Irin
wannan mutumin zuciyarsa ba ta taimaka masa da tunani mai kyau, saɓanin
wanda ya taso maraya ya sami jarin galam ɗin kalanzir ya
fara sayarwa, ta kai ga yana ɗaukar jarka. A
hankali ya shiga ɗaukar
durom.
Sai ga shi...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 4: Saƙar Zuci
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
A wani Hadisi Annabi SAW ya
ce a cikin jiki akwai wata tsoka in ta gyaru to mutum ya gyaru, in ta baci shi
ma ya baci gaba dayansa, a ƙarshe
ya nuna cewa zuciya ce, kenan zuciyannan yadda za ta iya taimakon mutum ya ci
nasara a rayuwa za ta iya wargaza shi gaba daya, mun dai sani cewa ita ce za ta
taimaka masa wajen gano sabbin abubuwan da za su taimake shi a rayuwarsa, kuma
ita ce dai take taskace masa hanyoyin da wasu suka bi kafin a ƙarshe suka isa matakin da suke a yau,
misali; na ga wani bawan Allah da mahaifinsa ya bar masa gadon miliyoyin kudi.
.
Nan da nan ya sami sabbin
abokai, wasu ma ba sa'o'insa ba ne su ma binsa suke yi sau da ƙafa, ya bar gida ma ya koma hotel, sai abin
da yake so zai ci, sai wanda yake so zai gani, a irin kudin da ya samu dinnan
zai iya gina irin wannan hotel din a wani wuri, ya zuba duk abin da ke ciki,
amma haka ya yi ta kashe musu kudin, ogan wurin ma girmama shi yake yi bare
sauran ma'aikata, kudin da ya samu raguwa suke yi tsakanin abin da zai ci, inda
zai kwana, suturar jikinsa, tafiye-tafiyen da yake yi, daukar nauyin masu taka
masa baya, da kuma 'yammatan da yake nema, ma'ana kudin ba ya ƙaruwa sai raguwa kullum, a ƙarshe dai ya dawo kamar sauran jama'a,
shi ma dole ya nema tunda wanda aka taskace an yi masa illa.
.
Irin wannan mutumin
zuciyarsa ba ta taimaka masa da tunani mai kyau, saɓanin wanda ya taso maraya ya sami jarin galam
ɗin kalanzir ya fara sayarwa, ta kai ga yana ɗaukar jarka. A hankali ya shiga ɗaukar durom. Sai ga shi yana da tankuna
ma ba tanki ba, a maganannan yana da gidajen mai a ƙarƙashinsa
kamar ba shi ne wancan ba, tabbas Allah ya shige masa gaba, sannan zuciyarsa ta
riƙa bugawa ga abubuwan da za su yi masa
amfani, akwai kansiloli da suka sami kudi tun lokacin ba a bincike, wasu sun yi
abin da suka ga dama da kudin, wasu kuma sun tunano halin da suka shiga kafin
suka taka wannan matsayin, sai suka fara tunanin yadda rayuwar za ta kasance
bayan sun sauka don duk dadewarsu ba za su wuce shekara hudu ba.
.
Duk mutumin da ka ga yana
taka-tsantsan wurin kashe kudi ko yana cire su kamar yana yankar naman jikinsa,
kar ka taba tsammanin bai son jin dadi kamar yadda kake ji ne, tunaninku ne ya
sha bamban, shi yana tuna yadda ya tara su ne, kai kuma kana tuna yadda za ka
kashe ne, duk wanda ka ji yana cewa "Kudi Allah ke ba da su a kashe su kawai"
to ka duba yadda yake kashe su, shin ta yadda Allan yake so ne? In ba haka ba
ne ai bai da sakankancewar in sun ƙare
za a sake ba shi wasu, Allah SW ya yi maganar zakka ne sai sadaka da sauran
wuraren ibada, in ba haka ba kuma to da walakin wai goro a miya.
.
Za ka sami mutum yana burin
kama sana'a, bai shiga ba amma ya fara tunanin in kuma kayan suka yi kwantai ko
aka ƙi siya ya zai yi? Ko yana son ya shiga
soja amma kuma ya ce "In aka tura ni Bama ko Sambisa ko Zamfara fa?"
Ko zai gina makarantar Furamare a Kaduna ya ce "In kuma L-Rufa'i ya ci
gaba da inganta makarantun gwamnati ai ba zan sami dalibai ba, dame zan biya
malamai albashinsu? Ya za a yi makarantar ta dore? Ba wanda zai kawo wannan
tunanin zuciyarsa sai ka ga jikinsa ya yi sanyi, in ba a yi sa'a ba komai
daganan zai tsaya, ba wani abu ya ja masa ba sai irin tunanin da ya sako cikin
zuciyarsa kafin ya fara.
.
Da yawa za ka taras ana son
a yi wata harka ta hadaka amma wasu suna dan jajja da baya, ka ga kamar ba sa
so ne, ko kuma wani abu na rashin natsuwa yana musu ƙaiƙayi
a zuciya, gaskiya ba komai ne ba sai irin saƙe-saƙen da suke yi a zukatansu na yuwuwar
rashin nasarar tafiyar, in sauran abokan za su zama haka to an gama, ba abin
alkhairi da za a iya tsinanawa, har a koma zargin juna cewa wane ne ya ja, shi
kuma ya fara ƙoƙarin kare kansa.
.
Mu dauki addinin muslunci a
matsayin misali, mahaddata Ƙur'ani
a lokacin su ne sojojin muslunci kuma su ne malamai, su din ne dai suka riƙa fita jihadi, ba su ce in aka kashe su
ya za a yi Ƙur'ani ya zo gare mu
ba, haka suka riƙa
fita ko a mutu ko a yi rai, Allah ya kalli zuciyarsu ya ba su kariya ga shi
muna amfani da ƙoƙarinsu, haka a yau mutum zai narka
miliyoyin kudi ya gina makaranta, ko kamfani ko wata ma'aikata, ba tare da ya
yi tunanin in kuma bai dawo da kudin ba fa? A koda yaushe yana tunanin cin
nasara ne, tabbas zai ci din da izinin Allah, kowa da ka gani a cikimmu ya san
da cin nasara ko faduwa, amma masu cin nasarar kau da kansu suke yi ba sa
tunanin faduwar kokadan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.