Ticker

    Loading......

Gudummawar Harshe da Al’ada Ga Bunƙasa Tattalin Arziƙi Da Zaman Lafiya Da kuma Ci gaban Al’umma Mai Ɗorewa


Waiwayen tarihin irin rawar da harshe da al’ada suke takawa ga ci gaba mai ɗorewa, lamari ne da aka ayyana shekarun 1980 da kuma farkon 1990 a matsayin wani zango na baiwa mutane dama ta bayar da gudummawarsu a wajen ayyukan ci gaban al’umma. Taron duniya na Meɗico a 1992...

_____________________________________
Daga
Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
syakasai2013@gmail.com
(+234) 08035073537
_____________________________________
1.0 Gabatarwa
Waiwayen tarihin irin rawar da harshe da al’ada suke takawa ga ci gaba mai ɗorewa, lamari ne da aka ayyana shekarun 1980 da kuma farkon 1990 a matsayin wani zango na baiwa mutane dama ta bayar da gudummawarsu a wajen ayyukan ci gaban al’umma. Taron duniya na Meɗico a 1992 akan matsayin harshe da al’ada, ya jaddada nasarar samuwar ci gaban al’umma domin amfanin kansu. Da tafiya ta yi tafiya, sai hukumar raya ilimi da kimiyya da kuma al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ƙaddamar da bukin shekara goma (1988-1998) na ci gaban harshe da al’ada a duniya. Sakamakon wannan gangami ne ya haifar da tanadin wasu ma’aunai na ci gaban rayuwar al’ummar duniya. A shekara ta 1990 kuma sai hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ta yi amfani da waɗancan ma’aunai ta wallafa rahoton irin ci gaban da ake samu. Haka dai lamarin ya ci gaba inda a shekarun (1992 -1996), hukumar inganta harshe da al’ada da kuma ci gaban al’umma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya rahoto akan yadda za a faɗaɗa ƙumshiyar al’adun al’umma. 

Nan take taron ƙarawa juna ilimi na gwamnatocin ƙasashe da aka yi a Stockholm a 1998 ya amince da yalwata hurumin harshe da al’ada ga ci gaban al’umma. Daga nan  kuma sai wani taron ƙarawa juna ilimi na haɗin gwiwa tsakanin hukumar UNESCO da Bankin Duniya a 1999 akan matsayin al’ada ga bunƙasa tattalin arziƙi. Sai kuma a 2001 da hukumar UNESCO ta ayyana harshe da al’ada a matsayin ƙashin bayan tattalin arziƙi da zamantakewar al’umma. Da shekara ta 2005 ta zo sai UNESCO ta tanadi matakai na kariya da na bunƙasa harshe da al’ada domin ci gaba mai ɗorewa. A wannan maƙala za mu yi tsokaci ne dangane da gudummawar harshe da al’ada ga bunƙasa tattalin arziƙi da zaman lafiya da kuma ci gaba mai ɗorewa. A sashe na farko da na ƙarshe, jawabin gabatarwa da kuma na kammalawa ne. Sashe na biyu ya kalli irin dangantakar da ke akwai ne tsakanin harshe da al’ada. Daga nan kuma sai sashe na uku inda muka kalli harshe da al’ada a matsayin madubin al’umma. A sashe na huɗu kuma muka taskace irin rawar da harshe da al’ada suke takawa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da kuma kawo zaman lafiya mai ɗorewa ga al’umma.

2.0 Dangantakar Harshe da Al’ada

Kalmar dangantaka na iya ɗaukar ma’anoni kamar alaƙa da zamantakewa da ƙawance a tsakanin abubuwa biyu ko fiye. Saboda haka, ta ɓangaren deangantaka, muhimmancin harshe da al’ada ga rayuwar al’umma ba abu ne ɓoyayye ba. Trudgil (1974), wani masanin ilimin walwalar harshe ya bayyana ƙwararan ayyukan harshe da al’ada guda biyu: (a) na farko shi ne sadarwa ko isar da saƙo ta bayar da bayani (b) na biyu kuma shi ne tabbatar da alaƙa da dangantaka tsakanin jama’a. Ita dangantaka tana wanzuwa ne a tsakanin ɗaiɗaiku da kuma tsakanin al’umma. Shi kuwa harshe shi ne hanyar furta ma’anoni da tunane-tunanen da suke ran ɗan’Adam. Wato dai ita ce hanyar sadarwa tsakanin mutane. Ita wannan hanya kuma ba ganinta ake yi ba, jinta ake yi kawai, wato hanyar sadarwa ta ɗan’Adam (harshe) saututtuka ne masu ma’ana da ake furta su, kunnen mai sauraro ya ji, kana basirarsu ta kama ta fahimta domin amfaninsa. Ita kuma al’ada ɗabi’a ce da ɗan’Adam yake ɗaukar wa ransa, har a ƙarshe kuma ya riƙa ganin ta zame masa tilas (Gadanya, 1977). 

Hasali ma, ai kowace al’umma ta duniya tana da nata al’adu waɗamnda take ganin su ne mafi kyau ga duk sauran al’adun duniya. Wato dai yadda ‘yan-Adam suka bambanta ta kowane fanni, haka ma suka bambanta ta fannin al’adu. Saboda haka, abu ne mawuyaci ka ga al’ummu guda biyu suna da al’adu iri ɗaya, sai dai akan samu kamanceceniya, amma kuma harshe ne babban ginshiƙin gina kowace  al’ada. Manazarta al’ada daga fannoni daban-daban kamar addini da kuma kimiyar kiwon lafiya suna kallon al’ada gwargwadon mizanin darussan nazarinsu. A fannin walwala musammanm ma cikin dangantaka da harshe, ana iya kallon al’ada ta hanyoyi biyu. Hanya ta farko tana iya nufin dukkan abubuwan da suka shafi ci gaban basirar ɗan’Adam. Hanya ta biyu kuma (wadda masana kimiyar rayuwar ɗan’Adam na ƙarni na ashirin suka fi ƙarfafawa) ita ce ta kallon al’ada a matsayin jimillar dukkan ilimi tare da hanyoyin cuɗanyar yau da kullum na kowace al’umma (Nelson, 1960). 


Idan muka ɗauki gundarin abin da waɗannan bayanai ke nunawa, sai mu ga cewa nuni suke yi da cewa al’ada dai kamar ita ce rumbun dukkanin tunne-tunane da falsafa da basira da kuma dukkan sauran ginshiƙan rayuwar ɗan’Adam (cf. Salim, 1985). Kenan idan aka yi la’akari da dangantakar da ke tsakanin harshe da al’ada, to sai a ga harshe a nan ya tashi a matsayin ƙofar shiga da fita (wato ajiyewa da ɗaukowa) daga cikin wannan rumbu. Wato dai ta wannan hanya ce kawai za mu san me ke cikin rumbun. Wannan shi ne ya sa cewa, da wuya a iya ware harshe daga al’ada. Haka kuma shi ne kaɗai mafi muhimmanci daga cikin dukkanin hanyoyin bayyanawa, da kuma gane sauran ginshiƙan al’adar kowace al’umma (Lado, 1964). Saboda haka, dangantakar harshe da al’ada dangantaka ce  irin ta jini da tsoka. Wato yin nazarin harshe ba zai yi wu ba sai tare da sanin al’adar da wannan harshe ya ɗamfaru gare ta. Rayuwar mutum ita ke shirya masa dukkan halayen zamansa a garinsa da kuma garin wasu. Hasali ma, har da irin abin da zai ce idan ya tashi yin magana da mutanen gida da waje. Ita wannan magana tana ginuwa ne a kan rayuwa gaba ɗayanta domin ita ce ma ke shiryawa mutum yadda yake magana da yara da tsara da mahaifa da kuma shugabanni. Harshe ba shi da alaƙa da mutum, wato ba wai haihuwar mutum a awuri ke sa ya ji harshen su mutanen wurin ba, sai dai idan ya tashi da amfani da shi. Saboda haka, duk wanda ya tashi da wani harshe, to lallai harshen zai koya. Jinin mutum ba ya da alaƙa da harshensa, domin sai a samu Baturen Ingila yana Larabci, ko kuwa Bafaranshe yana Hausa. Kenan furucin mutum ba ya nuna ƙabilarsa, domin furuci ba manunin ƙabila ne ba sai dai idan mutum ya faɗi ƙabilarsa, tun da duk inda mutum ya tashi, furucinsu zai koya ya kuma iya. Sai dai kuma furuci yana nuna matsayin mutum da iliminsa, amma ba asali da jini ba. An kuma yi amanna da cewa Bahaushe zai yi Hausa, Balarabe kuwa ya yi Larabci, Bafillace zai yi Fillanci da dai sauransu, amma ba dole ba ne.

3.0 Harshe da Al’ada a Matsayin Madubin Al’umma
Al’umma ita ce tarin ɗaiɗaikun mutane da suke zaune a gari guda ko yanki ko lardi ko jiha ko kuma ƙasa. Al’umma tana iya ƙunsar ƙabilu daban-daban. Wannan ya nuna cewa duk inda aka sami  fiye da ɗan’Adam guda a wuri guda, to lalurar hulɗa da mu’amala ta kama. Hulɗa da mu’amala kuwa basa cika ba tare da magana ba. Kenan amfani da harshe da al’ada tilas ne a hulɗa, kuma lalura ce. Tun da yake haka ne kuwa, to bukatar harshe da al’ada ga ɗan’Adam ta kai ƙarfin bukatarsa ga abinci da ruwa, ko ma watakila har da iskar shaƙa (Rufa’i, 1986).
Ta hanyar harshe, ana iya samun hasken tarihin al’umma. Wato ta harshen al’umma ne akan iya gane ci gabanta musamman dangane da tsarin mulki ko shugabanci da sharia da ilimi da tattalin arziƙi da addini da kuma al’ada. Sauran maganar kuma ita ce, idan aka yi dace cewa al’ummar tana da hanyar rubutu, to ta rubuce-rubucensu za a ga gacin da suka kai domin a ci gaba. Idan kuma babu hanyar rubutu, to ta hikimarsu ne kawai za a iya ganewa cikin mu’amala da su. Ta adabin al’umma ma ana iya gane irin ƙwazonsu cikin tarihi. Ta nan ne wayonsu zai bayyana da kuma ƙoƙarinsu na kyautata rayuwarsu da irin gudummawar da suka bayar wajen ci gaban al’umma. Domin ƙara tantance dangantakar harshe da al’ada, da kuma yadda sakamako ko kuma tasirin wannan dangantaka ke zama matsayin madubin al’umma, bari mu ɗan yi nazarin jigogin rayuwar al’umma. Amfani ko kuma fa’idar yin nazarin shi ne fito da bayanan dangantakar a tsakaninsu. Da yake sadarwa tsakanin al’umma lalura ce wajiba, bukatun rayuwa za su matsa wa ‘yan wata ƙabila su yi hulɗa ko mu’amala da ‘yan wata ƙabula daban. Hakan ya zama dole domin ita hulɗa ko mu’amala ba ta yiwuwa sai fa ta amfani da harshe cikin dangantaka da al’ada. A taƙaice dai idan ana magana a kan matsayin harshe da al’ada na madubin al’umma, to wajibi ne batutuwa irin su koyar da harshe da ilimantarwa da tattalin arziƙi da tsarin zamantakewa da kuma nishaɗantarwa su bijiro.

4.0 Nazarin Jigogin Rayuwa
Da yake al’umma ta ƙunshi ɗaiɗaiku, to ashe al’umma aba ce rayayyiya wacce take da farko da halin rayuwa da kuma ƙarshe, ko kuma a cikin hikima a iya cewa al’umma tana da jiya, tana da yau kuma tana da gobe. A ra’ayin Rufa’i (1986), idan aka juya ta wata hanya, to muna iya cewa al’umma tana da tarihi, kuma a cikin wannan halin wanzuwar tana yaƙin rayuwa. Bugu da ƙari kuma, tana faman tabbatar da kyawawan abin da zai je ya zo. Wannan ya nuna cewa al’umma kamar tilon ɗan’Adam tana da alfahari da kuma buri. Alfaharin nan shi ne tarihi, buri kuwa shi ne kokawar rayuwa domin yau da kullum. Saboda haka, a fafutuka ta wanzuwa, akwai bukatar abubuwan nan da suka zama dole ga kowace al’umma domin rayuwa. Waɗannan abubuwa su ne: mulki da sharia da tattalin arziƙi da ilimi da addini da kuma al’ada.
Tsarin mulki a cikin kowace al’umma wajibi ne. Mulki shi ne kaɗai zai tabbatar da zaman lafiya yadda kowa zai sami damar yin harkokinsa na yau da kullum domin neman abinci da arziƙin duniya. Wato idan babu mulki a al’umma, to ruɗani da yamutsi da hargitsi da kuma cutar juna ne za su tabbata. Idan haka ya auku, sai al’umma ta kai ga halaka domin babu wanda zai sami sukunin neman abinci ballantana arziƙin ƙasa. Domin a sami cikakkiyar lumana da tabbatar da zaman lafiya, ya wajaba a sami fahimtar juna tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka. Mafi yawan kyawun hanyar fahimtar ita ce harshe wanda muka ce shi ne jigon sadarwa. Ga misali, kafin zuwan Tuarawa ƙasar Hausa, mutane ne daga cikinmu suke mulkin ƙasarmu. Wato harshenmu ɗaya da su, kuma duk hanyoyin rayuwa ɗaya ne tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka. Don haka, sadarwa take da sauƙi, wanda hakan ya tabbatar da bin umurni da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali. Daga nan Nasara ya ƙwace mulki, amma kuma harshenmu da na nasara ba ɗaya ba ne. Don haka sadarwa tsakaninsa a matsayinsa na mai mulki, da, mu a matsayin waɗanda ake mulka sai ta wuyata. Gaskiyar maganar ita ce, a yayin da aka rasa sadarwa tsakanin mai mulki da kuma wanda ake mulka, to babu yadda shi wanda ake mulka ɗin zai sami damar sa baki a yadda ake mulkin nasa. Sauran maganar ita ce, zuwan Baturen ne dai ya kawo mana tsarin mulki na siyasa wanda hasken saninsa yana cikin harshen da ba namu ba. Haka kuma Bature ya bar mana gadon tsarin mulki wanda a kan rubuta shi da harshen da ba na ‘yan ƙasa ba ne. Kasa fahimtar waɗannan abubuwa ya kawo matsala. Bayan tsarin mulki, kowace al’umma ba za ta gaza bukatar tsarin Sharia ba, da yadda za a tabbatar da adalci a mulki. To a nan ma harshe yana da rawar da za a gani. Wajibi ne ga jama’a su fahimci irin shariar da ake yi a ƙasarsu domin su tabbatar wa kansu adalci idan rigima ta same su. 

Mafi kyawun fahimta ita ce abu ya zama da harshen mutum ake yinsa, idan ba haka ba to wasu abubuwa za su shige duhu. Tun kafin zuwan Turawa, a ƙasar Hausa ana amfani da shari’ar Musulunci ne. Wannan tsari na sharia a cikin Larabci yake, wanda ba kowa da kowa ya iya fahimta ba. Don haka da wuya jama’a su san kanta sosai da sosai, musamman ma idan wata matsala ta taso. Da Bature ya zo, shi ma dai ba ta sake zani ba. Ita tasa shariar a cikin Turanci take, ko haifaffen harshen ma sai ya yi famar fahimta tasa, balle kuma ɗan koyo. Duk a waɗannan halaye guda biyu, da wuya mutane da yawa su fahimci nau’in shari’un domin ba a cikin harshensu suke ba, ga shi da wuya koyon baƙon harshe.
Babu shakka ilimi babban jigo ne a rayuwar mutum da al’umma gaba ɗaya. Hasali ma, ai ilimi wata hanya ce wadda mutum yake amfani da ita ya gane abubuwa, ya fahimce su ta yadda zai bunƙasa sulukinsa a rayuwa (Gusau, 2010). Wani mutum, ilimi yakan daidaita tunaninsa ya zama mai tsiwurwurin rayuwa nau’i biyu, wato rayuwa ta duniya da kuma ta lahira. Wani kuma yakan gane sassan rayuwa ne wadda ta shafi duniya, ya zama mahiri, ya tumbatsa wajen samar da ƙololuwar jin daɗinta. Ta haka za a tabbatar da fahimta ita ce ƙashin bayan ilimi wadda za ta yi jagora ga samun jin daɗi ko muni, sannan a iya bambance abubuwa masu baragada ko baragurbi. Haka kuma shuɗewar kwanuka da yau da gobe a rayuwa wani ƙari ne na daraja a ilimi (Bergery, 1934 da kuma Hornby, 1974). Don haka neman ilimi dole ne domin rayuwa ta yi armashi.
A ra’ayin Lepage (1964), a ƙasashe masu tasowa, ilimi mabuɗi ne ga abubuwa guda biyu ƙwarara: (a) mabuɗi ne ga samun abinci. Ta hanyar ilimi ana iya kyautata noma da sana’o’i da fasaha da tattalin arziƙi da sauran abubuwa da suka jiɓinci jin daɗin rayuwa. (b) mabuɗi ne ga kyautata al’adu da haɗa kan jama’a, da samar da manufa ko al’ƙibla guda. Baya ga ilimin addini, ilimin zamani Bature ne ya kawo shi, don haka da harshen Bature ne wannan ilimi yake, duk da cewa ba duka muka taru muka iya Ingilishi ba. Masana sun ce harshen da yaro ya tashi da shi, to ya fi tasiri a kansa wajen gina basira da hankali da wayo da kuma ƙwazonsa. Wannan yanayi ya bambanta da halin da ake ciki, domin muna neman ilimi da baƙon harshe. Haka ƙarin wahala ne domin sai mun iya harshen sosai kafin mu koyi ilimin.
Duk da cewa Hausawa sun naƙalci iya ciniki da safara da tajirci, to amma zuwan Bature ya kawo wani sabon salo dangane da tattalin arziƙi. Da yake babu ƙasar da za ta dogara da kanta kawai, to dole ne kafar hulɗa da mu’amala ta buɗe musamman ma da waɗanda suka ci gaba. Sai dai kuma kash, hasken da ya kamata mu yi amfani da shi yana cikin harshen da ba namu ba. Saboda haka fahimtarmu da su sai an yi ɗamara, musamman da yake ai rashin sanin sirrin tattalin arziƙin ne irin na zamani ya sa aka wawashe dukiyar  ƙasar a shekarun baya. Gaskiyar magana ita ce, idan ba ka fahimci abu ba, babu wuya a ƙware ka a cikinsa. Wato dai idan kana mu’amala da mutum, ya fahimci ba ka naƙalci sirrin abin da kuke mu’amala a kansa ba. to babu wuya a cuce ka. Rashin sanin sirrin tattalin arziki irin na zamani yana da illa, saboda haka babu makawa sai an rungume shi duk da kasancewa cikin baƙon harshe.
Kowace al’umma kan dogara da wani abu a matsayin mai wanzar da rayuwa. A al’umomin da suka waye akwai addinai da suka ƙudurce akwai ubangiji. A nan, addinin Musulunci ya daɗe a ƙasar Hausa, sai dai mafi yawan jama’armu ba su fahimci addinin ba, saboda ba su san ƙa’idojin addinin da iliminsa ba. Hakan ya faru saboda kasancewar ilimin addinin a harshen da ba  namu ba, wato harshen Larabci. Tun da dukkaninmu ba mu iya Larabci ba, to da wuya kowa da kowa ya sami sukunin karanta littattafan addini. Don haka dole ne a dogara ga ‘yan tsirarun mutanen da suka iya Larabci domin koyon addini ta kansu. Sauran maganar ita ce shin ko hakan zai wadatar? To a gaskiya ko da a harkar addini ba a rasa marasa gaskiya, waɗanda za su yi cuta su ribatu da jahilcin mutane. Saboda haka, maslaha ita ce fassare-fassare na littattafan addini zuwa harshenmu domin fahimtar addini sosai.    
Masana sun yi ittifaƙi cewa al’ada ita ce tarin hanyoyin rayuwar jama’a, musamman hikimominsu da fasaharsu da wayewarsu da iliminsu da hulɗoɗinsu da mu’amalarsu da kaɗe-kaɗensu da raye-rayensu da kuma sauran irin su. Kafin zuwan Musuluni ƙasar Hausa, adabin Hausawa na baka ne, wato waƙar baka da tatsuniyoyi da kuma labaru. Zuwan Musuluni ya sa wasu suka san Larabci har suka fitar da ajami a matsayin hanyar rubutu. Ta ɗaya haujin kuwa, zuwan Turawa ya kawo mana iya rubuta Hausa da boko. Harshe shi ne abin furta ra’ayoyi da ma’anonin al’adu, saboda haka, dangntakar da take tsakanin harshe da al’ada ƙaƙƙarfa ce. Wato ƙarfin ya kai babu yadda za ka koyi wani harshe ko ka yi nazarinsa ba tare da ka san al’adar masu harshen da ladabin amfani da shi ba. Ga misali, saboda irin wannan ladabi na amfani da harshe, masana suke cewa koyon harshe da koyar da shi ba zai yiwu ba sai da fahimtar al’adar masu harshen. Tun da yake haka ne kuwa, to ta tabbata kenan cewa akwai dangantaka mai ƙarfi tsakanin harshe da al’ada.
5.0 Kammalawa
Daga abin da ya gabata dangane da matasayi da ƙimar harshe da al’ada, ta tabbata cewa haɗakarsu (wato harshe da al’ada), tana share fagen ci gaban al’umma mai ɗorewa. Da farko dai akwai ɗorewar tsarin zamantakewa, wato da harshe da al’ada ne  ake sarrafa muhimman batutuwan da suka gina tsarin zamantakewar al’umma. Irin waɗannan batutuwa sun haɗa da harshe da addini da ilimi da auratayya da kuma yin sulhu a tsakanin al’umma.
Akwai kuma ilimi na sarrafa tadoji da aka gada tun iyaye da kakanni, da suka haɗa da ilimin noma da tsarin cimaka da kiwon lafiya da rainon yara ƙanana da kayan gine-gine da kuma amfani da sarrafa muhalli. Wannan tsari da aka gada tun iyaye da kakanni, da harshe da al’ada ne ake tafiyar da su, saboda haka duk wani tasiri ma a bisa wannan tsari yake ci gaba da tafiya. Shi tasiri yanayi ne na haɗuwa da baƙin al’adu a sanadiyar hulɗa ko mu’amala tare, daga nan kuma sai kwaikwayo da aro su bijiro a sanadiyar tasiri a kan juna.
Ta haujin al’adun gargajiya ma, da haɗakar harshe da al’ada ne ake sarrafa su. Wato da waɗannan ne (waɗanda sun haɗa da sana’o’i na samun abin ɗawainiyar kai da kuma iyali gaba ɗaya). A gaskiya ma, waɗannan hanyoyi na al’ada, naƙaltarsu ake yi kuma iliminsu na ɗorewa tun daga iyaye daga kakanni. Akwai kuma batun wasu al’adu na musamman, waɗanda al’umma suka ɗauka da matuƙar fa’ida da muhimmanci. Hasali ma, irin waɗannan al’adu na musamman (waɗanda kuma ake sarrafawa da harshe a cikin ma’auni na al’ada) suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar al’umma. Ga misali, ɗauki maganganun hikima da azanci da aka san a harsunan al’umma ne suke ƙumshe da kuma ɗimbin al’adun da suke koyarwa. Akwai adabi (wanda ya ƙumshe zube da waƙa da kuma was an kwaikwayo) da zane-zane da raye-raye da waƙe-waƙe da labarum gargajiya da ayyukan hannu da kuma fina-finai. Bugu da ƙari gudummawar harshe da al’ada ba a baya suke ba, dangane da yaɗa ilimi, musamman ma irin wanda zai haɓaka basira da aiki da basira da hikima ta ƙirƙira da kuma dabarun gina al’umma a matsayinsu na ɗaiɗaiku da kuma a ƙungiyance. Ana kuma tace gurɓatattun tadoji da al’adu, sannan a yi watsi da su domin kada su cutar da al’umma (musamman ma yara manyan gobe). Harshe a matsayinsa na hanyar furuci mai ma’ana, shi ne al’umma ke sarrafawa cikin magana domin isar da  saƙon da ke zukatansu na abin da ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum. 
Kenan tasirin harshe da al’ada ga al’umma tamkar rayuwa ce da ruhinta, wato harshe ba ya wanzuwa sai idan akwai al’ummar da ke amfani da shi. Haka kuma, al’umma ba ta iya gudanar da al’amuran rayuwarta sai ta yi amfani da harshe a cikin dangantaka da al’ada. Ashe kenan ɗaya ba ya yin tasiri sai da ɗayan. A gaba ɗaya dai harshe da al’ada haɗaka ce ta muhimman abubuwa guda biyu da suka zamo kafa wadda ɗaiɗaikun mutane (da kuma ma a ƙungiyance) suke bayyana ƙwazo da hikima da kuma karsashinsu na gina kansu (da al’umarsu). Saboda haka, harshe da al’ada suna daga cikin ɓangarorin ci gaban al’umma mai ɗorewa.
MANAZARTA

Post a Comment

0 Comments