Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma’aurata 36: Me Ya Sa Ake Son Ki?


Akwai wasu abubuwa guda 3 waɗanda kowani namiji yake biɗa a wurin mace. Ko da yake mun faɗe su a warwatse cikin rubuce-rubucen baya (Kundin Ma’aurata 1-35), yanzu ya kamata a dunƙule su...


Kundin Ma’aurata 36: Me Ya Sa Ake Son Ki?

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunna

1) ZAMA TA ƘWARAI: Wannan ba ƙaramin abu ba ne, tunda rana guda mace ba za ta iya dakar ƙirjinta ta ce "Daga yau shi kenan na zama ta ƙwarai" ba, dole dai lamarin yana buƙatar ilimi koda kuwa wanda za a dauka daga wurin uwaye ne a dabi'ance, kamar dai kyautata hali a adɗinance, shi ya sa ma Annabi SAW yake cewa a ruwayar Bukhari da Muslim "A dabi'ance akan auri mace don abu 4 ne: Don kuɗinta, danganenta, kyawunta da addininta, amma ka auri mai addinin don ka rabauta".
.
Kamar mutum yana buƙatar natsuwa da gina zuriyarsa a kan aƙida ta ƙwarai da kamewa, sai da tashinsa ya auro 'yar Shi'a, wace ta saba holewa a mutu'ance ana biyanta, anan an yi asarar abu biyu, ba addini ba dabi'a, koda kuwa mace ce da take son aure ta yi kuskuren auren dan Shi'a a sakamakon rashin binciken addininsa, ita ma irin abin da zai faru kenan, ba a jima ba wani abu ya faru, inda wata bisa kuskure ta auro dan Shi'a, ana rayuwa cikin rade-radi, har dai abubuwa suka bayyana mata, ta jure ta zauna kan ba yadda za ta yi.
.
Bayan wasu 'yan kwanaki sai ya ce mata zai yi tafiya zuwa Katsina, can zuwa dare sai ga wani dan-uwa (Kamar yadda suke kiran kawunansu) ya shigo, ya tambaye ta "Nan ne gidan wane kaza-kaza?" Ta amsa masa, ta ba shi kujera ya zauna, ya ci abinci suka ci gaba da hira, zuwa can da yake dare ne sai ya yi yunƙurin kulle ƙofa, ta ce "Ya haka?" Ya yi mata bayani a Shi'ance sannan ya ce mata yanzu haka mijinta yana wurin matarsa, shi ma ya je aron al'aurarsa saboda namiji garkuwa ne.
.
A taƙaice dai ta ce masa "To bari na zo" ta shiga makewayi daganan ta sami sa'a ta yi waje, rabuwarta da Shi'a kenan na har abada, irin wadannan zinace-zinace da sunan addini ba sabon abu ba ne, ko a watan da ya gabata wani fitaccen dan Shi'a a fesbuk yake cewa ya hole da mata sama da 20 da sunan mutu'a, kuma ya ce duk 'yan sunna ne, cikin alfahari da sakin jiki, wato Nasir Jafar, idan irinsa da ake ganin malami ne, kamamme, mai cusa aƙida ta ƙwarai da tsawatarwa don gudun saba wa mahalicci a cikinsu yana alfahari da holewa da 'ya'yan mutane waɗanda a aƙidarsu hakan zina ce, ya labarin gama-garinsu waɗanda babu ilimin ma?
.
Bisa ga wannan dalili dole ki san wanda za ki aura, meye aƙidarsa da addininsa? Don kar ya kai ki ya baro, jiya-jiyannan wata take cewa ƙawarta ta yi kuskuren daukar ƙara da kiyashi, ta auro dan Shi'a ba ta sani ba, ta yi matuƙar adawa da addinin nasa, amma daga baya an ga tana sanya baƙaƙen kaya, na ce dama Bahaushe ya ce "Zama da madaukin kanwa yana kawo farin kai" wannan madaukin kanwa ne kawai, ya maganar masoyi?
.
Shi ya sa addini ya tsawatar kan mummunan zabi ya ce "Bawa, mumini ya fi (da) mushriki koda ya ba ku sha'awa" mas'alar ba tana liƙe da mutum ba ne a kan kansa, a aƙidarsa ne ko addininsa, kuma duk yadda kika kai da fahimtarki da wayewarki ba ki isa ki gano namiji ba, sanya a yi miki bincike 'yar uwa, ko binciken ma sanya na jikinki, su ma ɗin ba mutum guda ba, kuma kar ki yarda masu binciken su san juna, ki bincika har mutanen unguwarsa waɗanda kike ganin sun san shi kuma za su iya gano aƙidarsa, ko ya kika sami abin suka a cikin dabi'arsa da addininsa to ki bincika, yanzu shi wancan da ya hole da mata sama da 20 in ya dauko ƙanjamau wa zai fesa mawa?
.
Idan mace ta zama ta ƙwarai akwai abubuwa da dama da ake sa rai da cewa za su fito a ƙarƙashinta:-

i) Lada a sakamakon tsayawa ƙyam da ta yi wurin bauta, kodai bauta wa Allah SW kai tsaye, ko kuma yi wa maigidanta hidima, Allah SW ya ce duk wanda ya yi aiki koda da ƙwayar zarra ne zai ga abinsa.

2) Rayuwa ta jin dadi, saboda abin da Mahalicci SW ya ce "Wanda ya yi aiki na ƙwarai, namiji ne ko mace a matsayin mumini za mu sanya masa rayusa ta ƙwarai".
.
3) Ma'auratan za su ji daɗin zama da juna, wannan kam kowa yana gani a aikace, duk auren da aka yi a kan imani da tsoron Allah.

4) Tarbiyantar da yara a turba ta ƙwarai.

5) Maigida da uwargida kowa zai sami cikakkiyar damar bautar mahalicci.

6) Samun natsuwa a duk lokacin da matar ko mijin  za su fita, ba mai yi wa wani zaton ya je holewa da 'yammata ko matan aure da sunan mutu'a ko aron al'aura.

Post a Comment

0 Comments