Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma’aurata 26: An Ji Kai Ne Babba!


Da dama wasu mazan ba su ɗauki mace a matsayin mai hankali da tunani ba. Shi ya sa ma ba sa tuntuɓarta a komai. Kai an kai matsayin da in wani ya faɗi magana za ka ji an ce "Wannan maganar mata ce" wato dai maganar banza! Alhali ba kowace magana ce ta mace take maganar banza ba. Asali ma in ka ga gidan mutum a ɗinke tsab-tsab to akwai fahimta mai ƙarfin gaske tsakaninsa da iyalinsa. Wasu lokutan da dama za ka ga matan su suke...


Kundin Ma’aurata 26: An Ji Kai Ne Babba!

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Zamanka babba ba ya nufin ka zama baba, mu a wurin 'yammata duk ranar da ka ji za ta gaishe ka ta ce "Sannu baba!" To ta yi niyyar wulaƙanta ka ne, in kana da tunani ka taimaki kanka ka kama hanya, mata masamman wace ta san namiji sosai, in har za ka neme ta, ko ta boye sunanka wata rana zalla za ta kira ka, ba zancen malam Ƙasim, "Ƙasim" ɗin zalla za ta kira.
.
Irin wannan tana ganin wai tana da wani matsayi kenan ba kamar sauran mata ba a wurinka, sai kuma in ta aure ka malam ɗin ko Alhaji ya dawo, in kuwa haka ne to ka lura da wannan matsayin a cikin gida, kai ne mai gidan, ita kuma uwar gida ce, ita ce mutum na biyu a wannan masarautar, kuma tana darewa kujerar a duk lokacin da ba kanan, ya dace ka ba ta wannan matsayin yadda za ta jagoranci gidan sosai.
.
In kana yawan zubar mata da ƙima a gaban 'ya'yanta ba za su taba jin cewa tana da wani matsayi na jagoranci ba bare ta ba su umurni ko hani, ka ga babu wata cikakkiyar biyayya da za ta samu kuma kai ka zubar mata da wannan ƙimar, ka riƙa sauraronta a lokacin da take magana, in ta kawo ƙarar wani gabanka ka yi gaggawar daukar mataki a kai, albashi ka ja mata kunne a gefe in abin bai kai yadda ta dauka ba, ko kuma ba ta fahimce shi ba samsam.
.
Wani abu ya taba faruwa ban san lokacin da ya faru ba, amma na ji maigidan yana jawo hankalin iyalinsa da cewa bai son zubar mata da ƙima ne shi ya sa ya saka baki, amma ta kiyaye gaba, ta dena yi wa 'yan uwansa irin wannan mu'amalar, ya ce yana lura da yadda take mu'amalla da 'yan uwansa, bayan kuma su ne masu gida 'yan uwanta 'yan karo ne.
.
Ya gaya mata maganganu masu zafi, wadanda in ita mai hankali ce za ta shiga taitayinta, ban san abin da ya faru ba ba kuma zai yuwu na bincika a matsayina da dan jarida ko mai bincike da fashin baƙi kan ilimin zamantakewa ba, amma bisa ga dukkan alamu tana munana wa 'yan uwansa ne, kuma tana kyautata wa nata, shi kuma ya san haka sai dai yana jiran lokacin da ya dace ne ya yi mata magana, 'yan uwan nasa sun yi mata wani rashin kunya ta kawo ƙararsu wajensa, ya ɗauki mataki a gabansu kamar yadda ya dace.
.
Duk da cewa ya yi musu fada, sai dai kuma ya same ta a gefe don jan kunnenta da nuna mata cewa ta shiga taitayinta, kuma ta san matsayinta a gidan, sannan ta san cewa yana sane da duk abin da yake wakana a gidan, in har maigida ya mutunta matarsa ya karramata, tabbas za ta fi samun ƙarfin jagorancin gidan kamar yadda ya dace.
.
In kuwa ya yi mata riƙon sakainar kashi, ko ya wulaƙanta ta, mai zubar mata da shara ma ba zai dauke ta wani abu ba, daganan babu gida kuma, babu ko shakka sakar wa mace gida gaba daya kuskure ne, ba don ba za ta iya jagorancinsa ba, wasu abubuwan ba nata ba ne, na namiji ne, ita kuwa mace ce, to amshe gidan kuma gaba daya ya fi matsala, don ita take ciki kullum, ka bar mata sitiyarin gidan, amma ka riƙa sanya ido kan yadda take tuƙawa.
.
Ka san inda take aje kowa; ya take mu'amalla da uwayenka, 'yan uwanka da sauran jama'a? Inda bai kai ba a ƙara, inda ya wuce a rage, wannan duk za ka iya yinsa cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, na sha ganin mutanen da ba wani abu tsakaninsu da iyalinsu sai umurni da hani, "Ke, yi kaza! Bar kaza?" Irin wadannan mutanen in har iyalinsu suka yi kuskure fada za su fada ta da ita, ba ruwansu da kula su ga ko waye a wurin, ga shi kuma ba sa daukar raini komin kasawarsa, shi ya sa ƙaramin abu ma a wurinsu raini ɗin ne komai ƙanƙancinsa, to yaushe za ka sa rai za su zauna da iyalinsu don tattauna wata matsala?
.
     KAR KA RAINA MATA HANKALI
Da dama wasu mazan ba su ɗauki mace a matsayin mai hankali da tunani ba. Shi ya sa ma ba sa tuntuɓarta a komai. Kai an kai matsayin da in wani ya faɗi magana za ka ji an ce "Wannan maganar mata ce" wato dai maganar banza! Alhali ba kowace magana ce ta mace take maganar banza ba. Asali ma in ka ga gidan mutum a ɗinke tsab-tsab to akwai fahimta mai ƙarfin gaske tsakaninsa da iyalinsa. Wasu lokutan da dama za ka ga matan su suke ba wa mutum shawarar yadda zai gyara zumuntarsa, da ma mu'amalarsa da gidansa, matarka tana shugowa gidanka tarbiyantar da ita, saka ta a hanyar da kake so ka gan ta, nuna mata abubuwan da suka dace da wadanda za ta guje su, wannan shuka alheri ka yi, kuma za ka girbi abinka, don za ta dawo tana gyara maka gidanka, tana ba ka shawarwarin abubuwan da suka kamata.
.
Wadanda suka raina hankalin mace duk in ta yi magana tsoki za su yi "Mts!", ko su yi watsi da ita, wani cewa zai yi "Rufa min baki" ko kuma "Ka ji maganar banza!" In ta gaji watsi da shi za ta yi, da wahala kuma ka ga suna tattauna wani abu na gida ko na rayuwa, gida kuma ya rasa wani abu mai mahimmanci, maigidan ma ba kowani abu zai sani ba, in ma 'yan uwansa ne suka yi wani abu matar kama bakinta za ta yi don ta san ƙarshen lamarin, Allah ya kyauta.

Post a Comment

0 Comments