Tabbas wasu rashin iya
magana ne da mutane, wasu kuma rashin gwanancewa ne wurin hulɗa da
jama'a. Wasu tsabar wauta ce da
rashin sanin ƙimar mutan. Akwai kuma masu ƙarancin hangen nesa... Sai dai ko ya mutum yake, iya magana wajinbi
ne matuƙar za ka yi hulɗa da
jama'a. In ba haka ba sai a
guje ka a bar ka kai kaɗai. In sana'a ce ka ga...
Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 7: Ka San Me Zai Fita
Bakinka
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunna
Abin da babu kokwanto a
cikinsa shi ne duk wani mutum a gidansa sarki ne, kowaye kuwa, zan ba ka dan
misali a kaina, a matsayina na malamin makaranta, na koyar da wani dan-sanda,
to halin rayuwa sai na sami matsala na katin gidan talabijin wanda wani mutum
ya zurma ni ciki, ina zaune aka ce ana gayyata ta a State CID, na tafi, sai na
iske wannan mutumin da na sami matsala da shi, aka yi min wasu ‘yan tambayoyi
na fara ƙoƙarin
yin bayani, nan take wani agana min tsawa agana dena daga masa murya, a lokacin
na san ogansa dalibina ne, in ya zo wurina ka ga yadda yake maƙe-maƙen
murya, to kowa a gidansa sarki ne.
.
Duk da cewa kowa ka gani a
gidansa sarki ne zai yi kyau mu koyi yadda za mu yi agana da abokan hulɗanmu,
duk wanda yake da kayan sayarwa so yake ya ƙare,
zai yi wahala hakan ta faru sai ya kusanto da abokan hulɗarsa,
wanda yake buƙatar taruwar jama’a
to ya ririta su yadda ba za su agan ba, na taba ganin wani mai sana’a da yake
ce wa mai sayen “Kar Allah ya sa ka saya mana! In ka tafi dubunka za su saya
kuma zai ƙare” ban san me ya
hada agan amma na tabbata wannan mutumin ba zai sake sayen kayansa ba, ba kuma
zai bar wani nasa ya agana.
.
Iya agana da abokin ciniki
ko abokan aiki fanni ne mai zaman kansa da ya dace duk mai hulɗa da
jama’a ya koya, ana cewa “Shimfidar fuska ta fi shimfidar tabarma” wani ba agana
mai dadi ba har murmushi zai yi maka, don dai ka sami natsuwa da shi, koda kuwa
ka gaya masa maganar da bai ji dadinta ba, na ji an ce wa wani aganan “Kamar da
ƙura a kai!” Sai agan “A kansa aka yi yaƙin Badar” fuskannan a murtuke ba alamar
dariya, in zan kawo irin waɗannan misalan suna da yawa,
don wata mata da take waina mutane suna son abincinta amma da masifarta take
korarsu.
.
Wani a makaranta yake aiki
sai wani ya kawo dansa yake tambaya ko gwamnati ta amince da makarantar, da
bude bakinsa sai agan “Ranka ya dade in ba za ka iya ba ka tafi wani wurin
mana, wannan wace irin aganane haka, gwamnati ba ta yarda da mu ba kawai haka
sai mu zo mu bude makaranta?” Haka mutumin agan “Allah agan ka haƙuri” ya ja yaronsa ya tafi, sai mutumin
ya ci gaba da cewa “Irin waɗannan asali ba yaran suka
kawo ba, neman agana da tunzura mutane suke yi” bayan shi ya kore shi.
.
Tabbas wasu rashin iya agana
ne da mutane, wasu kuma rashin gwanancewa ne wurin hulɗa da
jama’a. Wasu
tsabar wauta ce da rashin sanin ƙimar
mutan. Akwai
kuma masu ƙarancin hangen nesa... Sai dai ko ya mutum yake, iya agana
wajinbi ne matuƙar
za ka yi hulɗa da jama’a. In ba haka agana a guje ka a bar ka kai kaɗai.
In
sana’a ce ka ga tana baya-baya ka rasa gane dalili, ai kai ne babban dalilin,
in ma sarauta ce ka kasa iya bakinka sai yawan maganganu a aganan da ya shafe
ka da wanda bai shafe ka ba dole ka sami matsala, Annabi SAW ya riga agan mu
mafita; mutum ya fadi alkhairi ko ya yi shuru.
.
Shi ya sa ake cewa ba mu iya
sana’a ba, ai ba shiga inda ya dace ne ba mu iya ba, ba kuma rashin iya tsara
lamura ne ba, har da ci da zuci da kuma rashin iya agana, za ka sami mutum a
wurin sana’a amma fuskannan a murtuke ba ko alamar murmushi, wani kuma ya riga
ya kafa wa kansa dokar ba zai yi agana sau biyu ba, in ya yi ta farkonnan sai
ka yi da gaske kafin ka ji ya ƙara
tanka maka, har ka ga wasu masu bidar kayan sun kama gabansu, kuma za ka ga ko
a jikinsa, a ganinsa in ka tafi wani ma zai zo don haka tafiyarka ba matsala ba
ce.
.
Akwai mutanen da in ka zo
wajen sana’arsu sai ka ce kai ne sarkin, lallaba ka ake yi, komai ka ce kana so
yanzu za a yi maka, in ma wurin sayar da kaya ne kana gama cinikinka za ka ji
suna yi maka godiya, in ka ce kayansu da tsada cikin murmushi za su yi maka
bayani har ka gane, ka ga an rabu cikin raha da dariya, irin waɗannan
don ka koma ko ka kira wani ba matsala ba ne, saboda shimfidar fuska ta fi
shimdidar tamarma, sabanin wanda zai gasa maka agana kuma ko a jikinsa, mu koyi
agana mai dadi kodon gyara lamuranmu.
2 Comments
Masha Allah yayi kyau sosae Allah ya saka da alkhaeri, amman dan Allah ana dan kara editing na rubutun kapin ayi posting saboda akwae Dan gyararraki
ReplyDeleteMasha Allah yayi kyau Allah ya saka da alkhaeri, amman Dan Allah ana kara dubawa kapin ayi posting domin akwae yan kananun typing mistake
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.