"Anya
wannan mutumin ba zai bi ta ba kuwa?" Don wasu matan da dama ba sa iya
tsawon rai bayan rasuwar maigidan da suka ƙwallafa
rai a kansa. Na san
matan da suka bi mazansu da 'yan kwanaki kaɗan.
Akwai
ma wata da yanzu take gidan mijin, uwayenta sun yi faɗa har sun gaji ta ce....
Kundin
Ma'aurata // 22:
Don Me Na Ƙaunace
Ki?
Baban Manar Alƙasim
Zauren
Markazus Sunnah
Ina
ganin akwai zubar da ƙima
ba kadan ba mace ta yi tsammanin don zaman gida da harkokin shimfida kawai aka
auro ta kuma iya abin da za ta yi kenan, akwai mata barjak a duniya, kuma kowa
na da wannan halitta ta matantaka, me zai sa na watsar da kowa sai ke, har na
riƙa jin in ba ki rayuwata ba za ta kammala
kamar yadda nake buƙata
ba? Ba shimfida ce ba kadai Hajia, akwai wasu abubuwan ƙari a kan haka:-
1)
Zan danƙa miki komai ne na rayuwata a hannunki,
ina sa rai za ki kula da duk abin da zai sa raina ya yi haske, ki sa a yi nesa
da duk abin da zai baƙanta
min rai, za ki sa wata kadada tsakanina da abin da yake so ya wargaza min gida
ko zumuntata, za ki yi ƙoƙarin ganin farin cikina a kullum yana
hannunki, za ki dauki ragamar kawar min da baƙin
ciki a duk lokacin da kika ga yana ƙoƙarin kawo min farmaki.
.
2)
Duk wani abin da zanci kuma a cikin gida zabinki ne, ke ce za ki rarrabe abin
da nake so da wanda nake buƙata,
gwargwadonsa da dandanonsa, da yanayin dafuwarsa har ma da abubuwan da aka zuba
a ciki, gami da sanin lokacin da za a ci din, kin san abin da in na ci zai bata
min ciki da wanda zai kwanta lafiya, kin kiyaye irin abincin da ba na buƙata da daddare saboda kauce wa
matsalolin shimfida, kamar zobo mai sanyin gaske ko cin ganyen latas mai dama a
lokacin kwanciya, kiyaye waɗannan abubuwa ne na
tsayayyiyar mace.
.
3)
Idan rashin lafiya ya kama ni ke ce ta farkon da zan nema, ba don kina ba da
magani ko waraka ba, yanayin kularki da tausayinki, da kawo min duk abin da
nake buƙata, har ki mai da ni tamkar danki,
wajen rarrashi da sauransu, ba ki ƙyamar
wani abu a wurina kasancewar ban da lafiya, da haka ko ciwon kai nake yi sai na
gaya miki, don kin san irin magungunan da nake buƙata,
duk abubuwan da likita ya yi bayani kina wurin kuma kin haddace su gaba daya,
lokutan shan maganina na zuwa kin dauko min ga ruwa kin kawo min, ko na ƙi sha za ki matsamin ta wajen gaya min
dadadan maganganunki, za ki yi iya ƙoƙarinki wajen ganin yara ba su dame ni
sun hana ni barci ba, za ki tantance irin maganganun da za a iya gaya min a
lokacin, da waɗanda ba na buƙatarsu.
.
4) Dukiyata
kina ganin naki ne da duk waɗanda suke cikin gidan, amma
ba ke ce kike da haƙƙin
taba su ko juya su ba, don haka ba kya sanya ido ko kadan a ciki in ba wanda
aka ba ki a hannu kuma aka nuna miki ga abin da ake buƙatar ki yi da su ba, sannan za ki yi iya
ƙoƙarinki
wajen ganin ba a yi almubazzaranci da su ba, in buƙatun yau sun biya sai a adana sauran don
gobe, kina iya bakin ƙoƙarinki wajen asusunta abubuwan dake
shiga hannunki don magance ranar da za a rasa wani abin, akwai daɗi a
ce komai ake buƙata
kuna da shi amma almubazzaranci saboda wadata ba dabi'ar mace ta ƙwarai ba ne, takan dafa ko ta sa a dafa
abin da suke da buƙata
ne kawai, ba wai a ci a bar shi ya lalace a zubar ba.
.
5)
Ina sa rai da komai na gida yana hannunki ne, in bananan kamar inanan ne, don
kin wuce mataimakiyata, gidan kacokan dinsa naki ne, 'yan uwana ba za su ji
wani bambanci tsakanina da ke ba, to bare kuma mahaifiyata, har 'yan uwana mata
su gummace su yi magana dake sama da ni don ke ce 'yar uwarsu mace za ki fi
fahimtar abin da suke nufi cikin sauƙi,
'yan uwanki in sun zo sun san darajar nawa, sun kuma san iyakarsu, don haka
akan hadu cikin mutunci a rabu ba tare da matsala ba, duk wani abin da zai bata
sunan gidana kin taka masa burki ko ma kin kawar da shi, mata masu gulma da
tsugudidi kin yi musu iyaka da gidanki don neman zaman lafiya da maigidanki,
idonki a bude yake ga duk abin da yake faruwa a cikin gidan.
.
6)
Ba wani abu a dakinki wanda zan kalla ban yi sha'awa ba, komai an gyara shi
kuma an ajiye shi a inda ya dace, wurin da yake buƙatar guga da tsaftacewa tuni kin gyara,
haka kicin dinki da ban-daki kamar tsakar gida ne, ke kanki suturarki
tsaftatacciya ce, in ina ɗaki daga ni sai ke ƙamshinki kawai yake tashi sai jan
hankalina kike yi da halittarki da kwalliyarki da adonki, maganarki mai daɗi
cikin kwanciyar hankali, a tsawon zamanki da ni, in zan shugo sau dubu ba abin
da nake gani sama da wanda zai faranta rai, sam ba ki yarda kin girma ba bare a
yi maganar tsufa, a kullun kina jin cewa jin daɗina
yana hannunki ne kuma ke din ce dai za ki ba ni, ƙamshinki
sai tashi yake ta ko'ina, ɗaki ga kayayyakin ado a inda
na juya, kin yi shafe-shafe ga tozali rambadadau, lallen dake hannunki kuwa ko
ke kanki kin san yana jan kankali, suturar jikinki ko diyarki ce ta cikinki za
ta shugo dakin sai kin ɗan gyara, ta ya ba za ki
mallake zuciyata ba?
.
6)
'Ya'yana da kika haifa da wanda wasu suka haifa min duk kin mayar da su
'ya'yanki na cikinki, kin ba su tarbiyya ta ƙwarai
don gyaran sunan gidan da ke kanki gaba daya, ba ki taba rarrabe cewa waɗannan
ke kika haifa ba a baki bare ki raba abincinsu ko suturarsu ko tarbiyarsu, duk
abin da za su yi tare suke yi, hatta maganganunsu kina lura da irin furucin da
suke yi, kin ƙi ba su damar kishi
ya shiga tsakaninsu bare wani ya ware daya daga cikinsu da tunanin cewa ɗan dakinsu
ne ko ɗan wani
daki, kin yi ƙoƙarin hada kansu tun suna ƙanana, ta yadda kowa zai yi wani abu
gidan gaba dayansa yake kallo, kowa a cikinsu yana ƙaunar ɗan uwansa
ba tare da jin cewa a dakinsu yake ko a wani ɗaki ba,
duk wannan kina yi ne don kin sani cewa wajibinki ne da ya zama dole ki kiyaye
ba don mijinki ya yaba miki ko don jama'a su ce kin yi ƙoƙari
ba, shi ya sa ma yaran ko kadan ba su san cewa ke ce mahaifiyarsu ko ba ke ce
ba, in mahaifiyarsu na tare da su duk daya suke ji, in ma ba tanan ko an hure
musu kunne sun san abin da yake wakana.
.
Wannan
ba ƙaramin aiki ba ne, kin ga in kika yi
tsammanin jikinki kawai namiji yake buƙata
kin zubar da ƙimarki, kina da
abubuwa da dama waɗanda ba za su samu ba sai a
wurinki, in ma rasuwa kika yi zai dade bai manta ki ba, kwanannan ba a jima ba
wani mutum da ya rasa matarsa na je yi masa ta'aziyya, a maganganunsa na ce a
zuciyata "Anya wannan mutumin ba zai bi ta ba kuwa?" Don wasu matan
da dama ba sa iya tsawon rai bayan rasuwar maigidan da suka ƙwallafa rai a kansa. Na san matan da suka bi mazansu
da 'yan kwanaki kaɗan. Akwai ma wata da yanzu take
gidan mijin, uwayenta sun yi faɗa
har sun gaji ta ce ba za ta yi aure ba sai ta aurar da duk 'ya'yanta maza da
mata, ta dena fita waje gaba dayanta in ba wasu sha'anunnuka na addini ba,
madalla da matar da ta san ƙimar
namiji, ta san cikakken abin da ake kira aure, Hajiya don waɗannan
na auro ki ba don jima'i kadai ko zama a gida ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.