu,
Naja’atu: Komai akwai gida na kuma ba ka taɓin hauya.
Kabiru: Ɗaukar rigima ta sai fati marinjayi,
Naja’atu: Ko kare ya kai gwarzo ai ba ya cin tayi,
Kabiru: Lema nika so don ita kowa yake yayi,
Naja’atu: Bam barin ɗiya
in tahi don tambaɗa
goya.
Kabiru: Ai gaskiya guda sure shi yake zautu,
Naja’atu: Mu
mata har abada ba ma gudun shantu,
Kabiru: Na daina jin a Zamfara an zagi
Dallatu,
Naja’atu: Sukar mashi
ta gagari masu ingwayya,
Kabiru: Za ni jaddad maku ni Allah nake
bauta,
Naja’atu: Shi ka ƙara kwana na to kun jiya ƙatta,
Kabiru: Ga duniya tana so na ni ina ƙinta,
Naja’atu: Don na
ga ta kashe Jama’a
duniya manya.
Kabiru: Ga ma'aikatan Zamfara nan za su yin
bore,
Naja’atu: Mai shan nonon ‘yan soke bai gudun saye,
Kabiru: Mai ƙaramin albashi bai shan miyar sure,
Naja’atu: Kai wanga bala’i
don Allah Kabir saya.
Kabiru: Wani ya ja ni faɗa kolo mai ƙujen
baki,
Naja’atu :
Wai istigifari mai kwana yana tsaki,
Kabiru: Sai ya ga fasiƙanci
sannan yake ɗauki,
Naja’atu: Ɗan
tsurku moriyarka butulci ka kan koya.
Kabiru: Duniya katifa ce kullun ina lura,
Naja’atu: Mai dakonki bai hau ki ba don ba a yin kara,
Kabiru: Dama ɗan dako gun kwana ba shi yin tara,
Naja’atu: Fatansa ya farka da lafiya aji za ya.
Kabiru: Wani kwamishina da nig ga har ya ban
tausai,
Naja’atu: Ya ɗau
fasinja Naija nib bi in fansai,
Kabiru: Nig gane ya ji kunya na kwana jin
tausai,
Naja’atu: Lallai
Kwamishina kan mulkinku na da wuya.
3.4.7 WAƘAR GASKIYA TAKOBIN YARO
An
samu hira a cikin wasu baitocin wannan waƙar ta Gaskiya Takobin Yaro a tsakanin
Kabiru da Naja'atu. Misali:
Kabiru: Yau na yo guɗaɗɗar waƙa kowa ya gane a misali,
Naja’atu: Kafin in shiga tsabar waƙar zan kafa tau hujja da dalilai,
Kabiru: Yau magidanta Zamfara Kabiru an haɗa al’umma
da iyali,
Naja’atu: Asusu yau ya
zan tarihi ba maganar ajiya aka yi ba.
Kabiru: Ko wane za ya sauka in hau ɗan Ali ɗin nan dai nika
ƙauna.
Naja’atu: Idan lalurata
ta taso ku bar ni kullun in yi da kai na,
Kabiru: Ba ni buƙatar
komi gare ku ƙadangare tuni ya aje zana,
Naja’atu: Bai dawo wa inda ya bar ta to ko can mi zai yi da saɓa.
Kabiru:
Ni Mafara nike iccen mangwaro Kabiru ya watsa mani
shadda,
Naja’atu: Allah mai hana bawa kuka sai wani
yam miƙa mini
kaɗa,
Kabiru:
Nar rufe kunne nar rufe hanci sannan yam miƙa
mani
adda,
Naja’atu: Yac ce anshi Kabiru Classic faskari
saƙon
mai
maka
zamba.
Kabiru
: Ni da nar rayu Sabon Birni har wani zai nuna mani tsage,
Naja’atu: Karyarka wane ta sha ƙarya
fara ta grime maka sunge,
Kabiru:
Ƙuru in gaskiya gare ka wajen tafiya
mis sa ka ka waige,
Naja’atu: Ya karkace wurin sata don ba yanke
hannu aka yi ba.
Kabiru:
Ku zo ku je kallon ta tuba wai jiya an jefe muna wada,
Naja'atu:
Inda ina wajen aka jifar da sai na kwaɗa
masa sanda,
Kabiru:
Talakka ka iya ɗaukar fansa don fansa tai
ba ta da tsada,
Naja’atu: Mai mulki kowa ab bai
so noma nai shine yaka girba.
Kabiru:
Indai ana zuwa ruwa Kabiru ai wata ran sai an kasha tulu,
Naja’atu: Mai gaugawa ga dama
koko can wata ran sai ya kwaɓa
ƙullu,
Kabiru:
Sara ni kai ina dubawa cikin duhu na lura da ƙyallu,
Naja’atu: Ko an rufe tukunyar kashi
ba tausan hanci taka ji ba.
Kabiru:
Ba saukar ƙuru ba ga mulki ni
EFCC nika hange,
Naja’atu: Ko shi yag gina EFCC
ni na san sai tai masa dabge,
Kabiru:
Sata har ta rashin lissafi ya yi ta wai don ba ya da shinge,
Naja’atu: Lalli zamu ga wasar kura
gardawa sun ƙoshi da gumba.
Kabiru:
Ni Mafara nike kowa nau ne a bincika min ba ni da bare,
Naja’atu: Matizkabura Kabiru
Classic mu garzaya har in wuce
ware,
Kabiru:
Baƙin ɓarawo
ɗai
ab ban so sala ya bar muna yar riƙe
sare,
Naja’atu: Bai ƙaunar jajjayen kaya shin ba ‘yan banga
ya ka so ba.
Kabiru:
Ba ni cikin tawagar masoyanka hannu riga mun yi da
tsaido,
Naja’atu: Na san ka sadda da
ba ka da sisi na fi ƙarfin
kai mani
dodo,
Kabiru:
Za ni faɗi
ƙaramin taƙadiri tun Mafara har in wuce
Mando,
Naja’atu : Babu mutum ɗaya
mai kwaraka tai ka aza na mance
haba duba.
Kabiru:
Ina uowan biri da gada kuma babu rowan riga da farari,
Naja’atu: Ban bin wane
a kowace hulɗa buri nai lalata samari,
Kabiru:
Ai gara in wuce da talauci ko kuma kullun in jiƙa
gari,
Naja’atu: In sha in riƙe
nawa mutunci ko da kullun ba ni kwabba.
Kabiru:
Yau ga ƙurungu mugun kifi hulla ya soke ta ga
goshi,
Naja’atu: 2019 zan maku kyauta ga ƙato
nan ba mu da mai shi,
Kabiru:
Nan gaba bai iya ɗaukar kainai tun da haramce
zai ci ya
ƙoshi,
Naja’atu: Tun da haramun ba ta
narewa ba wai sai waƙa
muka yi
ba.
Kabiru:
Babban gida yana ban sha’awa
za ka ga ɗa
na gidan
maganarci,
Naja’atu: Yai tausayi da tsoron Allah ya ɗauka ya ba mabuƙaci,
Kabiru:
Dangi sui fahari da shi Kabiru domin ya fidda su takaici,
Naja’atu: Yai musu aure yai musu suna ba ya
gajiya da hakan ya
ka yi ba.
Kabiru:
Kwamishina zai aurar da ‘yar
shi ba
ya da kuɗɗi
yas saɗa
ganga,
Naja’atu: Yat tafi ƙauyen
Birnin Gwari yac ce shi a’a na gadanga,
Kabiru:
An kawo masa fura da nono har da tuwo nai shaƙe
da
langa,
Naja’atu: Muna ido huɗu sai yas sarƙe
idanuwa nai sun daɗa
taiɓa.
Kabiru:
Ni Mamuda ina ƙaunarka kai nika
hange safe da yamma,
Naja’atu: Ni biyarka ta yi min rana don ba ni
da yunwa ba ni da
tsuma,
Kabiru:
Ko da ban da ƙiba ki faɗa
musu kowa ya san ba ni da
rama,
Naja’atu: Allah ya
kau da ɓacin
rana mu roƙon Allah mu ka zaɓa.
Kabiru:
Ni can dori ina ɗan yaro duk sata ba ta
wuce jakkai,
Naja’atu: Zuwa-zuwa loto na canji har sata ta
kai ga dawakai,
Kabiru:
Sata ta wuce doki Zamfara yau ta kai an saci Sarakai,
Naja’atu: Shi ke nan kuma sai
tarihi kamar ruwa in sun wuce
gyabba.
Kabiru:
Ba don ƙaunnar wane ba Kabiru jemu na sai ya
kashe
gora,
Naja’atu: Baƙar wuya da azabar yunwa ta saka al’umma tuna
bara,
Kabiru:
Isa ka kawo tsanda Classic mai nema ai ba ya da tara,
Naja'atu:
Lallai mai nema bai tara sai in ba yunwa ya ka ji ba.
Kabiru:
Zamfara ba ta mutum ɗaya ce ba gida na gado ne
na
marayi,
Naja’atu: Allah ya jaraba mu Classic ta faɗa hannu na ɓarayi,
Kabiru:
Za ta fito da hukuncin Allah ka taimaka Allah mabuwayi,
Naja’atu: Zamfara mu Mamuda muke
so Allah ba kwana ya ka yi
ba.
Kabiru:
Kabiru hawan kuka wuya gare shi ba a hawa sai an yi
dabaru,
Naja’atu: Amma wanda sana’a tai ce hawan
miya mi zai yi wa
daru,
Kabiru:
Wutar ga an daɗe da kasha ta ni kuma na so yanzu ta
huru,
Naja’atu: Idan akwai tafki kusa na san kashe
wutar ba za ya daɗe
ba.
Kabiru:
Tun lokacin da yay yi jawabi tun nan nis san ba ya da
wayo,
Naja’atu: Kai bari mamakin shi Classic ɗan duƙushi sharri yaka
koyo,
Kabiru:
Ruwa idan da rabonka cikinsu zuba ga kwando bai maka
yoyo,
Naja’atu: Don haka ɗan
Ali ja mu ka kai mu mu kori burgun nan
yai laba.
Kabiru:
Ku jama’a ga mai ƙaton
kai ya zaka ya sace mani hulla,
Naja’atu: Ai ita zai sa wa
ran salla mu kuma sai mun sa masa
ƙwalla,
Kabiru:
In taƙamarsa ɓoyon
kurya mu sai mun watsa shi ga talla,
Naja’atu: Dama waƙa ce aiki na ban da hasumi ban iya
gaba.
Kabiru:
Mai iya noman Najeriyag ga duk mun ce mun bar mas
hauya,
Naja’atu: Mun so mu taimaka a yi noman yac ce
shi ya
ƙoshi da
gayya,
Kabiru:
Tun jiya ga shi a kuyyar fari don Allah dai Alhaji sauya,
Naja’atu: Komai da shawara yaka kyawo
to akasin nan za a ga
kwaɓa.
Kabiru:
Mai kallo na hunta Kabiru to Ali Bagudu yai mani riga,
Naja’atu:
Yai maka taggo yai maka wando ba ka da sauran mai
maka burga,
Kabiru:
Jarman Bargu ya riƙe
ni amana a rijiya ta kai mani guga,
Naja'atu:
In sha in shayar da Musulmi mun gode ɗan
Amadu
Baba.
Kabiru:
Hauka tana ga dogo Kabiru salo da kuri na ga gajeru,
Naja’atu: Kabiru ai kai ma dogo ne
sanar da ni don gobe na ƙaru,
Kabiru:
Ko ni ina ciki yarinya hauka ta suka ga tsageru,
Naja’atu : Ni ko salon da kac ce
gare ni na kama sai nai masa
ƙwamba.
3.4.8 WAƘAR IBRAHIM GWAGGO
An samu hira a tsakanin
Kabiru da Naja'atu a cikin wasu baitoci na wannan waƙar
ta Ibrahim Gwaggo. Misali:
Kabiru:
Iliminka ya kai ga komai mai daɗin jingina sannu bango,
Naja’atu: Ni dai Classic ina son
na tambai ka wurin Maji daɗin mi
ka hango,
Kabiru:
Shi bai halin 'yan siyasa su shanye madara su ce yaro an
shi gwango,
Naja’atu: Ya tsarkake zuciya tai Maji
ɗadi
mu ba mu fatan a ce
bai zamo ba.
Kabiru
: Kashin kare ya fi taki a gonarsu sai ɗan
sheri kawai zai yi
noma,
Naja’atu; Ka jawo faɗa Classic da bakinka sai ranar tammaha
in
shigar ma.
Kabiru:
Na bar faɗan ba ni yi je ki fanshe ni na koma
innuwa in ci
girma,
Naja’atu: Girman dutse kawai za ya ruɗe ni lallai na
yarda ba
allaƙa
ba.
Kabiru:
Ni dai Classic komai ya same mu na san Allah ka yi ba
wani ba,
Naja’atu: Mai garwayen tanadi ɗan maƙwabcin mu ya yo sata tsayi bai
ga nai ba,
Kabiru:
Ya raina kowa gida ko iyayensa sun san sheri yake bai
baro ba,
Naja’atu: Da in haihi ɗa
mai irin ɗabi’unsa har gara na ƙaura ban
samu ɗa ba.
Kabiru:
Kaiwa a hau ai raha in ji kakanmu sai dai ya ce ƙaya
na
magarya,
Naja’atu: Mai son nama farauta ake ba
shi shi dai talgin taɓi na
tukunya,
Kabiru:
Ni dai waƙar ga ban yo
garaje ba gona ta ruhe gaya
banya.
Naja’atu:
Mai gaskiya kai riƙe
gaskiyarka ba za a gwadama
kunya gida ba.
Kabiru:
Ibrahim Gwaggo ka gadi kakanka gun san Jama’a
da son
tallakawa,
Naja’atu: Ko ni ma nan ina son zurri’arku
Naja’atu ce tsasto gun
Kanawa,
Kabiru:
Mu dai Allah muke kai wa kayanmu na san ko dole in
girmi wawa,
Naja’atu: Lallai da kuɗɗin ƙwarai nas sayo ƙyalla
kowa ya lura
ban sa na yi ba.
Kabiru:
Ashe tsaka mai wuya ba a ƙaunarta
na sai nonon dala mai
ƙudahi,
Naja’atu: Duk wanda yah haihu ƙarfi
a ‘yayansa
ba na sa tammahar zai
yi ƙarhi,
Kabiru:
Nonon da nis so in sha an umurce ni lallai an ce dawon
dunyi hyahi,
Naja’atu:
In ka sai wanda ba don ni ba Kabiru ai dambu za ka sha
ba fura ba.
Kabiru:
Mutane Jama’a ku kalle
su in kura ta wuce ga ƙasa
nan,
Naja’atu: Can da iyaye ake
wa da matansu to yanzu ni na faɗi ga
ɗiya
nan,
Kabiru:
Ibrahim Gwaggo mai so ya cuce ka mu dai mun ce bari
nan gani nan,
Naja’atu: In Allah ya yi gwarzo mutanen mu ƙaryar
wancan ya
ce
bai zamo ba.
Kabiru:
Fagen siyasa a Shinkafi zan tare don aiki na wa mai
gida na,
Naja’atu: Ko ni Classic ina so na rakke
ka amma in ya bari mai
gidana,
Kabiru:
Zan je wajen nasa in Jalla ya yarda ko da Maji daɗi
zan
sanya rana,
Naja’atu: Allah yake
fidda shuka mutanenmu ba wai ruwa ko
yawan ƙoƙari
ba.
3.5 KAMMALAWA
A wannan babin an kawo ma’anar Salo da kuma ma’anar Salon hira,
tare da yadda ake gane hirar a cikin waƙoƙin.
An kuma kawo sunayen abokan hirar Kabiru Classic tare da kawo wasu waƙoƙin
da suka yi hirar a cikinsu.
Babai
na Huɗu: Kammalawa
4.0
Gabatarwa
A wannan babin za a yi
bayanin kammalawa ne da yadda tsarin aikin ya kasance tun daga babi na farko
har zuwa na ƙarshe. Wannan babi
ya ƙunshi waiwaye da sakamakon bincike da
waɗanda
aka yi hira su da kuma Rataye.
4.1 Waiwaye
Hausawa na cewa ‘waiwaye
adon tafiya’. Don haka za a dubi ayyukan da suka gabata na masana, domin ganin
irin koƙarin da suka yi wajen fito da ma’anar
salo da ireirensa, musamman masana irinsu Yahya, Sa’idu Gusau, Ɗangambo, Sa’id, Guban da makamatansu.
Ga irin yadda kowannen su ya kalli ma’anar salo
kamar haka:
Ɗangambo
(1981) Ya bayyana salo da cewa “Salo shi ne yadda mawaƙi ya zana tunaninsa a takarda".
Sa’id (1981) yana ganin
cewa “Salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo”,
Guban (1993) ya bayyana
salo a wakokin Hausawa da cewa “Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce wadda makaɗi
yake kyautata zaren tunaninsa ya sarrafa shi cikin azanci don ya cimma burinsa
na isar da sako ko waƙa".
Yahya (2001) ya bayyana
salo da cewa “Salo yana nufin duk wata dabara ko hanyar yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar
zai isa ga mai saurare ko karatun waƙa”.
Gusau (2002) cewa ya yi
“Salo wata hanya ce da ake bi a nuna gwaninta a cikin furuci ko rubutu, kuma
yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta yanayin harshensa da zaɓar
abubuwan da suka dace da abin da yake son bayyanawa”.
Ta la’akari da waɗannan
ma’anoni daga bakin masana kuma magabata ya sa aka karkata akalar wannan aikin
akan salon hira a cikin wakokin Kabiru Classic inda aka dubi wasu waƙoƙinsa
kamar waƙar Sarkin Gobir da waƙar Sarkin Ɓurmin Jabo da waƙar Hana Kishiya Waƙar Miji da waƙar Gaskiya Takobin Yaro da waƙar Rayuwa Dukiyar Ɓoye da waƙar Ciroman Wamakko da waƙar Ganin Ido da kuma waƙar Ibrahim Gwaggo.
4.2 Sakamakon
Bincike
Wannan aiki ya gano cewa
ana samun salon hira ta hanyoyi da dama a cikin waƙoƙin
Kabiru Classic, wanda yake yin hirar tare da abokan waƙarsa. Kaɗan
daga cikin hanyoyin da aka samu salon hirar a cikin waƙoƙinsa
akwai:
1. Ta hanyar tambaya.
2. Ta hanyar musu .
3. Ta hanyar roƙo
.
4. Ta hanyar kirari.
5. Ta hanyar zambo.
6. Ta hanyar habaici.
7. Ta hanyar ba da labari.
Waɗannan
su ne manyan hanyoyin da aka fi samun hira a cikin waƙoƙin
Alhaji Kabiru Yahaya Classic.
4.3 Shawarwari
Shawara abu ce mai
muhimmanci ƙwarai, da wannan
ne ya sa aka ga ya dace a keɓe wani sashe a cikin
wannan kundi domin ba da shawarwari a matsayin gudummuwa wajen fito da salon
hira a cikin Waƙoƙin Kabiru Classic. Ga wasu daga cikin
shawarwari, musamman ga ɗalibai da malamai da
manazarta masu nazarin Adabin Hausa musamman abun da ya shafi waƙa.
1.
Wannan bincike na bayar da shawara kan yin
nazarin salo a cikin waƙoƙin Hausawa, domin ƙara haɓɓaka
harshen Hausa.
2.
Nazarin salo na ƙara bunƙasa
tunanin mai yinsa, don haka wannan bincike na bayar da shawara kan mayar da
hankali wajen nazarin salo musamman a cikin waƙoƙi.
3.
Nazarin salo abu ne da ke fito da wasu keɓaɓɓun
kalmomin harshe, ke nan nazarin salon na bunƙusa
harshe. Don haka wannan bincike na bayar da shawara kan mayar da hankali a kan
nazarin salo domin ƙara
bunƙasa harshen Hausa.
4.
Haka kuma wannan bincike na bayar da
shawara musamman ga ɗalibai da su duƙufa wajen nazarin waƙa domin fito da irin hikimomin da ke
ciki.
5.
Salo abu ne mai faɗin
gaske, don haka wannan kundi na bayar da shawara kan cewa, mai nazarin salo ya
zurfafa wajen nazarin salailai
gwargwadon iyawarsa.
Manazarta
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.