Nazarin hikimomin al’adun Hausawa da harshensu kullum sai ƙara bunƙasa yake yi saboda irin ƙoƙarin da masana da ɗaliban
Hausa ke yi na rayar da su. Adabi kuwa, rumbu ne da
ake hango rayuwar kowace irin al’umma da iri-iren abubuwan da take cuɗanya
da su a rayuwarta. Saboda haka, dangantaka tsakanin al’ada da adabi, aba ce mai
ƙarfin
gaske, tamkar harshe ne da haƙori. Masana sun tabbatar da cewa al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki, kuma hulɗar, ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin
addininsu na gargajiya. Maƙasudin wannan muƙala shi ne hango wani babban gurbi a cikin al’adar Bahaushe, wato yadda iskoki suka mamaye tunanin Bahaushe, har
aka wayi gari, da wuya ya faɗi, ko ya rubuta, wata
fasaha ko hikima, ba tare da ya saka iskoki a ciki ba. Hasali ma, saka iskokin
shi ke haskaka fasahar da ya rubuta, kamar yadda littafin Ruwan Bagaja zai
tabbatar.
Yakubu Aliyu Gobir
Tsakure
Nazarin hikimomin al’adun Hausawa da harshensu kullum
sai ƙara bunƙasa yake yi
saboda irin ƙoƙarin da masana da ɗaliban Hausa
ke yi na rayar da su. Adabi kuwa,
rumbu ne da ake hango rayuwar kowace irin al’umma da iri-iren abubuwan da take
cuɗanya da su a
rayuwarta. Saboda haka, dangantaka tsakanin al’ada da adabi, aba ce mai ƙarfin gaske, tamkar harshe ne da haƙori. Masana
sun tabbatar da cewa al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki, kuma hulɗar, ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin
addininsu na gargajiya. Maƙasudin wannan muƙala shi ne hango wani
babban gurbi a cikin al’adar Bahaushe, wato yadda iskoki suka mamaye tunanin Bahaushe, har
aka wayi gari, da wuya ya faɗi, ko ya rubuta, wata
fasaha ko hikima, ba tare da ya saka iskoki a ciki ba. Hasali ma, saka iskokin
shi ke haskaka fasahar da ya rubuta, kamar yadda littafin Ruwan Bagaja zai
tabbatar.
Gabatarwa
Masana al’ada da tarihi na ganin,
hikima da tunanin mutane da ke bayyana a adabinsu na baka, da rubutacce wata
fitila ce, ta ƙyallaro
al’adun rayuwarsu da yadda suke more mata. Saboda haka, dangantaka tsakanin
al’ada da adabi, aba ce mai ƙarfin
gaske, kamar harshe ne da haƙori.
Nazarin al’ada cikin adabi ko adabi cikin al’ada abu ne da masana tuni suka
hange shi (Abdullahi 2000). Maƙasudin
wannan takarda shi ne, fito da wani babban gurbi a cikin al’adar Bahaushe, wato
iskoki a matsayin babban tubali wajen gina ƙagaggen labarin littafin Ruwan Bagaja. Ƙagaggen
labari wani nau’in rubutaccen adabin Hausa ne da ya haɓaka bayan zuwan Turawan
mulkin mallaka, a sanadiyyar kafa wasu hukumomin samar da littattafan karatun
Hausa a makarantun boko. Duk da yake, muƙalar a kan ƙagaggen labari ne, da gangan ta kauce wa, duba tarihin ƙagaggun labarai da nau’o’insu, saboda sun gabata a
wasu ayyuka (Yahaya, 1988 da Malumfashi, 2006/2009/2010/2011 da Bakura, 2011 da
Adamu, 2013). Da farko, muƙalar
ta fayyace ma’anar fitillun kalmomin
matashiyarta domin share fagen nazarin.
Iskoki a Tunanin Hausawa
‘Iskoki’, kalma ce
mai nuna jam’i na ‘iska’, wadda ƙamusoshin Hausa zuwa Hausa, suka ba ta ma’ana kamar haka: Ƙamusun Hausa na
Jami’ar Bayero, Kano, ya ba ta ma’anar ‘Mutanen ɓoye’. Shi kuwa Calvin Y.
Garba[1], ya ba ta ma’anar ‘Rahwani, musamman na bori’. Waɗannan
ƙamusoshi sun bayar da
ma’anar iska ne a matsayin kalma kawai, ba ma’ana ta ilimi ba. Bisa ga haka, ga
abin da masana ke cewa:
Iskoki a wajen Bahaushe wasu halittu ne masu kama da mutane ta fuskar
halittarsu, da surarsu, da ayyukkansu, da al’adunsu, da ɗabi’unsu, da
harshensu, da siyasar rayuwarsu, da dai makamantansu. (Bunza, 2006:1)
A
nan, Bunza yana son ya tabbatar da imanin Bahaushe dangane da iskoki cewa, su ma halittu ne kamar mutane. Masu
ayyuka da sunaye irin na mutane. Duk da yake ba mutane ba ne, za a iya fahintar
haka tun daga irin sunayen da yake kiran su da shi. Misali, Bahaushe ya kira su
‘iskoki’ ne domin ba ya ganin su kamar yadda ba ya ganin iskan da yake shaƙawa.
Yana kiran su ‘Masu abu’ don suna nuna isa ga duk abin da suka nufi aikatawa ko
suke buƙata. Yana kiran su ‘Mutantani’ saboda sun yi tarayya da mutane ta ɓangaren jinsi da hali.
Masana
al’adun Hausawa irin su Greenberg (1946), Besmer (1973), Ibrahim (1982), Bunza
(1990/2006), Ismaila (1991), da sauransu, sun yi rubuce-rubuce da dama a kan
iskoki da matsayinsu a rayuwar Bahaushe. Magabata sun tabbatar da imanin
Bahaushe a kan samuwar iskoki. Haka kuma sun tabbata ba a ganin su. Hausawa sun
yi imani iskoki buwayayyi ne, masu ban tsoro, masu ƙarfi a kan
mutane, kuma masu iya cuta musu. Bayan bayyanar Musulunci a ƙasar
Hausa cikin ƙarni na 14 - 15, Hausawa suka fara amfani da sunaye irin su: Aljani, da
Ira'izzai, da Jinnu, da Rafani, da Shaiɗani, da dai makamantansu. Dalili kuwa shi ne, waɗannan
sunayen sun zo cikin nassoshin littattafan addini, waɗanda suka haɗa da Alƙur'ani da Hadisai da sauran litattafan Furu'a da na
Tauhidi da na Adabi (Bunza, 2004:4-5). Bisa ga haka, addinin Musulunci ya yi
tasiri ga sunayen iskoki da Bahaushe ke amfani da su a yau. Don haka, sunayen
da yake amfani da su na Hausa, suka rafashe, sai a bakunan bokaye da 'yan bori,
saboda kusancinsu da bori da tsafi[2]. Wannan,
ya tabbatar da daɗaɗɗiyar hulɗa tsakanin iskoki
da Hausawa tun ga addininsu na gargajiya da samar da waraka daga cutuka.
Watakila, wannan ya sa aka kawo bayanin neman waraka daga ciwon Yarima ɗan sarki da
Ruwan Bagaja a cikin labarin, yana cewa a shafi na 5:
Ina
nan wata rana an taso daga Juma’a, sai na ga Liman babana ya dawo gida idanu
sharaf sharaf da hawaye. Na tarye shi da kuka, na ce, “Baba, lafiya?” Ya ka da
baki ya ce, “Ina lafiya, yau Sarki ya muzanta ni cikin taro?” Wai don yau ana
cikin fadanci, ya ce ɗansa Yarima ba ya da lafiya, sai a kwantar a tayar. Ni kuwa na ce na ji
an ce da za a sami Ruwan Bagaja a
wani gari, da mutanen garin nan duk sun huta da masassarar zamani. Daga wai na
faɗi ’yar wannan, sai Sarki ya harzuƙa, ya ce wai ba’a nake jan shi da ita. Ya ce wai in ba shegantaka ba, da shaƙiyancin da na saba, ina na taɓa ganin wanda ya sami Ruwan Bagaja a duniya?
Rabe-raben
Iskoki
Masana
tarihi da al’ada sun yi bincike game da rabe-raben iskokin da Hausawa ke
mu’amula da su wajen neman biyan bukata. Ibrahim (1982), ya raba iskoki kashi
biyu ta fuskar ɗabi’a: ‘Farare’ da ‘Baƙaƙe’.
Fararen su ne masu kirki, masu taimakon mutane, ba su son dukiya ko sarauta.
Suna bayar da maganin cuce-cuce, ciki har da na ‘baƙaƙen’.
Baƙaƙen kuwa su ne, maƙetata, masu neman mutum da sharri, kamar a yi wa wani
magani ya mutu ko ya sami taɓin hankali, da sauransu.
Bunza (2006:9-10), ya kalli
rabe-raben iskoki ta fuskar
halitta da ɗabi’arsu. Duk da kasancewar Bahaushe ya yi imani cewa
sifar iskoki ta halitta ta bambanta da ta ɗan Adam, amma ya yarda cewa, suna da jinsin mata da
maza. Ta fuskar shekaru kuma, ya yarda cewa akwai yara matasa da manya da kuma
tsofaffi. A tsarin tunaninsu kuwa, ya yarda suna da masu hankali cikinsu, akwai
kuma mahaukata.
Haka su ma malaman Ruƙiyya,
sun kasa aljannu gida biyu: Akwai Musulmi akwai kuma Kafurai, akwai masu sauƙin
kai ga mu’amula akwai kuma masu taurin kai. A cikin labarin littafin Ruwan Bagaja, an yi amfani da aljannu
masu kirki, kuma Musulmai, kamar yadda ya zo a shafi na 16, yana cewa:
Sai na diro daga jirgi wai in faɗa ƙasa. Da faɗawata sai na nutse, na yi ƙasa! Abin ikon
Allah sai na isa wani gida a ƙasan tabkin, na tarad da waɗansu irin mutane masu manyan kawuna. Ashe ’yan ruwa ne. Suka yi maraba
da ni. Bayan na huta, suka tambaye ni labarina, duk na kwashe na faɗa musu. Da suka ji haka, sai suka ji tausayina, suka ba
ni magani, idona ya warke. Sarki ya sa aka kai ni tudu, aka sa ni hanya.
Haka
kuma, aljannun da aka yi amfani da su aka gina labarin, an nuna Musulmai ne,
saboda an yi amfani da kalmomin ƙissar Annabi Sulaiman da Babansa Annabi Dawud, a cikin
Alƙur’ani Maigirma. Shafi na 36 yana cewa:
Ina cikin ramin nan, ina jiran mutuwa, sai na ga waɗansu aljannu
guda biyu sun ɗauko wani ɗan’adam.
Suka sauke shi nan kusa da ni kaɗan, suka tona rairayi kamar shan ɗaki. Sai na
ji babban ya ce, “Bi hurmati Sulaimanu Ibnu Dawuda, iftah!” Sai na ga ƙasa
ta buɗe, suka
shiga da mutumin nan.
Haka
kuma, ta fuskar yanayin wurin zaman su, ko kuma inda suke rayuwa, ana iya kasa
iskoki zuwa kashi biyu kamar haka: iskokin tudu da na ruwa: Iskokin tudu su ne
iskokin da ke zama a farfajiyar sararin duniya, ko a cikin gari ko a dokar
daji, ko gindin itatuwan da aka zayyana a baya, da sauran wurare da aka ambata.
Ana samun ’yan kaɗan daga cikinsu masu kirki, amma masu sharri sun fi yawa. Ta fuskar rikiɗa kuwa,
sukan rikiɗa su koma irin
sifar mutane ko dabbobin da suke tare da su, kamar su dawaki da raƙumma,
da shanu da tumaki, da alfadari, da
jakuna, da sauransu. Iskokin ruwa kuwa, su ne iskokin da ke zama a cikin ruwan
teku ko na rafi ko na gulbi, ko kududdufi, da sauransu. Sukan fito waje a
sararin duniya ɗan lokaci, sannan su koma inda suke rayuwa, wato cikin ruwa ko kuma can ƙasan
ruwan teku. Wannan ya sa Bahaushe ke kiran su ’Yan ruwa. Kamar yadda
iskokin tudu ke rikiɗa, haka su ma iskokin ruwa kan rikiɗa su koma irin dabbobin ruwa, kamar su kada, ko tsari,
ko dorina, ko kifi, da sauransu. Ta fuskar mugunta kuwa su ma kamar na tudu
suke. Akwai na ƙwarai kaɗan, sannan mafi yawa daga cikinsu miyagu ne, sukan
cuta wa ‘yan Adam, musamman waɗanda suka shiga ruwa don wata lalura ko tsallakawa.
Dangane
da labarin littafin Ruwan Bagaja
kuwa, an gina labarin ne da nau’in iskokin ruwa (’Yan ruwa), kamar yadda aka faɗa a littafin,
a shafi na 6-7:
Ruwan Bagaja dai akwai shi a duniya, amma yana hannun aljannu. Ƙarewa
ma ba shi a bisa ƙasan nan da muke takawa.
Aljannun
da ke kula da rijiyar Ruwan Bagaja,
suna can ƙasan tsakiyar teku ne, lokacin da Imam ya ga wasu aljannu sun zo wurin,
sun yi addu’a, ƙasa ta buɗe suka
shiga. Yana cewa a shafi na 36:
Suka sauke shi nan kusa da ni kaɗan, suka tona rairayi kamar shan ɗaki. Sai na
ji babban ya ce, “Bi hurmati Sulaimanu Ibnu Dawuda, iftah!” Sai na ga ƙasa
ta buɗe, suka
shiga da mutumin nan. Ni kuwa na yi bulum na sha jinin jikina, duk na rufe jikina da rairai wai na
yi wa kaina kabari, shi ya sa Allah bai ba su ikon ganina ba. Can sai na ga sun
fito, sun ce, “Bi hurmati Sulaiman Ibnu Dawuda, igliƙ!” sai na ga ƙasa ta rufe. Suka mai da rairayin bisa, kamar da ɗai duniya ba
kome.
Matsayin Iskoki a Adabin Hausa
Adabi,
wani hoto ko madubi ne da ake iya hango al’ada da hikimomi da fasahar wata
al’umma. Haka ma iri-iren abubuwan da take cuɗanya da su a rayuwarta.
Daga ciki akwai ɓangarorin siyasa da tattalin arziki da zamantakewa da addini da
sauransu. Ta la’akari da yanayin adabin Hausawa, masana sun kasa shi gida biyu:
adabin gargajiya da adabin zamani (Ɗangambo, 1984).
Adabin gargajiya shi ne adabin baka. Ya ƙunshi fasaha da hikimomin da Hausawa suka gada kaka da
kakanni. Ya kuma ƙunshi
tatsuniyoyi da labarai da almara da tarihi da tarihihi da ƙissa da hikayoyi da kirari da karin magana da waƙoƙin
baka da wasannin dandali da camfe-camfe da kacici-kacici da roƙo da ba’a da barkwanci da baƙar magana da sauransu (Malumfashi, 2009:89). Kowane
reshe daga cikin rassan adabin baka, aka ɗora a mizanin tubalan
gininsa, za a samu iskoki dumu-dumu a ciki. Dalili kuwa, saboda a cikin tunanin
tubalan ginin duk wata tatsuniya ko labari ko tarihi ko hikaya da sauransu, ana
son a samu burgewa a ciki ko buwaya[3] ko ɗaukaka ko neman maganin wata matsala. Shi kuwa Bahaushe a tunaninsa, duk
waɗannan abubuwa ba su samuwa kai tsaye sai da taimakon iskoki. Wannan
tunanin ya shiga jinin Bahaushe, ya tashi da shi, kuma ya yi tasiri a rayuwarsa
ta ilimi da addini da siyasar zamantakewa.
Adabin zamani kuwa, shi ne rubutacce.
Ƙunshiyarsa ita ce, ƙarin fasaha da hikimomin da Hausawa suka samu bayan
sun iya karatu da rubutu, ko sun shaƙu da wasu al’ummomi, musamman Larabawa da Turawa. Bisa ga haka, Hausawa
suka fara rubuta hikimomi da fasahar da suke da su cikin adabin baka. A wajen rubutun, akan samu tasirin adabin baka a cikin rubutun nasu. Domin kuwa, tunani da ƙirƙirar marubuci tare suke tafiya da fasahar harshen da
yake rubutu da shi. Harshe kuma shi ne, taskar da ke ɗauke da al’adu da sassan
adabin bakan al’umma. Wannan shi ne dalilin da ya sa sassan adabin baka na
Hausa suka sami kansu a cikin rubutaccen adabi ta hanyoyi daban-daban: wasu a
matsayin tubalai, wasu kuma domin kwalliya irin ta rubutun adabi. Samun sassan
adabin baka a cikin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai, ya sa aka riƙa samun tubalan iskoki a ciki saboda dalilan da aka ambata a baya. Idan
aka duba littattafan ƙagaggun
labarai musamman na farko-farko, masu cike da fasaha za a samu haka. Misali,
littattafai irin su: Ganɗoki na Malam Bello Kagara, da Jiki Magayi na
Malam Tafida, da Iliya Ɗan Maiƙarfi na Ahmadu Ingawa, da Taurariya Maiwutsiya na
Ummaru Dembo, da shi kansa Ruwan Bagaja na Alhaji Abubakar Imam da
sauran ire-irensu, duk an gina labaransu da tubalan iskoki.
Haka
kuma, wani dalilin da ya ƙarfafa
amfani da tubalin iskoki a cikin rubutaccen adabin Hausa shi ne, samun fahimta
makusanciya a kan iskoki tsakanin al'ummar
Larabawa da Hausawa. Kasancewar su nesa ga juna a doron ƙasa, al'adunsu ta fuskar yadda suke kallon iskoki ya
yi kusa da juna ƙwarai
da gaske. Haka kuma, Labarawa suna ɗaya daga cikin al’ummomin farko, masu hanyar karatu da
rubutu da Hausawa suka fara cuɗanya da su. Littattafan adabin Larabci cike suke da
tubalan aljannu. Misali, Alfu Laila Wa Lailah da Kalilah Wa Dimnah
da Rauzul-Jinan da Kitab Nuruz Zaman da Maƙamatul Harir da sauransu. Ƙarawa
da ƙarau, sai addinin
Musulunci ya zo da cikakken bayani a kan halittar aljannu da halayensu da
sauran al’amurran da suka jiɓince su. Misali, akwai sura mai sunan ‘Surar Aljannu’
a cikin Alƙur’ani.
Ƙissar Alƙur’ani ta dangantakar Annabi Sulaiman da aljannu ta
isa misali babba.
Iskoki a Littafin Ruwan
Bagaja
Littafin Ruwan Bagaja yana ɗaya
daga cikin littattafan da aka rubuta na gasar farko ta rubuta ƙagaggun labaran Hausa da Hukumar Talifi ta shirya a
shekarar 1933. Haka kuma, shi ne ya lashe gasar (Yahaya 1988). An yi nazarin wannan littafi a matakai
daban-daban na ilimi ba su da iyaka. Kaɗan daga cikin su akwai
na Ingawa (1969) da Yunusa (1985) da Kudan (1987) da Bunza (1991) da Malumfashi
(1996, 2009) da dai sauransu. Marubucin Littafin Ruwan Bagaja, wato Abubakar Imam, ya shahara ƙwarai a duinyar Marubuta. Rubuce-rubucensa sun taka
muhimmiyar rawa a dandalin nazarin ƙagaggun labaran Hausa a duniya. A fahimtata, idan aka cire Adabin
Abubakar Imam daga cikin rubutaccen adabin Hausa, ɗan abin da za a bari bai
taka kara.
A cikin littafin Ruwan Bagaja an samu tasirin sassan adabin bakan
Hausa. Misali, an yi amfani da tatsuniyoyin Hausa a matsayin tubalan ginin waɗansu
sassa na littafin. Akwai tatsuniyar Ruwan
Bagaja, wadda ita ma haka aka gina ta kamar yadda aka gina labarin littafin Ruwan Bagaja, sai dai da ɗan
sauyi. Akwai kuma tatsuniyar Gizo da Tsuntsaye, inda Gizo ya
faɗo ruwa ya gamu da ‘yan ruwa (iskokin ruwa), ta taimaka wajen gina zaman
Alhaji Imam a Ɗandago
da yadda ya daɗa kogin Ƙaruna
ya gamu da ‘yan ruwa. Haka kuma, an ɗauko tatsuniyar Gizo da amaryarsa da ta Gizo da Sarki[4], don su taimaka wajen gina waɗansu sassa na littafin, musamman a zaman Alhaji Imam a
wani gari, Baku da wani Zango da ƙasar Hindu da kuma zamansa a gidan Sarkin Gardi (Malumfashi,
2009:89-90). Duk waɗannan tatsuniyoyi suna ɗauke da tubalan iskoki a cikinsu.
Bayan haka, tubalan
iskoki sukan shigo a cikin labari don a nuna burgewa da buwaya ko ɗaukaka
ko kuma neman magani. Littafin Ruwan
Bagaja, tun daga farko, an nuna saƙon wannan muƙalar,
domin Ruwan Bagaja ruwa ne da ake
magani da su ga wata cuta mai wuyar magani, shi ya sa aka nuna ruwan ga hannun
aljannu suke. Ya fara fito da maganar tun a shafi na 5, inda babansa Liman ya
dawo daga fadar Sarki. Yana kuka, ɗansa Imam ya tambaye shi me ya faru? Sai ya ce:
Wai
don yau ana cikin fadanci, ya ce ɗansa Yarima ba ya da lafiya, sai a kwantar a tayar. Ni
kuwa na ce na ji an ce da za a sami Ruwan Bagaja a wani gari, da mutanen garin
nan duk sun huta da masassarar zamani. Daga wai na faɗi ’yar wannan, sai Sarki
ya harzuƙa, ya ce wai ba’a nake
jan shi da ita. Ya ce wai im ba
shegantaka ba, da shaƙiyancin
da na saba, ina na taɓa ganin wanda ya sami Ruwan Bagaja
a duniya?
Har ila yau, Imam ya ci
gaba da bijiro da yadda za a yi ya samu Ruwan
Bagaja da inda zai same su. Ya nemi tsohon da ya tarar a cikin kogon dutse
da ya buga masa ƙasa,
(wato ya yi masa duba) ya ga ko zai dace da
Ruwan Bagaja. Ga abin da ya ce a shafi na 6-7:
Bayan mun saba da juna na ce masa ya buga min ƙasa, ya gaya
mini labarina da labarin niyyata. Ya buga ƙasa, ya ce,
“Ruwan Bagaja dai akwai shi a duniya,
amma yana hannun aljannu. Ƙarewa ma ba shi a bisa ƙasan nan da
muke takawa.
Imam
ya fara haɗuwa da ’yan
ruwa a lokacin da ya diro daga jirgi da nufin ya sauka ƙasa.
Kwatsam! ya ji shi a nutse cikin ruwa, sai ga shi tare da ’yan ruwa, yana cewa,
a shafi na 16:
Ko da na ji haka, sai na ce, “Yau ga yaran banza, sun dai mai da mutane
makafi. Ai na san mun kawo.” Sai na diro daga jirgi wai in faɗa ƙasa.
Da faɗawata sai na
nutse, na yi ƙasa! Abin ikon Allah sai na isa wani gida a ƙasan tabkin,
na tarad da waɗansu irin
mutane masu manyan kawuna. Ashe ’yan ruwa ne. Suka yi maraba da ni. Bayan na
huta, suka tambaye ni labarina, duk na kwashe na faɗa musu. Da suka ji haka, sai suka ji tausayina, suka
ba ni magani, idona ya warke. Sarki ya sa aka kai ni tudu, aka sa ni hanya.
An sake kawo maganar aljannu a shafi na 20. Sai dai a nan, ba a matsayin
tubali ba. A matsayin kwalliya ga labarin. Domin haukan ƙarya
ne aka yi, da sunan aljannun ƙarya sun taɓa shi. Buƙata
ya samu kuɓuta daga
hannun sarki a kan abin da Zurƙe ya yi masa, na tura shi ɗakin matar aure cikin dare. Don haka ya yi tabarmar
kunya, ya ce turo shi aka yi. Kuma ya ɗauki haukan ƙarya don ya kuɓuta. Ga abin da yake cewa:
Kowace tambaya ya yi mini, sai in ce, “Haka aka yi.” Sai ya ce, “Na san
a rina! In ba motsattse ba wa zai faɗa ɗakin wani ya ce wai turo shi aka yi? Lalle aljannunsa suka turo shi.” Ya sa aka kai ni
gidan mahaukata aka sa a turu. Da Wazirin garin ya ji labari ya ce ƙarya
nake yi. Lafiya ta lau!. Saboda haka Sarki ya taho gidan mahaukata, bayan an
kwana bakwai, wai don ya jarraba ni. Ya sa aka kira ni, ya ce, “Ina sunanka?”
Na ce, “Mai ’Yangabas.”
An ci gaba da gina labarin da
tubalan aljannu a shafi na 35. Imam ya isa wani gari mai suna Baitul Maƙaddas.
Ya sauka gidan sarki, kuma ya nemi sarki da a tara masa tsofaffin mutane su ba
shi labarin ko akwai wanda yake da labarin Ruwan
Bagaja? Yana cewa:
Sa’an nan aka kira wannan tsohon, aka ce ya ba da labarin. Ya ce, Ruwan Bagaja dai yana cikin ƙasar
Irami ne, ƙasar Irami kuwa ƙasa ce ta aljannu. Ruwan
Bagaja kuwa ma ba nan ƙasar yake ba, yana can bisa wani dogon dutse da ake
kiransa Dutsen Ƙaf. Babu mahalukin da yake iya zuwa can sai aljannu,
ko aljannu ma sai masu fikafikai kaɗai. Amma na mance sunan rijiyar yanzu. Ko aljani ya yi
ƙoƙari ya isa dutsen nan kafin ya ɗebi ruwan sai wani ikon Allah. Akwai waɗansu
maridai, masu jiran rijiyan nan, kuma akwai waɗansu ’yan karance-karance kuma da ake yi kafin a sami
damar shiga. Akwai kuma dokoki da ake bi in an shiga, da cewa mutum ya kuskure ɗaya daga cikinsu sai a yi ban da shi. Ko kakan namu ma
ya manta da waɗannan
dokokin da addu’o’in. Ka ji abin da na na sani na labarin Ruwan Bagaja, ranka ya daɗe!”
Imam ya samu labarin Ruwan Bagaja na ƙasar Aljannu
da ake kira Iram. Bisa hanyarsa ta isa Iram, jirginsu ya yi karo ya nutse, kowa
ya halaka sai shi kaɗai ya tsira. Ya samu kansa a kan wani tsibiri tsakiyar teku. Yana
tunanin mutuwa ta zo masa, sai ya tona yashi ya yi rami ya shige a ciki yana
jiran mutuwa. Ga abin da yake cewa a shafi na 36:
Ina cikin ramin nan, ina jiran mutuwa, sai na ga waɗansu aljannu
guda biyu sun ɗauko wani ɗan’adam.
Suka sauke shi nan kusa da ni kaɗan, suka tona rairayi kamar shan ɗaki. Sai na
ji babban ya ce, “Bi hurmati Sulaimanu Ibnu Dawuda, iftah!” Sai na ga ƙasa
ta buɗe, suka shiga
da mutumin nan. Ni kuwa na yi bulum na sha jinin jikina, duk na rufe jikina da rairai wai na yi
wa kaina kabari, shi ya sa Allah bai ba su ikon ganina ba. Can sai na ga sun
fito, sun ce, “Bi hurmati Sulaiman Ibnu Dawuda, igliƙ!” sai na ga ƙasa ta rufe. Suka mai da rairayin bisa, kamar da ɗai duniya ba
kome.
Imam
ya fara ganin hasken biyan bukatarsa na samun Ruwan Bagaja. Domin kuwa, ya samu
kutsa kai ƙarƙashin ruwa ta hanyar jin adu’ar da aljannu suka yi, shi ma ya yi , ƙofa
ta buɗe ya shiga.
Bayan ya shiga, kuma abin da ya gudana tsakaninsa da Saƙimu, ya kiciɓis da
takobin zinari, wanda yake da bawa aljani. Yana shafa[5] takobin
cikin rashin sani, sai wani aljani ya fito. Ga abin da ya ce masa a shafi na
36-37:
Faɗi bukatarka
ya ubangijina!... Ni ne bawan takobin nan. Yafisu ɗan Nuhu ya ajiye ni nan in yi wa takobin nan bauta,
don da shi ya yi yaƙi sa’adda yake da rai har ya ƙaura. Da na
ji haka, sai zuciyata ta yi fari, na ce, “To, in haka ne, kai ni in samo Ruwan Bagaja. Da jin wannan kalami nawa,
sai ya yi ƙara ya ce, “Ba ni da iko!, amma na kai ka wurin wani babbanmu, in ya
yarda shi kaɗai ke da ikon
wurin duk ƙasan nan. Tun da aka halicci duniya, aka halicci Ruwan Bagaja a nan, don
dukan aljannu. Tun lokacin nan kuwa zuriyarsu ke riƙe da ita har
yanzu. Da na ji haka sai na ce, to ya kai ni. Kafin ƙyaftada
bismilla, sai muka iso wani ƙaton kogo, kusa da babban Birnin Iram. Ya ce, “cikin
kogon nan yake!”
Tun daga farkon babi na takwas na wannan littafi, wato
shafi na 37 har zuwa ƙarshen littafin, bayani ne na gwagwarmayar ɗebo Ruwan Bagaja. Imam ya sha wahalhalu
tsakaninsa da aljannu, har zuwa inda buƙatarsa ta
biya. Ya samo Ruwan kuma ya dawo gida lafiya, ta hanyar rijiyar Maiburgami da
ke Kano. An kuma ba Yarima ɗan Sarki Ruwan, ya sha, ya samu lafiya, nan take.
Abubuwan da suka bijiro cikin littafin Ruwan Bagaja a kan zamantakewar al’umma,
abubuwa ne da suka dace da wannan lokaci, musamman abin da ya shafi
tsafe-tsafen neman kuɗi da mulki da bugun ƙasa, na daga ayyukan malaman
budeji da bokaye waɗanda ke haɗa maganinsu da sharaɗin samo wani abu mai wuyar samu. Misali, sukan ce
mutum ya nemo gashin gezar zaki, ko kitsen ƙuda, ko ayyana wani abu wanda ba a san inda za
a nemo shi ba, amma sai su nuna su, suna iya nemo abin, a ba su kuɗi. Duk da kasancewar littafin ya shekara
tamanin (80) da wallafawa, amma saƙon da ke cikinsa ya dace da zamanin yau, musamman ta
fuskar rayuwar Hausawa ta yau da kullum.
Naɗewa
Littafin
Ruwan Bagaja littafi ne da aka gina a kan hikima da fasahar al’ummar
Hausawa da ta Larabawa. Al’adun waɗannan al’ummomin guda biyu, ta fuskar yadda suke
kallon iskoki sun yi kusa da juna ƙwarai da gaske. Wannan shi ya ba marubucin damar gina
labarun da ke cikin littafin da tubalan iskoki. Tun daga harsashen ginin
labarin littafin, da iskoki aka fara kuma da su aka yi rufin ginin. An yi
ginshiƙai a wurare goma sha biyu da tubalan iskoki a cikin littafin. Amfani da
tubalan iskoki ko aljannu ya taimaka ƙwarai wajen isar da saƙon littafin.
Da babu tubalan iskoki a cikin ginin labarun, da saƙon littafin
bai fito ba. Tubalan iskoki sukan shigo a cikin labari inda ake son nuna
burgewa da buwaya ko ɗaukaka ko kuma neman magani. Littafin, tun daga
sunansa, an nuna magani ne saƙonsa. Domin Ruwan Bagaja, ruwa ne da ake magani da shi
ga wata cuta mai wuyar magani. Shi ya sa aka nuna Ruwan, ga hannun aljannu
yake. Babu shakka, bijiro da tubalan iskoki a cikin ginin labarun littafin, ya
taimaka masa wajen lashe zaɓen gasar farko, ta rubuta ƙagaggun
labaran Hausa da Hukumar Talifi ta shirya a shekarar 1933.
Manazarta
Ahmad, I. A. (1984) “Cututtukan Ciki da Magungunansu.” Kudin digiri na farko, (B. A. Hausa) Jami’ar
Bayero. Kano.
Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa
Da Muhimmacinsa Ga Rayuwar
Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.
Bunza, A. M. (1990), “Hayaƙi Fid Da Na
Kogo: (Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa)”, Kundin digiri na biyu (M.A.
Hausa), Jami’ar Bayero. Kano.
Bunza, A. M. (1991) “Sharhin Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja.” Maƙalar
da aka gabatar a taron Makon Hausa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo. Sakkwato.
Bunza, A. M. (1995) “Magungunan Hausa a Rubuce: (Nazari
Ayyukan Malaman Tsibbu),” Kundin digiri na uku (Ph.D. Hausa) Jami’ar Bayero. Kano.
Bunza, A. M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada . Tiwal Nig. Ltd. Lagos.
Gusau, S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gobir, Y. A. (2002) “Iskoki a Idon ’Yan bori da Masu
Ruƙiyya”. Kundin digiri na biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Gobir, Y. A. (2010). “Hulɗar Soyayya Tsakanin Ɗan’adam da
Iska” a cikin KONJOLLS:
Kontagora Journal of Languages and Literatures. Kontagora:
FCT.
Greenberg,
J. (1946). The Influence of Islam Sudanese Religion. Monographs of the American
Ethnological Society. New York Seattle. London.
Hamza, M. W. (1977) “Magungunan Hausawa”. Kundin
digiri na farko, Jami’ar Bayero. Kano.
Ibrahim, S. M. (1982). “Dangantakar Al’ada da Addini:
Tasirin Musulunci Kan Hausawa”
Kundin digiri na biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Isma’ila, H.
A. (1991). “Islamic Medicine and Its Influence on Traditional Hausa
Practitioners in Northern Nigeria. Unpublished Ph.D Thesis. Madison: University
of Wisconsin.
Imam, A. A.
(1999) Ruwan Bagaja, Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.
Ingawa, A.
(1969) Ruwan Bagaja. The Water of Cure. Fassarar
Hausa zuwa Ingilishi. Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.
Kudan, M. B. T. (1987) “Kwatanta Jigon Ƙagaggun
Labaran Gasa.” Kundin digiri na farko, Jami’ar Ahmadu Bello. Zariya
Malumfashi,
I. (1996) “The Making of Abubakar Imam’s Ruwan
Bagaja: A Preliminary Investigation.” Maƙalar da aka gabatar a taron ANA Arewa House, Kaduna.
Malumfashi,
I. (2009) Adabin Abubakar Imam,
Sokoto: Garkuwa Media Services Ltd.
Mora, A. A.
(1989) Abubakar Imam Memoirs.
Northern Nigerian Publishing Company. Zaria.
Mukhtar, I.
(2004) Jagoran Nazarin Ƙagaggun
Labarai,
Kano: Benchmark Publishers Limited.
Tremearne,
A. J. N. (1913) Hausa Superstitions
And Customs. Oxford: John Bale Sons and Danielsson, Ltd.
Tukur, A. (1988) “Nazari a kan Cututtukan da suka
shafi Fatar Jiki da Magungunansu a Bahaushiyar Al’ada.” Kudin digiri na farko,
(B. A. Hausa) Jami’ar Bayero. Kano.
Yahaya, I. Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.
Yunusa, M. M. (1985) “Kasancewar Tatsuniyar Ruwan
Bagaja tushen littafin Ruwan Bagaja
na Abubakar Imam” Kundin digiri na farko, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Sakkwato.
[1] Dubi Calvin Y. Garba (1990) “Kamus na Harshen Hausa” Evans Brothers
(Nigeria Publishers Ltd) shafi na 75.
[2] Daga cikin sunayen
iskoki na gargajiya akwai: Kayehi da Ɗantsatsumbe da Doguwa da Inna da Jitakuku da Gajimare da Kure da Duna da
sauransu.
[3] Domin ƙoƙarin
neman buwaya ga jama’a ake samun Sarakuna da Fatake da Tajirai da Mayaƙa da Ɓarayi
da mutanen alfarma cikin jama’a, suna neman yin tsafe-tsafen baduhu da zana da
kauda da fasa-taro da shashatau da sauransu.
[4] Tatsuniyar Gizo da sarki ita ce, inda Gizo ya je gonar sarki yana tsinke ɓaure yana sha har ya gama, ya koma wurin sarki ya ce ya
gama aiki, ashe akwai wata tsuntsuwa tana saman wata itaciya tana kallon duk
abin da Gizo yake yi. Bayan an kai masa amarya da gararta gida, sai ta fara rera waƙa cewar Gizo ya ci ɓaure ya sha ruwa ya sakace haƙoransa ya kurkure bakinsa, domin kar a
gane cewa ya ci ɓaure. Bayan an saurari tsuntsuwar da kyau, sai aka mayar da
amarya gida da gararta, shi kuma ya ji kunya
ya rasa ta.
[5] Wannan ya yi kama da
wani labari da ake bayarwa, wanda ya faru a garin Kaduna a Masallaci. Wani
ladanin masallaci ne ya tsinci zobe a cikin masallacin, bayan an watse daga
sallar Subahin. Da ya zo da zoben gidansa, da niyyar cigiyar wanda ke da zoben.
Cikin rashin sani, ya shafi zoben, sai ya koma kan mutum, yana cewa, “zafi nake
ji, zuba mun ruwa”. Yana zuba ruwan sai ga kuɗi ’yan naira dubu-dubu,
suna fitowa daga bakin kan. Da Ladan ya dawo ya yi cigiyar zoben, ashe na wani
hamshaƙin mai kuɗi ne,
kuma sananne a cikin Kaduna.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.