Wannan
shigar kawai suka kalla suka manta da duk sifofin da yake da su. Wai
da na tambaye su dalili sai suka ce ba addini zai riƙa koyarwa ba... Wannan
ya sa ban yi mamaki ba da na ga takardar wata da take neman aiki a wani gidan
talabijin ta rubuta cewa ita fara ce kyakkyawa. Na
tabbata da gidan Radiyo ne ƙila sai ta ce tana da...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 6: Kyakkyawan Tanadi
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Wani abu da ya zama dole a
rayuwar mutum shi ne samun yanayi mai kyau ga abin da mutum yake buƙatar ya yi, da kuma shigar da ta
dace, suna daya daga cikin abubuwan da
suka wajaba ga mutum, duk abin da zai yi ya dubi dacewa da kuma yanayi, ko
sana'a za ka fara ka duba inda za ka yi din in mutanen wurin suna da buƙatar kayan da za ka sayar, ba yadda za a
yi wanda yake son gina makaranta ko dakin watsa labarai ya je tsakiyar kasuwa
inda ake hayaniya ga ƙara
gami da hargowa ya ce anan zai yi.
.
Wanda zai bude maƙerar da zai riƙa ƙera
kayan gona to zai fi kyau ya zauna inda manoma za su riƙa ganin abin da yake yi, don wani wucewa
kawai zai yi in ya ga abin da yake so zai tsaya ya saya, ko in zai dawo ya riƙo kudi, zan ba da misali daya, wani
bawan Allah ya wallafa wani littafi da yake koyarwa game da mutuwa, tun daga
rashin lafiya, da yadda ake jinya zuwa fitar rai, wankan gawa, ginin ƙabari da zaman makoki, littafi ne mai
matuƙar mahimmanci.
.
Zai yi kyau Musulmi ya
mallake shi ya yi nazari don sanin yadda zai suturta waninsa, sai dai ya yi wa
littafin suna "MUTUWA" ga gawanan cikin likkafani an dora ta a kan
anna'ashi, na ce wa mai sayarwan da za ku canja sunan littafin da hoton da aka
saka a bangonsa da littafin ya fi shiga, misali a sanya fure a maimakon gawa,
sunan kuma a ce "Tafiyar da ba makawa" ya ce ai komai ya yi daidai,
ko ba a gaya wa mutum ba ya san cewa maganar mutuwa ake yi da abin da ya shafe
ta.
.
A taƙaice dai wallahi littafin nan ƙwara
daya sai da ya gama cin dukar rana ya ƙoƙe ba wanda ya saya, kuskuren wajen nuna
wa mutane abin da ba sa son gani ne, duk wanda ya kalli bangon littafin zai yi
wahala ya yi sha'awar siyansa, akwai wata yarinya da take tallar abinci,
wallahi abincinta akwai dadi ga arha, komai kake so akwai, amma yanayin kayan
da take sakawa, da wurin da take zama, da nau'in abincin da mutanen wurin suke
buƙata ya sa sam-sam ba a sayen abincinta,
ga masu abincinnan a wurin ko kusan nata bai kai ba amma suna samun ciniki ba
kadan ba.
.
Sun gyara shagon, ga kujeru
da teburi, fanka na kadawa, a gefe ga firinji, na ci abincin wata a cikinsu sau
daya ban ƙara ba, wancan ta
farkon da za ta riƙa
kawo abin da ake buƙata
a hankali ta kwaikwayi waɗannan, ta kiyaye dadin
abincinta kar ta canja, tabbas sai ta ƙwace
komai, akwai kuma lokacin da aka zo daukar malamai aiki, ana neman malamin
Turanci, an sami wani Bayerbe komai ake so yana da shi har da ƙari, amma yana da ƙasumba, ga shi ya zo da jallabiya da
wando rabin ƙwabri da takalmi
silifas.
.
Wannan shigar kawai suka
kalla suka manta da duk sifofin da yake da su. Wai da na tambaye su dalili sai suka ce ba
addini zai riƙa koyarwa ba... Wannan ya sa ban yi mamaki ba da na ga
takardar wata da take neman aiki a wani gidan talabijin ta rubuta cewa ita fara
ce kyakkyawa. Na tabbata
da gidan Radiyo ne ƙila
sai ta ce tana da daddadar murya.
Wannan
ma abin nema ne a wurinsu can. Duk abin
da za ka yi ka dubi buƙatun
jama'a da kuma yadda za su kalle ka.
.
An yi wani zamani a ƙauyemmu lokacin da fulani suka rabu
biyu, akwai masu sayar da nono a kwano da masu sayarwa a ƙwarya, masu sayarwar a kwano sukan ci
ado ka gan su tsab-tsab koda yaushe amma fa suna da tsada, na ƙwaryar ne dai da arha, na tabbata shigar
masu sayarwan a kwanon da yarda da kai da yadda suka ƙawata sana'ar suke ganin abin da ya dace
a yi kenan, domin duk da tsadarsu da komai wasu sun fi natsuwa da su, ba su
sayen nono sai a wirinsu, ko lauyoyi da likitoci gami da manyan ma'aikata ba
wani abu ya sa kake ganinsu tsab-tsab ba sai inganta ayyukansu, ana ƙimanta mutum wani sa'in da irin shigar
da ya yi ne.
.
Ka lura da kyau ka gani, ko
tsayuwa ka yi wurin wanda ya fito tsab za ka ga shi ake girmamawa, na taba yin
tafiya wani lokaci da maigidanmu, akwai kuma ma'aikatammu, cikinsu akwai wani
Bakatsine da ya sha shakwara da jamfa, duk inda muka shiga sai ka ga an
tsallake mu an fuskance shi, ba wani abu ya fi mu ba illa irin shigar da ya yi,
ana ganin shi ne ogan gaba daya, zaben wurin aiki, shigar ma'aikacin, nau'in
irin aikin duk abin dubawa ne, mu tara a gaba kan wannan batun.
Mun
yi shekara ɗaya
cur tare da malam muna ƙaruwa. Tsakani da Allah ba abin
da muka sani.
Shi ya riƙa ɗora mu a kan hanya. A
shekara ta biyu ya ce mana shi fa...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 5: Guji Yawan Kawo Hanzari
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Wasu za su iya yin duk abin
da ake buƙata, hasali ma su ne
kawai za su iya yi din, amma yawan koke-koke ko kawo hanzari shi zai ruguza su
ya bata tafiyar gaba daya, wani kana tuntubarsa a kan wani abu mai matuƙar mahimmanci a rayuwarsa sai ya ce maka
mu yanzu ai mun girma ya za a yi mu iya? Hanzarin dai shi ne yawan shekaru,
akwai kuma wanda zai ce gaskiya ba zai iya ba saboda ƙarancin wayewa, ko ilimi, ko kudi, ko
shekarun, ko dai wani abin na daban, matuƙar
mutum ya ce ba zai iya yin abu ba saboda wani dalili da ya dogara da shi, da
wahala ka ga ya motsa, ya haƙura
da nasarar kenan.
.
Wani maƙwabcimmu yake cewa "Lokacin da muka
shiga JSAIE (Junior Secondary School for Arabic and Islamic Education) ba mu
san komai ba, gaskiya ni ko baƙaƙen da Larabci ban iya ba, mun dai yi
karatun allo kuma mun sauke, mun haddace wurare da dama amma sunan Nahawu ma
lokacin na fara ji, don haka muka nemi wani malami da zai taimaka mana, shi ya
koyar da mu littafai da yawa, a dalilinsa muka fara sanin inda aka dosa, mun ga
sa'o'inmu a ajin, da ƙanninmu
da ma waɗanda
suka haife mu ba yayyimmu ba.
.
Mun yi shekara ɗaya cur tare da malam muna ƙaruwa. Tsakani da Allah ba abin da muka sani. Shi ya riƙa ɗora
mu a kan hanya. A shekara
ta biyu ya ce mana shi fa iyakarsa kenan sai dai mu nemo wani malamin,
hankulimmu ya yi matuƙar
tashi, haka dai muka yi ta bundun-bundun mu fada nan mu tashi can, cikin ikon
Allah muka shekara shida muka kammala karatun, muka wuce kwalejin share fagen
jami'a muka samo kwalin diploma, muka dawo gidan da muka zauna muna tuna baya,
cikin ikon Allah a ranar sai ga malamin namu ya yi sallama ya shigo.
.
Abin mamaki sai ya sami wuri
a ƙasa ya zauna bayan mu muna kan kujeru a
zaune, sai ya ce wai ya zo neman sani ne, haka dukammu ukun muka yi ƙasa, ya ce wallahi shi tun daga shekara
ta biyu ya rabke ya kasa ci gaba, yana ganin ya girma ga kuma ƙarancin abubuwan masarufi, mu ga shi
Allah ya taimake mu har mun kai ga Diploma, tsakani da Allah ba don neman sani
ba da ba zai zo ba, saboda haka mu koma kan kujerarmu in ta so in mun ba shi
amsa ma sauko ƙasa, muka ce masa
wallahi in dai yana ƙasa
ba wanda zai hau kujera.
.
Da dai ya ga da gaske muke
sai ya hau din kuma ya umurce mu da mu hau, da farko mun ƙi, amma da muka ga zai shiga wani hali
muka hau, sai bayan mun gama sai ya yi mana nasiha da cewa kar mu taba samun
raunin gwiwa a kan karatu, da ma duk abin da muka shiga, na san dai yana yin
wata sana'ar da tun farko muka san shi da ita, mu kam yanzu muke tasowa amma a
dalibansa wasu sun zama marunbuta, wasu
malaman jami'a wasu manyan 'yan siyasa, wasu 'yan kasuwa da malaman muslunci, a
sa'o'inmu ni na san waɗanda suka zama manyan
sojoji, 'yan sanda, alƙalai,
lauyoyi, malamai a jami'u da sauransu, akwai waɗanda
suka koma suna koyarwa a zaurukan gidajensu ana ba su sadakar Laraba".
.
Wasu tabbas sun sami karayar
zuciya ne a dalilin ƙarancin
kudi, wasu za su ce maka ba sa ganewa, akwai wanda muna karatun ya arce abinsa
wai shi aure yake so, ya yi auren amma ya kasa dawowa fagen da yake ciki har
abokan tafiyar nasa suka yi masa nisa, sai ya gan su ya yi ta sha'awa, akwai
wanda ya ƙi karatun wai za a
maida shi dan Izala, a daidai lokacin mu kammu muna kukan cewa Dariƙar ake koya mana, don littafan tauhidin
sam ba sa taimakon 'yan Izalan a aƙidunsu,
amma duk da haka muka yi haƙuri
muka dage har muka gama, kuma ba abin da ya shafi aƙidummu, shi kuma har yanzu yananan yau
kamar jiya.
.
Akwai kuma wani bawan Allah
da muka zauna wuri guda, yana HND a bangaren kimiyyar noma da tsire-tsire, muna
koyarwa wuri guda, ya ba ni shekaru da dama kuma ya fi ni wayewa da sanin kan
rayuwa ta ko'ina, a haka na je na yo digirina na farko a waje, na dawo na ba
shi shawarar ya canja layi kawai ya dawo bangaren koyarwar tunda yana da
sha'awa, na yi dace ya manta da shekarunsa da wayewarsa ya koma makarantar,
cikin 'yan shekaru ya samo kwalin Digirin shi ma, ya dora digiri na biyu, a
maganannan da muke yi shi ke jagorantar wani babban kwaleji.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.