Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 3: Kar Ka Bar Jaki Ka Koma Dukan Taiki

Rashin yarda da kai matsala ce mai zaman kanta, ko na ce cuta ce da ke damun mutane da dama, kuma ita ke hana su isa ga burinsu. Amincewa da kai wani abu ne da...


Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 3: Kar Ka Bar Jaki Ka Koma Dukan Taiki

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wato dai kar mai haƙilon cin nasara a rayuwarsa ya bar abin da ya dace ya koma ga wanda bai da alaƙa da abin da yake nema kuma ya nace a wurin, ba yadda za a yi mai son zuwa Gabas ya kama hanyar Yamma kuma ya zaci inda yake so zai je, mun dan yi tsokaci a kan wannan a baya, Allah ne ke ba da arziƙi kuma bai boye hanyar da za a bi don isa gare shi ba, wanda yake son tara kudi sosai to ya nemi sana'ar da take kawo kudin kuma a inda ya dace, kar ya watsar da babbar harkar ya koma yankar farce a karkara kuma ya ce kudin zai tara.
.
Wanda yake son ya zama babban malamin Ƙur'ani to lallai ya rungumi Ƙur'anin ya sa a gaba, ya sami mahaddata ya bi layin da suka tsara domin cimma biyan buƙata, kar ya nace wa zaman kasuwa kuma ba shi ma da cikakken lokacin zuwa makarantar, irin wannan wahala mutum zai ci abin da yake so kuma bai samu ba, duk wani malamin Hadisi da ka ji ko na Fiƙihu ka tambaye shi irin wahalar da ya sha kafin ya gagara, zai gaya maka gudu tare da susar katare nau'i ne na bata lokaci kawai, dole ka fuskanci gaskiya don cimma manufa, in kuma aka matsa sama da buƙata shi ma wata rigimar ce ta daban.
.
Yarda Da Kai

Ƙa'idar kamar yadda muka gani a baya ita ce: Duk wanda ya sanya wa zuciyarsa ba zai iya yin abin da yake so ba, to ba fa zai iya ɗin ba. Rashin yarda da kai matsala ce mai zaman kanta, ko na ce cuta ce da ke damun mutane da dama, kuma ita ke hana su isa ga burinsu. Amincewa da kai wani abu ne da ke tasowa daga cikin mutum, ƙwaƙwalwa, zuciya da ma gangar jiki gaba daya, duk su suke taimakawa wurin ganin mutum ya ci nasara a rayuwarsa, mu dauki masu wasar dambe a matsayin misali, kalli dai yadda kowa yake dagewa sai ya yi nasara ta wurin rinjayen abokin gasarsa.
.
In Allah ya taimake ka kana burin sai ka ci nasara, ka tsaya wurin yin aikin da ya kamata, ka inganta aikin, ba shakka ka taka matakin farko na cin nasara a rayuwa, sabanin kallon abin da za a samu a maimakon ingancin aikin, ko kallon yawan mabuƙatan aikin a maimakon masu yabon ingancin nasa, in ka fara ka raina mabuƙata aikin ƙila ka gaya wa zuciyarka cewa ba za ka iya ba, matakin farko kenan kuwa na karaya, wato rashin samun ƙarfin gwiwa, sai abin ya fita daga zuciyarka kadan-kadan sai ma ka bar shi gaba daya, a duk lokacin da ka bar abu don ka raina shi wani zai dauka ya ririta shi, in ba ka yi sa'a ba sai ka yi masa aiki ya biya ka.
.
   KWATANCIN BURI DA ISA GARE SHI
Wannan labarin wani mutum ne da ya girma a gaban kakarsa saboda mahaifin ya rasu tun yana jariri, da yake mai kudin ƙauye ne yaronsa ya yi ta amfani da gadon da aka bar masa ta wurin biyan kudin makaranta na karatun da ba a maida hankali ba, ko kuma yanayin karatun ƙauye, yadda yaro bai samun tagomashi a gida, makarantar ma ba sa ba da abin da ya dace, haka har ya gama sakandare ba tare da ya ji Turanci ba.
.
Ganin haka ya sake maimaita sakandare a wata makarantar da kudinsa, tunda a lokacin ya riga ya girma, inda ya fara ƙwadago wato noma a gonakin jama'a yana samun na makaranta, wani sa'in kuma ya koma wanki da guga, masamman idan rani ya yi, yana kammala sakandare na 2 ya wuce kwalejin share fagen jami'a ya yi shekara 2 da kwalin Diploma, Allah ya taimaka ya sami karatu a waje, tun daga can ya fara aiki a fagen da jama'a za su san shi, a taƙaice maganannan tamu malami ne a dayan jami'o'innan na Nigeria.
.
Binciken da na yi burin mutuminnan tun yana yaro shi ne karatu, babban dalilin da ya sa ya ƙi yin auren ƙauye kenan da wuri kamar yadda sauran abokai suka yi, burinsa shi ne a ce yau ya zama malami yana koyarwa, an ce tun yana ƙarami yake da burin koyarwar a makarantu da daidaikun mutane har Allah ya kai shi wannan matsayin, kuma a yanzu haka wai yana so ne a ce yana da makaranta tasa ta kansa wace yake jagoranci, a tarihinsa bai taba nisa da burinsa na zama malami ba, duk mutanen da ya san su a fagen suka hadu.
.
Iya bincikena game da shi bai da wata gata ko ƙwara daya wace za ta sa ya kai matsayin da yake a yau, hatta aikin da yake yi a yanzu, ya sami taimakon Allah ne kawai, sannan jajircewarsa da ƙoƙarin kaiwa ga wannan matsayin shi ma ya taimaka, shi ya sa makarantu ke sanya wa yara rigunan lauyoyi, injiniyoyi, sojoji, likitoci da ƙarfafa musu gwiwar cewa za su kai ga cimma burinsu, na san wanda duk maganarsa ba t wuce soja, kuma ya sami biyan buƙata, wani dan sanda shi ma yana ciki, amma fa sun tsaya ne sosai har suka kai ga cin nasara.

Post a Comment

0 Comments