Hausawa na cewa: “Komi ya ɓace maza ka biɗo shi”. Babban tunaninsu a kan haka shi ne, wuyar aiki ba a fara ba. A kowane lokaci mutane ke jayayya ana buƙatar raba gardama. Idan sa-in-sa ya yawaita, gaskiya ce ba ta bayyana ba. Da ta leƙo, ita ce raba gardama. Labarin masu yunƙurin fayyace da buhun gero da ‘yan Nijeriya wa ya fi yawa, ya bice duniyar kafafen yaɗa labarai na BBC da VOA da RFI da jaridun ƙasa da kafafen yaɗa labarai na jihohi. Da masoyansu, da masu mamakinsu, da masu musunsu, da masu adawa, dole su yarda da cewa, wannan al’amari ya gawurta kuma ya yi tasiri ga duniyar lokacinmu. Ganin irin ƙwazon matasan da suka assasa wannan batu, suka ba lokacinsu, da tunaninsu, na ganin sai sun kuranye yanar da ke ciki, ya san a yi wa wannan takarda taken: Wurin da babu ƙasa nan ake gardamar kokuwa”. Yanzu sai a biyo mu a ji ina salka ka tsatsa.
Wurin Da Babu Ƙasa Nan Ake Gardamar Kokuwa
(Sharhin Littafin: Da ‘Yan Nijeriya da Buhun Gero Wa Ya Fi Yawa?)
Aliyu Muhammadu Bunza
Tunanin Na Bayan Fage
Wani da ji zancen ƙidayar buhun gero zai ce, marasa aikin yi ne. masu wannan tunanin sun manta da cewa lissafi rabin ilmi ne kuma babban aiki ne. a ganin wasu, wai, zauna gari banza ne da suka rasa ta yi. Assha! Ai zauna gari banza ba ya tunanin komai sai tunanin banza. Wanda duk tunaninsa ya doshi sanin ƙididdigar mutanen ƙasarsu da abincinsu babu ɗan kishin ƙasar da ke gabansa. A ganin wasu, marasa karatu ne ke son su sami wata dama ta sake jiki. Ina! Ai daga cikinsu akwai masu karatun addini da na boko, don haka da gafaka da digiri duk ba su jin tsoron a yi taho-mu-gama da shi. A nawa hasashe, matasan da suka haɗa wannan muhawara cikakkun ‘yan kishin ƙasa ne, gogaggu, wayayyi, managarta da ke son a kan kowane al’amari a riƙa sara ana duban bakin gatari.
Tunanin Ɗaliban Ilimi
A namu tunani, ruwa ba sa tsami banza. Yunanin mutane abin sauraro ne da girmamawa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Idan muka faɗaɗa darasin da rashin tayi a kan bar arha, za mu fahimci ana tsintuwar guru cikin suɗi ba abin mamaki ba ne a yi tsintuwar dami a kala. Babu wai, da rashin kira Karen bebe ke ɓata. Fahimtarmu ta cewa, rashin sani ya fi dare duhu ita ta ba mu damar gano rashin sani ke sa Karen gwauro yi wa gwauruwa/bazawara haushi (barazana). A taƙaice, tunanin waɗannan matasa wata babbar makaranta ce da buɗa ƙofar kowane irin tunani. Daga cikin abubuwan da ya kyautu mu hango akwai:
1. Me ya sa suka yi tunanin
yawan ‘yan Nijeriya?
2. Me ya sa buhun gero kawai
ya zo a tunaninsu?
3. Me suke son su nuna wa
‘yan Nijeriya da wannan tunani?
4. Me ya sa wannan tunani bai
zo musu a mulkin soja ba?
5. Me ya sa sai a wannan
gwamnati suka fito da wannan ra’ayi?
6. Don me ba su bar tunaninsu
tsakaninsu ba sai da suka yayata?
7. Mene ne dalilinsu na yin
wannan muhawara?
Duk wani ɗalibi irinmu ya tsura wa waɗannan tambayoyi idon nazari sai tabbaatr da cewa, Turancin direba sai fasinja. A namu tunani matasan sun yi amfani da buhun gero a matsayin sabara, wadda Bahaushe ya ce sai an laɓe gare ta a harbi barewa. Ina barewar take? Ku bi ni a sannu.
Gero a Bahaushen Tunani
Gero na da wata martaba ga Bahaushe wadda babu wani nau’i daga cikin nau’in tsaba/hatsi, mabunƙura ƙasa, ‘ya’yan itace, da ganyen da ya kai shi. Ga alama gero shi ne abincin farko da Bahaushe ya fara fahimta da sanin yadda ake sarrafa shi. Kaɗan daga cikin tunanin Bahaushe a kan gero sun haɗa da:
1. Gero ne limamin ƙida cikin zuriyar
tsaba/hatsi a Bahaushen lissafi a kan ce: gero da dawa, gero da maiwa, gero da
masara, da sauransu, amma ba a limanta gero a ce: “dawa da gro” a al’adance.
2. Daga cikin dangogin
tsaba/hatsi gero kaɗai ke da martabar a gasa
shi a ci yana ɗanye da sunan tumu, in ya bushe a gasa
a ci da sunan babbaka, a tafasa shi haka nan da kayan haɗi a ci da sunan rummace/rumbaye, a
saka shi a baka gayansa a ci da sunan mummuƙe. Ashe gero ya buwaya, ya
cancanci a yi masa karatun kansa.
3. Daga cikin sunayen
Bahaushen gero kawai ake yi wa Bahaushen suna laƙabi da shi, ba tare da
wani madanganci ba, za ka ji sunan mutum “Gero” amma babu “Nagero” ko “Maigero”.
4. A ɓangaren sauran hatsi: Maidawa,
Namaiwa, Mainasara, Maishinkafa da sauransu, ɗaukar gero a idon Bahaushe
ta tun fil azal ce ba ta girshi ba.
5. A tsayin cimakar Bahaushe,
da fura da kunu da ɓula da zaɓu da kafa da dambu da rumbace/rumbaye
da daƙuwa da tukkuɗi gero ne maganaɗison haɗinsu. Ba don ge ba da an tasarin more
wa daɗinsa.
6. A Bahaushiyar al’ada, da damen gero ake toshin aure da kai kayan haihuwa, wanda duk aka kai ba shi ba rashin sa ya haifar da haka.
Na tabbata Narambaɗa bisa gaɓa ya sara a fadarsa da ke cewa:
Jagora: Maɗi bai kai ga zuma ba
Yara: Kowal lasa shi ka hwaɗi
Kwandon wake bai kai ga damen gero ba
Jagora: Ai ɗan akuya ko ya yi ƙahoni,
Yara: Ya san bai yi kamar rago ba
Jagora: Duk wada ɗan Sarki yaƙ ƙasura
Yara: Kak ka raba shi da bawan Sarki
Gogarman Tudu jikan Sanda
Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa.
Ashe tunanin matasanmu a kan gero ba bidi’a suka yi ba, sun dai yi cikon sunna makaho da waiwaya.
Kwatanta ‘Yan Nijeriya da Yawan Buhun
Gero
Wanda duk ke da tarihin yawaitar bil Adam a doron ƙasa ya san akwai buƙatar ana sara ana duban bakin gatari. Kamata ya yi abincinmu ya fi mu yawa ba. Halin da muke ciki yanzu mun fi abincinmu yawa, wanda ya haifar da hauhawan farashinsa da ragaitar marasa abinci su kutsa cikin aikata miyagun ayyuka da ƙazantattun laifuka.Tunani makaɗa Ɗangiwa da Ɗanƙwairo ya tabbatar da wannan hasashe:
Jagora: Ashe likkita ba shi maganin yunwa
Yara: Wanga magani sai a biɗo hura
Gindi: Cikin duniya ba abin da yak kai ga
faro-faro
Ɗangwairo na cewa:
Jagora: A samu na shan dawo
Yara: Ka a ragaice
Bi da kayan hwaɗa maigida Ali
Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba.
Hikimar Buhun Gero a Tunanin Littafin
A tunaninmu buhun gero ba ya ƙidayuwa kai tsaye a samu
haƙiƙanin abin domin saninmu na ƙwarorin gero ƙanana ne adadin da ke cika buhu ba su
da iyaka. Wanda duk ya ce zai ƙidaya su ya ɓaro jan aiki. Da wuya a samu ƙaton da zai ɗora buhun gero a kansa shi kaɗai dole sai an aza shi. Ba a san
namjin da ke rabin yini da buhun gero a kansa ba. Duk wanda aka ɗora masa shi a ka sai an taru za a taya shi saukewa. To
kwatanta wannan da yawan ‘yan Nijeriya da buƙatocinsu da ke kan mutum ɗaya kacal tsawon shekaru huɗu. Wazirin Gwandu Alhaji Umaru ya ce a
dinga tanya wa wanda kaya suka rinjaya:
Kwaɗ ɗauki kaya sun fi ƙarfi nai ga kai
Yaf fara hanya tabbata masa ba shi kai
Tafiya kaɗanna shi kai shi ɗaura takai-takai
Indai ya yas in ko su faɗi shi haushi
(Waziri Umar: Waƙar)
Karatun Kiɗan Buhun Gero
Mazajen da shiga wannan aiki su bakwai
ne domin su dace da ranakun mako. Binciken ya ɗauke su kwanaki ɗari biyar (105), kusan wata uku da ‘yan kwanaki (kwana biyar)
a kan ƙidan farilla, idan bai
cika farilla ba wata uku da kwana takwas. Yawan adadinsu su bakwai ya nuna muna
kashin baƙi sai taro, hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinƙa. Idan aka ga cikas ga
abin taro a bar zargin mutum ɗaya matsala kurar gardi ce. Idan za a
yi wata uku na ƙidar buhun gero, to wata
ko shekara nawa za a ɗauka na tantance matsalar da ke ga
kowane kwano ko sa’i ko tiya? Kwatanta wannan da matsalolin ƙasarmu da mutanenta da
jihohinta da yankunanta da ƙabilunta da addinanta da
al’adunta kuma duk a ce mutum ɗaya ne limaminta. Yaya za a yi ya kauce wa rafkanuwa? Saƙon Narambaɗa shi ne:
Jagora: Kowac ce shina iyawa ga hili nan
Yara: Sai ya ƙetare gudanai ba ban kwana
Gindi: Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
Me Ya Sa ba a Yi Tunanin Ƙidan Buhun Gero a Mulkin Soja?
Hausawa cewa suka yi dama da damun
dawo in babu dama ana dama shi gaya. Mulkin soja tuƙin tsaye ne aikin mutum ɗaya. Talaka ba ya da wata walwala ta zaman tunanin me ya
kamata ya yi? Me ya kamata a yi wa ƙasa? Don haka, ko da akwai wannan
tunani ba zai yi tasiri ba domin ‘yan ƙasa na tsakanin bakin bindiga da
kurkuku da gudun fanfaƙe. Mulkin dimokraɗiyya ke da walwala da sakewa da ba
talakka damar taka rawa har da wuce gona da iri. Don haka idan aka samu dama
irin ta dimokraɗiyya a yi amfani da ita
yadda za a more mata, ba yadda za a wargaza ta gaba ta koma baya. Masu
jagorancin dimokraɗiyya ga saƙon malamin kiɗa:
Jagora: Abin sarauta abin rabo ne
Yara: In an samai a ba mutane
Amma shi wanda bai sani ba
Sai ya ci shi ɗai ya ɗaura gyashi
Ya zaɓi gwalo ya wa mutane
Sai ya wuce kamar ruwan faƙo
Gindi: Tattaki maza ɗan Sanda na Iro
Gamda’are Salau mazan ƙwarai.
Me Ya Sa Sai a Wannan Gwamnati Karatun
ya Tusgo
A tunanina, gwamnatin da ke ci yanzu ta karvi mulki ga wata gwamnati irinta. Duk lokacin da aka ba da mulki cikin lumana ba da juyin mulki ba, ba da zanga-zanga ba, wanda ya miƙa mulkin zai tsura wa mai karɓar mulkin ido sosai ya ga irin rawar da zai taka. Don haka, tsakanin wanda ya noma gero da wanda ya sussuke shi da wanda ya ɗura shi a buhu da wanda ya zube shi a ƙasa ya ƙyarga shi ƙwara-ƙwara wa ya fi saninsa? Yadda kowanensu ke da masaniya kan matsalolin jama’arta, ƙwazon kowace ya danganta ga irin adalcinta. Yawan ‘yan Nijeriya ya kai miliyan ɗari biyu (200,000.000) buƙatocinsu ya nunka haka. Dole a ce, abin da yawa inji mutuwa da ta shiga kasuwa.
Hikimar Yayata Karatun Ƙidan Gero
Babu shakka ba bil Adama kawai Allah Ya halitta a duniya ba, akwai dabbobi da ƙwari da tsuntsaye da Iskoki, da Mala’iku duk ba su gagari Allah mulki ba domin buwayarSa da iyawarSa. Duk wani wanda ba Allah ba zai iya da mutane ba komai ƙwarewarsa da ilminsa da soyayyar da ake yi masa. Buhun gero da aka haɗe ƙwarori miliyan barkatai a ciki aka ɗinke wuri ɗaya ba magana suke yi ba, ba su da wata buƙata, ba a yi musu wani alƙawali ba, ba su da bambancin yanki da jiha da jinsi da addini da harshe. Da tsuntsaye ne ko dabbobi ko ƙwari ko kiyafu aka tara wuri ɗaya dole sai an nemi agajin tattaro su da haɗe su wuri ɗaya su zauna lafiya. To, ina ga mutane? A haɗe mutane gaba ɗaya, a mallake su lamui lafiya sai Allah. A koyaushe, a kowace ƙasa, a kowane mulki, akwai mutane shida da ba sa barin a zauna lafiya inji Narambaɗa:
Jagora: Sarki Ka ga mutum shidda
Yara: Babu mai zannawa lafiya da su
Jagora: Wanga azuji wanda butulu
Yara: Guda asheraru guda maɓannaci
Jagora: Wanga guda tsohin munahuki
Yara: Akwai wani na nan mai ƙure mutum
Gindi: Ya ci maza yak wan shina shire
Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.
Me Ya Haifar da Wannan Mahawara?
Babu abin da ya haifar da wannan muhawara face muna cikin ƙasar da kowa ya iya, kuma ba a yarda da kowa ya iya ba. Ƙasa ce da masoya ke makaftar soyayya, maƙiya ke makaftar ƙiyayya. Babu abin da za a yi wa mutane face hannunka-mai-sanda ko za su ahumo su waiwayo a koma tsaka-tsaka. Yawanmu na ƙaruwa, matsalolinmu na daɗuwa, fitinu da rigingimu na daɗa wanzuwa da barbazuwa. Da za mu yi wa kanmu adalci mu zauna mu riƙa tunanin irin halin da ƙasarmu take ciki, da dabarun tunkararsu da zai amfane mu.
Raba Gardama
Ma’aikatanmu talatin da bakwai da suka
yi kwana ɗari da biyar suna ƙidayan buhun gero sun samu ƙwara miliyan goma sha ɗaya da dubu ɗari tara da saba’in da tara da ɗari takwas da sittin da takwas (11,979,868). A ma’auna buhu kashi uku yake
kamar haka:
1. Mudu ɗaya na ciyar da mutum 3 ci ɗaya kacal.
2. Buhu ɗaya na ciyar da mutum 210 ci ɗaya kacal.
3. Mutum ɗaya na buƙatar mudu ɗaya a yini ci 3 kacal.
4. Buhu ɗaya na ciyar da mutum 70 a yini ci 3
kacal.
5. Yawan ‘yan Nijeriya
200,000,000 a raba da 70 = 2,857,142.857.
6. ‘Yan Nijeriya na cin buhun
gero 952,380,9524 ci ɗaya a wuni.
7. ‘Yan Nijeriya na cin buhun gero 2,957,142,857.
Sakamakon Bincike
Muddin ta tabbata yawan ‘yan Nijeriya
ya kai miliyan ɗari biyu (200,000,000)
dole hukuma ta zage damtse wajen inganta noma ta fuskar tallafa wa manoma,
inganta ma’aikatun gona, da faɗaɗa bincike a kan sha;anin noma. Gina
makarantu da ma’aikatu da gidaje da kamfuna a rayayyen
wurin nom aba ci gaba ba ne komawa baya ne. Da za a kawo sharaɗin zama manomi ga duk wanda zai yi
takarar shugaban ƙasa da gwamna da majalisun
tarayya da an taimaka. Babu shakka ‘yan Nijeriya sun fi buhun
gero yawa don haka suna buƙatar gero mai yawa domin su rayu.
Naɗewa
Ta tabbata ƙwarorin gero 11,979,868 aka samu a buhun da aka ƙyarga. Masana noma sun tabbatar da cewa, damin gero biyar ke buhu. Matsakaicin manomi na noma dame saba’in wanda zai ba da buhu goma sha huɗu. A cikin kowane dame ana samun ƙwarori 2,395,973,6. Manomi ɗaya mai noma dami (70) buhu (14) buhunsa ɗaya na ciyar da mutum 210 nomansa gaba ɗaya zai ciyar da mutum 2,940. Madalla da muhawarar matasa da ta buɗa mana kafar sanin ƙasarmu da shugabanninta da yadda za a iya wadatar da ita da kyan tsari (hurar gero) bisa ga riwayar Muhammadu Sani Ɗanbalɗo da ke cewa:
Jagora: Kun san layun tsari gare ni,
Mi al layun tsarinka Mamman?
Dunƙullan dawo gami da nono,
Ko was sha su ba shi jin kasala
In ko an yi gardama a dama
Gindi: Rabbana Allah Ka taimake mu
Mu samu fitar kai cikin tukunya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.