Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata // 21: Wasu Mazan Ke Kaimu Wuta



In dai tana son ta yi aure dole sai ta nuna rashin damuwarta da tsohon mijin, gami da nuna wa sabon bazawarinta muguwar ƙauna yadda ba zai canja ra'ayinsa a kanta ba ko da 'yan uwansa mata sun kawo masa gulmar cewa kashe wuta za ta yi da shi. Wanda idan haka ne, to zai aure ta kuma ba zai sami kwanciyar hankali ba sai ya sake ta. Don kuwa ba shi a zuciyarta ko kaɗan. Duk soyayyar da ta nuna masa a waje ƙarya take yi. Kenan...

Kundin Ma'aurata // 21: Wasu Mazan Ke Kaimu Wuta

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Tabbas wasu mazan kan taimaka wajen kai matansu wuta, ƙila kuma wannan kan fara ne tun daga zabin miji har zuwa rayuwar aure, ko dai uba ya ce ya yi wa yarinya miji don haka ba ruwansa da wanda ta ce tana so, ko uwa ta zabar mata wani ɗan uwanta saboda zumuncinta, ko kuma tana ganin abin kunya ne ɗan wajen wane ko wance ya ce yana son diyarta amma ta kasa hada auren, in ba haka ba kuma shi kansa mijin, yarinya ta nuna ba ta son sa shi kuma ya dage sai ya aure ta, duk ƙiyayyar da take nuna masa ya ce wai yaranta ce ko kuma kunya, bayan waɗannan abubuwa guda biyu sun yi nesa da ƙiyayya a zahiri.
.
Hidimar mace ga mijinta, tsafta da gyaran gida, jiki ko sutura, gami da ƙoƙarin faranta wa maigidan ta kowane hali, da tausaya masa ko gyara abincinsa, gami da ƙoƙarin tada masa da sha'awarsa ta fuskoki daban-daban yadda zai kai ga biyan buƙatun shimfida, da ƙoƙarin kauce wa duk abin da zai baƙanta masa rai ta kowace fuska wannan ake kira soyayyar da mace za ta bayar, kuma su din ne dai ake kira aure, bai yuwuwa a same su kafin auren, dalilin da ya sa muke kawar da tababar cewa ba wata soyayya kafin aure, in ka auri mace ba ta son ka ba yadda za a yi ka ga wannan soyayyar a wurinta, duk abin da ta san cewa ranka zai yi daɗi in ta yi ma shi ba za ka gani ba a wurinta, don ma kar ka zaci tana son ka.
.
Na taba yin gardama da wata marubuciya kan samun soyayya kafin aure, inda ta kafe kan cewa tabbas mace tana fitar da soyayyarta ta gaskiya gaba daya ga namiji kafin aure, duk sauran abin da muka ambata a sama ta ce wannan hidima ce ko tana son namiji in ranta ya baci za ta iya bijire masa, na ce "Ya kike gani kuma idan ba ta son sa?" Na ce "Meye fahimtarki idan mace tana mugun son namiji kowa ya sani, ga shi ma har tana da 'ya'ya tare da shi daga 4-7, sai wani tsautsayi ya sa maigidan ya banka mata saki 3, amma shi ma yana mugun son ta!" Ita marubuciya ce ta san inda nake son zuwa, sai ta tsaya a kan ra'ayinta ta ƙi ba ni amsa.
.
In dai tana son ta yi aure dole sai ta nuna rashin damuwarta da tsohon mijin, gami da nuna wa sabon bazawarinta muguwar ƙauna yadda ba zai canja ra'ayinsa a kanta ba ko da 'yan uwansa mata sun kawo masa gulmar cewa kashe wuta za ta yi da shi. Wanda idan haka ne, to zai aure ta kuma ba zai sami kwanciyar hankali ba sai ya sake ta. Don kuwa ba shi a zuciyarta ko kaɗan. Duk soyayyar da ta nuna masa a waje ƙarya take yi. Kenan irin maganganun da muke gani a fima-fiman Hausa labarai ne kawai, soyayya ta gaskiya a gidan miji ake farawa, in ma'aurata daya ba ya so to babbar mafita a nan kar uwaye su hada auren, komai ƙaunar da suke yi su haƙura shi ne kawai mafita.
.
Wani hadisi da Buhari da Muslim suka rawaito, Annabi SAW yana cewa "In mace ta kwana nesa da shimfidar mijinta (ta ƙi yarda ya sadu da ita), mala'iku za su yi ta tsine mata har ta wayi gari" to ko tsinuwar mahaifa ya take bare ta mala'iku? Macen da aka yi mata auren dole ko wace ta yi auren kisar wuta abubuwan da suke faruwa kenan, to da muguwar rawa ai gwara ƙin takawa, ba ƙaramin abu ba ne mace ta riƙa saba wa maigidanta, wanda wani lokaci mu mazan muke tunkuda su wajen auro su ko aurar da su ba bisa son ransu ba.
.
A wani hadisin na Buhari da Muslim Annabi SAW yana cewa "An nuna min wuta sai na ga galibin 'yan cikinta mata ne,  saboda kafurcewarsu" aka ce "Suna kafurce wa Allah ne?" Ya ce "Kafurce wa miji da kyautatawa, da za ka kyautata wa wata tsawon rayuwarta, in ka yi mata wani abin (da ranta bai so ba) sai ta ce " Me ka taba yi min!" Wannan in tana son ka kenan fa! Ina ga tun asali ba ta ƙaunarka? Wannan farar fatar ko muguwar sha'awar da kake yi mata in har ka aure ta ba ta son ka wallahi har mai sunanta sai ka ji ba ka so.
.
LADABI DA BIYAYYA
Asalin aure kenan a wurin uwayemmu, shi ya sa yawancin fadan da suke yi wa 'ya'yansu ba ya wuce "Yi na yi, bari na bari" in ba wannan to ba aure, don shi ne yake tabbatar da ƙaunar juna a zukatan ma'aurata, duk abin da maigida zai yi umurni da shi, matuƙar babu sabon Allah a ciki, yana da alaƙa da aure kai tsaye ko babu, kamar shimfida, hidimar miji ko na zumuntarsa, kasuwancinsa, ko tarbiyar yara, ya dace mace ta yi masa, kuma kar ta yi gardama, da yawan mata yawan gardamarsu take kashe musu aure, don za ka taras maigidan yana fada suna fada, har ransa ya baci ya dauki wani matakin da bai yi niyya ba.
.
Nawawiy a sharhin Muslim wurin da aka ambato cewa A'ishah RA ta wanke wa Annabi SAW tufafinsa yake cewa: "Ya halasta mace ta wanke wa miji kayansa, ta dafa masa abinci bisa yardarta, saboda dalilolin da aka samu a hadisan Annabi SAW, da yadda matan magabata suka yi da mazansu, da maganganun malamai a kai" yanzu wasu matan ba wankin kayan da sauran hidima ba ko gidan ba za su zauna ba, su ma ma'aikata ne, hatta tarbiyar yaran nasu sai dai a yi musu, a ganinsu wannan ma haƙƙinsu ne a kanka.

Post a Comment

0 Comments