Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma’aurata 28: Mummunan Zato!!


Mutane da dama za ka ji ana fassara hakan da kishi, wanda haka ɗin ne ya bayyana. Ana cewa "Wane yana da zafin kishi!" Ba kishi ba ne. Mummunan zaton kaza zai iya faruwa ne ya haifar da haka. Na ga wani dan boko da ake yaba wa mugun kishi. Shi yake kai matarsa Islamiyya, ya jira sai ta gama abin da take yi ya ɗauko ta ya dawo da ita. Duk da cewa makarantar mata ce, bai damu ba ya tsaya a cikinsu yana jiran matarsa sai ta fito ya ɗauke ta su...


Kundin Ma’aurata 28: Mummunan Zato!!

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Shi zato kowani iri ne yana bata alaƙar dake tsakanin mutane, don haka barinsa shi ya fi, za mu iya kasa shi biyu, na farko dai da zarar saurayi na ƙwarai ya zo neman mace, komai kintsuwarsa da sanin ya-kamatansa sai an sami wanda yake cewa ai a danginsu akwai wane, ga dabi'unsa da halayensa, in ba a yi sa'a ba sai ka ga ana neman kai ruwa rana, wani auren ma babban dalilin da zai hana yuwuwarsa kenan, duk da cewa kowa ya san saurayin da dabi'unsa da addininsa da halayensa duk na-gari ne, kuma ba a taba jinsa da wani ba, amma mummunan zato ya hana a ba shi mata, ita ma kazalika, don an yi wani lokaci da uwayen wani yaro suka tsaya kan cewa ba su yarda ya auri wata yarinya ba saboda shahararta.
.
Shi kuma yaron ya kafe a kan cewa in ba ita ba sai rijiya, bayan tsawon lokaci, da kuma tsoron cewa in fa ba a yi ta halas ba za a iya yi ta haram, sai uwayensa suka sauko aka daura auren, tsakani da Allah yaron ya sami albarkar da bai da irinta a wasu wuraren, kuma kullum suna cikin soyayya da fahimtar juna, ni ban ƙi ba a yi zabin na gari, amma mummunan zato bai yi ba, kafin a daura aure har an fara tunanin in auren bai yi kyau ba ya za a yi? Ko in aka sake ta daga baya alhali ta riga ta tara yara ya za a yi? Me zai sa ba za a yi tunanin cewa auren zai yi kyau ba, kuma daganan an huta kenan in sha Allah?
.
Abu na biyu kuma maigida ya riƙa sakawa a ransa cewa yanzu haka wance ta yi kaza, ko tunda na ga kaza so take ta yi kaza, irin wannan ƙananan zace-zacen su ke tunkuda mutum ya fara tunanin cewa "Tunda wance ta ce tana wuri kaza, na kira wurin aka ce ba ta, ina ta je kenan? Ƙila ma kaza ne" Sai ka ga ya fara bibiyarta yana bincike kamar wace take aikata mummunan abu, daganan kuma ya hana zuciyarsa hutu kenan gaba daya, don in ya shiga damuwa zai yi wahala ba ta bayyana a ma'amalolinsa na yau da kullum tsakaninsa da ita ba.
.
Mutane da dama za ka ji ana fassara hakan da kishi, wanda haka ɗin ne ya bayyana. Ana cewa "Wane yana da zafin kishi!" Ba kishi ba ne. Mummunan zaton kaza zai iya faruwa ne ya haifar da haka. Na ga wani dan boko da ake yaba wa mugun kishi. Shi yake kai matarsa Islamiyya, ya jira sai ta gama abin da take yi ya ɗauko ta ya dawo da ita. Duk da cewa makarantar mata ce, bai damu ba ya tsaya a cikinsu yana jiran matarsa sai ta fito ya ɗauke ta su koma gida.
.
Amma ba wata shiga ta sosai irin wace matan masu kishin suke yi, shi kansa irin riƙe ta da wasu ayuyyukai irin na turawa da yake yi da ita a gaban jama'a ba sa nuna cewa kishi yake, na fi ganin cewa shi a dolenan wayayye ne, kuma mu'amalarsa na nuna cewa yana mugun ƙaunarta ne, sai dai kuma ba ta isa ta yi wani motsi ba koda ya shafi lafiyarta ko zumuntarta ko cikinta in ba yananan ba, ita da kanta tana kukan irin halin da take ciki, duk kuwa da cewa mata da yawa suna yaba irin rayuwar soyayyar da take yi da maigidanta, gaskiya addini ya yi, ba tsanani ba sakaci, kishin namiji ga matarsa abin ƙauna ne, fitar da sirrin gida kuma rashin kishi ne.
.
                ME ZA KA YI?
Mun yi maganar dabi'o'in mace a baya, masamman yadda wani sa'in take daga wa maigidanta murya, akwai macen da harshenta kullum a sama ne, sai dai shi namijin ya yi haƙuri ya ƙyale ta, kafin ya faɗi 2 ta faɗi 10, sannan ta ƙi fahimtarsa da gangan, komai ya faɗi sai ta canza masa, irin wadannan dabi'u ba sa fitowa fili ga mace sai ta jima tare da namiji, kodai don ta zuba masa 'ya'ya, ko kuma togo da ta kwashe shekaru da shi ita ce tal kuma ƙwallin-ƙwal, akan iya magance matsalar ta hanyoyi biyu, hanyar farko ka yi mata shuru ka kafe ta da ido kar ka yarda ku riƙa musayar yawu, wannan ba ƙimarka ba ce, sannan in ka fusata sosai za ka iya yin hujuncin da ba ka yi niyya ba.
.
Ja bakinka ka yi shuru, ba za ta yarda ku hada ido ba, za ta yi iya ƙoƙarin kauce wa hakan, idan ta natsu ka jawo hankalinta ka nuna mata kuskuren ƙarshe na rashin daukarka da wata ƙima, shi ma ɗin za ta yi ƙoƙarin yin gardama tare da dawo da abin da ya faru a baya, anan in ka yi mata tsawa za ta natsu, sabanin farko, daidai wannan lokacin sai ka koma rigimar farko ɗin ka yi mata irin maganar da ta dace da abin da ta aikata, in wannan ba zai yuwu ba to babban abin da ya kamata shi ne ka yi tafiyarka ka ƙyale ta, wata saboda da bala'i za ta jira ka sai ka dawo, wata in ma daki ka shiga za ta bi ka, wata ko waje ka fita za ta biyo ka ta shaƙe ka a can.
.
Irin wadannan matan in dai ba tsaface ka aka yi a cikin ƙwai ba, to gaskiya ba ta dace da kai ba, in so cuta ne to haƙuri magani ne, ka zama namiji ya fi a ce kana kallon kanka cikin sutura, kowa yana ganinka tsirara, wasu matan ba kowani namiji ne yake yin daidai da su ba, na taba jin ana maganar wata da irin halayenta yadda ta zauna shuru a gidan mijinta, sai wani yake cewa wannan duk yadda ta kai da iskanci ko rashin mutunci mijinta ya dama ta ya shanye, shi ne ya kawo keta masa riga da ta taba yi a gidan haya, shi kuma ya hada mata yawu da majina, duk jikinta ya tashi, yarinyar ta yi yaji uwayenta suka mayar da ita a ranar ba tare da biko ba, na ce "Maganin shege dan banza!".

Post a Comment

0 Comments