Allah maɗaukakin Sarki
ya halicci mutum, ya kuma hore masa lafiyar da yake amfani da ita wajen
fantamawa a harkokinsa na yau da kullum, shi kuma ke ƙaddara cuta bayan ya tanadi maganinta. Akwai nau’o’in magunguna daban –
daban waɗanda Hausawa suke amfani da su...
Dr. Haruna Umar
Bunguɗu
Ƙibɗau:harunaumarbungudu@gmail.com
Lambar waya: 08065429369
Da
Bashir Aliyu Tsafe
Lambar waya: 08066785802
Tsakure.
Allah maɗaukakin Sarki
ya halicci mutum, ya kuma hore masa lafiyar da yake amfani da ita wajen
fantamawa a harkokinsa na yau da kullum, shi kuma ke ƙaddara cuta bayan ya tanadi maganinta. Akwai nau’o’in magunguna daban –
daban waɗanda Hausawa suke amfani da su, waɗanda ko suka tanada da kansu, ko kuma suka nema daga
wani. Akwai wasu nau’o’in magunguna da Hausawan suke amfani da su tun asali
kafin shigowar addinin Musulunci a ƙasar Hausa waɗanda ga jama’a
suke samunsu, kuma ana aiwatar da su a gargajiyance. Su kuma wasu magungunan
sai bayan shigowar addinin ce aka same su, ko kuma a ce addinin ne ya samar da
su, tare da bayanan yadda ake amfani da su. Wannan takarda ta lura cewa akwai
nason gargajiyar Hausawa a cikin magungun addinin Musuluncin ta hanyoyi da
dama, don haka za ta fito da ire – iren nason gargajiyar a cikinsu. Yaya
magungunan gargajiyar suke? Yaya magungunan addinin Musulunci suke? Yaya hanyar
jirgi ta haɗu da ta mota a waɗannan nau’o’in magunguna? Idan an karanta wannan muƙala za a sami bayanai masu inganci da kwarjini.
1.0
GABATARWA
Allah
(S.W.T) Ya yi halittu daban-daban kuma Shi ke sarrafa komai da kowa da dukkanin
abubuwan halitta masu rai da waɗanda ba su da rai, kamar Mala’iku da Aljannu da
Mutane da sauran dabbobi. Kuma Allah mahalicci
a bisa hikimarsa Ya yi halitta mabambanta ta fuskar launi da kuma ƙabila
(Suratul Hujrat:12).
Kamar yadda
Allah (S.W) Ya yi halittu haka kuma ya ƙagi
cututtuka masu tarin yawa ya watsa su tare da su, kuma ya sanya kowace cuta
tana da magani sai dai mutuwa da tsufa ne kaɗai ba su da magani, kamar yadda
manzon Allah ya faɗa (Bukari
littafi na farko shafi: 602). A dalilin cututtukan da ke addabar mutane tun a
lokacin da aka fara halitta ya sanya su kuma mutane suka duƙufa wajen
neman magani ko magungunan cututtukan da suka dame su, kuma haka ya wanzar da
samun waɗansu daga
cikin mutanen sun ɗauki hidimar
ta kasance abin da suka sa a gaba a zamansu na duniya har ma suka ɗauke ta
hanyar neman abincinsu tun a farkon lokaci har zuwa yau.
1.0.1 Ma’anar
Gargajiyar Bahaushe
Kalmar gargajiya kalma ce da ta samo
asali daga gado ne aka samu gadajje da gargajiya. Kalmar gargajiya ta yi ƙauri
musamman idan aka ce gargajiyar Bahaushe da ke takin saƙa da
kyawawan aƙidun musulunci. (Bunza, 2006)
1.0.2 Ma’anar
Magungunan Gargajiya
Magani wata
hanya ce wadda ake amfani da ita don kuɓutar da rai daga wata cuta ko damuwa
da ya kamu da ita wadda ta dami zuciya ko sassan jikinsa. Duk da cewa ba mai
iya warkar da mutum daga kowace irin cuta sai Allah amma kuma Ya ba da iznin a
nemi magani, don bai halicci cuta ba sai da ya saukar da maganinta. (Bunza,
2006)
Domin haka ne ya sa ake fafitikar
neman magani don ko a sami yin gamon
katar da maganin da ya da ce wajen warkar da cutar da take damun mutum. Haka
kuma kwantar da hankali bisa amfani da maganin da mayar da komai ga Allah yana
taimakawa matuƙa wajen waraka daga cutar jiki ko neman biyan buƙata.
2.0 Asalin
Magani
Abin da
kamar wuya “wai gurguwa da aure nesa” a iya cewa ga yadda magani ya fara
samuwa, domin babu wanda zai bugi ƙirji ya ce
lokaci kaza aka fara samunsa. Wannan ya yi daidai da ra’ayin wani masani Adamu
M.T (1998) inda yake cewa:
“Idan muka juya wajen binciken ta
yadda magani ya samu a duniya, sai mu ga abu ne mai matuƙar wuyar
gaske, domin kuwa tun farkon samuwar mutane a nan bayan ƙasa, suke ta
ƙoƙarin kare
kansu daga cututtuka, ko kuma yin maganinsu gaba ɗaya, malamin ya cigaba da
cewa suna yin hakan ne kuwa ta yin amfani da wasu tsire-tsire ko sihiri ko ƙage-ƙage da dai
makamantansu. Ba a nan ya tsaya ba, ya bayyana muna cewa: ko da masana
magunguna na duniya sun yi matuƙar saɓani wajen
bayanin asalin shi magani da kuma tabbatar da haƙiƙar
samuwarsa, wasu daga cikinsu suna ganin asalin magani shi ne ilhama, wasu suna
ganin mafarki shi ne asalin magani, wasu sun ce haatifi wasu na ganin dabbobi
ne asalin maganin wasu ƙiyasi, wasu
jarrabawa wasu ƙwayoyi wasu kuma addini. (Adamu, M.T. 1998).
Magani ya samo asali ne tun lokacin
da Allah (S.W.T) ya halicci cuta. Manzon Allah Annnabi Muhammad (S.A.W) ya faɗa cewa
kowace cuta tana da magani. Don haka magani ya samo asali tun lokacin da Allah
ya halicci cuta. (Bukhari: 602)
2.1 Addinin
Musulunci
Addinin
musulunci shi ne miƙa wuya ga Allah (SWT) baki ɗaya tare da
kaɗaita shi da
kuma dogaro gare shi da yi masa ɗa’a da kuma tsarkake shi daga
shirka. Addinin Muslunci shi ne addinin da Allah maɗaukakin
sarki ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da shi zuwa ga bayinsa a duniya baki-ɗaya. (Bunza, A. M. 2005)
2.2 Mene
ne Cuta
A harshen
Hausa idan aka ce cuta ana nufin zalunci, domin idan an ce wane ya fara cuta ko
ya iya cuta ko kuma macuci to duk dai ana nufin azzalumi kenan.
A maganance
kuwa, cuta tana nufin rauni da raɗaɗi tare da wahalar da mutum kan gamu
da su a sanadiyar gazawar wata halitta a jiki ko kuma damuwa a zuci. (Adamu, M.
T 1998).
2.3 Nason
Gargajiyar Bahaushe A Cikin Magungunan Muslunci
A nan za a
dubi wasu wurare ne don a ga irin yadda magungunan gargajiya ko hanyoyin amfani
da su suka yi naso a cikin magungunan zamani na addinin Musllunci ne.
2.3.1 Magunguna
A Addinin Musulunci
Addinin
Musulunci ya zo da hanyoyi daban-daban na yin maganin cututtuka don waraka daga
cuta, (Bunza, A. M. 2006). Daga cikinsu akwai wanda za a karanta a tofa a jiki
akwai wanda za a sha a shafa akwai kuma wanda za a yi wanka da ruwan maganin.
Daga cikin ire-iren cututtuka da kuma maganinsu akwai:
2.3.1.1 Sihiri
Sihiri shi
ne a kawar da mutum daga wani tunani na abin da yake so ko kuma a sanya masa ƙyama daga
wani abu da yake amfana da shi (Al’ilaju Birruka Shafi 2-3). Wato dai yin amfani da wata hanya da za a sa wani
abu ya faru ga wani mutum ba tare da ya gani ko an gane shi ba, ba tare da ya
taɓa ko an taɓa masa ba.
Wannan hanya ce ake yin amfani da iskoki don samun biyan buƙata; ta
hanyar binne wani abu ko jefawa a rijiya ko kogi da sauran irin waɗannan
dabarun.
Ana yin sihiri tun kafin shigowar
addinin Musulunci a ƙasar Hausa, kuma akwai hanyoyin da ake bi domin
a warware sihirin a al’adance. Amma da addinin Musuluncin ya shigo sai aka
samar da wasu hanyoyi waɗanda akwai
nason tsofaffin hanyoyin warwarewar na gargajiya a cikinsu. Bari mu dubi yadda
abin ya kasance.
Daga cikin
hanyoyin maganin sihiri da aka samu bayan shigowar addinin Muslunci kamar yadda
ya zo a cikin littafin Al’ilaju Birruka akwai:
i. Karanta Ayoyin ƙarshe na
Suratul Baƙara Da Suratul Ikhlas Da Mu’awwazatain sau uku koma
fiye da haka har tswon kwana uku ko kwana bakwai
ko wata ko ma fiye da haka sai a sami kofin ruwa a tofa a ciki, sa’annan a riƙa ɗebowa da
hannun dama ana shafawa a jiki. Wannan maganin
akwai nason gargajiyar Bahaushe a cikinsa saboda ko da ana yin ƙulumbuttai
ko shingidi-bagidi a tofa ko a shafa ga jiki domin a karya sihiri.
ii. Haka kuma ana yin ƙaho a wurin
da aka ga wata cuta ko ciwo ya bayyana sai
a jaye jinin da ke a wannan ciwon, sa’annan sai a karanta Suratul Ikhlas sau uku a tofa a wurin. Shi ƙaho ana
yinsa tun kafin zuwan addinin muslunci a
ƙasarmu
inda akan janye jinin da ya mutu da shi sai mutum kuma ya sami lafiya, don haka ya zama wani naso
ne da gargajiya ta yi a kan wannan hanyar
da addinin Muslunci ya zo da ita.
iii. Idan ana tunanin an yi wa mutum wani
sihiri ne ko kuma shi ya faɗa cewa an
yi masa sihiri, sai a samu ganyen magarya ɗanye kamar kunne bakwai a daddaƙa shi sai a
samu ruwa a wani ƙaramin bokiti a zuba tare da ganyen magaryar da aka dagdaga a cikin bokiti sai a
karanta waɗannan ayoyin kamar
haka:
1. Ayatul
Kursiyu ƙafa ɗaya
2. Suratul
A’araf Aya ta 117-122
3. Suratul
Yunus Aya ta 79-82
4. Suratul Ɗaha Aya ta 65-70
5. Suratul
Kafirun Ƙafa ɗaya
6. Suratul
Ikhlas Ƙafa ɗaya
7. Suratul
Falaƙ Ƙafa ɗaya
8. Suratul
Nas Ƙafa ɗaya
A lokacin da
ake karanta waɗannan ayoyin
za a yi karatun ne numfashin mai karatun na shiga a cikin ruwan, idan an
kammala sai a ba maras lafiya ya sha kamar sau uku, sai kuma a wanke jikin
maras lafiyar da sauran ruwan. Za a ci gaba da yi wa maras lafiya haka har
tsawon kwana uku ko kwana bakwai ko wata ɗaya (Imam Sa’id Aliyu bn
Rahman:Addu’a Al’ilaju Birruka).
A gargajiyar
Bahaushe za a yi ƙoƙari a gano
inda ake tunanin an bizne wani abu sai a je a tono shi a warware abin da aka
biznen, sai mai ciwo zai warke. Haka kuma wata hanyar ita ce wadda za a yi hayaƙi domin
kiranye ga wanda ya yi sihirin don ya warware shi, ko kuma a yi turare wanda
mai ciwon zai yi tari a ƙalla sau uku sai ya faɗi sunan
wanda ya yi masa sihirin da kansa. Haka kuma akan yi wa marar lafiya mai wannan
sifar wanka da ruwan magani ko a fesa masa ko ma a shafa masa don a warware
sihirin da aka yi masa. A wannan zamani kuwa an samu nason gargajiyar Bahaushe
a cikin maganin addinin musulunci domin Bahaushe na da wannan hanya ta maganin
ko waraware sihiri tun kafin addinin musulunci, sai kuma addinin ya tanadi a
gudanar da irin wannan maganin ta irin wannan hanyar. (…..)
2.3.1.2 Maganin
Zazzaɓi
Mai Zafi
Zazzaɓi ciwo ne da
ke shigar mutum ta wasu dalilai da dama waɗanda suka zama sanadiyar samuwar
zazzaɓin. Manzon
Allah (S A W) ya ce zafin zazzaɓi yana daga cikin numfashin jahannama don haka ku sanyaya shi da ruwa (Sa’id Aliyu
bn Rahman:138). Don haka idan mutum yana fama da rashin lafiya ta zazzaɓi mai zafi
sai a yi masa wanka da ruwa ko kuma a jiƙa wani ƙyalle da
ruwa a riƙa goggogawa a jiki, mai zazzaɓin zai samu
sauƙin
ciwon in Allah ya so. A gargajiyar Bahaushe idan zazzaɓin ya yi
zafi ana samun sayyun sanga-sanga a dafa watau a tafasa su sai a yi wa mai fama
da ciwon zazzaɓi suraci
idan aka yi haka a ƙalla sau biyu ga yini har kwana bakwai za a samu
sauƙin
ciwon cikin lokaci. Da wannan an samu nason gargajiyar Bahaushe a cikin maganin
addinin musulunci.
2.3.1.3 Maganin Basir
Basir ciwo ne da ke faruwa a dalilin
bushewar ciki wanda hakan kan haddasa kashin jini ko na majina ko fitowar
dubura daga jikin mai fama da ciwon basir. Idan haka ta faru ga wani, Manzon
Allah (SAW) ya ce a samu zira’in Akuya a dafa a yi romonsa a ci, a kuma shanye
romon za a samu sauƙin ciwon basir/ɗankanoma. (Za’adul Ma’ad
shafi 521). Haka ma a gargajiyar Bahaushe akwai hanyoyi da ake bi don samun
waraka ga ciwon basir, ana amfani da saƙe-saƙin iccen maɗaci a jiƙa a sha ko
kuma a daka bedi a sha, haka kuma akwai ɓawon Hano da shi ma za a jiƙa a sha, waɗannan duk
hanyoyi ne da ake amfani da su a gargajiyar Bahaushe tun kafin zuwan musulunci,
don haka wannan ya yi naso ga magungunan da addinin musulunci ya zo da su a
wannan cuta.
2.3.1.4 Ciwon
Ido
Manzon Allah (SAW) ya ce a shafa
kwallin ismit yana maganin ciwon ido. (Musnad Ahmad hadisi na 7934) Kuma yana ƙara kariya
daga ciwon ido ko dundunin ido (wato gani garaye-garaye). Haka kuma ana amfani
da ruwan zuma a yi kwalli da ita a ƙalla sau uku
ga yini yana maganin ciwon ido. A gargajiyar Bahaushe ana shafa kwalli domin a
yi kwalliya tun kafin zuwan addinin musulunci, haka kuma ana amfani da shafin
kwalli wajen maganin tsuna ko ma ciwon idon. Wannan ya yi naso matuƙa ga yanayin
maganin ciwon ido da addinin Muslunci ya zo da shi wanda aka yi bayaninsa a
sama.
2.3.1.5 Ciwon
Naƙuda
Ciwon naƙuda ciwo ne
da ke zo ma mace musamman a lokacin da ta zo haihuwa. A lokacin da Maryam ta zo
haihuwar Annabi Isah (A.S) sai Allah Ya albarkaceta ta hanyar yi mata ishara ta
bakin ɗanta cewa ta
ci dabino domin rage raɗaɗin haihuwa.
Don haka idan mace na da ciki musamman ta kusa haihuwa ana so ta riƙa cin dabino
za ta samu sauƙin raɗaɗi a lokacin da ta zo haihuwa, ke nan
dabino magani ne mai rage zafi da raɗaɗi a lokacin haihuwa. (Haƙƙul mubin:
hadisi na 831) A gargajiyar Bahaushe a kan yi amfani da sayyu da saƙe-saƙi a jiƙa a ba mai
naƙuda
ta sha don samun sauƙin naƙuda tun
kafin zuwan addinin musulunci. Ke nan wannan hanya ta jiƙe-jiƙe ta yi
tasiri matuƙa a wajen ciwon naƙuda da
addinin musulunci ya zo da ita.
2.3.1.6 Ciwon Da Ya Shafi Ƙoda
Da Anta Ko Wata Cuta Da Ta Shafi Ciwon Ciki
Ciwon ƙoda da Hanta
ciwo ne da ke addabar al’umma musamman a wannan lokaci don haka addinin
musulunci ya zo da hanyoyi na waraka daga irin wannan cuta, daga cikin irin
wannan hanya akwai. Za a samu dabino a ƙalla bakwai
mai kyau a wanke shi da ruwa mai tsafta a ci da safe da kuma yamma. Za a yi
haka sau da yawa har lokacin da ake ganin an samu waraka. (Du’a Ilaju bir ruƙa hadisi na
107). A gargajiyar Bahaushe akwai hanyoyi da ake bi musamman waɗanda za a jiƙa sayyun ɗoruwa da na Bagaruwa a jiƙa su tsawon
kwana uku, idan an tabbatar da cewa sun jiƙa sai a ba
maras lafiya ya sha, wannan hanya ce da ake amfani da ita a gargajiya tun kafin
bayyanar addinin musulunci kuma ko da ya zo bai sa aka bar amfani da ita ba sai
dai kawai hanyar da ya zo da ita, (Bunza, A. M. 2005).
Kammalawa
A wannan
takarda, an bayyana magungunan addinin Muslunci ne da yadda gargajiyar Hausawa
ta yi naso wajen aiwatar da shi. Akwai wasu magungunan da addinin musluncin ƙara tabbatar
da su kawai ya yi, kamar irin na basir da sauran irinsa. Wasu magungunan kuwa
hanyoyin aiwatar da su ne suka ɗauki samfurin na gargajiyar Hausa, kenan dai
gargajiyar ta yi naso cikin magungunan addinin Muslunci.
MANAZARTA
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.