Talla Cikin Siddabaru


A wannan bincike mai taken Talla Cikin Siddabaru, ya yi tsokaci ne a kan abubuwa da dama, inda aka dubi ma’anar talla da ire-iren talla da kuma asalin kalma Siddabaru, da kuma ma’anar siddabaru. Aka fito da hikimomin da masu talla ke amfani da su domin jawo hankalin masu sayen hajarsu, aka duba abubuwan da ake amfani da su domin aikata siddabaru da waɗanda ke aikata siddabarun talla. Haka ma, wannan bincike ya duba ire – iren magungunan da masu siddabarun talla ke bayar wa, da amfani da ‘yan kore wajen ƙawata sana’arsu, da amfanin da ke cikinta har ma, da matsalolin ko haɗarin da ke tare da ita. Haka ma an duba siddabarun baka da amfani hoto da Dabbobi da makamantansu.

Talla Cikin Siddabaru

Shehu Adamu
Phone N0: 08038403450


Gabatarwa  
            Al’ummar ƙasar Hausa, al’umma ce mai ɗauke da ɗinbim hikimomi wajen gudanar da al’amuransu na rayuwar yau da kullum. Haka ma, a ɓangaren tallata hajarsu ba a bar su a baya ba domin, suna amfani da salo da dabaru domin jawo hankalin masaya. Ganin tasirin da  siddabaru yake da shi a cikin talla ya sa wannan bincike ya ƙuduri anniyar duba wannan fage don fito da wasu abubuwa domin nazari. Daga cikin abin da wannan bincike ya ƙunsa sun haɗa da  hanyoyi da suke amfani da su domin jawo hankali masaya da yadda suke gudanar da siddabaru da waɗanda abin ya fi faruwa a kan su.
            Amma, a wannan nazari, zai fi karkata ne ga masu siddabaru a fannin tallar magungunan gargajiya waɗanda ke cin kasuwanne birane da kuma ƙauyuka.

Dabarun Bincike
            Haƙiƙa akwai hanyoyi da dabarun gudanar da bincike da dama, sai dai ba kowace hanya ce ke ɓullewa ba. Kusan kowane aikin bincike yana da waɗansu hanyoyi da dabarun da ya fi dacewa a bi wajen gudanar da shi. A wannan nazari ma, za a bi hanyoyi da dabarun tattara sahihan bayanai ingantattu da za su taimaka wajen aiwatar da wannan aikin. Waɗanda suka haɗa da:
            Ziyatar ɗakunan karatu, musamman na jami’a da kuma na sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, domin duba muhimman ayyuka da suka haɗa da littattafai da kundaye da maƙalun da aka gudanar a tarukan ilimi da waɗanda aka wallafa da ma waɗanda ba a wallafa ba.
            Amfani da kafar yanar gizo don tattaro muhimman ayukkan da wasu suka yi da ke da dangantaka da wannan bincike.
            Ziyartar kasuwanne ƙauyuka da birane kamar Argungu da Bacaka da Yeldu da Kangiwa da Ambursa da Amagwaro da Daɗin Kowa da Kalgo da Dodoru  domin gani da ido,  ga masu wannan sana’ar da wannan bincike ya shafa.
Hira da masu gudnar da wannan sana’ar, da kuma waɗanda suka sayi maganin, da kuma wanda ake ganin za a iya samun wani bayani da zai taimaka wajen gudanar da wannan aiki cikin nasara.
Kadadar Bincike
            Da ka ji an ce wane ya wuce iyaka, to, shakka babu bai tsaya a inda aka ajiye shi ba. Duk wani aiki da za a gudanar a rayuwa, yana da kyau a tantance iyakar inda ake son mai yin aikin ya killace kansa a lokacin da yake gudanar da shi. Wannan bincike ya taƙaita ne ga siddabarun da ake aikatawa a cikin talla. Muhallin wannan bincike na iya zama ƙasar Hausa, sai dai a ɓangaren Arewacin Nijeriya, a ƙasar Kabi.
Ra’in Bincike
            An ɗora wannan bincike ne a kan Bahaushen ra’i na karin Magana mai cewa “Gonar baba da ita da Biri sai kallo”. Idan aka yi la’akari da wannan karin magana yana nuni ne a kan masu wannan sana’ar ba su fito ba sai da suka shirya, kuma duk wanda ya riski suna wannan aiki na siddabaru sai dai kallo kawai domin an wuce da tunaninsa,  ba ya da ilmin a kan abin da suke aiwatar wa. Da yawa wasu mutane ke yi musu ɗaukar sun yi ratse, amma su sun san abin da suke yi ba kaucewa ba ce, dabaru ne da hikima na ɓadda hankalin bami.   
           
Ma’anar Talla
Akwai ma’anoni daban-daban waɗanda aka samu daga wajen masana da manazarta dangane da ma’anar talla.
Jefkinsa, F (1996) cewa ya yi: “Talla hanya ce mafi sauƙi da tasiri wajen sanarwa domin sakawa a sayi wata haja”.
Ita ma Hajara da Liman  (1997)  maƙalarsu mai taken “The Use of Hausa Song in the Production of Radio Jingles in Kano” sun bayar da ma’anar talla da cewa ‘Talla na nufin faɗi in faɗi tsakanin kamfani da masu sayen haja, ko kuma al’umma.
Shi ma Malumfashi (2002) ya bayyana talla da cewa “ita ce a tallata wata haja ko yekuwa don wani bayani ko akida ko kuma idan ana so mutane su bar aikata wani abu akan yi talla”, ya ci gaba da cewa, kuma akan yi tallar ra’ayi, amma idan tafiya ta yi tafiya waɗanda suke tallata wannan abubuwa ko ra’ayi sun  fi kowa amfana fiye da waɗanda ake yi wa tallar.
Haka ma Gillian (1982) ya ce, “talla dabarar jawo hankali ne ga wani abu ko sanar da wani abu, ko kuma gaya wa mutum wani abu”.
Josef Bel-Molokwu (2005): Ya bayyana talla da cewa ita ce “nau’in sadarwa ta kafar yaɗa labarai dangane da wata haja ko wata manufa da wani ya ɗauki nauyin tallatawa” ko kuma fasahar sadarwa ta hanyar talla.
Akwai buƙatar a yi bayanin talla a bisa la’akari da muhimancinta, da abinda takan haifar, yaya take ko yaya ake yinta. Kalmar talla a turance wato “Adɓertising” ya ce an ƙirƙiro ta ne daga kalmar latin ta ‘Adɓertere’ wadda ke nufin ''jan hankali''. Masanin ya ce akan gina talla ne a bisa muhimman ginshikan da suka haɗa da:
Jawo hankali ga wata haja ko hidima ko manufa ta hanyar ilmantar da jama’a.
Sanya mutanen da ake nufi su amince da abin ta hanyar sanya musu sha’awarsa, da sanya mutane su mallaki abinda aka tallata musu.
Rike  nasarori da aka samu na amincewar jama’a da abinda aka tallata musu da cigaba da neman ƙarin wasu jama’ar.
A bisa la’akari da yanayin da ya gabata dangane da ma’anar talla da manufarta, muna iya fahimtar cewa dole ne a yi wa mutanen ƙasar Hausa musamman Bahaushe talla da Hausa.   



Asalin Kalmar Siddabaru
Hassan, D. (2012), cewa ya yi” asalin kalmar siddabaru an same ta ne bayan haɗuwar Hausawa da Larabawa, wato kalmar asalinta balarabiya ce.  A wajen Larabawa kalmar ta tana ɗaukar ma’anar kamar haka: yin duk wani aiki na hila da wayau, kuma mai tafi-da-hankali. Idan aka lura za a ga kalmomi biyu ne suka haɗu suka samar da kalmar siddabaru. Kalmomin su ne, sid ko sidda da dabbara ko dabaru. Abin da kalmomin sidda ke nufi kuwa, shi ne (sirri) wato a bayyana wani aiki na zahiri, amma a baɗini abin ba haka yake ba, wato abin bai auku ba, ita kuma kalmar “dabaru” abin da take nufi shi ne; dabaru ko dubara. Abin nufi a nan shi ne wayau wanda ake nufi da shi domin ɓatar da mutum bami, yau da gobe sai Hausawa suka haɗe kalmomin biyu wato “sid” da “Dabaru”, sai suka zama “Siddabaru”, ta la’akari da waɗannan ma’ana, sai masana suka baiwa kalmar siddabaru ma’ana zaunanniya ma’anar siddabaru:-
            Masana da dama, sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar siddabaru kamar haka:
            Abdullahi, (2000) cewa ya yi “siddabaru na nufin duk wani rufa-ido da aka yi domin a aiwatar da wani abu wanda a zahirinsa ya saɓawa baɗininsa, musamman a tunanin Bahaushe”.
            Adamu, (2013) ya kawo ma’anar siddabaru da cewa “Dabaru da cukurkuɗa abubuwa da rikirkita su, tare da ɓatar da bakin zare a rasa kasa gane lissafi. A wani lokaci kuma, siddabaru na nufin wayau da dabara wajen kare kai, ko kuɓutar da kai tare da amfani da sihiri da tsafi”
            Zailani, (2014) cewa ya yi; “Siddabaru abu ne da duk wani mai sana’ar gargajiya ke yi. Wato siddabaru wata ‘yar dabara ce da ake aiwatarwa wani lokaci da ‘yan sihirce-sihirce don ƙoƙarin fito da wani abu ko kariya ga wani abu, tare da jan hankali a tare da shi”.     
            Saboda haka, za a iya kallon siddabaru a matsayin wani rufa ido ne da ake yi wa mutane don aiwatar da wani abu mai ban mamaki, wanda a zahiri ana gani, amma a ɓoye abin ba gaskiya ba ne, misali kamar masu sana’ar cin kasuwar sama.
Talla Cikin Siddabaru
          Talla ce da masu maganin gargajiya ke baje  kolin tunaninsu, domin jawo hankalin mutane zuwa sayen sana’arsu ta amfani da hikima da dabara na siddabaru.  A wannan ɓangaren, za mu duda wasu daga cikin talla, ɗaya bayan ɗaya da ake gudanar siddabaru wajen aiwatar da ita.
Tallar Kore
            Wannan talla ce da mai magani ke shirya wa da wasu mutane kafin ya fara gudanar da tallarsa, domin su taimaka masa wajen sana’arsa, zai yi amfani da su a matsayin waɗanda bai sani ba, zai ba su umurni a kan abin da yake so su aikata a lokacin da yake dandali. Wannan ya danganta da yadda suka shirya, duk abin da za su yi abu ne da zai jawo hankalin mutane zuwa ga sayen tallarsa. Akwai waɗanda za su nuna sun taɓa amfani da maganinsa yana aiki, a ƙara basu wani. Akwai waɗanda su za su fara sayen maganin, saboda ga al’ada da mutane sun ga wani ya fara saye, sai ka ga kamar magani mutane sun yi ciri suna ta saye, tau da an samu wanda ya fara saye shi ke nan.
Tallar Gwaji
            Wannan wani salon talla ne da mai magani ke gwada maganinsa a gaban ‘yan kallo, domin nuna wa mutane cewa maganinsa karta’un na, ya jawo hankalinsu su saya, tare da amfani da ‘yan kore.
Misali. A kasuwar Bachaka, ƙaramar hukumar mulki ta Arewa, mai hedikwata Kangiwa, wani mai bada maganin bi-ta-zai-zai ya yi tallar maganisa tare da gwaji gaban ‘yan kallo, inda ya kira wani yaro ya bashi wata laya, ya ce ya duba cikin dandalin duk yarinyar da ya gani ya je ya kira ta. Yaro ya ga mata uku ya je wajen ɗaya ya kira ta biyo shi cikin fili duk inda yaje sai yarinya ta bishi, sai fili ya ɗauki kuwwa. Bayan ya gama wannan gwaji sai mutane suka yi ciri suna ta sayen maganin, sun ga zahiri.
Bayan ya gama tallarsa kowa ya waste, da aka yi bincike, sai aka gane ashe waɗannan matan uku ‘ya’yansa ne shi ya zo da su a matsayin ‘yan kore.
Talla Da Addini
            Wannan talla ce, da mai talla ke amfani da wa’azi na addini, tare jan ayoyi da hadisai, yana cewa Allah ya ce, Annabi ya ce, tare da Alaramma mai jan baƙi, amma duk a baki kawai. Yana yi ne domin ya samu amincin mutane, sai shi biyo da tallar maganinsa, wanda akasari suna ci da addini ne, ba gaskiya ba ne. Sun zaɓi wannan hanya ce ta damfara ganin cewa ta fi sauƙi, sanadiyar mutane suna yarda da masu wa’azi.           
Yadda Suke Aikata Siddabaru
            Masu sayar da magungunan gargajiya ta hanyar siddabaru suna amfani da hanyoyi daban – dabam domin aikata siddabarunsu kamar yadda za mu duba wasu daga cikin hanoyin da suke amfani da su.
Siddabaru Na Magana
            Masu talla, musanman ta magani, waɗanda ke da ilmin addini daga cikinsu  suna amfani da kalamai masu ratsa zukata domin jawo hankalin mutane su karkata zuwa gare su, ta amfani da tarihi da ƙissoshin Annabawa da wasu labarai da suka shafi addinin Muslunci, masu ɗauke da abin al’ajabi da bayar da tausayi ko da labarin ba na gaskiya ba ne, tare da hargowa da barazana kamar abin a gaba gare su ya faru. Suna amfani da ƙissa Annabi Suleiman da ta Annabi Musa, waɗanda duk suna ɗauke da abin al’ajabi a cikin su. Kafin ƙiftawar ido mutane sun cika dandali har da turereniya da juna. Dabarun da suke amfani da su a wannan ɓangaren shi ne lokacin da duk suka fara bayar da labarin wani abin al’ajabi, sai su katse, su ci gaba da wata haraka ta daban domin cin lokaci kawai, shi kuma mai saurare yana nan yana jiran ya ji ƙarshen labarin, bayan an ɗauki lokaci kuma sai a ci gaba da labarin. Haka suke yi suna janyo hankalin mutane, har su fara tallata hajarsu, su fara bayyana laƙanin da suke bayar wa da kuma goron sadaka da ake bayar wa domin karɓar laƙani. Haka ma, suna amfani da ambatar sunayen manya garuruwa, kamar Kaduna Kano Bauchi da sauransu, domin ƙara jawo hankalin masaya.
Siddabaru Ta Amfani Da Hotuna
Masu talla suna amfani da hotuna domin kiran kasuwa, wani salo ne na siddabaru ta amfani da hotunan wasu mutane da suka gabata, kuma suka yi fice a zamaninsu, waɗanda sai dai aji tarihinsu cikin Al’ƙur’ani mai girma, amma sai mai talla ya bayyana cewa yana da hotunansu, domin ya san cewa duk wani Muslimi yana muradin ganin hotunan waɗannan  mutane. Abin lura a nan shi ne, ko da ba gaskiya ba ne ba ya da waɗannan hotuna, zai ci gaba da surutu yana jan ra’ayin masu saurare da cewa zai fitar hotunan kowa ya gani, sai ya fitar da su amma a dunƙule ba zai buɗe ba, sai ya fara tallar maganinsa, sai ƙarshe idan da gaskiya yana hotunan zai buɗe wa mutane su gani, idan kuma babu sai ya shashantar da maganar, har ya ci kasuwarsa ya watse  ba wanda zai ga hotunan. Amma a mafi yawan lokuta ba su da hotunan, dabaru ne kawai na kiran kasuwa. Suna da’awar suna da hotuna na kamar:
1.      Fir’auna
2.      Ƙaruna
3.      Hamana
Siddabaru Ta Amfani Da Dabbobi
Siddabaru ne da masu tallar magunguna ke yi ta amfani da dabbobi domin jawo hankalin jama’a zuwa ga hajarsu, ko da ba ta shafi maganin da suke  bayar wa ba. Saboda Bahaushe ya yi imani a duk lokacin da ya ga wani mutum yana sarrafa wata dabba da ba ta gida ba, tau wannan mutum yana da magani ko ya shahara. Ta haka ne, masu magani ke amfani da dabbobi domin su nuna wa jama’a cewa sun shahara, a ɓangaren bayar da taimako. Suna wasa da dabbobin a dandali jama’a na kallo. Suna amfani da dabbobi kamar su:-
1.      Maciji.
2.      Kada.
3.      Kura.
4.      Biri.
Siddabaru Ta Amfani Da Sassan Jikin Dabbobi
Wannan wata hanya ce da masu tallar magani ke baje kolin sassan manyan dabbobi, domin neman jama’a zuwa ga hajarsu, domin lokacin da duk mutane suka ga mai magani ya kasa sassan jikin manya dabbobi, za su yi imani da cewa, sha yanzu magani yanzu, sai mutane suka riƙa ribibi, domin sayen magani, ko da ba na gaskiya ba ne, waɗannan sassan dabbobi su suka jawo mutane ga hajarsa. Suna amfani da sassan jikn dabbobi kamar su :-  Hauren Giwa, Kan Gwamki Kitsen Zaki Takon Giwa Fatar Kura, Fatar Kada da sauran su.
Siddabaru Ta Amfani Da Kiɗa Da Waƙa
            Kiɗa tamkar jinni da tsoka ne, ga rayuwar Bahaushe, sanadiyar haka ne masu tallar magani ke amfani da kiɗa, domin janyo ra’ayin mutane zuwa ga abin da suke sayar wa. Suna kiɗa da tafi da hannu da waƙa, lokacin da wanda ke cikin kasuwa ya ji kiɗa na tashi da waƙa, zai zo ya ga abin da ke faruwa. Suna amfani da ‘yan kallo domin tafi da amshin waƙa. Suna waƙa kamar haka:-
Haba! Yara kun ɗan ban taɓi,
   Haba! Cali Baturen ganga,
   Duk wanda bai taɓa ba,
   Ubansa bai yi tsawon batur ba,
   Amma ya ɗara jaki bura.
Haka suke yi suna janyo hankalin mutane, lokacin da suka ga cewa mutane sun taru, sai su fara tallata hajarsu.
Siddabaru Ta Amfani Da Agogo
            Wannan wata hanya ce, inda mai magani ke amfani da agogo sababbi uku ko huɗu ya dunƙule cikin takardar nama ko jarida, wasu kuma a saka minti a ciki, a cika akwati da su. Lokacin ya riga ya shirya da yaransa watau ‘yan kore, duk wanda ya saye magani a ba shi ɗaya, ‘yan koren za su fara saya, idan sun saya za a buɗe takardar gaban ‘yan kallo da an buɗe za a ga agogo sabo hul. Da yaransa uku ko huɗu sun saya, sai ya ba da dama ga duk mai saye. Lokacin da mutane za su fara saya sai ya sanya sharaɗi idan ka saya ka ɗauki dunƙulallar takarda ɗaya, ka da ka buɗa ka saka cikin aljihu sai ka tafi gida, lokacin suka tafi gida sai su tarar da minti.
Siddabaru Ta Amfani da Kendur Ko Tunfafiya
          A wannan ɓangaren masu siddabaru sun amfani da kendur ko ruwan tunfafiya domin aikata siddabaru, wannan dabara ce da suke amfani da ita inda suke rubutu da kendur ko ruwan tunfafiya a farar takarda, kasancewar kendur ko ruwan tunfafiya farare ne ko an yi rubutu a kan farar takarda ba za a gani ba. Idan sun yi wannan rubutu idan aka zo dandali ko kasuwa sai su sami cikin ‘yan kallo su kira ɗaya, su ba shi takardar domin ya goga a kan sa lokacin aka ba shi ita ba ta da rubutun komi, amma da ya goga ta a kai sai a ga rubutu ya bayyana, sai ‘yan kallo su yi ta mamaki.
A ci wawa a watse
          Wannan wata dabara ce da suke yi, lokacin da aka kammala talla, ragowar maganin za a kada farashinsa, domin a samu masaya da yawa.
Misali: Kamar wanda muka ci karo da shi a Karar Argungu. Bayan ya kammala tallarsa sai ya ce akwai wanda zai fanshi Al-ƙur’ani mai girma, kowa ya bada duk abin da Allah ya hore mai. Sai yara Almajirai suka yi ta bada kuɗi, wasu ma kuɗin mutane ne domin ‘yan talla ne, bayan ya ƙare amsar kuɗi sai ya ce kowa ya duƙa a yi addu’a  aka sanya su cikin addu’a, kowa ya watse. Har da maganin ba a basu ba.       

Taimakon Da Suke Bayar wa
            Masu tallar magani ta amfani da siddabaru suna bayar da taimako ne na magungunan neman suna ko buwaya, ba magani ne na neman waraka ba. Abin nufi, akasari ba sa bada maganin warkar da wata cuta da ake fama da ida, sai dai maganin bajinta, kamar su.
1.      Bi-ta-zai-zai
2.      Ƙago/Sagau
3.      Baduhu
4.      Tsari
5.      Mallaka
6.      Ilimi
Abubuwan Da Suke Bayar wa A Matsayin Magani
            Suna amfani da abubuwa masu jan hankali, a matsayin abubuwan da suke bayar wa, su yi masu ƙawa ko ado, tare da bayar da ‘yan sharuɗɗa waɗanda ba za a iya cika su ba, sai bayan an waste daga dandali. Suna bayar da abubuwa kamar:-
1.      Hatimi.
2.      Laya/Guru
3.      Karho
4.      Takarda naɗe da zare
5.      Magini cikin kwalba.
Wurin Da Suke Aikata Talla
            Masu tallar magani, suna amfani da wurin da aka fi samun cinkoson mutanen ƙauye masu cin kasuwa, domin baje hajarsu, ganin cewa mutanen ƙauye sun fi sauƙin kai. Suna amfani da wurin sayar dabbobi watau Kara da kuma Masallacin juma’a ga masu talla da ta shafi addini. Dabarar da suke amfani da ita, idan suka ci kasuwa, sai su   ɗauki dogon lokaci ba su koma ba, saboda ba su da gaskiya.
Muhimmancin Siddabaru
            Bahaushe yana amfani da siddabaru, domin nuna hikima da dabara da ƙwarewa a kan abin da ya sa kan sa, kuma ya zama tamkar hanya ta nuna al’adunsa masu ɗauke da kaifin basira. Muhimmancin siddabaru sun haɗa da waɗannan:
i.                    Siddabaru yana ƙara ɗaukaka da kwarjini a idon jama’a, domin mai aikata shi ana yi masa wani kallo na musamman.
ii.                 Siddabaru yana taimaka wa wajen samar da magungunan gargajiya, domin yana ƙara amana cikin zukatan masu karɓar magani.
iii.               Siddabaru yana ƙara wa talla armushi da sha’awa, ga masu tallar maganin gargajiya.
iv.               Siddabaru yana ƙara wa al’adar Bahaushe daraja a idon sauran ƙabilu, domin yana saka tsoro a zukatan waɗanda ba muhallinsu ba ne.
v.                  Siddabaru yana adana Adabin Bahaushe da yaɗa shi.
Illolin Siddabaru
            Siddabaru yana da illoli ga rayuwar Bahaushe, kasancewar akwai abubuwan da ake cin karo da su, da suka saɓa wa addinin musulunci. Illolin sun haɗa da:-
i.                    Hanya ce, ta saɓa wa addinin Muslunci saboda ba gaskiya ba ne, domin addinin Musulunci yana umurni da gaskiya da kuma hani da ƙarya.
ii.                 Kasancewar ana aikata damfara da siddabaru, ya zama cutar wa ga mutane.
iii.               Akasarin magungunan da masu siddabaru ke bayar wa ba na ƙware ba ne, abin nufi ba a cika samun biyan buƙata ba.
iv.               Ba kasafai mutane ke yarda da siddabaru ba yanzu, saboda sun gano ƙarya ne, ba gaskiya ba ne.
Haɗarin Da Ke Tattare Da Wannan Sana’ar
          Masu gudanar da wannan sana’a ta talla tare da amfani da siddabaru suna  fama da ƙalubale, kasancewar sana’ar akwai damfara a ciki, saboda idan wasu suka sayi magani suka yi amfani da shi bai yi aiki ba, idan suka haɗu da mai maganin ba za su ƙyale shi ba, za su ɗauki mataki.
Misali: irin wannan ta taɓa faruwa a kasuwar Dakin Kowa masu wannan sana’ar suka damfari wani kuɗi naira dubu saba’in bayan sati biyu sai ga su sun dawo. Dawowar su ke da wuya sai ‘yan uwan wannan mutane suka hau su da duka, da ƙyar a cece su a hannu mutane. Ire-iren waɗannan sun sha faruwa a wurare daban-daban. Shi ya sa suke dabarar idan suka ci kasuwa suna daɗewa ba su koma ba sai sun ɗauki lokaci mai tsawo, lokacin mutane sun manta.   
Sakamakon Bincike
Wannan bincike mai taken talla cikin siddabaru, ya gano cewa siddabaru ba tsafi ba ne, ba magani ba ne illa tsabagen wayo, da basira da hikima da masu gudanar da shi ke amfani da shi, domin kauda tunanin ‘yan kallo. Kuma an gano cewa masu talla cikin siddabaru ba magani na warkar da wata cuta da ake fama da ita suke bayar wa ba, face maganin bajinta da buwaya da neman biyan buƙata. Binciken ya gano abubuwan da suke aikata siddabaru da su, domin jawo hankalin mutane zuwa ga sana’arsu.  A wannan binciken an gano, siddabaru yana da muhimmanci da kuma illoli ga rayuwar Bahaushe.
Wannan bincike ya gano cewa wannan talla da masu magani ke gudanar wa tare da siddabaru, tana ja baya ko kuma muce ta yi kusan zama tarihi a ƙasar Hausa, saboda ƙaramci masu gudanar da ita, da kuma wayewar kan mutane a kan siddabaru.

Kammalawa       
      Wannan bincike ya yi bayani a kan siddabaru da masu tallar magani ke yi a ƙasar Hausa. Zai taimaka wa ɗalibai masu nazarin wannan fanni da samun wani haske a kan yadda masu tallar magani ke nuna hikima da dabaru da kaifin basira, domin jawo hankalin jama’a zuwa ga kasuwancinsu. Wannan siddabaru yana ɗaya daga cikin abin da ke ƙarawa tallar armushi da sha’awa.

Post a Comment

0 Comments