Idan muka yi la’akari da abin da shaihin malami Aliyu
Bunza ya faɗa a cikin wannan ma’ana da ya bayar za mu fahimci cewa, ma’anar
ta bayar da ƙarfi ga abin da yake da ƙudurin ganowa a bincikensa. Wato ya ta’allaƙa ma’anar ga bincikensa. Wannan kuma ba ya rasa nasaba da
ƙishirwar da ke cikin zuciyarsa ta ganin ya bayyana
matsalar da yake yunƙurin gudanar da bincike a
kai...
Ɗora ma’anonin Wada Hamza da Aliyu Muhammadu Bunza a kan ‘Cuta’ a Mizanin Awon Al’ada.
Haruna Umar Maikwari
07031280554
Gabatarwa
Wannan jinga za ta mayar da hankali a
wasu ma’anoni na “Cuta” da wasu masana suka bayar, kuma a cikin za a ɗora ma’anonin a
mizanin awon al’ada domin a tantance ma’anonin da kuma abin da suke magana a
kai. Amma dai kafin nan za a yi shimfiɗa da ma’anonin magani. Kasancewar idan cuta
ta harbi halitta ko wani abu, magani ake nema domin a samu waraka ko sauƙi ko gyara ko canza a abin da nan da cuta ta
yi wa illa. An samu wasu masana sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da
ake nufi da magani. Kamar Bunza (1989) ya bayyana ma’anar magani da cewa, wata
hanya ce ta warkarwa ko kwantar da ko rage cuta ta ciki ko ta waje, ko
wadda ake samu daga haɗari ko kuma neman kariya ga cutar abokan hamayya
ko cutar da su ko neman ɗaukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar
siddabaru da sihirce-sihirce na ban al’ajabi.” Ahmad (1984) yana cewa, magani
shi ne duk wani abu da za a yi, ko wata hanya, ko kuma dabara da ake yi don gusar
da cuta daga jikin mutum ɗungurungum, ko kuma kwantar da ita don kawo
jin daɗi ga jiki ko ga zuciya da sawwaƙe duk wata wahala da damuwa da ita cutar kan iya
haifarwa. Musa (1986) yana cewa, magani wata hanya ce kawai ta neman biyan buƙatar wata matsala da ke damun mutum, ko
kuma yana ganin matsalar tana yi masa barazana. Sarkin Sudan (2013) cewa ya yi,
kalmar magani na nufin duk wata hanya da ɗan Adam zai bi wajen warkar da cuta ko rauni
ko neman kariya daga cutar. Saboda haka, ana iya cewa, magani shi ne duk wani
abu da aka yi amfani da shi domin magance wata cuta, ko cutar da wani aka saka
ta ga jikinsa.
A ganina, magani shi ne duk wata hanya
da aka yi amfani da ita domin samun sauƙi ko waraka ko mafita a kan wata matsala da take damun
jikin mutum ko zuciya ko kuma rayuwarsa gaba ɗaya. Maganin gargajiya kuwa shi ne, yin
amfani da itatuwa ko rubutu ko addu’a ko surkulle, don warkar da wata cuta, ko
neman wani amfani, ko gusar da sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buƙata (Alhassan da wasu 1986).
Ma’anar Cuta
Masana da
Manazarta sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da ake kira ‘Cuta’? ga
dai wasu daga cikinsu:
Shi kuwa Adamu (1998). “Cuta tana nufin rauni da raɗaɗi tare da
wahala da mutum kan gamu da su a sanadiyar gazawar wata halitta a jiki ko kuma
damuwa a zuci.”
Cuta na
nufin wani yanayi ko damuwa ko matsala ko muradi ko ma wani abu makamancin waɗannan da
ke kama wani abu mai rai ko maras rai ya zame masa illa ko barazana ko tarnaƙi ko sauya wannan abin daga ainihin yanayinsa na asali da
aka san shi, zuwa wani yanayi ko hali na daban. Kuma wannan yanayi yana buƙatar samar da wata hanya da za a magance wannan matsala,
ko damuwar ko yanayin ko muradin ko dai wani abun da ya hardasa neman hanyar
warware wannan abin.
Ɗora ma’anonin Wada Hamza da Aliyu Bunza a kan
‘Cuta’ a mizanin awon al’ada.
Mene ne Cuta?
Wada Hamza
(1977) a cikin kundinsa na digirinsa na BA mai take “Magungunnan Gargajiya”
kundin wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya na Jam’iar Bayero.
Ya bayyana cewa, “Cuta na nufin wani yanayi ko wani abu da zai matsa wa rai ko
ya kawo rashin gamsuwa a rayuwa”.
Shi kuwa
Shaihin Malami Aliyu Muhammadu Bunza(1990) a cikin kundinsa na MA da ya gabatar
a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar
Bayero da ke Kano. Kundin mai taken “Hayaƙi Fidda na Kogo”. Ya bayyana cewa, “Cuta wata damuwa ce
da ke shiga jikin halitta, domin raunana lafiyarsa, ko kuma ta shafi zuciyarsa,
ta fuskokin buƙatocinsa na jin daɗi, ko ɗaukaka
darajarsa da sauransu”.
Ma’anar Wada Hamza a Kan “Cuta” a Mizanin Awon Al’ada
“Cuta na nufin wani yanayi ko wani abu da
zai matsa wa rai ko ya kawo rashin gamsuwa a rayuwa”.
Idan muka lura da waɗannan
kalmomi da aka jama layi a sama su ne suka gina wannan ma’ana.
Yanayi: Wannan wani
hali ne da rayuwa kan shiga.
Wani Abu: Wannan yana
iya shafuwar duk wani abu mai rai da wanda ba ya da rai.
Matsa Wa Rai: Wannan ya
ƙunshi wani hali da ke kawo tarnaƙi, ko illa ga rai.
Wannan
ma’ana ta bayar da haske sosai a kan abin da ake kira “Cuta”. Amma kuma ma’anar
ta kalli gundarin aikinsa. Don kuwa ya ɗan rago wani abu da ba a
rasa ba, musamman cewar da ya yi “yanayi ko wani abu da zai matsa
wa rai ko ya kawo rashin gamsuwa a rayuwa”. Kenan sai wani abu mai rai
kawai zai iya kamuwa da cuta a tasa ma’anar.
A Bahaushiyar al’ada ‘Cuta’ na iya kama komai wato abin
da yake da rai da ma wanda baya da rayuwa.
Ma’anar Aliyu Bunza a Kan “Cuta” a Mizanin Awon Al’adar Bahaushe
“Cuta wata damuwa ce da ke shiga jikin halitta,
domin raunana lafiyarsa, ko kuma ta shafi zuciyarsa, ta fuskokin buƙatocinsa na jin daɗi, ko ɗaukaka darajarsa da sauransu”.
Damuwa: Damuwa wata
abu ce da kan shiga jikin halitta ko wani abu don ta raunana wannan halitta ko
abun ta fitar da shi daga hayyacinsa da aka san shi da shi a al’adance.
Halitta: Wannan kuma a
al’adance tana nufin duk wani abu mai rai da yake rayuwa a doron ƙasa. Halitta na iya kasancewa mutum, ko dabba, ko dangin
tsutsaye, ko ƙwari, ko tsirrai, ko dai
duk wani abu da Allah ya halitta kuma yake rayuwa a doron ƙasa ko a a cikin ruwa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin dutse, ko cikin dutse, da dai sauran wuraren da ake
iya samun halittun su rayu.
Raunana lafiya: Kalmar
‘Raunana’ ta samu ne daga ‘Rauni’ wato mai nufin wani abu da ke naƙasa rayuwa ko wani abu ya fitar da shi a cikin yanayi ko
halin da aka san shi da shi tun asali.
Zuciyarsa: Zuciya na nufin wata tsoka da ke cikin jikin
halitta.
Buƙatocinsa: Wannan
kalma ce da ta samo asali daga “Buƙata”, wato
tilo, idan buƙatar ta fi ɗaya za a
kira su da “buƙatu” ko “Buƙatoci”, idan kuma an mallaka su buƙatun ga wani kuma za a ambaci kalmar da “Buƙatocinsa”.
Idan muka yi la’akari da abin da shaihin malami Aliyu Bunza
ya faɗa a cikin wannan ma’ana da ya bayar za mu fahimci cewa,
ma’anar ta bayar da ƙarfi ga abin da yake da ƙudurin ganowa a bincikensa. Wato ya ta’allaƙa ma’anar ga bincikensa. Wannan kuma ba ya rasa nasaba da
ƙishirwar da ke cikin zuciyarsa ta ganin ya bayyana
matsalar da yake yunƙurin gudanar da bincike a
kai.
Mizanin Awon a Al’adar Bahaushe
Babban mizanin awon al’adar Bahaushe dai shi ne hankali
da tunani. A tunanin Bahaushe idan aka faɗi wata kalma yakan kalle ta
ciki da waje ya kuma ɗora ta sama da ƙasa da
tsakiya ya ga ko za ta yi aiki a wurin da ya ɗora ta ko
inda ya saka ta. Don haka idan aka ce wa Bahaushe “Cuta” zai duba kalmar ciki
da waje ya ga ko za ta iya tasiri a kan “halitta” da kuma “ƙira”? Ko ga “Halitta” kaɗai ta
dogara?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.