Wannan
aiki ya gudana ne a kan saɓa ƙa’idar rubutun Hausa da aka yi a
cikin tallace tallacen wasu finan Hausa. Rubutun Hausa yana da ƙa’idoji da aka shata da ya kamata a
kiyaye, da su domin ya zama karɓaɓɓe
kuma mai ma’ana. Fahimtar ma’anar abun da aka rubuta kuwa ta ta’allaka ga bin
waɗannan
ƙa’idojin don a inganta rubutu, yanzu
wata kila saboda zamananci da kasala tare da son burgewa ya sa ‘yan fim suka ɗauki
wani salon amfani da haruffan da babu su a harshen Hausa, wani lokaci kuma
haruffan Hausa ne amma ba a bin ƙa’ida
ta haɗawa
da...
________________________
Saɓa Ƙa’idar Rubutun Hausa A Cikin Tallace-Tallacen Wasu Fina-Finan Hausa
NA
MUBARAK
MURTALA
_______________________
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan aiki ga iyayena
Alhaji Murtala Abubakar Baƙo da Hajiya Safara’u Hamisu da yaya ta
Farida Murtala da ƙanne na. Da fatar Allah ya saka musu
da mafificin alhairinsa. Amin
GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga
Allah Maɗaukakin
Sarki mai rahama mai jinkai, Allah ya daɗa
tsira da amanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) da alayensa gaba ɗaya.
Bayan
haka kuma, ina ƙara
jaddada godiya ta ga Allah (S.W.T) wanda cikin ikonsa da yardarsa ne na sami
damar yin wannan binciki a kan saɓa
ƙa’idar rubutun Hausa a cikin
tallace-tallacen wasu fina-finan Hausa.
Ina
miƙa godiya ta musamman ga Malam Nazir
Ibrahim Abbas wanda shi ne ya duba wannan aiki nawa.
Bayan
haka ina miƙa kyakkyawar godiya ta ga Dr. Umar
Bunza a kan taimakon da ya ba ni. Haka kuma ina miƙa godiya ta musamman ga Dr. Ibrahim
Abdullahi Sarkin Sudan wanda a ƙarƙashin Jagorancinsa na shugaban sashe
(H.O.D) mun sami ingantaccen horo, a matsayin ɗalibai
masu nazarin harshen Hausa.
Kuma
ina ƙara miƙa
godiya ta ga ‘yan uwana ɗalibai musamman Abubakar
Macciɗo
da Abdulullahi Hussaini Idris da Mardiya Umar da Umar Shehu waɗanda
su ka taimaka matuƙa
wajen ganin wannan aiki ya samu nasara. Haka ma ina miƙa godiya ga abokaina musamman Auwal
Sani da Aliyu Yahuza Kiliya da Musa Yahuza Kiliya da Abbas Ya’u Kagara da
Mansur Yahuza Kiliya da Sadik Sanusi Hussaini da Mubarak Abubakar wanɗan
da sun taimaka wurin wannan aiki ya
kamala. Da fatar Allah ya sa ka musu da mafificin alherinsa.
Daga
ƙarshe ina miƙa godiya ta ga dukkan malamai na sashen
Koyar da Harsunan Najeriya.
BABI NA ƊAYA:
GABATARWA
1.0 SHIMFIƊA
Wannan
aiki ya gudana ne a kan saɓa ƙa’idar rubutun Hausa da aka yi a
cikin tallace tallacen wasu finan Hausa. Rubutun Hausa yana da ƙa’idoji da aka shata da ya kamata a
kiyaye, da su domin ya zama karɓaɓɓe
kuma mai ma’ana. Fahimtar ma’anar abun da aka rubuta kuwa ta ta’allaka ga bin
waɗannan
ƙa’idojin don a inganta rubutu, yanzu
wata kila saboda zamananci da kasala tare da son burgewa ya sa ‘yan fim suka ɗauki
wani salon amfani da haruffan da babu su a harshen Hausa, wani lokaci kuma
haruffan Hausa ne amma ba a bin ƙa’ida
ta haɗawa
da rabawa kamar yadda yake a tsarin ƙa’idojin
rubutun Hausa.
Ana
samun irin waɗannan kura-kurai musamman a cikin
tallace tallacen wasu fina finan Hausa wanda mafi yawa masu amfani da su matasa
ne saboda suna ganin rashin issashen muhallin rubutu da lokaci ke kawo haka.
Cigaba da yin hakan babban illa ne ga harshen Hausa, wannan bincike zai zaƙulo irin-irin wannan saɓa
ƙa’idojin da nufin gyara kura-kuran da
ake yi.
Wannan binciki zai gudana ne a cikin babi
biyar. Babi na ɗaya ya ƙunshi shimfiɗa da bitar ayyunkan da suka gabata da manufar
bincike, hujjar cigaba da bincike da hanyoyin gudanar da bincike da farfajiyar
bincike da kuma Naɗewa.
Babi
na biyu ya ƙunshi shimfiɗa
da ma’anar fim da rabe- raben fina-finan Hausa da Ma’anar talla da yadda ake
gudanar da tallace-tallacen fina-finan
Hausa.
Babi
na uku ya kawo Tarihin rubutun Hausa, da sauye-sauyen ƙa’idojin
rubutun Hausa da muhimmancin ƙa’idojin
rubutun Hausa da Naɗewa.
Babi
na huɗu
ya ƙunshi shimfiɗa
da amfani da babban baƙi
in da bai dace ba, da amfani da baƙaƙen da ba na Hausa ba da ingausa a
wajen rubutun Hausa, da amfani da alamomin rubutu ba bisa ƙa’ida ba da naɗewa.
Babi
na biyar ya ƙunshi taƙaitawa da kammalawa.
1.1BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
An gudamar da ayyuka da yawa waɗanda
suke da kama da wannan aika wasu daga
cikin waɗannan ayyukan da na ci
karo da sun haɗa
da: Amfani (2010) a muƙalarsa
mai taken “Hausa internet Terms” shi ma ya buƙaci
a faɗaɗa
kalmomin Hausa a internet ta hanyar fassara su.
Bambanci sa da nawa aiki shi ne zai yi
bayani akan saɓa ƙa’idar
rubutun Hausa a cikin tallace-tallacen wasu fina-finai.
Bello (2010) a kundin digirinsua na farko mai
taken “Keɓantaccen nazari a kan haɗa
kalma da rabata a Hausa” Shi ma ya yi aiki sosai a kan ƙa’idar rubutun Hausa ta fuskar haɗe
gaba da in da ake rabata.
Kiyawa
(2013) maƙalarsa
da ya gabatar a taron ƙasa
da ƙasa wanda hukumar a dana tarihi da
raya al’adu da haɗin guiwar Jami’ar Umaru
Musa yar’ aduwa Katsina suka shirya mai
taken “Tsokaci a kan fina-finan Hausa”.
Adamu (2011) ya gabatar da
wata maƙala mai taken ‘Gudumuwar fina-finan
Hausa wajen taɓarɓarewa
tarbiya’. A wajen wani taro wanda hukumar adaidaita sahu ta jahar Kano ta
shirya a ɗakin taro na Murtala Muhammad a garin
Kano.
A
cikin takardar ya yi bayani kan taɓarɓarewar
tarbiya da ake samu sanadiyar fina-finan Hausa da kuma hanyar da za a bi domin
magance matsala.
Abubakar (2011) A kundin
digirinsa na farko da ya gabatar a Sashen nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato mai taken: Tasirin fina-finan Hausa a kan al’adun
Hausawa. Ya fito da gurɓa cewar da al’adun
Hausawa suka yi sanadiyar kallon fina finai da kuma nuna illolin da kan iya
faruwa a sanadiyar wannan tasiri nawa ko zai yi bayani ne kan saɓa
ƙa’idar rubutun Hausa a cikin
tallace-tallacen wasu fina finan Hausa.
Gandu
(2012) A kundin digirinsa na biyu da ya gabatar a Sashen koyar da harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, mai taken ‘Tasiri fina-finan
Indiya kan na Hausa”. Ya yi bayani tarihin fina-finai a ƙasar Hausa da yadda fina-finan Indiya
suka yi tasiri a kan na Hausa da kuma dangantakar da ke tsakanin fina-finan Indiya da na Hausa .
Ni ko nawa aiki zai yi bayani ne kan saɓa
ƙa’idar rubutu Hausa a cikin tallace
-tallacen wasu fina-finan Hausa. Duk waɗannan
ayyuka da na yi bita suna da alaƙa
da aiki na domin sun danganci fina-finai sai dai sun banbanta, domin ni zanyi
nazari kan saɓa ka’idar rubutun Hausa a cikin
tallace-tallacen wasu fina-finan Hausa.
Duk waɗannan ayyuka da na yi bita suna da
alaƙa da aiki na domin sun danganci
fina-finai sai dai sun banbanta, domin ni zan yi nazari kan saɓa
ƙa’idar rubutun Hausa a cikin tallacen
tallacen-tallacen wasu fina finan Hausa a kan wasu matsalolin fina- finan
Hausa. wajen ɓata tarbiya ya yi tsokaci kan irin
rawar da fina-finan Hausa suke takawa wajen gurɓata
tarbiyar yara maza da mata a wannan zamani. Nawa aikan kuma zai yi Magana ne
akan saɓa
ƙa’idar rubutun Hausa a cikin tallace
–tallacen wasu fina-finan Hausa.
Chamo (2013) Muƙalar
sa da ya gabatar a taron ƙarawa
juna sani na ƙasa da ƙasa Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya
ta Jami’ar Bayaro Kano, mai taken “Language and Globalization: eɗpression
of Loɓe
in Hausa Society and its representations in Hausa film.” Ya yi bayani yadda
‘yan wasan fim na Hausa suka ɗauko al’adun wasu mutanen
waje (ya wanci daga fina- finan indiya) suka zo da su da sabbin dubaru kuma
suna aiwatar dasu a ƙoƙarin bayyana soyayyar Hausa a
fina-finan.
Bambanci da alƙara aikin sa da nawa aikin shi ne nawa zai yi
bayani a kan saɓa
ƙa’idar rubutun Hausa a cikin tallace
–tallacen wasu fina- finan Hausa.
Duk waɗannan ayyuka da na yi bita suna da
alaƙa
da aiki na domin su na magana
akan ƙa’idojin
rubutun Hausa da nazari akan fina-finai, sai dai sun banbanta domin ni zanyi
nazari akan saɓa ƙa’idar
rubutun Hausa da aka yi wurin gudanar da tallace-tallacen wasu fina-finan
Hausa.
1.2
MANUFAR BINCIKE
Manufar wannan bincike shi ne jawo hankali musanman Hausawa domin su
gano cewa wannan ɗabi’ar rubutu da suka ɗauko
a wajan gudanar da taken tallace- tallacensu ba ƙa’idar
rubutu ba ce da aka aminta da ita ba kuma tuna da illa wajen sauya
daidaitacciyar hanyar rubuntun Hausa. Haka kuma akwai manufar su gano karan
tsaye ne suke yiwa harshen Hausa wannan aiki zai taimaka ga waɗanda
ba Hausawa ba su tantance haruffa da kalmomin da babu su a harshen Hausa ,
Saboda
su kiyaye amfani da su ya yin rubutu, bugu da ƙari
zai taimaka wajen banbancewa tsakanin in da ya kamata a raba kalma da haɗa kalma da farawa da babban baƙi ko karamin baƙi a wajen rubutu.
1.3 HUJJAR CI GABA DA BINCIKE
An gudanar da ayyuka da ya
wa masu alaƙa da wannan aiki
kuma babu wani aiki irinsa shi yasa na gaya dace in gudanar da wannan bincike
nawa mai taken saɓa ƙa’idar rubutun Hausa a cikin
tallace-tallacen wasu fina-finan Hausa.
1.4 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE
Daga cikin hanyoyin da na bi wajen
gudanar da wannan bincike sun haɗa
da shiga ɗakin
karatu domin nazarin muƙalu da littafai da kundaye da suka yi
nazari kan ayyukan da suka shafi: saɓa
ka’idar rubutu da fina-finai da kuma yan
fim , haka kuma na tattara wasu fina-finai da na kalla domin nazarin saɓa
ka’idar rubutu da ke cikin su fina-finan sun haɗa
da Ranar Aure da Kalan dangi da burin duniya, da mijin yarinya da Mansur da ɓarayin
zamani da ɗan bazawa da aminai da Farmaki da Yusra da amaryar mahaukaci.
1.5 FARFAJIYAR BINCIKE
Wannan bincike ne akan saɓa
ka’idar rubutu a cikin tallace-tallacen wasu fina-finan Hausa, dukkan binciken
zai gudana ne kan fina-finan Hausa na kannywood kawai, aikin zai ta’allaƙa ne kawai ga saɓa
ka’idar rubutun Hausa a cikin fina-finai musamman a wajen harkokin shirya
fina-finai da kuma tallace-tallace su.
1.6 NAƊEWA
Wannan babi na ɗaya
shi ne gabatar wa wanda ya ƙunshi
duk wata gabatar wa ta wannan binciken babin ya kawo bitar ayyukkan da suka
gabata da manufar binciken da hujjah ci gaba da bincike da hanyoyin gudanar da
bincike da kuma farfajiyar bincike.
BABI
NA BIYU : TAƘAITACCEN
TARIHIN FINA-FINAI DA TALLACE-TALLACE
2.0 SHIMFIƊA
Babi na biyu ya kawo ma’anar fim da rabe-raben fina-finan Hausa da
ma’anar talla , da yadda ake gudanar da
taken tallace-tallacen fina-finai Hausa.
2.1 MA’ANAR FIM
Fim kalma ce ta turanci wato (film) da take nufin ‘jerantuwar hotuna masu motsi waɗanda
a ka ɗauka
tare da sauti domin bayyana wani labari a kan allon talabijin ko sinima ko
majigi ko wurin nuna shirye-shirye’. Fassarar (adɓanced
learner’s dictionary 2005, 7th edition).
Ahmad (2002) ya bayyana ma’anar cewa ‘fim wata hanya ce ta faɗakar
da alumma ana amfani da fim domin ilmantar da mutane a kan wani abu da ya shige
musu duhu ko kuma da ake son suji ko su ɗauka’’.
Usman (2007) ya bayar da ma’anar fim da cewa; wata
hanya ce da ɗan adam yake amfani da ita domin
samun nishaɗi da raha da annashuwa da kuma gusar
da ɓacin
rai ko wata damuwa da ke tare da shi, tare da kwaikwayon halaye na gari da kuma
guje wa halaye marasa ƙyau.
La’akari da waɗannan
ma’anoni muna iya cewa; fim wata hanya ce ta sanya rayuwa cikin raha da nishaɗi
da annashuwa don kawar da wata damuwa tare da cusa ko isar da saƙo ga mai kallo’’.
2.2 RABE-RABEN FINA-FINAN HAUSA
Masu
shirya fina-finai Hausa sun kasu zuwa gida biyu kamar haka:
i.
‘yan fim ɗin
sentimental’
ii.
‘yan fim ɗin
camamsa’
wadannan
sune kasha-kashe ko rabe-raben fina-finai
Hausa .
i.
Sentimental wani rukuni ne na al’umma masu
shirya fina-finan Hausa na zamani,musamman fina-finan soyayya domin faɗakar
da al’umma da nishaɗantar da su da kuma
gargadi. Suna ɗaukar tsawon lokaci kamin su haɗa
fim guda. Wasu daga cikin yan fim ɗin
sentimental sun haɗa da: Ali Nuhu da, Adam
A. Zango da Sadik Ahamad da Sani Musa Danja da Yakubu Muhammad da Sha’aibu
Lawal da Nafisa Abdullahi da, Rahama Sadau da Aisha Aliyu Tsamiya da, Fati
Washa da, Jamila Nagudu da dai sauransu. Duk da yake wani lokaci kana iya samun
ɗaya
daga cikin su a fim ɗin camama.
ii.
Camama wani rukuni ne al’umma da ke shirya fina-finan Hausa na barkwanci da ban
dariya domin nishaɗantar da al’umma da ban
dariya da sanya su cikin farin ciki da annashuwa. Mafi yawan fina-finansu na
gargajiya ne domin nuna tantagaryar al’adar hausawa. Ba su cika daɗewa
ba wajen shirya fina-finan su domin bai kai wahalar na sentimental ba. Daga
cikin waɗanda
suke yi fice wajen fim ɗin camama sun haɗa
da:Rabilu Musa (Dan Ibro) da Katakore da Bawa Mai Kanwa da Wanzam da Hankaka da
Husaina Tsigai da Ladi Tubulas da Mai Aya da Daushe da Moɗa
da dai sauransu. Duk da yake suma wani lokaci suna yin fim ɗin
sentimental to amma anfi saninsu a fim ɗan
camama.
Dukkansu suna a cikin masana’anta wadda
suka sama suna (kannywood) ita wannan masana’anta da’yan sentimental da’yan
camama duk cikinta suke tare suke gudanar da al’amurransu na shirya fina-finai,
suna da kamfunna daban-daban da suka haɗa
da FKD da ABNUR da 2 EFFECT da ZANGO MOƁIES da BARUMI
MOƁIES, MJ ƁIDIO ENTERTAIMENT da MAI
SANA’A ENTERTAIMENT da KOMO PRODUCTION
2.3
MA’ANAR TALLA
Gillian Dyer (1982) ya bayyana ma’anar talla da cewa talla wata hanya ce
ta jawo hankalin mutane zuwa ga wani abu wanda akan haɗa da ƙarin gishirin don kara inganta abin .
Bagudu (2005) ya bayyana talla da cewa ‘daɗaɗɗiyar
hanya ce da al’umma ke amfani da ita donsu bayyana ko kuma su isarda saƙo
zuwa ga jama’a ta amfani da hausar da za ta ‘iya jan hankalin jama’a su saye ko
su yarda da wata haja ko manufa, haka kuma yace Kalmar talla wata abu ce da aka
daɗe anayi a bakunan mutane jama,a maza da mata manya da yara amma
kuma ba kowa Zai iya bayarda cikakkiyar ma’anar ta ba sai mutumin da keda
Ilimin Kasuwanci na saye da sayarwa da kuma sanin manufofi;
INUSA
(2007) yace’’ Talla na ɗauke
da ma’anar guntayen zantuka da ake wa Kwalliya da nau’oin adon harshe,don jawo hankali da cusa ra’ayi
ga mutane kan wani al’amari na aiki ko ra’ayi ko shawara ko haja da dai sauransu”.
TAMBURAWA
(2008) Shi ma tasa fahimta ya bayyana talla da cewa,talla wata hanya ce
sassauka mai arha wadda ake bi don sayarda kaya ga jama’a ko masu bukata.
YOLA
(2008)ya bayyana talla da cewa’’Talla tana nufin yaɗawa ko yekuwa ko sanar wa akan wani abu
ga mutane ta hanyar jawo hankalinsu zuwa ga abin da ake tallatawa.
2.4 YADDA AKE GUDANAR DA TAKEN
TALLACE-TALLACEN FINA-FINAI
Akwai
Hanyoyi da dama da ake amfani dasu wajan gudanar da tallace-tallace.
i.
Ana
gudanar da tallar fim farkon wani fim na daban
ii. Ana gudanar da talla a tsakiyar fim
iii. Ana gudanarda tallar wani sabon fim a
karshen wani fim
A cikin fim ɗin Ga GiDA-GA GIDA an yi tallar fim ɗin ‘’Burin
Duniya’’
a ciki kamar haka
Kamfani; A B ZANGO MOƁIE
Shiryawa; Yusuf KHALID
Ba da Umurni: ISAH UMAR (TURAKIN KANGO)
Sunan
fim;
BILKEESU- A Mai makon Bilkisu
Shiryawa; Adamu Amart a maimakon Amat
Cigaban
shiri; Yakubu A.I.K
Ba da labari ; Aisha Tijjani
Mataimakin Mai ba da Umurni: Ahmad A.
Bifa
Umurni Kamal S. Alkali
Kamfanin: MIA INTERPRICE
KAUYAWA 2017 – MAIMAKON ƘAUYAWA
Kamfani: mai shadda Inɓestiment NIG LTD
Labari Falalu A Dorayi – A maimako Ɗorayi
Tsara labari: maje el Hajij hotoro
A mataimakin mai bada umarni: Bello
Shatima
SHIR yawa: Muhammad Bashir Mai Shadda a
maimakon shiryawa
Ɗau
kar nauyi: Sani Haruna mai makon ɗaukar
Bada umarni: Sadiƙ M Mafiya maimakon sadik
2.5 NAƊEWA
Wannan
babi na biyu mai taken “Takaitaccen Tarihin Fina-Finai da tallace-tallace” ya
kawo ma’anar fim da rabe-raben fina finan Hausa da ma’anar talla da yadda ake
gudanarda taken tallace-tallacen fina-finai Hausa.
BABI NA UKU:- RUBUTUN HAUSA DA ƘA’IDOJINSA
3.0 SHIMFIƊA
A
wannan babi za a yi bayani a kan ƙa’idojin rubutun Hausa daga tarihin
rubutun Hausa da yadda ake yinsa da sauye- sauye ƙa’idojin rubutun Hausa da kuma
muhimmancin kiyaye ƙa’idojin rubutun Hausa.
3.1
TARIHIN RUBUTUN HAUSA
Tarihi
ya nuna cewa wani bature mai suna J.F Schon ne ya fara rubutun Hausa a
littafinsa mai suna “Magana Hausa” amma bai san karin harshen Hausa ba don haka
ba a yi zama kan ƙa’idojin rubutun ba don haka ba a damu ba. Bayan shi an rubuta wani
littafi mai suna “Dictionary na Abram da Bargery, duk lokacin babu amintaccen
tsarin rubutun Hausa irin na yau.
A shekarar (1955) wani ɗan
majalisar wakilai ta arewacin Najeriya da ke Kaduna daga Bauchi Bawa Bulkacuwa
ya kawo kuduri a majalisar don samarda hukuma mai kula da rubutun Hausa, “hausa
Language Board” wadda daga baya ta koma “centre for the study of Nigerian
Language”
A (1960-2000) an samu gyare-gyaren da suka kai ga samar da daidaitaccen
tsarin rubutun Hausa (standard Hausa
Orthography) ko da ya ke an rubutu
abubuwa masu kama da ƙaidojin, masali a shekara ta 1912 Hanns
Ɓischer
Dan Hausa ya ba da dokokin wasulla a littafinsa “ Rules for Hausa Spelling. A
1938 Gwamnati ta amince da amfani da haruffa masu lanƙwasa kamar haka /ɓ/ɗ/ƙ/. mai makon ɗago a ƙasa
/b/ɗ/ƙ/
kamar yadda ya zo a lamba ta 396 na
kundin da aka tattara dokokin Najeriya (Nigerian Gazette)
A
shekarar (1966) ƙungiyar O.A.U ta ɗauki nauyin wani babban taro a kan ƙa’idojin
rubutun Hausa a Bamako (Mali) duk da nufin samar da ƙa’idar
rubutun Hausa, an kuma yi wani a Jami’ar Ahmadu Bello a shekara ta 1970
A
shekara ta 1972 cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayaro ta yi taron ƙarawa
juna sani a kan ƙa’idojin rubutu, wanda bisa amincewarsa ne M.K.M Galadanci a matsayinsa
na sakataren taron ya tattara matsayar har ya buga littafin sa mai suna “An
induction to Hausa Grammar a (1976)
wanda a ciki ya sa ƙa’idojin rubutu (Authograph) amma ya
tabbatar cewa wannan yarjejeniyar malamai ce.
Bugu
da ƙari
Gwamnatin Ƙasar Najeriya da kuma jamhuriyar Nijar sun shiryar taro ta
sakamokon daidaita ƙa’idar rubutun Hausa a (1980) mai taken Najeriya / Niger Hausa
Authography”. Haka ma a wani lokaci an yi wani taro mai taken “History of Africa CELTHO”. O. A U, In da aka shekara 12 wajen fassara a ƙarshe
Jami’ar Ahmadu Bello Uniɓersity
Zaria ta buga shi.
Amfani
(2004) ya kawo bayani akan yarjejeniyar shekarar dubu ɗaya da ɗari
tara da talatin da takwas akan amfani da haruffa masu kugiya.
Wannan
taƙaitaccen
tarihin ƙa’idojin
rubutun ta, to bai kamata yau saboda zamani ya zo da kafar sadarwa ba, a riƙa
saɓa ƙa’idojin haka kawai ba.
A
ƙarshe
(2011) wasu manyan cibiyoyi watau “ Centre for the Black and Africa Arts Ciɓilazation”
(CBAAC) da “ Centre for Adɓance Study of African Society (CASAS) sun yi taruka
a gabascin Afrika harsunan Hausa da Igbo da yaruba da Ijaw. Suka tattara ƙa’idojin rubutun domin nazarinsu, suka kuma samar da wani kundi mai
suna: A unfied standard Orthography for the Hausa Language Nigeria, Niger,
Cameroon,Ghana & chad monograph series No: 241.
3.2
SAUYE - SAUYEN ƘA’IDOJIN
RUBUTUN HAUSA
A
shekarar 1950 hukumar NORLA ta buga wani littafi mai suna “HAUSA SPELLING” da
kuma gyare-gyaren da hukumar Hausa ta yi wanda aka buga mallakar Gwamnati mai
lamba (396) “Nigerian Gazet 24-03-1958” wannan ya sa mutane ba su cigaba da
rubutu barkatai ba, wasu su na haɗe wasu kalmomin wajen rubutu kuma wasu
su na raba kalmomin waɗannan
sauye-sauyen baƙaƙe daban-daban.
Wannan matsala ta sa aka yi taruka
daban-daban har karo (3) uku domin gyara da kuma samar da hanya wajen ƙa’idojin
rubutun Hausa.Taron farko anyi shi ne ta bai ɗaya a kasar Mali, taro nas biyu kuma an
yi shi ne a Jami’ar Ahmadu Bello Uniɓersity Zaria a
shekarar 1970, taro na uku kuwa ya gudana a bayero Uniɓersity Kano a cikin 09- 1972.
Ga kaɗan da ga cikin cigaban da aka samu a
sauye- sauye ƙa’idojin rubutu.
NAU’IN GYARA
|
TSOHUWAR HANYA
|
SABUWAR HANYA
|
1.
kalmomin gama gari ko jam’u
|
Ko ina
Ko mai
Ko wacce
Ko wane
Kowaɗanne
|
Ko’ina
Komai
Kowace
Kowane
Kowanne
|
2. lamirin lokaci
|
Zaka
Nake
Ya na
Ta na
Su na
Mu na
|
Za ka
Na ke
Yana
Tana
Suna
Muna
|
3. Shadda ko ɗauri
|
Gyagygyara
Sakwkwato
Gwagwgwada
Shashshafa
Shashshare
|
Gyaggyara
Sakkwato
Gwaggwada
Shasshafa
Shasshare
|
4. kalmomi masu Amsa kama
|
Mutun
Malan
Kullun
Jingin
Sukutun
Kundun
|
Mutum
Malam
Kullum
Jingim
Sukutum
Kundum
|
5A. Baƙaƙen Nasaba
|
Sarkim maƙarfi
Sarkim fada
Akwatim fata
Sarkim baka
|
Sarkin maƙarfi
Sarkin fada
Akwatin fata
Sarkin baka
|
5B. Baƙaƙen Mallaka
|
Akwatim Musa
Gonammu
Gidammu
Matammu
Rigammu
|
Akwatin Musa
Gonarmu
Gidanmu
Matanmu
Rigarmu
|
6. Fi’ili
|
Ya kan
Ta kan
Ku kan
Ki kan
A kan
|
Yakan
Takan
Kukan
Kikan
Akan
|
7. karan Dauri
|
Faɗi tashi
Kwan gaba
Bar ni da mugu
|
Faɗi-tashi
Kwan-gaba
Bar-ni-da-mugu
|
8. Gajeriyar Kalmar Mallaka
|
Doki na
Rigar sa
Zanen ta
|
Dokina
Rigarsa
Zanenta
|
3.3
MUHIMMANCIN ƘA’IDOJIN
RUBUTUN HAUSA
Shi yahaifar da ƙoƙarin da malamai
da kuma hukumomi daban-daban ne suka yi taruka domin daidaita rubutun
Hausa a tarihi kamar yadda ake kawo a sashe na 3.1 na wannan babin.
Babu shakka ayyukan malaman Hausa da suka gabatar
da kuma tarihin da hukumomin suke yi sune suka samar da tsarin rubutu na
daidaitacciyar Hausa wanda ake amfani da shi a yau.
Ƙa’idojin
rubutun kuwa suna taimakawa wajen daidaita rubutu na bai ɗaya
tsakanin al’umma kuma sune suka ɗaukaka
harshen Hausa a kasance mai tsarin rubutu na bai ɗaya
da ake amfani dashi a makarantu, da kafofin watsa labarai
(Jaridun Mujalla, gidan radiyo da talabajin ) da wajen rubuce- rubaucen adabi
da wasu harkokin da suka danganci hukumci.
Bugu da ƙari ƙai’dojin
suna taimakawa wajen sauƙaƙa karatun abun da aka rubuta da kuma
fahimtar shi ga mai karatu.
Hasali
ma samun dadaitaccen tsarin rubutu,ƙa’idojin
rubutu wani ma’auni ne da ake kimanta daraja ko ɗaukakar
harshe tsakanin harsuna a idon masana harsuna. Sabo da haka ƙa’idojin rubutu suna da matuƙar muhimmanci ga cigaba da bunƙasar harshe, babu shakka a harshen
Hausa ya taimaka wajen samun.
Daidaitacciyar
Hausa tare da sautukan baƙaƙe 34 da kuma sautukan wasulla goma
sha uku 13, sautukan baƙaƙen Hausa kuwa sune:
/b/
da /ɓ/
da / m/ da /F/ da /fy/ da /t/ da /d/ da/ɗ/
da /i/ da/r/da/n/da/n/ da/n/ da/s/da/z/ da/ts/da / r/ da/ sh/ da /c/ da /j/
da/y/ da/k/ da/ky/da / kw/ da /ƙ/
da/ƙw/ da/g/ da /gy/ da /gw/ da /w/ da
/h/ da /‘/ da /‘y/
Yayin
da a sautukan wasullan Hausa tare da gajerun wasulla 5, ne a,i,o,u,e, da
dogayen wasulla biyar ne aa, ii,uu,oo,ee,da kuma tagwayen wasullan ai da au da
iren, wi duk rubutu Hausa ana yinsu ne da waɗannan
baƙaƙen
ko wasullan a tsarin Daidaitacciyar
Hausa.
A
fina finan Hausa ana samun saɓanin harshe a cikin tallace-tallacen fina-finai
domin kuwa suna amfani da wasu sautukan baƙaƙen da ba na Hausa ba.
Musamman
wajen rubuta sunayen taurari fina-finai, wasu da wani bincike.
3.4 NAƊEWA
Wannan babi na uku mai
taken “Rubutun Hausa da ƙa’idojin
sa” ya tattauna tarihin samuwar rubutun
Hausa da yadda masana suka fito da daidaitaccen rubutun Hausa, Bugu da ƙari babin ya kawo sauye-sauyen ƙa’idojin rubutun da kuma muhimmancin ƙa’idojin rubutun Hausa.
BABI NA HUƊU: SAƁA
ƘA’IDAR RUBUTUN HAUSA A CIKIN TALLAR
WASU FINA- FINAN HAUSA.
4.0 SHIMFIƊA
Duk
da cewa a babi na ukku mai taken rubutun Hausa da ƙa’idojinsa wannan babi na huɗu
mai taken saɓa ƙa’idar
rubutun a cikin tallace- tallacen wasu fina-finan Hausa, ya kawo amfani da
baban baƙi in da bai dace ba da amfani da baƙaƙen
daba na Hausa ba, da ingausa a wajen rubutun Hausa da amfani da alamomin rubutu ba bisa ƙa’ida ba Hausa.
4.1 AMFANI DA BABBAN BAƘI IN DA BAI DACE BA.
A
ƙoƙarin
yin nazari na kallon wasu fana-finai da aka kalla zan kawo wuraren da aka saɓa
ƙa’idar rubutun Hausa ta amfani da
babban baƙi in da bai dace
ba.
Akwai fina-finai da aka
kalla na Hausa waɗanda aka sami irin wannan
saɓa
ƙa’idojin rubutun Hausa a taken
tallace-tallacen su fina-finan kuwa shi ne kamar haka:-
Duk da cewa fina-finan
sun kasu kasha biyu akwai fina-finai sentimental da camama.
FINA-FINAI CAMAMA
Sunan
Fim: Kauyawa 2017
Kamfani:
Mai Shadda Inɓestiment
Furoduusa:
Abubakar Bashir Mai Shadda
Darakta:
Kamal S Alkali
A cikin fim an yi amfani da babban baƙi sai kuma aka idar da ƙaramin baƙi. Misali:
KUSKURE GYARA
*TSAra
labari Tsara
labari
*SHIRyawa Shiryawa
*ƊAUkar nauyi Ɗaukar nauyi
*BAda
umurni Ba
da umurni
Sunan
Fim: Mijin Yarinya
Kamfani:
Mai Kwai Moɓies
Furodusa:
Abdulmuminu Tantiri
Darakta:
Abdulmuminu Tantiri
KUSKURE GYARA
*BaDA
umurni Ba da Umurni
*LaBARi Labari
*ƊauKar Hoto Ɗaukar
Hoto
Sunan
FIm: Ruwan Dare
Kamfani:
Yamsa Multimedia
Furodusa:
Yasin Auwal
Darakta:
Yasin Auwal
KUSKURE GYARA
*TSAra
labari Tsara
labara
*SHIRyawa Shiryawa
*ƊAUkar nauyi Ɗaukar nauyi
*BAda
umurni Ba
da umurni
Sunan
Fim: Babban Yaro
Kamfani:
Prince Zango
Furodusa:
Falalu A Ɗorayi
Darakta:
Adam A Zango
KUSKURE GYARA
*ADam
A. Zango Adam A
Zango
*TIjjAni
Asase Tijjani Asase
*BAda
UMURni Bada Umurni
*ShirYAwa
shiryawa
FINA-FINAI SENTIMENTAL
Sunan
Fim:Mai Farin Jinni
Kamfani:
F K D production
Darakta:
Yakubu Muhammad
Furodusa:
Mal Aminu Saira
KUSKURE GYARA
*WaKA Waƙa
*ALi
Nuhu Ali
Nuhu
*MAImuna Maimuna
*SuTUra Sutura
*HAske Haske
Sunan
Fim: Ranar Aure
Kamfani:
M.J Moɓies
Furodusa:
Yakubu Usman
Darakta:
Falau A Ɗorayi
KUSKURE GYARA
*Ranar
aure Ranar
Aure
Sunan
Fim: Kalan Dangi
Kamfani:
Tsamiya
Inɓestiment
*Furodusa:
Abubakar Bashir Maishadda
Darakta:
Ali Gumzak
KUSKURE GYARA
*Maishadda Mai
Shadda
*DAUkar
Nauyi Ɗaukar Nauyi
*
TSAra labara Tsara
Labari
4.1.2 AMFANI DA BAƘAƘEN
DA BA NA HAUSA BA
Daidaitacciyar Hausa akwai haruffan da aka
aminta da su da waɗanda ba a aminta da su
ba, Masana sun yi bayanin ayyuka daban-daban.
A daidaitacciyar Hausa
tana da sautukan baƙaƙe 34 da kuma sautukan wasulla goma
sha uku, sautukan baƙaƙen Hausa kuwa Su ne: /b/ da /ɓ/
da / m/ da /F/ da /fy/ da /t/ da /d/ da /ɗ/
da da /r/ da /n/ da /n/ da /n/ da /s/ da
/z/ da /ts/ da / r/ da /sh/ da /c/ da /j/ da /y/ da /k/ da /ky/ da / kw/ da /ƙ/ da /ƙw/
da /g/ da /gy/ da /gw/ da /w/ da /h/ da /‘/ da /‘y/.
Yayin da a sautukan
wasullan Hausa tare da gajerun wasulla 5, ne /a/ /i/ /o/ /u/ /e/ da dogayen
wasulla biyar ne /aa/ /ii/ /uu/ /oo/ /ee/ da kuma tagwayen wasullan ai da au da
/ui/. Duk rubutu Hausa ana yinsa ne da waɗannan
baƙaƙen
ko wasullan a tsarin Daidaitacciyar
Hausa.
A
fina-finai Hausa ana samun saɓanin harshe a cikin
tallace-tallacen fina-finai domin kuwa suna amfani da wasu sautukan baƙaƙen
da ba na Hausa ba.
Musamman
wajen rubuta sunayen taurarin fina- finai wasu misallan da wannan bincike ya
samo a fina-finan kamar haka:-
Sunayen
Fina-Finai su ne
Bilkisu
Kalna
Dangi
Mijin
Yarinya
Mansur
Mariya
Sabon
Dan Tijara
KUSKURE N SUNAYEN ‘YAN WASA
KUSKURE GYARA
*Ɗainab
Zainab
*Ƙasim
kasim
*Bunɗa Bunza
*Phatima Fatima
*Ishaƙ Ishak
*Baseeru Basiru
*Ɗuwaira Zuwaira
*Ummee Ummi
*Bilkeesu Bilkisu
*Mubaraƙ Mubarak
*Ruƙayya Rukayya
*Faruƙ Faruk
*Mustpha Mustafa
*Parida
Farida
*Sadiƙ Sadik
*Naɗeefa Nazifa
A taƙaice haruffan da harshen Hausa ya
aminta da ayi rubutu da su, su ne wajibi domin kaucewa saɓa ƙa’idar rubutun Hausa, wanda ba shakka
karantsaye ne ga Hausa da rubutun hausa baki ɗaya.
4.1.3
INGAUSA A WAJEN RUBUTUN HAUSA
Ingausa
na nufin haɗa
wani harshe da wani a lokacin Magana. Misali haɗa harshen Ingilishi da Hausa
Ingausa
wata Magana ce wadda ake haɗa
turanci da hausa, ya ba da ma’ana ga
wanda duk ake mu’amalar da shi.
Ingausa
wata Magana ce wadda ake haɗa
Hausa. Da turanci kuma ta ba da ma’ana.
A
cikin wasu fina-fanin Hausa a kan samu irin wannan ingausa a tsakanin mutane
biyu ko fiye a cikin fina-finai Hausa. Ga wasu daga cikin misallan ingausa
kamar haka:-
MISALIN
INGAUSA DAGA FIM ƊIN SENTIMENTAL
Sunan Fim: Mai Kyau
Kamfani: ABNUR
Furodusa: Abdul Amad Mai Kwashewa
Darakta: Sadik M Mafia
Misali kamar hirar da ta wakana a tsakanin Ali Nuhu da budurwarsa:
*Kina da ɓalue a wurin shi
*Haba Baby na
*To ba ni One Minute Kacal
*Haba ki rage yin fushi mana baby
Sai sauran wurare da aka samu irin wannan ingausar a cikin wannan fim ɗin:
*One Million kawai nake so
*To kina da Account ɗina?
*Sady baby ta shi ki buɗe
*Yau za mu sha party wurin nan
*Anty Lubnat
*Tana prision
*Ai kana da account number
*Bani ni Two Fifty
*Ke ‘yar Gold
*Sai dai in ba da appointment
MISALIN
INGAUSA DAGA FIM ƊIN CAMAMA
Sunan Fim: Ruwan Dare
Kamfani: Yamsa Multimedia
Furodusa: Yasin Auwal
Daracta: Yasin Auwal
An samu ingausa a tsakanin Aminu Sharif da abokinsa Sadik Sani Sadik a
lokacin da suka je wurin fira tare da Rahama Sadau. Misali:
*O Raliya long time
*Ka ga Credit ɗina ne zai ɗan ɗare
*Dady na bai nan
*Sai neɗt week zai dawo
*No Turkey ke nan
Sai kuma wasu wurare da aka sake samun irin
wannan ingausar a cikin wannnan fim ɗin mai suna Ruwan Dare. Misali
*Irinku ne ku ke ciwa Degree Mutunci
*Aikin Gandiroba Shi ma ka Raina shi
*Wow! Wow! Maintain mana
*Da a yi aure na ba Dinner ba Picnic,
to wallahi da in yi aure a haka gwamma in mutu ban yi aure ba.
4.1.4 AMFANI DA ALAMOMIN RUBUTU BA BI SA ƘA’IDA BA
Amfani da alamomin rubutu a fina-finan Hausa
duk da cewa a fina finan Hausa ba’a cika amfani da alamomin rubutu ba, amma an
samu wasu kaɗan
daga cikin alamomin rubutu a fina-finan Hausa.
Alamomin
rubutu wasu abubuwa ne da ke gudana tsakanin kalmomin mai rubutu irin waɗannan alamomi kamar rini suke a cikin
rubutu watau da zarar an raba su,to rubutu ba zai yi armashi ba wani lokaci ma
ya kasa karantawa, alamomin rubutu suna taimakawa wajen fitar da ma’anar abin
da mai rubutu ke nufi sosai.
Misali,
1.
Aya
(.) Aya wata alama ce mai nuna Magana ta cika sosai ko inda jimla ta ciki tare
da ma’ana mai fa’ida don haka duk Magana da za ta biyo baya ta zama sabuwa,
haka kuma, dole duk harafin da zai biyo bayan aya ya zama babban baƙi. Misalin Aya,
*kasa mu wuri ka zauna mana.
2.
Waƙafi
(,) wannnan kishiyar aya ne aya na nufin
dakatawa gaba ɗaya.
Waƙafi
kuma ya na nufin ɗan
hutawa na ƙaramin lokaci domin gyara murya, wannan alama na nuna ba a
kai karshen Magana ba, amma yana dama ya ɗan dakata amma a kada ta tsawaita da
katawar kuma bakin da za a tashi dashi ya zama ƙaramin baƙi.
3.
Waƙafi
mai Ruwa (;)wannan ita ma wata alamace mainuna tsagaitawa, watau a ɗan nunfasa, kuma harafin da zai biyo
baya a rubuta shi da ƙaramin baƙi. Misali
*sannu samira,
Bismillah shigo ki zauna.
4.
Alamar
Tambaya (?) duk wurin da ake da ita wurin tambaya ne dole ne kuma alamar
tambaya ta kasance a karshen tambaya. Baƙin da zai biyo baya ana rubutashi da
babban baƙi. Wannan yana faruwa ne duk locacin da aka yi tambaya.
Misali, miko kun san inda samira taje?.
5.
Baka
biyu [()] A rubutun Hausa ana sanya wani zance a cikin baka biyu, to duk zancen
da aka sanya a cikin baka biyu to ba dole sai an karanta shi ba. Ana amfani
dashi ne domin ƙarin bayani a kan abin da ake Magana a
kai. Haka kuma, ana amfani da baka biyu wurin bada ma’anar wani harshe ko karin
harshe. Misali
(Kunɗin mota daga Kano zuwa Kaduna 1000).
6.
Ayar
Motsin Rai (!) Ana yin alamar motsin rai ne domin a nuna alamar tsoro ko shan
wahala ko fushi ko farin ciki da sauransu. dazarar ana yi amfani da alamar
motsin rai abin da zai biyo baya dole a rubuta shi da babban baƙi.
Haka a lura ana amfani da wannan alama da dama kamar haka:
·
Kai!
·
Ihu!
Hushi: Haka
·
Wuce!
·
Maza!
Murna:
Madalla
·
Yauwa!
·
Allahu
Akbar!
Alamar motsin rai matsayin aya take,
saboda haka duk hukunce-hukuncen aya sun faɗa mata.
4.2
NAƊEWA
Wannan
babi na huɗu ya tattauna a kan amfani da babban
baƙi in da bai dace ba da amfani da baƙaƙen
da ba na Hausa ba da ingausa a wajen rubutun Hausa da amfani da alamomin rubutu
ba busa ƙa’ida ba.
BABI NA BIYAR: TAƘAITAWA DA KAMMALAWA
5. O SHIMFIƊA
Wannan babi mai taken taƙaitawa da kammalwa ya ƙunshi taƙaitawa duk kan wannan bincike da a ka
gabatar.
5.
1 TAƘAITAWA
Wannan
bincike mai taken saɓa
ƙa’idojjin rubutun Hausa a cikin
tallace-tallacen wasu fina-finan Hausa
ya gudana a cikin babi biyar. Babi na ɗaya
ya ƙunshi gabatarwa mai ɗauke
da bitar ayyukkan da suka gabata da manufar bincike da hujjar ci gaba da
bincike da hanyoyin gudanar da bincike da kuma farfajiyar bincike
Babi na biyu ya kawo ma’anar fim da
kuma rabe-raben fina-finan Hausa da
ma.anar talla da kuma yadda ake gudanar
da taken tallace-tallacen fina-finan Hausa.
Babi na uku ya tattara tarihin rubutun Hausa da sauye-sauyen ƙa’idojin rubutun Hausa da kuma
muhimmancin ƙa’idojin rubutun
Hausa.
Babi na huɗu
ya yi bayani kan saɓa ƙa’idojin rubutun Hausa a cikin
tallace-tallacen wasu fina-finai da suka haɗa
da amfani da babban baƙi in da
bai dace ba,da amfani da baƙaƙen da ba na Hausa ba,da ingausa a
wajen rubutun Hausa ,da rashin amfani da alamomin rubutu.
Babi na biyar shi ne taƙaitawa da jawabin kammalawar aikin.
5.2
KAMMALAWA
Wannan aiki mai take “saɓa
ƙa’idar rubutun Hausa a cikin tallace-tallacen
wasu fina-finan Hausa” ya fito da tarihin fim da bunƙasar da ke akwai tsakanin al’ummar
Hausawa da fina-finan Hausa. Haka ma mun fahimci cewa ‘yan fim sun kasu gida
biyu wato ‘yan fim ɗin camama da ‘yan fim
sentimental,kuma duk kansu suna ƙarƙashin masana’antar “kannywood” mai
hedikwata a garin Kano.
Da yadda dukkan waɗannan
bincike ‘yan fim ke saɓa ƙa’idojin rubutun Hausa a cikin
tallace-tallacen fina –finan. Saɓa
ƙa’idojin rubutun fim ya danganci
wannan binciken zai fitar cewa za su yi ƙoƙarin gyara irin wannan kura-kuran a
nan gaba.gyara irin wannan kura-kuran babu shakka zai taimaka wajen bunƙasa Harshen Hausa ta hanya kiyaye ƙai’dar da daidaitaccen tsarin rubutun
harshen da aka tanada.
5.3
NAƊEWA
Wannan
babi na biyar Shi ne na ƙashe wanda ya kawo kammalawa da taƙaitawa.
MANAZARTA
1 Comments
Aiki yayi kyau Allah yakara fasaha. Yakamata masana'antar Fim taga wannan sakon.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.