Ticker

Adabin Siddabaru Tsakanin Na Hakika Da Na Tarihihi


Idan aka kalli kalmar siddabaru ta fannin Ilmi kuwa, masana al’ada da rayuwar ɗan Adam sun bayyana ta a fuskoki daban-daban. A wata ma’ana ta isɗilahi kalmar siddabaru tana nufin dabaru na cukurkuɗa abubuwa da rikirkita su tare da ɓatar da bakin zare har a kasa gane lissafi. Wani lokaci kuma tana nuni a kan wayo da dabara wajen kare kai ko kuɓutar da kai tare da yin layar zana. Wasu kuma suna ganin, siddabaru ya ƙunshi yin surƙulle da ɓatar da abubuwa ko a gudanar da wasu ayyuka na ban mamaki.


Adabin Siddabaru Tsakanin Na Hakika Da Na Tarihihi

Umar Buba
07030156552

Gabatarwa
Dukkanin rayuwar Bahaushe wanda ta ƙunshi tun daga zuwansa duniya har zuwa koma ga mahaliccinsa, tana ƙunshe da wasu abubuwa da ake ganin su ne al’adunsa da ɗabi’unsa da tunane-tunanesa da tarihinsa da sana’arsa da harshensa wanda da shi ne ake gane halin da yake ciki da muhallinsa da addininsa da duk wani abu da ya shafi rayuwarsa ta duniya da ta zamani.
Wannan ya shafi abin da yake gudanarwa, ko ya gudanar, ko kuma zai gudanar nan gaba, cikin sauran rayuwarsa. Mafi yawan wannan rayuwa ta yau da kullum, mai kyau da marasa kyau tana ƙunshe da wasu abubuwa masu rikici da tayar da hankali da baƙin ciki a ɓangare ɗaya, a wani ɓangare kuwa tana ƙunshe da haƙuri da juriya da murna da farin ciki da hutu.
A taƙaice, a kan yadda aka samu irin waɗannan al’adu masu tafiya kafaɗa da kafaɗa da rayuwar Bahaushe. Sannan a ga yadda shi adabin ya samu har ya karkasu a dalilin hijirarsa daga wani wuri zuwa wani da kuma wucewa da tasowa tsararraki waɗanda ake ce ma lokacin gargajiya. Lokacin da komai a gargajiyance ake yin sa shekaru da dama da suka wuce. Haka kuma haɗuwarsu da wasu al’adu baƙi na Larabawa da Turawa ya sa an samu sauyin rayuwa ta zamani, wadda ta kawo halayyar rayuwa wanda ta samar da wata halayyar raywa ta zamani, wadda ta kawo rubutu da karatu na ajami da boko. Kamar dai yadda manazarta suka ambace ta da adabin zamani, wato rayuwar Bahaushe wadda take a rubuce da sauransu.
To! Kowane ɓangaren adabin an yi ƙoƙarin bayyana shi dalla-dallada fitar da matsayinsa a halin rayuwar Bahaushe duk da yake an riga an daddaƙi fagen nazarin adabi, kamar yadda masana irin su Ɗangambo, (1984) suka tankaɗe da raraye tsarin fasalolin adabin Hausa.

Dabarun Bincike
Da yake ana son yin nazarin ne kan wani ɓangare kamar adabin siddabaru tsakanin haƙiƙa da tarihihi, ana buƙatar da a tara bayanai da suka jibinci wannan gurbin gaskiya da kuma waɗanda ke magana akan adabin siddabaru tsakanin haƙiƙa da tarihihi shi kansa. Ta haka ne za a samu damar da za a cimma manufa.
Saboda haka ne ma aka ƙudurta yin amfani da dama kamar haka:
1.      Tattara bayanai daga littafai da aka wallafa waɗanda suka shafi bigiren binciken. Watau daga ɗakunan karatu na makarantu; ko na gwamnati da ke garuruwa ko kuma a samo a kasuwa da sauransu.
2.      Nazarin kundayen binciken da aka yi don neman digirin farko ko na biyu ko na uku ko wasu muƙalu da aka gabatar duk a manyan makarantun Kwaleji da Jami’o’in ƙasar nan da kuma waje.
3.      Yin hira da tattaunawa da neman bayanai daga wasu masana da manazarta da mawallafa littatfai da suka danganci muhallin nazarinmu.
4.      Amfani da na’urar ɗaukar hoto. Ko ta ɗaukar murya ko ta hanyar sauraron radiyo ko kallon talabijin don tattara bayanai a kan aikin daga manya har zuwa ƙanana, maza da mata, na abin da ya samu.
5.      Tambaya kai tsaye ko a taƙaice ko kuma sauraron hirar wasu, a gefe guda, kan abin da ya shafi muhallin Nazarinmu a ko’ina ta samu.

Ra’in Bincike
Wannan bincike ya dogara ne kan ra’in son banza tsakanin jama’a. wannan ra’in yana bayani aa kan sakamakon yadda `yan siddabaru suke hulɗa da jama’a. daga cikin wannan hulɗa da `yan siddabaru ke yi tsakanin jama’a. kamar yadda ɗan siddabaru zai cewa mutum ya na da naira ɗari a yi masa naira dubu (1,000).
Wannan ra’i namu za mu ɗora shi a kan son banza da jama’a keyi da sauransu.
Ra’i na nufin ganin dama, ko ra’ayoyi kamar yadda muka ambata a koyaushe ya yi wajibi ga mai bincike ya yi wa aikinsa shimfiɗa da ta dace da shi, domin ta yin haka ne za a ɗora aikin bisa alƙiblar madaidaiciya. Wannan ne ya sa muka soma tsokaci kan ra’in da za mu ɗora aikin.
Kadadar Bincike
Wannan shi ne iyakar da aka ɗibar wa wannan aikin bincike ba ta wuce ta tattauana matsayin Adabin Siddabaru tsakanin haƙiƙa da tarihihi. Sai dai domin taƙaitawa a mayar da hankali wajen tattaro bayanai game da matsayin siddabaru a idon Bahaushe. Saboda haka za a tattauna ma’anar adabi da kuma ma’anar siddabaru, sannan da asalin siddabaru da siddabaru na ƙasashe da inda ake aiwatar da siddabaru da makamantansu da yadda ake gudanar da su da dai sauransu.
Ma’anar Siddabaru
A ɓangaren lugga kalmar siddabaru kamar yadda Bargery (1934:988 – 946) ya nuna a katssaki: Siddabaru Kn! Siddabaru, daidaitacciyar Hausa. Siddabaru na nufin dabo, shi kuma ƙamusun Hausa (CNHN, 2006:395) ya nuna kalmar siddabaru ita ce, wasu dabaru na sihiri waɗanda suka wuce fahimtar hankalin ɗan Adam. Sannan kuma kalmar siddabaru tana iya zama dabo ko rufa-ido.
            Idan aka kalli kalmar siddabaru ta fannin Ilmi kuwa, masana al’ada da rayuwar ɗan Adam sun bayyana ta a fuskoki daban-daban. A wata ma’ana ta isɗilahi kalmar siddabaru tana nufin dabaru na cukurkuɗa abubuwa da rikirkita su tare da ɓatar da bakin zare har a kasa gane lissafi. Wani lokaci kuma tana nuni a kan wayo da dabara wajen kare kai ko kuɓutar da kai tare da yin layar zana. Wasu kuma suna ganin, siddabaru ya ƙunshi yin surƙulle da ɓatar da abubuwa ko a gudanar da wasu ayyuka na ban mamaki.
            Domin haka, siddabaru yana nufin yadda za a yi wasa da hankalin mutum har ya yi mamakin yadda abubuwa ko ayyuka suka faru. A wannan madosa za a daɗa da azanci da dibilwa da rufa-ido da surƙulle da dabo da sihiri da saɓa al’ada da makamantansui waɗannan abubuwa. Ta waɗannan hanyoyi ne ake yin siddabaru da cakuɗe-cakuɗen abubuwa domin a gigitar da hankalin mutane ta yadda duk mutum ya kai da wayo ko ganewa sai an shigar da shi duhu.
Siddabaru A Matsayin Ilimi
            Idan aka yi la’akari da yadda ake bayyana ma’anar ilimi, musamman kamar yadda Ƙamusun Hausa ya nuna, Ilimi shi ne sani ko ganewa ko fahimta (CNHN, 2006:205), to, siddabaru wani limi ne na musamman wanda ba za a iya aiwatar da shi ba sai an fahimci dabara da hanyoyin gudanar da shi. Dabaru na gigita da hankali da cukurkuɗa tunanin mutum edole ne sai an biɗi sani na yin su, in ko ba haka ba, sai a faɗa rijiya da baya.
            Ilimin siddabaru ya ƙunshi hanyoyi na amfani da wasu surƙulle da rufa-ido da ɓad-da-sau da fyauce hankali da tafi-da- gani domin a cimma magaryar zakuɗa hankalin mutum a dame masa lissafi. Ta haka siddabaru zai kai ga samun sakamako a ganar da shi.
            Ilimin siddabaru har wa yau, babu wata hanya guda ɗaya rak wadda ta zama dole sai ta kanta za a iya aikata shi. Akwai hanyoyi da yawan gaske waɗanda kuma za su iya bambanta a tsari da yanayi na tafiya da su, wasu hanyoyin ma mutum zai gan su kamar mafarki.
Tarihin Ilimin Siddabaru A Al’ummar Hausawa
            Allah mai girma da ɗaukaka, Ya hore wa al’umma hanyoyi na sarrafa tunani su dinga sama wa kansu hanyoyi na sarrafa tunani su dinga sama wa kansu dabaru na zaman rayuwa. Haka kuma ya laƙanta hikimomi da azance-azance waɗanda suke yi wa al’umma jagoranci wajen tafiyar da tunanin nasu da yake ba su damar ƙullna da kwance abubuwa.
            Siddabaru da sihirce-sihirce wasu abubuwa ne waɗanda kamar yadda ake nuna a baya, suke gudana ta hanyar tunani da azanci. Ire-iren waɗannan abubuwa da tunani yake yi wa jagoranci sukan zama ta wasu ga al’umma, kuma su kasance sarƙe da rayuwarta tun a tumun fari.
            Olomom siddabaru a wajen Hausawa abu ne mai daɗaɗɗen tarihi, wanda Hausawa suka same shi daga haujin kansu tun a rayuwarsu ta zaman farko, tun a rayuwa ta maguzawa, Hausawa a mabambantan hanyoyimsu na tunani da samar da abubuwa da za su ba da mamaki ko su ɗaga hankali ko shashantar da matakan lura da tantancewa waɗanda aka ɗauka siddabaru ko sihiri ne.
            Tun a lokacin da Hausawa suka fara farauta ta tudu da ta ruwa da yawace-yawace a dazuzzuka suna neman `ya`yan itatuwa da tariyar namun daji gaba-gaba domin samun abinci suka sami dabaru na siddabaru da sihirce-sihirce na kariyar jiki. Ta haka suka fara sama wa kansu matakai na kare rayuwarsu daga wasu hallittu waɗanda suka fahimci masu cutarwa ne a gare su.
            Haɗuwar Hausawa da aljannu ta hanyar addinin gargajiya na bautar Iskoki da dodanni ya ba Hausawa wata mayalwaciyar dama su daɗa bunƙasa matakai na yin siddabaru, musamman yadda wasu Iskoki suke taimakawa Hausawa wajen tafi-da-gani na mutane.
            Ta haka bori da tsafe-tsafe da sauran abubuwan da suka shafi addinin gargajiya wajen aikata abubuwa masu ba da mamaki.
            Hulɗoɗin rayuwar Hausawa a wajen tafiyar da abubuwa ne buƙataun rayuwarsu kamar sana’o’i na rayuwa da wasanni na kyautata jiki da ƙwaƙwalwa da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe na yi wa rai yayyafi da yin abubuwan siddabaru da sihiri da kau-da-ido. A kowane rukuni daga cikin waɗannan rukunoni na tafiyar da rayuwa akan sami wasu mutane waɗanda a ayyukansu za su yi ta ƙoƙarin yin wasu abubuwa domin su ba da mamaki ko don burgewa ko don fito da ƙwarewarsu da nuna matuƙar azanci nasu. A wajen yin hakan ne suke tafiyar da hankali na mutane ko su sace fahimtarsu ko ganewarsu, daga nan ne asalin siddabaru.
            Duk da zuwan addnin Musulunci a ƙasar Hausa da shiggar sa lungu-lungu, siddabru ya shiga a tunanin wasu Hausawa waɗanda suka ci gaba da gudanar da abubuwa na mamaki a kaikace wasu lokuta har da neman taimako daga aljannu wato Iskoki.
            Ma’amalar Hausawa da magungunan gargajiya domin neman waraka daga cututtuka da bokaye da `yan bori da sauransu suka yi fice wajen badawa, ita ma hanya ce wadda ta daɗe da yin dabdala ta yin siddabaru.
            Waɗansu masu ba da nagungunan sun ɗauki siddabaru wata hanya wadda za ta ƙara sanya a amince da magungunan da suke ba dawa. Ta haka sai su dinga yin abubuwa na ɗaga hankali da kawar da tunani amma ta hanyar siddabaru.
            A dunƙulle, ilimin siddabru, ilimi ne wanda Hausawa suka ƙirƙire shi da kansu tun a lokacin daɗaɗɗe na rayuwarsu ta garagajiya sannan ya ci gaba da bunƙasa a lokacin da Hausawa suka dinga nuna dabaru ba buwaya da nuna ƙwarewa da kuma nuna fififkon fasaha da gwaninta tsakanin masu ayyukan bajinta ko sana’o’i da sauran mu’amaloli.
            Haka kuma siddabaru ya ƙara samun ranar shanya gari a lokutan da Hausawa suka dinga hulɗoɗi da baƙin al’ummu har suka sami fannoni ilimi iri-iri har gami da ilimi na tafi-da-hankali, musamman bayan zuwan addinin Musulunci da fahimtar ilimin Larabci da na shari’a. ga kuma zuwan Turawa da Indiyawa da Fulani da Bare-Bari da Yarbawa da Igbo da sauransu.
            Bayan Hausawa sun yi nisa cikin wannan cuɗanya da ma’amaloli kuma sun sami ilimi na addinin Musulinci da na boko, sai suka shiga rarrabe siddabru a matsayin dabaru na kawar da ido ko rufa-ido ko tawalwaniya ko sihiri ko tsafi ko surkulle ko kuma wasu dabaru na ɗauke hankalin mutum.
Ire-Iren Siddabaru na Hausawa
            Akwai hanyoyi daban-daban, kamar yadda aka nuna a baya waɗanda ake bi ta kansu ana gudanar da siddabaru a al’ummar Hausawa. Daga cikin ire-iren hanyoyi na yin siddabaru a wajen Hausawa akwai:
1.      Sihiri ko tsafi
2.      Rufa-ido
3.      Surkulle
4.      Damfara
5.      Bori
Adabi da Samuwarsa
            Idan muna so mu ba da bayani kan samuwar adabi to ya dace mu yi tsokaci a kan yadda mutum ya fara rayuwa a bayan ƙasa, ta hanyar mazauninsa. Wannan zai ba mu haske da samuwar al’umma da adabinta.
            Da farko dai za mu yi bayanin saukar mutum bayan ƙasa wanda ake dangantaka da tarihin saukar kaka mutane baki ɗaya, wato Annabi Adamu (AS), a wajen wani dutsi wanda a dalilin saukarsa a can, ake kiransa da ‘dutsin Adamu’ a yankin Jidda ta ƙasar Saudiya, wurin da masana yankuna ƙasashe ke ce ma ‘gabas ta tsakiya’. Daga nan ne ake nuna cewa, duk kowace ƙabila ta duniya ta samo asali.
(Malumfashi, 2000) ko a ina ta samu kanta kuwa kuma ko’ina take gudanar da rayuwarta. Wannan shi ne adabinta a cikin duniyar nan.
            Ana iya hasashen adabi ta ɓangarori da dama. Ɗan Adam dai yana zaune a bayan ƙasa a kan itatuwa da duwatsu da kuma a cikin ƙogonni da hakukuwa tare da namun daji. Daga nan sai tun yana zamansa shi kaɗai har ya samu iyali, ya kuma gina al’umma ta shi ta hanyar aure tare da yaɗa zuriya. Da ya haɗu sai ya yi yaryajejeniya da `ya `uwansa da abokan halittarsa maza da mata, don zaman tare da juna. (Gusau, 1993). To! Ko ma ya ya aka yi dai, muna iaya cewa, a duk wurin da al’umma take rayuwa to a nan ne adabinta yake. Watau rayuwar al’umma mai kyau da mara kyau shi ma adabinta ne. (Malumfashi, 2000). Ana iya hasashen wannan adabi ta hanyar tatsuniyoyi da labaran al’ummomin Indiyawa da Jafanawa da Girkawa da Romawa da labaran Farisawa da ke cikin littafan tarihinsu da na adabinsu. Saboda haka, tatsuniyoyi da labarai sun daɗe suna yawo a matsayin adabin baka a cikin al’ummomi daban-daban.
            Haka kuma suna sauyawa ne dalilin ƙaura da al’ummomi ke yi suna sauya muhalansu. A cikin sauyin ne ma suke haɗuwa da sabbin abubuwa da a dab a su san sub a, tare da haɗuwa da kuma wasu baƙin al’ummomi. (Ɗangambo, 1984). Waɗannan abubuwa su ne ka shiga cikin labaran da tatsuniyoyi da zantukansu na baka. Su ne kuma ke ƙara masu aramashi da wani salon nuna halayyar rayuwa don amfani da wasu abubuwa da ke kewaye da su a cikin tatsuniyoyi da labaran nasu.
Samuwar Adabin Hausa
            Kamar yadda al’ummomin duniya da yawa ke rayuwa a wuraren da suke zaune, haka su ma Hausawa suke yin tasu rayuwar. Kamar yadda adabin kowace al’umma ke bin ta, su ma Hausawa dabinsu ke bin su (Gusau, 1985).
            Duk da cewa akwai ra’ayoyi da dama da ke hasashe game da farkon zaman Hausawa amma mafi karɓuwa (Malunfashi, 2000) shi ne yadda Hausawa suka kasance suna zuwa suna komowa wurare da dama, suna farauta da tsintar `ya`yan itatuwa, sannan daga baya har suka kama noma da suka samu zama tare da yin iyali mai yaɗo, wanda ta haka ne aka samu yaɗuwar zuri’a da harkar ɗaukar gabata a tsakaninsu. (Umar, 1987). Da haka ne kuma aka samu shugabanci ta hanyar gwarzantaka a fagen yaƙi ko wajen noma ko ta wajen sana’o’in dogaro da kai da sauransu.
            Wannan shugabanci ya kasance na gida ne ko na sana’o’i ko na addini, watau bautar Iskokki da tsafe-tsafensu da sauransu. To, ta haka ne aka samu al’umma tsayayya mai dogara da kanta.
            Idan mka dubi fuskokin samuwar adabin Hausa, za mu ga cewa adabin ya na danagane da mazauninsu da halayyar rayuwarsu ta yau da kullum. Adabin kuma ya samo asali ne tun lokacin da Bahaushe ya fara Magana har kuma a fahimce shi. Saboda haka, a nan ma muna iya cewa duk inda Bahaushe duk ya je to, tare da adabinsa yake tafiya, kuma yawanci ginin adabin da siffarsa, ta yadda ake bayar da shi, duk iri ɗaya ne. misali, tatsuniyar Ruwan Bagaja yanayi ɗaya aka bayar da ita al’ummar Bantu a ƙasar Afrika ta kudu da Jamusanci da Turanci da sauransu. Ta haka dai ne adabin ya haɗu, ta hanyar ƙaurar al’ummomin Hausawa da hidimar addininsu na gargajiya da kuma raya al’adunsu.
Ma’anar Adabin Hausa
            Kalmar adabi dai ga Bahaushebaƙuwar kalma ce, watau Balarabiyar kalma ce wadda Hausawa suka aro, suka ce hankaka ‘mai da ɗan wani naki’ ma’anarta da Larabci ita ce ‘halin ɗa ko fasha ko ƙwarewa’. (Ɗangambo, 1984). Ko kuma ‘walima’ ko ‘liyafa’ ko ‘ladabi’ (Umar, 1987).
            A Hausa kuwa, Kamar a Larabcin, tana nufin dukkan abubuwan da suka shafi al’adu da ɗabi’u da halin rayuwa da fasaha ta al’umma wanda har da nazarin al’ummar ɗungurum (Gusau, 1986).
            Saboda da kasancewar Larabawa masu harkar rayuwa ce irin tasu da mazauninsu da harshensu na musamman, Hausawa ma suna da nasu halin rayuwa da nasu mazaunin daban ta fuskar nazarce-nazarce da aka yi a kansu ya sa irinsu na gargajiya wasu sun samu siga ko yanayi na adabin zamani, a yanzu suna a rubuce cikin littattafai. Haka kuma, za aga cewa Karin maganganun Hausa a matsayinsu na dabin gargajiya, ko nab aka a yanzu sun zama na zamani, don irin sigar da suka samu a rubuce cikin ltattafan adabin Hausa. Sannan an samu ci gaba wajen manazarta inda aka raba shi, adabin na Hausa gida biyu, ta la’akari da wasu matakan ko zamunan da al’ummar Hausawa ta ratso kamar haka:
a.       Adabin Hausa kafin zuwan Musulunci, watau tantagaryar adabi na gargajiya na al’adun maguzawa (Gusau, 1985) wanda babu wani gauraya da wata baƙuwar al’ada cikinsa.
b.      Adabin bayan zuwan addinin Musulunci, watau mai nuna sauyin tunanin Bahaushe ga buƙatarsa da bautarsa da saninsa da fasaharsa da dangantakarsa da wasu al’adu na Larabawa.
c.       Adabin Hausa bayan zuwan Turawa, wanda shi ke nuna wani sauyi na matakan rayuwar Bahaushe. Rayuwar da ta zama Baduniya mai cike da ruɗani, tatare da wani sabon salon bauta ya Allah ta wani sabon addini ko kuma ta neman duniyar ɗungurugum.
Saboda dangankatar Bahaushe da wasu baƙin al’adun mutanen hayin ruwa daba addininsu ɗaya ba da su ba, balle halin rayuwarsu ta yau da kullum, shi ya saya aka samu sauyi arayuwarsa.
            Saboda haka za mu kalli adabin Hausa ta fuskoki guda biyu, wanda su ne kashe-kashensa ayanzu.
a.       Adabin baka, ko na ka, ko na gargajiya, ko na kafin zuwan Musulunci
b.      Adabin zamani ko rubutaccen adabi ko na bayan zuwan Musulunci ko na bayan zuwan Turawa ko bayan da al’ummar Hausawa ta samu `yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Wannan shi ne taƙaitaccen bayani game da adabi.
Wannan ya nuna cewa kowace al’umma na da nata adabin, watau halin rayuwar. Kuma akwai wurin da kowace al’umma ta fi ƙwarewa wajen aiwatarwa.
            A dalilin haka ne muke ganin cewa ba komai ne adabin ba, in mun dangata shi da Hausawa, face nazarin rayuwarsu ta yau da kullum wadda suke gudanarwa ko ake gudanar ma su da ita lokacin da suka bayyana a cikin duniyar nan har ya zuwa komawarsu ga mahalicinsu.
            Ta fuskar nazari kuwa, masana kamar su Ɗangambo, (1984) sun daidaita ra’ayinsu da cewa dabai wani hoto ne ko madubi na haska rayuwar Hausawa, wadda ta ƙunshi tunaninsu da ɗabi’unsu da harshensu. Harshen kuma da fasaha da na karantar da matasa gargajiya da sarrafa hanyoyin rayuwarsu. Haka kuma, ana haskaka muhallinsu da maƙwabtansu da wasu al’ummomi da abincinsu da irin bautarsu (addininsu) da tsare gaskiyarsu da rashin tsareta, ko wautarsu da sauran duk abin da suka gada kaka da kakanni.
Rabe-Raben Adabin Hausa
            Masana fannin nazarin adabin Hausa (Ɗangambo, 1984, Umar, 1987, Gusau, 1985, Yhaya, 1988) sun yi ƙoƙarin fitar da rabe-raben adabin Hausa dalla-dalla ta yadda za mu ce kusan ba su bar wani ɓangare da ba su tattauna a kansa ba.
            Yawancin sun rarraba shi ta yadda suka dubi shita ta fuskar zamansa na gargajiya ko na zamani, watau adabin gargajiya a ɓangare ɗaya a wani ɓangaren akwai adabin zamani. Sai dai wani (Malumfashi, 1998) na ganin cewa duk yadda aka raba shi a wannan lokacin, waɗannan manyan kashe-kashen suna yi wa juna shigar giragizai. Dalili kuwa shi ne za a ga cewa tatsuniyoyi da labarai da waƙoƙin baka na Hausa, duk akwai su a rubuce a yanzu.
Asalin Tarihihi, Ma’anarsa Da Kuma Misalansa
            A cewar Ibrahim Yaro Yahaya, Mu’azu Sani Zariya, Sa’id Muhammad Gusau, Tanimu Musa `Yar\aduwa a cikin aikinsu mai suna Darussan Hausa don manyan makarantun sakandare cewa suka yi.
            “Tushen Kalmar tarihi an tsago ta ne daga Kalmar ‘tarihi’ shi dai ‘Tarihihi’ labara ne na haƙiƙa dangane da wasu abubuwan da suka taɓa faruwa na al’umma. A da can a kan riƙe irin waɗannan abubuwa da ‘ka’ ne. to kasancewar kai ba mariƙi ba ne, ballantana har ya yi  ajiya, sai wajen rayuwa ake cukuɗa su har ma waɗanda ba su faru ba. Daga nan ne aka sami adabin baka na ‘tarihi’don a nuna tarihin gaskiya wanda ya cuɗanya da tatsuniya ko ƙirƙirarren labari.
            Ma’anar ‘Tarihihi’ shi ne gurɓatattcen tarihi wanda aka cusa masa labarai masara kan gado, na suki buruku, har ya fita daga ainihin lamarinsa na gaskiya, ya wofinta daga siffarsa ta asali”.
            Labaran tarihihi: Yawanci ya ƙunshi labarai ne na kunne ya girmi kaka waɗanda ba a iya tabbatar da haƙiƙaninsa. Kuma labarai ne da suka suka ƙunshi abubuwan da suka danganci rayuwar Hausawa, musamman a jiya. “masu yin sa a lokacin yin sa”. Masu yaɗa labarai na tarihi akasari tsofaffi ne waɗanda ba su iya riƙe ainihin aukuwar abubuwa ba, ko masu yawan hira da kan zo da kowane irin labari ba tare da haƙiƙanin gaskiyarsa ba, ko kuma a tsakanin samari. Kuma an fi yin sa a lokacin shaƙatawa ko ana hira ko na kawo misali.
            Tubulan gininsa: Sun haɗa da mutane ko wurare ko garuruwa da sauransu. Misalan tarihihi sun haɗa da:
i.                    Labaran Bayajida
ii.                  Labaran Barbushe
iii.                Labaran Bagauda
iv.                Labaran Amina Sarauniyar Zaazau da sauransu.
Amfanin Tarihihi: Duk da lalacewar tarihi yakan taimaka wa masu tarihi samun wasu bayanai da hujjoji da sukan tace su amfana da su. Yakan bai wa yara ƙanana damar fahimtar wani abu game da asalin al’ummarsu da wasu ayyukan da magabata suka aiwatar da dauriya da haƙuri da karsashi da nishaɗi daga darussansa da suka samu.
            Ga misalin ɗaya daga cikin Tarihihi
            Wata rana Akuya da Kare da jaki suka hirya za su je wani ƙauye domin su halarci taron buki, sai suka zo tasha suka shiga mota. Da za a tashi sai aka nemi su da su biya kuɗin mota na kowane ɗaya daga cikinsu. Daga nan sai jaki ya ɗauki kuɗinsa ya biya daidai kare kuma sai ya ɗauko fiye da abin da ake biya ya bayar da nufin a ba shi canjinsa.
            Akuya kuwa sai t ace da masu motar. “Da zarar an isa da su gurin za ta karɓi kuɗi ga wani ta biya. Da suka isa garin daidai wurin da za a sake su, sai Direba ya tsayar da mota. Jaki sai ya sauko ya yi tafiyarsa irin ta taƙama. Kare kuma daya sauko ya tsaya jiran a ba shi canjinsa. Abin ban takaici a wurinsa da akuya ta sauko daga cikin mota, sai ta ƙi ta tsaya, ta sheƙa a guje.
            Da masu mota suka ga haka, sai suka shiga motarsu suka yi tafiyarsu, ba tare sun ba kare canjinsa ba. Nan ne sai kare ya rinƙa bin motar da gudu yana kuka (haushi) da nufin su tsaya su ba shi canjinsa. To wai wannan dalili ne ya haifar da idan akuya ta tsikayi mota sai ta ruga da gudu domin ka da motar ta riƙe ta, ta ce, sai ta biya ta kuɗinta:, shi kuwa kare da zarar ya ga mota sai ya bita da gudu da nufin ta tsaya ta ba shi canjinsa shi kuwa jaki da ya gan ta ko tana a guje saman titi, sai ya hau ya yi tafiyarsa irin ta taƙama domin da shi da mota ba mai bin wani bashi”.
            Idan muka yi nazarin wannan tarihihi za mu iya fahimtar cewa lallai babu wata cikakkiyar hujja mai iya tabbatar da faruwar wannan al’amari daga hadisi ko aya ko ijima’in malamai.


Asalin Siddabaru Da Sihiri A Ƙasar Hausawa
            Da wuya mutum ya tanatance cewa ga ranar da Bahaushe ya fara yin siddabaru, balle yace ga siddabarun da Bahaushe ya fara yi. Amma da yake, lamarin ya shafi ilmi ya kyautu mu ɗan yi hasashe ta amfani da kirdado da kintaci faɗi mu ga ko ma cimma nasara.
            Ina ganin, gane asalin siddabarun Hausawa yana da wuya idan ba a san sana’o’insu ba. Kuma sanin sana’o’insu kawai ba zai warkar ba sai an san wace sana’a ce ko waɗanne ne suka shahara kuma suka daɗe a ƙasar.
            Bayanai da dama sun nuna farauta da noma da ƙira ne daɗaɗɗen sana’o’i. ana jin farauta ce ɗan Adam ya soma yi ta hanyar bin dabba da ƙarfin tuwo a kama ta a kashe. Da abin ya fara a gaba ya fara tanadin makaman da zai yi wa dabbobin da yake yin farauta. Ana jin sannu sannu ɗan Adam ya fara yin amfani da `ya`yan itace, yana ci yana yar wa har ya fara tunanin yadda zai ƙara kyautata su, daga nan ne soma samun tushe.
            Don haka, ina ga siddabaru da suka shafi farauta da noma da ƙira kusan za a ce su ne, Bahaushe ya fara yi sannu-sannu har abin ya ci gaba, ya zo yau.
            Na biyu, da yake masana sun amince da cewa addinin Hausawa na gargajiya ya haɗa da bori da camfi da tsafe-tsafe. Babban abin kula a nan shi ne, Hausawa a addininsu na gargajiya suna cewa kowane mutum yana da aljaninsa na musamman. Wannan aljani idan sun so shi suna iya ɗaukaka shi ta hanyar ba shi wasu hikimomi da babu wani mai samun irin su sai ya haɗa da sha’anin aljannu. Ta yi yiwu, a wannan fage a samu wanda ya yi nisa ga tsafi da camfe-camfe ya ƙago wasu dabarun yin wasu abubwan mamaki da mutane za su ɗauka siddabaru, dalili daya san a ce haka shi ne, mafi yawan siddabarun Hausawa ana haɗa shi ko yana da dangantaka ga magungunansu.
            Wani hasashe na uku shi ne, kan sana’o’in gargajiya ta fuskar sarautunsu, kowace sana’a da Bahaushe yake yi za a samu za a samu irin su shugaba a unguwar ko a garin ko a ƙasar gaba ɗaya. Alal misali akwai irin su sarkin noma da sarkin wanzamai da sarkin ƙira da sauransu.
            Waɗannan sarakai ana zaɓen su ne ta fuskoki guda biyu, na farko dai ko sun gada na kaka da kakanni sun san abin ciki da waje a ciki suka tashi suka tara da uwa da uba a ciki. Na biyu ko don sun ƙware ga snaa’ar matuƙar gaske, wato ya kasance a koyaushe za a iya yin Magana da hikima da zalaƙa kan wannan sana’ar kan tuna da su. Irin waɗannan mutane  saboda ƙwarewa da sabo kan sa wasu asiran sana’ar da wasu masu sana’ar ba su sani ba.
            Kuma sukan yi ƙoƙarin yin wasu ƙage-ƙage da ƙaƙale-ƙaƙale don buyawa da bajinta a wannan sana’a, ta yiwu ta wannan fuskar sihiri da siddabaru suka samu a ƙasar Hausa.
            A wani hasashen kuma ina ganin bai kyautu a manta da bukukuwan Hausawa na gargajiya ba, kamar su bukin buɗar dawa da wasan maƙera dawasan wanzamai da dambe da kokuwa da wasan mafarauta da dai sauransu. Waɗannan wasannin Hausawa kan yi sun a lokuta na musamman ne kamar a sau ɗaya shekara ko kuma wani farin ciki ya samu kamar aure ko haihuwa, idan za a yi wasan akan yi a dandali ne kowa ya zo ya gwada hikimarsa da bajintarsa.
            Za mu iya cewa wataƙila waɗannan bukukuwa suna da alaƙa da asalin siddabaru a ƙasar Hausa, domin mafi yawan abubuwan da ke wakana a dandali za ka ga sihiri ne da siddbaru. Don haka, ta yi yu mu ce samuwar sana’o’in gargajiya ya haifar da siddabaru amma kafuwar bukukuwan gargajiya ya wanzar da su da habakar da su.
            Hasashe na ƙarshe, shi ne dangane da samuwar magungunan gargajiya na Hausawa. A Bahaushiyar al’ada bokaye da `yan bori su suka shahara a fagen ba da magungunan gargajiya kafin bayyanar addnin Musulunci, bayan zuwan addini muka samu `yan tsibbu suka cika gurbin na uku. Ba su kaɗai ba, masu sana’o’in gargajiya kamar su wanzamai da maƙera da masunta da sauransu duk suna ba da magungunan gargajiya. Shi dai magani ana bayar das hi da niyyar kore cuta ko a arge ta ko a kwantar da ita, don haka, kowane mai magani yana son a yaba da irin maganinsa a kuma amince da shi.
            Wataƙila, wannan ne ya sa masu magungunan gargajiya ke ba da wasu dokoki da umurni a magungunasu, tare da ba da lokuta da za ɗibar su da yadda ake ɗibar su da yadda ake sarrafa su. Da haka ne ake samun wasu `yan ƙaƙale-ƙaƙale da siddabaru a magungunan gargajiya domin yin barazana ga masu karɓan maganin, sannu-sannu ta wannan fannin siddabaru ya fara wanzuwa a magunagunan Hausawa.
            A taƙaice, za mu iya cewa, siddabaru abu ne a bayan ƙasa, musamman a al’ummar Hausawa. Kuma gano asalinsa dole sai an haɗa da sanin sana’o’in Hausawa da addininsu da bukukuwansu da kuma magungunasu na gargajiya. Kuma ni a irin nawa hasashen daga waɗannann abubuwa ne siddabaru ya samo asali a ƙasar Hausa.
Siddabrun Dandali Da Yadda Ake Aiwatar Da Shi
            Mafi yawan siddabaru ban al’ajabi da ƙayatawa ga masu kallo a ƙasa a dandali ake aiwatar da su. Ganin irin wannan wainar da ake toyawa a dandali ya san a ga ya kamata a yi masa bincike mai cin gashin kansa. Manufar wannan bincike ita ce sai mai da himma ga fito da fayyace ire-iren siddabaru da sihirce-sihirce da ake gudanarwa a dandali a ƙasar Hausa.



Ma’anar Siddabarun Dandali
            A gwarwadon `yan karance-karance da na yi ban sami wani manazarci daya yi wani dogon bincike a kan siddabarun dandali ba. Wannan ce ta sa zan ce ban sami wani bayani ba kai tsaye a rubuce cewa ga abin da ake nufi da siddabarun dandali ba.
            Hausawa sun ce mai ɗaki shi ya san gefen da yake yi masa tarara, don haka a irin manufar da na fuskanci wannan bincike ga ma’anar siddabaru dandali a taƙaice.
            Wannan suna, “Siddabarun dandali” ni na ƙago shi gwargwadon binciken da na yi wa siddabaru a ƙasar Hausa. Abin da nake  nufi da wannan shi ne, Duk wani siddabaru ko sihiri da Bahaushe ya ƙago kuma yana  tara jama’a ya aiwatar da shi a gaban idonsu a dandali don su gani su yi sha’awa su kuma yaba masa, ko ya samu abin cefene a hannunsa wanan shi ne ake kira siddabarun dandali.
            Babu shakka, duk wani siddabaru ko sihiri da ake gudanarwa ta wannan fuskar ya zama siddabarun dandali ko da mai yin siddabarun bai amince da haka ba. Kuma duk wani siddabaru da ba a aiwatar da shi ta wannan fuska da irin wannan manufa yana nan zamansa siddabaru amma ban a siddabarun dandali ba. A wannan bincike wani siddabaru da za mu nuna dole ya kasance yana da siffofi biyu, na farko dai a yi shi a dandali don burge mutane, na biyu ya kasance an yi shi da wata manufa ta samun tamanin ko wanin wannan.
            Yakasance wasu sihirce-sihirce ko siddabaru ana yin su a sana’ar tsibbu ne ko a magungunan gargajiya kamar yadda ya gabata, amma kuma a zo a bayyana su gaban jama’a a dandali. Idan irin haka ta faru har yanzu siddabaru yana nan zamansa siddabarun dandali.
            Masu aiwatar da siddabarun dandali sun haɗa da Bokaye da `yan tsibbu da wasu masu sana’o’in gargajiya na musamman da kuma masu jiɓantansu don koyo.
            Da yawa akan sami wasu daga cikin su bayan suna siddabaru a zauruka kuma su fito dandali suna ƙara baje kolinsu. Yanzu kuwa ya kyautu mu ga shin siddabarun dandali yana da wasu rabe-rabe kamar sauran siddabaru da suka gabata.
Siddabaru na Haƙiƙa
            Wannan shi ne sihiri da Hausawa ke yi a bainar jama’a su gani kuma babu wani wayo ko tambayar da za taba ka gaskiyar lamarin. Abu ne da ake yi a gaban idonka a bayyane kuma babu wata gada-gada ko wani wayo a ciki, an yi amfani da ƙarfin magani da tsafi ake gudanar da shi ko wani na son ya ƙaryata shi ba zai kawo wata hujja da za ta iya karɓuwa ga hankali ba.
            Daga cikin ire-iren waɗanann sihirce-sihirce akwai ‘Cin ksauwar sama’. Mutum zai zo gaban jama’a ya ɗaga kansa sama sai ya ga doguwar igiya ta zuro daga sama, ya kama ta ya dinga tafiya tun ana ganinsa har ya zo ya ɓata a cikin giragizai. Idan ya dawo sai ya zo da kayan kasuwa iri-iri kamar su dankali, rogo da ƙosai da waina da gishiri da sauransu.
            Sannan na biyu, Akwai kuma mai miƙa ƙafarsa ta yi tsawo har ta taɓo sama kuna gani a gaban idonku. Wanann sun fi ƙarfin mutum ya yi tunanin yadda ake yin su sai kawai mutum yace tsafi ne gaskiyar mai shi na uku, Akwai mai shiga cikin duburan jaki ya fito ta baki ko ya shiga cikin tulu a gaban jama’a. Sannan na huɗu Akwai malaman da ke jefa buzun sallah sama ya tsaya su hau kansa yana sama ba su faɗo ba. Sannan na biyar Akwai kuma waɗanda sun taɓa mutum sai kawai ya ji zakarinsa ya ɓata.
            Idan muka hangi waɗannan sihirce-sihirce za mu ga abubuwa ne da suka gagari ƙwaƙwalwa mutum ta yi bayanin yadda ake yin su balle ma a ƙaryatasu. Idan kuma siddabaru ya kasance irin haka sai kawai mu ce siddabrun haƙiƙa ne na tsafi.
Siddabaru Na Tarihihi
            Wannan wani kasha ne na siddabaru da babu tsafi ko magani a cikinsa sai dai wuru-wuru kawai. Mafi yawan siddabrun da ake gudanarwa a ƙasar Hausa musamman a wannan zamani namu da shekaru sama ga tamanin ko ɗari da suka shige na barazana ce. Siddabaru na tarihihi siddabaru ne da ake yinsa a bainar jama’a kuma a ga abin ya yi sosai gwanin ban sha’awa. Amma idan mai wayo da basira ya kwantar da hankalinsa sosai ya dubi abin da idon natsuwa zai gane abin shiri ne da gada-gada da wasa ƙwaƙwalwa. Babu gaskiya a cikinsa, abin ban haushi ko ka so ka yi musu ga mafi yawan mutane basa yarda domin ga an yi abin  a gaban idon su, kuma a lokacin wannan tunani bai zo musu ba.
            Ga kaɗan daga cikin waɗannan siddabaru sun haɗa da dabon kuɗi da dabon turamen atamfa da toka a cikin ƙwali da sa wuƙa ta yi Magana da dafa abinci a kan bishiya babu wuta, da yanka mutum ya tashi, da sa ka allurai a hanci, da huda baki da masilla ko dogon tsinke da dai sauransu.
            Waɗannan duk sihiri ne da ake amfani da ƙarfin wayo da dabara da kuma taimakon `yan kore. Idan an tsaya aka yi bayani sosai kowa zai ga yana iya yin abin idan ya gano irin wayo da ake yi ayi abin.
            Babu shakka, duk wani siddabaru da ake gudanarwa a dandali a ƙasar Hausa dole ne ya ɗauki ɗaya daga cikin kashe-kashe. Idan ya ɗauki ɗaya daga cikin kashe-kashen za mu san irin matsayin da za mu ba shi.
Lokutan Aiwatar da Siddabaru
            Siddabaru kamar yadda sunansa ya nuna, ana yin sa a dandali kuma a wasu lokuta na musamman. Kuma za a fara tsara da cewa kowane iri siddabarun dandali a ƙasar Hausa da irin lokacin da ake aiwatar da shi.
            Mafi yawan siddabarun dandali ana gudanar da su da dare musaman bayan an ci abinci ana hira. Wannan lokaci yana taimako ainun saboda wasu `yan dalillai na farko dai lokacin akwai duhu da zai iya zama wani rufin asari ga wasu abubuwan da ake aiwatarwa. A wasu lokuta akan yi siddabarun dandali da rana domin mutane su ga komai da idonsu ƙiri-ƙiri su ƙara yarda da abin.mafi yawan ƙwararrun `yan siddabaru sun fiyi da rana ido na ganin ido.
            Dangane da bagiren da ake gudanar da siddabarun dandali kuwa yakan sha wani lokaci zuwa wani lokaci. A mafi yawan lokuta akan yi shi a kasuwa, musamman a kasuwar ƙauye idan ƙauyawa sun taru sun ƙare sayar da kayan da suka zo da shi kasuwa musaman bayan sallar jumma’a. a wasu lokuta akan yi siddabarun dandali a wajen taron buki kamar raɗa suna na `ya`yan maƙera da wanzamai da masunta da malamai da sauransu. Uwa uba ana yin siddabarun dandali a bukin naɗin sarauta ta mai unguwa ko dagaci ko wata sarautar gargajiya kamar naɗin sarkin Aska da sarkin noma da sarkin Ɗori da sarkin ruwa da sauransu.
            A ire-iren waɗannan bukukuwa da na ambata akan share kwanaki ana ta shagulgula siddabaru mutane daban-daban suna fitowa dandali suna kirari suna nuna irin buwayarsu ta siddabaru. Duk da haka a wasu lokuta masu yin siddabaru sukan yi abin su a duk lokacin da suka ga dama musamman in suna da nishaɗi ko neman na cafene.
            A ƙasar Hausa, yana da wuya a sami ɗan siddabarun dandali da ke gudanar da siddabarunsa a wuraren da ba waɗannan ba. A wannan bincikenmu zai taƙaita ga siddabarun da ake gudanar wa a wuraren da muka amabata kawai.
Halayen`Yan Siddabaru
            Masu aiwatar da siddabaru suna da wasu halaye da ɗabi’u na musamman. Waɗannan halaye wasu koyo ake yi wasu kuma sabo ne kawai ke taimakansa. Ga kaɗan daga cikinsu.
            Halarta da taro, dole duk wanda zai fuskanci dubban jama’a a dandali babu wasu matakan tsaro, kuma yana saon ya karɓi tamanin a hannunsu, dole ne sai ya ƙware ga iya Magana sosai. Bayan haka da azanci da luguden Nahawu da sarrafa harshe da Karin Magana, kuma da sanin wasu harsuna na musamman kamar Turanci da Larabci da Fulatanci da dai sauransu. Ya kyautu ga ɗan siddabarun dandali ya zama mai wayo sosai domin idan ba da wayo ba, ba za a shawo kan jama’a ba.
            Bayan siffofin halitta dole ɗan siddabarun dandali ya zamo mutumin da baya gudun rikici da tataso da kwana gidan kurkuku. Kuma sai ya kasance yana iya cin amanar kowa yaro da babba Musulmi da kafiri ko da kuwa sun saba da wannan mutumin, ɗan siddabarun dandali yana ƙoƙarin ya nuna wa jama’a cewa shi fa bai damu da dukiya ba, domin tana can gida ya tara ya taso, ya zo ne ya taimaki mutane kawai.
            Bugu da ƙari, wasu yan siddabarun dandali musamman masu sayar da magani sukan fito da warki da ƙaho na busa da layu da guraye da kanbuna da hular gashi kan baƙin biri da shuni a idon da kiɗa da akwati da kwalaye da sauaran tarkace. Irin wannan `yan siddabaru suna ƙoƙairin danganta kan su da maguzawa ko Arna marasa addini suna kuma nuna tsafi suke yi su yi magani da shi.
            Amma `yan siddabarun dandali masu yin damafara ba su fita da dauɗa, sukan fita cikin wasu kaya masu tsada na musamman wannan ya zama dole domin su nuna wa jama’a cewa su dama suna da dukiya ba kuɗin jama’a suke so ba. Wani lokaci sukan saka haƙoran gol da makawuya wai su Alhazai ne sun je hajji ba sa cin amana ba sa son kuɗin kowa. Wannan shi ne taƙaitaccen bayanin halayen `yan siddabaru.
Salon Aiwatar Da Siddabaru
            `Yan siddabru kafin su aiwatar da siddabru suna buƙatar mutane su taru a dandali a yi shiru ana sauraren su, da irin abubuwan da suke faɗa ana kalon su ga abubuwan da suke aiwatarwa ko kaɗan ɗan siddabaru ba ya buƙatar ko ya ji surutun wani bayan fage ko a cikin fage a yayin da yake gudanar da siddabarunsa. Yana jawo hankalin mutane irin haka ba ya samu wa dole sai tare da wasu dabaru na musamman ga kaɗan daga ciki su.
            A mafi yawan lokuta `yan siddabaru musamman masu da’awar cewa suna sayar da magani suna amfani da kiɗa da waƙa. Kuma suka sami ɗan ƙaramin yaro su koya masa kiɗa da waƙa, yadda baƙauye da ya ji sautin ɗan ƙaramin yaro yana yin waƙa mai azanci da zalaƙa ya kan zo ya tsaya ya saurara, domin Hausawa sun ce gani ya kori ji. Kuma a wasu wurare su kan ce sauran yara su dinga tafi da hannayensu sautin tafin yana zuwa daidai raujin waƙar da ƙafafunta. Idan yara na tafi shi kansa Uban gidan siddabaru zai shiga cikin tafin yana yi yana rera waƙar bobanci wai don a ce ba ya jin Hausa sosai. Wani lokacin waƙar takan zo kamar haka:
                                    “Arne ɗan Bima
                                    Shiga Dogo
                                    Ga Dakare
                                    Ga ɗan baya
                                    Ga halakakke
                                    Ga matsiyaci
                                    Ba ka da kowa
                                    Ba ka da komai
                                    Ga ɗa babba
                                    Ka shiga dodo”.

            A wani lokacin kuma akan sake wa chali zaren waƙar ya dinga yi, yana kiɗa yana tafi. Idan kiɗa ya soma daɗi jama’a sun fara taruwa sai ɗan siddabaru ya fara:
                                    “Yara ku tafa yara
                                    Haba yara ku tafa sosai
                                    Haba yara manyan gobe
                                    Kai cali Baturen ganga
                                    Ka dinga bugawa sosai
                                    Yara ku tafa daidai
                                    Duk wanda bai tafa ba
                                    Uba nai maye uwa tai mayya
                                    Ubansa ya ɗore jaki sanda
                                    Kaɗannan ba da abin kirki ba”.


Haka mafi yawan waƙoƙinsu suke tafiya da tafi da kiɗa da batsa, kuma waƙoƙin ba su cika tsawo ba.
            Daga cikin salon aiwatar da siddabaru akwai rawa da mosta jiki. Uban tafiyar da kansa (Watau mai siddabaru) zai dinga yin wata rawa ta musamman mai ƙayatarwa wasu sukan dinga yin tsalle suna direwa a ƙasa, wasu sukan dinga yin tafiya a kan gaɓobin jikinsu. Waɗannan duk dubaru ne ma kiran jama’a, sai sun taru a fara sayar da magani ana yi musu siddabaru.
            A wasu lokuta kuma, masu siddabarun sukan faɗi wasu abubuwan da za su yi waɗanda ba su yi yuwa, kamar a mayar da mutum biri ko a ɗora yaro a kan sanda ta tashi da shi ya je sama ko shiga cikin kwalba ana kan keke ko dabon dandana Uban Aljannu. Da zarar mutum ya ji za a yi irin waɗannan abubuwan al’ajabi, yakan so ya tsaya don kar a ba shi labari.
            Da zarar mutum ya tsaya an gama da shi, domin za a dinga tallar maganin sanyi da ciwon baya da sauransu ne domin a mantar da wancan Magana da ake yi. Idan ya ga lokaci zai ƙure mutane sukan kasa jira suka fara watsewa sai ya dinga yin kirari yana cewa, “yanzu za’a yi abin”. Haka za a dinga yi har rana ta faɗi ko kasuwa ta watse ba a yi komai ba.
            Wani salon da suke bi wajen kiran mutane shi ne, ‘kuwwa’. Watau a yayin da ɗan siddabaru ya ga jama’a suna son su soma gajiya da shi, sai ya ɗauko wata yar gora ko wani ɗan ƙaho ko wata laya ya gaya wa yara cewa: “Duk wanda ba ɗan gidan maye ba ne ya yi wa wannan gora kuwwa sau uku”. Idan sun yi ihu! Ihu! Ihu!! Sai duk kasuwar ta game da kuwwa mutane su ruga su ga abin da ake yi wa kuwwa, daga nan sai gogan naka ya dinga sayar da magani yana nunawa.
            Ýan siddabarunsa na kallo, a wasu lokuta kuma zai dinga yin Magana da mutanen sama da ƙarfi kowa na jin yana ihu! Shi kaɗai sai a dinga taruwa ana mamaki da ya ga ana fara taruwa sai ya fara baje kolinsa. Waɗannan su ne kaɗan daga cikin dabarun da `yan siddabaru ke bi wajen ya wo jama’a a gan su. Da yawan `yan siddabaru suna yawo da akwati ko kwali domin yin dabon kaya daga ciki. Duk inda wurin da ɗan siddabaru mai yin dabo yake ba ka raba shi da babbar riga da `yar ciki mai aljifai kamar takwas ko tara da wando toroza mai aljifai gaba da baya. Wasu kan je da dogayen huluna da rawani da sauransu. Wannan shi ne taƙaitaccen bayani game da salon aiwatar da siddabaru.
Sakamakon Bincike
             A taƙaice, a nan ina son in nuna hoton bincike na. Na farko, na fahinci gano kowace al’ada ta Hausawa ba zai ci wata nasara ba in ba san asalin Hausawa ba. Amma kuma abin baƙin ciki har yanzu masana ba su yi mana matsaya a kan ainihin asalinsu ba.
            Dangane da magungunansu na gargajiya, na fahimci da wuya mutum yace, ga yadda Hausawa suka ƙago magani. Abin da zai fi alheri ma ce “Ubangiji daya yu shi ya san yadda ya cusa masu dabarar magani”. Amma kuma kusan san duk mai maganin gargajiya ba zai rasa yin tsafi da siddabarun ba. Bugu da ƙari, yana yin lokacin ɗiban maganin gargajiya da du’ain ɗiba da wani tasiri ga maganin illa barazana ne.
            A ɓangaren siddabaru kuma zan ce ba zai kyautu ba in babu `yankore. Kuma duk wani ɗan siddabrun daya shahara yana da `yan kore masu mara masa baya ko ba a sani ba da dai sauransu.
Naɗewa
            A halin yanzu bincike da nazari a kan magungunan gargajiya da siddabarun Hausawa zan ce yanzu a ka dena hasashe, kuma da alamun Nasara, Amma ya kyautu manazarci ya kula cewa kowace hanyar nazari da irin matsalolinta; matuƙar a ka dage aka yi haƙuri za a ci nasara sosai. In Allah Ya yarda ba da daɗewa ba za a samu isassun kayan karatu a makarantun sakandare da kuma jami’o’i kan siddabaru da sihirin Hausawa.

Post a Comment

0 Comments